Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kuka tana kallon Anty dan neman ta yi wani abu. Dady ya sake nufarta yana fadin bari in zane miki jikin ki in ya so sai kiyi kukan mai dalili. Ta fada dakin su ta kullo kofa tana ta rusa kuka. Anty tace Lallai abin naka da gaske ka ke yi to kuwa ba zai yiwu ba ko asiri aka yi maka sai na karya shi.

Ta nufi wayarta ta dauka ta shiga neman number Adamu Ya daga yana gidan amarya lokacin ya shiga wanka. Amarya ta daga wayar Anty cike da bacin rai tace Ina mai wayar bashi maza . Amarya tace ya shiga wanka.
To yana fitowa ki ce ina neman sa maza yanzu yanzu a gida Amarya tace haba Anty yanzu fa ya dawo kwana biyu ba ya gari, gaskiya sai da safe zai zo koma meye abarwa safiya. Anty ta kara zuwa iya wuya, tace "Ke zan dura miki ashar ina wasa da ke ne dan uwarki,Ina kiran dana ki na fada min cewa sai gobe zai amsa kiran!!" Sa ar uwarki ce ni?" Katse wayar ta yi sannan ta goge kiran ta kuma kulle layin Anty data Hafsi ko sun kira zasuji yana amfani da wayar. Dan haka babu abinda ya fahimta da ya fito, sai ma ciwon cikin da ta hau murkusu, tun yana mata sannu abin babu sauki har dai ya ce ta tashi suje Asibiti. Ta yi ne shima dan su fice ta san Anty zata iya zuwa gidan.

Ta kira Halifa ya dauka, tana kuka take fada masa cewa Dady ya na wulakan ta ta akan wannan gidan daya bashi dan haka ita tana neman su yanzu. Halifa wanda ke cike da jin haushin ta yace gaskiya ba zai iya zuwa yanzu ba sai da safe, tace Halifa ni ke kiran ka kana fada min sai da safe? Yace "To Anty kin san uzrina ne? Jiki ba kwari tace a a, yace" To a barwa safiyar.

Anty ta furta cewa lallai ta kare min, me ya rage min na kima yanzu, ta fashe da kukan gaske ba kamar na dazu na wasan kwaikwayo ba.

Washe gari tun safe masu kawo kayan Bintu suka shigo da sabon gado wanda Dady ne ya siya da kujeru sai sauran tarkacen ta na akin da kayan sawa. Yan gidan su sun zo da yake yan gwale ne, suna taya ta gyaran gurin Dady ma yana tsaye a gurin yana sabe da Ahmad a kafadarsa.

Halifa ne ya shigo gidan bayan ya yi fakin din motarsa, suka gaisa da Dady ya tambaye shi ko anyi baki ne a gidan ya ga yaro. Dady yace Bintu ce ta dawo gidan, dama ina son magana da ku na kira Adamu ma yana hanyar zuwa. "Wacece Bintu?" Halifa ya tambaya. Matar marigayi abokina wadda ka ke ba su zakka. Oho to madallah. To bari in shiga ciki, Dady ya ce to.
Jim kadan sai ga Bros shima ya shigo. Ya tambayi Dady su waye ke tarewa a gidan? Yace muje ciki akan magnar ne na kira ku..

Anty tana ganin Halifa ta dora sabon kuka, shi kuwa Baice kala ba haushin Anty ma yake ji in ya tuna abubuwan da ta yi masa.a haka tana ta rattafawa Halifa zance har su Bros suka shigo lokacin tana fadin wai ya kama Hafsa yana ta duka. Halifa yace "Dady baya duka gaskiya abinda ya saka Dady ya daki Hafsi to ba karami bane."

Dady ya cafke maganar da fadin Wai Yarinyar nan ta bude baki tana neman zagina a gabanta gata nan. "Zagi!!!" Halifa da Bros suka hada baki. Gata nan Ai a gabanta aka yi. Dady ya fada yana nuna Anty. Bros yace "Dady ai da ka yi ma shegiya dukan da zata suma, kyashi Dady ta fito da miji ko kuma a samo ko waye a dangi a tura masa ta karata mara hankalin banza kawai. Dady yace Nima na yi tunanin haka amma bari mu gama da abinda ya tara mu.

