Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan take.
Tana ta sauri ta kwashe awarar da ke cikin mai ta. tashi ta shiga gida domin ga shi can ana ta salla a massalaci. Tana cike da tunanin yau yanmata layin su sun bata mamaki sai zuwa suke suna tambayarta Wai lefenta aka kawo yau she ne bikin? Har da masu cewa ta kawo masu ankon in an fitar. Hakan ya sa taji ashe ita ma takai.
"Nawa awara?" Aka katse mata tunani da tambaya. Uku Hamsss ta kasa karasawa lokacin da ta dago ido ta kalli mai tambayar ba zata tantance saurayin nata ba, amma wannan taga ya mata kwarjini ya kuma cika gurin. Ya tsuguna ya dauki guda daya, tare da fadin." Akwai alakoro kasuwa?" Ta sunne kanta a cinya sannan ta tashi da gudu ta nufi cikin gida.
Sadiya ta taimaka mata ta gyara duk da wata zuciyar tana tambayar ta cewar tana da tabbacin shine? Ta fesheta da turaruka ta yi gayunta cikin atamfarta raifes ta sallah ce. Sadiya tace to kije zan zubawa Abba awarar ya kawo masa. Inna tace ga hamsin yazo ya amso fiya wata me sanyi gida Maman Huda.

Asiya ta kalli dakalin bayan ta fito. Yana zaune yana danna waya hasken fitilar kofar gidan ta haske masa fuska. In banda Allah wa zai maka Haka. Asiya ta darsa a zuciyar ta. Tasan ko kusa da ajin wannan gayen bata zo ba.
Ta taka a hankali ta isa gurin ta rusuna sannu da zuwa. Ta furta tana Kallon fuskarshi dan samun tabbacin ko shidinne..
Ya Kalle ta "Tashi mana ammmm Sadiya ko?" Tace Asiya dai Sadiya yayata ce. Yace sorry tashi Asiyatu. " Yanzu kam ta tabbatar shine. Ta zauna da yar tazara tsakanin su. Ya kalleta "Asiya ya jikin Baba ina fata yana samun sauki?" Tace so sai ma kuwa musamman jiya zuwa yau tamkar ka zo masa da waraka Muna ta yi wa Allah godiya.
Ya yi murmushi ashe tana da magana haka. Ya darsa a zuciyar sa. Sannan yace, "To Malam Asiya ya ki ka ga angon na ki?" Ta dan yi murmushi sannan ta sunkuyar da kai, tace me kake son infada? Yace Duk abinda ya zo bakin ki. " Ta danyi jim wani jin kai wanda bata san tana da shi ba ya motsa ta saci Kallon shi ta ga ita yake kallo, tace masha Allah barakallah.
Ya yi murmushi ya ga wani hali guda daya da yake so, yana son mace mai jin kanta cewa ita mace ce, yarinyar in ta samu kula zata yi yadda yake so. A zuciyar sa yace Bari ya sake latsata.
Ya dan yi gyaran murya. "Na yi mamaki fa wai ya akayi kika amince da ni haka? Da ga ganina fa baki sanni ba."
Ta danyi jim tana nazarin me zata fada, can tace Duk abinda na roki Allah a kai yana amsa min. Kullum Babana yana cewa "Allah ka kawo wa Asiya da Sadiya miji wanda zai kula da su ko bayan raina. Kasan ina girmama kalaman Babana jin haka sai nima na dora da adduo'in ina rokon Allah ya cika burin Babana ya kawo min mijin wanda yake zabin sa shi. To kana ganin cewa ba kai ne amsar addu a ta ba? Ya yi murmushi Ni ne gaskiya domin ba zance ga dalilin da yasa na yi miki maganar aure ba, Allah ne ya aiko ni, to kuma kina so na?" Tace Ni ban san so ba, amma zaka iya yimin bayani yadda ya ke.
Yace shike nan zan koya miki "amma sai na cire son wata a zuciyata." ya tsura mata ido. Itama ta kalle shi sannan ta sunkuyar da kai. Tace" To. " Abba ya yi sallama ya aje flas din awara da fiya wata a Leda. ya gaishe da shi ya amsa tare da tambayar kai ne Abba? Abba yace,"Nine. Halifa ya ce to Malam Abba maida wannan abin gida naci dazu." Ta kalleshi. baza ka kara ba?
Ya girgiza kai, tace shikenan Abba wuce da shi amma ka aje masa ruwan. Ta ciro daga Leda ta mika mishi, wani abu da yake ji tun da ya shaki wannan hodar ya kuma taso masa, ya danja tsaki sannan ya ce" Ki barshi . " lokaci guda kuma ya mike tsaye, ina ga zantafi ina jin kamar bana jin dadi."
Gaban Asiya ya fadi. Allah dai yasa ba ni ce na bata maka rai ba. Ta fada cikin damuwa. Yace ko kadan ya cije game da sabon yanayin yace "Amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida, haka Hausawa suke fadi ko?" Asiya ta marairaice murya tace Yaya ban iya hira ba ko? Ta. mike ita ma, ka yi hakuri ban taba zance bane amma zaka koya min? Yace "Ai zancen mu bashi da tsawo ya kamata daga yau ma a dena wanna awarar a soma gyaran jiki ko?" Ta ce to duk yadda ka ce. Ya soma tafiya tare da fadin dan takamin mana."

