Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da motar sa in dauke shi muje gata gashi a yi musu ba cuta ba cutarwa. Inna tace shike nan a yi hakan abin babu dadi Sam. Wa ya sani ko akan tace sai ta zo gurina ne? Inna ta fada ta na Kallon Asiya wadda take tunani anya zata iya tona asirin Uban ɗanta kuwa?

Inna ki bari mu nutsu Zan fada miki komai.

Asiya ta furta cike da son a bar maganar. Ta ci gaba da fa ɗin Ina Abba da Su Annur Maman Annur tana zuwa gidan aikin ta kuwa? Inna tace Tana zuwa kullum dai ita ma tana cikin damuwa da kewa amma ta kusa daina aikin ma. Abba kuma jiya muka dawo daga Asibiti. ‘Bashi da lafiya ne? Sadiya ta katse Inna.
Sulaiman ya yi karaf ya ce ai ya samu sauki ma. Asiya ta yi shiru tana tunanin kamar akwai wata matsala game da Abba.Har suka isa gida.
Sulaiman ya kira Inna gefe yace kar ki yi mata zancan Abba tun da dai shi bai fada mata ba. Kinsan dai tana da ruɗewa Inna tace shike nan. Ya kira Asiya itama yace, kar ki fada wa Inna matsalar mijinki kin san dai har yanzu ba a warware wata matsalar ba sannan ban da haka kuma Inna tana da wuyar fahimta . Asiya tace shike nan.

Ga mamakin Asiya sai ta ga sun zo wani gida wanda ba gidan su ba, dan madaidaici mai kyau ba ginin kasa ba kamar na su. Ta cika da mamaki tana kallon Inna, “Nan kuka dawo Inna?” Tace Nan muka dawo bamu jima ba.Sadiya taji tsaiwar mota ta bude gidan ta fito da gudu tana fadin Asiya ! Asiya tace
Maman Annur Suka rungume Juna Sadiya tana murna ta amshi jariri tana kallo ranar har ukun dare suna hira kafin kowa ya kwanta. Inna ta sauka a ɗan gadon ta tace ki kwanta ke da ɗan na ki. Asiya tace a a Inna shima ya kwanta a ƙasan dan ya saba. Inna ta amshe shi tana fadin kawo shi mu kwanta in ya farka kya tashi ki bashi ya sha. Asiya cike da farin ciki ta kwanta iyaye daban ne ta ayyana a zuciyarta. Sai dai fa kogin tunani ta fada maimakon bacci rayuwa baza ta yiwu mata ba babu Halifa ba haka kuma akan kunnen ta aka kira salla dan haka ta tashi ta fita ta tayo alwala tabi gidan da kallo ko ya akayi su Inna suka dawo nan gidan Mai kyau ga tayas ko ina ga ruwa daki uku ne da Siti rum da safe dai taji yadda aka samu gidan. Ta zo tana nafila, motsinta ya tada Inna ta ce baki tashe ni ba na makara koda yake bamu kwanta da wuri ba Asiya tace shiyasa na barki amma ba'a shiga salla ba har zakiyi raka atanil fijir. Inna ta fita tana fadin Asiya dan naki bashi da rigima.

Tana idar da salla bacci mai nauyi ya dauke ta Kuka ɗanta ya tashe ta, taga Inna ta rufo kofa tana mishi wanka. Ta bisu da kallo cikin farin ciki tace “Inna a ina kuka samo robar wanka?
Inna tace a makota na aika aka karbo min. Asiya ta gaida Inna ta tashi ta nufi tsakar gida ta wanke baki Sadiya tana hada abin kari kunu da dumamen shinkafa. Asiya tace maman Annur sai ga ku a sabon gida, wai ya akayi ne? Sadiya tace Hummm wallahi kuwa tun daga abin Abba Halifa ya dawo da mu nan ko bai fada miki ba? Asiya cike da rashin fahimta tace ban gane ba.
Inna ta kwaɗawa Asiya kira ta amshi ɗanta yana ta ragsa kuka. Inna tana faɗin zauna ki bashi ai yana da hakuri tun jiya bai farka ba. Ta zauna tana bashi, tace ai bai cika tashin dare ba, . Inna tace. Wai kuwa me ya hada ku da Mijin naki har ya mare ki? Lamarin fa ya tsaya min a rai. Bana son auren duka.

