Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni ban isa ba sam bani da wata daraja a idon ka. Sai yadda ka ke so? Kala baice ba ya nufi hanyar fita. Da gudu ta nufi Dadi ta kira shi tace yabi Halifa. Ko kafin su fito har ya dauki Keke napep tunda bakin titi Asibitin yake.
Dady yace "Wai me kika fada masa ne haka gaba daya Yaron nan a rikice yake fa tun da ya samu matsala da yarinyar nan wai ma me ya kawo ta ne.?" Cike da jin haushi Anty tace Kaga dan Allah ka sama min lafiya ina ce muna tare da Kai ta shigo sai kuma ta ja tsaki ta fice daga Asibitin domin bata bukatar Halifa ya shiga gida saboda binne binnen Sahiba.
Asiya ta wayi gari kamar mara lafiya domin bata samu kiran Halifa ba, ga kuma batun waccan da ta kira ta duk da tana ta son ta nuna wai kamar abin bai dame ta ba. Gabanta yana tsananta faduwa idan ta tuno da wani mafarki da tayi wai wasu macizai suna ta kaiwa Halifa sara shi kuma yana ta fesa musu wuta da bakin shi.
Ta shiga gidan su Sulaiman ta gaida mahaifiyar su sannan ta ce, ko Yaya Sulaiman ya na ciki? Ya fito ta gaida shi da girmamawa. Yace ya aka yi ne Asiya ta nufo waye sai ya biyo ta. Ta tsaya a soro ta dube shi cike da kunya tace Amma ka samu labarin Yaya Halifa kuwa? Yace "Me ya faru jiya dai kafin ya zo gurinki ya biyo shagona yace in amshi dinkunan ki na biki nace masa sai yau zan saka yarinyar shagona ta zo ta gwada ki ta amshi kayan nan da shabiyu ta ke zuwa."
Asiya tace jiya ya bani wayarsa ka gan ta, kuma yace zai kira ni, sannan kuma bai kira ba. sai naji kuma kamar wani abu ne ya faru da shi. Sulaiman ya yi murmushi," Ki kirashi shi mana to da wannan Wayar." Ta girgiza kai bayan ma ban iya wayar ba kuma akwai lambobin sirri, banda hakan ma bai bani Umarnin in kira ba, yace shine zai kira.
Sulaiman ya ce Ina zuwa. Ya dakko wayar shi ya danna kiran Halifa. Bayan sun gaisa yace kana ina ne haka.? Halifa yace "Yanzu na shigo gida Asibiti na kwana jiya bayan na bar unguwar ku sai a mai nake ta yi wai ance Ulcer ce." Sulaiman yace Subhanallah Allah ya baka lafiya. Shiyasa mutuniyar tazo min ka ga ta nan wai taji a jikinta kamar da wani abu kace zaka kirata baka kira ba. Halifa Yace" Allah sarki kace zan kirata.
Bilkisu ta dauki abincin ta cikin kunan rai ta nufi gida ba a taba wulakanta ta kamar haka ba. Suka yi jugum ita da Uwar suna lissafin mafita. Ina zata sami malami me zafin hannu wanda aikin shi zai zama sha yanzu magani yanzu. Can ta mike tare da fadin duk wanda ya ci tuwa dani miyar ma baisha ba. Halifa zai gane shayi ruwa ne tashi mu tafi indai na haifu sai Halifa ya zama abin sarrafawar ki.
Hafsi ta kawo masa wani makullin domin bai San yadda ya yi da na hannun shi ba jiya. Anty ta shigo ta kwada masa kira tun daga bakin gate ya tsaya bai bude dakin ba, tace Halifa ka fita waje gidannan an binne wasu asirai saboda kai bari a tone ko kaje gidan Bros tunda shi kadai ne na dan wani lokaci. Halifa ya yi murmushin takaici ya fara gajiya da wadannan zantukan, shi baima fahimci me take fada ba.
