Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce, “Ummie na i miss you”.
A bazatar da ta bamu matuƙar mamaki mukaga ta saki murmushi tare da kai hannu ta shafa kaina. Sai kuma ta saki kuka. Ruɗewa mukai mu duka. Ƙoƙarin miƙewa nake a jikinta amma sai ta riƙeni da ƙyau, sai kawai na sake rungumeta nima ina kukan. Mun jima a haka kafin na ɗago jin kamar jikinta ya saki. Mama na kalla, ta sakar min murmushi itama tana share ƙwallar idonta. A raunane ta ce, “Tayi barci. Dan tasha maganinta bayan na gama bata abinci. Gani nayi ga sake jawo kwanon sai nayi zaton bata ƙoshi ba shine na sake zaman bata kika shigo.”
Nawa hawayen nima na share. Sai kuma na tashi a jikinta muka taimaka mata ta kwanta. Zama nayi a kusa da ita hannunta cikin nawa ina jin matuƙar farin ciki da ganinta. Sai matuƙar tausayinta dake cimun rai da zuciya dan duk ta rame min a ido alamar ciwon ya bugeta sosai wannan karon...

🩸🩸🩸🩸

“Kamar ya an sallamesu? Waye ya sallame sun?”. Ta faɗa cikin daka tsawa. Ƙanƙame jiki nurse ɗin tayi jikinta na rawa. Cike da tsorata da birkicewar Hajiya ƙaramar ta ce, “Am sorry Maa. Wlhy ni ban san wanda ya sallamesu ba, naga kawai sun fito ne amma Dr Larai ce ta musu rakiya har mota. Muma ganin haka yasa muka rakasu”.
Wani irin tashi sama jijiyoyin Hajiya ƙarama sukayi, a fusace ta sake dakama Nurse ɗin tsawa. “Get out of my side!!”.
Ai da gudu Nurse ɗin ta fice kuwa. Har neman faɗuwa take, ALLAH dai ya taimaketa ta dafe bango. Tana fita itama Hajiya Ƙarama ta fice a fusace. Sai da taje ƙofar office ɗin Dr Larai sai kuma ta gyara yanayinta cikin jan numfashi da saukewa. Knocking ƙofar tayi, aka bata iznin shiga. Dr Larai na zaune da waya a hannunta da alama akwai abinda take yi. Shigowar Hajiya ƙaramar ya sata ajiye wayar tana murmushi. Da girmamawa matsayin Hajiya ƙarama na shugaba a asibitin ta ce, “Welcome Doctor ashe kin shigo? Yanzu nake tunanin zuwa na duba kafin na wuce gida ai dama”.
Murmushin yaƙe Hajiya ƙarama tayi, tare da jan kujera ta zauna. Hakan yasa itama Dr Larai komawa ta zauna. Gaisuwa sukai a mutunce. Kafin Hajiya ƙarama ta tambayi bataga petient ɗinta ba. Kota canja musu ɗaki ne?. Da ɗan mamaki Dr Larai ta ce, “Kunyi saɓani kenan? Dan sun wuce gida. Yaron nan naku rigimamme ne na bugawa a jarida. Dan har office ɗin nan yazo ta tirkeni sai na bama yarinyar nan sallama. Babu irin son fahimtar da shi ɗin da banyi ba dan ya barta ta ƙara samun sauƙi sosai amma fir yaƙi. Wai a dinga zuwa gida ana dubata. Ko kuma ya kawota asibitin kullum. Rikitaccen mutum ne na lura mai ra'ayin riƙau gaskiya.”
Da ƙyar Hajiya ƙarama ta ƙaƙaro murmushi. Sai kuma ta miƙe tana faɗin, “Ai in dai Awwab ne ƙyaga da yawa wlhy. Shike nan bari zanje gidan mu haɗu ai.”
Murmushi itama Dr Larai tayi da faɗin, “To shike nan hakan ma yayi, amma ina tausayama matarsa dan zata sha fama. Stubborn namiji irin wannan idan baka karancesa ba wahalar zamane da su. Dan su abinda suke so kawai za'ayi tilas.”
Murmushi kawai Hajiya ƙarama tayi dan ita abinda ya dameta shi ya dameta. Cikin wayancewa dai tace bara taje taga petient sun taru. Miƙewa itama Dr Larai tayi tana tattara kayanta. “Okay nima ai wucewa zanyi. Nasan Alhaji bazai wuce ba sai na koma.”

