Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302*

Ta na gama jera abinci akan Dining ya fito wanka, yana gama shiryawa ya same ta akan Dining ɗin tana haɗa masa shayi, bai zauna ba ya karɓa kafin ya kurɓi shayin daga tsaye, ya ɗora da fadin ana jirana Baby ba zan iya zama ba, akwai wani baƙo yana jira na kwastoma ne daga nesa yake, ki kula sosai kar fa kije ko ina. Bata amsa ba tana kallon shi yana magana yana satar kallon ta, yana in'ina, shi dai mara gaskiya ko aruwa sai ya yi zufa ta ɗarsa haka a zuciyarta. Ya matso ya shafi kumatun ta, kina bukatar wani abu ne? Wayar shi ta sake rigin ya kalle ta da sauri bayan ya kalli fuskar wayar, ya daga minti biyar kacal dan Allah gani nan yanzu. Ya katse, yasake dubanta zan kawo wani abu ne? Ta girgiza kai, To kimin addu'a mana ya fada kamar dai mara gaskiya. Ta danne zuciyar ta, ta ja dogon numfashi, a hankali ta furta Allah ya tsare. Na gode ya fada da sauri. Gudu gudu ya fita.

Wata zuciyar tace dama ki bishi ki ga ina zashi haka, ya zuba kaya masu kyau yana ta kamshi, da ka ganshi kaga matashin mai kudi, ko karyawa ya kasa.

Ta tashi a gurin ta koma falo domin ita ma baza ta iya cin komai ba. Ta shiga zirga zirga da tunanin mafita,wayar ta ta tuna lokacin da Hajjo suke nan suna sauraron shirin rai dangin goro ta ji Labarin Hamshakiyar Uwa tun bata sauraro in suna ji har itama tazo tana ji, Fati ce ta bata lambar marubuciyar da niyyar zata sai littafin tun da bataji farkon labarin ba, bata ma samu ta siya din ba, amma dai zata kira marubuciyar dan ta nemi shawara tana kyauta ta mata zato.

Ta kira layin sau biyu duk ba a daga ba, tace Ummm dama fa ana cewa irin wadanan suna da wulakanci bari dai in sake tunanin wa zan kira. Doni in rage wannan damuwar ta hanyar fada wa wani halin da nake ciki.Kukan danta ta jiyo dan haka ta nufi dakin da sauri,tana daukar shi wayarta ta soma ringing. Ta kalla Number da ta kira ce, da sauri ta daga tana Sallama marubuciyar ta amsa amma sai ta jiyo kukan jariri, sai tace a kula da me kukan nan tukunna. Asiya tace "To Anty zan kira ki anjima kadan.

Anty Halima tace ba damuwa. Sai taji kamar matsalar ta ta yaye, kamar ta gama samun mafita,ba shakka Anty Halima zata bata shawara.

