Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ji ta tashi, yace Auzubikalimati lahitammat min sharri ma kalaka. Take ya ji wata tsanarta a zuciyar shi. Ta nufo shi tana yanga tana fadin sannu da zuwa Yayana. Tsawa ya daka mata, karki sake ki karaso nan shedaniya. Ni bana son ko ganinki a rayuwata. Mamaki ya cika Ma u Mamanta ta bata tabbacin cewa yau dai Halifa ko dame yake takama sai ya rusuna kuma zai birkice yace sai an daura musu aure nan take kuma wata sha awar ta ce zata kama shi harma ya ji yana da bukatar saduwa da ita, in ya nemi hakan su amince, domin daga ranar kuma sai yadda suka yi da shi. To ya kuma abin ya fara da haka tafi awa tana wanka na magani ta jima tana kwalliya amma tana zuwa ga abinda ya biyo baya.

Ya kalli Anty wai ina makullan gidan nan ne? me hada sola nan ya same ni a kasuwa dazu, yana son kara sa aikin shi. Tace "Wa zaka sa a gidan? " Ya kalle ta cike da mamaki. Yace Wai Anty meyasa ki ke min Haka fisabilillahi bakwa wani shirin biki kamar yadda kuka fara a farko kin daina tattaunawa komai na shirye shirye ko da yake ni bani da matsala in aka daura aure an gama min komai.
Anty ta ce "Kai ashe yarinyar tana da aljanu hauka tuburan take yi in sun. tashi shine iyayenta basu fada mana ba. Halifa yace wace yarinya ke nan? Tace wadda zaka aura yanzu.
Halifa ya danne mamakin sa yace ni sun sanar dani tun a ranar da nace zan aure ta kuma na musu Alkawarin, zan rabata da su. Anty ta tsaya tana Kallon shi cike da mamakin yadda ta zabga karya kuma ya kare hakan duk da ya sa mata kokwanton ko dai da gaske tana da aljanun ne?. Shi kuma mamaki yake tana da aljanu aka boye masa, ya dai sha alwashin in Allah ya yarda sai ya auri Asiya ko ma wane aibu gareta. Anty ta katse shi to gaskiya tunda tana da larura, ba zai yiwa ka kaifa wannan katon gidan ba, ka kawo ta nan gidan ku zauna a sashen ka har muga kamun ludayin jikin,kada wata rana ta fita ba a sani ba suje su halakata. " Shiru Halifa ya yi can kuma ya ce kawai ki bani makullan zan ga ya za ayi. Magana kamar wasa sai gashi ta watsu a dangin Halifa cewa mai ciwon hauka zai aura

*** *** ***

Asiya ta saka hijabin ya mata ƙato har kasa kasancewar ba dai dai girman ta bane na cikin lefen ne Halifa ne ya kira ta a waya yace ta fito yana gurin shagon Sulaiman zasu unguwar da ya faɗi mata duk da be ce mata ga wajen da zasu ba ya ce ta shirya ne kawai,ta rasa wane hijabin zata saka Inna tace saka na lefenki sai gashi ya mata ƙato tunda Bilki tana da tsawo da kuma kiba, ita kuma yar tsuntsuwa.

