Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk ba sune a binda ya kamata in duba ga uwar 'ya'yana ba.
Ta kara matsowa" Halifa ka tashi muyi magana ban amince da wannan huce haushin da za ka yi ba, kai ba mijin kowace irin mace bace, kana da bukatar macen zamani yar gidan girma."

Ya tashi da sauri ya dauki makullin mota dake kan durowar gefen gado tare da fadin, zan nemi wani gurin in kwanta ko hotel haka dan ina son zafin da kaina ya dauka ya sauka ko zan samu bacci.

Da sauri ta nufi kofa dan tasan halinsa ficewa zai yi, tana fadin yi kwanciyar ka da safe zamu yi magana domin bazan laminta ba. Har ta kai kofa sai ta tuna sunan yarinyar tazo tambaya, dan Haka ta tako ta dawo, to "Wai ya sunan yarinyar ne ma? "
Cikin kagara yace ban rike ba Anty amma kamar Sadiya ko wa, ina ga kamar haka.
Tafice cikin sauri.


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: *🧳 HASASHE🧳*



*Sabon littafin*



*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*




*Page 3*

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*


Daga sallar asuba Halifa ya wuce gidan Baffan sa Alhaji Ali wanda babu nisa mai yawa da gidan nasu, kanin mahaifin sane wanda shine ya rage masa Uba duk sai Yayinsa wanda suke uba daya a bangaren Mahaifinsa. Kamar yadda ya zata ya same shi yana karawa wa su dattijai karatu ya zauna gefe yana sauraro Har suka gama, ya sallame su, sannan ya dubi Halifa yace " Umaru kai ne da safe Haka?" Halifa yace ni ne Baffa, ya gaida shi cikin girmamawa sannan ya soma magana akan abinda ya kawo shi.
Baffa zuwa na yi in sanar da kai anjima kamar sha daya in ba wani uzri zamuje kai da Dady Mijin Anty gidan su yarinyar da zan aura. Baffa Ali ya dube shi.
" Lokacin daurin auran za a ɗaga ne, naga sai rana ita yau ne, koko wani abin ne ya taso?" Nan dai Halifa ya zayyane wa Baffansa komai game da matsalan su da gidan su Bilki da kuma canjin da aka samu na Asiya.
Baffa yace "Wannan dalilin ya sa yanzu maza ke kai lefe in da mazane ba za a tsaya wannan shirme ba, to sai muce Allah ya sa hakan shine alkairi sai mu tafi kamar shadayan ya yi."

A hanyar Halifa ta komawa gida ya kira mijin Anty a waya ya san lokacin basa tare da ita ya sanar da shi sha daya zasuje gidan surukansa.
Hafsi ta kawo masa karin kumallo bayan ta gaida shi tace " Anty tace tana jiranka" . Ya dan kurbi kunun kadan sannan ya ce ki fada mata sai na dawo tukunna.
Anty ta kalli Hafsi me yake yi to? Hafsi tace na dai same shi yana danna waya ne, ta mike bari ni inje. Ta same shi yana kokarin shiga wanka, ta kalli wayar shi da ke ta ringing ta ce, "Ka daga mana." Yace barta Bilkisu ce tun asubahin fari take kirana kuma ni na rufe shafin ta inna zauna ma zanyi blocking din number ta ne, gaba daya.
Anty tace "Haba Halifa, ka sawa zuciyar ka salama mana, yanzu ya ake ciki ne?" Ta yi maganar cikin sigar lallashi. Yace game da me kenan? Tace kajika, maganar yarinyar nan mana aikwai bukatar ka nutsu ka yi adduo'i kafin ka fadawa wata maganar auren. "
Halifa ya dube ta Anty a wannan karon gaskiya sai na yi aure, abin ya isa haka kadan ya rage in kai arba in, dubi Adam Bros nafa girme shi amma yaran shi biyu, auren kawai nake bukata da koma wacece indai sunan ta mace, an wuce gurin sai wance da sauran su. Anty tace "Kaji ka da zaka kawo batun Adam shi da ya yi gaggawar yanzu ina matar ba sai yaran ba, kuma hakan dadi ne? Matar sa fa zagina ta yi kasan komai nace kuma sai ya sake ta. Ta saki huci sannan ta danne zuciyar ta ta kuma tausasa murya. Ta ci gaba da fadin" Halifa ka san dai kai kanina ne maraya ne kuma amana a gurina, duk da ni na Haifi Adam wallahi na fi son ka akan shi, kai ne wanda na fara raino kafin shi, bana son abinda zai cutar da kai yin hakan cin amanar da mahaifiyar mu ta mutu ta bar min ne a tsumman goyo." Ta soma shashshekar kuka. Halifa ya numfasa. Karki damu Anty nima Kallon mahaifiya nake miki, nasan kina kokari a kai na. Ina son kiyarda da batun yarinyar nan ina yi mata Hasashen alkairi. Ta ce shike nan" Ina son ka kaini gidan su yarinyar in gani ko zan samu natsuwa. "
Yace shike nan. Ta fita tana fadin Allah ya yi albarka.
A fili ya furta Anty bazan kai ki ba hakuri kawai zakiyi.
Mijin Anty bai sanar da ita komai ba game da inda za suje domin tunjiya ta ke yi masa mitar abinda Halifa ya yi, shi kuma a nasa gurin yana kallon Halifa a matsayin wanda ya san kanshi kuma duk abinda Halifa zai yi yana da tabbacin abin nan yana kan daidai.