💦🩸💦🩸💦

Tuni ganin Ummie yasa na manta da dokarsa ta kar na daɗe. Na shagala sosai da kwance mata gashinta bayan nayi sallar azhar, kanta na a saman cinyata ƙamshin turarensa ya cika ɗakin. Da farko ban maida hankali ba saboda nasan na saka wani a jikina. Sai da naji alamun mutum na nufoni sannan na farga. Shi ɗinne dai sanye cikin brown wando da ash ɗin riga mai gajeren hannu. Gashin nan a ɗaure ta can ƙasa sosai dan har yana taɓa bayansa. Saukar iska a cikin idanuna ya sani jan numfashi da ƙarfi na lumshe idanun, sai kuma duk kunya ta kamani irin wannan abin kunya haka na kure bawan ALLAH da ido. A zatona zaiyi maganar kallon sai naji baice komai ba. Sai ma hannunsa da ya ɗaura saman nawa dake tsefe kan Ummie. A hankali na ɗan ɗago na kallesa. Shima ni ɗin yake kallo. Ƙure juna mukai da ido ga hannayenmu akan Ummie.
“Kinga mamanki kin manta da umarni na ko?”.
Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa. Fuska na ɗan marairaice masa da karyar da kaina gefe a shagwaɓe na ce, “Kanta ne fa ya tsufa”.
Idanunsa ya ɗan ja luuu kamar zai lumshe sai kuma ya buɗesu tar akan nawa. Bazan iya jurar salon kallon nasa ba a yanzu dan haka na janye nawa a hankali na duƙar da kan. Shima sai bai sake cewa komai ba ya ɗan janye hannun nawa ya ƙarasa tsefema Ummien. Dama ɗayan da nake yinne ya rage. Dan bana mata kitson da yawa. Koda ya kammala cumb dake saman cinyata ya ɗauka ya taje mata kamar yanda naima sauran. Sannan ya tattare gashin cikin hannunsa. Kallona yay a hankali ya furta, “Cire band ɗin kaina, idan kin dawo kwayi kitson”.
Kai kawai na jinjina masa. Kafin a kunyace na kai hannuna saman gashinsa dake kwance luff yana ƙyalli kona wata macen albarka na zame sililin baƙin band ɗin daya haɗe da gashin sai ma ka ƙura ido kake ganewa. Koda yaushe kuma zakaga da irinsa yake ɗaure gashinsa. Ina gama zarewa gashin nasa ya tarwatse a baya. Sai kawai na shagala da kallonsa har sai da naji saukar hannunsa cikin nawa zai zare band ɗin sannan na dawo hankalina. Duƙar da kaina nayi kunya duk ta isan. Yau dai na kula kamar ina sakin layi da yawa. Sai dai yanda ya basar yasa na ɗan ji nutsuwa. Yana gama ɗaure mata ya gyara mata kwanciya shima ya miƙe yana faɗin, “Lets go”.
Dole na mike a hankali ina gyara mayafin jikina. Wani kallo ya dinga bina da shi daga sama zuwa ƙasa. Sai kawai nai gaba da sauri. A falo muka samu mama Balki ashe bata fita ba. Tana ganinmu ta saki murmushi da faɗin, “Har kun fito.” a kunyace na jinjina mata kaina. Shi kuma ya sanar mata akwai baƙi a gidan zuwa anjima zai kira wayarta tazo su gaisa. Ya kuma roƙeta ta rufe ƙofar falon ko Paah ne yazo karta barsa ya shigo. Maganar tasa ta ɗan ban mamaki, har na kasa haƙuri sai da na kallesa. Amma sai ya ɗauke kansa kamar ma bashi ne yay maganar ba...

