Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamata har muka shiga mota zuwa anguwar da Hajiya take....
Babbar anguwace mara yawan cinkoson jama'a kamar ba'a cikin Lagos da nake jin ana faɗa ba. Duk da kuwa kafin mu iso cikinta mun shiga cinkoson matuƙa wani gurin ma da ƙyar muka fita, dan tafiyarmu daga filin jirgi zuwa gida yafi tafiyarmu daga Kano zuwa Katsina nisa, duk da dai shi wancan gari da gari ne, wannan kuma cikin gari dole akwai banbanci. Iya ƙagara na ƙagu a zo gida, dan a yanzu ma amai ne keta faman taso min tunda muka shiga motar. Da alama Hajiya ta fahimci halin da nake ciki ne ya sata siya min lemon zaƙi a hanya tace na dinga shanshana ɓawon, sai goro da shi kuma na dinga ɗan ci kaɗan-kaɗan. Wannan ne ya riƙeni zuwa gidan Hajiya.
Anan ɗin ma dai maigadi ya buɗe mana gate, sai faman washe baki yake da jerama Hajiya sannu da zuwa. Da taimakonsa mai taxi ɗin daya ɗakkomu ya fidda mana akwatinansu biyu madaidaita. Janny ta tsaya biyan mai taxi ɗin, yayinda ita kuma Hajiya ta kama hannuna muka nufi wata ƙyaƙyƙywar ƙofa fara da adon golden. Wannan gidan yafi gidan Abuja girma, lokacin da muke shiga falon kuma ya sake tabbatar min da yafi wancan ɗin kayan alatun more rayuwa ma. Dan falon ƙato ne na gaske, ga wasu manya-manyan hotunan Hajiya da wani mutum a jiki tamkar zasuyi magana dan girma. Sai ƴammata biyu masu tsananin kama da juna sannan suna kama da mutumin. Fitowar wasu ƴammata biyu da dattijuwa ya katse min kalle-kallen hotunan da nakeyi. Nai tsai ina kallon dattijuwar da ƴammatan da suka zube gwiwa bibbiyu suna gaida Hajiya da jera mata sannu da zuwa. Itako amsawa take cike da nuna isa da gadara tamkar ba Hajiyar dana sani daga jiya zuwa yau ba. Dan bayan ta gama amsa su a taƙaice tai musu nuni da ni. “Kuje da ita sashenku kafin na nemeta, duk kuma wanda ya mata wata any magana sai na wulaƙantasa ta yanda sai yayi dana sanin sani na a gidan nan. Ina sauran suke?”.
Da sauri dattijuwar ta amsa mata da “Madam Oyinka ta ɗauki Surayya da Umayyah, dan tare sukazo da wata baƙuwa tun jiya da yamma kamar yanda na sanar miki a waya”.
Kaɗan Hajiya ta yamutse fuska tana kallon agogo, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, dai-dai nan Janny ta shigo maigadi biye da ita jaye da akwatuna. Hannu kawai Hajiya ta ɗagama Dattijuwar alamar suje. Miƙewa duk sukayi suna min nuni da ƙofa.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_

_______________

Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE
Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne
Muna da
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Mai bunsuru
Dan jarida
Soyayya dole
Bakin kyalle
Tadire ta girke
Gumba mai likkafani
Maza taye
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Mallakoki
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su
Kayan mu tested and trusted ne
Muna maraba da masu siyan Daya ko sari
Muna Nan cikin garin kaduna
Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah

Ni ce taku har kullum
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975

____________

......Wani irin yamutsawa kaina ya shiga yi, dan gaba ɗaya suffar ƴammatan nan da dattijuwar batai kama data mutanen kirki ba, sai irin gogaggun matan barikin nan da idanunsu ya gama gogewa. Juyowa nai a karan farko na dubi Hajiya, itako ta ɗauke kanta gefe fuskarta babu alamar wasa a yanzu. Kamar ba itace keta faman min murmushi ba a Abuja da lallaɓani. Kallona na maida ga Janny da itama take kallon Hajiyar, a karo na farko na ce, “Dan ALLAH Hajiya ku barni a wajenku”.
Wata irin tsawar data gigitani Hajiya ta daka min. “Ka jimin shegiyar yarinya, su ɗin sama suka ce miki suna da gida bayan wannan da suke ciki?!! Zaki wuce ko sai na banbance miki tsakanin aya da tsakkuwa ku gammin yarinya da tsurku. Kin fini sanin abinda ya dace ne!”.
Rawa jikina ya cigaba dayi har ina neman kifewa ƙasa. Bamma san sanda nabi wanda akace nabin ba. Da harara Hajiya ta raka bayansu, sai dai suna ficewa taja tsaki da fincike gyalen abayar data naɗe kanta da shi. Tuni gashin dokin kanta ya bayyana, ta jefar da ɗan vail ɗin tana magana cikin yare, sai kuma ta miƙe ta fincike abayar ma. Anan ɗin ma wani wandon bomshot ne na jeans ya bayyana a jikinta da riga best....
“Hajiya ya haka?”.
Cewar Janny tana dariyar shaƙiyanci. Da sauri ta harari Jannyn da zagaya hannunta saman kai ta ce, “God for bed yoo, sunana Jannifer Can hajiyansu su ƙarata da shi bani ba Mtsowww!!. Yanzu ma zanyi shirin Church pastor yay min addu'a akan hakan. I beg, give me wine na ɗan sha ma ko zandawo hankalina da ƙyau”. Tai maganar tana komawa saman kujerar ta zube. Wucewa Janny tai hanyar kitchen, babu jimawa ta dawo da kwalban giya mai tsadar gaske da cups guda biyu. Ita ta ɓalle ta zuba musu tare da miƙamata itama ta ɗauki ɗaya, sai da suka ɗan haɗa kofunan alamar chess sannan kowa ya kai bakinsa yana murmushin samun nasara. Dan kuwa dai sun samo nasarar da suke buƙata a wannan tafiyar.

(Tofa abin mamaki, idan na fahimta dai wannan Hajiya ta bogi ce, hasalima ba musulma bace, ba kuma bahaushiya ba. Ko kuma dai bahaushiyar ce musulma ada tayi ridda? Tirƙashi, muje zuwa wai maƙwafcin mai akuya ya sai kura)..

_______★

“Duk yanda na lissafa miki kayan nan haka zatai amfani da su Jalilah. Sannan wannan da za'a dafa abincin da shi ki tashi da kanki kiyi girkin bawai kiba wannan shegiyar mai aikin da kika kwaso ba. Ni wlhy haka kawai yarinyar sai bata min ba, dan kawai kinƙi jin shawara ne”.
“Wai Umma ya kike so nayi dan ALLAH. Mai aikin nan fa dolece. Sanin kanki ne da ga Baby har Bibaa babu abinda suka iya na aikin gida, ni kuma wlhy yanzu na riga na sangarce tunda shegiyar yarinyar can ke komai tun tana ƙanƙanuwarta. Da nasan haka abin zai ƙwaɓe min ALLAH da auren zan hanata gaba ɗaya a rayuwarta”.
Dariya Umman tata tayi da faɗin, “Daga baya kenan. Ni dai muyi abinda ke gabanmu nata kuma ya zama labari ai tunda kin ɗebi rabonki. Yanzu babban burina Bibalo da takwarata su auri mazan kere sa'a. Dan haka bana son wasa. Awakina na sayar har Niger naje amso kayan nan kema kin sani, dan haka kiyi yanda nace ni zan wuce bana son mijinki yazo ya sameni anan. Magana ta gaba kiyi duk yanda zakiyi waɗan nan samarin biyu ƴan uwan yarinyar nan suma su bar miki gida dan nafi son na cigaba da ganin daga ke sai ƴan ƴaƴanki a cikinsa.”
“Banƙi na naki ba Umma, sai dai fa yaron nan yanzu shine komai na gidan nan, ina mora a jikinsa wlhy bazan so yabar gidan ba. Shiko ƙaramin dama yana makaranta sai lokaci-lokaci yake zuwa. Mudai sake shawara yanzu ne lokacin cin amfaninsu su dama macen ce nauyi ai”.
“Eh to da kuma wannan dan wannan. To wai tsaya ma, idan yaron nan kinga yana samun wasu manyan kuɗi ne mizai hana mu haɗa shi aure da Bibaa”.
“Bibaa kuma Umma?”.
“Ƙwarai da gaske. Ga gida bai ƙoshi ba sai a kaima dawa. Ke dai ki nutsu ki sake tabbatar da nauyin aljihunsa. Dan ni dama hidimar da yay a bikin ƙanwar nan tasa da wadda yake a baya tana firgitani”.
“Amma Umma iyakar yaron nan fa Sakandire”.
“Ina ruwanmu da wani Sankandire ɗinsa ko digiri. Shi namiji ai aljihunsa adonsa. Yo ko besan (A) ba indai akwai babbar (N) a aljihunsa miya damemu. Kidai yi nazari nima zan sake tunani”.
Cikin jimamami Mom ta ce, “To shikenan Umma ALLAH yasa mu dace, sai na jiki ko kin jini.”
“To mu huta gajiya. Amma ki tabbatar sunzo sun gaisheni fa ita da shi idan ya iso”.
“Zasu zo Umma kar ki damu”.