Halifa ya fashe da dariya lokacin da ya kalli Asiya, Kingan ki kuwa kamar wata tattabara a cikin leda? Asiya ta yi takwa takwa da fuska, cike da shagwaba tace yaya harda kai a yi min ba 'a ko? " Kamar ya zube damun daɗi, yana son shagwaba sosai abinda Bilkisu bata iya ba ita sai izza. Yace. " Yi hakura kanwata, ni nafi son ki a haka, yadda zan jefaki sama in cafke kayana." Ta sunne kai a tafukan hannayen ta cike da kunya da nauyin abinda ya fada. Yace zo muje tabishi ya nufi wata mota yana yi wa Sulaiman alamar sai ya dawo da yatsan sa. Ta Kalle shi kasa kasa yana cikin motar kwayar idanunta dauke da alamar tambaya. Yace" Shigowa za ki yi mu tafi. " Tace Ina Kenan? Ta tambaya cikin salo. Yace" Saida ke zanyi. Ta kama murfin motar ta bude tare da fadin lahiya lau, inji katsinawa. Ya tintsire da dariya, "Ina matukar samun nishadi in muna tare, da alamu na yi sa ar mace wadda ta iya hira." Ya kai karshen maganar tare da juya motarsa dan fuskantar inda za su bi. Nishadin na ka ai ba zai yi tsawo. ba" Saboda me? " Ya fada yana kokarin tattara hankalinsa gareta. Saboda ga shi zamuje ka sayar da ni. Ya girgiza kai," Ba saida ke zan yi ba, gurin mai magani zamu je." Ya fada cike da son bugun cikin ta. Ta Kalle shi da sauri Wani ne ba lafiya? Ta jefa masa tambaya cikin sauri. Ya Dan yi shiru domin kamo bakin zaren, tana da wayo fiye da shekarunta. Ya yi gyaran murya sannan ya soma magana a hankali, Asiya zan kai ki gurin mai rukkhya ne kinsan in mace zata yi aure ana bukatar ta zama komai lafiya a yi gwajin jini da sauran su," . Ta ce rukiyya ai sai masu Aljanu Yaya ni kuwa tunda Allah bai dora min ba ai sai mu gode masa. Jinin dai muje a gwada dama Innarmu ta yi wannan Hasashen cewa jini zamuje gwaji lokacin da kace in zo. Kuma kasan abin mamakin shine ni A A ce, kasan yadda aka yi na sani wata rashin lafiya na yi, kowa ya ganni sai ya ce sikila ce shine aka yi min gwaji ashe ma nidin AA ce.

Ya kalleta da mamaki " Allah na zaci ke As ce, kuma duk da cewa ni A S ne wallahi ban damu ba ko ke din AS ce na fi damuwa da ace kina da Aljanu amma kin taba yin su?" Tayi dariya nifa ko mugayen mafarkai bancika yi ba domin bana manta adduo'in idan zanyi bacci Allah ya tsare ni da sharrin su. Yace"Alhamdulilah yanzu bari muje gwajin jini." Ta kasa danne Hasashen ta tace. Labari ka samu cewar ina da Aljanu kenan. Ya yi yar dariya." Ina zan samu wani labari kawai dai kinsan anayin gwaji." Tace nasan ana gwaji amma ban taba jin na Aljanu ba, Yayata ta yi aure amma ba ayi mata rukiyya ba, bana son ni da kai mu samu shakkar wani abu tsakanin mu, ko me kake son sani game da ni kar ka damu ka tambaye ni kai tsaye zanyi maka bayanin shi. Haka nan nima zan yarda da duk abinda zaka fada min. Dan Allah kar ka yi min karya a duk irin rayuwar da zamu yi bana so ta sam.
Kunya tana son kama shi lallai wannan yarinyar itace matar da ta dace da rayuwarshi, dole ya yi taka tsatsan ta sake kashe shi da cewa. Ka dai yi min Alkawarin zan rayu cikin aminci ko? Bai amsa mata ba sai da ya yi fakin a cikin asibitin Malam Aminu Kano sannan ya dauki waya ya kira wani likita ya sa a sanar da shi sun karaso yace to ya jira shi gashi nan zuwa. Ya kalleta na miki wannan Alkawarin matsawar ina numfashi. Ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin na yarda.
Bayan angama dibar jini suka dawo mota tare da rakiyar abokin na shi tanaji su suna tattauna yadda akayi aka fasa da Bilkisu Abokin yace " Ka samu yar shila. Suka sa dariya yace ka fa yi dabara abokin a in namiji yana da jiki yar shila zai samu, Halifa yace au ni yanzu ina da jiki? Suka yi dariya suka tafa. Asiya dai ta kashe kunne tana jin su.