A falon ƙasa muka ci karo da su Azizat. Tunda muka fara sakkowa duk suka miƙe tsaye tamkar waɗan da ke cikin shock. Dan su duka bakunansu a buɗe suke kallonmu idan ka cire wata farar budurwa da ban sani ba a gidan dake zaune ita bata tashi ba. Sai dai itama ta zuba masa ido kamar zata cinyesa. Kallo ɗaya na musu na ɗauke kaina. Kamar yanda shima naga baima nuna yasan da zamansu ba ya wucewarsa. Ina jiyo Malika na yin ashar a hankali. Ban san miya basu mamakin ba. Ganina a gidan? Ko kuwa ganina tare da shi?. Oho dai can ta matse musu. Dan ni su duka ukun a yanzu na shirya duk wadda tace zata shigo sabgata wlhy sai na mata zanen yarabawa a fuska.
Koda muka iso ƙofar shiga sashen nasa sai da na tsaya na ɗan gyara mayafina sannan na bisa dan shi har ya riga ya shiga. Da Hayatu na fara cin karo tsaye a ƙofa yana waya, muna haɗa ido ya wani rissinar da kai. Harara na balla masa na wuce ciki abuna. Bana ganin fuskar waɗanda ke a zaune, sai dai haka kawai zuciyata ke wani irin sanyi da jikina. Gani nike kuma kamar na sansu. Tamkar wadda ƙwai ya fashema a ciki na ƙarasa sosai cikin tsakkiyar kujerun ina sake yin sallama ƙasa-ƙasa batare dana kallesu ba. Turus na tsaya zuciyata na bugawa da ƙarfi sakamakon jin muryoyin da ko'a cikin barci bazasu taɓa iya su ɓace min ba. Jikina har rawa yake na ɗago dan tabbatarwa. Sai kawai naci karo da fuskar Yaya Musaddiq da ke faman min murmushi da ta Hafizzullah. Yanzu kam sosai rawar jikina sake bayyana tayi, ga lips ɗina na rawa kamar yanda hannuna ke rawa ina son nunasu amma na kasa........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚_


*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

........

......Cikin rawar jiki na nufesu da wata irin sassarfa na faɗa jikin Yaya Musaddiq na saki wani irin kuka da ni kaina bamma san na minene ba, sai kuma na jawo hannun Hafizzullah shima na haɗasu na rungume. “Oh oh Kandala na ashe bata canja hali ba har yanzu jama'ar ALLAH”. Yaya Musaddiq ya faɗa cike da tsokana yana ɗagoni a jikinsu. Cikin dariya da sharar hawaye Hafizzullah ya ce, “ALLAH Yaya bata canja ba sai ma abinda ya ƙaru.” hannu nasa a kansa na dungure nima ina sharar hawayen na ce, “Magulmaci kana nan da hali”.
Dariya muka sanya mu duka ukun. Kafin na sake kamo hannayensu cikin nawa su dukan. Cikin shagwaɓa na sake fashe musu da kuka ina faɗin, “Ya akai kuka zo nan? Waye ya kawoku? Yaya wlhy nayi kewarku, kullum da dare sai nayi kukan rashinku. Yaya dan ALLAH kuce kun dawo nan zaku zauna tare dani?”.
Murmushi kawai yaya Musaddiq keyi, sai Hafizzullah ne cikin dariya ƙasa-ƙasa ya ce, “Sai dai idan zaki bimu mu koma Kano. Dan ni ban wani yarda kinyi kewarmu ba Addah. Jibeki kinyi wata fresh kamar ɗanyan nama sabon yanka. Ga ƙiba kin haɗa kamar ke kaɗai ake ma tirka a gidan. Kai gaskiya ba wani kewarmu ke dai gidan miji daɗi kinma manta da mu”.
“Yaya ka ganshi yana tsokalana ko?”. Na faɗa a shagwaɓe batare dama nasan mi nake ba. Dan wlhy duk jina nake a ruɗe kamar a cikin mafarkin dana saba. Dana farka zan nemesu na rasa ne. A hankali Yaya Musaddiq dake murmushi har yanzu yana kallona kawai ya kai hannu ya share min hawayen yana faɗin, “Manta da shi, har kin manta da halin auta ne ma. Bayan da yaji zanzo badashi ba ya zauna ya dinga rusa kuka harda birgima a tsakar gida wai shi idan baizo yaga Addarsa ba zai faɗa rijiyan gidan su Mama Sadiq maƙotanmu”.
Dariya na ƙyalƙyale da shi, tare da kai hannu kan fuskar Hafizzullah daya kwaɓe ta cike da shagwaɓa naja kumatun, sai kuma na dunguresa da faɗin, “Ashe dai yaron nan na sona har yanzu”...

