Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau din nan yana cewa Anty Umma ku raba kuma yan uwana ne,kuma daga yau kowa babbane a cikin ku duk mai son wani abu ya kirani kai tsaye duk daya ku ke da kowa." Anty ta zauna ragwaf a bakin gado, lalacewar tawa har ta kai haka a gurin Halifa? Tabbas sako ya bada kuma ya iso,zan kuma same shi har dakin sa. Ta mike fuuu ta nufi dakin Halifa amma sai ta hange su tsaye da Dady suna tattauna wasu zan tuka da zata so jin abinda suke cewa. Kai tsaye ta nufi gurin su,abinda ta iya ji shine insha Allahu Dady ranar litinin a office din Barrister Sani makoda. Sai Dady yace Ina fatan dai lafiya in kuma maganar kudi ne in taho da listening abinda ke guri na.Halifa yace ka yi hakan ma,domin maganar ta shafi hakan. Shima Bros na sanar da shi. Halifa Anty ta kwada masa kira cikin tashin hankali .Ya kalle ta duk da duhun magariba tana iya kallon yadda ya daure fuska yana kallon ta ba tare da yace kala ba.

Tace "Gidan uban wa ka kai Akwatunan nan? Sannan mitin din uban me ka ke hadawa!!!
Ya Kalli Dady sai kuma ya nufi motar sa ba tare da ya yi magana ba. Hakan ya bata kwarin gwaiwar karasawa kusa dashi cike da gadara ta ce Ni sa ar ka ce harda zaka wuce ina yi maka magana? Ya daga Murya "Kama kan ki Anty!! Karfa ki kure ni!! Dady ka fada mata karta fusata ni ba danta bane ni, bata da wani karfi na hani ko Umarni a kaina fa!!!!Ya bude motar ya shiga ya tashe ta ya fita da mugun gudu gudu. Anty ta yi tsaye cike da mamakin irin daga muryar da Halifa ya yi mata, har su Hafsi da Talatu sai da suka leko ta window. Dady ya sa kanshi ya wuce ya bar ta tsaye cike da mamaki da tsoro.

Ta koma ta zauna bakin gado suka yi shiru dukkan su. Hajiya Talatu ta mike ta janyo jakarta, ta shiga linke kayanta dake bakin gado. Hafsi Tace "Anty shawarar da zan baki ki rage matsawa Uncle Halifa akwai matsala sosai. Hajiya Talatu ta ce "Kodai ya samu labarin...Anty ta daga mata hannu ba wannan bane, Halifa ne ya dawo asalin Halifansa, fatana malaman nan su dukufa aiki,domin akwai katuwar matsala. Abinda ya daure min kai nake son sani yanzu wane shiri ya ke yi da lauyoyin ? Zaman me zasu yi harda Dady da Adamu? Dukiyar sa yake shirin karbewa ? Ina son sanin wannan amsar.


Hafsi tace to Anty kije ki tambayi Dady mana bazai rasa sanin wani abu ba. Zaraf ta mike kamar mai jiran madafa ta nufi dakin Dady.
Yana waya daidai lokacin yana fadin To da zaki barsu a gidan ko zaki rufe su ta baya ne? Ya danyi jim sannan yace, ok tunda Shafa tana nan shike nan kuje sai ki min message zan tura miki kudin Allah ya bashi lafiya da safe in na fito masallaci zan zo inga jikin nashi. Yana kashe wayar ya dago kai suka yi ido hudu da Anty.

Duk da faduwar gaban da Dady ya ji amma sai ya dake, maimakon ta tambayi a binda ya kawo ta sai ta bige da tambayar Da wa kake yin waya? " Baki sansu ba. Ya bata amsa a
takaice .Ta danyi tsam kamar me nazari . Sannan ta taɓa baki tace Halifa ya ke nufi da yace Me Halifa yake nufi da yace ku hadu ku yi mitin? Me yasa baki tambaye shi ba? Ya fada cike da daure fuska. Tace Au me kake nufi wai kaima kulle ni zaka yi? Dady ya zauna bakin gado "Dan Allah kije bacci nake ji."
Ta fita tana huci ta zauna bakin gado inda Hajiya Talatu da Hafsi ke jiran ta. Hafsi tace Anty karfa ki saka wa ranki damuwa ki zo ki kwanta ciwo. Amma me Dady yace?

Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce wai ni kuwa Hafsi Babanku na da yan uwa ne a nan Unguwar? Hajiya Talatu tace kaji wata maganar kuma an tambayi wani abu kema kuma wai kina tambaya..
Anty tace Talatu Alhaji na samu yana wata waya wadda ta daura min kai,shine nake tambayar ko yana da wata yar uwa na manta.

Hafsi ta kalle ta "Me yake cewa,da wata yake waya wai Bintu. Hafsi ta sa dariya Anty kin manta ne da matar Abokin shi marigayi Bintu matar Alhaji b
Baita.? Anty ta taba baki. "Wallahi shaf na manta, yana taimaka musu, ni kinsa ko a matan abokai in har baza a kira ki ki amsa ba to hanyar jirgi daban da ta mota. Ta sauke ajiyar zuciya dan jin hasashenta bai tabbata ba. Tace Dadyn ma yaki fada.

Halifa tafe yake ko ta kan shagon Sulaiman bai bi ba ya nufi gidan su Asiya yana son zuwa ranar litinin ta tare a sabon gidan shi insha Allah.

Gidan nasu a rufe da wani dan karamin kwada hakan yana nufin basa nan. Ya kira wayar ta kamar kullum a kashe sai yaji zuciyar shi tana hasala dan haka sai ya juya ya dauki motarsa ya tafi.
Kasuwa ya wuce rai babu dadi, saidai yana zuwa yaran shagon suka bashi wata takarda inji wani mutum yace daga Kotu. "Kotu! Ya furta cike da mamaki bashi da abokin rigima ko daya waye zai yi karar shi.

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[10/1, 10:07] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w

Halifa ya sha mamaki ganin wai Asiya ce ke karar shi, ya shiga shago ya zauna duk da sanyin A C hakan bai hanashi zufa ba.

To me ya yi mata har da zafi haka zata yi kararsa?
Bayan shi da ta yi wa laifi yace kar ta fita ta fita,kuma taki yarda su hadu,ta tafi wani gari duk bada izninsa ba, sannan ya nemeta a waya duk abin ya gagara yaje gidan ma basa nan,shine yanzu kuma zata tsaya da shi a gaban kotu, gaskiya shi kam ba zai tsaya da ita a kotu ba,sai dai ta fadi duk abinda take so alkali ya yi mata kawai ya hakura, dan kila saki take nema,sannan zai dauki nauyin cikinta amma a sani da ta haihu zai amshi dansa.
Ko da ba su yi soyayya ba,tana da wani mahimmaci a gare shi,tana bai taba sanin mace ba sai a kanta,kuma ita ce kadai ta ganshi a wani yanayi da ba zai iya fassara shi ba.

Ya mike ya fita a shagon yaje mota ya zauna sannan ya kira Bros a waya, ya sanar dashi abinda ya faru da kuma abinda ya yanke. Bros ya cika da mamaki, yace "Ka kira waliyinta mana babu mutunci fa kuje gaban Kotu ku tsaya,kuma dole ne fa in alkali ya kira ka kaje,amma in kun samu masalaha a gida sai ta janye batun Kotu.

Halifa yace Zan fi son hakan saki take bukata zan bata. "Karka yi saurin yanke haka, ka fara kiran waliyyin nata sai muji yadda za a yi.

Halifa ya ja tsaki kan mace Bros bazan dauki rainin hankali ba, babu wanda zai mutu dan baya tare da wani. Yarinyar nan fa ta wani gefen alfarma na yi mata,amma wai har ita ta kai mutum!!

Adamu yace "Haka ne amma abi komai sannu.