Wani shagon gyaran jiki na yan birni ya gani akan titin gidan su kawai ya ja birki suka shiga. Yace yana bukatar su yi mata gyaran jiki na amare nawa ne, suka fada mishi farashin daban daban yace mai tsadan nake so amma ta yi kyau sosai, suka ce to zata zo na kwana uku gobe zata fara zuwa, ya basu rabin kudin da suka caje shi, yace sauran sai ya ga yadda sukai mata.
Bayan ya yi mata siyyar kayan kwalama suka tsaya inda yake fakin ya taka mata sannan ya ce to zai kirata anjima. Asiya tun a ranar ta tabbatar rayuwarta ta canza Wai ita za abiya irin wadannan manyan kudin dan kawai a mata gyaran jiki. Gashi ashe Halifa yana da mota, sai taji ta kara aji kuma ya shiga ranta, dan gaskiya bata taɓa sa ran auren mai mota ba, amma ta na mugun son mota sosai.


Halifa ya kebe da Sulaiman ya tambaye shi akan dan Allah ya fada masa gaskiya ko Asiya tana tada Aljanu. Sulaiman yace gaskiya bata da su, ita tace maka tana da su? Yace a a, kasan sharrin mutane wani aka samu ya fadawa Baffa na da kuma Anty. Sulaiman yace shiyasa Anty da Hafsi suka zo gidan su Asiya jiya kenan.? Halifa ya zaro ido, Anty da Hafsi fa kace kai gaskiya ba su ka gani ba. Sulaiman ya ce ni fa na raka su har gidan. Mamaki ya cika Halifa daga Anty har Asiyan ba wanda ya fada mishi. Ko shine dalilin da Asiya ta dage cewa ya mata Alkawarin cewa za ta samu aminci a gurin sa.?"Dole dai akwai wani abu.. Ya yi sallama da Sulaiman ya tafi.


Yan mata ne kyawawa guda biyu suka amsa mishi sallama a Falon Anty, shi bai cika kallon mutane ba musamman mata, dan haka ya amsa sannun da suka hada baki suka yi masa ne ya nufi Dakin baccin Anty. Ya kwankwasa ta ce waye, yace "Anty ni ne, ta fito tana fadin dan Halas ka ki ambato irin albarka kai nake ta kiran wayar ka taki shiga. Ya katse ta Anty me kukaje yi a gidan su Asiya?" Tace zo muje zan amsa maka wanna tambayar daga baya. Kamar ƙaramin yaro taja hannun shi zuwa falo da kyawawan yan Matan ke zaune. Tace duba a cikin su ka zaba dukan su wayayyu ne in sun yi maka duk biyun ma baka da matsala. Suna Jami a ƴaƴan masu da shi ne, kuma'ya'yan kawaye na ne. Ta kalli dayar Amina mike ya ganki. Ta mike tsaye tana takun kasaita, ta zauna, dayar ta tashi ita ma tana rangaji. Anty tace wannan kuma Kamila sunan ta. Ya bita da kallo domin gaskiya tana da kira ta jan hankalin ɗa namiji, ya kasa dauke idanun sa daga kirjinta....

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
[5/26, 09:17] Ummi Tandama😇: Cike da farin ciki Aunty ke kallon Halifa ganin yadda ya kasa magana, da alamun yarinyar ta dauki hankali sa daga ganin yanayin kallon da yake mata.

Ganin haka yasa ta katse shi da faɗin Amina zo mu basu guri su yi magana. Cikin sauri yace "a a," Gaskiya bana bukatar ko daya ciki su. Ki zo muyi magana ya koma dakinta.

Tsaki ta ja ta zauna a falon tana fadin kai ka yi kaɗan ka bi mutane wato sai dai kai a bika ko? To kowa ya rike maganar sa. Ta kalli yan matan tace ku yi hakuri, zan zo gidan. Wata ce take son mallake shi.

Muryar Hafsi Halifa ya jiyo a cikin kicin sai ya nufi can ya tsare ta da ido, me kuka je yi gidan su Asiya? Hafsi tace Uncle ni kawai rakiya na yi sai dai ka tambayi Anty. Yace "Karya kike yi, to da kuka je gidan me kuka ce?" Hafsi ta fito daga cikin kicin din, dan ta fara tsoron abinda zai biyo baya, zai iya yi mata duka, tace Uncle Anty ce tayi magana da su fa. Halifa ya yi tsaki ya fita.