Tofa ban ganeba wai anyi gabas da kare🤔🥱


★★★★

Gaba ɗaya a firgice nake da komai, dan wani irin juyewa ƙwaƙwalwar kaina ke neman yi. Musamman ma da naga inda ƴammatan nan suka nufa da ni. Tacan bayan gidanne alamar Bq. Sai dai an raba tsakaninsu da inda su Hajiyan suke da katanga harda ƙofa. Akwai ɗan filin tsakar gida, wanda ke da ƴan kayayyakin ajiya kamar su drum na ruwa guda uku, sai botikai da yan tarkace na aiki. Sai murhun gawayi guda biyu da wasu tukunya masu girma guda biyu. Duk da gidan a share yake tsaff ko kusa bai kama ƙafar ƙyawun inda muka baro ba. Lokacin da muke ƙoƙarin shiga ƙofar da nake ƙyautata zaton ɗaki ne na kusa cin tuntuɓe da tarin takalman dake a wajen, sai da ɗaya daga cikin ƴammatan ta taroni. Sannu tai min cike da nuna alamar tausayawa, na gyaɗa mata kai kawai ina mai haɗiye abinda ke min kaikawo a maƙoshi. Ƙaton falone sosai, sai dai babu komai a cikinsa sai carpet blue da aka malale ƙasa da shi. Sai ƙofofin ɗakuna a jajjere a kowanne bango akwai biyar. Shima falon dai babu datti, sai dai carpet ɗin yay masifar tsufa har a wasu wajajen ya yage wani gurin kuma ya gurje alamar yawan takawa, duk naga hakane saboda hasken wutar lantarki dake haske dako ina. A hankali nakai zaune kamar yanda suka umarceni, na takure jikina waje guda ina ɗan kalle-kalle. Kusan minti uku dattijuwar nan ta kawo min abinci a plate ɗin roba. Shinkafa ce da wake da mai da yaji. Sai ruwan ƙwara ɗaya.
“Bissmillah kici abinci ƴar nan. Sai kije kiyi wanka kizo ki kwanta”.
Kasa cema tsohuwar komai nai, sai binta da kallo kawai nake. Babu alamar ta damu da hakan itako tai gaba abinta ta sake fita. So nake na danne komai a raina karna sakama kaina wata damuwa ko tsoron inda na tsinta kaina. Dan haka na shiga turereniyar ture komai na fara cin abincin. Kaɗan naci abincin dan bakina sam babu daɗi har yanzu, hakama jikina babu ƙarfi sosai. Ruwanne na shanye gaba ɗaya, cikin sauke numfashi nai hamdala ga UBANGIJI. Ƙoƙarin miƙewa nake dattijuwar nan ta shigo, kallonna tai ni da plate ɗin abincin, da yanayin mamaki da gurɓatacciyar hausarta da zaman Lagos ya ɓata ta ce, “Ƴar nan badai har kin ƙoshi ba?”.
A hankali na gyaɗa mata kai alamar hakane. Mama tai ɗan jimm kamar mai tunani, sai kuma ta amshi plate ɗin ta ajiye tana faɗin, “Shikenan muje kiyi wankan sai ki kwanta ko?”.
Kai na girgiza mata, cikin yanayin dana tsinta kaina na sanyi da rashin ƙarfin zuciya kamar wadda aka jefa na ce, “Mama zan kwanta kawai basai nayi wankan ba, dan in har nayi zan iya samun matsala koda da ruwan zafi ne”.
Jimm mama tayi kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Cikin sauke ajiyar zuciya tai min nuni da hanyar ɗaya daga cikin ƙofofin dana gani. “Ba damuwa muje ciki to”. Ɗaki ne ƙarami sosai. Amma duk da haka akwai katifu ƙanana irin na ƴan makaranta har guda biyar jere reras. Kowace katifa akwai filo da bargo. “Nan shine zai zama ɗakin ki. Ba kuma ke ɗaya bace za'a iya sake kawo wasu kuna kwana a tare. Sai dai a yanzu babu kowa sai ke kaɗai dan ankwashe wanda suke ɗakin gaba ɗaya”.
“Mama saboda mi to?”.
Na faɗa cikin suɓucewar baki da jin wani irin ƙarfin zuciya a lokaci ɗaya. Komai mama batace da ni ba. Sai ma juyawa da tai abinta ta fita kawai tana faɗin “Sai da safe”. Sosai mamaki ya saka ni ƙurama ƙofar ido na tsawon lokaci. Sai kuma zuwa can na taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar oho muku nai kwanciyarta. Amma a can ƙasan raina aikin jaridancin ne ke faman yinƙuromin, dan haka kawai nake ji a raina a wannan gidan akwai abinda ake ƙullawa. Abin mamaki na farko canjawar Hajiyar nan da mai aikinta a lokaci ɗaya, ita da suketa tattalinna tun daga jiya kamar wata ƙwai amma muna shigowa gidannan kamar basu ba. Na biyu wannan ƴammatan dana gani anan da kuma shi kansa wannan part ɗin da alamu suka nuna mutanene da yawa ke mu'amala da shi. Na uku ganin kusan ƴammatan duk hausawa ne musulmai haihuwar arewa. Lallai ina buƙatar nasan wani abu kam. Sai dai ta yaya? A wajen wa?. Wannan shine babban tsallen baɗaken....

