Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tai mun cikakken wankan jego ina shagwaɓa ina wash tana lallaɓani. Yayinda tsohuwa da kanta ta sulluɓe baby tas ita kuma. Kafin kace mi mu duka an shiryamu tsaf. Ummie kuma ta dama min kunun kanwa da duk suka taho da kayansu, sai gasashen naman rago da yaji haɗi na musamman 😋🥱 sai uban ƙamshi gidan yake yi. Aka kuma baɗesa da yajin daddawa da suka taho da abinsu dai. Haka Ummie ta zauna cikin kulawa ta sakanni a gaba naci naman nasha kunun wai kuma sai ga tea, aiko na fara mata kuka wlhy na ƙoshi. Dole aka barni haka. Sai lokacin na samu mukai gaisuwa da su. Sunata ƙara jerama Baby addu'a da ni kaina. Kasancewar su a tare da ni ta ƙara min farin ciki da walwala. Haka mukai shirin kwanciya cike da kulawarsu. Baby dake barci tun ɗazun ta farka. Haka aka tsareni nai feeding ɗinta dan sunce yunwa ce. Na dai sha zafi, to amma yaya na iya tunda muma haka iyayenmu sukai haƙuri da mu a lokacin tamu haihuwar da rainon. Ga kiran waya tako ina shigowa yake kamar wayata zata tashi aiki. Kowa ya kira ɗaga masa nake. Dan masoyi na gaskiya ne ma zai tayaka farin ciki idan abin farin cikin ya sameka. Ya kuma tayaka kuka idan na jajen ya sameka. Nasha mamakin ganin harda Hajiya Mammah a masu kira, cike da farin cikinta kuma tanatama Baby Addu'a kuma dan tuni hotunanta sun kai garesu. Hakama Maman Malika da Malikar duk sun kirani. Suma zuwa gobe in sha ALLAHU sun ce suna tafe. Ƴan Kano ma harda wanda bamma yi zato ko tsammanin suna da number ta ba duk sun kira. Aunty Halime ce ke sanar min da aka faɗama Mom na haihu kuka wai ta fashe da shi. Gata babu isashshiyar lafiya. Kullum bakinta nakan Baby yanzu. Duk ta bushe ta lalace a tsaye. Ummanta kuwa wajen neme-nemen asirinsu taje mai mashin ya kadata a hanyar wani ƙauye ta karya ƙafa har waje biyu. Cinya da gwiwa. An ɗaura baiyi ba aka sake har sau uku. Ga ƙafar nan tana neman zame mata jangwam. Dole sai ƙanwar Mom ɗin ce tazo tana kula da ita. Ita Mom ɗin taƙi wai abarta ta kanta takeyi. Abinda ya dameta shi ya dameta. Umman tata dai har ranta ya ɓaci taita kuka akan furucin Mom ɗin tana ja mata ALLAH ya isa da faɗin ai duk ta dalilinta ne komai ya faru da yaƴanta, amma shine zata mata sakayya da halin ko'in kula........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏_


Follow this link to join my WhatsApp group:

https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq


*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._

.......Washe gari su Maman Malika da Hajiya Mammah suka iso suma. Hakan sai ya sake bani mamaki. Na tambayesa wai ba gida zamu tafi ba. Dan ina jin kunyar tambayar su Ummie. Shine yake sanar min ai batun tafiya babu shi. Babu mai kwasarma yarinyarsa sanyin jirgi. Za'ai suna anan kawai. Hankalina ya tashi, ta ina zan yarda da hakan. Idan shi danginsa na da ƙarfin tahowa nan ni kuma nawa fa? Ai ni za'a cuta kenan. Bamu ƙarasa maganar ba ya fita saboda kiran da akai masa a waya. Dama ya shigo ne mu gaisa da safen nan bayan Mama Balki ta mun wanka Mammi tama Baby. Da wannan damuwar na yini a rai dan bai dawo gidan ba har su Hajiya Mammah suka iso. Ummie ce ta ɗan lura da yanayina shine take tambayata mike damuna. Har nayi niyyar ɓoye mata sai naga bayan ita inada wata uwar ne. Sai kawai na fito na sanar mata ina hawaye. Murmushi tayi da rungumeni, cike da kulawa ta ce, “Karki tada hankalinki kinji yarinyata. Nima ina bayansa, dan ba baby kawai ba koke bazan yarda kisha iskar nan ba. So nake ki samu jego mai ƙyau da kulawa. Shiyayasa ma muka taho nan. Tunda kuma kikaji ya faɗa nasan yanada nashi shirin shima a ƙasa. Dan yanzu haka bamu jima dayin waya da Gwaggo Gudidi ba ma. ALLAH ya ƙaddara anan ɗin za'a haihu, sai kawai ayi haƙuri a ƙarasa komai”
Kaina na jinjina mata ina godiya. Daga haka muka cigaba da sabgogin mu. Bai dawo gidan ba sai dare. Koda ya shigo muka gaisa ban masa maganar ba. Sai ma zancen isowar su Yaya Musaddiq da Hayat gobe idan ALLAH ya kaimu yay min. Tare da nuna min wasu kaya wai idan ina son su zasu taho dasu ne. Idan kuma bana so su barsu kawai. Cikin farin ciki na sanar masa ni komai ransa ya biya masa yayi basai ya bi takaina ba. Daga haka mukai ƴar hira yana rungume da ƴarsa sai da Ummie tazo ta korashi. Dan tare da Mama balki muke kwana anan.