*** *** ***

Ƙarfe goma kamar yadda masu gyaran jiki suka bukata Halifa ya kira Asiya yace ta shirya yana hanya. Yau Asiya nutsuwa ta yi domin tun amsa gaisuwarta Halifa bai sake magana ba, wannan ya sa ta shiga taitayin ta, tare da kame kanta. Har suka isa shagon yace in sun gama ta kira shi zai wuce kasuwa ne, ta yi masa addu'ar Allah ya bada sa a. ko da ya tafi bata bar mamaki ba tsoronta kardai wani laifin ta yi masa, ko kuma yanayi ne da ke sa mutum kan canza oho.


Yana tsaka da kasuwa kamar daga sama sai ganin Bilkisu ya yi a gaban shagon sa, duk da facemaks ɗin da ta saka hakan ba zai hana ya gane ta ba. Daya daga cikin yaran shi yace, me take son siya? Tace gurin Megidansu ta zo. Yace Bari a sanar dashi.

Halifa yace ta shigo ta zuna a kujera suka kawo mata lemo. Yana ta rubutun sa a wata takarda sai da yagama sannan ya kalleta. Lafiya na gan ki a kasuwa? Ta cire fasemarks din da ke fuskarta,ƙwalla na taruwa a idon ta ta ce. "Kaima ka san abinda zai kawo ni gurinka. Yanzu duk yadda muke baza ka yi min uzrin karamin kuskure ba? Afwa a soyayya wajibi ne Na maka Alkawarin har abada bazan sake ba, Wallahi Halifa ina son ka sosai bana bacci bana iya cin komai, zan iya mutuwa fa."ta ida maganar hawaye na ida saukowa kumatun ta.

Ya kalli yaran shagon sa dake ta Kallon kallo, domin kowa najin abinda take fadi. Ya yi kasa da murya domin zuciyar shi tana rawa, haryanzu yana son ta in har ya barta ta ci gaba da zantuka nan ba shakka zata iya shan kansa. Yace kije gida za muyi magana. Tace " Kai min rantsuwa akan cewar zaka zo, in har ka rantse na yarda ya yi shiru. Yana son ya Lallaba ta kawai ta tafi." In baza ka zoba kawai ka sanar dani gaskiya." Baka saba yin karya ba kar ka fara domin ka faranta min. Ta sake daure shi,. Kije zan zo amma gaskiya ba yau ba, amma tabbas zan zo. Ta mike tare da faɗin "Ina jira dan Allah. "

Zuciya Halifa ta fara rawa game da Bilkisu dan yana son ta, harya fara ganin kamar bai kyauta mata ba. Dole ya duba ya gani menene ya kamata ya yi.
Sam ya manta da batun Asiya tana gurin gyaran jiki yace in an gama ta kira shi zai zo da kansa ya maida ta gida,, kiran mai gyaran jikin ta sanar dashi sun gama tun dazu ya sa ya tuna. Ya tashi ya sallami yaran shagon sa ya nufi titin gidan zoo. Sai dai ya na zuwa gadar dangi sai ya samu kanshi da tunanin ya fara zuwa cikin gari akwai bukatar ya yi magana da Bilkisu. Ta yi mamaki sosai lokacin da ta fito tabbas kuwa shine.

Ta zauna a kujerar gefe bayan ta bude motar. Suka kalli juna tausayin ta ne ya cika zuciyar shi. Yace Bilkisu gaskiya har yanzu ina son ki, ina kaunarki matuka, amma kaddara ta sa zan auri Asiya, babu yadda za ayi in kaucewa Auren ta. Ina son ki dan bani lokaci kema zamuyi aure. Ta yi Dim domin taso ace ya hakura da batun wata sun shirya kan su. Ta soma hawaye cikin shashshekar kuka, tace "Bakomai na hakura zan jiraka, kuma ko ta Hudu ce in har zan same ka zan jira dan in ceci kaina daga mutuwa, nasan in har na rasa ka mutuwa zanyi." Yace baza ki rasani ba. Sun jima suna tattaunawa game da son da suke yi wa junan su daga bisani suka yi sallama bayan mai shagon ta sake kiran sa cewa sun kusa rufe shagon su.

