Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya gogayya da kowace mace.


Halifa tun da ya sauka a ma sauki ya kasa aiwatar da komai har kusan kwana uku sannan ya fita kasuwa dan duba kayan da zai siya, ko yawan magana baya so abinci kuwa sai mara nauyi, bai sami nutsuwa ba sai da ya dira a Madina Ya yi ta gwada lambar Asiya har yau dai babu labari.

Anty ta kira Hajiya Talatu domin tattauna batun su Halifa, duk da tana ganin ta gama da Talatu amma tana zaton zata yi mata wani amfani. Cike da mamaki Talatu ta daga a tsorace ta amsa dan yanzu tana dan shakkar Anty. Kamar babu abinda ya faru Anty ta soma fadin "Sahiba kin dai yarda ni, tun daga biki na rasa me na miki tunda ni na damu da ke sai nace bari ni in kira. Talatu tace" Sahiba haka ma zaki fada ni da kika yi barazanar halaka ni. Anty ta saka dariya cike da makirci tace Ai ranar na tabbatar cewa ke matsoraciya ce wasa fa na miki haba Sahiba karfin jarumtarki na jarraba, in na barki kuma in kama wa? Talatu tace Humm ina jin ki, fadi abinda kike son fadi nasan amfani na ne ya tashi da kin gama sai ki yasar da ni.

Anty tace To kin yi min mummunan zato da ba haka bane. Yanzu dai ina son ki saurareni ina ganin lokacin auren Ma u da Halifa ne ya yi nasan dai shine matsalar ki, Anty ta ci gaba da fadin nasan kinga abinda yake yawo a Tiktok na Halifa.? "Mun gani inji Talatu sai dai ko kaffara bazan yi ba Idan na rantse da cewa sharrin ki ne. Anty tace " Banyi mamaki ba dan kin gane, domin a sharri ke uwata ce yanzu dai ina son ki bani haske game da yadda zan fidda yarinyar nan daga Rayuwar Halifa, Na fahimci asirin baya cin su makircin yafi aiki, dubi wannan fa cikin yan mintuna na yi tunanin sharrin nan kafin awa shida har Duniya ta dauka. Talatu ta katse Anty da fadin "Yanzu dai menene muradin ki? Tace Shawara nake son muyi dake game da yadda za a barar da cikin tunda na yi kokarin kar a same shi, amma sai da ya samu, Na sake yin abinda za a zubdashi har wa yau suka rayu to yanzu tunda na yi nasarar rabata da gidan sai dai hankali na ya tashi da naji Halifa yana fadin matar shi ce kuma dansa ne.

Hajiya Talatu tace "Kuma muka ji ance ya sake ta ya kuma koreta da muka kalla a Tiktok da Ma u ta kamo gurin? " Anty tace Yan karawa miya gishiri ne mu ai mune muka sa a Tiktok din ba wani ba, sauran mutane suka ci gaba da ingiza mai kantu ruwa kuma sai hakan ya kara armasa abin da zama ya gagare shi yanzu haka zancan da nake miki yana can chaina sai kura ta lafa zai dawo.

Hajiya Talatu tace har na hango abinda zai faru tunda baya nan amma ni menene ladana idan na tsara miki yadda komai zai kasance?" Anty tace A daura mishi aure da Ma'u shine kawai, sai mu hada kai da ita mu sa mu biyan bukatar mu.
Hajiya Talatu ta saki dariya tare da fadin na yarda da wannan Dan haka yanzu zan shirya in bar Zariya in nufo Kano kinsan ance shirin zaune ya fi na tsaye zamu tsara yadda za a sace ta a zubar da cikin Ko mu sake danna mata wani sharrin da zai kaita gidan Yari. Anty tace ina fatan ki Iso lafiya Sahiba ta. Hajiya Talatu ta saki dariya bayan ta kashe wayar tace lokaci ya yi da zan rama wukancin da aka yi min......