Washe gari kamar yanda ya faɗa da yamma sosai sai ga ƴan China sun iso. Basufi awa biyu ba sai ga kuma ƴan Spain suma. Hafizzullah, da Fahad da Bahijja. Aiko gida ya sake kacemewa. Dan har ma ya fara mana kaɗan. Sai da aka buɗe na kusa da mu ban taɓa sanin nashi bane ba sai yau. Ina dai ta ganin gidan a rufe koda yaushe sai nayi tunanin masu shi banan suke zama bane maybe zuwa suke time to time yin hutu kawai. Wannan taron ya sa naji a raina dama ya shirya abinsa fa. Dan tabbas-tabbas a haka yaso al'amarin ya kasance. Shiyayasa ya dinga min wayo da su Ummie ɗin kansu wai sai na shiga watan haihuwa saboda doctor yace ina son kulawarsa. Kai ya Awwab sai a barsa dai kawai. Yanda kowa kenan nan da Baby nece lallai kam naga haihuwar dangi. Dan daga Fahad har Yaya Musaddiq, aunty Falaq da Yaya Hayatu uban kayan da sukazo da shi na baby sai kawai nai tagumi ina kallonsu. Bayan ma anan shi uban gayyar ya loda wasu, saboda har ɗaki an haɗa mata. A ɓoye kam sai da nayi kuka Bily, dan sai nake jin kamar soyayyar ma ta mana yawa.
Mammi dai ta kafa ta tsare, duk abinda ake mun na jegon nan irin na mutanen da ne. Tsohuwar nan da uban guzirinta ta taho na kayayyakin itatuwa. Ga Hajiya Mammah nata ƙoƙarin ganin ta goge laifinta, sai dai fa masifar tana nan, wannan kam sai haƙuri dan kowa yasan halittarta ce. Itama Aunty Mama a yau ta iso da nata yaran. Sai fa aka sake kacamewa. Jikina duk ya fara yin sanyi, ƴan uwana uku ne fa sai matar Yaya Musaddiq a cikin duk wannan taron. Ina zaune a ɗaki nayi tagumi na saka Baby da nake feeding gaba da kallo ya shigo da sallamarsa. Ganin yanda ya tasamu gaba da kallo idanunsa ƙyam a kammu yasa naji kunya, janyeta nai na gyara jikina na miƙa masa ita. Ɗan murmushi yay da faɗin, “Oh baki so naga kina mun feeding Mamana?”.
Nima murmushin nayi ina ɗan girgiza kai, na ce, “Kai yaya kunya kuma. Kawai dai naga baka ganta bane tun safe shiyayasa. Ka dawo lafiya?”.
“Alhamdullahi, kuyi haƙuri na kasa baku attention ɗina yanda ya kamata. Ni kaina ina son ko yini ɗaya nai a gidan ayi jegon da ni amma uziri yamun yawa”.
Cikin ƴar dariya na ce, “Namiji kuma da jego? Kayi harkokinka mu zamu maka jegon”.
“Kin tabbata?”.
Na jinjina masa kai alamar tabbatarwar. Murmushi yay shima tare da ɗan jamun hanci. Sai kuma ya ɗan bata fuska da faɗin, “Duk sun saka min ke kinyi duhu. Nace ma Ummie a daina miki amfani da wannan ruwan zafin ga wani traditional medicins a ciki dani ko kallonsu ma bana son yi amma Ummie tace babu ruwana. Kema baƙya so ko?”.
Fuska na marairaice masa ina kwanciya a jikinsa da faɗin, “Yaya bawai fa ina sha bane ba. Kuma suna da amfani sosai. Duhun nan kuma wanka da ruwan zafi ne yasa ba wani abu ba. Zamu washe ne. Ni yanzu ma ba wannan ba, wai taro zakayi ne naga invition card a hannun su Hafizzullah?”.
