Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cike da son nuna kulawar ta. Hafsi ta kalle ta kallon ke kuma a su wa, Sannan ta fice.
Halifa wanda bai kula da abinda Hafsi ta yi ba yana bude abincin yace sunan ta Hafsatu muna ce mata Hafsi. Asiya tace Yawwa na rike.

Bayan sun karya Asiya ta na ta jin kuyar cin abinci gaban Halifa har yana tsokanarta da cewa a haka za mu yi sallar ma auratan da ki ke ta fada? Bayan kina jin kunya? Tace to salla menene damuwarta ita kuma.? Yace shikenan har na matsu dare ya yi muyi salla da sauran ibadu. " Asiya ta shiga daki tana yar dariya.


*** *** ***

Wayar ta shiga ruri ta dakko sunan. Sabon malamin ta ne, ta kalli Talatu wadda ke gyara farce, Anti ta kai makura da gajiya da Talatu lokuta da dama tana son sirri amma ta zo ta yi mata katutu, ya ma zata amsa kiran Malam a gaban ta, bayan bata son ta san shi. Wayar ki ake kira fa. Talatu ta fada tare da kokarin leka fuskar wayar. Anty ta dauke wayarta tare da fadin bana son tsegumi Talatu dan Allah tunda an gama biki sai ku hada kayanku ku koma gida kin bar mijinki shi kadai gashi kin gama da shi ba zai iya cewa kala ba.

Talatu ta taba baki shege yi da mai zina, Allah ya sa kema dai naki Mijin a shanye yake, au korarmu ki ke yi ne, to gobe zamu daga mu bar miki gidan ki. Talatu ta fada tana danna Rikodin na wayarta. Ta aje wayar ta mike bari ince Ma u ta hada kayan ta mu wuce.

Tana fita. Anty ta kira Malam suka gai sa, tace yanzu na ga missed call Malam. Yace Kinga da zaki yi wani abu da kun samu biyan bukata da daukaka sai dai yana da wahala. Anty tace menene zanyi? Malam yace ki kawo min yarinyar nan gobe da safe, ya zama ni ne zan fara kusantar ta akwai wani lakani da rauhanai suka bani yanzu sunce in yi biyan bukata da sabuwar Amarya mai irin tauraron ta, da maijego sabuwar haihuwa da kuma tsohuwa muharramata ko Mahaifiyata ko wata yar uwarta. In na yin wannan aikin Hajiya zan samu wasu damarmaki ne da iko, zan iya yi miki aikin da in kina bukatar dukiyar Halifa ta dawo hannunki kaf zata dawo ba lauyoyi ba ko alkalai ne sai sun kawo komai da kan su na game da dukiyar shi sun baki matsawar ki ka tambaya za su baki, kuma ba wanda zai taba tambayar ki ina wata kadara ta sa.

Sannan zaki zama mai shahara a Duniya ta yadda ko ina za a sa ki, gwamnati sai ta so ta yi hulda da ke ko da kuwa ba wani Abu da zaki amfana mata." Anty ta mike cike da jin dadi Malam ka tabbatar hakan da ka fada za su faru? Yace "Kar ki yi wata shakka hakan zai bata mana aiki. Abinda kawai nake son ji zaki kawota?" Anty tace to ina zaka samu sauran Matan? Yace " Duk na samu, domin matar ɗana ta haihu zan yi amfani da ita kuma ina da Uwa ina da kanwar ta samu daya cikin su ba zai min wahala ba, samun sabuwar Amarya ma ba zai min wahala ba mai irin taurarin ta ne wahala dan baifi kamar a watsa biyar a cikin dubu ba, haka ta ke, yanzu dan ba a bude taurarinta ba ne shiyasa bazan gane ba, yana kwanciya da ita kuwa shikenan ya bude mata taurari kuma tauraron sa da nata tamkar bawa ne da ubangidan shi.kuna kallo zaku hakura dashi. Dan haka ni zan bude su taurarin na ta." Anty tace na gane zan San yarda zanyi tun yau ba sai goben ba in kawo ta. Sai dai ina tsoron karta zo ta fada masa. Ya saki dariya mai karfi. Zan mantar da ita komai, banda wannan tauraron nata ai kasheta zan yi kuma ba wanda zai tambayi ina take har abada.