Asiya ta yi shiru tana tunani ta ina zata dakko maganar. Inna tace “Ban tsanan ta sai kin fada min ba amma aure da duka Asiya ba zai yiwu ba dan haka shi yasa tun jiyan bance komai ba da yace mu taho.

Sallamar Sadiya ce ta dakatar da Inna , ta kawo musu abin kari, Abba ya shigo yana gaida su Asiya ta bishi da kallo ya dashe ya rame cike da mamaki Asiya tace Inna “Me ya samu Abba haka?” Sadiya cike da mamaki tace wai baki sani ba? Asiya tace “Maman Annur in har na sani bazan tambaye ki ba. Inna tace Wai kina mufin shi Halifa bai sanar da ke komai ba?
Sallamar Sulaiman ce ta katse su.Ya shigo Halifa yana bayan sa. Sadiya ta yi musu shinfida suka zauna Halifa ya gaida Inna ko inda Asiya take bai kalla ba bare ɗanta. Ya amsa gaisuwar Sadiya. Sadiya ta miko musu ɗan sai Sulaiman ne ya amshe shi Halifa dai a fusace yake har Wannan lokacin Asiya ta dake domin zuciyar ta
ta fada mata cewa ta dake kawai Yanzu lokaci ne na kwatar yanci kodai ya tuba nan gaban Inna akan bazai ƙara ba, kokuma ta haƙura da shi domin sai ta fallasa shi.
Halifa ya katse ma Asiya tunani da faɗin Inna kamar yadda na fada jiya na mari Asiya har ture ta na yi domin har sai da ta yi habo wannan tabbas na aikata shi. To amma ko zata iya fada miki abinda ya jawo hakan? Asiya ta kalle shi cike da mamaki wannan yana nufin baima damu ba da abinda ya aikata. Yanzu har ya kai ba zai iya boye zunubin shi ba.Ya katse mata tunani bance ki rufamin asiri ba fa, nan gurin babu bakon ki mahaifiyar ki ce da yar ki, Sulaiman ma kamar wane a gareki dan haka karma ki tsaya boye komai.

Kawai ki tona shi zuciyar ta ta faɗa mata haka.
Asiya ta kalli Inna wadda yanayinta ya canza tunda Halifa ya ambaci cewa ya dake ta. Ko mutuwa ance tana jin kunyar idon mahaifi amma Halifa kamar yana gadara da ya dake ta. Tace ‘Inna ki yi hakuri ki yafe min har da alhakin ki na gudu na tafi Gurin Halifa ashe ban sani ba ya canza daga Halifan da na sani.

Da na haihu ya kawo min wata Dattijuwa mai suna Hajjo ita da jikarta sai jikar ta fara nuna tana son shi, sai kuma wai ya biye mata. Har na kore su shine kuma ya ci gaba da kulata. Ya ma kama fa kulakulen mata shine har dayan dare sha biyu ba zai dawo gida ba gashi bani da sirri gurin matan Duk ya fada musu wai na gudo ne na dawo gurin sa. Ta kai karshen maganar da fashewa da kuka. Cikin kuka taci gaba da fadin wai dan na masa maganar ya daina jiya shine ya dake ni wai kuma zai sake ni.

Idanun Halifa suka kada suka yi ja ya kalli Inna bazai iya fassara me take tunani ba. Dakin ya yi tsit sai kuka Asiya. “In kare kai na ko kawai Inna ta yanke hukunci? Halifa ya tambaya cike da bacin rai. Sadiya ta yi saurin fadin Ka kare kanka shine adalci Sulaiman yace Ka yi maganar ka aboki na.

