Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

ai nasara ce, ki koma ga malamai ki ki sa a haɗa Halifa da Aljana ta aure shi bazata taɓa bari ya yi aure ba bare ya haihu, sannan ki dage ki mallake shi, farraƙa Dady da matar nan ba wani dogon aiki bane, abin kunya ne su Hajiya Gaji su ji wannan yadda suke gulmarki cewa kin tare gaba kin tare baya."
Anty ta ja tsaki Bana son wannan mafitar.domin sabga ce ta cin kudi kuma bani da su.

"Habiba kina da hanyar samun kudi tun kwanaki na fada miki, kin ki ne da yanzu ba wannan magnar ake yi ba. Tsaki Anty ta ja dan ta tuna abinda Hajiya Talatu ta yi ta bata shawara a kai. Tace dan Allah ki bar wannan maganar domin yanzu ko da mun hada baki yan bundiga sun dauke ni ba wanda zai damu sai su Hafsy ƙilama Dady murna zai yi ya rabu dani. "Ga Halifa? "Hajiya Talatu ta katseta. Anty tace tab ai Halifa yanzu ya fi kowa tsanata. Kwabon shi ba zai bayar ba dan fansa ta, ni dai kawai zan taho wajen ki in dan huta, dan naji Halifa yana fadin zai kira zama ina tsoron ma ko ya gano wani abu ne. Hajiya Talatu tace "Dan wannan ba damuwa zan turo miki kudi sai ki zo mana da shinkafa,kinsan Kano tafi sauki. " Anty ta fusa ta, tace Au kina fada min inzo da abincin da zanci ke nan ko? Ni da kike zuwa gidana ko sanar dani zuwanki ba kya yi sai dai ki diro min fa?" Hajiya Talatu tace "Wallahi Sahiba ba haka bane maida wukas Allah ya kawo ki lafiya." Anty tace na fasa zuwa ma ta kashe wayar.

Hajiya Talatu ta sa dariya ta ce shegiya dadina da ita saurin gano inda mutum ya dosa,kar ta zo da shinkafar aikuwa ta kwashi faten tsaki.

Asiya ta kula da yadda Halifa sam baya son ta kusanci wayar sa, ba kamar da ba in ankira zai ce miko min watarana ma har in yaga wani abu a tiktor zai ce zo ki gani, hatta lambobin sirrin shi ta sani, amma yanzu sai taka tsantsan. Alamu sun gama nunawa akwai abinda yake boyewa dan haka sai ta fara tunanin abinda ya kamata ta yi, dan ta dakile abin da take zargi.Abu dai mai muhimmanci shine ta hadu da Innar ta kafin komai dan haka bari ya dawo.

Abinda ya daure mata kai shine yadda Halifa yau shine har karfe shabiyun dare bai dawo gida ba, mutumin da sai ya dawo gida ma sannan ya fita sallar magriba, ta kira wayar shi yafi sau hamsin amma bai daga ba, kuma ta mai text tana tambayar ko lafiya, amma babu amsa,dan haka ta sawa zuciyarta cewa tabbas Halifa ko dai ya fara neman matan da yace, ko kuma yaje gidan su Fati.

Ta yi kuka har ta godewa Allah abinda ya bata mamaki da ya shigo ya ganta zaune a falo. Wai sai yace "Lafiya ba ki yi bacci ba har yanzu? Ta danne komai ta tausasa murya, ina fa lafiya baka dawo ba,yaushe zan iya kwanciya Yaya ta nufe shi da nufin rungumewa. Sai ya dakatar da ita tare da faɗin muje ciki bari inyi wanka. Kuma sai ya yi gaba ya barta turus a tsaye.

A sanyaye ta bishi ciki tini har ya shige ban daki, ta kalli wayar shi akan madubi zuciyar ta tace kul karki taba masa waya baki san me zaki gano a ciki ba.Wata zuciyar tace ki duba kila ta haka zaki gano matsalar har ki san ta yadda zaki dauki mataki.

Abin mamaki Halifa ya canza lambobin sa na sirri. Ko iya haka hujja ce,ta fada cike da tashin hankali.

Tana canza kaya zuwa na bacci ya fito ta sani yanzu kam in komai bai kawo shi ba jarabar shi zata kawo shi tunda wani sa in ko kwaurin kafar ta ya gani ko ya yi shirin fita zai iya sake wanka.