Anty tace to Malam ina godiya in mun samu zuwa yau in kuma sai goben to ba matsala? Yace "Ba damuwa kar a wuce gobe dai.


*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[6/9, 10:43] Ummi Tandama😇: Anty ta yi sallama a kofar dakin Asiya, Halifa ne ya amsa, gabanta ya dan fadi amma saita dake, yace ki shigo Anty mana. Ta shiga tana waige waige," Ina yarinyar nan ta ke?" Yace tana bandaki bari na kira ta. Tace Dama so nake anjima idan rana ta kara sanyi zan kai ta gidan Baaba harda Baffanku Dan 'yan uwanta ba su kai ta ba, sun bada sallahu cewa a kaita, to bana son abin ya ja lokaci ya zama shiri ririta." Halifa yace Anty ki barshi kawai ni sai muje tare in kaita na hutar da ke. Da sauri tace, " Wa ya fada maka ana haka? Ai wannan al adace mai girman sai a dorawa iyayenta laifi ace sun rai na danginka , kuma bayan sun bar sallahu. Dan haka ni zan kaita. " Halifa yace to ba matsala ni sai in kai ku. Da sauri tace. "Sai kuma ya zama abin magana, ba a zuwa da Ango." Halifa yace a musulinci ne zai zama abin maganar ko a me? Anty wani abin ma ku mata kuke ruruta shi, to yanzu sai a kira Bros ya kai ku ko? Tace Dan Allah ka samin ido kawai bazan jera da shi ba, dan shima ina cike da shi na tura mishi lambar yarinyar da na samo mishi yaki kiranta, sai yana ce min wai wayar bata shiga kuma karya ne. Halifa ya ce Anty Dan Allah ki kyale Bros da batun auren nan, kawai ki bari ya zaba da kansa, ko zamanin ku fa ba ayi muku haka ba.

Karo na farko da Halifa ya kware mata baya akan maganar Bros. Ta dan yi dim Dan tana samun kwarin gwiwa daga gunsa da kuma tirsasa Bros din ta gurin shi. Tace "Bar maganar shi kawai ka fada mata in ta fito sai ta shirya. Yace to ba damuwa.

Asiya tana toilet ta gama ta kasa Floshing tana ta tarar ruwa tana makawa amma yaki wucewa duka, bata san Halifa ya shigo ba. Sai taji maganar shi a dakin yana fadin lafiya kuwa fin minti arba in. Ta leko ta bata rai ni kam in da wani ban daki a tsakar gida can zan na shiga. Ta fada tana tura baki cike da shagwaba. Yace to wannan menene matsalar shi?" Tace ina ta zuba ruwa amma yaki wanke wa. Halifa ya gane fuloshin ne matsalar, yace" Kuma kin danna gurin zubowar ruwa?" Tace ina ne gurin? Ya nufo ban ɗakin ta kulle da sauri tace ka fada min yace to ki danna wani guri a sama tukunyar nan ta makale. Allah ya ba Asiya sa"'a ta danna sai taji ruwa da gudu ya wuce da bayan gidan nata. Ta sauke ajiyan zuciya tare da fadin Allah ya kyauta rashin sani.

