Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuka in sun rasa yadda za su rerrashe su. A bashi magani. Ya dawo ya same ta ya zauna kusa da ita, kiyi shiru shike nan ina maganin na shi kin kuwa bashi? Kai ta girgiza alamun a a. Ya bashi maganin ya yi ta jijjiga ta zuba tagumi tana kallon su, gaskiya Halifa namiji ne da kowace mace zata so shi. Ta darsa hakan a ranta. har ya yi bacci. Ya je ya shimfide shi ya yi masa addu'a ya dawo ya zauna ya rungumo ta, Babyna sannu da kokari kiyi hakuri haka iyayen mu suka yi ta fama har muka zama mutane, kwana kadan kema zaki saba da komai, ai kina kokari Allah ya saka miki da Aljana. Asiya ta sauke ajiyar zuciya. To yanzu me ya kamata ta ce masa? Ta dube shi. Kana son ka kara aure ne? Ta jeho masa tambayar. Ya kalle ta. "Me kuma ya kawo wannan tunanin Baby?" Kawai amsa zaka bani. Ta katse shi. "A a " Ya amsa a takaice. Wata ce muka hadu a Asibiti na ganta a tashin hankali sai na tambaye ta ko lafiya, shine ta ke fada min ta ga mijinta a Hotel da wata. Ya dubi Asiya da sauri, "To ita me taje yi Hotel ita ma gurin wani taje kenan? " Asiya Tace ita ta ce min zargi ta yi sai ta ke bibiyar shi.

Halifa yace Ta kuwa sa kanta a wahala, Ai be kamata ta yi haka ba ita ma Addu'a zata yi masa kawai. Asiya ta zuba mishi ido, ya kalle ta, ko a kwai wanda ke shiryawa banda Allah? Tace Babu amma shi ba zai ji kunyar Allah ba, sai yaje yana bin mata kuma bata kasa biya mishi bukatar shi ba. Ya dan yi tsam, kamar tana jefa mishi magnar ne. Amma sai yace Allah ya kyauta ta shi ki gyara mana gurin kwanciya. Ya wuce ciki. Yana bandaki ta shigo. Ta zuba ma wayar shi ido. Ta dauka tana juya ta dan bata san Sabuwar lambar sirrin sa ba.

Sako ya shigo ta sama a whatsapp hotuna ne suka shigo amma ta kasa shiga domin shima whatsapp din a kulle yake. Bata ji fitowar shiba sai dai taji yace Me ki ke nema kuma a wayata? Ta dan firgita ta mika mishi tana fadin sako naji ya shigo kuma sai na yi mamakin ka saka sabon Security a wayar.
Ya fizgi wayar, saboda irin ku ne ake saka Security a waya, na taba daukar wayar ki na duba? Me ki ke son ki gani? Ko nima bincike ne zaki fara min. Lallai zamu samu matsala in har zaki taba min waya.Ya bata rai sosai kar ki sake ko da wasa ki sake daukar min waya da sunan bincike baki da wannan hurumin na faɗa miki, na kula kwanakin nan fitina kawai ki ke so bana son in nuna miki rashin hakuri na, kar kuma ki bari ki kai ni bango.

Ya yi tsammanin ta bashi hakuri,kawai sai yaga ta bata rai ta shiga gyaran gado. Tsaki ya ja ya dauki filo ya fice.

Asiya ta yi shiru tana mamaki, a yi maka laifi kuma a fika fada, daga ganin yadda ya haukace an taba masa waya wallahi bashi da gaskiya ko kadan.Ta fada a fili.


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[12/17/2025, 19:26] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt

*Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302*

Da safe Halifa bai bi ta kan Asiya ba, ya shiga ya yi wanka ya shirya hatta ɗan sa bai kula ba, ya fice abinsa. Hakan ya daga mata hankali kodai sai ta fito masa a mutum ne ta nuna masa tasan me yake aikatawa a fili sannan zai haɗa hankalin sa, kila jikin sa zai yi sanyi ya shiga faɗin ta yi hakuri. Laifin nan ya bayyana karara koda yake wani nuna mata yaji haushin abinda Anty ta fada duk munafirci ne.