Sai da ta gama dashi tsaf ya sha wanka ya koma bacci sai ta koma falo ta zauna ta sake kiran Anty Halima. Bayan sun gaisa Asiya tace To Anty ni bansan yadda zan yi miki bayani ba, ni dai na kasance ina karanta littafin ki kuma ina da shawara da nake nema. Anty Halima tace babu damuwa ina sauraron ki ki yi magana kamar kina tare da mahaifiyar ki ko wata yayarki ta jini. Asiya ta sake samun nutsuwa ta kwashe dukkan labarinta har zuwa inda ake yanzu ta sanar da Anty Halima.lokacin katin Asiya ya kare, tana kokarin cin bashin kati sai ga shi Anty Halima ta kira, . Asiya ta daga tace bari in saka kati Anty Halima tace babu damuwa ci gaba. Asiya tace Yanzu dai haka kinga ya fita yau ko karyawa bai yi ba, kuma ina zargin wata ce ta kira shi. Sai ta fashe da kuka. Anty Halima tace Yi hakuri ki saurara da kukan haka, kina jina, ki nutsu, kuma yadda baki masa magana ba ina baki shawara karki yi masa maganar, domin shiru hanyace ta dafa mutum a ruwan sanyi musamman abokin zama, kuma ki daure ki daina nuna masa wata alama da ke nuna kina zarginsa. Abu na farko ki rage bacci ki fadawa Allah duk wata damuwar ki cikin dare, sannan ki daina saka ido akan wayarsa karma ki sake dauka,domin zaki iya ganin abinda zai kawo karshen zama lafiyar ku har na nan gaba. Asiya tace Allah ya sa in iya zan gwada. Sai abu na gaba maganar Mahaifiyar ki tun da abin da zai faru ya riga ya faru, to kawai ki saurari lokacin da ya ce ki bashi din, domin tafiyarki ke kadai kuma kina cikin damuwa zai iya haifar da komai tunda kina son mijinki ko kuwa? Asiya tace haka ne. Ni yanzu abinda yafi daga min hankali Anty Halima guda ɗaya ne ya fita gurin wata zuciya ta wallahi tana cike da kunci. Kina da tabbacin gurin wata ya fita? Anty Halima ta katse ta. Asiya ta soma kuka Ina da tabbaci Anty, boye boyen da yake yi min fa? Kuma ai ko me aiki na ya nuna damuwa da na sallame su. Ina zargin ma ko ita yake bi. Assha!! Inji Anty Halima, ta katseta, kar ki yanke hukuncin da iya hasashe ba lallai ya zama gaskiya ba, amma ki daure ki kau da kanki, kinsan fa zargi in ya yi yawa yana bata aure. Ki yi masa addu'a ko ya dawo kar ki nuna masa, cin amana bata dorewa a cikin aure, kuma yana bukatar ki kusa da shi tunda shi ba mai abokai bane barkatai yawan shige masa da bashi shawara za su taimaka miki gurin maido shi hanya,karki nuna kyankyami a gare shi ko da ta tabbata cewa kin kamashi dumu dumu na abinda ki ke hasashe. Hakan zai ba matan wajen damar samun shi, kin fada min cewa shi mutum ne mabukaci ga kudi ga lafiya dan haka ki ja abinki a jiki, Mata da ki ke gani a wannan zamanin su ne ke neman mazan da kansu Dan haka ki kula sosai amma addu'a tafi komai muhimmanci kar ki manta.

Asiya ta yi godiya suka yi sallama duk da ta samu kwanciyar hankali kadan sai dai fa bata yarda wai ta kauda kai ba.

Ina zata samu labarin su Fati, tana son sani ko fati ya ke so. Ta tuna da nurse wadda ta ke kula da baby, ta daga waya ta kira ta suka gaisa, ta tambayi yaro tace ko anyi masa allurar wata ta farko da ake yi? Ta ga ya wuce sati shida. Asiya tace ba ayi ba, ai su basu san anayi ba. Nurse tace ya kamata ku kai shi yau ko gobe, Asiya tace insha Allahu. Sannan tace yawwa wai kuwa kinsan wannan Hajjo din da suka min aiki Ina nufin Unguwar su. Nurse tace kinsan tana aikin shara ne a Asibitin mu,na dai san kamar a Darmanawa aka ce take amma bansan gidan ta ba. Asiya tace Allah sarki Dan Allah ko zaki iya samo min lambarta sai dai dan Allah karki ce ni ce, ina son ne in ziyarce ta, na bazata, ta yi min mutunci kamar yarta ko jikarta muka zauna. Nurse tace "Ki tambayi megidanki mana ai kamar ba zai rasa ba. Asiya tace bashi da ita gaskiya, domin dashi mukayi maganar yace in tambaye ki.
Nurse tace to in naganta zan karba miki, in kuma bata bayarba shike nan.Sai bayan sun yi sallama zuciyar ta ke ce mata wai me kike son aikatawa ne Asiya.