Anty ta kalli Bros Dan uban ka kai har kana da bakin magana, jiya in kira ka har sau nawa matarka ta daga tace bazaka zo ba dare ya yi ta kashe min waya ?Bros yace wace matar a ciki? Har nawa ne matan naka? Anty ta katse shi. Gabanshi ya fadi ya yi katobara,sai ya wayance da fadin To abin ne da mamaki Anty kin ce mata tace bazan zo, ba, to tama isa ta daga min waya ne,ki dai duba kinyi kuskuren kira ne amma jiya da dare ina gida. Anty tace 'E ai bansan lambar ka ba kuma kowa ya sani wallahi babu wanda zai yi wa Hafsa auren dole wallahi garama ku sake shawara,sannan dole Dady ya janye batun dawo da wacan matar nan gidan dan kuwa sai dai ya zaba ko zamanta ko nawa,dan kuwa bana son ganinta a gidan nan.

Dady ya kalli Halifa da Adamu yace ku bani hankalin ku kuma ina son ku fahimce ni sosai game da Zaman matar can a gidan nan.Acan inda take ni ke biyan haya kuma ni ke ci dasu,nan kuwa in tadawo na huta. Anty tace shi bata yarda ba. Bros yace To ke Anty menene matsalar ki da haka kowa da gefen ta? Tace haka kawai,nan gaba kuma sai yace zai aureta, ni ba damuna zai yi ba dan ya aureta amma abin kunya ne ace na hada miji da ita. Halifa ya ja tsaki yace duk kishi ne banda abin Anty tunda shine da gidan sa kuma kema karkashin sa ki ke ya yi yadda yake so da gidan sa.

Anty tace "Haka ka fada to ni na hakura da gidan nasa ya bani takarda ta zan kama haya. Dady yace To bari kiji cikakkiyar Magana sai dai karki zauna amma Bintu mata ta ce,na aure ta shekaru hudu da suka wuce muna da yara biyu Ahmad da Nasir yanzu kuma tana da wani cikin...


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

[11/25, 17:05] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt


*Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302*



Tamkar mafarki Anty ta ji kalaman Dady wan da ke magana babu alamun wasa bare tsoro kokuma shakka .

Ba iya Anty ba Bros da Halifa sun girgiza da jin wadannan kalamai na Dady, dakin ya yi shiru kowa da abinda yake tunani, Lallai wata damuwar tafi karfin kuka, domin Anty da a banza ne da yanzu ta fadi tana farfarin mutuwa,amma yanzu gata zaune ta zubawa Dady ido wanda ke sauraro ko wani zai furta wata magana amma duk anyi shiru.

Ya yi gyaran murya babu mai abin fadi, in babu to kuna iya tafiya dama na sanar da ku ne dan naji Habiba tana ikrarin yi mata wani abu, karta sake ta soma,ku ne dai yanzu wadanda dole ku fada mata gaskiya. Cikin wata irin murya wadda da kyar Anty ta tattara yawun bakinta ta soma magana, "Yanzu kana ganin ka yi daidai kenan wannan cin amanar da ka yi min? Halifa ku du ba fa, kuji zancen nan shekaru hudu baya ya yi aure ban sani ba, ku baku sani ba,yanzu kana bashi gida har ya kawo matar,kuka ya kufcewa Anty Halifa in har ni yar uwar ka ce kuma na isa da kai ina son ka janye wannan kyautar Gidan da ka bashi." Ta ci gaba da rusa kuka.
Dady yace ki godewa Allah da ya tsaya a kishiya kawai, in dan ta halinki ne ba sai mutum ya kama bin matan banza a waje ba, me kika sani na kula da miji? Abinci saidai ki aiko yara su kawo min, shinfidata zaki iya tuna rabonki da kakkabe min bare ki kwanta akai? In na matsu da bukata ta sai dai na zo dakin ki inkin gama wulakantani da min ba a da gori da kira na jarababbe sannan in naci sa a ki bani hakina shima kina yi kina ke inyi sauri kina jan tsaki. A haka na rayu da ke, yanzu kuwa in azuminan ya zo shekara guda kenan rabon da ki bani abinda ya shafi hakki na kwanciya.