Amma abin alajabi ko kula hakan bai yi ba ya tada salla ya yi magariba da Isha 'I. Asiya tana zaune bakin gado tana kallon shi har ya idar ya isa gadon Jariri ya sunbace shi sannan ya yi masa addu'a. Asiya jiki ba kwari tace abinci fa? Ya zauna kusa da ita ya dafo kafadarta, shayi kawai zan iya sha.Ta mike zuciyar ta tana fada mata cewa tabbas Halifa ya tara da wata domin ga hujjoji, ya zo da janaba, ya yi wanka hatta sallama hadawa ya yi ke nan tun kafin magariba suke tare, wata zuciyar tace in haka ne me zai hana ya yi wanka acan inda ya yi abin? Halifa yana da kyankyami ba zai iya wanka a kowane irin bandaki ba. Daya zuciyar ta fada mata.

Sannan shayi kawai yake sha bayan ya gama nutsuwa a duk dare in ya kwanta da ita. Da waɗannan tunanin Asiya ta hado shayin ta kawo masa ya karba tare da fadin "Allah ya yi miki albarka. Ta kwanta ta yi lamo. Ya gama shan shayin sa, ya kwanta ya kawo hannu ya janyo ta zuwa jikin shi, sai taji kamar tana kyankyamin shi dan haka sai ta saɓule. Yace Baby wai kina fushi ne dan na jima a waje ? Bata yi magana ba, yace To kiyi hakuri ni namiji ne, kinsan dole wani lokacin ana iya samun haka. Asiya tace "La ba komai Yaya tunda ka dawo lafiya Alhamdulillah. Dama nima wata magana nake son mu yi. Ta mecece? Ya tambaya da sauri tare da kara matsowa kusa da ita, kamar yana tsoron ta fadi wani abu da yake boyewa.
Ta yi dan murmushi mai sauti na takaici, ta ce "Ba wani abu bane ina ganin gobe zanje gurin Inna kawai domin bana son alhakinta ya taba ni,tana can tana tunanin na banda ta yi tawakkali ciwonta baya son ta shin hankali. Halifa ya tashi zaune yana kallon Asiya "Na miki wani abu ne? Ya tambaye ta cikin tsoro, itama ta tashi zaune tana kallon shi. "Me zakamin Yaya kuwa? To me zai sa kice zakije gurin Inna ki bari na gama hada hujjojina ina tsoro kar ta rike ki tace na sake ki. Asiya tace In bata yarda in dawo ba,in ka hada hujjojin sai ka kawo mata shike nan sai mu dawo. Halifa ya tsorata sosai ya sauka daga kan gadon ya na Fadin kinga Baby kar ki min haka ki yi hakuri mana. tare dan Allah kar ki yi min irin wannan hukuncin, wallah rashin ki komai zai iya faruwa da ni. Ta kafe shi da ido. Ka wai ka yi hakuri Yaya. Ya soma fusata saboda ƙin jin maganar sa da ta yi, Ya kama kafadunta yace "Asiya ban yarda ki taka nan da can ba, idan har ni ne mijin ki, ina fatan kin jini ko?!!! Ta tsorata da yadda ya riƙe mata kafaɗu idanun shi sun kada sun yi jajir dan haka ta kwanta ta yi lamo,shi kuma ya koma falo yana kai kawo. Tana jiyo shi yana ta ɓari.
Bai kwana dakin ba, sai dai ko da Asiya bata fita duba ina ya kwanta ba, sam bata yi bacci ba sai gefen Asbahi dan haka ta makara salla. Tana idarwa ta dauki ɗanta dake kuka tana bashi nono. Tambayar kanta ta ke wai dama haka rayuwar aure take cike da kalubale ko kuwa dai nata ce ta zo a haka? Tun da ta yi aure daga wannan sai wannan Hasashen da ta ke yi a cikin aure ashe abin ba haka bane ance ana yin aure dan a huta ita dai har yanzu baza ta dorar da komai ba,to yanzu wane mataki ya kamata ta dauka, tana bukatar me bata shawara amma waye? Ta gaji da yin shawara da zuciyarta. A lokacin kuwa zuciyar ta faɗa mata cewa kawai ki tafi gurin Innar ki, dubi yaje gurin wata kilama wani abin suka aikata ya dawo kuma zai hau wani fushi. kawai ki gama shirin ki kiyi wucewar ki duk abinda zai faru ya faru.
Ta kwantar da yaron ta fita falo zuwa kitchen. Yana zaune akan kujera yana jan carbi sai dai kayan da ta gani a zube a kasa duk an watso su wasu ma sun fashe shine a fushin jiya ya yi wannan aikin baya iya zama bai yi barna ba in ya fusata fushin sa baya sarrafuwa ta daɗi, kamar ta wuce sai wata zuciyar tace Asiya ki gaida shi mana. Dan haka ta dube shi tace ina kwana Yaya? Ya kalle ta ya kuma kalli inda yake zaune ta gane me yake nufi wai ta kusan to shi,amma sai ta kasa kusanto shi tana jin tsoro gashi bai yi magana ba, bare ta gane ina ya saka gabanshi.
Yana cikin fushi ko ya sauka. Ki wuce kawai ai Allah ya gani kin gaishe shi. Zuciyarta ta rada mata. Dan haka sai ta wuce zuwa kicin. Tana kokarin hada karin kumallo yayin da wata zuciya ke faɗa mata cewa ba fa ta kyauta ba, Lalai ta koma ta kusance shi ta gaidashi kamar yadda suka saba.