Cikin sa a ba a jima ba,lambar ta shigo. Asiya kuwa ta kira Hajjo suka gaisa da ta tabbatar Hajjo bata gane ta ba, sai tace wai ita kawar Fati ce daga Maiduguri ta kira lambar Fati bata samu ba shine ta ke son a hada su. Hajjo tace Allah sarki ga shi kuwa Fati yau tun safe suka fita ni ma na kira layin nata ma baya shiga ko bata da caji ne. Gaban Asiya ya fadi, zufa ta karyo mata kenan dai suna tare, tace na shiga uku.ta darsa a zuciyarta ta. To dan Allah ko zaki tura min lambar ta wannan da nake ta kira din kamar tsohon layinta ne Intel ko shine har yanzu? Hajjo tace A a wannan MTN ne bari zan turo miki sai ki gwada,amma yau ko kunu bata sha ba ta fice tana sauri. Asiya tace Allah sarki ko ta samu aikin ne da tace min tana nema? Hajjo tace gurin wani ma ta tafi da zai saka sunan ta a aikin poliyo zan turo miki lambar yanzu sai anjima.

Asiya ta yi shiru tana nazari kenan karya Fati ta yi wa Hajjo dan ta fita da Halifa maganar aure suke yi kokuwa dai sakarcin su za su yi?

Kuka Asiya ta zauna tana rerawa, zuciyar ta tana tafasa wata zuciyar ta faɗa mata cewa kuka fa bazai zame mata mafita ba. Ta kira layin Halifa bai daga ba sai a kashi na uku, ya daga kafin ta yi magana ya rigata,muryarsa can kasa kasa, gashi sai taji gurin yana amsawa. Yace "Baby Yaya akwai damuwa ne? Ta ce dama Nurse ce muka yi waya tace min ya kamata a kai yaron nan allurar sati shidda yau ko zaka zo yanzu ka kai mu? Yace Baby tace dole sai yau ba za a bari gobe ba? Inda nake yanzu ba zan iya fitowa ba gaskiya. Gaban Asiya ya kuma yanke wa ya fadi, kenan wata ta fi su muhimmanci. Kin san ya za ayi?" Ya katse mata tunani. "Ki samu dan Adaidaita sahu sai ki hada ni da shi muyi magana,amma ki kula kar ki fita ba tare da kin rufe fuskar ki ba, kar ki hadu da wani. Asiya ta kuma hadiye fushinta tace Yaya ba kudi a gurina. Yace "Ki bude Sif din nan karama zan turo miki lambar da zaki saka ki bude yanzu sai ki dauki dubu goma in na zama free zan kira ki kinji, ki kula da kanki. Bai jira amsarta ba kawai ya kashe wayar. Hakan ya tabbatar miki da cewa suna tare da wata Zuciyar ta ta fada mata. Ta soma hasaso su shi da Fati da abubuwan da suke aikatawa.

Karar shigowar sako taji a wayar ta, lambobin da zata buda ma adanar kudin ce. Tana kuka ta bude, kudi ta gani kaloli na kasashen waje ta kirgi dubu goma ta kudinmu na Najeriya ta mayar ta rufe.

Ta saka face marks amma bata kira shiba lokacin da ta samu me dan sahu. Taje Asibitin ta kira Nurse aka yi musu allurar ta tambayi. Nurse ko sunyi waya Nurse ta ce mata a a bai kira ba, har ta tambayi Asiya ko lafiya ta ganta duk a Hargitse Asiya tace ba komai bari ta tafi. Zuciyarta tace kawai ta wuce gurin Inna dan haka ta samu dan sahu dan ya kaita Fage, sai dai suna kaiwa kwari tace da me Adaidaita dan Allah ka kai ni Hotel. Ya juyo ya dube ta da sauri,"Hotel kuma baiwar Allah?" Tace wata kawata zan duba. Yace To wane Hotel din aciki? Asiya ta dan yi shiru ta manta ashe fa Hotel din da yawa. Can tace wanda haka maza ke zuwa da mata ni na manta sunan shi, kai baka san wani Hotel haka ba wanda maza ke kai mata ka kaini in duba ta sai ka maida ni Gandun sarki zan biya ka. Dan sahu ya yi yar dariya wannan kuwa tasan adadin Hotel din garin nan? Sannan ya juya kan Adaidaita ya nufi hanyar Nasarawa yace zan kai ki dai inda mutane suka fi dabdala Tahir ko kuma Ni'i ma sai ki duba.Tace To gaban ta ya kara tsanan ta faduwa, Daidai rawul din gidan Gwamna kawai ta hangi motar Halifa ta daya hannun suna fitowa daga titin da za su hau, da sauri tace wa mai keken Juya ka bi waccan bakar motar ga su can. Ya yi ganganci ya yanke ya fasa shaga titin ya sha rawul suka bisu. Duk da danja ta tsaida su bayan wucewar motar su Halifa shima mai dan sahu ya bisu bai tsaya ba,. Yace mata wannan ai kasuwar Farmcenter ya nufa, tace muje dai. Kafin su same su har sun bar gurin sun dai samu motar, a gurin paking na kasuwar.
Asiya ta kalli lokaci a wayarta, karfe uku tun safe. Ta dubi me a daidaitar tace hanyar Hotel din ne suka fito ko? Yace e nan ne. Tace shike nan kaini Gandun Sarki.