Ta fito ban ɗakin domin ta fesa turare duk da ba wari amma sai tana jin kunyar fita. Daga can cikin falo ta jiyo ana magana kamar muryar Maman Annur da sauri ta leko, su ne kuwa da yan layin su wasu yan mata. Murna Asiya kamar ta cinye su. Halifa ya gaisa da su ya koma daki, suka zauna ta bude firji ta dakko musu ruwan roba da lemo, suna ta Kallon ta cike da shi awa. Ta nufi dakin tana ce musu ina zuwa. Yana zaune bakin gado yana danna waya, tana shiga kamar ya dan razana ya aje wayar ta share kamar bata kula ba, tace zan dafa musu abinci. Yace "To ai kinga ban kawo kayan abinci ba, kawai ki kawo masu kayan tea da baredi kajin da baki ci ba suna firji sai ki kunna gas ki sa su a oven su yi zafi." Tace Ban iya. ba fa ko kunna gas ban taba yi ba, kuma bansan ina ne ma oven din ba. Yace muje in nuna miki ya koya mata komai sannan yace yar kauye, cike da tsokana. Tace naji Dan birni na samu karin ilmi yanzu ko ina naje na san oven da yadda zan sarrafa shi, kuma na iya kunna gas. Ya fito yana dariya ya shiga daya ɗakin ya sake daga kiran da Bilkusu take masa ta Vedio call.

Kuka sosai take tana tambayar shi cewa "Dan Allah ya fada mata ya kwanta da Asiya ajiya? Yace Bilkisu ina rokonki ki daina wannan maganar sirrin gida na ne, bana cikin masu irin wannan shirme, ki yi magana akan abinda ya shafe ki ya shafe ni kawai.

Ta sake fashe wa da kuka "Wai tafi ni kyau ne ko ta fini dirin jiki ne har da zaka kwanta da ita bayan ka jima kana fada min cewa tun da kake baka taba sanin wacece mace ba a kaina zaka fara, me yasa ka kasa sadaukar min da kyautar da ka jima da bani. Halifa ya yi shiru ya kasa magana, abinda bata sani ba, zantukan ta suna motsa shi suna tada masa hankali yana jin bukatar sanin macen. Ya jure yace, "Ki yarda da kaddara mana.

Asiya ce ta sake murda kofar ta shigo ya sake kife wayar da sauri yace ya aka yi na barki na gudo nan kin biyo ni?" Tace dama zance maka in kai su su gaida Anty ko? Ya kalli sashen kirjin ta, sai ya ji wani abu tundaga tsakiyar kan sa ya dira babban dan yatsan sa. Da gira ya amsa mata tace Kamar kana jin bacci yace" Sosai ma zan kwanta Dan Allah ki saurari bakin ki ko? Tace to, ta Juya yabi dan kugunta da kallo "Shine halas dinka wata zuciyar ta sake rada masa ya yi mika ya kwanta sannan ya daga wayar shi da ya kifa ta ganin ta kashe, ko data kira ya ki daga wa.

Asiya ta raka su Maman Annur gurin Anty sun gaisa ta yi musu fara a ta sa aka aiko musu da abinci. Suna gidan har bayan magariba haka ya yi wa Anty cikas, dan ta kira Halifa yafi sau shida yana cewa bakin ba su tafi ba, ya kara da cewa Anty a bari sai gobe mana tunda yanzu magariba ta yi ba iya gaisuwa zataje ta musu bane ki daina daga hankalin ki akan karamin abu mana. Tace so nake in wuce gurin kawai in huta ba wai dan wani abu bane.

Yace ki bari sai gobe, tace to Allah ya kaimu, sannan ina sake roka mata alfarma ka barta ta warware kaga yadda take a jeme. " Cike da kosawa yace to Anty ya kashe wayar.
Asiya ta idar da sallar ta dakko maganin da maman Annur ta kawo mata a jarka ta daga tana sha, duk da bata fada mata ko na menene ba ta san dai na mata ne tana karantawa a litattafai. Ya shi go ta yi sauri ta boye dan tace mata karta bari ya gani. Ya tako a hankali zuwa kusa da ita ya kai hannu ya dakko robar, yace menene wannan ki ke sha ki ka boye dan kar ki sammin? Yar rowa ce tsakanin mu.