Ji tayi an rungume ta ta baya, a kunne yake rada mata cewa Baby da gaske tafiya za kiyi ki barni? Kece fa komai nawa kece rayuwata bani da kowa sai ke sai danki. Asiya ta juyo ta rungume shi, " Ba iya son ka kawai nake ba Yaya Ina kaunar ka sosai Yaya dan Allah kar ka kawo ruɗani a zaman mu wallahi bazan jure ba.

Ya sauke ajiyar zuciya ya dago fuskarta hawaye suna sauka akan kumatun ta, Baby Wallahi bazaki taba danasani na aure na ba. Ki kwantar da hankalin ki, cikin satin nan zaku ga Inna ta dauki Babana ta yi masa addu'a cikin farin ciki, in kinje yanzu ba wani bayani kin fini sanin wacece Inna.
Asiya ta sauke ajiyar zuciya miji da mata sai Allah wanda ya shiga zai ji kunya

Asiya ta sauka kuma ta hakura da zuwa gurin Inna saidai ta kara jaddada masa lallai ya sada ta da Inna nan kusa. Ya yi mata alkawarin haka.

Wayar shi ta shiga ruri ya sake ta ya ciro wayar ta kai duba fuskar wayar ko zata ga sunan waye, ta dai ga wasu haruffa ya yi saurin fita a kicin din ya bar falon ma can harabar gidan ya fita tana kallon shi ta window yana kai kawo duk da bata iya jiyo me yake fada ta tabbatar da mace yake wayar domin tana iya hangen hakan a fuskarsa.
Hawaye suka zubo mata a fili tace wannan kuma wace irin masifa ce? Gaskiya ina bukatar mai bani shawara akwai bukatar in sanar da wani damuwata ko zan samu sauki.

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[12/4/2025, 12:12] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt

Inna bata gamsu da abinda Sulaiman ya fada ba,dan haka ta taka da kanta ta je har gidan su yaron ta same shi ta fadawa uwarsa komai, tace ita tana son yaro ya fadi gaskiya game da abinda ya sani na aiko shi da aka yi,kamar yadda ya fada haka ya maimaita Inna tace wa uwar dan Allah su lallaba mata shi ko zai fadi gaskiya. Ta kama hanya ta tafi.
Yaro kuwa ya yi ta rantsuwa akan cewar iyakacin Gaskiyar shi kenan dan haka suka shedawa Inna halin da ake ciki Inna dai zuciyarta ta kasa yarda amma bata da wani zabin ko tunanin face ita dai aga ƴarta.

Anty tana zaune ta zabga tagumi abin duniya ya ishe ta,wai yau duk takamar ta isarta da ikonta da juya Dady da take yi ita ya yi wa kishiya da wata mara aji. Matar da bata fi ta yi mata wanke wanke ba.

