Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

💢🌟💢🌟💢🌟💢

Kwanaki na biyu kenan da dawowa gida. Kwanaki biyu kuma kacal ya rage ɗaurin aurena. Dan zuwa yau har baƙin kusa sun fara isowa musamman dangi na jiki sosai. Ga Aunty Zakiyya ta duƙufa min gyaran jiki da ɗuramin abubuwa. Niko dana faki idonta sai na zubar dan bana sha sosai. Abinda zai baku mamaki duk da haramin biki da gida ya fara ɗauka ga masu gidan babu wani alamar motsi irin na biki a tattare da su. Dan hatta da abinci da aka girkama baƙin dake a gidan yau Yaya Musaddiq ne ya kawosa. Suko su Gwaggo suka girka batare da sun bi takan Mum daketa faman ɗacin rai ba. Shi dai Abba saboda su Gwaggo Gudidi yana ɗan nuna alamar damuwa da shirye-shirye. Sai dai fa bana aljihu ba na gayyatar mutanensa kawai, sai kuma takurama Yaya Musaddiq da yake ta bayan fage akan kuɗin kayan ɗakina da wanda za'ai hidimar abincin biki. Shiko Yaya Musaddiq nata masa zame-zame. Sai a yau ya fito fili ya shaida masa karya damu shi ya riga da ya kammala komai. Dan hatta da kayan kitchen ɗina ma a tanade suke tuni. Hakama kayan gado kafintan ya jima da kammalasu duk da Mansoor yace kar ayi shi baibi ta nasa ba. Wannan zance ya ƙona zuciyar Abba matuƙa. Amma ya gagara magana kodan mutane dake cike a gidan, yasan fitowar zancen babban abin kunya ne a garesa musamman a wajen danginsu dana ɓangaren mahaifinmu.
Ban gayyaci wasu ƙawaye ba dan banda su, amma a ranar da yamma sai ga su Ruƙayya ƴan Office dinmu da gayyar ƴan ajinmu na islamiyya. Naji daɗin ganinsu sosai, dan ko kusa banyi zato ba. A bakinsu na fara jin ƙananun maganganu akan rashin kawo kayan da zanyi amfani dasu na biki da Mansoor ya ce sai daga baya dan ba'a saka ɗinkakken kaya ko ɗaya a lefen ba, kuma kowa na saka ran yau ne za'a kawo ɗin saboda kamu da ake shirin yi gashi babu kayan dazan saka. Amma har yamma shiru kake ji. Gashi yanzu banda waya a hannuna ko ɗaya. Rabona da Mansoor kuma tun jiya da dare. Koda yake nice nace yau kar yazo, kai daga jiya ma bazan sake yarda mu haɗu ba sai a gidansa. Shiko ya yarda da hakan acewarsa zai gwada yaga ko zai iya. Nayi tunanin kiranshi amma zuciyata ya ƙwaɓeni game da hakan, dan haka bance da su komai ba na haɗiye zancen a raina har sai bayan sallar isha'i da nasan Yaya Musaddiq ya dawo gida sannan na lallaɓa ɗakinsa na samesa, a wajen kamu kuwa Aunty Zakiyya ta samo kayan dana saka kawai........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_