Ta ji kunya ta turo baki cike da shagwaba tace Haka aka ce kar in Bari ka gani, nima bansan ko na meye ba wai ance maganin sanyi. Ya yi dariya ya dan kurba tare da fadin "Wai nan ke harda maganin mata ki ke sha ko? Ta zaro ido tace me yasa ka sha ance fa banda maza. Ya aje robar" Ta shi muyi sallar jiya da ake ta min korafi. Suna idar wa ya kawo kaza mai dumi daya ciro a oven da madara mai sanyi ya aje gefen Sallaya yace, wannan ake fara ci idan aka idar da sallar. Ranar kam ta ci, suka gama yace sai kuma ibada ta gaba nace miki a hade suke. Tace gashi bani da carbi ko zaka bani naka. Ya yi dariya yace kiyi wanka ki shafa turare ki sa kayan bacci ki same ni a wancan dakin tace to. Duk da gabanta yana faduwa kuma sarai tasan nufin shi, amma ta yi alwashin zata jure komai dan ta same shi.


Yana kwance rigingine yana danna waya ta shigo ya bita da kallo ki cire hijabin mana. "Ta zaro ido yace in ba zakiyi ba koma ki kwanta shiyasa ai na fada miki. Cikin kunya.,ta cire sai kayan baccin sun mata yawa wando gere da riga wando ma kulle shi ta yi da dankwalin jallabiya, ya yi kamar bai gani ba ya kumshe dariya.

Ya taso ya janye mayafin da sauri wando ya fadi ta tsugunnna da sauri tana fadin innalillahi na bani. Ya kamo hannun ta, "Kina ta yin saurin cewa mu yi salla to munyi sai kuma ki zo mu kwanta. Kallon shi cikin firgici ta yi, a idanun shi da zargi abinda ke shirin faruwa, ta zauna shima ya zauna. a gaban ta. "Ta so muje gado. Ta girgiza kai me zai faru? Ya kai bakinsa kunnen ta yace ibadar zamu yi." Tace a gado kuma? Ya ce "E mana."
Ta girgiza kai ina jin tsoro. Ta fada cike da tsoron. Ya dauke ta cak domin shagwabar tana kara tsuma shi.ya dire ta kan gado. Wayar shi ta soma ringing tace ana kiranka a waya. Cikin rawar murya yace ki barta kaiwa.

Hajiya Talatu ta gama sauraron rikodin din da ta yi, ta girgiza kai, tare da fadin Koda naji, lallai ruwa baya tsami banza tasan dole akwai wata a kasa. Anty ta zarce ta a mugun hali. Aiko zata ga yadda ake yin bariki ta sha alwashin sai ta cimma nata burin da wannan muryar da ta dauka. Ta shiga shirin tafiya Dan tsarawa ta yarda zata fita da fitar ta. Duk su biyu sun wahala kafin su cika wannan ibada. Halifa har ya ji tsoron kar wani ya jiyo muryar Asiya da irin magiyar da take masa, Amma sai ya rasa dalilin yadda ya ke jin cewa kaimi take. kara masa. Ya kai hannu ya rungumota zuwa kirjin sa yana maida numfashi. Ya kasa magana. Asiya ta lumshe ido tabbas tasan ana cewa ana kwanciyar aure domin tana karance karance amma batasan lamarin ya kai haka ba,amma ta gode wa Allah da ya sa mijinta shine mutum na farko da ta sha wannan wahakar a gunsa, a hakan mata suke mika kansu gurin wasu mazan na waje a banza kawai a ba su wasu yan kudi. Gaskiya ita dai aure kadai zata iya yi wa wannan sadaukarwar..


Halifa ya ji wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali, sannan ya ji wata kauna ta yarinyar ta mamaye shi..Duk da cewa a. makarantar su ta islamiya an koya musu wankan tsarki amma sai Asiya tace wa Halifa bata san ya ake yi ba a aikace yace yanda ki ke yin na wata wata ne, niyarce banbanci. Tace to.