“Eh mana, ALLAH zai mun ƙyautar nan ne ban nuna farin cikina ba. Banyi na aure ba fa, dan ina kishin Matata. Wannan kuma ya kamata nayi dan kowa yasan Maash ya zama Baba shima”. Ya ƙare maganar da kashe min ido ɗaya. Murmushi kawai nayi da faɗin, “ALLAH to ya taimaka. Amma a ƙasan raina ina jin damuwar babu nawa dangin sosai a cikin sabgar. Ya jima a ɗakin sosai yau kam Hajiya Mammah tazo ta korashi. Ni saima suke ban dariya. Duk yanda suke tunanin rashin kunyar Yaya Awwab yana kuma fa da kawaici. Duk abinda kuma yasan zan cutu yana matuƙar ƙoƙarin kauda masa ido koda yana a buƙace da shi, dan ni kaina nasan a takure zai kasance a tsakanin nan. Amma idan bashine yaso ka fahimta ba bazai taɓa nunawa ba. Washe gari na tashi sukuku dan sabgogin bikin suna sun kankama a ƙasar da ba tamu ba. Sai kawai gasu Hafizzullah da Fahad suna shigo da kaya. Da mamaki nake kallonsu saboda a lokacin na fito zan nunama Aunty Falaq abu a kitchen basu ganshi ba. Ga Nasreen sun fita ita da yaran Aunty Mama kasuwa. Gaba ɗaya sai na saki baki da hanci da idanu ina kallon masu shigowar. Abba ne kan gaba. Sai Gwaggo Gudidi da aunty Halime Aunty Zakiyya a bayanta ɗauke da Babyn aunty Haline ɗaya. Sai Mom a ƙarshe Bibaa da Auta biye da su, sai Matar Kawu Musa da ta Kawu Sabi'u da Aunty Magajiya. Na zata sun ƙare sai ga Adda matar Uncle Sulaiman da yaranta sai Mamin su Mansoor da ƙannen su Mansoor ɗin biyu da matansu, sai uwargidan Sheikh, maman Bahijja kenan. (Ikon ALLAH, sai kace ba daga wata ƙasa zuwa wata bane) na faɗa a zuciyata wata irin ƙaunar bawan ALLAHn nan na ratsa ɓargo da jikina..
Gida kam ya amshi baƙi fiye da yanda nayi zato, tsabar farin ciki harda hawaye bayan na rungumesu ko nace nama rasa wazan rungume a cikinsu. Gwaggo Gudidi nata mun tsiya wai ko dai na suma ne. Ashe Ummie ma tasan da isowar tasu mune dai aka ɓoyema ko nace ni. Kowansu ya ɗauki Baby anata sanya mata albarka da addu'oi da kwarzanta kamanninta da babanta. Yayinda Mom ta zama wata abar tausayi, dan bata ma ɗauki Baby ba sai da Abba ya daka mata tsawa da faɗin, “Oh hassadar taki ce ta motsa nan ma kenan Jalilah”.
Yanda yay matan sai ma ta bani tausayi, amma sai naga su su Gwaggo Gudidi ko'a jikinsu. Auta dai na nane dani anata bani labarin Nigeria. Bayan sun huta sunci abinci suma aka kaisu ɗayan gidan domin suyi wanka su huta. Abba kuma aka wuce da shi nashi masaukin shima inda su Fahad zasu kwana yau tunda an ƙara yawa. Koda ya shigo dubamu da dare kasa haƙuri nayi na rungumesa ina hawaye da jera masa addu'oin gamawa lafiya. Murmushi kawai yay da nuna min lips ɗinsa wai na masa kiss. Na maƙe kafaɗa da faɗin, “No Mammi ta hana sai nayi arba'in biyu”.
“Ashe zan gudu dake basu sani ba”. Ya faɗa yana kaiwa zaune. Idanu na waro na ce, “Guduwa fa?”.
“Sosai ma kuwa, su gwada su gani. One week kawai gashi na jigata ace har 80days haba kanwa na kawo duniya ma kenan. ALLAH sai dai su nemeki su rasa sace ki zanyi.”
Ni dariya ma abin ya bani a raina nace lallai ashe da sabon tsalle. Ko na samu tsarki dole na kama kaina kada mutumin nan ya sani inba hakaba ya buɗe min aiki tsaff da laɓuɓuwar jaririya shi ba damuwarsa bace.
A daren akai min ƙunshi da kitso, dan cikin yaran Uncle Sulaiman akwai wadda tai masifar iyawa harda su gyaran jiki. Duk wanda ya kalleni yaga maijego ɗanya jagab. Dan sosai gaskiya jego ya amsheni sai godiyar ALLAH.......✍️