Kamar yadda Hajiya Talatu tace,tana idar da sallar asubahi ta kama shiri ta kalli Anty wadda ta idar da sallar tana kwance tana ta saka da mugu zare. Tace "To Sahiba nifa zakara zai bani sa a, zan zarga wa kare na igiya in yi gidana bazan bari wancan bomb din ya tashii da ni ba,dan kuwa dole zai tashi.sai dai in har ki ka kiyaye abinda zan fada miki to ba shakka asiri ba zai
tonu ba, ke koda asirin nan ya tonu to zai tonu a kuraren lokacin da sai dai su yi da sun sani.

Anty tace Hakan ma in yafaru ni ce da godiya.

Hajiya Talatu ta yi kasa da murya tace 'Kamar yadda na fada miki,wannan takardar sakin in har su ba jahilai bane kotu za su nufa shi kuma bai san zance ba yaga sammaci a zuciya irin tasa da kike fada ba zai je ba,saidai ya tura lauya to ke kuma sai ki maza ki siye lauyan kiyi ta tsara masa abinda zai fada masa da kuma yadda zai yi a kotu.'
Anty tace Kash ga bikin zuwa amma babu zanin daurawa.

Bani da kudin da zan baiwa lauya kina dai kallon rigimar dana dakko ta kudin mutumin nan gashi saura dari da Talatin duk na Bawa malamai. Hajiya Talatu tace Sai a kuma tambayar sa ya karo wani abu,naga fa kamar wani wawa sai sanda kika samu kya bashi. Anty tace 'Tab wannan fa daga gani dan tijara ne, amma dai bari mu gani in har suka kai shi karar ko ina ne zan nemo kudin dan dai inga bayan su. Hajiya Talatu tace Da kinyi kyan kai,yanzu dai ki samo min kudin mota in sa kai. Anty tace ko kwabo,ke din da duk kudin da kike min kwange ,ina kudaden da kika yi ta amsha gurin malaman nan ki na cewa zaki yi musu Transfer banga kin tura komai ba."Zan tura musu a hanya,network ne jiyan nan,zanci musu kudi ne?" Haka dai suka rabu suna ta yi wa juna ba a,da cin fuska.

Tana isa gurin Get Halifa ya shigo daga masallaci. A tsorace ta kauce ta yi gefe. Ya ja dogon tsaki.

Asiya ta na zaune kan gadon Asibitn kuka take kuma ta ki ci ta ki sha,bakin cikinta an kai Halifa Kotu,sannan sun ki sauraron ta tana fada musu akwai alkawura da Halifa ya yi mata ciki harda alkawarin ba zai taba sakinta ba,dan haka ita bata yarda cewa shine yayi sakin ba. Sai likitan ya bada shawara cewa a kaita Dawanau,akwai alamun Depression a tare da ita.

Halifa ya shiga cikin gida ya sauya riga ya fita zuwa gidan Baffan shi bayan sun gaisa sai Halifa ya sanar da Baffan sa halin da ake ciki na kararsa da Asiya ta yi, sannan ya nemi shawarar Baffan sa game da shi hukuncin da ya yanke, na bada takarda a kai kotu. Ko kuma ya aika mata da ita gida.Baffa ya yi salati daga bisani ya ba Halifa shawara cewa ya koma gida,insha Allah zai taka har gurin Waliyyin yarinyar su yi magana. Da ciwon kai ya koma gida. Yana ta kai kawo ga takarda da biro tun jiya ya kasa rubuta saki, sai yana ganin kamar ya karya alkawuran daya daukar mata.
Wata zuciyar tana ta zuga shi akan ya sake ta kawai tunda ita har ta iya kai shi kotu.

Washegari
Hafsi ta kwankwasa dakin yace shigo ta turo kofar tare da fadin "Uncle ga break fast din ka." Tafi dashi banaci, daga yau karki kara kawo min abinci dan Allah !! Ya daka mata tsawa .A gigice Hafsi ta fita. Anty kam dama ta san haka ce zata faru,Ada ma lokacin da bai fara zuwa kasuwa ba in yana fushi ba zai ci abincin gidan ba, kafin tasa a raunata mata zuciyar sa. Tace yarinyar nan da za su koma zama iya fushi da bakar zuciyar nan ta Halifa ka dai zata koreta gidan su.