Ya kalli Bros wanda ya sunkuyar da kai,zantukan sun yi wa kunnuwanshi nauyi, Dady ya ci gaba da fadin dukkan ku ba yara bane yanzu, kowannen ku ya san yanayin da nake magana a kai, idan na yi aure dan in tsare mutuncina da na iyalina akwai laifi a ciki? Suka girgiza kai alamun babu. Anty ta katse shi da fadin Wallahi gara ace ga ka can an kama ka da wata akan wannan ranar ta yau ni a guri na. Bros Yace "Au'zubillahi minna shshaidani rajim,Allah ya tsare mu da mugunji da mugun gani, Anty infa rai ya baci hankali baya bata,ko mu da muke matasa bama fatan a samu haka a garemu bare mahaifinmu Dady Allah ya kara rufun asiri,in hali ya samu ka kara mata biyu Allah ne ya yarje maka, zan tafi dan bazan jure jin wadannan zantukan ba. Bai jira amsa ba ya wuce cike da bacin rai.

Halifa ya dago ya kalli Dady zuciyar shi tana fada mishi cewa kenan wata rana Asiya zata iya yi mishi fatan ya yi zina idan har Anty a matsayin uwa kuma kaka tana kauracewa mijinta tare kuma da mishi wannan fatan kila duk haka mata suke domin dai ba a haka suka yi aure ba. Halifa ya sauke ajiyar zuciya,Yace "Dady lokacin da zaka auri Anty amma tilasta mata aka yi ko? Cikin sanyin murya ya yi maganar.

Dady yace inji wa? Tana sona ina sonta aka yi mana aure, mun dai samu yar tangarda kafin bikin da yake muna tare da ita tun tana primary lokacin mahaifinsu yana raye, bayan rasuwar shi lokacin ina dako a singa ni na ci gaba da daukar nauyin karatun ta da kananan bukatu har zuwa lokacin da mahaifiyar ku ta auri mahaifin ka. Ganin sun koma gidan masu hali tunda shi mai kudi ne. Sai ta tsiro min da matsaloli da bukatun da suka fi karfina,nace na hakura shine mahaifiyar ku tace bata isa ba, kawai ma ayi auren mahaifinka shine ya yi mata komai kuma da zai yi auren yayansa ya hada da namu bai fi sati daya ko biyu da auren ba mahaifin ka ya rasu lokacin da cikin ka.

A haihuwarka Allah ya yi wa mahaifiyar ka rasuwa lokacin ni na bata shawara aka ta amso ka mu rike ka.Da kyar baffan ka ya yarda domin yace bamu taba haihuwa ba baza mu iya kula da yaro ba. Ni na dage muka amso ka, haka duk yadda za ayi ta samu ruwa nono na yi amma abin ya faskara sai dai madara na dinga saye duk sati wannan abokin nawa mijin Bintu ya sai madara ba sau daya ba
Na kawo an baka. Ai gata zaune tace karya ne in ta isa.
Lokacin da ta samu cikin Adamu renon ka gurina ya dawo, da kyar nake fita a gidan nan in kana kuka sai ka bini. Lokacin da ta haifi nata dan haka ta juya maka baya Lokacin na mata uzri dama ba kowace uwa bace zata fifita dan wani akan nata. Amma sai ta zo ta soma nuna kishi akan ka wai nafi kula da kai na fi sonka. Anty ta Katse shi "Au har sharri zaka hada min da shi?" Dady yace Ki rantse baki taba yin yaji kince in zauna gani ga Halifa ba, ai Babarku tana raye bata mutu ba. Sai da kika yi yaji akan na saka Halifa makarantar kudi wadda kike korafin nawa nake samu da zan saka shi, in bari danki ya isa makaranta shi a saka shi naki. Duk kayan wasan da nake kawo wa Halifa ba boye wa danki ki ka yi ba?