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[8/13, 17:12] Ummi Tandama😇: Anty ta kalli Hajiya talatu cike da mamaki tace Wallahi Sahiba nasan kin iya shirya tuggu amma ban yi tsammanin har haka ba, yanzun nan sai da kika lissafa min kala daidai har a shirin wanda duk wanda na dauka a ciki sai na yi nasara. Cikin alfahari Hajiya Talatu tace "Ai Sahiba in kika ga na bar mutum ni na so, mutum nawa ke gidan yari wanda na yi silar zuwan su.? Kinsan Allah abinda kika min kwanaki wallahi wani abu na duba daban kawai na kyale ki, mutuncin da kika min a farkon haduwar mu bana manta alkairi ko yaya yake,amma wallahi da badan haka ba, da sai na shirya miki abinda dangin ki ma sai sun tsane ki.

Anty ta yi yar dariyar yake tace Sahiba kenan ai nima kawai dan na duba din ne amma wallahi danabi ta Malamin nan tuni zai batar da ke. Talatu ta saki dariya, tace "Ke matsalar ki tana da yawa wallahi. da kina duba mutunci bazaki sako dan kanin ki a gaba haka ba, duk abinda yake miki bakya gani kawai dai ki yarda ke muguwa ce ko ta ina." Anty tace naji yanzu dai mu koma kan maganar mu dan Allah na baki wuka da nama. Hajiya Talatu ta ja tsaki tare da fadin." Wai ba iya cikin kike son a zubar ba? " Anty ta amshe da faɗin Sai sakinta da nake son Halifa ya yi, wallahi da Adamu ne da tuni na sa shi ya sake ta, amma Halifa yana da taurin kai da muguwar zuciya, abinda ke bani haushi ya kasa kwada zuciyar akan yarinyar nan Sam. yanzu ma fa saboda damuwar ta ya bar gari ko kasar ma zan ce so nake kafin ya dawo na kammala ko mai sai kawai ya yi sabon Aure. Hajiya Talatu tace "Da Ma u na ba, "karamin alhaki ne wannan case din kawai zuwa zamuyi gidan nasu mu dauke ta zuwa Asibiti a kwakule abin banza a watsar mu maida ta mu dire. "
Anty ta ce to wane Asibitin zamu kaita kinsan dai babu wani Asibitin da za su yarda su cire mana ciki haka siddan ko? Hajiya Talatu ta yi wa Anty wani irin kallon raini Sannan ta ja tsaki, tace." Karki fada min cewa baki da daurin gindi a garin nan? Kina nufin baki da likitoci kamar uku da zaki iya kira su miki abinda kike so nan take? Baki da Yan sanda kamar biyar da zaki kira su a take ayi miki yadda kike so? Baki da lauyoyi da alkalai a hannun ki? Ke har faraskiton kotu da gandiroba San ina da su sunfi guda nawa. Ke yan daba ma ina da su saboda tsaro. Kuma duk wadannan Umarni kawai zan basu. Ta sake jan tsaki gaskiya naji kunyar hada hanya dake ashe ke gaba daya ma gwara kifin rijiya dake. "

Anty cike da muzanta tace Nifa bana rigima da kowa harda zan damu saina hada wannan gayyar ina zube musu kudi na. ke kuwa ai yar harkallace ko yaushe kin ari kudin wane kin cinye na wance. Hajiya Talatu tace" To yanzu wannan da zakiyi ya ci uwar harkalla, tunda kisan kai ki ke son a yi kuma Kaninki da ya yarda dake, ni kuma kinga ko wanda muke Uba daya bazan iya cuta ba bare cikin Ummana. Ta sauke numfashi. Kinga da kina da likita minti biyar ya yi yawa za a watsar da shi yabi sokawe. " Anty tace Menene abin yi dai yanzu? Hajiya Talatu tace yanzu muje yan magani mu sayi na zubda ciki muje gidan mu dauke ta mu kaita wani guri mu bata, ko kuma mu bata ma a gidan na su, in kuma zamu ja abin ya yi tsawo ka wai sai mu saka wani ya bata. Saboda karma a gane mu ne, amma fa zamu zama cikin zullumin na rashin tabbas. "

