Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko ba dade ko ba jima. Haka suka yi sallama kowa yana cike da yakinin shike da gaskiya.

Anty ta tura Adamu Bros gidan wata kawarta wadda suka yanke shawarar hada yaran bayan fahimtar da ta yi cewa Mijin kawar ta ta ya samu kudi harma ya tsaya takardar dan majalisar jiha. Da ta share Hajiya Mairo bata ko daga kiranta bayan mijina ya samu karayar arziki, sai gashi harda kai mata ziyara daga jin labarin abin Duniya ya kara dawo musu. A nan ne tace "Kai najima banzo ba haka Huda ta girma gaskiya baki kyauta ba ko ita ai da kin turo min ta dan yi min kwana biyu anyi hutu Hafsa fa tana nan kinga ai da sun saba. Ta fadi hakane bayan Huda tazo ta gaida ita.

Hajiya Mauro tace Kaji ki da kare kai keda kika watsar da mutane yaushe har zan turo miki ita? Anty tace hummm ni da zaku ba wannan yaron ita wallahi da nayi murna ga hankali masha Allah. Hajiya Mairo tace Da dai kafin ya yi aure ne gaskiya ba zata gidan Mijin wata ba. Adamu ai yaron kirki ne kawai dai bazan kai yarana gidan kishiya bane. Anty ta amshe da fadin "Wace kishiya kike ta fadine Adamu yanzu bashi da mata sun rabu, yarinyar da harni ta zazzaage a gaban sa nan take ya dan kara mata saki uku ya aunata gidan su." Hajiya Mairo tace Ko dai ke ce kika shiga shirgin su shiyasa har ta yi miki rashin kunya. "Haba Hajiya Mairo ashe baki ma san ni ba ko ince kin manta ni. Anty ta cafke maganar, taci gaba da fadin zan turo shi in har ya yi mata shikenan muyi tuwon mu manmu.
Sun shirya cewa yaje a ranar Lahadi Dan haka ta kira Bros ya zo har gida ta kwatanta masa gidan Hajiya Mairo tare da bashi Umarnin lallai ya shiyar a ranar Lahadi ya tafi su hadu da Huda.


Maman Nihal ce ta karfafa masa tare da tilasta masa cewar yaje din domin bashi da wata mafita dole ya yi biyayya ga mahaifiyarsa. Huda tana da kyau dukda ya kula tana da jin kanta sannan kuma ta aminta da shi. Ta gefensa dai kawai yace mata su yi tunani zuwa sati mai zuwa zai dawo in har sun ga ya dace su yi aure. Saidai kafin satin Huda ta fada da Bros ta matsa masa da kira da sako. A gurin Hajiya Mairo Anty ta ke samun labarin zuwa Bros da yadda Huda ta amince da shi.

Anty ta kira Adamu ta yi masa tatas sakamakon baizo ya sanar da ita yadda suka yi da Huda ba. Kuma tace lallai da kanshi take son ya kawo kudin da za akai yaba Dadin su hannu da hannu, wanda za a kai gidan su Huda tace kuma ya bada kudi masu kauri domin tuwo girma dai miyarsa nama
.
Kafin zagayowar satin da yace su yi tunani Anty ta tilasta aka kai kudin auren har aka saka rana wata biyu.


Halifa ji yake kamar karya dawo Nigeria domin ya samu nutsuwa zuciyar shi abu daya zai dawo danshi Asiya. Ya kasa samun ta balle labarin ta. Ya yanke shawarar yana dawowa zaije ya dakkota su koma sabon gidansu Koda Anty bata amince da hakan ba.

Asiya kuwa tana shirin dawowa domin soyayya da kewar mijita sun hana ta kwanciyar hankali. Saiga Inna cike da tashin hankali take sanar da su Abinda Anty ta yi mata. Sannan ta kara da fadin cewa tana zargin cewar Halifa ya san komai tunda har baizo ba ko hakuri ya bata. Asiya ta sha kuka dan takaici gaskiya Halifa ya sani domin tana da Tabbaci Sulaiman ya kira shi ya fada masa ya kamata ya zo ya wanke kansa a gurin Inna. Dan haka ta kudure a ranta cewa duk wanda ya taba mutuncin Innarta zata iya hakura da shi da soyayyarsa. Saidai wani sashe na zuciyata ya ki yarda da cewa Halifa yana da masaniya. Ta dai yanke shawarar ci gaba da zama a Malumfashi har sai ta haifi dan cikin ta.