Keke nan da na sai wa Halifa kwacewa ki ka yi,duk sharri ne na yi miki? Halifa ya tuna maganar Keke lokacin da tace wai tana tsoro kar yaje mota ta takashi amma tabbas daga baya Bros yana hawa keken. Ya tuna wannan lokacin yana da wayo.

Ya yi murmushin takaici, yace Dady ka share min tantamata da kuma mamakina akan abubuwa da Anty ta yi min ko take kan yi min zan tafi amma ka sani nima ina goyon bayan ka dawo da matarka nan kuma suma yaranta zan dauki nauyin karatun su kamar dai na yan uwansu.

Sannan nima zan kira irin zaman nan nan da lokaci kadan. Anty tace "Halifa zo kaji karfa ya hada mu duk abin da yake fada son zuciyar sa ce kawai.

Halifa yana tuki yana tuna zantukan Dady ba shakka bai yi kuskuren ba wa Dady gida ba, duk da tarihin da Dady ya bashi ya dame shi amma fa babu kamar waccan kalma da Anty ta furta ta cewa gara ace ga Dady can an kama shi da wata yana zina da ace ya kara aure, duk mata haka suke? Wata rana Asiya zata iya fada masa haka dama yanzu ma ta nuna kishin ta mai karfi. Cikin wannan tunanin ya iso gida, Asiya tana kichin ta tasa Fati suna yin miyar nan margi special. Bata san ya shigo ba sai da suka gama ta nufi daki dan ta yi wanka sai kawai ta ga mutum kwance. Da sauri ta nufe shi ta zauna bakin gado ta kamo hannunshi ta saka a cikin nata tana tambayar shi, Yaya lafiya dai? Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya maida kallon shi gare ta yana tunanin abinda zai faru gaba.
Tsoro ya kama Asiya tace Yaya kamin magana baka da lafiya ne? Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya tashi zaune, ya "Asiya zan tambaye ki wani abu." Asiya ta danji dim domin duk lokacin da zai yi magana yace Asiya ba shakka magana ce mai muhimmanci.

Cike da tsoro da kasala tace to Yaya ina jinka. Yace Zan baki zabi daya a cikin biyu. Gabanta ya fadi ba dai zai ce ta tafi gida ba, ko maganar saki. "Kina ji?" Ya katse ta. In inajinka Yaya ta fada da in'ina, Yace Nan gaba in Allah ya amince ina son kara aure,in kuma ba haka ba to zaki lamun ce min in nemi mata banza a waje kinga ba ruwanki da kawo miki kishiya."

Asiya ta mike tsaye da sauri tana fadin Au'zubillahi minna shshaidani rajim. Allah karka kama shi da wani laifi mai kama da wannan. Allah kar ka sa mala'iku su amsa wanna magana.Ta kalle shi, Yaya daga ina ka ke? Taje ta kama fuskarshi ta kai hancin ta gurin bakinshi ta shaka. Tace Yaya duk da bansan wari kayan maye ba banji alamun kasha wani abu ba, nasan baka sha kuma ba su ka shaba. Menene ya kawo wannan tunanin a zuciyar ka? Me zai sa ka ce zaka nemi mata a waje. Ta fashe da kuka, ta durkusa a gaban shi Yaya wallahi na yarda ka sake ni ka auri mata hudu in baka bukata ta, da ace ga uban dana yana bin matan banza gara a ce ka auri mata hudu. In har maganar da na yi maka ce dana ce bana son ka kara aure ta kawo wannan tunanin Yaya ka yafe min wallahi bazan sake ba. Ka yi auren ka ko yanzu ka ke so Allah ne ya baka dama kar ka damu da kishina. Ta fashe da sabon kuka. Halifa ya tashi cike da tausayin Asiya ya kamota ya rungumeta yace ki daina kuka wani abu ne na gani ya rudani dan Allah ki yafe min Baby. Asiya tace Yaya Allah ya yafe maka da ka ayyana kan ka da aikata zina,dan Allah kar ka sake, Ina son ka min alkawarin yadda baka aikata zina ba kana samartaka yanzu ma baza ka yi ba. Yace na miki alkawari Baby.