*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[12/11/2025, 08:53] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt


*Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302*


Bintu tana girki a kicin ta ji an banko kofar falo ta fito Hafsi ce ta shigo. Bintu tace Au ke ce ? Hafsi ta amsa cike da rashin kunya wallahi fa sai kin bar gidan nan tunda ba gidanku bane. Bintu tace ki fada wa wanda ya kawo mu mana sai ya zo ya fitar da mu. Ta dungure kan Ahmad tana fadin kai dena kallo na mummunan banza. Bintu tace Ko zaki mutu ki dawo dai kanin ki ne shi ba yadda zaki yi. Fitar min daga nan. "Bazan fita ba. 'Bintu tace OK jira,ta dauki waya karki fita dama ai ba wannan ne zuwanki na farko ko na biyu kina min rashin kunya ba, bari in sanar da Ubanki sai ya taka miki birki.

Har lokacin da Dady ya daga yana jiyo muryar Hafsi tana zazzagawa Bintu rashin kunya. Ta ce Abban Ahmad Yarinyar nan ba yaune na farko ta zo ta ci mutunci na ba, ta dinga dukan yaran nan, in ba dama gara ka sama min wani gurin. Dady yace "Kiyi hakuri Bintu karki da mu kar ki kulata uwarta ke turo ta, zan yi maganin abin idan na dawo. Tace To.a Hands free ne Hafsi ta ji komai.
Dan haka ta saki dariya,wai Abban Ahmad duk mu ba Abban mu bane to sai kun jira daga ke harsu akwai wasu a gaban ku. Ta yi ball da wani filet na tangaran dake kusa da ita ta wuce.

Tana fita Bintu ta maida kofa ta rufe ta lallashi yaranta.

Da dare Dady ya samu Hafsi a dakin Anty dama tun da taji dawowarshi ta shige dakin. Yace ke dama wato zuwa ki ke kina cimin zarafin mata kina dukar min yara ko? To wallahi na gargade ki duk san da kika kara taba min su sai na rama masu, sannan kuma zuwa ranar asabar in saurayin ki bai fito ba ranar Lahadi zan saka ranar auran ki da duk wanda na ga zai rike ki,wanda in iyashege ki ke ji ya fiki, ya fice abinsa.
Anty ta kalleta, Wai bana ce ki daina shiga harkar matar nan ba ne? Kinsan dai Dady tunda ya furta maganar aure kuma ya samu goyon bayan su Halifa ki bishi a hankali. Ni yanzu kinga ina kula shi ne? Hafsi tace Wallahi Anty kamar in kashe matar nan da yaranta na ke ji na tsane su,tsana me tsanani. Ke kuma sai ki zuba musu ido su zauna lafiya a gidan nan? Anty tace 'To fada min yadda zan yi tunda kin ce i na saka musu ido,, fada min. Kina kallon yadda na koma abin Duniya ya ishe ni, ba wanda na isa in fadawa ya ji, shi kanshi Dadynku da yake matukar shakkata yanzu tsoron shi nake yi, tun da abinda na yi ya karye. Hafsi tace to ki sake yi mana Anty ki dawo da izzarki kin fi kwarjini dubi yadda kika koma yanzu ko su Nihal ba tsoron ki suke ji ba. wallahi. Anty ta ja tsaki tare da faɗin Ana baki kina kin karɓa. Ni dai yanzu kinji abinda ya fada ki turo min Hafizun inyi magana da shi wannan kwane kwane da yake yi fa ya isa haka. Hafsi ta dan yi shiru can tace "Anty wai kawun sa dake Abuja ne ya tafi Ummara sai ya dawo tukunna. Anty tace ai ki fada masa kawai ya zo ina son ganin sa. Kema na ga nema ki ke ki sa min ciwon zuciya bayan na hawan jini da suka sa min. Hafsi ta fita tana kunkunai.