___________

_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_


https://chat.whatsapp.com/Cce1etNkvVKCBlgSqXa4Ek

___________


........Kai tsaye ɗakin Yaya Musaddiq na nufa. Bayan na gaishesa ya ɗan tsokaneni nai masa zancen da naji ana tsogumi ɗazun a kai. Murmushi yay min da faɗin, “Kandala ƙyale batun mutane da halinsu. Dan su basu iya komai ba daman sai gulma kawai. Yanzun nan babu jimawa muka rabu da Mansoor ɗin ma, dan munje can gidan nasa ne da kafintan da yay kayanki saboda zasu kaisu da sassafe gobe in sha ALLAHU. Ya kuma min batun kayan sai gobe in sha ALLAHU zasu kawo wata ƙanwar Mamynsu ce da zatazo da ga Dubai a yau da dare ake jira dan akwai wasu kaya a hannunta, amma shima yana cikin damuwar rashin kawo su shiyyasa ma ya kasa neman ko Hafizzullah a waya ya haɗaku dan kunyarki yake ji”.
Ajiyar zuciya na sauke a hankali. Dan nama san ƙanwar Mamyn tasu, yasha bani ita muyi waya. Murmushi yay min yana kai ma kaina rankwashi da faɗin, “Sam yanzu Kandala baki da kunya. Yanzu ni kike zuwa tambayar batun kayan aurenki ma”. Hannu na saka na rufe fuskata ina dariya. Shima dariyar yake yi. A dai-dai nan Hafizzullah ya shigo ɗakin da sallama. Dan tun washe garin da aka ganni yazo gida dama. Ledar hannunsa na warce ina faɗin, “Zaga gari mi kuma ka samo anan?”.
Ƙoƙarin warce ledar shima yake a hannuna yana hararata. Ban yarda masa ba har sai da na buɗe. Ganin awara yasa na taɓe baki ina miƙa masa. “Oh oh kwantar da hankalinka ashema naman talaka ce”.
“Oho dai, kema naga ci kike”.
“Ai ni in naci ba komai bane. Amma kamarka dai saurayi mai hurama ƴammata hanci abin kunya ne. ALLAH yau da ina da waya saina ɗauki hotonka nasa a status ƴan matanka sun gani”.
Dariya ya sanya da yimin gwalo, ya ce, “Ai sai ki samama kanki lafiya tunda baki da. Kuma sai na zuga Yaya Mansoor kar ya saya miki waya har sai kin shekara a gidansa”.
“ALLAH sarki jiki duk baƙin ciki su Hafizu. Aiko zakasha mamaki, kafin rana ita yau kasa a ranka na mallaki waya”. Na ƙare maganar ina kai masa rsankwashi a kansa.

💥💫💥💫💥💫

Kamar yanda Mansoor ya faɗa hakance ta kasance. Dan washe gari misalin sha biyu na rana ƴan kawo kayan nan suka iso gidanmu su uku. Zuwa lokacin baƙi sun ƙaru. Dan wasu matan ma a cikin ƴan Gwarzo ma sun iso. Tuni Aunty Zakiyya ta shiga maƙwafta tai kiransu dan Mum taki aikawa a kira kowa aiki. Sai ma yi take kamar wadda ta ruɗe. Dan ma ƙanwarta na tare da ita tana saitota. Baby kam ban san ina ta tafi ba dan tun jiya da yamma ban sake ganinta a gidan ba kuma. Waɗan nan kaya sun matuƙar girgiza sukata. Dan da gasken gaske Mansoor da ahalinsa sun nuna bajinta. Duk da ba fariyya akayi ba komai na nan dai-dai misali amma kuma na bajinta da zai tabbatar maka an kashe kuɗaɗe sosai. Dan komai acan-acan ko maƙiyi yasan kaya sunyi ga kuma kayan lefe da dama sun riga sun kawo.
Har aka gama karɓar kayan ni dai ban ko leƙo ba sam. Sai da dangin Mansoor suka wuce sannan aka maido kayan nan ɗakin da muke da su Gwaggo Gudidi sannan su Asiya suka tsareni sai na gani harda Aunty Zakiyya. Na ɗan kalla sama-sama na rufe akwatin ni dai. Har raina ina sake jin kima da girman Mansoor matuƙa dama ahalinsa gaba ɗaya....