A mota Halifa ya sanar da Dady Mijin Anty komai. Dady yace ai kaima da baka tsaya biyewa Antynka kuka yi wani gwaji ba, sai dai tunda mai aukuwa ta auku sai muce Allah ya sa hakan ya zama alkairi. Baffa yace ai maza ke kai kaya na fada masa dazu. fatanmu dai wannan din ya zama alkairi sannan tunda yace Fage ne ina da wani aboki na da mukayi harkar goro da shi a kurmi iyayen su sune suka kafa unguwar na tabbatar zan samu cikakken bayani game da yarinya da kuma iyayenta. Mijin Anty yace yawwa nima dai ina son a samu dan wani bayani game da yarinyar duk da nasan Halifa baya abu da ka. Ko tak Halifa bai furta ba
A kofar gida suka samu Sulaiman domin Halifa ya sanar dashi da suka taso.
An saka shimafida a soro inda mahaifin su Asiya ya dogaro ya fito ya zauna, ya tarbi baki cikin fara a da murna duk da yana cikin yanayin rashin lafiya mai tasanani, ya umarci Sulaiman ya sanar da mahaifin sa da daya makocin na su cewa bakin sun iso domin tun Daren jiya ya tura mahaifiyar su Asiya ta sanar da makotan zuwan bakin, bayan ya samu labari daga bakin Sulaiman.
Kamar arashi sai gashi ashe Abban su Sulaiman shine abokin Baffan su Halifa da yake maganar zai nema, dan haka Baffa ya ce shike nan kaya ya tsinke a gindin kaba ai muna tahowa yanzu a hanya nake tadin ka.
Baban su Sulaiman yace "Yace ashe ni abin duk nawa ne, dama shi Halifa nasan shi duk da bansan iyayenshi ba yaron kirkine abokin dan waje na ne, ko azumin da ya wuce ya kawo min kayan shayi. Ita kuwa yarinyar kamar diyata haka take."
Baffa yace Allah sarki, hakika Halifa dana ne wanda dan uwana Alhaji Umaru ya haifamin ai sunan mahaifinsa yaci, domin kwana uku da rasuwar mahaifinsa aka haife shi, kafin a yaye shi kuma uwar ta rasu sai rukonsa ya koma hannun wannan bawan Allahn ya nuna Mijin Anty ya ci gaba da fadin shi wannan ya auri Yayar Halifa ko wata biyu ba su yi ba, ita kuma Uwa suka hada da Halifa su shida ne Ubansu ya mutu ya bari rabon Halifa sai Uwarsu ta auri Dan uwana Alhaji Umaru shine aka samu Halifa to kunji yadda muke da Halifa. Wannan ne Ubanshi duniya bashi da sama dashi, amma yana da yan uwa su shi da suke uba daya amanar da ya rika yasa ko dukiyar Halifa da aka raba gado gaba daya muka basu, kuma har yau bamu taba jin wani korafi daga Halifa ba. Yaro kuma gashi yanzu ya zama mutum.
Mijin Anty ya yi gyara murya, yace "Gaskiya dai Halifa dana ne, domin ko Adamu dan nawa bani da shakuwa da shi kamar Halifa, duk inda ka ke neman Yaro dan albarka Halifa ya kai. Fatanmu Allah ya sa a kulla alkairi.
Baban su Asiya ya ji dadi kuma ya tabbatar musu ya ba Halifa auren Asiya ya kara da cewa ko bai kai rana ita yau da rai ba yana rokon karsu daga auren daga wannan ranar su tabbatar sun ba Halifa matar sa. Nan dai suka yi adduo'i aka shafa bayan sun bada kudi dubu dari biyu harda sadaki.