Suka zauna tace Yaya ina ga dai da zarar jini ya dauke min zan dawo maka rashin samun kulawata sosai ne ya saka ka soma saka da mugun zare ko?
Yace " Anty ce ta firgitani naga cewa idan har Anty da girmanta a matsayin ta na uwa kuma kaka zata yi fatan da Dady ya yi aure gara a kamashi da mace to ke kuma da kike karama sai Yaya kenan? Asiya ta zuba ido cike da mamaki tana kallon Halifa kamar shine ya fada, tace amma kaji da kyau kuwa? Halifa yace Ba ni kadai bane bare ince kunne na ya yi tsatsa. Asiya tace Allah ya kyauta abin dai ba dadin ji.
Ya bata labarin duk abinda ya faru. Ta sha mamakin Dady ya yi aure ya boye ma matarshi tsawon shekaru. Ga Maman Nihal ita ma Bros ya boye ta. Ta kalli Halifa Yaya Dan Allah zan nemi wata alfarma in zaka yi aure wallahi ba zan taba hanawa ba, kawai ka fada min karka damu da kishi na, kar ka boye mace saboda ni. Ta kama hannuwan shi ta matse cikin nata. Ni da kai wallahi abu daya ne. Ya sunkuyar da kai cikin rashin Walwala Baby sai dai kar a kuma ni ma dai na boye mace kuma har ta haihu. Asiya ta zabura ta mike tana fadin Innalillahi wa Inna ilaihirraji un. Tun wane lokacin ka yi haka? Ya Kalli yadda ta firgita ya kamo hannun ta yace ke ce ai wadda na boye, ya saki dariya yanzu wa yasan muna tare? Ta sauke ajiyar zuciya Yaya ka tsorata ni walllahi dan Allah kar ka boye min komai. Ya kamota ya zaunar da ita a cinyar sa. Asiya wallahi na rantse miki da Allah a yanzu gani nake bani da wani wanda ya kai ki zama jini na, ke ce komai nawa, na baki amanar kaina Asiya wallahi da gaske nake yi, ki sani komai zan yi ki hanani zan hanu amma banda abinda ya shiga hurumin Allah.

Asiya ta rungume shi, nima haka Yaya kuma insha Allah bazaka taba yin danasanin bani amanar kanka ba.

Sulaiman ya taso yaro da yamma zuwa gaban Inna, ta tabbatar masa da cewa shine ya kawo takardar a gaban Inna ya tambayi yaron yaron yace 'Ni dai wasu mata ne suka bani suka ce ince inji ko wa ma nace da nazo na manta sunan har suka bani dari biyar. Sulaiman yace To kinji dai Inna da kunnan ki, wallah sharri ne kawai, Inna tace kayya to yanzu ina ma Asiyar take,ta fada cikin yanayin tausayi. Sulaiman yace Allah zai dawo da ita lafiya kuma wallahi mijinta bai zauna ba, yana can yana neman matar sa.

Sulaiman ya kira Halifa ya fada masa halin da a ke ciki Inna ta fahimta fata dai Allah ya bayyana Asiya. Halifa ya ji dadi kuma ya yi godiya. Yace dan Allah zai neme shi akan ya kawo Inna akwai zama da za ayi Sulaiman yace Insha Allahu ba damuwa.

Kafin Asiya ta yi arba'in sai da ta tabbatar ta koyi duk wani salon girki da Fati ke yi,ta kau da kai daga duk wani kini bibi da Fati ke yi idan taga Halifa.

Ta kuma sa ta yawo da hijabi a gidan da ta kula takan fizgi hankalin Halifa in tana kai kawo.

Bangare Hajjo ma Asiya ta ko yi wankan yaro dan haka bata da matsala da wannan.

