Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com
to download more hausa novels visits our site at www.NovelsHQ.com

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ

Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ

Telegram : https://t.me/NovelsHQ

[5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: *🧳 HASASHE🧳*



*Sabon littafin*



*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*


https://chat.whatsapp.com/Cg5ZwzwtDQ1A4W6sJ0mLgl

*Page 1*

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/100083170164617/posts/668798479235818/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*



Halifa ya kalli Abokan sa dake ta daga ɗinkin
Sulaiman daya daga cikin su , suna ta farin cikin gabatowar bikin Halifan wanda ya rage saura kwana tara, dai dai lokacin ma ƴan kai lefe suna can gidan su Bilki amarya.

Kati suke kasaftawa wanda za su fara rabon shi nan da kwana uku.
Wayar Halifa ta yi kara, cikin zumuɗi ya ciro da zaton amaryar ce dan yana ta dakon kiranta.
Hafsi ce yariyar Antysa wadda tana cikin yan rakiyar kai lefe.
Ya ɗaga da tambaya. •Hafsi har kun fito?” Muryoyi ya ji suna tashi kamar ana rigima. Ta katse shi da fadin “Uncle Halifa wallahi sun raina kayan nan. Kuma wai ba a sako kaya sa lalle ba, Baba ta fada musu yanzu ba a yin kayan sa lalle tunda turare ake fesawa sai suka ce su har yau suna rike da wannan al adar. Wai atamfa goma leshi biyar shadda biyu wannan harkar tsiya har ina…
“Me Umman su Bilki tace? Halifa ya katse Hafsi.
Tace “Cewa ta yi Allah ya so ba ta gayyato ƙawayanta gurin kaɓar lefen ba da ta sha kunya.
Wai a saka su ƙasan gado gara ace ba a yi lefen ba, kuma wai kayan tukwicin ba za a bamu ba wai tunda mun sha fiya wata a mai da lemun da cincin ba kuma zata bada ko nera ba.”
Halifa Ya sauke wata wawuyar ajiyar zuciya sannan yace ina Bilkisu? Tace “Gata can tana kuka.” Yace kai mata wayar, karki kashe.
Yana jiyo muryar ƙanwar mahaifiyar shi Baba tana cewa mun zata kayan nan al adace kuma kowa yana yin daidai ƙarfin sane.
Yaji lokacin da Bilkisu take cewa Hafsi bazan amshi wayar sa ba, sai kuma tace kawo dai. ya ji daya daga gare ni.
Ta shiga zazzaga masa bala’ i tana fadin ya bata mamaki ashe duk kiran sun shiga kasuwa da cewa ya yi aike Dubai da yake yi iya tsiyar da ya siya kenan aƙwati uku da gana masgo. Wallahi Halifa ka bani kunya.
Halifa ya share zufar fuskarshi ya kalli abokan shi da suka yi cirko cirko cikin sanyin murya yace Bilki kin raina waɗannan kayan?
Cike da gadara tace “Na raina su Halifa!! Yace kenan dan kaya ki ke sona? Tace “Halifa zan fison a ce ba a kawo ba sam!” Yace shike nan ku basu kayan su maido min. Tace. “Yanzu kuwa har katin daurin aurenka da ka bado dashi.
Bai kuma cewa komai ba ya kashe. Take ya soma kiran layin Baba.
Ta daga yace Baba ku dawo da kayan kawai,. Baba tace “Bari mu gani ko za a samu maslaha. Megidan muke jira . ” Yace Baba kawai ku rabu da su ku taho. Ta katse wayar tare fadin zan kira ka ga Antyn ka tana kira na.”
Ya dubi. Abokan sa da suka cika da al’ajabi yace ku kona katunan nan Wallahi na fasa. Suka ce ka a hankali
Suka fito suka zauna a dakalin kofar gidansu Sulaiman suna bashi baki tare da shawarin yadda ya kamata a yi. Bashir ne kadai ke goyon bayan shi dan yace ko shine fasawa zai yi.