Bros ya shigo dakin da sallama ta daga kai ta kalle shi tun ranar da aka yi wannan hatsaniyar rabon shi da gidan. Fuskarshi babu walwala ya gaida Anty ta amsa ita ma fuskar ta a dake, tana ganin bai kyauta mata ba,tunda ya zabi Babanshi. Ta Katse shiru da faɗin "Ai na zaci baza ka kuma zuwa inda nake ba tunda na fadawa ubanka magana bayan ni baku kalli girma zunubin da ya aikata min ba. Bros yace Anty ni ba wannan ya kawo ni ba, na zo ne in fada miki in su Nihal sun taso daga makaranta zan zo da dare zan tafi dasu su koma gida. Ta kankance ido tana kallon shi, me kake nufi gurin wannan shashashar matar ta ka zaka kai su? To ban yarda ba, in har ina raye baza a kai su ba makira ce ba yarinyar arziƙi bace. Bros yace ita ma kuma makira ce, to aike kika zaba min ita saboda kin yarda da ingancinta. Kuma dai zuwa yanzu banace ga laifinta ba. Anty tace "Kara da kiyashi ne daukar marasani na yi. Ya gyara zama, gurin uwarsu ma zan kai su, akwai abinda ban fada miki ba, Ya kalli Anty wadda ta zaro ido tana kallon shi so yake ya maida matar shi ke nan, aiko ba zai yiwu ba. Kinsan na maida mamansu. Ya katse mata tunani." Ka maida wa ka ce?" Wannan mai kashin tsiyar ka maida wadda ka shiga matsala saboda farar kafarta, ai kuwa zaka kuma sakinta domin ba zai yiwu ba. In ko ba haka ba,gara in tsine maka gaba daya.

Bros yace "Anty na maida matata tun a satin da kika sa na sake ta, mun zauna a Hotel kafin na kama haya, yanzu haka ta haihu muna da yaro wanda na yi wa Dady takwara da shi, har ma ya fara tafiya, dan haka babu wata farar kafa da mata ta take da shi, domin duk abinda na samu yanzu ina tare da ita na samu dan haka sai dai ki tsine min din in kina son hakan amma babu hujja, babu kwakwkwaran dalili sannan ina me neman gafarar ki idan abinda na aikata ya bata miki to ki yafe min, zan dawo anjima in dauke su su koma gurin maman su.

Saboda tsanani mamaki Anty bata iya furta ko kalma daya ba, har Bros ya fice,ta yi mutuwar zaune. Wane irin wasan kwaikwayo ne ake yinsa a gidanta haka?

Da farko mijinta ya zo da mace da yara biyu ya yi aure a boye, yanzu kuma Babban danta ya zo wai ya maida matar da ta tsana, kuma har sun haihu, bayan ta bibiya an fada mata cewa matar nan ta yi aure a wani gari. Wai tana ina duk haka ta faru, bacci ko me?
Zufa ta soma karyo mata me yasa abubuwa yanzu suke ta zuwa mata bai bai? Me ta yi ba daidai ba a rayuwar ta. Kuka ta ke son yi amma ta kasa. Tabbas inta mike zata faɗi a zaunen ma jiri take gani dan haka ta jingina bayanta da bango. Ta lumshe ido da kyar ta samu wasu hawaye suka soma ziraro mata ta gefen ido.