Haka ya taho yana dan jin haushin Asiya.
Kallo daya ya yi mata tare da amsa sannu da zuwan da ta yi masa. Yace ta taso, bai kula wasan da mai shagon take tsokanar sa da shii ba tana cewa ya kaga amaryar fatan mu zamu yi mata kwalliyar ranar biki, ya dan yi yake tare da fadin " Insha Allah.
Asiya ta yi tsam da ranta sannan ta kame kanta ganin yadda Halifa ya zo mata ayau. Sai da suka hau titi sannan ta dan saci kallon shi tace" Shi bawa yana barwa Allah lamarin shi a duk yadda ya tsinci kansa. Kuma nuna bacin rai a yayi da aka samu kai a cikin wata jarrabawa tamkar kin karbar ƙaddara ce. "Wani Abu ne kika ga ya faru?" Ya jeho mata tambaya cikin kamewa.. Ta girgiza kai ba da kai nake yi ba ina kokarin haddace karatun mu na jiya ne na islamiyya. Ya kalleta ita ma ta dake kamar gaske. "Ina wayata?" Ya tambaya ta dakko cikin sauri tace gata nan. An cika ta da chaji a shagon matar nan. Ya kallo Wayar sannan ya maida kai titi tare da fadin " Zaki iya gane gurin nan gobe kar ki jirani zan baki kudin mota ki zo ki koma." Tace sosai kuwa ina fage ina gidan zoo da kafa ma zan iya zuwa sai in bullo ta gadar Nasawa. Gidan Murtala ina tsallakawa sai layin gidan IG in fito layin gidan Bashir Tofa.

" Ya aka yi kika san duk wadannan guraren? " Ya katseta da sauri. Tace na yi tallar Kankana da abarba a lokacin kakar su, yanzu ma ba dan zuwan ka ba da lokacin su na yi zanje Na'Ibawa yan lemo insaro in hau Dansahu zuwa titin gidan zoo daga nan in jera a tire ina tafe ina siyarwa har fage kafin naje ya kare. Kaga kuwa dole insan hanya. Bai kara magna ba har suka tsaya abin ya dame ta ta kalle shi. Tace To bansani ba nice ko a kasuwa ne wani ya sosa maka zuciya, amma dai ina mai baka hakuri Allah ya huci zuciyar ka a madadin koma wa nene . Bata jira amsa ba ta bude mota tafice ta nufi gida.


Ya kira Sulaiman a waya yace yazo mota za suyi magana. Ya dubi Sulaiman ya ce ina jin wani bacin rai game da Auren Asiya kamar in fasa, gaba daya da yamman nan haushinta nake ji. Sulaiman ya rasa abin cewa dan takaici dan haka ya zuba masa ido yana ta kallo da sauraron abinda yake fada. Sai daya gama Sulaiman ya bude mota zai fita. Halifa ya rike masa gefen riga tare da fadin ka ce wani abu mana.
Sulaiman yace babu abinda zance ka yi duk yadda ka ke so. Ya fizge rigarshi ya wuce.
Lamura sun cude, an taso Halifa gaba Hajiya Talatu na yi ga Anty, gidan su Bilkisu suma basu, zauna ba. Duk da Halifa mutum ne jarumi yana tsaye kan ibada, ga sadaka ance tsafi gaskiyar me shi, dan haka sai da abin ya taba shi har ya rasa gane abinda ya kamata ya yi.

Lamarin ya Shafi Asiya sosai har zuwa Ana gobe daurin aure bata samu ganin shi ba tun ranar da ya sauke ta. Dan haka bata koma takan mai gyaran jiki ba ga kuma jikin Baban su ya yi zafi. Ya sa aka kira mishi Baban su Sulaiman. Ya bar masa wasiyya cewar Koda Allah bai nufa ya ga gobe ba, yana rokon shi da su tabbatar an daura Auren Asiya, kuma yana son dan Allah ya sanar da Halifa cewa ya rike amanar Asiya kar ya barta ta yi kukan maraici.