Anty tace Allah na tuba tunda ba wasu masu hali bane Uwar ma kamar wata sakarya a gaban ta ma sai mu bata. Haka dai suka gama kulle kullen su suka tashi.
Inna tana wanki na wankau da aka kawo mata, sai taji an doko sallama. a murya bibbiyu ta amsa tare da daga kai ta kalli su Anty duk da gabnata ya fadi amma sai ta dukar da kai ta ci gaba da wankinta bayan ta amsa sallamar a zuciyatar ta ci gaba da adduo'in neman tsarin Allah daga sharri su.
Anty tace Ko da kika kallemu kika watsar muma ba zama muka zo ba, ina yar iskar yarki mai bin maza gurinta muka zo za ayi gwajin kwayar halitta dan musani ko cikin ba jinin mu bane.

Inna bata tanka ba Hajiya Talatu ta fusata, tace "Ke baiwar Allah dake muke magana, kamar ke matsiyaciya har kin isa muna magana ki yi mana banza?
Inna ta sake dago kai ta dube su tace, Wai me yasa Mutane suke hana kansu sukuni saboda son zuciya kuma su hana wani? Anty ta ce ba gurin ki muka zo ba, mun zo ne gurin yar iskar yar ki ta zo muje a yi gwaji dan mu rarrabe domin bazamu dauki dan wani a matsayin dan mu ba, yawwa. Inna tace ikon Allah to bari in fada muku babu inda Asiya zata kuma ciki dole ku karba duk sharri da tuggu da kike shirya wa yarinyar nan da wani kaita gidan boka ko ki bata guba duk na banza ne domin zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho sai ya yi ina son ki sani tsakanin dan Asiya da Halifa sai yazo Duniya kuma sai ya gaji abinda ki ke kwadayin mallakewa.!!! Kuma kina raye zaki ga haka!!!

Ke!!! Anty ta daka mata tsawa. Taci gaba da fadin Ina son ki iya bakin ki ki kama kanki banda dalili ke kin isa ki fada min magana? Yar wanke wanke na tafi ki komai banza talaka matsiyaciya.

Ga ki matsiyaciya kina gorin arziki jahila baki san cewa wanda yake rabon arzikin shine Ubangijin talaka ba, kuma hakan ba yana nufin ya manta dashi bane. Kije ki nemi ilmi. kuma ku fitar min a gida ta dauki ruwan dauda na wa kin data tsoma tsumman share ruwa ta nufi kansu da shi tana fadin babu wanda bai iya tijara ba sai in bai so ba!!! Ta sheka musu a jiki ta nufi ruwan zafi dake kan wuta tana dumamen tuwo,. Tace sai in kona ku ku kukazo har gida. Da sauri suka yi baya sai dai tuni Inna ta wanke su da ruwan datti kuma tana fadin Auzu billahi minnashaidanirrajim.

Hajiya Talatu mamakin Inna ya cika ta, wai dama tana magana? Gashi ta wanke su da ruwan dattin ta kuma wawuro na kan murhu da gudu suka fita Anty tana sai na sa yan sanda sun rufe min ke.!! Inna tace na isa dauri muguwar mace wadda ke zalintar Dan Uwan ta to haka bakin ciki zai kashe ki insha Allah mutu ka raba Halifa da Asiya.

Lamarin nan ya bataran Anty sosai ba a taba ci mata zarafi kamar haka ba tunda Uwar ta ta haife ta. Har suka kai gida bata ce komai ba tana saka abinda zata sa a yi wa Innar su Asiya ne kawai dan ta gane tazarar da ke tsakanin mai arziki da matsiyaci.

Hajiya Talatu tace Ga abinda nake fada miki, yanzu in kina da yan sanda saidai ki bada Adireshi aje kawai a aje miki ita sai jibi zakije sai a lokacin zaki fadi abinda kike son a yi miki da ita. Idan nice fa wallahi matar nan sai taje gidan yari ko na kwana daya ne.