*** *** ***

Asiya ta shiga gida cike da bakin ciki, ga dai gida har gida haka kuma ga ababen more rayuwa amma babu farin ciki a cikin shi bare kwanciyar hankali. Asiya ta darsa haka a cikin zuciyar ta lokacin da take bin ko ina na gidan da kallo. Ta zauna a kujera ta sauke danta wanda ke ta kuka saboda allurar da aka yi masa dama an fada mata zai ta rigima. Wai haka rayuwar take ne babu wani sauki a cikinta? Asiya ta tambayi kanta a fili. Ta sa yaron a kafada tana jijjiga shi, tana kai komo a tsakiyar falo gashi tun abin kari bata ci ba komai,yau ko gado bata gyara ba bare kuma gidan, kuma bata jin zata iya yin wani abu. Motar baƙin gilashi gareta hakan ya hana ta ga ko wacece a ciki, bata da tabbacin cewa Fati ce shine ya hana ta dauki mataki akan ta. Cikin yanayin ta yini ba ci ba sha salla kawai ta ke yi sai jijjiga ɗanta da yake ta kuka, sai kuwa kukan ita ma da take sha.

A haka goma ta wuce sha daya ta kawo jiki na dare. Ta ji shigowar motar sa, tana ta shawara akan abinda zata yi masa ko zata ji sanyi Tana ga kamar ta tunkare shi da zancan. Zantukan marubuciyar suka fado mata, anya zata bi wadannan shawarin sun mata tsauri addu'a dai zata ta shi ta yi dan ta san bazata iya bacci ba ma, amma ta kauda kai kar ta nuna ko alamar ta na zargin sa abu ne mawuyaci.
Bata san ya shigo ba, tana kai kawo a falon ɗa na kuka. Sai Murya shi taji yana tambayar me ya same shi? Tare da kai hannu zai dauke shi, ta ja da baya cikin sauri kamar wadda taga abin tsoro fuskatar ta ta yi suntum da kuka, yace "Ya Subahanallah, Kema taya shi kukan kika yi? Ta kau da kai,kowa da nashi dalilin kuka. Yace To kawo shi sai ki fadamin naki ga mai share miki hawaye Allah ya dawo da shi lafiya.faɗa min dalilin domin shi na san nashi, munyi waya da Nurse ta fada min cewa zai yi kuka kuma kar ayi masa wankan yamma, saboda allurar nan,
na yi ta kiran ki in fada miki baki daga ba. Ta kalli wayar dake gefe sanna tace banga kiran ba. Yace ki dai duba kafin ki musa, kawo shi. Ta sake kallon shi cikin ido, ka yi wanka tukunna. Ya matso ya karbe shi ba tare da jira ta miko shi ba. 'Ki huta kema ai kin sha aikin jijjiga ga shi da alamu yau gidan bai samu gyara ba,komai yana nan yadda na barshi.

Dole fa sai an sama miki mai aiki gaskiya zata taimaka miki mussaman irin wannan lokacin kina fama da yaro, ko ba yaro gidan nan Baby ya yi miki girma da aikin gyaranshi kullum. To ka dawo da su Fatin mana tunda dama na ga bakaji dadin tafiyar su ba. Ta fada cikin gatse. Sai lokacin ya fuskanci abinda take nufi. Allah ya baki hakuri, ni shawara nake badawa Gida dai na ki ne Baby ki yi yadda ki ke so dashi su Fati tunda kika sallme su na kara magana? Kuɗin su ma sai daga baya na ba su.. Su Fati kuma ai sun zama tarihi a gidan nan.

Ya nufi daki, turus yayi yana kallon ko ina ba a gyara ba. Ya fito ya same ta zaune ta dora sabon kuka,ya tsaya cike da mamaki da fargaba yana cewa wai me aka yi ne,ki fada min mana?
Ta yi masa banza ga yaro na kuka, ya koma ciki ya kira Nurse ya tambaye ta ko akwai wani abu da aka gani na rashin lafiya game da yaron tace babu, ya fada mata yaron ya yini kuka jikinshi ya dauki zafi. Tace "An kuwa bashi maganin da aka bata na zazzabi? Yace bari ya tambaya, ya fada mata yanzu ya dawo ya samu Uwar da dan suna ta kuka. Tace akan samu haka a haihuwar fari, sukan taya yaran

Please Login or Register in order to submit comment