Da idon ya ke binsu amma ba lallai yana fahimtar inda suka dosa ba. Zuciyar shi da kwakwalwar shi suna maimaita masa zafafan kalaman Bilki. Wanda kullum ta ke nuna mishi in bashi bazata iya rayuwa ba amma sai gashi akan lefe gaskiya Antynshi ta yi gaskiya da tace su gwada su. Gefe kuma yana tuna kudin da Abokan shi suka kashe na game da shirin fati wanda Bilkin ta matsa sai anyi. Iya Hall dubu dari uku su ka biya banda sauran abubuwa ga shi abokan nashi ba masu karfi bane.
Siririyar murya ta katse masa tunani, sannunku Yaya Sulaiman. Halifa baya ciikin waɗanda suka amsa, amma ya bita da kallo bazata fi shekara sha bakwai zuwa takwas ba, sanye da kayan islamiya waɗan da suka jeme suka kode kwadat.
Sai yaji bakın shi ya furta cewa ke zo. Ta dawo baya ta ce “Gani.” Ga zaton ta aiken ta zasu yi. Halifa yace "Zaki aure ni? Ta ce “Mene?” Yace nasan kinji amma bari in maimaita kuma ki bani amsa zaki aureni?
Tayi yar dariya zata wuce, yace na yi miki kama da wanda zai miki wasa? Su Sulaiman sun kasa magana dan mamaki. Domin dai sun san gaske Halifa baya cikin yanayin da zai yi wasa, ko da dama ba mai wasan bane.
Ta daga kai alamar eh. Halifa ya kalli Sulaiman “ina ne gidan su?” Sulaiman yace Asiya ki shiga gida. Sannan ya dubi Halifa “Dan Allah ka nutsu ka bari a sasanta waccan maganar yarinya nan kamar kanwata take kaga gidan su da namu katanga ta raba, ba zan so wata matsala ta same ta ba.
Halifa yace wallahi ita zan aura, kawai sanar dani ina Baban ta?
Sulaiman yace Halifa wannan halayyar ta ka ta saurin yanke hükünci kayi kokarin rabuwa da ita, Baban ta yana cikin gida yana fama da ciwon suger kafa daya ma gare shi an cire dayar, dan Allah kar ka sa su a damuwa. Yarinyar nan ga wurin da take tuyar awara can, yayar ta Sadiya bazawara ce mijinta ya mutu tana gidan da yaranta biyu , aikatau take zuwa gidan masu hali kusan su ke rike da gidan. Namijin su karamine tallar fiya wata yake zuwa a danja, tuni sun dai na boko sai islamiya. Na san ba irin matar da ka ke so bace Asiya.
Halifa ya mike, muje kamin sallama da Baban su kawai na canza ra ayi irin wadda nake son yar gayu yar birni wayayya baga shi kana gani abinda suka min ba . Usman ya dagawa Sulaiman hannu tare da fadin kar ka hana shi kaje kawai.
A soron gidan suka zauna a tabarma kallo daya zaka yi wa Baban ka tabbatar yana jin jiki. Bayan sun yi masa sannu, sai Halifa ya fara magana.
Baba dama ni ne nake son auren.. ya kalli Sulaiman dan baima san sunan ta ba. Sulaiman yace “Asiya ya gani yake so. Halifa ya amshe da fadin kuma Baba ina son nan da kwana tara in zai yiwu,aure na za ayi suka raina lefen maganar ta watse, in har ka amince min yanzu za a kawo kayan nan gidan nan Baba.”
Baban su Asiya ya yi dan tari, murya can kasa yace “Samari , ba a saurin yanke hukunci gaggawa wani lokacin daga shedan take, hakika naji dadi har da ka ga ‘ya ta ka ce kana so, amma ita tana son ka? Wannan abu na farko da ya kamata in sani. “. Halifa ya yi karaf yace a kira ta a tabbatar Baba amma ni ta fada min cewa ta amince.
Ya kalli Sulaiman “Leka kace. Asiya ta zo” Daidai lokacin tana ba Sadiya da Innar su labarin yadda su kayi da abokin Sulaiman kuma shine wanda ya yi sallama da Baba. Innarsu duk sai taji tsoro ya kamata domin bata taba ganin irin wannan abu ba.
Sadiya kuwa cewa ta yi Allah ya sa ya zama alkhairi tasan Sulaiman ba zai cutar da su ba.
Kiran da Sulaiman ya kwado cikin gidan shine ya sa hantar cikin Asiya ta juya har taji tana jin bayan gida. Innarsu tace “kije amma karki ce kin yarda kice wasa ki ke yi. Asiya tace to.