Hafsi tace lokacin da zan shiga naji yana ta maimaita cewa wai ni Asiya zata kai kotu. Menene me zafi har haka? Anty ta tashi tsaye tana fadin anzo gurin bani wayata ta soma neman wayarta cike da murna. Hajiya Talatu tana dagawa ko gaisuwa bare ta tambayi ko har ta isa gida,abinda kawai ta ce Sahiba sun kawo masa sammaci. Hajiya Talatu cike dariya tace Alhamdulillah. Komai ya zo kamar yadda muka tsara,da sauki, kije ki lallaɓa shi kiji komai dan mugano bakin zaren muna bukatar samun lauyan, ta yadda zamu saye shi ya yi mana aiki." Anty tace wai ba yanzu ba, dan kuwa a fusace yake da kowa'zai iya komai in ya hau dokin zuciyar nan tashi.

Zanbi a sannu in dinga samo labari ko ba ta gurin shi ba.
Baffa ya samu Abban su Sulaiman a bakin wapa inda suka yi mahada,sun tattauna game da matsalolin kafin suka tsaida shawara cewa Abban su Sulaiman zai samu Inna da yarinyar kuma duk yadda ake ciki zai sanar da Baffa.

Abban su Sulaiman ya Isa gidan su Asiya ya yi sallama, daga ciki Sadiya ta amsa dama ita da yaranta ne a ciki Inna tana Asibiti da Asiya Sadiya ta fada masa cewa suna Asibiti bayan ta gaishe shi, yace To amma Yaya baku fada ba ko ke ba sai ki shiga ki sanar da Umman su Sulaiman ba?Sadiya tace an fada musu Abba inaga dai sun shafa a ne basu sanar da kai ba. Ya tambayi Asibitin ta sanar da shi, ya yi addu'a ya ce yaje gobe da sassafe ko kuma bayan issha yau in ya samu sarari.

Sannu a hankali Halifa ya gama kwashe kayan shi ya kai su sabon gidan shi duk ba tare da kowa ya sani ba.
Abban su Sulaiman ya kira Baffan Halifa ya sanar da shi cewa ya yi hakuri yarinyar bata da lafiya tana Asibiti in ta samu sauki za su zauna. Shima da safe zaije ya ga jikin.

Ya samu Asiya tana zaune Inna tana ta godo da ita akan tasha kunu amma taki. Yace" Ki amsa mana ki sha magani ai sai da abinci." Inna tace ka ganta nan tunda mijin ya aiko mata da takarda gaba daya ta haukace, sai zantuka take yi wai wallahi bashi bane ya mata alkawarin bazai sake ta ba,wai sai abarta taje ta tambaye shi. Taki ci ta ki sha, sunce ma zamu je dawanau ayi mata gwajin kwakwalwa. Ga hawan jini sai ya sauka ya kuma hawa,Wallahi Malam ina yin dana sani akan wannan aure na gaggawa da aka yi huce haushi kawai ya yi amma sam Halifa baya kaunar yarinyar shida yan uwansa har fa cewa ya yi shi ciki ba nasa bane.

"Subahanallahi " Abban su Sulaiman ya fada, abin har ya yi tsamari haka? Ashe har ya aiko da saki,ni da na zo ne akan batun kotu waliyinsa ya fada min suna son a yi masalaha a gida."

Inna tace "Masalaha yanzu ne suke son masalaha tunda su masu dashi ne suna jin kunyar tsayawa a gaban alkali masalaha daya ce ya karbi cikin shi domin ba zai yiwu ya tarwatsa mata yau sannan ya tarwatsa mata kuma goben ta ba. Ta tashi da dan da bashi da uba,wa zai aureta, shi kanshi dan an tarwatsa masa rayuwa fa kenan.

Abba cikin rashin fahimta yace "Wai tsaya, kina nufin cewa ya yi ba dansa ba ne?" Haka yace a jikin takardar daya aiko mata ta saki har uku. Na ce ko daya ma ya yi mata dama ni ba bari zan yi ta koma ba cutar ta isa haka.