Halifa yace “Lokacin da na fahimci cewa Sulaiman ya gama yi min kokari Inna ta gane gaskiya ba ni ne na saki yarinyar nan ba, sai na fara kokarin yadda zan kawo ainihin wadda ta yi laifin ta fada a gaban Inna da kanta kuma in yi musu ba zata daga Antyn nawa har Inna wato in kawo musu Asiya da ɗanta su san tana cikin koshin lafiya.
Katsam sai wani tashin hankalin ya samu Anty an mata kishiya a boye,dan haka na jinkirta, nan ita kuma wannan yarinyar naga ta soma damuwa da harkar masu mata aiki tana bay yana kishinta har da korar su. Duk ban damu ba har gida naje na basu hakuri na kuma biya su hakkin su,gata nan ko faɗa ban mata ba tunda nasan ina da fushi Sosai.
Ranar da da na lura ta soma bata rai game da gida ta damu da son ganin ku sai na yanke shawarar in zo in sanar da Inna Asiya tana gurina kuma in tafi da su Innar can gurinta.

Sai da na fara duba Sulaiman a shago baya nan sannan na nufo gidan ni daya, tun daga nesa na hango mutane cike a layin sai na yi tunani in juya domin gaskiya bana zuwa inda duk ake fada.
Muryar Sulaiman na jiyo yana cewa ba zai yiwu a bashi hakuri ba, dan yana ganin ba su da wanda zai tsaya musu.
Kawai sai na koma ashe rigimar a gidan su Inna ce. Naje na dafa Sulaiman ina tambayar shi, abinda ke faruwa sai na ji Yayi hamdala yana fadin ga me tsaya musu ya zo.

Na tambaye shi abinda ke faruwa sai ya nuna wani mutum yana tsaye sanye da jallabiyya fara yace “Ga wanda ya dake su kuma wai kar su yi kuka, ya samu yara ya lalata su kuma Abba da ya tona asiri bayan ya haike masa shine ya zo yana fuffka zai kai kara.
Na kalle shi cike da mamaki ban gane ya haike musu ba su da ba mata ba. Halifa yace mazan fa kuma yara kanana kowa ya sani a layin nan an kasa yi masa magana dan yana da abin hannu.
Bansan lokacin da na zabga wa uwar sa zagi ba, nace za a kai yaro Asibiti in ya tabbata wallahi sai kaje gidan yari. Saboda ƙarfin hali wai ya taso zai mare ni, ni kuwa na dinga jibgarsa sai da naga baya motsi sannan na kyale shi.

Muna Asibiti aka tabbatar an haike wa Abba Sai da aka yi masa karamar tiyata. Yan sanda suka zo suka same ni a Asibiti suka tafi dani wai ana za ton Mutumin ya mutu ne.

Na kira Yaya Bashir Babanmu daya shine mataimakin Kwamishina na faɗa mishi halin da ake ciki take ya kira DPO yace ni kanin sane ya na son case din ya koma hannun sa dan haka akai ni can yanzu.

Lokacin karfe tara sun ta shi aiki tuni amma ba su tafi ba. Muna zuwa ya fara min faɗa bana neman shi kaza kaza na bashi hakuri domin gaskiya dai ban saba da su ba, amma mukan hadu a gida lokacin duk da za ayi wani shi ani Ina zuwa, da Ina karami ne Anty bata cika kai ni ba. Amma dana girma Dady ne yake fada min in bi yan uwana mu yi zumunci.

Sai sha biyu suka fito ya sauke ni a gida yace da sassafe in same sh office nace to.

Shine ranar da na kai sha buyun da take magana sai wani irin kallo take yi min dana dawo na shiga wanka dan ina ta jin kyan kyamin jikina tunda an sakani a sell Gurin ƴan sanda kafin muje Bamfai. Ga gajiya na ki fada mata ne dan bana son ta tada hankalinta Babu abin da ke daga min hankali sama da in ga Asiya a damuwa. Dan ina ganin yanzu ita ce komai nawa kuma na fada mata hakan gata nan Tana jina.