Suka jera a hankali suke tafiyar yace Wai kuwa kina samun nawa a rana wannan awarar? Tace "Gaskiya muna samu, har dubu biyu fa wata ran muna ci a kwano daya, kai ko anyi kwantai fa muna samun abinda Baba zai ci mu kuma sai muci awarar ka san ba kowane abinci yake ci ba. Wataran kuma sai Maman Annur Sadiyarmu tana zuwa da abincin da zai iya ci daga gidan aikin ta sai musaka kudin sai masa abinci a bankinmu na kudin maganinsa. Yace Allah Sarki Ubangiji ya baku lada, ku kuke ta fama da gidan da kudin jinyarsa, ba masu taimaka wa ne a unguwar? Tace "Sun yi fa, yanzun ne kowa yana fama da kanshi, kuma gaskiya ni nafi son mu yi sana a da mu tsaya neman taimakon." Yace Haka ne yanzu kuma gashi zan dauke ki wa zai ke yin awarar? "
Asiya tace Abba zai ci gaba ko don kula da Baba, ta fada a rauna ne, domin sai taji wani yanayi na kewar rabuwa da ahalin ta. Daidai lokacin sun Iso shagon saida kayan masarufi ya ce ina zuwa, ya shiga, tana bakin shagon daya daga cikin masu saida kayan yace "
Asiya waken awara kwano nawa? " Tace ba siya na zo ba yanzu. Yace "Asiya Wai ance za ki yi aure da gaske ne?" Tace injiwa? Wani daga ciki ya am she da fadin gaske ne mana, har lefe an kawo. Wanda ya yi tambayar yace harda su lefe abin azimun amma waye wannan haka zai yi jihadi?"
Sai lokacin Halifa ya sa baki don tunda suke magana bai ce kala ba yana dai ta fadin a miko masa wannan nawa wancan. Yace Ba musulma bace dama? Suka ce Musulma ce yace me ya kawo batun jihadi? Wanda ya furta kalma yace to Megida duk yan matan garin nan ga sunan kosassu wannan kalleta fa kamar ka hureta ta fadi, anya ma ta isa aure? Halifa yace " Ina dai tana da halin kwarai?" har suna hada baki gurin cewa wannan kuma sai ince kaf unguwar nan da wuya asamu wadda tafi yarinyar hankali ga nutsuwa inda wata ce muna fara mata wannan wasan kasan da yanzu ta zage mu.
Halifa yace "wannan ai ba wasa bane, kuma ni ne wanda zai yi jihadi da ka ke magana, ni ne mijin Asiya sai ka duba ka gani dame ka fini kai da kake kushe ta?"
Mamaki ya ishe su, duk harda masu siyayyar suka kalleshi babu wanda ya kara magana cikin su sai wani da shima ya zo siyayya yace Allah ya sanya alkairi.
Kayan shayi da sabulan wanki da omo su makilin su ya siya da bread leda biyu ya biya su ya dakko. Asiya wadda taji duk ta muzanta a gaban saurayin ta an ci mata fuska kuma tanaji duk jikinta a sanyaye ta kalli fuskar Halifa. Tace kaji me mutane suke fada game da ni ko? Kamar bai ji me tace ba ya mika mata ledojin "Amshi wannan maza kije gida zan kira ki". Tace ai ba waya a gidan mu. Ya ciro wayoyin sa guda biyu ya mika mata babbar ki rike ta da kyau akwai muhimman abubuwa na aciki, zan kira ki. Duk wanda ya kira ki daga ki ce a neme ni ta daya layin. Tace To. Mun gode Allah ya jikan mahaifa ya kara budi. Cikin jin dadi ya ce "Ameen."
Ya nufi can inda ya yi fakin ta kwashi kaya Niki niki ta nufi gida.