Washe gari kiran sallar farko Maman nan ta tadamu, salla muka farayi, muna idarwa ta tattaramu zuwa ainhin cikin gidan. Babu motsin kowa alamar mutanen gidan basu tashi a barci ba. Aiki Mama ta rarraba mana, ta kuma tsaya a kanmu sai da kowa ya kama nashi yanda ya kamata. Kafin kace mi cikin abinda baifi awa ɗaya da rabi ba mun kammala ko ina ƙal, sai ƙamshin fresheners ke tashi da girkin da Mama keyi a kitchen. Can sashen nasu muka koma, yayinda muka bar mama na ƙarasa girkin, a can ɗin ma ba zaman mukai ba, gyara ko'ina muka shigayi, wasu kuma na haɗa wutar gawayi domin ɗora abincin kari. Ni dai duk abinda akace nayi yinsa nake yi, yayinda nake faman bin kowa da komai da idanu cike da nazari. Babu wanda ya tambayi sunana nima kuma ban tambayi sunan kowa ba, sannan ko'a junansu bana jin suna hira balle ambatar sunayen juna, kowa aikin gabansa kawai yake baki ruff. Kafin goma na safe mun kammala komai, masu shiga wanka nata ƙoƙarin yi duk da banɗaki biyune kacal a sashen na toilet dana wanka, amma haka suke bin layi kamar wasu ƴan makaranta. Kasancewar basu da yawa sosai basuja wani dogon lokaci ba suka kammala wanka. Zuwa sannan mama ta dawo, ita ta rarraba mana abincin kowa yazo ya ɗauki nasa yaja gefe yana ci, sai a sannan wasu ke ƴar hira ƙasa-ƙasa. Ni dai nama gagara cin abincin sai kallonsa kawai nake har sai da Mama tai min magana akan na maida hankali naci dan Madam na buƙatar ganinmu.........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆_