Abinda ya bani mamaki muna dawo wa daga Bomfai Washe garin ranar ni da lauyana wai kawai sai na ganta a dan sahu bayan Asibiti tace min zata je kuma ba hanyar bane. Har mun wuce sai na juya nace masa kamar naga wani da nake son haduwa da shi a Keke Napep Na yi haka ne kawai dan ta ga mota ta. Cikin sa a ta ganni ta sa mai keke ya bini. Na sauke lauya na a kasuwa ya dauki motar sa dama nan ya barta muka hau tawa. Ina zaune a motar ina mamaki kenan yarinyar nan bibiyata take yi tana zargina. To halin da nake ciki bana bukatar wani tashin hankali a gida domin mutumin da na buga har lokacin baya gane kowa duk da ya farka.
Sannan nima na shigar da ƙara akan abinda ya yi wa yaran nan bani da ishshen lokacin da zan zauna ko abinci in ci, kasuwa ma bana samun zama sam daga gurin yansanda zuwa Asibiti kuma ni na bada jini da aka yi wa Abba aiki amma matar nan tana ta zargina har da cewa ina tona asirinta a gurin matan da nake nema . Ta tashi dan hauka ta tafi gidan su Fati me aikin ta dan wulakanta kai da zubar da aji . Hajjo ta kira ni ta faɗa min har lambar da ta sa aka turo mata duk babu abinda ban sani ba. Na shanye to wai kuma jiya na shigo gida Ina waya zan kira Barista ka wai kiran ya tafi ashe wayar Bilkisu na kira yarinyar da zan aura a da, gudun kar ya zama kamar na wulaƙanta ta sai na tsaya muna gaisawa sannan na shigo gida da kwarin ta kai tsaye tunda nasan bata nan kuma Ina da kwarin gwiwar cewa yanzu suna tare da Inna taji komai dan haka na shigo Ina wayata kai tsaye, ganinta zaune yasa naji na dan kadu domin dama ga halin da nake ciki game da ita kuma gashi taji ina waya. Yadda na tsargu shine ya bata damar fada min magana wai ina kai mata Hotel. Raina ya sake ɓaci sakamakon tuna batun cikin fushi yace aure baya yi wuwa da zargi dan haka na fada mata wallahi ta fara dusashewa daga raina ta zabi abinda take so wallahi zan mata in gaba ɗaya take son sakinta zan bata, sai inje in yi sharholiya ta yadda nake so,.

Ya mike bayan ya kai ƙarshen bayanin shi, Inna wadda duk jikinta ya yi sanyi tace to aiba tafiya zaka yi ba,, ka tsaya a warware maganar . Sulaiman ya ce Inna kiyi hakuri zamu dawo wallahi dama da kyar na sha kansa ya zo. Shima ya fice. Asiya wadda kunya da bakin ciki suka hana ta dago kai sai da ta tabbata Halifa ya fice. Ta mike tsaye tana fadin Innalillahi wa inna ilaihirraji un.
Inna wallahi nayi kuskure na zargi yaya Halifa cike da jahilci. Inna tace Nan fa shine ya tsaya mana kare wa ma wannan gidan shi ya saya mana yace mu bar unguwar saboda abinda aka yi wa Abba. Ya kawo kayan abinci ya jibge mana hatta Sadiya yace ta daina zuwa aikin nan dan kuɗin makarantar yara zai biya musu dan dai matar da ta ke yi wa aikin taje Umara ne amma da ta dawo zata daina zuwa.

Sadiya tace to wai ke Asiya duk wa ya zuga ki kika dinga wannan shirme babu lissafi? Dan gaskiya da ba haka ki ke ba, wallahi gaba ɗaya duk kin sa kunya ta rife ni, na kasa magana. Asiya tace sharrin zuciya ne wallahi sai ta yi ta raya min ni kuma inta hasashe cewa fa ga shi can kuma bugu da kari Fati me aikina da ta fada min cewa yace na gudo ne. Asiya tace aikin banza kila ma jinku ta yi ba kince a gidan sauke yini ba? A kwai wanda ya kai masu aiki gulma da bin diddigin masu gida ne aka fada miki? Gidan aikina gashi nan ina gani a gurin sauran masu aikin har labe suna yi. Asiya tace Ita wannan shegiyar zata iya aikata wa . Inna tace Ni na ma rasa ta inda za bullo wa lamarin shi yana nan yana kare miki mutunci iyaye da kanin ki ya kuma kasa faɗa miki dan kar hakalin ki ya ta shi ke kuma kina can ki nai masa cin zarafi.