Kafin Halifa ya kai gurin mota ya soma amai da kyar ya ke jan motar, yana ta amai. Yana shiga gida ya aje motar ya fito. Kanshi ya sara da ciwo ya nufi dakin shi, jiri na dibar shi. Yana kokarin ya bude kofa sai ya fadi a gurin yana maida numfashi. Yana son ya ciro Wayar shi daga aljihu Hafsi tana isowa gurin kamar yadda Anty ta turo ta ta duba mata ko shine dan taji shigo war mota.

*** ***

Bilkisu ta kalli mahaifiyar ta tace na gama jan Ya Wadudu kafa dubu kuma ba wanda na kuskure ban hada da sunan shi ba, yanzu saura sadakar kosan da zanyi da safe ko?
Mahaifiyar tace e "Ai insha Allah gobe da kafarshi zai shigo gidan nan yana baki hakuri har sai kin ja masa aji." Bilkisu tace humm ya dai zo din Umma ko ban ja masa yanzu ba muna komawa daidai sai ya gane Allah daya ne, dan zan rama abinda ya yi min. Umma ta sa dariya "Sun isa su sani inji kunya Asa bikin shekara guda sai da lokacin ya zo ya fasa, aiko da na kai shi Human rayit su bi miki hakkin ki na bata miki lokacin da ya yi sannan ya hana ki kula kowa, ta ina zaki fara yanzu shekarun ki a shirin da bakwai fa dan ma muna zabge uku muna cewa ashiru da hudu ki ke. " Bilkisu tace ai Halifa ma ba zai iya rabuwa da niba, na fa san irin son da ya ke min, duk barazana ce.

*** ***

Hafsi ta juya tana kuka, da ihu ga Uncle Halifa ya fadi. Da gudu suka fito Hajiya Talatu da Anty shigowar Dady kenan ya dakko mota sai Asibitin.
Likitan ya gama gwaje sannan ya sa a bashi taimakon gaggawa sai da aka gama tsaf yana kwance an sa masa ruwa. Ya dubi su Anty me ya ci na karshe? Duk suka yi Jim Anty tace sai dai kuma shine zai fada tunda daga waje ya ke. Dady ya kalli Likitan menene a cikin abinda ya ci?...



*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: Page 5

Likita yace "dole aƙwai abinda ya ci ko ya shaƙa ko kuma ya jima bai ci komai ba kuma yana da ulser. Halifa dake jinsu sama-sama har dai bacci ya yi gaba da shi.

Hajiya Talatu ta kira Ma u suka fita waje, ta Kalle ta tace, Allah ya sa aikin nan bai baci ba, dan Malam bai ce mana zai yi jinya ba. Ma u tace "Ki kirashi mana, shi malamin." Uwar tace sai dai in tafi gobe kinsan na Shuri baya son daga waya a tsakiyar wata sai farko ko karshe. Ma u tace "To Wai saboda me?" Uwar tace Aljanu sun hana, Ma u kin kuwa binne layun nan? Tace " Tun yaushe Mama nifa yanzu jiran sakamako nake yi zuwa gobe. Tace to Bari mugani in ta kama sai na koma Shurin gobe zance zani Rimin kebe ko Wudil sai kawai in koma Zariya in tafi shuri. Ki koma ki kwanta kar waccan anamimiyar yarinya ta farka.
Hafsi dake labe ta girgiza kai bayan taji komai domin lokacin da Uwar ta zo ta tashi yar Hafsi ba bacci take yi ba tana chatin ne a cikin bargo da saurayin ta.