Halifa da Sulaiman suna zaune a dakalin kofar gidan su, suna kara tattaunawa game da batun daurin aure har suka yi yar gardama kan batun fati Halifa yace na saka su maido muku kudin ku, dama waccan yarinyar ce ta matsa. Sulaiman yace "To wannan ai bakaji ra ayin ta ba. " Halifa ya ce na yi hasashe a kanta bata bukata amma ka fada mata zanzo anjima da dare, inna zo na tambaye ta lokacin in tana so zan mata. Sulaiman yace to ai shike nan. Suka fito inda suka raka su har mota.
Anty tana idar da salla ta kira layin Malami na farko danjin sakamakon bincike. Ko gaisawa basu yi ba tace Malam yaya? Yace "Kedai ban taba ganin mai wutar ciki irinki ba, to gaskiya sunan da kika bada na Sadiya babu wata alaka ta aure sai dai kuma ga auren nan yana tunkarar sa wanda ba wani abu dai zai dakatar da shi."
Tace ka bincikami taurarin wadda zai aura din da kuma yadda auren zai kasance.
Yace na yi yunkurin haka amma ban iya gane komi ba, kila da a kwai sunan yarinya sai mu fahimta sunan da kika bada kuwa in har itace to sam tauraron su bai zo daya ba, kuma arzikin sa zai karye,abinci sai ya gagare shi. Sai dai ita kamar yadda na fada miki ba muga aure a kanta ba.
A gigice ta kira sauran malaman suma dai kusan bayanin daya ne sunga aurensa amma ba su ga na yarinyar ba.
Dole ta tafi gidan Hajiya Kaka dan ta watsa wuri ta yi bincike a gaban ta kuma ta dakatar mata da auren.
Tana shirin fita Mijinta yana shigo wa yace ina kuma zaki yanzu? Ta bishi da kallo daga ina kake kuma yau she ka fita? Yace " Kina can kina baccin asara na fita.,kuma daga gidan surukan Halifa muke mutanan kirki sun bashi yarinyar. "
Tace to be karba ba, nifa ba zan yarda da auren yar matsiyata ba kuma kilama baƙi ne tunda naji an ce Fage ce unguwar ta su.
Dady Yace wallahi ba matsiyata bane, yana da kyau ki gane arziki daban da kudi, sannan maganar baƙi a kano ke ki fada min tushen ku,? Ajiye batun wannan ma har akwai wani mutum a duniya wanda ba bako ba, wadanda a kayi duniyar domin su ina suke yanzu ke da har abada bazaki canza ba, ina son ki sani zaki iya duk abinda kike so, amma abinda Allah ya yi shine kadai wanda zai wanzu. " Ya wuce ya barta tsaye cike da mamakin Dady, kenan shima aikin da ta yi akan sa ya yi kasa, lallai a kwai bukatar sabunta aiki domin yana da ga cikin wanda za su bata matsala.
Hajiya Talatu da Ma u suka yi sallama Har cikin falo ba a amsaba da alamu basa nan. Ta zauna kan kujera tace da Ma u aje jakar kema ki ki zauna kila ta tafi shegen yawon malamnta yaran kuma kila suna makaranta. Tana zama Hafsi na shigowa falon tace "Oyoyo Hajiya ku ne da yamma haka, ta dubi Ma u Sis harda ke yaushe rabona dake tun bikin Bros Adamu." Ma u cikin murna tace shine ai nace nima sai nazo bikin Halifa. Hafsi tace "Ai dama bikin Uncle Halifan kuka zo sai rana ita yau fa? " Hajiya Talatu tace To zamu zo sayayya muka hada tafiyar ma yi zuwa biyu, kuma banda abinki suwaye abokan sharawar, kinga Hafsa je ni ki kawo mana abinci mun kwaso yunwa da kishi. Hafsa tace "Aiko sai dai a dafa muku taliya dan dazu yarannan suka cinye ragowar abincin rana da za su islamiya. Ta dubi Ma u zomuje mu dafa."
Hajiya Talatu tace taliya ba wata tsiya ba sai an mata gayya kije ki dafa mana Ma u tasha gajiyar mota daga Zariya zuwa kano lafiya ba ne.