💦💦💦💦💦💦💦

“Aunty dan ALLAH ki kwantar da hankalinki ni banga aibun yarinyar nanba sam wlhy. Ga danginta mutanen kirki. Karfa kiga irin tarbar da akai mana ta girmamawa wlhy.”
“Humm Anesa ni fa bance tanada aibu ba. Amma ya kamata ku fahimci abinda nake nuna muku. Yanzu dan ALLAH da kikaga yarinyar tayi kama da wadda akai kidnapping na tsawon sati biyu da wasu kwanaki? Nafa fiku son yarinyar nan, kuma har yanzu ina jin sonta a raina”.
“Aunty wlhy ni ban ganta ba.”
“Humm to ai naso ki ganta da kin tabbatar. Amma al'amarin da mamaki ace ai kidnapping yarinya budurwa ƙyaƙykyawa kamar wannan wai ta tsallake tarkon namiji. Sannan kuma basu nema kuɗin fansa ba saboda sun sami abinda yafi kuɗin kenan. Ya kamata kowa ya gane maganar matar kawunta da abar a duba ce fa. Dan dolene ɗayan biyu a samu ɗaya. Kodai da ƙafarta tabi wanda suka sacetan nan zuwa wani hotel ko guest house. Ko kuma wanda sukai kidnapping ɗin nata sun samu abinda yafi kuɗi a jikinta. Wai Kinga kuwa yanda ta ƙara wani fresh na haske da laushin fata tamkar wadda ke rayuwa a ac. Ai bana jin ko kafin a sacetan jikinta yay wannan luf-luf ɗin. Amma da yake yaron nan ya makance da shirme shi ko sau ɗaya bai zauna yayi tunanin komai ba. Na rasa mike damun kan Mansoor ne. Ga ubansa shima yama ƙi ya sauraran balle ya gane abinda nake nufi. Kema kuma gashi kina nuna bazaki fahimceni ɗin ba”.
“A'a Aunty, ba fahimtarki ne bazanyiba nikam. Abinda kawai nake son ki duba bakin alƙalami fa ya riga ta bushe. Tunda gashi yau har sauran kayan lefe mun damƙa musu. Sannan Mansoor ya sanar min sun kai kayansu can gidansa wasuma a dangin nata na jerensu yanzu haka. Sannan Aunty gobe ne fa ɗaurin aure. Kuma kin ce Abban Attahir ma yaƙi fahimtarki balle ma shi Mansoor ɗin da kin gagara tunkararsa da batun, to tayaya kike tunanin zamu iya wani abu a ƙurarren lokacin nan?”.
“Zamu iya kuwa Aneesa. Dan anma zauna a filin ɗaurin aure ya watse ballema wannan da sai gobe. Mansoor da kike gani sam bashi da wani isashen wayo. Wlhy koda yasan yarinyar nan bata ƙwarai bace zai iya shanyewa saboda son da yake mata na masifa da ni sai a yanzu ma zuciyata kemin wasuwasin bana lafiya bane. Dan abun yayi yawa wlhy. Wace soyayyar haukace haka kamar wani labaran littafin hausa. Ku shaida ne nima naso yarinyar nan a baya, dan ina gaba-gaba wajen shawo kan Abban Attahir harya amince da auren nan duk da fama da aka sha sosai saboda dagewar da yay akan sai Attahir ya fara aure sannan Mansoor ɗin yayi. Amma magana ta gaskiya zancen matar kawunta na jiya ya dawo dani a hankalina. Sannan ganin yarinyar a cikin hayyacinta fes saima ƙyau data ƙara shima ya tsaya mun a rai. Dan haka shekaran jiya nace Mansoor ya kamata ya nema likita yasa a mata gwajin ciki amma yaron nan sai ya koma min wani kalar tausayi kamar zai yi kuka, yana faman roƙona nabar wannan maganar dan ALLAH kada wani yaji, shi yasan wacece Samraah. Da ace wata matsala ta faru da ita acan sai ta faɗa masa bazata munafuncesa ba. Kajimin yaro fa dan ALLAH”.
“Humm Aunty kar kiga laifinsa. Dan dama abin da kamar wuya ace ya fahimta kai tsaye. Amma dai kam al'amarin akwai ɗaure kai”.
“Bana wasa ba ma. Inda shi wani ne dan ALLAH basai ya haƙuraba, idan ma ya matsune yay auren dole a goben basai a ɗaura da Waleeda ba. Nasan dai Daddynta bazai ce komai ba wlhy”.
Idanu sosai ƙanwar tata ta waro waje. Sai kuma ta ɗan murmusa da faɗin, “Kai Aunty wannan ai babbar magana ce. Ni dai abinda nake gani anan kawai addu'a ce tafi dacewa. Sannan kisa a ranki in sha ALLAHU abinda zuciyarki ke ayyana miki bazai zama hakan ba.”
Baki kawai Mamy ta taɓe batare data sake cewa komai ba.....