Abin duniya ya ishi Asiya dole ta nemo hujjar da zata nuna masa tasan me yake yi. Karshe ta yanke shawarar kiran Fati akwai bukatar ta yi magana da ita. Tana ringing Fati ta daga,, Asiya tace Kingane mai magana ? Fati tace .Na gane ki, Asiya ce me miji,. Asiya kanta ya daure, tace bangane Asiya me miji ba Maman Umar ce fa daga Gandun Sarki. Fati tace ke dai nake nufi nima. Asiya tace To ai naji kin kirani da wani suna ne wai Asiya me miji. Fati tace ina dai jinki faɗi abinda ya sa kika kira ni. Asiya ta rasa me zata ce tunda Fati ta Faɗi wannan sunan. Kiyi magana ko in kashe tunda yanzu dai ba a gidanki nake ba bare ki yimin iko.Asiya tace Shikenan na fasa maganar da zan yi miki sai anjima. Fati tace mu jima da yawa, mijine dai kuma nima yanzu sai dai in banso auren shi ba, amma ya zo hannu. Gaban Asiya ya faɗi tace saidai ki nemi naki mijin amma ba nawa ba me zai yi da ke? Fati ta cafke da faɗin duk abinda ya yi da ke shi zai yi da ni.Koda kika kore mu ya zo har gida kuma yana ci gaba da zuwa in kina son ki sheda zance na,ki zo anjima ki ganewa idon ki,in baki bari mun shigo ba, mu zamu zame miki kishiyoyin waje.
Asiya tace Allah ya kiyaye ni mijina ba dan iska bane, babu abinda zai yi dake. Fati ta sa dariya, sai dai kar a kuma ke ma din ai ya fada min ki gudo ne kin dawo gidansa bayan Mahaifiyar ki tana zargin cewa ya sake ki, dan haka kika haihu ba dangin iya bare na Baba munzo mu taimaka miki kuma shine harda cewa mu shirya kin sallame mu, ke ga matar gida. To mun ƙaru ba shakka amma kin bar baya da kura ko ince kin kashe maciji baki sare kan ba.. Git Asiya ta kashe wayarta. Ta zauna cike da bakin cikin abinda Fati ta fada mata, wato dai ta tabbata Halifa yana nema Fati hakan bai isheshi ba har sai ya hada da tona mata asiri. Duk zantukan Fati ba karya a ina zata ji in bai faɗa mata ba.Wata zuciyar tace ki tafi gidan ku kawai ki bar masa gidan sa. Asiya ta shiga hada kayanta da na ɗanta. Babu shakka ta hakura da Halifa in ba haka ba zuciyar ta zata buga. Ta gama komai bata da kudin mota, ko a kafa gara ki tafi. Wata zuciyar ta faɗa mata. Tana kaiwa bakin gate Motar Halifa tana isowa kofar gidan da alamun mantuwa ya yi ya dawo dauka. Cike da mamaki yake kallon Asiya da akwati tana ja. Ta kalle shi rai bace,zantukan Fati suka yi ta zuwa mata. Baice kala ba,ya wuce cikin gidan ta miƙi layin tana tafiya. Ya dakko abinda ya manta ya dawo ya wuceta ya tafi. Asiya cike da mamaki tace kenan ko kallo bata ishe shi ba, bare yace mata ina zata a zaton ta zai tsaya ya yi mata magana daga fara neman matanshi har daraja da kimarta ta zube a idon shi haka?.

Ta tsaya tana tunanin inda zata samu kudin mota domin tasan karya ne taje Fage da kafarta ga goyo ga kaya. Ta karasa gurin wani mai P.O.S dake kan titi tace dan Allah in baka wayata ka bani dubu daya zan kawo maka sai in karba jakar kudin nawa na yarda. Ta sheka masa karya. Wani dake kirga kudi a gefe ya ciro dubu daya ya bata yace je da wayar ki ga wannan saboda Allah. Asiya ta karba ta yi godiya ta kama hanya tana tare mai Adaidaita.