Hafsi ta wuce tana kunkunan cewa nifa shiyasa na tsani matar nan wallahi ta zo gidan ku ta kama yi maka iko, masu shagen kwadayi.
Ita kuwa Hajiya Talatu ta kalli Ma u, tace tun yanzu zaki fara baza kafasitin ki a gidan nan domin ke ce zaki auri Halifa kuma shine gidan. Kinsan fa wannan gidan daya daga cikin gidajansa ne suke zaune, Haka gidan da Adam danta ya sa matarsa kafin ta sa ya sake ta. Haka kudin Halifa Adam ke juyawa a kasuwar kwari sannan shi kanshi Dadyn na su store dinshi na singa ai dukiyar Halifan ce gidajansa ance sunfi a shirin na haya domin komai da ki ke gani nashi ne. wannan ce amsar tambayar ki ta rannan, shine dalilin da yasa nake son ki auri Halifa, kuma shine dalilin da yasa ita Habiba take son sai wadda ta ga dama zata aura wa Halifa. A haka ma ta boye min wasu abubuwa fa.
Ma u ta mike ta yi rawa tace "Allah ya nuna min in auri Halifa duk sai na yi maganin kowa wallahi. " Sai sun tashi a gidan nan.
Hajiya Talatu tace abinda ya sa muka zo gidan nan da wuri saboda ki aiwatar da abubuwan da Malam na shuri ya bada, kuma ki natsu ki yi su cikin hankali kar a samu kuskure, sannan ki hada da kirsa.