Anty kije ciki kawai ki huta dan Allah bana gane me kike cewa. Tace Halifa kana cusa min bakin ciki da wannan gaddamar taka, dan Allah iya yau ka saurare ni in ceci rayuwar ka. an binne mugayan asirai dan a cutar da kai a gidan nan. Yace "Anty waye shi a gidan nan da zai min wannan mijinki ko yayanki haba Anty dan Allah karki ruda kanki mana."
Hajiya Talatu ta kara so tana fadin sannu mai jiki, yanzu nake cewa Sahiba nace mata zani duba ka sai suka wuce bata tashe ni ba. Halifa yace na samu sauki sosai. Anty tace Halifa In mutum zai cuce ka ai ba sai na gida ba, amma tabbas gidannan anyi binne binne saboda kai, ta kalli Hajiya Talatu wadda ta zaro ido cikin faduwa gaba tana sake tambayar Anty waye kuma zai masa hakan.? Anty ta yi murmushin yake, Sahiba kenan ke dai ki ga mutum ni dai kawai ya fita. Halifa ya dafa kafadar Anty yace kiyi hakuri babu wani abu da zai same ni wanda Allah bai kaddara min ba, karyar mutum ko aljani. Ya jiya ya bude dakinsa ya shige.
Shirin kasuwa ya yi yana fitowa falonsa Hafsi na kawo masa kunu yace a sa sugar a ciki? Tace "E" Yace je ki kawo min mara sugar. Tace "Sai dai a dama." Yace to ayi hakan bakina babu dandano. Kafin ta kawo sai ya yanke shawara kiran Asiya.
Tana kwance kan yar yaloluwar tabar marta baza ta iya fassara halin da zuciyar ta ke ciki game da Halifa ba, amma dai da ace akwai dama to zata so ta ganshi ta ga jikin shi ta kuma bashi wata kulawa wadda zai samu sauki. Kamar daga sama wayar ta soma kida, ta dauka da rawar hannu sannan ta sa a ku ne bayan ta tashi zaune, sai kuma abin ya motsa wato jin kan. Tayi sallama a natse, ya amsa, ta gaida shi gami da tambayar jiki, yace da sauki. Tayi dan dim saboda yadda ta ke jin muryar shi tana ratsa dodon kunnen ta. Yace to ya shirye shirye nace Sulaiman ya zo ya amshi kayanki. Ta lumshe ido,. "Ya fada min dazu zan bashi." Yace kin gano nawa ne ake yin gyaran jikin? Tace a a ai ban ma san wa zan tambaya ba, domin Maman Annur a bikin ta ita ta yi a gida na kurkur. Yace to bari zan bincika sai in kai ki ko baza ki bini ba? Ta yi yar dariya. Bana tunani su Baba za su hanani zuwa tunda kai ne. Yayi murmushi salon maganar ta yana birge shi. Sai me ki ke bukata bayan wannan kamar paty ko Walima haka? Kamar munyi wannan maganar ranar da ka zo nace saboda jikin Baba baza yi komai ba, garama dai walimar tunda akwai lada a cikin ta." Halifa yace haka ne yarinya da hankalin manya. Yaci gaba da fadin ina fatan baki ji haushin abinda masu shagon nan suka fada Akan ki ba jiya? Ta yi yar dariya " Zan iya tambayar ka? " Yace Sosai ina sauraron ki. Tace," Abinda suka fada ya kankare wani abu na daga kima ta a gurinka?" Sam Sam sai ma karuwa da ta yi bayan sun bani tabbacin da wuya a samu wadda tafiki hankali a cikin kaf unguwar . Ya fada cike da jin dadin hirar ta su. Ta yi yar dariya. Kasan ya nake jin kaina daga ranar da kafurtamin kamar aure? Yace a a, tace duk wata mace in dai ta wannan karnin namu ne farace ko baka mai kudi ko mai sarauta bata kaini ba. Halifa ya sa dariya lokacin Hafsi ta