Ta fi minti Talatin kafin ta samu wani da mata biyu a ciki zashi Kurna tace ya sauke ta Kano Gest in. Tun kafin ta shiga taji matar ciki tana yiwa diyarta faɗa. Tana faɗin na fada miki tun ba yau ba ki kauda kai daga abinda Baban su baby yake yi ki yi masa addu'a kika taurare ke bazaki zauna ba yana neman mata, kika dawo gida kika bar masa gidan to gashi in da yana dibansu zuwa Hotel ne yanzu kam kin hutar da shi, tunda makota sun fada miki yana kawo mata gidan aurenki ai gashi zaki koma babu shiri. Inda kina gidan karyarshi ya kawo mace gidan. An fada miki shifa namiji in yana boye miki abu ko kin gane karki nuna kimarki ta sa hakan to gashi dai tun yana zuwa lallashi kinƙi ki koma gashi yanzu zaki koma bayan ya watsar da ke. Asiya taji kamar wani karatu ake yi mata, kenan shima Halifa zai iya kawo su gidan hankalin sa kwance motarsa da gilashi baƙi ya wuce da mace ya fito da ita ba tare da an sani ba. Kuma babu tabbacin zai biyota ko ya gyara kuskuren sa,tunda gashi a gabanta ya wuce ko ajikin shi,ran nan da tace zata tafi ai lallashinta ya yi da ban baki, amma yau dubi yadda ya watsar da ita. Ba shakka ance in ka rasa uwar da zata yi maka fada,to ka saurari faɗan da wata uwar zata yi wa ɗanta sai ka dauka kai ya yi maka amfani. Wadda ake yi wa faɗan tace "Ni wallahi dan Baba ya ki ne, da kawai takarda ta ya bani yanzu gashi duk makota sunsan abinda ya aikata.Uwar tace ki fada min waye ya ja? Kece nan tun farko me ya kaiki bincike da saka masa ido. Allah ya hana bin diddigi.Kika kwafe ki duba masa waya ki bibiye shi har sai da kika ga no tashin hankali tun lokacin har zuwa yau wace ribar kika ci? Bayan da kuna zaune lafiya abin shi awa.

Me a daidaita ya karbe zancen da faɗin Babata in saka muku baki? " Ya ci gaba kanwata baki san me yake faruwa ba a wannan zamanin mu da muke jan Adaidaita mun san komai, mata ne suke neman maza yanzu, in har kika yi sakwasakwa da mijinki wata ce kawai zata samu ta yi ta masa abinda ke bazaki iya yi masa ba,wasu fa harda kuɗi suke kashewa maza,wasu malamai suke shiga. Shaiɗan fa da kika gani babu abunda yake so irin ya girgide auren sunna,dan haka ki koma gidan ki ki rike mijinki kici gaba da addu'a. Ki fita batun yan unguwa su aka san me mazan su ke aikatawa sanin na Allah ai sai Allah ko malami karyar sa yace miki ga na Allah

Sam Asiya bata san anzo Kano Gest ba sai da mai Adaidaita ya dakata yace munzo Ta sauka ta bashi dari biyar ta tsallaka ta kuma tare wata ta hau zuwa gandun Sarki. Domin dai ta wadatu da faɗan da aka yiwa yarinyar nan. Ta dawo ta bude gidanta ta shiga. Ta kwantar da ɗanta a kujera sannan ta koma gefe ta zabga tagumi dole ta sake kiran Anty Halima da alamu dai shawarar nan ta ta itace mafita.

Take ta kira bayan sun gaisa ta zayyana mata dukkan abinda ya faru a tsakanin su. Dariya ta ji Anty Halima tana yi.Haushi ya kamata kamar ta kashe amma saita share ta ci gaba da fadin Anty abin dariya aka yi? E mana abin dariya ne, ace wai kin tafi kuma kin dawo.Na faɗa miki fa,duk abinda zai yi karki nuna kin gane,baki ga abinda Baby ta cikin Hamshakiyar uwa ta yi ba? Ki karanta littafin zaki samu Illimin zama da miji me neman mata, naki mijin sabon shiga ne,kuma ke kike kara rura wutar dan haka ki nutsu in ya dawo ki bashi hakuri karma ki nuna kinyi waya da wannan yarinyar karki masa zanceta sam sam. Ki daure kishi da zafi musamman da matar waje amma Allah yana saurin amsar addu'ar wanda ke cikin damuwa.