💢💫💢💫💢💫💢💫💢

*_RANA BATA ƘARYA BILYN ABDULL. MASU IYA MAGANA SUN CE SAI DAI WAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA_*. Na yarda da batun masu hikimar zance. Domin kuwa nima da kaina na yarda wannan rana tawace kam. Sannan in har Mum na amsa sunan uwa a gareni to taji kunyar kuwa. Dan halayyar da take nunawa yasa dangin mahaifinmu suka gagara haƙuri sai da suka yayyaɓa mata magana. Dan har Kawu Lurwanu na iƙirarin mata dukan tsiya. Yaya Musaddiq ɗin da take gani aba komai ba a gareta ne yayta basu haƙuri da kareta har aka samu ƙurar ta lafa. Gida ya gama cika danƙam da mutane. Dangi na kusa dana nesa sun nuna halacci. Ga abinci kala-kala anyo daga Gwarzo batare da an zaman jiran sauraren na nan gidan Abba da kunya ta sakashi kawo buhun shinkafa a jiya da dare ba, sai wasu ƴan kayan miya cakwat da nama a baƙar leda abin zakkunya dai.
Kafin goma na fito shar dani a amaryata. Ga ƙunshin da ƙanwar mijin Aunty Zakiyya ta rangaɗa min a daren jiya ja da baƙi yay masifar fitowa kamar kaci. Duk da gyaran ƴan kwanaki akai mun na fito fes dani kamar fure a tsakkiyar lu'u-lu'u. Wani cotton lass ne a jikina lemon green ɗaya daga cikin kayan da suka kawo jiya aunty Zakiyya ta ciro min. Dan duk kayan da zanyi hidimar biki dama sai da Mansoor ya ɗaukan mukaje tela ya gwadani tun kusan wata biyu da ya shige. Aiko ɗinkin yay masifar zaunamin a jiki. Sai wata stones sarƙa mai ƙyalƙyali da walwali tamkar diamond na gaskiya. Awarwaraye zobba da komai sunji a hannayena. Ta sama gashina da a daren jiya shima yasha wanki daga ƙanwar mijin Aunty Zakiyyar dai dan aikinta kenan shima sai ƙyalli da ɗaukar idanu yake. Bayan ta gama tsaramin kwalliyar da naita zame-zame a farko aka naɗa min ɗauri na azo a gani. Nan take hasken camara na waya ya shiga kai-kawo a kaina. Nanfa wasu sukace sai sun turama ango fa. Ciki harda Hafizzullah. Ban tanka musu ba face murmushi kawai da nake yi........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*







*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_

____________

_Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me hamsin me dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata mai albarka..._

_idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo unguwar tarauni dake garin Kano sai akira number opay dincan dake sama_

_zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._

_kofa a bude take ga duk Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_

______________


......Daga can tsakar gida kam taro yay taro gida ya kacame da hayaniya irin ta biki, anan ɗakin ƙawayena na zagaye dani. Wasu na hotuna wasu na kwalliya, wasu na hirarsu akan batun dinner da za'ayi bayan an kai amarya. Dan can gidan su Mansoor ɗinne suka shirya. Kiran da Yaya Musaddiq yazo yamin ne ya sakani saka gyale na rufe har fuskata. Shine ya kama hannuna har falon baƙi. Tunda muka fito kuwa gidan ya sake ruɗewa da buɗe-buɗe. Ni dai kaina na ƙasa a cikin gyale dan haka kawai sai naji ina jin kunya kowa.
Ban ida daburcewa ba sai da muka isa falon baƙi. Dan ganin kaf kawunaina na ɓangaren uwa da uba harda Abba. Sai gwagganni da innoni suma dai duk suna nan na kusa sosai. A tsakkiyarsu Yaya Musaddiq ya kaini ya zaunar ƙasan carpet. Shima sai ya nema waje ya zauna.
Kawu Musa ne ya fara min da nasiha mai ratsa jiki. Kafin sauran ma su dinga karɓa ɗaya bayan ɗaya. Daga baya suka koma faɗa da gargaɗi, yayinda ni kuma nike sharɓan kuka ta cikin gyale. Dan babu abinda ya tadamin hankali sai jin muryar Yaya Musaddiq na rawa alamar karaya sanda yake min addu'ar zaman lafiya a gidan aurena. Abba ma dai yamun tasa a taƙaice, daga baya kiran wayarsa da akai ya nema excuse ya fita, da alama kuma kiran da akai masan nada matuƙar muhimmanci ne. Dan naga sai da ya fara magana da Kawu Musa suka miƙe tare suka fita. Fitar tasu bai hana iyayena cigaba da mun nasiha ba, sai da suka gamsu sun min yanda suke buƙata kafin suka sallaman Inna Hauwa ta kamani ta maidani ciki, dan mazan zasu wuce massalaci ne daga can kuma za'a ɗauro aure. Dole sai da aka sake min kwalliya bayan nayi sallar azhar saboda na ɓata fuskar dan kukan da nasha. Kaya na canja zuwa wata shadda da taci uban aiki da stones sai walwali take yi. Ga ƙamshi irin na amare ƴan ƙwalisa ina zubawa. Acan ƙasan zuciyata kuwa jina nake duk wata iri kamar yanda aka san duk amarya da shiga irin wannan yanayin a irin ranar nan. Lokacin da ƙarfe biyu ke cika maza suka fara dawowa alamar an ɗauro auren gabana sai ya shiga wani irin luguden daka da sauri-sauri. Wani irin tsoro da fargaba na ratsa min cikin ɓargo da jijiya har ina jin wani kalar sanyi-sanyi duk da kuwa uban zafi ake zugawa a gari kasancewar watan azumin Ramadan na kawo jiki. Ƙawayena sun shiga min shaƙiyanci da buɗa a saman kai, sai na samu kaina da sakin hawaye masu zafin gaske da ban san dalilin yinsu ba. Shin murna da farin cikin mallakar matashin saurayi ƙyaƙyƙyawa ɗan ƙwalisa mai cikar kamala da dattako irin Mansoor ne, ko kuwa fargabar rabuwa da ƴan uwana biyu ne da ke a cikin tarkon wancan terror ɗin. Bily a lokacin sam na kasa ganewa. Na gagara banbance komai a yanda ya dace na fahimcesa. Sai ma wani sabon bugun zuciyar da na sake ji sakamakon shigowar aunty Zakiyya kamar a firgice tana kiran Gwaggo Gudidi data shigo tana miƙamin fura a kofi da aka dama wai na sha. Koda Gwaggo ta tambayeta lafiya, sai tace mata su Kawune ke kiranta kuma sunce tai sauri dan kamar dai akwai wata matsala. Da saurin kuwa ta fita alamar itama tana a cikin ruɗanin ne..