Ta tsuguna Baba yace Asiya kin yarda cewa zaki auri wannan yaron abokin Sulaiman? Ta daga ido ta kalle su, baza ta iya tantance waye a cikin su yanzun ba.
Ta sake sunkuyar da kai sai tace daga kai alamar eh ta kasa yin yadda Innarsu ta fada mata. Baba yace mata kin tabbata?
Ta sake daga kai, yace ta koma ciki,
Ya dube su. “Sulaiman tunda Asiya ta yarda kuma abokinka ne gaka ga shi ni bansan shi ba amma na sanka, duk wani bincike kai ne dama zan sa a gaba dan Asiya kanwarka ce, ina son ka bani wani tabbaci game da shi.”
Sulaiman yace Baba bansan wani mutum mai saukin kai kamar Halifa ba, sannan yana da ilmi duka biyu yana da sana’a kuma yana da a kida ahlissuna ne, ga ibada. Tare mukayi karatun sakandire mu hudun nan duk cikinmu ya fimu sukuni amma komai tare muke, ya yi ta taimaka mana a makaranta kuma har zuwa yanzu, bai canza mu ba. “
Baban Asiya yace “To shike nan amma wani hanzari ba gudu ba, ni dai kaga a yadda nake da ina da hali ma yanzu ace ina gadon Asibiti dan haka bani da sukunin aurar da ita a yanzu. Sai dai a sa lokaci Muga abinda Allah zai yi.” Halifa yace me cece damuwar Baba? Baban Asiya yace “kayan daki mana na yarta kuma kwanaki da jikina ya motsa lokacin da za a yanke kafar nan aka sai da su da sai a kaimata duk da suma ba na zamani bane. Itama lokacin sasantawa mukayi da yaron suka kawo kudi madadin lefe ya yi mata dan kala biyu na fitar biki muka hada da dan abinda ke hannunmu a ka rufa asiri.
Kai kuma gashi da lefanka a hannu bare a yi hakan.
Halifa ya gyara zama Baba ni dai yarinya nake so ba kaya ba. In katifa ta samu ko da sadakin ta ne ku sai mata Allah shine mai yalwatawa. Dadi ya rife Baba yace “To yaro na amince, sai dai ina son ka kawo magabatan ka. “
Halifa ya ce za su zo amma dai yau ina son ku karbi kayan ku ajiye gobe zan kawo su. Baba ya amince.
Suka fito suna mamki lamari kamar wasa yana neman zama gaske.
Halifa ya daga kiran da ke ta shigo wa wayar sa yana katsewa lokacin da suke magana da Baban Asiya. Baba ce, tace ina ta kira kazo mu tafi an sasanta da Abban su ya zo akan za a karo wası abubuwan kuma za a kawo kayan sa lalle Antyn ka ta amince akan haka. “
Halifa ya yi wata yar dariya takaici kamar yarda ya zata shima Abban su Bilki jeka na yi ka ne. Yace Amma kuna gidan har yanzu? Tace e sun bamu kayan tukwaicin. “. Yace ku dai jirani a gidan.
Ya dubi Bashir zo muje ku kuma ku jiramu a nan. Suka fita a layin zuwa inda ya aje mota kasancewar layin in an shigo da mota sai dai a fita ta baya to baya shigowa da mota.
Suna isa yace Bashir kayan nan zamu amso fa. Bashir yace “Shine daidai fa. “ Suka sallama Hafsi ta fito Tana ta tura baki tana fadin”Wallahi Uncle duk da haka suna ta yarda magana“
Yace kuje ke da Bashir ku kwaso min kayana.
Baba tana ‘A a. " yace kiyi hakuri wani gurin za a kai kayan. Abinda wani ya raina shi wani ke farin ciki da şamun shi.
Umman su Bilki ta ce ya haka ? Bashir yace za a canza ne sai a hado da karin. Suka sa kaya a mota Halifa yace a maida ruwan da lemon da cincin din.
Bashir yace baza a maida ba, kamar yadda na tabbatar baza su maido maka da kudin auren ka ba, banda hidin dimu da kayi mata.
Kamar wasa sai ga kaya ankai gidan su Asiya makota suka shigo aka amsa cikin girmamawa ba kayan tukwici amma Innar su Asiya ta kebe da Umman su Sulaiman ta ari dubu biyar ta basu....