shigo ta kawo masa kunu. da hannu ya yi mata alamar ta aje ta fita ba tare da ya saurari abinda Anty ta aiko a fada masa ba, ko kadan baya son abinda zai katse masu hira. Kina nufin duk kin fisu? "Tace" Nisa sosai nake Kallon na yiwa kowace mace, bafa alfahari bane tuntuni inajin hakan a raina, samun ka a matsayin miji ya tabbatar min cewa yadda na ke Kallon kaina haka ne, domin na samu mijin da shima babu wani namiji sama da shi a cikin karninmu kaga na kara yi wa mata tazara. " Mamaki ya cika Halifa yace In tambaye ki? Tace" Baka bukatar izni ranka ya dade." Yace kina karanta littafin soyayya? Ta ce ban taba ba, amma in hakan zai fara ta maka zan fara." Yace ina mamakin yadda ki ka iya magana haka, farko na miki kallon mai shiru wadda magana bata dame ta ba. Asiya ta yi yar dariyar kirsa wadda hakan ke sa tsigar jikin Halifa tashi yarr." Kasan fa shiyasa ba kyau ka yanke wa mutum hukunci daga ka kalle shi akwai kuskure, sai dai kuma nima ina magana ne kurum a gurin da maganar tawa take da muhimmaci, kaga ai bai kyautu mutum ya yi asarar kalaman sa ba musamman a inda basu da amfani ko?" Yace Haka ne. To wai kin fara jin wani abu game da ni kuwa?" Kamar me kenan? " Ya gyara zama so nawa kika tuna ni daga jiya zuwa yau.? Ta numfasa sannan ta lumshe ido. Zan yi karya ida na fadin adadin domin da tunanin ka zuciya ta tare su ke bugawa, harma na tambayi kaina ko wannan shine son da kake magana, in kuwa shine Yaya Halifa ya min kamun kazar kuku, kasan Allah da girma yake yau kowa ya jiki yace min a gidan nan, to alamun rashin lafiya ya bayyana kanshi a gare ni, yanzu haka fa kwance nake ka kira ni, Innarmu ta aiki Abba ya siya min magani. Kasan abin da nake mamaki yanzu haka bai dawo sayen magani ba kaga har na warke da ka kira ni..
Halifa ya saki dariyar da bai san yana yin irinta ba. Yace Asiya kin iya wasa. Tace "Kila in na rantse da girma Ubangiji zaka yarda ba wasa nake ba a cikin duk maganganu na yanzu haka da zan ganka bansan kuma me zanji ba." Yace ko in zo kasuwa zanje yau. Kaje kasuwar ka, amma zan roki wata alfarma a gurinka. * Yace Na miki. Tace "Zaka iya tunani duk awa daya ko ta yi yawa?" Halifa yace zan kokarta. Amma baki tambaye ni ko na cire son wata ba da nace zan cire? Asiya ta tashi zaune. Kar ka wahalar da kanka gurin cirewa nice mai hakkin cire maka shi. " Yarinyar ta tashi kan Halifa sosai wanda har ya kasa shan kunun ya fita ya rufe dakin ya bar kunun a ciki, sakamakon yana tafe suna wayar har ya isa kasuwa sai da yaran shi suka soma bude shagon ya ce mata zai kira anjima.
Famcenter a nan ne Halifa yake kasuwancin sai da waya da kayan gyaranta. Shaguna ne guda uku a hade shake da kaya kuma sari yake bayarwa domin kai tsaye daga Chaina da Dubai ya ke kawo su. Da shi yake zuwa daga baya kuma sai dai oder tunda ya shahara.