Duk abin nan dake faruwa yana zaune a falon. Binsu kawai yake da kallon ƙasan ido wani abu na masa motsi a zuciya. Daka gansu kaga waɗanda sukai matuƙar shaƙuwa da juna, suke kuma tsananin so da ƙaunar juna. Wani irin lumshe idanunsa yay murmushi na suɓuce masa a bazata. Hoton Fahad ne ya fara masa gizo a cikin idanunsa dake rufe, da sauri ya buɗesu yana cizar lips. Dan wani irin zafi zuciyarsa ta fara masa. Ƙoƙarin ture tunanin dake neman kutso masa a zuciya yayi ya sake maida dubansa kansu. Hakan sai yay dai-dai da Samraah ta juyo suka haɗa ido kuwa. A mamakinsa sai ta sakar masa murmushin da har ya bayyana haƙwaranta. Sai ya samu kansa da lumshe idanun da buɗewa. A hankali ya furta, “Dama haka ake tarban baƙi da surutu?”.
Murmushin ta sake sakar masa tana miƙewa daga durƙuson da tayi a gabansu. Muryarta kanta na nuna alamun farin ciki ta ce, “Ya Awwab ALLAH daɗine naji kamar ya kasheni. Ashe dama kasan yan gidanmu amma baka tafa faɗa min ba? Nagode, Nagode kaima ALLAH ya faranta maka fiye da yanda ka faranta min”.
Kansa ya ɗan girgiza yana sakin murmushin daya kasa riƙewa. Sai kuma ya maida kallonsa ga su Yaya Musaddiq da suma ke murmushin, muryarsa da alamun tausasawa ya furta, “Bara na ɗan je bazan jimaba zamu dawo. Please ku ƙara cin abinci sosai nan ɗin gidanku ne.”
Faɗaɗa murmushin yaya Musaddiq yayi, cike da girmamawa ya ce, “Mun gode sosai ranka ya daɗe. ALLAH ya saka da alkairi”.
“Don't say me thanks you or ranka ya daɗe ɗin nan. You are my brothers. By now we are family ne okay. Nine zan kiraka Yaya, sai kuma small kiddo Hafiz a gefe”.
“Yes babban Yaya”.
Cewar Hafizzullah cike da farin ciki. Yayinda Yaya Musaddiq keta murmushi dan shi sake ganin al'amarin yake kamar a mafarkinsa. Duk da bayanin da Hayatu yay masa tare da Maash ɗin kafin shigowar Samraah zuciyarsa ta kasa daina mamakin komai. Cikin jinjina kai ya furta, “Ni ne ya kamata na kiraka Yaya, kaga dama ni kaɗaine banda Yaya. Yanzu kuma na samu. I am so happy inada wanda idan nayi ba daidai ba zai tsawatar min, inada wanda nima zan yima kuka a jiki. Ka mana komai na rayuwa. Daba dan kai ba da yanzu ban san a wane hali muke ba, dan in har wani abu zai taɓa rayuwan Samraah mu dukanmu tamu rayuwar zata girgiza ne. Saboda mu duka biyun itace rauninmu. ALLAH ya faranta maka fiye da yanda kai mana”.
Hayatu da Maash ɗin suka amsa da Amin. Dan gaba ɗaya ma Maash ɗin ya rasa abin faɗa. Idanu suka haɗa da Samraah dake kallonsa tana murmushi. Cikin ɗan ƙanƙance cat eyes ɗin nashi ya ɗage gira sama da ɗan ɗage kai alamar kallon fa.

Samun kaina nayi da jin kunya, dan haka na duƙar da kan nawa kawai ina murmushi. Dan har ƙasan raina ban taɓa jin ya sakani a farin ciki irin na yau ba. Ji nake kamar naje na rungumesa. Amma ina jin kunya. Ɗagowa nayi na ɗan kalli Hayatu, shima a karo na farko na ce masa, “Thanks You”.
Murmushi shima ya sakar min yana yin ƙasa da kansa. Sai kuma ya jinjina kansa da faɗin, “Nine zan gode ai Aunty na”. Yanzu kam Harara na balla masa ina ɗauke kaina da murguɗa baki. Sai ko muka sake haɗa ido da ogan nasa. Ɗauke fuskata nayi gaba ɗaya daga sashensu. Sai da naji Hayatu nama su Yaya Musaddiq sallama akan sai sun dawo sannan...