Biyun dare su Anty da Dady suka dawo Bros Adamu aka kira ya kwana gurin sa. Hafsi tana jin shigo war mota ta fita da sauri ta fara tambayar iyayenta jikin uncle Halifa. Suka ce mata da sau ki Sannan ta ja Anty gefe ta rattafa mata komai game da abinda taji. Tace banyi mamaki ba, domin na san ruwa baya tsami banza, matar nan da shirin ta ta zo. Shike nan kici gaba da samun ido sosai a kan duk wani motsin su.
Tana shiga dakinta Hajiya Talatu ta baje tana bacci sai uban minshari ta ke saki, Anty ta harare ta ta ja tsaki Sannan ta wuce bandaki.


Asiya ta ji waya tana ringing ga zaton ta shine duk da taga an rubuta favorite ba Wai ta iya waya bane, ta san dai koren shine dagawa.
Ta daga da sallama cikin wata muryar da bata san tana da ita ba. Sai taji an katse ta da cewa "Ke wacece ke? Ta ce ni ce Asiya ki kira daya layin nasa. Bilkisu ta yi shiru ko zata tuna mai irin sunan a dangin su Halifa. Rashin tunawa ya sa ta danja tsaki tare da sake fadin " Ke yanzu me ya kawo wayarsa gurin ki.?" Asiya ta danyi jim tana tunanin ko yan gidansu ne. Bilkisu ta katse ta da fadin cewa "Ni matar sa ce ina miki magana kin min banza." Wani abu Asiya taji ya daki kirjinta matarsa kuma. Ta sauke ajiyar zuciya tace A iya sanina ni ce matar sa domin ya biya sadaki na, ko da yake ki kirashi ta daya layin kinga sai da safe. Asiya ta kashe cike da tashin hankali.