.......Wanke-wankenta take hankali kwance, yayinda bakinta ke faman raira waƙar Ado gwanja ta Chass. Sosai zazzaƙar muryarta siririya ke faman ratsa zuciyar Abba dake falo zaune yana waya. Shi kaɗai ne a gidan sai ita. Dan tun ɗazun Mom da Baby da Bibaa suka fita kasuwa wai yi cefane Baby zata yi baƙo. Sai Auta dake ɗaki yana barci saboda zazzaɓi da yake yi kwana biyu. Abbas kam ma yanzu sai ya gadama yake kwana a gidan. Shiko Nabeel yana hostel ne. Ya Musaddiq ma ganinsa yayi wuya a gidan yanzu.
Halime kenan sabuwar mai aikin Mom da ta saka wata ƙawarta ta nemo mata tun bayan wucewar baƙi ƴan biki da kwana biyu. Dan kuwa daga ita har su Baby sun gagara gyaran gidan ga hargitsewar da yayi na hidimar biki. Da gaggawa ta buƙaci samun mai aikin dan haka ƙawar tata ta kawo mata Halime da itama ta samo wajen wata mata mai kawo ƴan aiki daga ƙauye. Da farko Mom taso ƙin amsar Halime, saboda ƙyaƙyƙyawar yarinya ce ga ƙirar jiki irin ta manyan mata ALLAH ya bata. Rashin gyara ne kawai da rashin suturar kirki ya ɓoye baiwar da ALLAH ya matan. Sai kuma ɗan shirme na rashin ilimi. Har tace ƙawar tata ta koma da ita a samo mata wata su Baby suka shiga roƙonta dan su kam aikin suke gudu, dole ta haƙura ta amshi Halime akan nan da wani lokaci za'a sake samo mata wata sai ta sallameta. Sai dai duk da haka ta kafama Halime dokoki sosai a gidan musamman akan Abba. Dan tunda tazo gidan ma kusan sati uku da wasu kwanaki kenan bai taɓa ganinta ba, itama bata taɓa ganinsa ba. Yau ma Abban har ya fita kasuwa mantuwa tasa ya dawo gidan, kiran wayarsa da akayi ya sakashi zama a falon yana amsawa. Gaba ɗaya wayar ta gundiri Abba, dan sosai muryar take sake tasiri a zuciyarsa. Sallama yay ya miƙe zuwa ɗakin barcinsa yana ƙwala ma Mom kira dan bai san basa gidan ba tunda ba gaya masa tayi zata fita ba. Cak Halime ta tsaya daga raira waƙar da take yi, tai ɗan jimmm alamar saurare. Jin da gaske dai muryar namiji take ji na kiran hajiyarta yasata ɗauraye hannunta a fanfo ta fito a kitchen ɗin. Dai-dai lokacin Abba na ƙoƙarin shigewa bedroom ɗin da cigaba da ƙwala kiran sunan Mom. Cike da rashin wayo da gaɓanci Halime ta ce, “Ikon ALLAH kai kuma waye haka kake kiran mafarauta sanƙamemen ƙato har ɗakin kwanan mutane?”.
A bazata furucin nata ya shiga kunnen Abba, dan shaf yama manta da wata batun mai aiki da Mom tace masa zata kawo, tunda shi dai bai taɓa ganinta na tunda tazo gidan, dan haka ya juyo gaba ɗayansa. Idanu sosai ya tsira mata, ganin yanda ta riƙe ƙugu tana hura siririn dogon hancinta da tura madaidaicin bakinta ya bashi dariya. Amma sai baiyi ba cikin suɓutar baki ya furta, “Aljani ne”.
“Na higa uku ni Halime aljani kuma? Ita dama Hajiya tasan da aljanu a gidanta ta kawoni nai mata aikatau”.
Murmushi Abba ya saki a karo na farko, yayinda a kaikaice yake sake ƙarema yarinyar kallo. A fuska dai bazata wuce sha bakwai zuwa kaɗan ba. Amma a jiki akwai ƙira ta manyan mata, dan tako ina a cike take. Ganin tana neman zurawa da gudu yay gyaran murya. “Kinga kwantar da hankalinki ba aljani bane. Mai gidan ne. Ina hajiyar taki?”.
Da mamaki Halime ta waro idanu waje sosai, sai kuma ta dafe baki tana juyawa ta kalla makeken hoton dake falon, wanda tunda tazo gidan Ita dai bata gajiya da kallonsa saboda ƙyawun da sukayi a jiki shi da Mom da su Baby. Su Samraah dai babu su daga ita har su Yaya Musaddiq. Tabbas mutumin dake zaune kusa da Hajiya ne. Amma duk da haka sai da ta sake juyowa ta kalla Abba. Kamar wadda aka tsikara ta zube ƙasa tana faɗin, “Na shiga uku wlhy kuwa kaine ɗin. Alhaji dan ALLAH ai min aikin gafara”.
Murmushi Abba ya sake yi, sai kuma a hankali ya furta, “Ba damuwa tashi abinki. Ina hajiyar taki?”.
Miƙewa Halime tayi, sai dai yanzu kanta a ƙasa alamar jin kunya. Cikin ƙanƙan da kai ta furta, “Sun fita da Aunty Baby da aunty Bibaa”.
Ɗan jimm yay yana kallonta. Sai kuma bai ce komai ba ya kaɗa kansa zai shige bedroom ɗin. Sai da ya juyo zai rufe ƙofar suka sake haɗa ido da Halime dake kallonsa itama. Da sauri ta juya masa baya har jikinta na kaɗawa. Numfashi ya ɗan furzar da cewa, “Je ki cigaba da aikin ki”. Bai ma kai ƙarshe ba ta zura da gudu hanyar kitchen. Kansa kawai ya girgiza yana murmushi shima ya ƙarasa shigewa ciki....