Asiya tace to wai ni ku fada min ta inada zan fara. Sadiya tace ki kira shi a waya ki ba Inna ta bashi haƙuri ko kuwa? Asiya tace dan yi shiru bari in gwada bashi hakurin ni da kai na mugani.

Asiya ta firgita da ganin yadda ta yi masa kira goma sha biyu bai ɗaga ba. Tace lamari fa ya baci ta kira Sulaiman yace ai ko ɗazu kafin na fito har ya tafi kuma nima bai daga kirana ba. Yace Asiya kema baki kyauta ba abin fa da ciwo ya zama iyalinka kuma basu yarda da kai ba. Asiya tace Na yarda Yaya Sulaiman na yi laifi hakuri zan bashi. Yace ki masa Message sai ki jira zuwa gobe ya huce. Bata da zaɓin da ya wuce hakan.

Sai dai wasa wasa yau sati daya ba wani ci gaba ta masa sako ya fi dari amma ba amsa kira kuwa da ya gaji ya saka layin a DNA.
Har kasuwa Sulaiman ya je yaran shagon suka ce ya yi tafiya.
Hakurin Asiya ya kare ga fargaba kar fa Halifa yace zai sake ta.

Ta shiga yi wa Inna kuka har ta ba Inna haushi Tace zata saba mata in dai bata nutsu ba wani yace ta yi laifin tunda ta san halinsa. Sadiya dai sai lallashi Su tufka wannan shawara su kwance.

Daga karshe ta sake kiran Anty K mashi bata boye mata komai ba. K mashi tace “Abinda ya faru dai ya riga ya faru, yanzu shawara daya ce waye kika sani guda daya wanda ba zai musa maganar sa ba? Asiya tace sai dai Baffan shi, K mashi tace to ki sanar da Inna cewa zaki je gurin Baffa din domin ya bashi hakuri ita rayuwa akwai yanayin da baka tsayawa ga mace musamman miji ya
diga miki alama ta cewa kin fara fita ransa har kuma ya maimaita hakan a gaban mahaifiyar ki. To ki aje wani batun wani aji ki sunkuyar da kai .
Asiya tace “Yanzu ma kuwa zan tashi in kama hanya . Ta sanar da Inna komai Inna tace Ni da zaki bi tawa ki jira shi ya huce ya kawo kanshi hakan akwai daraja kuwa? Asiya tace “Inna Ni nasan halin kaya na, Yaya da ki ke gani sai ya shafe labarina daga yadda ya bar wadda suka dade suna soyayya ya aure ni ya ishe ni misali.
Inna tace To ku tafi tare da Sadiya. Kuma dan Allah kar ki kuma tafiya ba da izini na ba.

Asiya tace kar ki damu Inna bazan sake yin wannan kuskuren ba.
Asiya da Sadiya suna zaune a gaban Baffa ta sanar da shi ko ita din wacece dan ba zai gane ta ba Baffa ya sha Mamaki wai dama an ganta . Tace ita dama gidansa ta tafi, ta zayyana wa Baffa komai . Baffa ya yi mata faɗa sosai sannan ya dauki waya ya kira Halifa yace Yace duk inda yake ya zo yanzun nan yana neman sa.

Halifa bai kawo Asiya cikin dalilin kiran ba, domin ai ba su san anganta ba. Sai dai abin mamaki yana shiga Falon Baffa sai ya ya ga Asiya zaune ita da Sadiya shi kuma yana rungume da jariri yana ta yi musu nasiha.