Abba ya yi shiru ya rasa abin cewa. Ya kawo dubu biyu ya basu yace "To ni zan tafi,insha Allahu zanje har can gurin Baffan na shi in ji."
Asiya ta dago ido tace Abba dan Allah ka ce su barni in koma gidan mijina wallah bai sake ni, sharri ne kawai, wallahi ko da zai sake ni ba irin kalaman da ke cikin takardar zai rubutaba na san Halifa kuma na san me zai aikata.

Abba yace "Allah ya baki lafiya lallai kam da matsala" Gara kuje a duba kan nata."

Asiya tace Abba dan Allah a maganganuna ina ne na yi maganar rashin hankali? Ya ce 'Babu Asiya " Tace to me yasa ake jifana da kalmar hauka? Shiya sa nake yin shiru.

Haka dai Abba ya tafi cike da jimami na halin da yarinyar ta tsinci kanta.
amma kanshi a daure,domin shi Baffa bai fada masa cewar anyi saki ba,hasali ma dai ya nuna masa sun kai kara ne akan a bata takardar ta.

Halifa ya gama shiri tsaf zai fita sai ga kiran bros yace masa lafiya yanzu na shigo gidan na samu ana rigima Anty Umma ta zo kwasar kayan dakin ka Anty ta hana kuma tana ta kiran wayar ka amma ba ka daga ba. Halifa yace na ga ni Bros kawai dai ban daga bane saboda bana son in fadawa Anty abinda yafi wanda na fada mata ran nan. Ni na tashi a gidan gaba daya na bawa Anty Umma kayan tafi Anty bukatar su. Da yake a hands-free Bros ya saka duk suna ji su Antyn. Lamarin ya girgiza Anty har ta fasa kuka yau ita Halifa zai guda sabodar matar sa,to wallahi in zata yi yawo tsirara sai ta raba shi da ita.

Bros ya ce Anty kar ki dauki wani alhakin mana.Ita kanta yanzu haka bata gidan amma kin dora alhakin a kanta maimakon ki yi tunanin ina ne ki ka masa ba daidai ba ya za ayi kuma a gyara!! ""Kai ka min shiru Halifa haihuwar sa ne kawai ban yi ba,kuma kafin ya auri wannan yarinyar lafiya lau muke kowa ya sani,dan haka bazan bar wannan ya tafi a banza ba. Ta nufi ciki tana kuka.

Halifa kuwa dama ya na kai karshen maganar shi ya kashe waya,sai dai kuma kukan da ya ji Anty ta saka ya tsaya mishi a zuciya. Ya soma tuhumar kan shi, wai ma akan wane dalili ne ya yi irin wannan fushin haka? Saboda abin duniya kudi abin banza. Kayan lefen me? Ya dauki waya kamar ya kira Anty amma sai ya fasa,domin ya san halinta yana kiranta dan ya nuna mata ya yi kuskure zata hau dokin zuciya sai ya yi ta bata hakuri zai jira ta neme shi tukunna.



*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w

Asiya Ta bude ido dakin kowa ya yi bacci Inna ma tana kan tabarmarta ta tada kai da da kullin kayan su wanda Inna ta hada da safe za su tafi Dawanau ganin likita. Asiya ta sauka a hankali ta fice daga dakin, Asibitin ya yi tsit wannan ke nuna dare ya yi nisa

Ina zata ga Halifa yanzu tana son ta samu tabbaci akan sakin da ya yi mata. Bata da kudin mota amma haka ta ci gaba da tafiya kanta ma gaba daya ya juye bata san ina take saka kafarta ba.

Kadan wani mai kekenapep ya bige ta, yace ke Malama ta shi a hanya mana? Tace dan Allah ina neman hanyar Gandune gandun sarki .Yace Kina kan hanya amma dai ba a kafa zaki ba ko? Tace to dan Allah ko zaka taimaka min wallahi daga Asibiti na ke. Yace can din gun wa zaki je? "Ta ce gidan mijina zani. Ya saki baki yana kallonta. Yarinya ce karama kuma gata wata iri amma kuma kamar mai ciki. Yace kinsan gidan kuma yana nan mijin na ki? Sai lokacin ta tuna in kuma yana can gidan su Anty fa? Amma saita ji zuciyarta ta yarda cewa zata same shi a sabon gidan.