Anty tace ko yanzu bazan barta haka ba. Bari mu canza kaya muje ofishin yan sanda. Suna zuwa Anty zata soma bayani ga dansanda dake kan teburin Hajiya Talatu ta jata gefe tace ke in kika biyo ta haka fa mune bamu da gaskiya tunda mu muka je gidan ta. Harkar girma kawai za ayi kinzo da kudi dai ko? Anty tace "A a sai dai ki Ara min." Hajiya Talatu taje muje ki ciro baza a rasa gurin POS a nan kusa ba, bani da kudin da zan aramiki ba biyana kike yi ba.

Anty tace Au harda gori kuma har nawa zan ciro? Hajiya Talatu tace dubu Hamshin shima maleji za ayi dan na sanki da shegen son kudi bazaki iya fidda dari ba. Anty ta danyi shiru can tace "Ko dai share matar nan zanyi kawai in samu mu gama da yar tata? " Hajiya Talatu tace ai kinji matsalar ki duk da munyi wanka har yanzu ina jin tashin warin ruwan dattin talaucin da matar nan ta watsa mana kuma daga yau raini ya shiga tsakanin ku. Dan taci bulus Anty ta fusata ta fita zuwa zuwa POS. Tun a can Hajiya Talatu ta amshe kudin tare da fadin kawo ki gani ba a shiga irin gurin nan da kudi ttsirara.

Suna komawa Hajiya Talatu tace D. P. O. yana ciki? Suka ce bai shigo ba,. Tace D. C. O fa suka ce yana hanya. Tace to ina son a dakko min wata ne a Fage ta ci mana zarafi daga kawai kaninmu yana auren Yarta, sai aka kama ta da wani shine mukaje gidan dan taje ayi gwajin Kwan halitta tunda tana dauke da ciki shima ta watsa mana ruwan dauda tare da zazzagi mu.

Ta sa hannu a jaka ta tsakuro kudin ta mika shi gashi ku sha mai ku kawo mana ita nan sai gobe zamu dawo.

Jiki na bari Shugaban su na gurin yace maza a dakko mota ta sake kawo dubu daidai ta ba yan gurin Shugaban kuma dubu biyar tace ku sha ruwa a hanya. Nan fa suka dauki mata biyu da maza da direban suka ce muje ina kuka aje motar ku? Hajiya Talatu da Anty suka kalli juna. Hajiya Talatu tace ai bamu zo da mota ba, me adaidaita ne gashi can motarmu mun aiki direba bai dawo ba. Dansandan yace Ku shige gaba muje ku nuna mana gidan sai ku tafi abinku.

A cikin adaidaita Hajiya Talatu tace "Kawata wallahi yau naji kunya da Dansandan nan ya yi maganar mota ya kamata ace kina da mota taki ba wai ta Dady ko ta Halifa ko Adamu ba, sai zaki Je Unguwar sirri kina hawa adaidata sahu. Kin girmi haka wallahi ke ba tsohuwa ba amma baki jan mota da kanki. Yanda mata suke baza kafasitin nan da hawa manyan motoci suje Dubai da Umara akai akai, gaskiya Sahiba akwai bukatar yiwa rayuwar ki gyaranbawul. Anty ta sauke ajiyar zuciya tace kibari dai komai ya daidaita zaki sha mamaki yanzu ina sauran kudin ko duka kika ba su?

Hajiya Talatu ta zage jakar ta tura sauran kudin a karamin zif sannan tace, "Har dubu ta da dari biyar ta shiga, kece bakuwar ba Yansanda kudi....


.
[8/20, 22:26] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w


Suka aje mota a kofar gidan Inna suka tsai tsaya tare da tura matan ciki dan su kamo matar gidan. Sulaiman sun fito gidan su shi da Abban su zai tafi shago Abba za shi Unguwa sai kawai suka ga Yansanda a kofar gidan su Asiya. Abba da Sulaiman suka kalli juna dan neman karin bayani, amma kuma babu wanda ya san komai.
Abba ya taka kofar gidan cike da al ajabi dan jin karin bayani daidai lokacin da Matan yansanda suka fito suna cewa matar gidan tana salla sai sun jira kadan.