Halifa da take hankoron yadda zata mallaki abinda ya mallaka ta juya ta yi sabuwar rayuwa, abinda ta gina a zuciyarta tsawon shekarun da ta rike Halifa Dady ya rusa komai ya hada ta dashi hatta danta da ta Haifa ya tsane ta. Ta farajin Duniyar ta isheta gara ma ta mutu ta huta.

Katsam sai ga kiran Hajiya Talatu, bata ji wani daɗi ba,domin zuwa yanzu tana jin kunyar faɗin wai an mata kishiya. Talatu tace Sahiba me yake faruwa ne haka ba kya ɗaga waya ta. Anty tace Talatu ina cikin masifa ba karama ba, Me kuma ya faru? Ki bari kawai Me gidan nan ne ya munafurce ni ya yi aure, ta fada mata halin da ta ke ciki. Talatu ta ce "Ba ki makara ba kawata, kishiya dai dama ki saka mata date na barin gidan ki dan haka kar ma ki sata a gabanki, shi kuwa Halifa har yanzu ba shi da mata bare ɗa, kuma duk a ciki ƙoƙarin ki ne haka ta faru,aikin ki ya sa ta haukace ta bi Duniya kin ga ko hakan ma ai nasara ce, ki koma ga malamai ki ki sa a haɗa Halifa da Aljana ta aure shi bazata taɓa bari ya yi aure ba bare ya haihu, sannan ki dage ki mallake shi, farraƙa Dady da matar nan ba wani dogon aiki bane, abin kunya ne su Hajiya Gaji su ji wannan yadda suke gulmarki cewa kin tare gaba kin tare baya."
Anty ta ja tsaki Bana son wannan mafitar.domin sabga ce ta cin kudi kuma bani da su.

"Habiba kina da hanyar samun kudi tun kwanaki na fada miki, kin ki ne da yanzu ba wannan magnar ake yi ba. Tsaki Anty ta ja dan ta tuna abinda Hajiya Talatu ta yi ta bata shawara a kai. Tace dan Allah ki bar wannan maganar domin yanzu ko da mun hada baki yan bundiga sun dauke ni ba wanda zai damu sai su Hafsy ƙilama Dady murna zai yi ya rabu dani. "Ga Halifa? "Hajiya Talatu ta katseta. Anty tace tab ai Halifa yanzu ya fi kowa tsanata. Kwabon shi ba zai bayar ba dan fansa ta, ni dai kawai zan taho wajen ki in dan huta, dan naji Halifa yana fadin zai kira zama ina tsoron ma ko ya gano wani abu ne. Hajiya Talatu tace "Dan wannan ba damuwa zan turo miki kudi sai ki zo mana da shinkafa,kinsan Kano tafi sauki. " Anty ta fusa ta, tace Au kina fada min inzo da abincin da zanci ke nan ko? Ni da kike zuwa gidana ko sanar dani zuwanki ba kya yi sai dai ki diro min fa?" Hajiya Talatu tace "Wallahi Sahiba ba haka bane maida wukas Allah ya kawo ki lafiya." Anty tace na fasa zuwa ma ta kashe wayar.

Hajiya Talatu ta sa dariya ta ce shegiya dadina da ita saurin gano inda mutum ya dosa,kar ta zo da shinkafar aikuwa ta kwashi faten tsaki.

Asiya ta kula da yadda Halifa sam baya son ta kusanci wayar sa, ba kamar da ba in ankira zai ce miko min watarana ma har in yaga wani abu a tiktor zai ce zo ki gani, hatta lambobin sirrin shi ta sani, amma yanzu sai taka tsantsan. Alamu sun gama nunawa akwai abinda yake boyewa dan haka sai ta fara tunanin abinda ya kamata ta yi, dan ta dakile abin da take zargi.Abu dai mai muhimmanci shine ta hadu da Innar ta kafin komai dan haka bari ya dawo.

Abinda ya daure mata kai shine yadda Halifa yau shine har karfe shabiyun dare bai dawo gida ba, mutumin da sai ya dawo gida ma sannan ya fita sallar magriba, ta kira wayar shi yafi sau hamsin amma bai daga ba, kuma ta mai text tana tambayar ko lafiya, amma babu amsa,dan haka ta sawa zuciyarta cewa tabbas Halifa ko dai ya fara neman matan da yace, ko kuma yaje gidan su Fati.