🌿🌿🌿🌿

A hargitse Hajiya ƙarama ta koma office ɗinta. Kofar ta kulle dan bata buƙatar ganin kowa. Kai-kawo ta shiga yi cikin Safa da marwa. Kafin ta jawo waya ta shige cikin toilet. Sau uku tana kira amma ba'a ɗaga ba. Kanta ta dafe cike da takaici. Yanzu haka yana can yasha giyar tashi yana shaɓar barci. “Motsoww” taja tsaki tare da fitowa. Wayar ta wurga saman desk ɗinta, itama ta zube a kujera tana mai dafe kai. Ji take yana wani irin sara mata. So take tai magana da wani ko zataji daɗi. Amma dawa ɗin zata yi. Da sauri ta sake rarumo wayar ta danna ma Jannifer kira. Bugu ɗaya kuwa ta ɗauka. Jin muryarta wani iri ta sata jan tsaki. “Malama dalla koma dawa koke tare ta tashi taba mutane waje magana zamuyi.”
“Bara dai ni in tashi”.
Jannifer ta faɗa tana ƴar shaƙiyar dariya. Tsaki kawai Hajiya ƙarama tayi batace komai ba. Sai da Jannifer ta sanar mata ta fito tana jinta sannan ta sake jan tsaki da fara magana. “Jannifer wai ina kika samo yarinyar nan ne? Wlhy tunanina gaba ɗaya nan birkicewa yake a wannan gaɓar?”.
Da mamaki Jannifer ta ce, “Kamar ya? Wani abu ne ya sake faruwa?”.
“Miye ma bai faruba. Yanzu nan nazo asibiti na samu wai banzan yaron nan Awwab yazo ya ɗauke yarinyar nan sun wuce gida?”.
“Tofa babbar magana. Wai Maash kike nufi?”.
“To in ba shiba waye zaima mutane wannan gadaran”.
Dariya ce ta kufcema Jannifer, sai da tayi mai isarta kafin da ƙyar cikin dariyar ta ce, “Kai amma yaron nan ƙwallon shege ne wlhy. I like him style wlhy. Komansa yake baya tsoron uban kowa. Ya taka na waje kuma na gidan bai barku ba ciwon kan da gwale-gwale yake baku. To wai kodai son yarinyar nan yake ne? Abinfa da mamaki wlhy, dan ni bammaga wani damuwa a tattare da shi akan abinda ya aikata ɗin ba. Ka ɗirkama yarinya fyaɗe amma ka dinga abu It's like you don't care, I really like this boy's style.”
“Mtsowww!! Jannifer ban son shirme. Ina miki maganar serious kina mun wani soki burutsu.”
“Ehm sorry Maa. ALLAH abunne ya ban dariya ya kuma burgeni. Samun irin stubborn mazan nan ba ko inaba. A Abuja nasan yarinyar ni gaskiya......” ta kwashe komai data sani akan Samraah ɗin tun daga haɗuwarsu da abinda ya faru kuma duk ta gaya mata”.
Cikin damuwa Hajiya ƙarama ta ce, “Amma kema kinyi ganganci da baki san labarin nata ba”.
“To banda abinki Hajjaju mizai sa na damu da labarinta. Ni fa dama irinta na fita nema. Sai kuma na samu miya rage min. Kaiwa na ɗako nazo na samu kuɗaɗena ai.”
“Mtsoww!! Aikin kenan. To ita kuma Mashi'a ya akai ta zaɓi yarinyar? Bayan nasan idan kin kawo yara sai sunyi fin wata biyu ma kafin ki saida su. Musamman irinta ma ai baki badata a masu aiki?”.
“Hummm ki bari kawai, wlhy kuɗaɗe kawai na gani. Dan an samu kuskure ne dana aika a kira min su ta biyosu. Nace ta koma Alaja Mashi'a ta ganta ta nace ita take so harda ninka min kuɗi. Ni kuma kawai naga bazan iya ba na sallama. Dan nasan ko ƙasar waje na kaita ba lallai na samu abinda na samun ba a wajenta. Kuma ina ma jin nauyin Alaja Mashi'a wlhy. Kin san dai ba wannan karon ne na farko dana fara samo mata masu aiki ba. Tunda kusan yaran gidankun nan duk a wajena aka amshesu mafi yawanci kuma itace ke zuwa da ɗauka musamman ma masu kula da Hajiya Babba.”
Numfashi Hajiya ƙarama ta furzar, dan tasan gaskiyar zance Jannifer ke faɗa mata. Mashi'a tana kallon Jannifer ne kawai a mai kawo ƴan aiki. Kuma zama ta iya cewa itace ta nuna mata gidanta a lokacin da take neman masu aiki da zata wuce da su can Germany, shine take faɗa mata gidan Jannifer ɗin. Tunda ta ɗauka wancan yaran biyu ta wuce da su taji daɗin zama da yaran sai yazam duk sanda ta shigo Nigeria takan ɗaukama Hajiya Babba masu kula da ita. Ko idan taji wasu nason masu aiki takan musu hanya. Da yake itama halin Maash ne da ita yanzu haka yaran data ɗauka su biyu duk sunyi karatu a can. Ɗaya a cikinsu ma ta kusa aure da ƙanin mijin ita Mashi'a ɗin. Ƙaramin tsaki taja da ture batun Mashi'a ta koma wanda zai amfaneta. Amma ba komai, ita Awwab ɗin ma ya saukaƙa mata aiki, a gidan ma wasan zaifi armashi tunda yarinyar a sashen masu aiki take. Zata dakata ta dawo sashenta da kwana, ta nuna saboda abinda ya faru ta ƴanta yarinyar. Zata nema mata makaranta kawai a wata ƙasar daga haka shikenan ta gama samun cikar burina..........✍️