Sulaiman ya tako zuwa gurin wani matashi kamar sa a cikin yansanda yana tambayar sa ko lafiya?
Ya kalli Sulaiman "Kai dan gidan ne? Kafin ya bashi amsa ya ji wanda Abban su ya tambaya yana cewa " Matar gidan zamu tafi da ita. Da sauri Sulaiman ya matsa kusa da su daidai lokacin da Abba yake cewa ina zaton dai kunyi kuskure ba matar gidan nan bace, domin babu wata matsala da zata saka har a dakko mata ku. Dansanda ya fusata bangane me kake nufi ba, kana son kace bamu San aikin mu ba? To tare da masu korafin muka zo suka nuna mana gidan suka wuce ka ga kuwa babu maganar kuskure. "
Ina suke masu korafi? Abba ya katse shi. Malam Dan Allah ka tafi abinka ko ka jira in anje can ka bi kaji komai. Sulaiman ya tsoma baki da cewa babu inda zaku tafi da ita domin dai babu wani laifi da Inna zata yi wa wani. Sai ka hana inji wani ɗan sandan dake gefen sa dan baki kerere lebensa ya farfashe saboda shan taba.
Ina takardar shedar kamun ta domin dai ku ba yansandan nan Unguwar bane. Abba ya furta yana Kallon babban su wanda ya ke kada kai cikin isa.

Malam a Najeriya fa muke inba manyan mutane ba waye ake zuwa kamashi da waranti? Matar nan sai taje tunda ta ci zarafin Hajiya kawai dan tazo akan maganar auren kaninta bayan yarinyar ma an kamata da wani!! Abba ya ja tsaki tare da fadin Koma menene dai sai naga takardar shedar kamunta sannan zaku kamata. Wanda baisan kanshi ba shine ake zuwa a diba kara zube,ko da muke a Najeriya ba kowa bane lalatacce wanda bai san doka ba.

Sulaiman wanda ya gano daga inda maganar ta taso ya shiga kiran layin Halifa yau dai kam ko shiga bata yi, ba kamar kwanaki ba da tana shiga amma ya ki dauka, har Sulaiman ya fusata ya daina kira, Kenan ma ya yi Blocking dina Sulaiman ya raya a ransa
Takaici ya kama Sulaiman ya sa kai ya shiga gidan daidai da komawar matan yan sanda viki. . Suka ce mama munzo zamu tafi da ke office din mu. Sulaiman yace babu inda Inna zata je. Abba ya kira makotan su a waya ya sanar da su, wadanda ke kusa duk suka zo harda me Unguwar su. Take ya kira D. P. O na nan Unguwar ya tambaye shi cewa yarana ne suka zo kama matar marigayi makocin su. Take ya bincika ya Tabbatar cewa ba daga gurin su bane. Nan fa aka ce babu inda Inna zata dan ba su da hurumin kamata daga wata Unguwa ko daga sama ne sai an biyo ta kan yansanda Unguwa.

Mutane suka cika matasa suka soma hayaniya tsageru suka soma jifan yansanda wanda haka ya tilasta musu fesa tiyagas sannan suka dauki motar su suka tafi.

Inna wadda har ta saka hijabi tana cewa aje duk inda za a ta zauna tana kuka tana baiwa Babar su Sulaiman labarin abinda ya faru. Makota suka yi ta shigowa suna jajantawa Inna. Abban Su Sulaiman ya gama sauraron Inna yace ko sun dawo kar kije zalunci ne kawai irin na masu kudi, zan kira kawun shi wanda shine waliyinsa tunda abokina ne dan inji duk da sanin su ake ta wannan bada kalar, ke baki sanar dani me ake ciki ba, yanzu haka ma shi din bai san komai akai ba.

Inna tace " Ba mamaki in bai sani din ba, amma abin ya bi gari ana ta cecekuce jiya zuwa yaune abin ya lafa." Yace Allah ya kyauta. Tayi masa godiya suka yi sallama.