*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: *🧳 HASASHE🧳*



*Sabon littafin*



*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*




*Page 2*

*Zaɓi biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*



Anty ta kalli Baba cike da tashin hankali tace, "Baba wai garin yaya kuka bar Halifa ya yi son zuciyar sa
Ya zai kai kaya gidan wata wadda ba a san ko wacece ba? Menene asali da tushenta shi kanshi na tabbata bai sani ba."

Baba ta numfasa tace " Habiba ni fa iyakacina kai kaya duk yadda ake ciki da yadda akayi gidan su Bilkisu munyi waya da ke, shi ya zo ya sa abokinshi da Hafsatu sune suka fito da kayan, mu muna waje ma. Anty ta kwalawa Hafsa kira, ta shigo tana cin cincin din da su ka ta ho da shi daga gidan su Bilkisu tana fadin ya yi dadi kyanshi da shayi.

Anty tace Wai Hafsa ya akayi ba ku dawo da kayan nan ba in ma bai amince da sharaɗin da akayi da gidan su Bilkisu ba? Hafsa tace "Anty kinsan Uncle Halifa babu wanda zai saurara in ya yi fushi. Wayata mutuwa ta yi shiyasa ban kira ki ba, ita kuma Baba katinta ya kare. Anty tace Ya Salam! Ta kai ta kawo a tsakar falon ta ce Baba zo kiga kayan da aka shirya tun farko za a kai gidan su Bilkisu.

Baba ta bi bayan Anty zuwa wani daki, akwatuna guda sha biyu blue da pink ga wasu adudu shake da kayan al ada an daure su da madaurin ado irin na zamani.

Cike da mamaki Baba tace Amma me ya hana a kai wadan nan? Hasashe na yi Baba.(, Anty ta cafke tambayar) . yadda suke nuna wa Halifa Kauna yarinyar nan kamar ta kawo kanta, sai na kalubalanci Halifa cewar yarinyar nan da bata kula yana samu ba da ba zata yi masa irin wannan son ba, sai yace sam ko bashi da ko sisi zata zauna da shi. Dan haka sai nace masa kar a kai kayanta wancan da aka kai na iyayenta ne da sun karba sun yi godiya sai a ba su mamaki da wannan.

Baba tace "Kash kinga rashin rabo amma kuma fa Habiba ba ku kyauta ba, ai wannan gwajin ba kowa zai cinye ba a wannan zamanin,domin 'ya' ya da iyayen su yanzu sun daura buri akan lefen nan."

Anty ta tabe baki ta ce, nifa dama yarinyar nan bata min ba idanunta sun bude da yawa wayo zata zo ta yi ta wa Halifa to shi bakar zuciya ce da shi, ga kafiya ko me zaki fada masa ba zai yarda ba sai ya gani da idanunsa shine na harba shi a haka bukata ta biya amma ya sake yin wani shashancin.

Baba tace "Su wadannan ai sai dai a kira musu babu, bashakka ba su da shi amma suna da mutunci kuma sunyi murna sosai." Anty ta zuba ido tana kallon Baba kamar wadda ta ji wata sabuwar kalmar da bata taba ji ba. Ta maimaita kalmar Babu!! Wai Baba kina nufin talakawa ne?!! Baba tace 'Yan uwana ne talakawa tilis kuwa amma ai wannan ba zai hana aure ba, domin baya cikin dalilan da suka hana a auri mace saboda shi."