Tabbas Halifa ya gaji dukiya daga gurin mahaifi sa Alhaji Umaru Madugu wanda tsohon attajiri ne, haka kuma 'Yan uwan shi da suke uba daya duk attajirai ne yanzu haka. Gidaje kawai Halifa yana da sama da goma banda wanda suke ciki da su Anty hatta wanda Bros ya zauna da matar sa na Halifa ne. Banda stor stor na aje kaya da ake haya, Shaguna a kwari da Singa duk ya mallaka. Saidai shi Sam bai taba damun kansa ba tun da aka tsakura mishi mikiyan a shirin bayan ya kammala digirin shi a Jami ar Bayero ta Kano ya fara kasuwanci lokacin ne aka ba Bros aron a shirin din shima ya shiga kwari. Duk da Anty ta na yadda take so da kudin Halifa amma ta kasa wadata kullum ya zata mallaki fin haka saboda akwai lauyoyin su na iyalin gidan mahaifinsa masu lura da shigi da fice kudin.
Halifa ke biyawa yaranta kudin makaranta kuma ya kawo abincin gidan Dadi cefane kawai yake yi, har su Nihal da Nur yaran Bros tunda suka dawo gidan lokacin da Anty ta sa a saki Uwar su da za a sasu makaranta Halifa ta fadawa ya bada kudi aka kai su, Bros lokacin ya samu karayar arziki Anty ta ce matar sa ce Malamanta suka fada mata, dan haka tace ai ta zage ta dole a sake ta. Halifa na cikin wadanda suka taso Bros saboda shi ya dogara akan inhar ta zagi mahaifiyar sa to ta cancanci saki, shine Bros ya yi kamar ya sake ta. Anty ta kara imani ganin yadda harkokin suka sake budewa Bros bayan ya saki matar sa kamar yadda ta ke zato.
Duk wani hakkin Allah kamar zakka Halifa baya Wasa gurin cireta, ga sadaka kullum a kasuwa akwai mutanan da shi suka dogara banda daidai kun almajirai. Baya yin rayuwar karya ko kuma ya nuna kansa a me kudi ko kamar mara shi. Har zuwa yanzu da ake daf da daurin aure Asiya bata san waye Halifa ba, abinda take hasashe a ranta shine yana neman kuma ya samun abinda zai iya rike ta da shi, ko Keke bata sa rai ya na da shi ba bare wata mota.
Hajiya Talatu ta shiga Rudani ganin magani bai yi tasiri a gurin Halifa ba, wannan ya sa ta fadawa Sahibar ta zata je wata gaisuwa a Wudil ta juya ta nufi Zariya gurin Malam na shuri, ita kuwa Anty sai ta yarda cewa Malamanta sun turo Aljanu sun cire bison kamar yadda suka yi mata Alkawari. Sai da suka shiga Adaidaita sahu Sannan Anty ta kallo Hafsi in munje fage zaki gane gidan da kuka kai Kaya? Gaskiya in dai ba ta layin ya shiga ba to gaskiya bazan gane ba. Dan Adaidaita yace "Hajiya Fage tana da yawa in baku San gidan ba ku kira waya." Anty tace kira Halifa ki masa siyasa ya fada mana sunan layin. Ta kira ya kai sau biyar bai daga ba, dan haka suka yita yawo, sai Hafsi ta ga kamar layin ne da sunje sai ta ga ba nan bane.. Cikin sa a ta hango Sulaiman a shago suna ta dinki shida yaran sa. Tace yawwa Anty ga Sulaiman can abokin nan na Uncle Halifa kinsan makotan su yarinyar ne. Tace Shike nan wahalarmu ta kare, bari mu same shi. Dansahu yace kodai tawa wahalar ce ta kare. Anty ta Kalle shi, wai kai da kake ta damun mutane da mita, ba kudi ka fito ne ba? Yace "Sune Baba." Tace to in zamu kai wata muna yawo baka da matsala shiyasa ko farashi ban tambaya ba dan haka ka daina damu na. Sulaiman ganin Hafsi ya gane su. Bayan sun gaisa Anty tace gidan su amaryar Halifa muka kasa ganewa, yace Allah Sarki muje in kai ku. Ya fito yana saka takalmi.