A gurguje Please 🥺


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚_


Follow this link to join my WhatsApp group:

https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq


*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._

.........Washe gari da safe kowa yasan sunan Baby Ummu-Hidaya, dama hakan dai duk mukai tsammani. Su Yaya Musaddiq da Yaya Hayat da su Fahad sun kasa zaune sun kasa tsaye. Ashe gagarumar walima ake shiryawa batare da mun sani ba. Sai da Hayatu yake sanar mana ya kamata ace duk mu kasance cikin shiri basai anzo ɗaukar mu ba aita wane bai shirya ba wane bai kammala ba. Makeup artist aka kawo min data san aikinta. Wannan kam duk aikin Ummie ne dan da farko Yaya Awwab yaso yin bore tai masa jan ido da faɗa masa kwalliyar ma ba rufin asiri bace tunda tana ɓoye kammanin mutum. A irin wannan taron kowa ke sanin iyalinka idan ma da wani nufi a ransa yay tunanin aiwatarwa, amma idan ya gagara ma riƙe kammani ba shike nan ba. Yin wannan magana sai tasa yay kamar ya ɗan fahimta. Amma dai baice komai ba ya shige ɗaki. Dariya su Fahad sukaita ƙumshewa. Sai da Ummie tace, “ALLAH dai ya baku Sa'a ya jiku kunga ai sai ya huce kanku tunda nidai babu yanda za'ai dani.”
Dariya su Mama Balki sukayi, yayinda Fahad da Hafizzullah ɗin suka fice da gudu. Haka dai badan fa yaso ba akai min wannan kwalliya. Ammafa magana ta gaskiya na haɗu ni kaina nasan nayi ƙyau. Kada fa kice na cika kuranta kaina Bily. Gaskiya nake faɗa miki. Bani kaɗai ba hatta Baby ta fito abinta kamar ka saceta ka gudu. Yayinda uban gayyar ya fito kuma sai kowa ya dinga faɗin, “Masha ALLAH Masha ALLAH. Ina ganin ƴammatan nan nata binsa da da ido harda Bibaa. A raina nace kwayi kwa gama in sha ALLAHU mijina yayi kenan. Koma akwai ƙaddarar ƙara auren a garesa bana fatan ace cikin ku ƴan uwansa gara ya auro bare da kowa zai goga sa'arsa. Haka dai Ummie ta tsayar da shi badan yaso ba ta mana hotuna, sai suka samu damar ɗauka suma. Sune suka fara yin gaba, ni da shi zamu taho ƙarshe. Aiko bawan ALLAH na ganin sun fice ya damƙoni ya shanye jambakin da aka samun tas. Fuska na ɗan ɓata da faɗin, “Kai Yaya”.
“Kina sake cewa tak ALLAH sai ma na kwashe sauran kwalliyan.” ya faɗa a fusace. Bam na rufe bakina kuwa ban sake magana ba. Shima sai ya ɗau yarinyarsa yana mata wasa ya shareni. Oho, ai bani na kar zomon ba rataya aka bani nima. Haka har akazo ɗaukar mu ni da shi kowa na zumɓurar baki. Haka muka fita yana riƙe da Baby, amma koda mukaje wajen motar sai da ya buɗe min da kansa na shiga ya maida ya rufe da gyara min rigata sannan ya zagaya nasa mazauni inda shima aka buɗe masa ya shiga. A motar ma shareni yay yanata ɗaukar ƴarsa hoto, ashe hoton na wayone duk harda ni a ciki. Bandai tanka masa ba nima na maida hankali akan tawa wayar.