Hafsi ta kira Anty a waya yafi sau Talatin amma bata daga ba, dan haka ta dafo musu farar taliya da mai da yaji. Hajiya Talatu ta ce "Lallai Hafsi mu zaki ba mai da yaji kamar yan iska?" Hafsi tace ba kayan miya ne ta wuce warta dakinta sai lokacin Anty ta kira, tana dagawa ta soma yi mata fada. "Kiran uban me ki ke min ne?!! Kinsan a tashin hankalin da nake ciki kuwa ance min masifa zata sauka min a gida ina nan ina ta fadi ta shin ganin na samu mafita ke kuma kin ishe ni da kira.
Hafsi tace " To ai masifar har ta sauka ina ta kira kin kasa daga wayata." Innalillahi wuta ce ko mutuwa aka yi? Hafsi tace kawarki ce Hajiya Talatu da Yarta Ma u suka iso da katuwar akwatin su wai sun zo bikin Halifa. " Anty ta kasa magana dan mamaki wato dama Talatu ce masifar da Hajiya Kaka mai wuri ta fara gani tana watsa wurin ta na bincike. Hafsi ta katse mata tunani da cewa kin taho ne.? ' Humm na taho lalai tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkairi ba....

*ƘARSHEN FREE PAGES*

*Zaɓi biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: Fage 4



Kafin Anty ta karaso tuni Hajiya Talatu ta yi wa kanta masauki a dakin Anty Har ta cire kayan jikin ta ta dauki zanin wankan Anty ta daura, zata fada bandaki ta ji sallamar Anty, da yake munafukan juna ne nan suka hau ihun murna kowace tana fadin sahiba ta ga sahiba.

Idan matan nan biyu suka hadu ko shedan nasan gefe yake komawa ya yi kallo, domin dukkan su sunfishi hau. Nan suka zube a kan gado suna hirar yau she gamo tare da nuna kewar juna, Anty ta yi ta nuna jin dadin wannan zuwa da Sahibar ta ta yi. Tace ai kin fi min yan uwana su hudun duk mata ne amma ko kai lefen Halifa ba su zo ba, ke ko ganin kayan ba su zo ba.
Hajiya Talatu tace,, "Watsar da su ai gani, sai ranar biki su zo su ishemu da kararrafi." Sai kuma suka bige da labarin dangin su kowa yana aibata na shi suna zagin su.
Halifa ya shirya tsaf cikin shadda mai ruwan siminti ya kalli madubi ya so ya saka hula amma kanshi ya yi masa nauyi tun da ya sako kafarshi gidan, ga wani bacin rai da ya ke ji kamar ya hau kowa da zagi. Cikin zuciyar shi yake nanata La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin. Ya sani duk bacin ran da Bilkisu ta haifar mishi ne, amma ko ajiyan baiji irin wannan yanayin tabbas ba. Ya fesa turare ko ma me yake ji dole ne yanzu ya tafi gurin yarinyar nan dan suga juna, domin yanzu in aka sata cikin wasu matan kamar ta ba lallai ya gane ta ba.
Ya fito yana rufe daki kamar daga Sama ya ji sallama a bayan sa, muryar mace ce dan haka bai amsa ba kuma bai jiyo ba saida ya gama kulle dakin, yana jiyo wa ga mamakin sa sai ya ga ta feso mishi wani gari kamar hoda, da sauri ya rufe fuskar shi tare da fadin a'uzu bikalimatillahi tammat min sharri ma kalaka. Ma u ta kyalkyale da dariya "Ango nice fa Asma u, ka tsorata ne hodar angwanci ce fa na fesa maka irinta al adar garinmu."
Ya bude fuska ya kalle ta rai bace. Ya daga murya "Ke wacece da zaki zo kina min irin wannan wasan ni sa an ki ne? Tace "Yi hakuri ta juya da gudu ya bita cikin gidan inda ya samu Hajiya Talatu da Anty a falo. Ko sallama bai yi ba ya dubi Anty Wace irin mara tarbiyyar yarinya ce ta shigo gidannan ta zo tana watsamin wata hoda wai wasa, da wa nake wasa a gidan nan har ita tasamu irin wannan damar!!
Anty ta mike, cike da fargaba da kuma zargin Hajiya Talatu. Tace Halifa nutsu ka fada min me ya faru? Hajiya Talatu ta yi caraf yanzu haka Ma u ce, Sarkin tsokana al adar mutan garinmu ta yi maka, ka yi hakuri. Halifa ya kalli Hajiya Talatu dan Allah ki gaya mata ita mace ce ya kamata ta kama kanta, amma ni in har ta sake yimin irin wannan haukan to zan mata jahilci. Ya juya ya fice ya koma ya bude dakinsa dan gyara jikin sa.
Anty ta kalli Hajiya Talatu ta ce Sahiba da wace fuskar kuka zo gidan nan? Talatu ta yi yar dariya "Wai har kin saka wani tunani daga dan wannan wasan Sahiba? To zuciya daya muka zo kuma lafiya zamu rabu." Anty ta soma kwalawa Ma u kira ta zo da sauri tana dariya kamar wata sakarya tun kafin Anty ta tambaye ta har ta soma zuba, Anty na ba Uncle Halifa tsoro ashe haka yake da fusata? Tsawar da ya yi min har yanzu hanjin cikina bai kwance wani kulli da ya yi min ta nan gefen ba. "Da Allah yi wa mutane shiru! Anty ta daka mata tsawa. Indai ma wani tunani ki ke akan Halifa to ki sani ba irin mace da yake so bace ke.!" Hajiya Talatu ta danne fushi da ke son ta so mata. Anty ta sake fadin "Ina mai gargaɗin ki da babbar murya daki bar bala i ya yi bacci, ki bar hanyar dakin shi har kubar gidan nan ke rashin kamun kan naki ko a ina sai kin nuna shi?!"
Ma u ta zo wuya ta kalli Mahaifiyar ta sai ta girgiza mata kai, sannan ta yi mata alama da ido wai ta bada hakuri. Dan haka cikin sauri tace Kiyi hakuri Anty bansan zaiji haushi ba. Ta kalli Hajiya Talatu Mama ki bata hakuri. Hajiya Talatu tace, " Ba zan bata ba, ai dama zane ki tayi ko shi Halifa ya daura miki mari kinga Ma u bana son dibar albarka ai da nasan haka zakiyi bazan taba zuwa dake ba sakara da Allah wuce mana a nan."