*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

[5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: ____
Daga ni sai Baba a gidan Inna da Maman Annur sunje kasuwar kurmi za sai min tukwane da ɗan tsince tsince.
Ina hura gawayi zan dora taliya wadda Halifa ya sai mana ajiya, kamar yadda Inna ta barmin sallahu tunda yanzu na daina awara su kuma sai bayan biki za su ci gaba.

Cike nake da shauƙi da kuma nishadi nan da wasu kwanaki kadan ina gida na kuma zan ɗora girki nawa na kaina ba tare da wani ya bani Umarni yin abinda zan yi ba. Ko iya haka aure ni ima ne ba shakka. Allah kenan duk yadda ya so haka yake faruwa kamar yadda na kabari bai san cewa zai mutuba ya wayi gari ya ganshi an turbuda shi cikin kasa, haka ma wanda zai yi aure ko haihuwa sai dai mutum ya yi hasashe.

Fargaba takan darsu a zuciyata idan na tuna zan koma rayuwa ta har abada da mutanan da ban san su ba, ko sati ban yi da sanin abokin rayuwata ba amma ina yi masa kyakyawan zato.

Sallama ce ta katse Asiya daga tunani ta amsa tare mikewa tana yi musu sannu da zuwa, ba Wai dan ta san su ba, sai dan girmamawa.
Sai dai kuma kallon da taga baƙin suna yiwa ko ina na gidan nasu tare da yatsina fuska gami da taɓe baki shine abinda ya fi daure mata kai. Ba shakka waɗannan ba alkairi ya kawo su ba. Ta ɗarsa haka a zuciyar ta,. "Ina matar gidan?" Anty ta tambaya cikin daga murya da izgilanci. Bata nan Asiya ta bata amsa cike da tsoro. Anty tace "Ina amaryar da Halifa zai aura? " Asiya ta ji gabanta ya yi wata mummunan faduwa, ta sunkuyar da kai alamun kunya. Hafsi tace Innalillahi kar dai ke ce? Asiya ta kalli Hafsi ta kasa magana. Hafsi ta matso ta kama fuskar Asiya ta dago tace kalli Anty munshiga uku wannan ai bakwaini ce kalli ta, ta kama hannun Asiya ta saki kamar kara. Gaskiya dai Anty kiyi wani abu dan kuwa karshen abin fadi ne zai faru a zur"iar mu. Baba daga cikin daki ya yi karfin hali yace "Wai su waye ke magana?" Mu ne Anty ta amsa tare da nufar gurin tana cewa " Wai dama megidan yana nan?" Bakin ƙofa ta tsaya tare da toshe hanci " Wai ɗaɗɗaɗoya, ta fada tana duban Asiya. Ta ci gaba Baba zuwa nayi in bada sako a baka ashe ma kana gidan to hakan ya yi, Baba Kana ji? Ƙanina dai ba zai auri wannan yarinyar taka ba haka sai kace sullen kara, Haka a tsiyace, kwarya ta bi kwarya wannan ai matar yan dako ce. ba irin Halifa ba shi ba ajinta bane. " Baba yace Au haka ne? To ko ya makance ne lokacin da yazo yana neman a bashi ita? Ya cije lefe dan karfin Hali ya ci gaba da fadin, to kije ki ce da yaron ya zo da kansa ya ce ya fasa kamar yadda ya zo yace yana so, ko da kike uwarsa ce ba yayarsa ba. Ko kuma ki turo waliyyan sa, wannan yarinyar a yanzu matarsa ce domin na bashi.
Anty tace zanga kuwa yadda za a fara tusa ta hura wuta. Dole ka bashi mana kullum burin matsiyaci shine ya hada kafada da mai arziki. Na san ta inda zan biyo wannan auren bazai taba faruwa ba. Baba Yace Ko bana raye za a daura.
Ta dawo gaban Asiya "Ke kuma munafuka mai kama da muciya in har kika yarda kaddara ta kawo ki Auren Halifa zaki gwammaci kida da karatu.. Asiya jiki na bari tace Kuyi hakuri. Hafsi tace Ke in har kika shigo zuri armu Ba Anty ba ko ni sai na gallabi rayuwar ki. Ta yi gaba tana faɗin Anty waɗannan ba su kai kiyi cacar baki da su ba, ki zo muje ni amai nake ji ma.

Suna fita ta shiga gurin Baba da sauri tana fadin Baba Dan Allah a janye maganar Auren nan ni tsoro nake ji. Yace "Shigo Asiya," Ta shiga ta zauna tana kuka, ya ce "Share hawayen ki. Ta share, ya ci gaba da fadin, wannan shine ya nuna cewa akwai alkairi a cikin wannan Auren na ki, kin san dalilin?" Ya jeho mata tambaya. Ta girgiza kai. Yace " Duk abinda ya fara da ƙalubale ba shakka nasara ce ke biyo baya. Babu abinda hargaginta zai sa, ko ya hana dan haka ko Innar ku karki sake ki fada mata in su dawo, ki bar abin tsakaninmu." Asiya tace Saboda me Baba ai da ka bari na fada musu, wallahi duk na tsorata. Yace" Asiya alkairi ake fada ba sharri ba, ki zama mai fadin alkairi karki tada mata hankali,kinji ko yar albarka. Ki fara da shanye kalubalen ki, ki koyi aje sirrin miji ki a kirjinki ki yarda Allah shine mai maganin duk wata masifa. da haka zaki zama Jaruma ranar da ki ka rasa Innarki ko ni zaki iya daukan damuwar ki, Asiya tace to Baba bazan
fada mata ba insha Allah.