Ana gobe daurin auren aka wayi gari da mutuwar mahaifin su Asiya, Babansu sulaiman shine ya kira Baffan Halifa ya sanar da su mutuwar mahaifin su Asiya kuma ya fada musu za a daura aure bayan an dawo daga Jana iza sakamakon ya bar wasiyya.
Halifa ya girgiza da jin labarin mutuwar kuma ya tausaya wa Asiya Dan haka shima ya nufo gidan mutuwar. Daren jiya ya gama yanke shawara da zuciyar shi cewa zai sa a daga bikin, sannan ya fara Auren Bilkisu, harma ya sanar da Anty hakan tana ta farin ciki tsarinta ya tafi yadda take so kuma aikin malaman ta ya yi ba shakka. To zata koma kan Bilkisu dan ta tsaya kar abin ya yiwu. Ita ce zata kawo wadda zai aura kamar yadda ta ke so.


Bilkisu ta yi farin ciki komai yana tafiya yadda malamin ya tsara mata, gashi dai Halifan nata ya dawo gadan-gadan.


Asiya suna ta kuka lokacin da za a dauki mahaaifinsu, ji take komai na duniya ya ishe ta, ina ma ace itace ta tafi ta bar su. Ji take bazata iya sake dariya ba har abada, Baban su ya tafi da dukkan farin cikinta.

Lokacin da aka dawo daga kai shi makabarta gidan cike da dangi da makota, sai kuma taji wai za a daura mata aure. Sabon kuka ta soma domin kanshi Auren ya fita a ranta, musamman yanda shi wanda zai aureta ya ja kafa cikin yan kwanakin nan har zuwa yau batasan ya lamarin ke tafiya ba.

Mijin Anty shine ya shiga da alawa da goro da kuma dabino yana sanar da ita an daura Auren Halifa. Kamar saukar aradu haka Anty da kawarta suka samu labarin, Cikin rawar baki Tace "Halifa munafirta ta ya yi kenan." Kar ki zarge shi. Inji Dady Baban yarinyar ne ya bar wasiyyar lallai a daura auren ko da bai tashi ba, sukuma dangi suka ga da cewar a daura bayan an dawo daga jana iza tunda duk watse wa za suyi ba zaman makoki za ayi ba.

Cike da izgili Anty tace ba dole a watse ba, tunda in sun zauna me zasu ci, sai dai ma su ci da su. " Dady yace Ai dama haka musulunci ya koyar ba a ce wai dan an yi maka mutuwa ba ka zo kana ci da mutane, cewa a kayi mutane su tausayawa iyalan mamaci su basu sadakar abinci. Dan haka na yi waya Singa nace a kawo musu buhun shinkafa da taliya. Anty ta ja tsaki "Wannan Auren ban yarda da shi ba, sannan kuma ka kira waya ka sa a dakatar da kai wani abu gidan. Alama ta rashin sa a ta bayyana ga yarinyar nan ba yar albarka bace, ubanta ya mutu ana maganar aurenta kai gaskiya akwai abin dubawa a lamarin nan. Tsaki ya ja sannan ya wuce.


Halifa suna tsaye da su Sulaiman mutane suna ta zuwa suna yin hannu da shi tare da masa murna. Shi dai amsawa kawai ya ke yi yana dan yake. Kana gani ka ga angon da ba shiri domin sanye yake da jallabiyya mai ruwan kasa wadda yake zuwa masallaci sallar asubashi da ita. Kiran Bros ya shigo cikin sauri ya daga yana cewa Bros ka dawo ne.? Yace na dawo tunda an daura maka aure yanzu haka ina kan titin IBB yi min kwatance in same ka a gidan inyi ta aziyya. Halifa ya yi masa kwatance . Sulaiman ya ce ya kamata mu shiga cikin gidan nan muyi ta aziyya. Halifa yace "Kalli jikina duk da dai gaisuwa zamuyi amma daga ni sai jallabiyar salla.

Asiya ma bata san sun zo ba, sai ji tayi Ana cewa wannan shine angon. Bata ko leka ba dan babu wani abu dake birge ta.


Halifa ya kira Bilkisu ya sanar da ita abinda ya faru ta zube tana kuka wiwi. abin ya zo mata a bazata

Please Login or Register in order to submit comment