Cikin dare Halifa ya farka bayan ya yi wani mummunan mafarki, Bros Adam ya gani yana zaune kan kujera ya kifa kai a jikin gado. Jin motsin shi sai shima Bros din ya farka. Ya yi masa ya jiki, ya amsa da sauki. Yace jiya naji zuwan ka ashe baka tafi ba bacci ya dauke ni. Bros yace "Ni ai mamaki naji kai da baka fiye yin ko zazzabi ba. ". Halifa yace Aii gara a dan dinga taba mu muma abin ne ya zo ba zato Allah ya kara mana lafiya. Kai kwana biyu bamu hadu ba, tunda aka soma hatsaniyar bikin nan ban ganka ba. Bros Yace "Munyi sabani na zo Anty take min korafin abinda ya faru, to bance komai ba domin kun fi kusa." Halifa yace au Haka ma zaka ce? "To me kake so ince Uncle Halifa, nan ka goyi bayan Anty aka wai dole saina saki mata ta, ina sonta yaran mu biyu amma aka kasa min uzri." Halifa yace Bros kaga dai Anty Yayata ce kai ta haifa ba ni ba ko? To mace ko yar uban waye zan iya sakin ta matsawar ta zagi Anty kamar yadda aka ce matar ka ta yi.
Bros yace to ba komai ai gobe saurin zuwa gareta, baga dai auren zaka yi ba, Allah ya kade fitina. Yanzu bikin yana nan a lahadi din?" Halifa yace ameen. Yana nan insha Allah Wai kuwa ina wayata? Sai ya tuna ya ba Asiya sai karamar dake kusa da shi, yasan yanzu tana bacci ya dakko kirane Kala kala. Bros yace jiya har zan shigo kasuwar ku in duba wa Maman Nihal waya bakin kwastomomin mu na nijar ba su tafi da wuri ba. Halifa ya Kalle shi " Wai kai duk da kun Rabun da kyar Amma har hanzu kuna tare? Bros yace " Nifa na maida mata ta kuma tuni na kama mata haya yanzu ma cikin ta ya kai wata biyar."
Halifa ya tashi zaune har yana yarda karfen dake dauke da ruwan da ake kara masa, Nus ta shigo da sauri tana ta bayar lafiya? Ta taimaka masa yace ta cire ruwan haka ya isa tun jiya ake dura min ruwan nan. Tace ka yi hakuri ya karasa, kafin ta rufe baki ya tuge allurar karin ruwan ya rataye, jini ya biyo baya. Bros yace kalli to abinda ka yi Uncle. Ya dafe masa gurin da yatsa. Ta kawo auduga ya manna ya dafe. Bros yace "Kai Uncle dan Allah ka rage wannan dabi ar mana ace shi mutum komai sai yadda yake so harda lafiyar taka ma sai ka yi wasa?". Halifa yace Amma dai Anty bata San ka dawo da matar ka ba. Bros yace "Sai dai ko in kaine zaka fada mata yanzu. " Halifa yace ai da kasan zan fada din baza ka fada min ba, amma ina tausaya maka duk radda ta sani. Bros yace Matata fa bata zagi Anty ba kawai Anty ta raina arzikin sune kamar yadda na yi ta kokarin fahimtar da kai, kuma wai ita ce ta yi silar karayar arzikina wanda kasan I yan damfarane ba kuma ni ka sai suka cuta a kwariba har Anty tana tutiyar wai yanzu da muka rabu gashi komai nawa ya dawo, bata san muna tare ba. Ta amshe Nihal da Nur a gurinta.
Halifa yace Kabi a hankali mahaifiyar ka ce ka samu ku rabu lafiya. Amma ina jiye maka radda ta sani to yanzu ya maganar auren da take nema maka? Bros yace "Ni dai ba ina bita da to ba. " Halifa ya yi dariya shiyasa muka matsa ka dawo gida ka ki yarda?
Bros yace Kai Anty in ta sako mutum a gaba sai Allah, harfa zuwan bazata take tayi akai akai gidana kamar tana zargin zata samu Aisha a gidan lokacin ma ban samu gida ba muna Hotel ai wannan cikin a Hotel muka yi shi, gidansu fa basu da labarin wani saki, kai Bari ma dai in bude ka a mutum lokacin da Anty ta matsa ta tsaya gaba na ita da wannan shedaniyar kawar ta ta ta Zariya wai in rubuta takarda a take in bawa Aisha a jikin takarta na rubuta cewa taje ta jirani a can wani kebabben guri za muyi waya. Ina bata ta karanta sai ta hau kukan murna su kuma sun zata saki ne suka kwashe yara suka wuce. Tun a ranar naje na kama mana Hotel na kai mata kayan ta ni kuma sai da safe nake zuwa inyi shirin kasuwa lokacin ne take zuwa Wai ta duba ko ta dawo Shine kai kuma ka bullo da zance wai in koma gida. Na ce kaji Uncle zai ha wata fitina. Lokacin kam na kashe kudin abinci ma ka dai ba sauki. Da Anty ta matsa su zo su kwashe Kaya sai na kama gida muka bi dare muka kwashe. " Cike da mamaki Halifa ke Kallon Bros. Yace to wace Unguwar kuka koma? Bros yace Kuntau na samu wani gida mai kyau" . Halifa ya numfasa. To Allah ya kawo abin da sauki, ina jinjinawa ace Anty ta samu labarin nan.
Bros yace kullum ina adduo'in Allah ya fahimtar da Anty gaskiya wannan kawayen nata su ke zugata. " Halifa yace jiya ai na kusa doke yarinyar kawarta ta Zariya din nan kawai ta fesa min wani abu wai murnar biki. Tun abine fa har yanzu bana gane kaina so sai wallahi Bros. Bros yace dama ka doke ta wallahi Allah ya sa ba wani mugun asirin na su bane suka fesa maka. " Halifa yace Sai sun jira, asiri su zai ci su da suka yarda da masu yin shi, ni ina tare da kariyar Allah ko da yau she bana wasa da azkar kaga kuwa sai dai wata kaddara. Sunata hira sai kiran salla suka ji.