Asiya ta yi wanka ta gyara jikinta sosai ta yi kwalliya tsaf. Zan tukan Fati suna ɓata mata rai in ta tuna.

Saidai kuma Halifa bai dawo ba sai sha biyu saura. Ran Asiya ya sosu amma ta dake ta zauna a falo. Ya sa makulli ya bude kofar falon dan bai zaci tana nan ba.

Ya shigo yana waya abinda taji kawai shine, dadin baki kawai ki ke yi min, domin yaushe rabon da ki nemeni amma ni yau gashi na kiraki da..... Maganar ta tsaya cak ganin Asiya ta zuba masa ido. Cikin yanayi irin na mara gaskiya yace zan kira ki da safe, barista zan kira. Bai jira me zata faɗa ba, ya kashe wayar.

Asiya ta daure ta kalle shi sannu da zuwa. Ya dube ta da in ina ya ce yaw wa, ya sa kai ciki, ta bishi yana cire kayan jikin shi ta iso dab dashi,in ka yi wanka akwai abinci. Ta fada tana kokarin ƙaƙaro fara a. "A koshe na ke, ya karkace wai dan kar ya taɓa jikinta ya nufi banɗaki.
Asiya ta rumtse idon ta zuciyar ta ta soma tuna mata da maganarsu da Fati, ina ma ace ta yi recoding din ta yana fitowa ta kunna masa ya san ta san komai.

Zuciyar ta tace ki hakura kawai. Wata zuciyar tace, kar ki hakura ki faɗa masa komai da zaran ya fito ki kunyata shi. Tana zaune bakin gado. Ya fito yana shafa turare ya yi wanka.Yana mata kwarjini ne amma ta daure tace Yaya ina son magana da kai.
'Bisimillahi " Ya faɗa lokacin da ya dauki filo zai fita kenan. Yaya dan Allah ban hana ka soyayya da kowa ba amma dan Allah kar ka kara faɗawa wata sirrina. Ga mamakin ta sai taji yace 'To' ya sa kai zai fita. Tace Yaya amma me yasa ka rasa wadda zaka nema sai Fati me mana aiki? Har ya kama kofa zai murda sai ya tsaya cak bai waiwayo ba, ganin ta fara kama shi sai ta ci gaba da faɗin kuma neman na na lalacewa har kai ne zaka dauki mace Yaya zuwa Hotel dan ka.....



*✍🏻 HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[1/12, 17:34] Ummi Tandama😇: *Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302*

Saukar mari da Asiya ta ji shine ya katse mata maganar ta,ta kalle shi sai tsuma yake "me yasa ne ki ke son in yi losing ɗin temper?" Kafin ta fahimci abin da yake faɗa ya kuma kifa mata wani marin ya jefa ta kan kujera,a tsorace ta ɗago hancinta yana zubar da jini, kamar dai ya haukace, ya kuma nifo ta, ta ruga ɗakin da ke kusa da ita ta faɗa ta rufo ƙofa jikinta yana ta ɓari tana jiyo shi gaba ɗaya ya haukace yana ta fashe-fashe yana cewa ki fito ki faɗamin ko saki nawa kike buƙata?.

Ya faɗa ɗakin su ya ɗakko takarda da biro "ki faɗi adadin sakin da ki ke so in yi miki yanzun nan na fara jin cewa na tsane ki. In har tsanar ki ta yiwa zuciya ta tasiri ko a hanya ba zan so ganin ki ba Asiya. Ta leƙo ta window tana kallon shi.

Baki da wani tunani sai na zargina mata mata dai in neme su mana ba kuɗina bane ko kabarin mu ɗaya? Kina da wuta ne ko kina da aljanna? Haba kin hanani zaman lafiya, me ma ya hana ki tafiya gidan naku ɗazun da kika fita? Ki fito ki tafi da hujjarki a hannu in huta nima.

Asiya ta firgita ta manta da dukan da ya yi mata ta isa bakin ƙofa ta buɗe a gigice ta zo gaban shi ta fisge takardar. "Yaya bana son ka sake ni don Allah" ta faɗa jikinshi ta rungume shi kam tana kuka tana faɗin "wallahi na daina zargin ka sherrin shaiɗan ne Yaya na tuba ka yi haƙuri. Jikinshi sai rawa yake kamar wanda ake kaɗawa gangi.... kamar minti uku ya ya kice ta ya jefar ita da biron ya fice daga falon ya shiga ɗaki ya fito ya fice

Asiya tana kuka ta ji tashin motar sa ya fice daga gidan.