*** *** ***

Anty ta wuce gidan Baffa Halifa wannan shine karo na farko da taje gidan sa, domin tana mugun Jin haushinsa yadda suka saka lauyoyi a kan dukiyar Halifa in tana son wani abu dole sai Halifa ya saka hannu anbi wasu kaidojin banza, karshe ace aro ne, har sai in Halifa yace mata ya yafe. ita da kullum burinta yadda zata hau kan dukiyar ta barje gumin ta yadda take so. Taje America taje Dubai irin na wayayyun mata masu kafasiti da aji.
Bayan sun gaisa tace Baffan Halifa zuwa nayi a yiwa Halifa fada kuma a bashi shawara, gaskiya yanzu duk ya canza, baya saurarona ko wannan Auren da ya rungumo na waccan yar matsiyatan bai kamace shi ba, yarinyar bata ma da lafiya aljanu gare ta naje na bincika har unguwar sun rufe masa ne. Baffa Yace "Kin tabatta haka ne? Tace ko kaffara ba zanyi ba inna rantse. Ance su ke tsotseta in sun tashi kuwa hauka tuburan. Baffa yace" In maganar nan ta tabbata ba shakka basu kyauta ba sun yi abinda Manzo Rahma ya hana a yi, sun boye aibinta a neman aure. Amma In Dan su ba masu kudi bane wannan baya cikin sharadin da musulunci ya saka akan aure.
Anty tace shiyasa nace Bari inzo in fada maka tun wuri kar ayi aikin nadama. Yace "Ba damuwa zan kira shi a waya domin ya zo ya janye wannan maganar. Anty ta fashe da kuka tana fadin Na gode Baffa dama na san kai kadai ne zaka taimake ni in cika a amanar da mahaifiyarmu ta barmin.
Yace Dai na kuka ni ba zan barshi da kanshi ba, duk taurin kansa sai ya hakura. ai mu iyayensa ne, Anty ta bar gidan Baffa cike da kwarin gwiwa.


Asiya ta kalli wayar Halifa dake ringing shine yake kira, a sanyaye ta dauka muryarta can kasa ta gaishe shi. Yace " Amma dai kina lafiya?" Ta ce to lafiya lau.zance. Yace "Naji muryar ki wani iri bayan ba haka muka rabu ba." Tace An tsoratani ne Yaya, wai kana ganin idan. na zo gurinka da zama zan zama cikin aminci kuwa? Cikin mamaki
Yace "Zaki zama cikin aminci bana shakkar haka insha Allah." Ta sauke wata ajiyar zuciya mai karfi. Sai yanzu ta da ji sanyi a ranta. Yace wani Abu ya faru daga jin yadda ki ke magana sanar da ni. Asiya tace ya wuce ai tunda na samu tabbacin cewa barazana ce aka zo aka min. ina rokon ka kar ka ce sai ka matsa na fada maka. Yace "Shikenan zan dai kira ki anjima Baffa na ke kira bari na daga.

Bayan sun gaisa yace Umaru wai kuwa kayi bincike game da yarinyar nan da ka canza? Halifa yace sosai kuwa. Baffa yace ciwon hauka fa aka ce tana fama da shi. Halifa yace Baffa gaskiya da Sulaiman zai fada min Sannan ba abokin ka ne makoci su ba, ka buga masa waya domin ka samu tabbaci. Baffa ya yarda da haka.
Mamaki ya kama Halifa duk yadda aka yi wani Abu yana faruwa in ya auna kalaman Asiya da na Baffa. Da wannan tunanin ya kai gida. Yarinyar nan ya fara karo da ita bayan ya fito a mota wato Ma u tsigar jikinshi

Please Login or Register in order to submit comment