Ta dube shi,in Allah ya yarda yana nan. Yace To hau muje amma ni da har na tashi daga aiki wai nawa ma zaki bada? Tace ko nawa ka ce zai baka muje kawai ta fada cike da kwarin gwiwa.

Sun fara tafiya sai yace "Wai to ki kira shi a waya mana. Tace wayata ta mutu ko kana da waya ka ara min ?' Yace kin rike number ne?' Tace Na rike.

Ya dakko wayar ya bata. Ta saka lambobin gabanta yana faduwa.

Tana kira ta fara ringing sai dai har ta katse ba a daga ba. Ta sake kira sai aka danna busy Tace Allah ka bashi ikon daga wa, wannan ce dama ta Allah ka ceci aure na. Me a daidaita ya ce ko baya daga wayar da bai sani ba? Asiya tace yana dagawa dan kasuwa ne fa.

Ta sake kira cikin sa a ya daga tare da sallama. Jin muryar shi sai tsoro ya kamata ta kasa magana. Yace "Hello ka na jina kuwa?" Cike da rawar murya Asiya tace Yaya ni ce Asiya kana ina ne gani nan zuwa. Ya maimaita sunan Asiya yanzu da tsohon daren nan daga ina ki ke tace daga Asibiti.
Nan take Halifa ya zabura ya mike dazu Baffa ke fada masa cewa Abban su Sulaiman ya fada masa bata da lafiya har ana maganar zuwa dawanau dan haka su aje maganar a gefe sai yarinyar ta samu sauki. Yanzu haka abinda ya hana shi bacci kenan yana tunanin wane irin ciwo ne sai anje dawanau? Zuciyar sa ta zuga shi akan kar yaje Asibitin domin yaji matukar bakin cikin sammacin da aka kawo mishi. Ya ce Asiya to kuna ina yanzu? Tace kana sabon gida ne can zamuje. Yace Ina can ke da waye? Tace Dan sahune yace bashi wayar." Ta mika mishi yana amsa Halifa ya ce kar ka tsaya ko ina ka wota nan Gandun Sarki ya yi masa kwatance.

Bakin layin ya fito ya tsaya. Sai ga su a dan sahu. Halifa ya tsaya cike da mamaki yana kallon yadda kiwon sa ya lalace, yarinyar ta rame ta yi baki ta koje,sai ciki kwi kamar an kifa kwarya. tana zare idanu. Ta nufo shi tana kuka ta shige jikin sa,ji ya yi gaba daya tana wani irin tsami. Ya dago fuskarta yace Asiya hakan da ki ka yi kuma adalci ne a gare ni? Bata yi magana ba,ya kalli dan sahu 'Nawa ne kudin ka?" Ya tambaya bayan ya rungumeta gefe daya yana laluba aljihunsa.Dan sahu yace kawai ka bada Megida aikin ma na tashi kawai dai taimakonta na yi can waje Tukuntawa na ganta.

Duk da Halifa bai zaci zai samu kudi ba domin jallabiya ce a jikin sa,sai ya ci sa'ar samun wasu sabbin yan dari biyu irin wadan da yakan je da su sallar Asubahi dan rabawa sadaka. Bai tsaya kirga su ba ya ce to Oga gashi ka yi hakuri da wannan na gode. Dan sahu ya amsa yana fadin "Nima na gode megida."
Har ciki Asiya ta yi karkadaf da Halifa kamar tana tsoron kar ya kwace mata.
Sai da suka shiga lafo ya sake tsorata da hasken fitila ya bayyana ta sosai, idanu sun yi jajir ya zaunar da ita kan kujera ya dakko ruwa mai sanyi daga firji ya bude ya bata. Ta amsa ta kama sha har sai da ya tsorata wata zuciyar tana

Please Login or Register in order to submit comment