Anty ta cika da mamaki domin wannan ne karo na farko da Sahiba ta yarda yarta ta yi ba daidai ba. Dan haka ta saka a ranta cewa da walaki goro a miya domin banza bata kai zomo kasuwa. Dan haka dole ta baza idanu ko ta ina dan kula da abinda Sahiba da yarta za su aikata mata a gida. Kalaman Hajiya Kaka suka dawo mata inda take cewa ga wata masifa nan zata sauka a gidan ki, gobara daga daji maganin ta sai Allah.

Hajiya Talatu ta mike ta bi bayan yarta, bari in je inci kaniyar ta. Ta katse wa Anty tunani.
Anty ta taba baki in ma lallashinta zaki je ku dai kuka sani.

Hajiya Talatu ta samu Ma u tana kai da kawo a cikin dakin Hafsi inda nan ta kwana. Ma u ta tari numfashin uwar da cewa amma Mama kina jin irin bakaken maganganun da matar nan ta yi min kuma wai ke ma ki ka biye mata. Hajiya Talatu ta yi kasa da murya tace "Dadina dake gaggawa, Ma u shifa yaki da ki ke ji da gani dan zamba ne. Kar wannan abin ya daga miki hankali nan gaba kadan komai zai dawo hannunki sannu a hankali sai kin rama duk wani wulakanci da kowa ya yi miki. Yanzu fada min kina ganin ya shaki wannan hodar? "
Ma u tace duk da dai ya sa hannu ya tare fuskar sa amma har atishawa naga ya yi, wannan ke nuna ya shaka. Hajiya Talatu tace angama sai mu jira sakamako nan da gobe.

Asiya tana yanka awara ta kalii Sadiya tace, Maman Annur kinji wai anjima abokin Yaya Sulaiman zai zo da bayan Isha i. Sadiya ta sa dariya tace "Mijin ki zaki ce." Inna tace to ai da baki yi awarar ba me ya sa baki fada ba?
Asiya tace to zamu fasa yin abinda zamu samu abinci? Ni ina ganin ko Abba zai iya zama ya siyar min idan ya zo. Inna tace shike nan in kin shigo sallar Ishai sai ki jira shi a gida kar ya same ki gurin suyar. " Asiya ta ce to. Sadiya tace" Inna a ciro mata dan turare a kayan lefen nata ko? " Inna tace e mana har da Hoda da janbaki. Murmushi Asiya ta yi a zuciyar ta tana kara sallamawa ga lamarin Allah. Wai ita ce yau zata yi aure wadda ko saurayin bata da shi, wadda yan matan layi suke mata Kallon kazama, gashi ita ba wata kyakyawa ba sirantaka kuwa wasu har ce mata suke sullen kara. Masu tura kurar ruwa sunfi nuna suna sonta wasu ma da lalata. Sai gashi jiya zuwa yau Allah ya kawo wani sauyi

Please Login or Register in order to submit comment