Anty tace Baba muje in raka ki, Baba ku na da ne bazaki gane ina lamarin ya sa gaba ba, yanzu ba duniyar ku bace irin ta da, yanzu sai dan yanzu, wake harka da talauci,ai ko a tafiyar kan hanya bana fatan haduwa da malam talaka bare aure wannan maganar babu ita ko me zai yi, ashe gara ma su Bilki su da dan abin karyar rayuwa ce tai musu yawa, karyar tafi arzikin na su yawa, wannan babu fa ake kira tab.

Baba ta cika da mamaki, tace"Habiba yau she ki ka zama haka? " Anty ta yi yar dariya dama fa Baba baki sanni ba ganina ka wai kike yi. muje a kai ki ki hau adaidaita sahu ki koma gida ko menene kwa ji daga baya.

Hafsi ce ta tafi saka Baba a Napep Anty kuwa kamar ta yi hauka domin ta kira Halifa ta gaji amma bai daga ba. Daidai lokacin yana gaban wanda ya buga musu kati suna magana kan cewa ya sake buga musu wani amma ya canza sunan. Sulaiman ya kira ya mikawa mai buga katin wayar tare da fadin fada masa sunan yarinyar nan. Bayan ya fada masa sai Halifa ya amsa yace yawwa ka sanar da mahaifin yarinyar nan goben zan zo da magabatana a ko wane lokacin daga goman safe zuwa azahar, ita kuma ka fada mata zan zo da dare ya kamata ko sunan ta in rike.

Sulaiman ya sa dariya tare da fadin Halifa sai a barka. Insha Allah zan isar da duk sakunanka.

Kiran Anty ya sake shigowa yana kokari kiran masu Hall da za ayi fati. Ya daga bai bari ta yi magana ba, yace Anty kiyi hakuri gidan fa zan kwana komai dare dole zan dawo bari na gama da kacaniyar waje, bai yarda ta furta komai ba ya katse domin yasan duk damuwarta ya yanke shawara kai tsaye bai tuntube ta ba.

Ya fadawa wa masu Hall an fasa party su ba wani date din ya maida musu kudin su.

Anty ta rasa inda zata sa kanta ta danno number aminiyarta Hajiya Talatu domin neman dauki na shawarar abinyi cikin gaggawa.

Hajiya Talatu ta kalli sunan dake kan screen din wayar Sahiba ta furta tare da kallon yarta Ma u, tace "Ga matsiyaciyar nan tana kirana duk yadda aka yi neman fatawa ta zo, ai Habiba in har ta ci gaba da nuna min cewar bata gane wai ke nake son Halifa ya aura ba sai na koya mata yadda ake duniya."

Ma u ta taɓe baki Mama tace" Bar yar hau sai jininta ya yi sama zan daga in ta kira kamar sau biyar." Ma u ta sheke da dariya, tace Mama da Sahibarta. Hajiya Talatu tace yar Hassada ce tuntuni ta ke aiki akan Halifa wai kar ya yi aure sai wadda ta zaba masa tun ina shuna mata ke cikin Hikima har na furta mata cewa a hadaku kai tsaye ta ce bazakiyi masa ba, abin yamin ciwo amma na danne kuma abinda bata sani ba, wannan auren da Halifan zai yi tuni na saka Malam na shuri ya tarwatsa komai na san ma yanzun kiran nan labarin fasa auren zata bani da neman yaya zata yi. "

Ma u tace Wai shi Halifan ba kaninta bane me ya sa ta ke masa haka?
Hajiya Talatu tace, ' Dalilin da yasa na ke son ya aure ki ya kamata ki tambaya, kuma shine dai dalilin ta na hanashi auren sai ta nemo wadda ta ke so, dafa zai yiwu Hafsi zata bashi, dan dai muharraman juna ne. Ma u tace Wai duk menene dalilin ku?

Hajiya Talatu ta dauki wayar ina zuwa bari in daga yanzu na san tana wuya.

Cike da barkwanci tace Sahibata yi hakuri kin kira ina salla banyi la asar ba ga magariba ta doso kai. Anty ta ja tsaki "Wai yau she zaki tsaida sallah ne Sahiba. Ni ba wannan ba, kinsan auren Halifa ya wargaje?" Hajiya Talatu ta dau salati tare da danna Hansfree domin yarta Ma u taji. Anty ta ci gaba da fadin "Menene a bin yin salati ni ai gaba ta kaini dama ni na saita hakan kuma hakan nake son ya faru. Sai dai wata masifar yanzu haka ya kai kayan gidan su wata wadda ban santa ba, ya kuma ki sauraro bare. ma in fahimci komai dan insan ta ina zan bullo masa in ya shigo gidan."