Ranar da zata cika arba'in ta sa su Hajjo suka zo mata da me lalle aka zuba shi ta yi mata kitso gurin mai kitso ta sai wasu magunguna duk da dai ta yi amfani da abubuwan da ta samu a soshiyal midiya na gyaran jiki ga masu jego. Da yamma ta zuba wanka ta yi kyau kamar amarya. Halifa ya yi ta kallon ta yana mamakin bayan fitar shi duk ta yi wannan gyaran kasa cin abincin ya yi dan doki, ya shiga nuna mata zalamar shi . Da safe ya tashi cikin yanayi mai dadi da farin ciki ya laluba gefe bata nan. Kichin ya same ta tana hada abin kari. Yace zomuje ki bari su Fati su yi. Ta kalle shi, ai na sallami su Fati tun jiya. Gaban shi ya fadi, cikin in'ina yace "To me suka yi miki? " Ta yi murmushi babu komai, aikin su ya kare tunda na yi arba'in. Ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin ok na fahimta. Amma ai baza ki iya kula da gidan nan ba,ga yaro tace Zan gwada in na kasa sai mu samu mafita.

Sai dai yadda Halifa ya yi ne ya sa taji kamar akwai wani abu. Ya fita da sauri bata bi bayan shi ba sai da ta dauki tiren abin kari ta fita. Baya falo kamar yadda ta zata dan haka sai ta gama hada komai sannan ta nufi dakin, karaf ya aje wayarsa da sauri bayan ta murda kofar ta shigo, ya kama fadin kin kin gama hada break fast din ne da wanka zan yi, Asiya ta yi saurin kauda shakkun ta tace yanzu muje in maka wanka sai ka zo mu karya din ko? Yace muje dai mu fara karyawa bari in yi brush. Ya kuma daukar wayar sa ya saka aljihun jallabiyar sa. Murmushin takaici Asiya ta yi sannan tace ina jiran ka a can. Ta kalli danta yana bacci a gadon sa sannan ta wuce.


*Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302*


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[12/4, 12:12] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt

Inna bata gamsu da abinda Sulaiman ya fada ba,dan haka ta taka da kanta ta je har gidan su yaron ta same shi ta fadawa uwarsa komai, tace ita tana son yaro ya fadi gaskiya game da abinda ya sani na aiko shi da aka yi,kamar yadda ya fada haka ya maimaita Inna tace wa uwar dan Allah su lallaba mata shi ko zai fadi gaskiya. Ta kama hanya ta tafi.
Yaro kuwa ya yi ta rantsuwa akan cewar iyakacin Gaskiyar shi kenan dan haka suka shedawa Inna halin da ake ciki Inna dai zuciyarta ta kasa yarda amma bata da wani zabin ko tunanin face ita dai aga ƴarta.

Anty tana zaune ta zabga tagumi abin duniya ya ishe ta,wai yau duk takamar ta isarta da ikonta da juya Dady da take yi ita ya yi wa kishiya da wata mara aji. Matar da bata fi ta yi mata wanke wanke ba.

Halifa da take hankoron yadda zata mallaki abinda ya mallaka ta juya ta yi sabuwar rayuwa, abinda ta gina a zuciyarta tsawon shekarun da ta rike Halifa Dady ya rusa komai ya hada ta dashi hatta danta da ta Haifa ya tsane ta. Ta farajin Duniyar ta isheta gara ma ta mutu ta huta.

Katsam sai ga kiran Hajiya Talatu, bata ji wani daɗi ba,domin zuwa yanzu tana jin kunyar faɗin wai an mata kishiya. Talatu tace Sahiba me yake faruwa ne haka ba kya ɗaga waya ta. Anty tace Talatu ina cikin masifa ba karama ba, Me kuma ya faru? Ki bari kawai Me gidan nan ne ya munafurce ni ya yi aure, ta fada mata halin da ta ke ciki. Talatu ta ce "Ba ki makara ba kawata, kishiya dai dama ki saka mata date na barin gidan ki dan haka kar ma ki sata a gabanki, shi kuwa Halifa har yanzu ba shi da mata bare ɗa, kuma duk a ciki ƙoƙarin ki ne haka ta faru,aikin ki ya sa ta haukace ta bi Duniya kin ga ko hakan ma

Please Login or Register in order to submit comment