Ta yi kuka har ta godewa Allah abinda ya bata mamaki da ya shigo ya ganta zaune a falo. Wai sai yace "Lafiya ba ki yi bacci ba har yanzu? Ta danne komai ta tausasa murya, ina fa lafiya baka dawo ba,yaushe zan iya kwanciya Yaya ta nufe shi da nufin rungumewa. Sai ya dakatar da ita tare da faɗin muje ciki bari inyi wanka. Kuma sai ya yi gaba ya barta turus a tsaye.

A sanyaye ta bishi ciki tini har ya shige ban daki, ta kalli wayar shi akan madubi zuciyar ta tace kul karki taba masa waya baki san me zaki gano a ciki ba.Wata zuciyar tace ki duba kila ta haka zaki gano matsalar har ki san ta yadda zaki dauki mataki.

Abin mamaki Halifa ya canza lambobin sa na sirri. Ko iya haka hujja ce,ta fada cike da tashin hankali.

Tana canza kaya zuwa na bacci ya fito ta sani yanzu kam in komai bai kawo shi ba jarabar shi zata kawo shi tunda wani sa in ko kwaurin kafar ta ya gani ko ya yi shirin fita zai iya sake wanka.

Amma abin alajabi ko kula hakan bai yi ba ya tada salla ya yi magariba da Isha 'I. Asiya tana zaune bakin gado tana kallon shi har ya idar ya isa gadon Jariri ya sunbace shi sannan ya yi masa addu'a. Asiya jiki ba kwari tace abinci fa? Ya zauna kusa da ita ya dafo kafadarta, shayi kawai zan iya sha.Ta mike zuciyar ta tana fada mata cewa tabbas Halifa ya tara da wata domin ga hujjoji, ya zo da janaba, ya yi wanka hatta sallama hadawa ya yi ke nan tun kafin magariba suke tare, wata zuciyar tace in haka ne me zai hana ya yi wanka acan inda ya yi abin? Halifa yana da kyankyami ba zai iya wanka a kowane irin bandaki ba. Daya zuciyar ta fada mata.