Da safe ma Halifa yana ta ji da Asiya duk wani motsin ta yana kula da shi sosai.. Anty da kanta ta kawo musu abin kari tace Asiya ta shirya kamar karfe sha daya za su tafi. Halifa ya kalleta zaki iya zuwa? Anty ta yi zaraf tace lafiya ka ke tambayar ko zata iya zuwa? Halifa yace bata jin dadi ne. Anty tace ashsha meke damu ta? *Asiya ta yi saurin cewa dan zazzabi ne zan iya zuwa. Bayan ta fita, Halifa ya kama tafin hannun ta me yasa ki ka bata amsa ai da kin bari na fada mata abinda mukayi. Asiya ta zaro ido" Da gaske kuma zaka iya fada mata? " Zan iya mana harma in fada mata irin kukan da kika yi kina bani hakuri. Ta saka fuskar ta a cikin cinyarta tana cewa Yaya bana so.

Hajiya Talatu suka fito Dan tafiya cike da murna Anty ta ba Ma u dubu goma gashi kwayi na mota. Ma u ta karba tana taba baki. Hajiya Talatu tace akwai dawowa fa Sahiba lokacin da Sabon malamina ya fada min cewa idan har sabon malamin ki ya yi nasarar kwanciya da Amaryar Halifa za a samu sabuwar daula a wannan gidan zan zo lokacin domin aurawa yata Halifa duk da cewa a cikin kudurorin ki shine ki amshe masa komai, to ni kuma a nan ne nawa Malamin zai banbance miki tazarar da ke tsakanin sama da kasa. Anty ta saki baki ta bi Hajiya Talatu da kallo.
Har suka bar gidan bata samu bakin magana ba. Lallai wannan babban lamari ne, amma zataji da ita Bari ta gama da wannan. Ta gama shirin ta tsaf ta saka hijabi ta fito falo inda yake zaune, ya kalleta bari dai ku dawo zan yi miki wata ba zata. Asiya ta kalli Halifa "Amma dai ba irin na jiya ba ko?" Yace a a sai dai ko zaki bani tukwici. Ta Harare shi, "Bani da abinda zan baka. " Ke ce kuwa mai abin badawa. Je dai ki dawo bari muje in raka ki gurin Anty. Dan ma ta ki yarda ma wallahi ni zan kai ku, dan Allah ki kula min da kanki sosai kinji? Kuma kar ki kalli kowa wani kishi nake ji za ayi ta Kallon min ke. Dadi ya kama Asiya tace Bazan kalli kowa ba, bare ma in san da wani, ta danyi kasa da murya nifa kasan Allah duk mazan nan a mata nake kallon su, bayan kai ina mazan suke? " Anty dake labe ta cika da mamakin wannan cilligar yarinyar ce ta iya fadawa namiji haka.

gara ta hanzarta kar ta bata musu aiki. Ta rafka sallama tare da fadin Asiya ta gama shirin" Asiya da Halifa suka amsa tare, shine ya raka su har titi ya saka su a Kekenapep Tunda ya yi ya yi da Anty ya kaisu ko a kira Bros amma sam ta ki. gidan Baaba za su soma zuwa kafin daga bisani su tafi gidan Baffa. Baba ta yi murna harda kudi ta ba Amarya, daga bisani suka nufi gidan Sabon malami a zuwa shine Baffa.