Ta nufi banɗaki ta wanke jinin, zuciyar ta ta rasa wane irin tunani zata yi,borin kunya yasa ya dake ta ko kuwa zafin ƙazafin da tayi masa ne?

Borin kunya ne zuciyar ta ta faɗa mata,ki zauna tunda ya fara dukanki ki zama jaka, yanzu ma ya fice zai je ya samu wadda ya kira ɗazu su ƙwana tare, gara fa kin koma gaban uwarki ki haƙura da talaucin ku yafi dukiya babu ƙwanciyar hankali. In ba haka ba wataran sai ya kashe ki kuma babu abin da za ayi.

Da sauri ta tashi fuska kumbure ta kuma janyo aƙwati ta loda kaya lokacin karfe ɗaya ta wuce na dare,bazata ƙara ƙwana a wannan gidan ba tafa a fili.

Tana kici kicin fito da aƙwati ta ji shigowar motar shi tace ai ko motar shi bazan hau ba gara in kwana a hanya cak ta tsaya a farfajiyar gidan tana kallon su sun nufo ta Inna da Sulaiman.

Asiya!! Inna ta furta da ƙarfi, Asiya ta saki akwati ta ruga ta rungume Inna ta ma manta wai tana da goyo sai kuka ita da Inna.

Sun ɗauki mintuna Halifa ya ce ya isa Inna ku shigo. Asiya ta ce Inna mu tafi kawai ni bazan kuma shiga gidan nan ba, tunda na ganki ƙafar ki ƙafata. Inna ta ce ina zaki da tsohon daren nan,bani ɗan naki in ganshi.

Asiya tace gurin ki zan je, kullum sai na yi yunƙurin tafiya. Halifa ya kalle ta fuska a ɗaure ya kau da kai. Inna tace "me kuma ya samu fuskar ki haka?"

Asiya tace faɗuwa na yi a banɗaki. Halifa ya yi karaf yace "marinta na yi Inna."

Ina ganin kawai ku tafi tare da ita zata fi samun nutsuwar zuciyarta. Sulaiman zai yi magana Halifa ya ɗaga masa hannu tare da miƙa masa makullin mota. Kuna iya tafiya za mu yi waya kawai.

Asiya ta yi gaba Inna ta bita a baya dan Sulaiman ya ɗauki akwatin,sai da suka fice a gidan Halifa ya dawo ya shige ɗaki


*** **** ***


Bros ya kalli Maman Nihal "ki daina wata faɗuwar gaba ita fa Anty yanzu tayi nadama,dan Allah kar ki nuna komai game da abinda ya faru a baya." Amarya dake riƙe da jaririn Maman Nihal mai sunan Dady tace Anty dan Allah ki daina wata fargaba.

Suka shiga su ukun domin ɗakko Nihal da Nur. Anty tana zaune a falo tana kallon T.V sai dai sam hankalin ta baya kan abin da ake yi tana can cikin tunanikanta mafarkan ta da har yanzu babu wanda ya zama gaskiya,sai zuwa yaushe zata samu nasara? komai ta shirya sai ya lalace.

Bata ji sallamar su ba sai da Bros ya ce Anty! Da ƙarfi sannan ta firgigit ta ɗauki sakwanni sannan ta fahimci su waye a gabanta.

Ta ɗaure fuska tare da kau da kai. Maman Nihal ta durƙusa ina yini Anty? Bata amsa ba amarya ta je ta ɗora mata yaron a cinya ga mijin ki nan. Ta yi kamar zata ture shi da taga zai faɗi kuma babu wanda ya yinƙuro dan kamashi sai ta yi saurin riƙe shi. Bros ya yi murmushi ya yin da amarya ta saki dariya tare da faɗin ashe dai ana so. Anty ta dubi amarya "ke bana son rashin kunya zanyi maganin ki wallahi in zaki kawo min raini,bana wasa da yara." Allah ya baki haƙuri ta faɗa tana dariya "bari in nemo su Nihal" amarya ta faɗa tare da nufar ciki.