Rikicewa nai sanda muka iso naga an cika hall fal da bayin ALLAH. Kai kace a ƙasarmu ta haihuwa muke. Kai Masha ALLAH. Dan waje yayi matuƙar ƙyau da ɗaukar idanu. Mun shigo kowa idonsa a kammu, ALLAH ma ya taimakeni shiga ce a jikina ta muntunci dan shigar cikakkiyar bahaushiya nayi ƴar Nigeria yankin arewa. Haka shima manyan kayane a jikinsa harda babbar riga ga hula kamar ba Maash ɗina ba. An mun gargaɗi yafi ashirin kafin mu shiga akan kada naje ina washe musu baki. Ni sai abun nasa ma ya bani dariya. Mun isa masaukin da aka tanada domin mu, aka fara da buɗe taro da addu'a. Da ga haka aka fara abinda ya zaunar da mutane. Ganin ya ƙi ajiye Babyn a gadon da aka tanadar mata nai masa magana, sai cewa yay shi bazai ajiye yarinyarsa ba a takura mata da ɗauka, yasan kuma kowa da niyyar da yazo wajen aje a masa kidnapping ƴarsa. Ikon ALLAH sai kallo na faɗa a raina. To in ba rigimar Yaya Awwab ba, duk uban securitys da aka zuba a wajen. Ga camaras tako ina, sannan gadon ma a kusa damu yake gab sosai taya wani zaiyi wannan ɗanyen aikin ni Samraah. To amma tunda ya sakama zuciyarsa haka sai na kama kaina kawai. Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain mahaifin Bahijja da wasu manyan malamai ne suka gudanar da wa'azi mai shiga jiki akan tarbiyyar ƴaƴan tun daga rainon cikinsu da rainonsu har kawowar girmansu. Sai lokacin nasan Malam ɗin yazo ashe harda Uncle Sulaiman da Uncle Abdullahi da Baban su Mansoor. Harma da su Mansoor ɗin da Kawu Jafaru. Bayan shi wasu malaman ma sunyi ƴan wasu ƙasashe daban-daban, daga nan aka fara cin abinci. Sosai Baby Ummu-Hidaya tasha addu'oi tare da ƙyaututtuka wajen abokan Babanta da har yau bai taɓa gabatar min da su ba matsayin abokai koni ya gabatar dani garesu matsayin mata. Sai na fahimci shifa komansa da tsari, akwai abinda yake alaƙantawa da aboki akwai wanda baya sakashi a wannan sabgar. Basu kawai ba ma'aikatansa ta fannonin kasuwancinsa daban-daban sun halarci wajen, sun kuma bama Babby gifts sosai kodan faranta ran mahaifinta kamar yanda suma yake faranta musu. Harda mutuniyata Juliet. Yau dai na ɗan sake mata fuska kaɗan kinsan ance mai ɗa wawa.
Ansha hotuna sai dai kowa sai dai yazo inda muke ya samemu, kamar yanda ya faɗa kuma bai bar kowa ya ɗauka yarinyar nan ba sai dai a ganta a hannunsa ai mata addu'a. Ai yau dai naga fitina ta Yaya Awwab. Babu kuma damar ayi magana. Koda yake tsoffin nan namu naga sun goya masa baya da abinda yay ɗin. Walima kam sai san barka dan taro ya tashi lafiya. Sai a lokacin ya bama malaman da sukai wa'azi a wajen Babyn suka ɗauka suma. Sun sanya mata albarka tare addu'oi. Sannan suka ɗora da ƙara mana nasiha ni da shi akan tarbiyyarta da rainonta.
A gajiye kowa ya koma gida. Sauran baƙi na'a masaukinsu. Wasu kuwa har sun wuce inda suka fito. Tsabar barcin da nake ji wanka ma da ƙyar nayi na kwanta. Koda ya shigo yimana sai da safe ma ni kam na jima a duniyar barci. Sai da Mama balki dake shirya baby Hidaya sukai ya fice. Washe gari muka tashi da ƙananun maganganun mutane da suka cika media, marasa aikin yi a Nigeria da wasu Malam suka dinga sharhi da caccakar al'amarin bikin sunan nan da malaman da sukai lectures wai kwaɗayi ya kawosu. Yayinda wasu suke ganin su basuga abin laifi ba. Maash dai ba aiki yakema gwamnati ba, ba wani muƙami garesa a gwamnatance ba, ba ɗan siyasa ba. Ɗan kasuwa ne da guminsa yake nema kowa ya sani. Ko mi zaiyi da kuɗinsa dan mi za'ai zaman masa sharhi tunda bana wani ya sata ba. Masu satar ma suke abinda suke so balle shi da

Please Login or Register in order to submit comment