Tafiyar da nisa sosai a wani kauye a gwarzo. Suna sauka suka nufi wani gida shi kadai ne mai kyau kaf kauyen tamkar an kawo shi an dasa. Asiya ta na jin wata fargaba a zuciyar ta kuma kamar wani abu zai faru. Dan haka ta tsananta adduo'in a kasan zuciyata. Wani Falo ne na alfarma suka shiga wani dattijo yana zaune sanye da manya kaya ya rufa kansa da fari da kuma koren hirami. Ya dago idanu ya kalli Asiya idanun shi manya sosai kamar za su fado kasa ga su jajir sai ta ji tsigar jijinta ta tashi.
Ya nuna wani farin buzu "Zauna a nan yata." Asiya ta zauna ya yin da Anty ta zauna gefe suka gaisa. Asiya ma tace Baffa barka da rana ya daga mata hannu tare da yi wa Anty alama da yatsa Wai ta fita....


*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

[6/11, 10:51] Ummi Tandama😇: Asiya ta mike ita ma ganin Anty ta tashi tana cewa bari in shiga mu gaisa. Yace" Zauna ƴata" Asiya ta zauna ta na jin zuciyarta babu daɗi, ga fargaba sai ta dora karanta addu a a zuciyar ta.

Ya ta so a hankali yana kanshin wani iri turare mara daɗi kamar zai sata jiri, ya zo ya tsaya a gaban ta. "Bari in yi miki addu'o'i ƴata ki nutsu kuma ki rufe idanunki.

Asiya ta cika da mamaki rufe ido kuma kamar addu ar wani addini. Amma sai ta rufe tana addu ar nemantsari. Ya shiga zagaye ta yana wasu zantuka da bata jiyo me yake fadi. Ta ji kamar jiri kamar garin yana juya mata dan haka ta mike zunbur ta yi hanyar fita, cikin zafin nama ya kamo ta, kokowa suka shiga yi Allah ya bata nasara ta yanka mishi cizo Ya sake ta tare da nufar kofa ya rufe ya dakko wata ƴar buta ya watsa mata ruwan ciki. Take ta zube bata kuma sanin ina take ba.


Ya kira wayar Anty yace ta shigo, ya kalleta yace yarinyar nan ba budurwa bace, Tace "Har ka yi ne ka tabbatar? " Ya dube ta, ban yi ba, idan nayi ai komai lalace wa zai yi, ta yi yunƙurin ta tonamin asiri ne,, ni kuma na sumar da ita, dan haka ki kwasheta ku bar nan kafin ta farka, har cizo na tayi, gaba daya kin bata min aiki da ace ba su sanar da ni ba na yi amfani da yarinyar bayan wani yariga ya yi amfani da ita, Allah da kin cu ce ni! " Ya kara sa maganar cikin fusata. " Ku bace min da gani bana bukatar in sake ganin ku.

Anty ta shiga bashi hakuri tana fadin Malam zan kawo maka wata dan ka cika bukatarka nima burina ya cika. Ka yi binciken Taurarin ƴata ta cikina Hafsa, in har zata yi yanzun nan zan kawo maka ita. Ya koma kan buzun sa yana fadin ki kauda wannan kazamar tana cike da datti...

Anty ta shiga tashin hankali da damuwa ga mamaki ya ishe ta wai yarinyar nan ba buduwar bace ke nan sai da ta gama lalacewarta a waje. Ya dakawa Anty tsawa yana cewa maza ta bar mishi gida bayan ya duba Taurarin Hafsa ya ga cewa babu wani amfani da zata yi masa.
Da taimakon wani yaron Malamin suka saka Asiya a Kekenapep suka nufi komawa, me Keke dai yana ta mamakin yadda Asiya ta zo da kafar ta amma yanzu sai da aka debota.

Son jin tsegumi me Kekenapep ya ce bata da lafiya ne dama naga da kafarta ta zo? Anty a fusace tace "Shafa kaji mana, ku masu keken nan kun fiye shegen tsegumi gashi bakwa ganin zarau sai kun tsinka." Yace Tofa! daga tambaya? Bani na kar zomon ba. Tace " Ka ga in ka gaji sauke mu. " Daga nan. Yace a a mai ya yi zafi? bai sake magana ba. Sunyi nisa kafin Asiya ta farka jikinta

Please Login or Register in order to submit comment