Halifa ya daure fuska yana kallon Asiya. Ta sun kuyar da kai, ya shigo ya zauna ya gaida Baffa . Asiya da Sadiya suka gaida shi, ya ƙi amsawa Yace Baffa ga ni.
Jikin Asiya ya yi sanyi amma ta saka aranta duk abinda zai faru sai dai ya faru domin kuwa tunda har ya zo sai ta sha kanshi.
Baffa ya Katse mata tunani da faɗin.
Matar ka ce ta zo kuma ta min bayani komai, ba tare da an maimaita zance ba ina son ka dauke ta ku tafi gida. Ka yi hakuri.
Halifa ya sunkuyar da kai “Baffa Umarni ne ka bani?” Baffa Yace A a shawara ce kawai. Halifa ya mike Tare da faɗin Baffa ka yi hakuri ba zan iya yafe wannan zargin ba, na so in yi hakan na kasa, Baffa ban taba aikata zina ba ko da ina saurayi Allah shine shaida ta, amma ace matar ka wadda ka auro ka aje a gida ita ce zata dinga bin al amuran ka dan kawai ta gano wani laifin ka.Baffa yace Ka yi hakuri Su mata haka suke. Halifa yace Anya ta fada maka abinda ta aikata kuwa ka ke bani hakuri ? Ta fada inji Baffa.
Halifa yace in kuwa haka mata suke to su sha zaman su na hakura. Asiya bata san lokacin da ta mike ba ta isa gaban Halifa ta zube tana fadin Dan girma Allah dan soyayyarka da manzo Allah dan darajar maihaifan ka da suke kasa dan kimar Baffa da muke gaban shi ka yafe min. Wallahi ba zan sake ko kawo hakan a raina ba, na tuba. Ta soma kuka, in kuma na sake ka dauki dukkan mataki a kaina. Baffa ka zama sheda. Halifa ya yi shiru domin dai Asiya ta gama daure shi ta hada shi da kokoluwar abinda za a hada kowane dan Adam da shi ya saduda.
Baffa bai ce kala ba domin in har Halifa bai duba kalaman Asiya ya ba su kima ba, to ido zai zuba.

Dakin ya yi tsit sai kukan Asiya da take yi na debe tsammani domin wadannan sune kalaman da kaɗai take da su in yaƙi sai dai ta koma gida ta rungumi kaddara. Ya sabule kafar shi ya nufi fita. Sadiya da Baffa suka bishi da kallo ya yin da Asiya ta saki sabon kuka.
Dafda zai fita ya furta Ki koma gidan ku zanzo. Baijira Jin komai ba ya fice.

Baffa ya ce zashi tunda yace za shi, amma dan Allah ki kiyaye gaba dan Allah Asiya tace Insha Allah. “Ya ce Allah ya shi muku albarka . Bayan sun dawo gida suka sanar da Inna komai tace To Allah ya kawo shi lafiya.

Sai dai ya zo yau ya zo gobe Asiya har da yin kitso aka yi lalle ana jiran zuwan miji amma shiru.Sai ranar Juma a daidai da cikar su kwanaki takwas da zuwa gidan Baffa Asiya tana kwance a tsakar daki ta yi nisa cikin tunanin mafita. Kamar daga sama taji Inna tana fadin sannu da zuwa Halifa kai ne da rana haka?
Yace Nine Inna kafin Asiya ta tashi ta kimtsa har ya iso dakin kofar ta yi masa shinfida cike da rawar jiki tana yi masa sannu da zuwa.Ya amsa fuska ba annuri

Suna gama gaisa wa da Inna yace Inna idan ta shirya ta same ni a waje kuma ta hanzarta. Inna tace ai gata nan tana jinka.
Yana fita Inna tace Anya Asiya kya koma gidan Halifa kuwa? Dubi yadda ko ta danki baya yi bare ke. Asiya tace Inna ya kike fadin haka? Ta tashi tana tattara Yan shirginta tana fadin Ance miji da mata sai Allah zamu shirya abinmu Inna ke dai ki yi mana addu a. Sadiya ta fitar mata da akwati ya bata leda da kayan sha yi da danyan Kwai.

Asiya ta yi sallama da Inna Abba da Sadiya suka rakota tana ce musu sai sun zo.

Asiya tana ta

Please Login or Register in order to submit comment