_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_


.....Suna gama ficewa cike da zumuɗi na maido hankalina kansu Yaya Musaddiq. Ƙoƙarin zama nake Hafizzullah ya ce, “Wlhy ji nake kamar a mafarki. Wai aunty Samraah kece matar mutum kamar Maash. Ya ALLAH Maash fa. Wai dan ALLAH Adda yaya akai haka ta kasance? Kodai dama ke kin san wa kika aura? Dan wlhy duk da sun sanar mana komai yanzu kuma a gabana komai ta faru lokacin auren sai nake ganin kamar dama dai kuna son junan ku ne ke da shi.”
Harararsa na ɗan yi, sai kuma na koma kusa da Yaya Musaddiq na zauna ina sauke ajiyar zuciya. “Yaya dan ALLAH mi sukace muku? Sannan dama kaima baka san shi bane?”.
Murmushi sosai Yaya Musaddiq yayi yana kallona. Sai kuma ya jinjina kansa. “Samraah wlhy har yanzu ni kaina ina a cikin yanayin da Hafizzullah ɗin yake ciki ne. Dan harga ALLAH ban taɓa sanin Maash ne mijinki ba, taya ma zan kawo hakan a raina to. Bama ni kaɗai ba, hatta su Abba babu wanda yasan wa kika aura. Koda aka ɗaukeni aiki a companynsa na amsa ne saboda dalilai uku. Na farko dai bazan iya bijirema umarnin ogana ba. Saboda yana treating ɗina like uba. Ko Abba dake ƙanin mahaifiyata muke a hannunsa tun bamu san kammu ba bana jin ya damu da tarbiyyata kamar yanda ogana ya tsaya a kaina. Hakan yasa babu abinda zai ce nayi a rayuwar nan naƙi yinsa sai dai ina na saɓama ALLAH ne ko cutar da wani. Wannan kam bazan masa biyayya ba. Na biyu maganar video ɗin nan. Na yarda zanyi aiki a companyn da tunanin ko zan fahimci wani abu dan na sanki da naci akan abu, komai tsahon lokaci da za'a ɗauka bazaki taɓa barin maganar video ɗin nan ba. Na uku amsar aikin kamar samun wata hanyar cigaban rayuwa ne yazo mana mu duka. Dan bamu

Please Login or Register in order to submit comment