Bilkisu ta shirya tsaf da safe ta hada abin kari ta nufi Asibiti ta samu labarin rashin lafiyar Halifa ne daga bakin Hafsi lokacin da Bilkisu din ta kira ta domin ta samu tabbacin abinda Asiya ta fada mata. Sai Hafsi tace mata ba shakka haka ne yanzu wata zai aura kuma a wannan ranar sai dai yanzu haka yana Asibiti bashi da lafiya.
Mahaifiya Bilkisu itace ta hada abinda za a zubawa Halifa a abinci dan sake maido shi ga Bilkisu suna son su gyara abinda suka bata.
Halifa ya kosa likitan ya shigo ya bashi sallama domin kwanakin biyu bai leka kasuwar shi ba, yau kam zai fita. Anty da Dadi suka shigo da sallama Tace "Alhamdulilah jiki ya yi sauki Amma na tsorata jiya Halifa." Suka sa dariya, suna cikin gaisawa Bilkisu ta shigo da sallama bisa Jagorancin wata Nus. Halifa ya kalleta sai kuma ya kauda kai yana jin su Anty suna amsa gaisuwarta har ma da bata gurin zama, zuciyar shi ta shiga harbawa da sauri, tabbas yana son Bilkisu har yanzu fa. Ta ce "Yaya Halifa ya jikin? " Yace da sauki ba tare da ya kalleta ba. Bros yace nifa ina son inje in fita da wuri yau muna da baki a kasuwa. Halifa ya kalleshi ya yi murmushi domin ya tuna da hirar su ta dazu. Yace to ya kamata ka tafi nima dai in likitan nan ya kai goma bai zo ba Allah zanyi tafiya ta. Anty Tace "Zuwa ina ai ka kwanta sai gobe ka kara warware wa. " Halifa yece kin san Allah Anty ba zan wuce goma ba, karma ki bata baki ki. Anty ta yi shiru tana tunani inko haka ne dole ta koma gida kafin goma domin ta sa a nemo gurin da Sahiba da yarta suka yi biso. Bilkisu ta katseta da fadin Anty ga abinci a ba Yaya Halifa. Anty ta kalleta to an gode zuba masa ya ci.
Halifa yace na koshi ina godiya sosai ki koma da shi. Bros ya fice Anty ta kalli Dadi zo muyi magana ta jashi waje da fatan su daidai ta zata fiye mata waccan yarinyar. Bilkisu ta tashi da sauri ta zube gwiwoyinta a gana gadon da Halifa ya ke zaune tace "Halifa dan Allah Don girma da darajar mahaifanka ka yafe min wallahi na yi kuskure. Bazan sake yin wani Abu mai kama da haka ba kar ka fasa aurena Halifa ina son ka. Kaima na sani Halifa kana sona."
Halifa ya mike tsaye ya bata baya Ki tashi Bilkisu na yafe miki tun a ranar, sai dai kin makara domin zance na da Asiya ya yi nisa, ki gyara a gaba. Maganar so gaskiya ne ina sonki sai dai dama ba kowane abu bane da ka ke son shi ka ke samu. Ki yarda cewa labarin soyayyar mu ya kare tun ba a fara cin gajiyar soyayyar ba. Bana son ki tsaya Kiyi ta magiya domin ban cika maimaita magana ba duk da nasan baki cika fahimtar hakan ba. Tafashe da kuka, ya fice a dakin domin bazai jure ba. Anty ta biyo shi har harabar Asibitin inda ya zauna a kofar masallacin Asibitin. Tace Me ya faru kuma naga ka fito. Yace "Anty dan Allah ki ce ta tafi ko kuma ni in tafi." Wani takaici ya zo wa Anty wuya, tana bakin cikin yadda Halifa ke kara fito da wannan shegen ra ayi na shi. Tace Yanzu Halifa

Please Login or Register in order to submit comment