Hajiya Talatu cikin mamaki tace Wai shi wannan yaron wane irin raini ne a tsakanin ku haka, na rasa sam bai maidake a bakin komai ba wallahi, banda haka ya Isa ya yanke irin wannan hukuncin kuma cikin gaggawa. Wai in tambaye ki Sahiba, kin yi masa aikin gurin Malam na daji kuwa?

Anty ta ja tsaki "Shin wai kin manta Halifan ne gurin Malamai nawa muka kai shi da ke, amma kamar ana shuka dusa. furar da Malam na kauye ya bani in dama masa, da yake gwanin fura ne a gabana ya shanye ta amma dan nan ko gezau."

Hajiya Talatu tace kira Malam na kusfa ya yi miki binciken gaggawa yanzu ki samu bayani, kinsan shi maza maza ne. Nima bari in kira na Shuri yanzu. Anty tace." To kirashi kin dai ki hada ni da shi. " Talatu tace Zan hada ku bari a gama wannan badakalar. Suna kashe waya Anty tace Matsiyaciya muguwa sai na gano shi in ma baki hada mu ba, kuma sai na gano dalilin ki na kin hadani da shi.

Itama Talatu a nata gefen cewa ta yi Bazan hada din ba mai mugun hali cinnaka baka San na gida ba, ni ce maganin ki.

Anty ta danna kiran Malam na kusfa a rude take fada masa cewa ya yi mata istihara yanzu a kan kaninta Halifa ta karanta masa komai yace bani mintuna, ta sake kiran wani malamin ta sanar da shi. Malamai ukun duk sun bukaci sunan yarinyar ko na Mahaifiyarta. rashin sanin sunan ya kawo tsaiko game da binciken dole sai zuwa gobe in Halifa ya shigo ya fada mata sunan domin kowa ya ce mata ya ga auren Halifa Amma baiga matar ba.

Halifa ya shiga gidan cike da gajiya ga damuwar abinda Bilkisu ta yi masa, ya kalli bangaren Anty bazashi yanzu ba ta kara masa wani zafin bandaki ya fada ya sakar wa jikinsa shawa sanyin ruwan ya ratsa shi, Har ya ji kamar zazzabi zai rufe shi ya fito ya dauki jallabiyya ya zura, ya nufi gadon sa zai kwanta idanunsa suka sauka kan hoton Bilki wanda ya kafa shi domin sanyaya idanunsa a duk lokacin da ya kalla. Ya isa gurin hoton cikin rangaji ya sa hannu ya ciro. kalamanta suna kaikawo a zuciyar sa ya nufi kwandon shara zai saka ya yin da wasu hawayen takaici suka sulalo akan kumatun shi.
Kafadar shi ya ji an dafa lokaci guda kuma ta soma magana.
"Dan uwana ka bani zuwa gobe zan gyara komai tsakanin ka da Bilki tunda ka zubda hawaye a kanta lallai sai ta karbi hukunci, ina son ka auro ta kuma ka rama abinda ta yi maka."

Ya dubi Anty bai ji ko matsin ta ba bare takun ta,sai kalamanta da suka dirar masa. Ya sa hannu ya sauke nata hannun a Kafadar sa Sannan yace Kar kiji cewa kin damu Anty, bana bukatar cutar da ita, na gode da hasashe ki domin kadan ya rage inyi kitso da kwarkwata na samu madadin ta ina hasashen alkhairi ga sabuwar yarinyar da na kaiwa kaya kuma zai tabbata khairan insha Allah. Ya kai karshe maganar tare da zama bakin gado.

Anty tace "Halifa ina kasan wannan yarinyar mecece nasabarta, menene matakin karatunta, wace gogewa gare ta game da duniya, wacce yadda kai mata?"

Ya zame ya kwanta, tare da fadin

Please Login or Register in order to submit comment