Anty ta zata Inna na kulle dan haka washe garin ma sai yamma sukaje ofishin yansanda sai dai wadanda suka samu jiya ba su ne yau a gurin ba, Hajiya Talatu tace ai ba matsala tunda dai mun san tana tsare bari mu nemi ganin D. P..O.

Bayan sun gaisa suka sanar masa cewa sune mutanen da suka yi rigima da wata mata ta kwana a nan. D. P. O yace bai San zan can ba, daga ina ne aka kawo ta? Suka ce daga Fagge Yace " Gaskiya bamu da hurumin yi muku case a nan kuje can Fagen ku yi case din a can. Daya sa aka bincika sai ya gano yan Unguwar sun hana a kamo matar. Yace to dama dai ba hurumin mu bane kuje Fagen.

Anty Wadda takaici ya hana magana har sai da suka zauna a Kekenapep ta ja tsaki ta ce Gaba daya kinsa na yi asarar dubu hamshin dina gashi babu wata nasara da aka samu shikenan matar nan ta ci galaba a kaina!
Hajiya Talatu cikin sigar wanke kanta daga zargin Anty tace "Ko kadan kar kiga laifina. Ke kika kaimu na Unguwar ku kuma ko yanzu din na can Unguwar ta su Fagen zamuje ai ba barin case din zamuyi ba." Bazanje ba"! Anty ta katse ta, " Kin ga Talatu na sako ki cikin sabgar nan ne dan ki sama mun mafita badan ki kara min damuwa da takaici ba. dan haka in baza ki iya ba, ina rokon ki da ki hada komatsanki ki koma garin ku. Hajiya Hajiya Talatu ta saka dariya tare da fadin Dadina da ke sahibata, idan kika fusata sai ki rasa abin fada, shiyasa ko me zakice baya damuna.
Anty ta ja tsaki Sannan tace sai ki fada min mafita dan wannan dai babu nasara. Hajiya Talatu tace mafita fa na fada miki kiyi duk abinda zaki yi amma ina son ki sani zakiyi komai ne kafin Halifa ya dawo domin ko yanzu bana tunanin zai ji dadin kiran yansanda da kika yi wa Inna. "
Anty tace Hakane yanzu dai menene mafita? Hajiya Talatu tace dole fa mu fara ta kan cikin a zubda shi sannan abubuwa su biyo baya.


Abban su Sulaiman ya kira Baffan Halifa a waya bayan sun gaisa sai yake tambayar Baffa da cewa Yaya anyi abu cikin mutunci da girmamawa yanzu kuma abu ya zo da cin zarafin Uwar yarinyar nan su Halifa za su kirawa yansanda. Baffa ya kasa gane kan zance kuma ya kasa hasko ma wace yarinya ake nufi. Sai da Abban su Sulaiman ya fayyace masa zance kamar dai yadda Inna ta sanar da shi. Baffa ya cika da mamaki yana shakku akan wai Aunty Halifa ce za ace duk ta kitsa wannan lamarin ko dai su binciki yarinyar nan yaran yanzu ka iya kulla abinda ba shi bane. Yace Kuma kuna da tabbaci akan abinda yarinyar nan ta fada? Saboda ni dai iya sanin na nayi wa Habiba mutuniyar kirki sbedar cewa ta na son Halifa kuma mu dangin Halifa na waje Uba, ta dauke mu kamar dangin ta, kuma ta bawa Halifa tarbiyya daidai gwargwado bana shakka akan haka. Sai dai kuma bari zan yi magana da Halifa idan ya dawo domin gaskiya baya nan ya yi tafiya, kuma dai ni bai sanar da ni komai ba. Abban su Sulaiman yace To Wallahi kamar yadda ka bada shedar matar nan haka zan baka shedar yarinyar nan da uwarta. Kusan sai ince maka kaf Unguwar nan tamu da kyar a samu mai hakuri da kirki Uwar yarinyar nan. Shi yasa muka hana yansanda su tafi da ita. amma ka bincika dai insha Allahu ai gaskiya zata yi halinta

Please Login or Register in order to submit comment