Sannan shayi kawai yake sha bayan ya gama nutsuwa a duk dare in ya kwanta da ita. Da waɗannan tunanin Asiya ta hado shayin ta kawo masa ya karba tare da fadin "Allah ya yi miki albarka. Ta kwanta ta yi lamo. Ya gama shan shayin sa, ya kwanta ya kawo hannu ya janyo ta zuwa jikin shi, sai taji kamar tana kyankyamin shi dan haka sai ta saɓule. Yace Baby wai kina fushi ne dan na jima a waje ? Bata yi magana ba, yace To kiyi hakuri ni namiji ne, kinsan dole wani lokacin ana iya samun haka. Asiya tace "La ba komai Yaya tunda ka dawo lafiya Alhamdulillah. Dama nima wata magana nake son mu yi. Ta mecece? Ya tambaya da sauri tare da kara matsowa kusa da ita, kamar yana tsoron ta fadi wani abu da yake boyewa.
Ta yi dan murmushi mai sauti na takaici, ta ce "Ba wani abu bane ina ganin gobe zanje gurin Inna kawai domin bana son alhakinta ya taba ni,tana can tana tunanin na banda ta yi tawakkali ciwonta baya son ta shin hankali. Halifa ya tashi zaune yana kallon Asiya "Na miki wani abu ne? Ya tambaye ta cikin tsoro, itama ta tashi zaune tana kallon shi. "Me zakamin Yaya kuwa? To me zai sa kice zakije gurin Inna ki bari na gama hada hujjojina ina tsoro kar ta rike ki tace na sake ki. Asiya tace In bata yarda in dawo ba,in ka hada hujjojin sai ka kawo mata shike nan sai mu dawo. Halifa ya tsorata sosai ya sauka daga kan gadon ya na Fadin kinga Baby kar ki min haka ki yi hakuri mana. tare dan Allah kar ki yi min irin wannan hukuncin, wallah rashin ki komai zai iya faruwa da ni. Ta kafe shi da ido. Ka wai ka yi hakuri Yaya. Ya soma fusata saboda ƙin jin maganar sa da ta yi, Ya kama kafadunta yace "Asiya ban yarda ki taka nan da can ba, idan har ni ne mijin ki, ina fatan kin jini ko?!!! Ta tsorata da yadda ya riƙe mata kafaɗu idanun shi sun kada sun yi jajir dan haka ta kwanta ta yi lamo,shi kuma ya koma falo yana kai kawo. Tana jiyo shi yana ta ɓari.
Bai kwana dakin ba, sai dai ko da Asiya bata fita duba ina ya kwanta ba, sam bata yi bacci ba sai gefen Asbahi dan haka ta makara salla. Tana idarwa ta dauki ɗanta dake kuka tana bashi nono. Tambayar kanta ta ke wai dama haka rayuwar aure take cike da kalubale ko kuwa dai nata ce ta zo a haka? Tun da ta yi aure daga wannan sai wannan Hasashen da ta ke yi a cikin aure ashe abin ba haka bane ance ana yin aure dan a huta ita dai har yanzu baza ta dorar da komai ba,to yanzu wane mataki ya kamata ta dauka, tana bukatar me bata shawara amma waye? Ta gaji da yin shawara da zuciyarta. A lokacin kuwa zuciyar ta faɗa mata cewa kawai ki tafi gurin Innar ki, dubi yaje gurin wata kilama wani abin suka aikata ya dawo kuma zai hau wani fushi. kawai ki gama shirin ki kiyi wucewar ki duk abinda zai faru ya faru.
Ta kwantar da yaron ta fita falo zuwa kitchen. Yana zaune akan kujera yana jan carbi sai dai kayan da ta gani a zube a kasa duk an watso su wasu ma sun fashe shine a fushin jiya ya yi wannan aikin baya iya zama bai yi barna ba in ya fusata fushin sa baya sarrafuwa ta daɗi, kamar ta wuce sai wata zuciyar tace Asiya ki gaida shi mana. Dan haka ta dube shi tace ina kwana Yaya? Ya kalle ta ya kuma kalli inda yake zaune ta gane me yake nufi wai ta kusan to shi,amma sai ta kasa kusanto shi tana jin tsoro gashi bai yi magana ba, bare ta gane ina ya saka gabanshi.
Yana cikin fushi ko ya sauka. Ki wuce kawai ai Allah ya gani kin gaishe shi. Zuciyarta ta rada mata. Dan haka sai ta wuce zuwa kicin. Tana kokarin hada karin kumallo yayin da wata zuciya ke faɗa mata cewa ba fa ta kyauta ba, Lalai ta koma ta kusance shi ta gaidashi kamar yadda suka saba.

Ji tayi an rungume ta ta baya, a kunne yake rada mata cewa Baby da gaske tafiya za kiyi ki barni? Kece fa komai nawa kece rayuwata bani da kowa sai ke sai danki. Asiya ta juyo ta rungume shi, " Ba iya son ka kawai nake ba Yaya Ina kaunar ka sosai Yaya dan Allah kar ka kawo ruɗani a zaman mu wallahi bazan jure ba.

Ya sauke ajiyar zuciya ya dago fuskarta hawaye suna sauka akan kumatun ta, Baby Wallahi bazaki taba danasani na aure na ba. Ki kwantar da hankalin ki, cikin satin nan zaku ga Inna ta dauki Babana ta yi masa addu'a cikin farin ciki, in kinje yanzu ba wani bayani kin fini sanin wacece Inna.
Asiya ta sauke ajiyar zuciya miji da mata sai Allah wanda ya shiga zai ji kunya

Asiya ta sauka kuma ta hakura da zuwa gurin Inna saidai ta kara jaddada masa lallai ya sada ta da Inna nan kusa. Ya yi mata alkawarin haka.

Wayar shi ta shiga ruri ya sake ta ya ciro wayar ta kai duba fuskar wayar ko zata ga sunan waye, ta dai ga wasu haruffa ya yi saurin fita a kicin din ya bar falon ma can harabar gidan ya fita tana kallon shi ta window yana kai kawo duk da bata iya jiyo me yake fada ta tabbatar da mace yake wayar domin tana iya hangen hakan a fuskarsa.
Hawaye suka zubo mata a fili tace wannan kuma wace irin masifa ce? Gaskiya ina bukatar mai bani shawara akwai bukatar in sanar da wani damuwata ko zan samu sauki.

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[12/8/2025, 09:11] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt

*Alhamdulillah

Please Login or Register in order to submit comment