Na cigaba da zama kamar butun butumi a tsakkiyar ƙawayena daketa hotuna abinsu batare da su sun fahimci kamar akwai abinda ke faruwa ba. Muna nan dai shiru hayaniyar gidan na sake ƙaruwa alamar mutane na sake cika gidan ƙananun magana suka ɗan fara fitowa. Sai dai anƙi a fito da komai a fili ana ta son basar da mutane dai. Abinda ya ɗan fara tsayamun a rai shine rashin zuwan Mansoor gidan. Dan a burikanmu akwai zuwa hotuna bayan ɗaura aure da yace zasuyi shi da abokansa da kuma ni da ƙawayena da ƴan uwana. Amma dai zuciyata nata tausata akan masa uziri, dan maybe mutane sun masan yawan da hakan bazai yiwu ba ya cika wannan alƙawarin. Wannan tunanin yasa na danne zuciyata na ajiye wannan batun a gefe.
Isowar masu kiɗan ƙwarya bayan sallar la'asar yasa Inna Hussaina zuwa ta fita dani a ɗakin ni da ƙawayena. Sosai gidan ya cika da mutane har sai da naji ƙwalla ta cika min ido. Dan ban san munada taron dangi har kamar haka ba da zasu iya nuna wannan soyayyar garemu a irin wannan ranar. Ko a wajen kiɗan ƙwaryar ma duk da ba rawa nake ba tsaye kawai nake tsakiya ƙawaye na da ƴan uwana masu rawar zagaye da ni sai da dinga shigowa ana min liƙi, wasu kuma sukanyi hoto dani a waya harda masu video. Kusan ƙarfe biyar sai ga Gwaggo Magajiya riƙe da hannun Yaya Musaddiq da Hafizzullah wai sai sun min liƙi. Kallo ɗaya na musu su duka biyun na fahimci sunyi kuka. Dan idanun Yaya Musaddiq jajur suke. Na Hafizzullah kuwa har sun kumburo saboda shima fari ne kamar ni, dan mu biyun munfi Yaya Musaddiq haske. Hankalina ne ya tashi a take nima idanuna suka ciko da ƙwalla ina binsu da kallo. Amma sai suka ƙi yarda mu haɗa ido sai liƙi da sukemin kawai ana ihu kawunansu a ƙasa suna murmushin da ni kaɗai na fahimci na yaƙe ne. Duk yanda naso riƙe kukan nawa hakan ya gagara, bamma san sanda na riƙo hannayensu su duka ba cikin nawa. Dole suka kalleni a tare. Kukan na sakar musu kawai na faɗa jikin Yaya Musaddiq. Shima sai Hafizzullah ya ya rungumemu mu duka biyun ya saki nasa kukan. A take wajen yay tsitt, wasu na ganin mun birgesu da fassara abin namu da tsananin shaƙuwa ne da soyayyar juna. Wasu ko da suka san wani abu dake ɓoye sai suke jin tsananin tausayinmu da jin karaya suma. Nan take aka ringa tuno alkairan iyayenmu da musu addu'a. Dole dai Yaya Musaddiq ya jamu muka fita daga filin. Nan Gwaggo Gudidi ta jamu zuwa ɗakinsa ta dinga lallashinmu da mana nasiha. Haka kawai maganganun nata sai suke ta min kai da kawo dan na gagara fahimta da fassara wasu nikam. Kiran Yaya Musaddiq da akai a waya ne ya sashi miƙewa ya fita. Babu jimawa ya dawo yay kiran Hafizzullah. Anan ne Gwaggo ke tambayarsa lafiya? Sai yake sanar mata zasu maida kayan can gidan ne dan an gama kwashesu. Cikin nuna gamsuwa tace, “Oh to hakan yayi, bari na tattara su Zakiyya su sameku acan yanda aikin zaiyi sauri. In sha ALLAHU ai yanzu zakaga an kammala”.
Da to ya amsa mata yana ficewa. Hafizzullah ya canja riga suka fice. Babu abinda na gane a zancen nasu, amma na gagara haƙuri sai da nace, “Gwaggo kodai akwai abinda ke faruwa ne? Naga sai magana kuketa yi kamar a ƙudundune?”.
Kai tsaye tace min, “A'a babu komai ƴar nan. Kinga tashi mu koma ciki dan da anyi magriba zaki yi wanka a wanke wannan fentin da aka cika miki a fuska. Koda masu ɗaukar amarya dai sun zo ɗin sai dai mu yazam mune muka jirasu basu zasu jiramu ba”.
Banda tacewa face bin umarninta. Tunda dama nasan dai ya kamata a kainin da wuri kodan dinner da su Mansoor suka shirya. Amma kwalliya kona wanketa dole a sake wata basai munje can gidan ba kuma aita dibi-dibi nasan Mansoor da ƙosawa akan abu, sam baya son jira. Acan ƙasan zuciyata kam ina jin babu daɗi saboda rashin ganin duk jama'ar gidan a cikin sha'anin bikin nawa. Dan yaran duka babu wanda na gani

Please Login or Register in order to submit comment