Anty ta kalli Maman Nihal ta taɓe baki, Maman Nihal ta sunkuyar da kai cike da tausayin Anty,duk ta yi baƙi ta rame. Anty ta katse mata tunani da faɗin "wannan yarinyar makira ce,naga take taken ta sai kinyi da gaske. Cike da mamaki Maman Nihal tace "to Anty zan kula." Bros yace amma kuma ni banga wani aibunta ba,tana girmama mu. Anty tace "in kai baka gane abin da nike nufi ba ita matarka ta gane" ta kalli ɗan dake cinyar ta tace "sai ya tuna min kai kana yaro sak haka kake." Cike da jin daɗi suka yi yar dariya.

Maman Nihal tace Anty shima bai yi rigima ba ke nan dan shi wannan bashi da rigima sai kirin kirin ba zai nutsu guri guda ba.

Haka dai uban yake. Amarya ta dawo da su Nihal cike da murna suka faɗa jikin uwar su abin tausayi Nihal tace Momy Baba ya faɗa mana kin haifa mana Baby boy shine wannan a gurin Anty? Ungo kayanku Anty ta faɗa tana miƙa ma Nihal shi. Nur kuwa ta kasa sauka daga jikin Mamansu domin ita dai baza ta sake yarda ta tafi ta barta ba.

Amarya ta ce Anty naga Hafsa tana kuka kuma bata faɗa min abinda ke damunta ba. Duk suka kalli Anty. Ta dubi Bros ita da Dadynku ne,ya ce ya saka mata ranar aure sati shidda bata san waye mijin ba." Maman Nihal tace Allah sarki amma ai da Dady ya bata dama ta fito da wanda take so tukunna. Bros ya ce "ya fa bata,ai munyi maganar da shi,banga laifin sa ba amma bari inga Hafsar shegiya sai dai ka shiga lamarin ta amma ba domin halinta ba." Ya nufi ɗakin.

Ganin shigowar shi yasa Hafsi da ke ƙwance tashi zaune,Bros yace "kinga sakamakon mugun hali tun yanzu ko? Hafsi tace don Allah ka bawa Dady haƙuri wallahi ba zan sake shiga harkar matarsa ba. Bros yace "mafita ɗaya ce ina shi wannan saurayin naki bani number ɗin shi inyi magana dashi, amma Dady wannan ranar da ya saka miki ta aure bazai taɓa ɗage ta ba." Cikin sauri ta tashi ta ɗakko waya ta fito da number ta miƙa wa Bros tana cewa nayi nayi dashi ya zo Anty tana kiranshi yaƙi zuwa yanzu ma baya ɗaga kirana. Bros yace zanga ya zanyi da shi. Ya koma wajen su Anty suka ƙwashe ƴaƴansu,Bros ya kawo kuɗi ya ba Anty suka tafi.

Anty har labulen window ta ɗaga tana leƙensu wai ashe aƙwai ranar da zata zo tana ganin Maman Nihal su jera da ɗanta a gabanta kuma har ta furta ku gaida gida. Batasan hujjar da zata bayar a matsayin dalilin hawayenta ba, abinda kawai ta sani shine bata yi nasara akan ta ba.

Akan wa kika yi nasara ma? Zuciyar ta ta tambaye ta. A fili tace akan Asiya matar Halifa na kashe kuɗi na wahala nayi asarori, amma ban faɗi ba, na yi nasara tunda Yanzun ta Haukace ta shiga Duniya ba shakka wannan nasara ce.


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

[1/31, 12:32] Ummi Tandama😇: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ

*Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302*


Inna ranta ya kasa kwanciya da kalmar da Halifa ya furta a gabanta cewar ya mari Asiya. Dan haka Inna tace to ke me kika yi masa har ya yi miki wannan mari haka? Nifa bana son aure da dole wallahi sai na samu kaina a sabon tashin hankalin da naji kamar ina ma banganki ba?

Sulaiman ya yi gyaran murya sannan yace Inna kar ki yi saurin yanke hukunci ki jira muje gida sannan da zai yiwu karki saurari me Asiya zata fada gobe zanzo

Please Login or Register in order to submit comment