💦★💦★💦★💦

Washe garin da nake cika kwana biyu a gidan bayan kammala aikin dana fahimci wajibine a garemu a gidan muna dawowa wanka nayi na shige inda ke matsayin ɗakina batare dana shiga aikin namu sashen ba. Kwanciya nayi wasu hawaye masu zafi na sauka min batare dana sani ba. Gaba ɗaya na rasa mike damuna. Koda tunani nai ƙoƙarin yi akan kaina da zaman wannan gidan sai kaina ya fara ciwo. A yanzu haka har ya fara saramin. Dole na tattara komai na watsar na cigaba da kwanciya shiru a wajen har suka kammala aikinsu Mama tazo tai kirana dan a zatonta banda lafiya ne. Da ƙyar na iya faɗa mata na ƙoshi. Jimm tai tana kallona, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta juya ma ta fita. Kusan mintun talatin da fitar tata sai gata ta dawo. Wai na taso Hajiya na kiranmu. Babu musu na miƙe dan bama zan iya musun ba. Hasalima sai wani irin tsoron Hajiyar ne naji ya sake shigata har zuciyata na rawa. Haka dai muka fito duk a ɗarare.
Mun kai tsahon mintuna goma a tsaye bayan shigar Mama cikin falon kafin a bamu izinin shiga ciki. Hamshaƙan mata muka samu har guda uku zaune cikin shiga ta alfarma. Basai an faɗa ba, a kallo ɗaya da zakai musu zai baka tabbacin daloli sun zauna musu bama naira kawai ba. Hajiya na zaune itama cikin tata shigar alfarmar tamkar mai shirin fita ma. Gefenta Janny ce ke tausa mata ƙafafu a hankali. Gaishesu mukai a tare, duk suka bimu da kallon ƙurulla batare da sun amsa ba.
“K fita anan banda ke”.
Furucin Hajiya ya samu ɗagowa gaba ɗaya dan bamu san dawa ake ba a cikinmu. Sai dai ganin kai tsaye ni ta nuna yasa sauran maida kawunansu ƙasa. Cikin dokawar ƙirji na yunƙura zan fita a cikinsu kamar yanda ta umarceni. Amma sai ɗaya a cikin matan ta katseni da faɗin, “Kamar ya banda ita? Ai ni gaba ɗaya ma hankalina a kanta yake Madam”.
Kai Hajiya ta girgiza mata. “No Alajah ita wannan sabuwa ce. Babu abinda ma ta koya balle nai cinikinta. Sannan ba aikatau ne aikinta ba”.
“Babu wani damuwa a hakan ni tamun. Dan dama irinsu nake so sunfi daɗin sha'ani ya

Please Login or Register in order to submit comment