*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*


[8/28, 10:09] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w


Hajiya Talatu ce ta binciko cewar Asiya tana garin su, ta hanyar yin amfani da wata makociyar su Inna. Kuma ta bata aikin cewar duk lokacin da Asiya ta dawo ga lambar ta nan Dan Allah ta sanar da ita, domin ita tana aiki ne da Hukumar kare hakkin dan Adam sannan taga Videon Asiya yana yawo wanda ta san cewa sharri akai mata.
Makociya ta saki jiki tare da fadin tabbas sharri ne, domin Asiya yarinyar kirki ce zan sanar da Innar su kuma nasan in ta dawo zata sanar da ni.

Haka kuwa makociya ta shiga gidan cike da murnar taimakon su Inna ta sanar da Inna komai. Inna tace to gaskiya dai ni bana ma son sai muje muna wata shara a ko wani maida zance. Allah dai na barwa komai Asiya zata dawo amma bansan rana ba wallahi. Makociya ta yi ta kokarin wayar wa da Inna kai amma Inna tace Allah ya zaba abinda yake mafi alkairi.

Ko dan wannan tashin hankali na yan Biñdiga da suka soma kawo hari makotan kauyen nan Asiya dole ki koma gida tun da can komai ya lafa ko kuma ki zauna a kurna. Domin muma kaura zamu yi daga nan zamu tafi Kankiya Baba Tabawa take fadawa Asiya. Asiya tace "Nima na yi tunanin haka amma ji nake gaba daya an cire min Kano a raina sai dai inje dole." Tabawa tace Hakuri za ki yi saidai in zaki bimu hijirar sai mu tafi. Asiya tace haba dai, babu wani abu zuwa gobe sai in koma Kano.


Makociya ta sanar da Hajiya Talatu bayan dawowar Asiya da kwana biyu dan haka suka soma shirya abinda za su aiwatar.

Sulaiman Asiya ta sa Abba ya kira mata. Suka gaisa a soro. Tace kasan abinda ya sa na kira ka Yaya Sulaiman? Yace 'A' a. Tace Ina son inji ko kunyi magana da Abokin ka ne, bansan zaman da nake yi ba har yanzu gara ya bani takarda ta sannan in san matsayin dan ciki na. Ta kai karshen maganar da kuka.
Sulaiman ya ce Kiyi Hakuri wallahi Halifa nima bai daga wayata ba tunda aka shiga wannan kwamacalar yanzu ma ina zaton ya yi Blocking dina ne dan bana samun shi, kawai, ina son Kiyi hakuri zanje har kasuwar su in same shi zuwa kamar karfe biyu. Duk yadda ake ciki zan sanar da ke zuwa magariba.
Tace to Na gode ina son zuwa Asibiti ne amma sai naji inda muka kwana da zancen shi. Yace ba damuwa.


Kamar yadda Sulaiman ya alkawarta haka ya yi. Yaje saidai yaran shagon sun tabbatar masa da cewa Halifa baya kasar kusan wata daya kenan amma suna sa ran dawowar shi cikin satin nan. Ya bukaci lambar da zai same shi. Suka ce ai ba a samun shi sai dai in shine ya kira.

Haka Sulaiman ya sanar da Asiya lokacin da ya shiga gidan bayan magariba. Yace ki kara hakuri nima sai yanzu na huce dana fahimci ashe baya nan ne, kuma gaskiya ko can dama abotarmu bawai ta yi mugun karfin da duk inda zashi sai ya sanar da mu bane. Yana dai son mu ne gaskiya dan kafin mu nemeshi ya nememu ya yi mana alkairi kinga kenan baya nan Anty ta kawo wa Inna yansanda bana tunanin ya sani. Asiya ta sauke Ajiyar zuciya Sannan tace haka ka ke gani? Yace Gaskiya dai haka ne ma ance ya yi wata baya nan su kuma ai ba ayi wata ba. Sannan a iya sanina da Halifa Koda abinda ya faru da gaske ne ba zai sa a kama Inna ba. Asiya tace to Allah ya sa hakan ne. Sulaiman ya kawo kudi dubu goma ya ba Asiya ga wannan kije Asibitin inhar da wata damuwa ki sanar dani. Asiya zata ki amsa ya yi mata tsawa da cewa baya son haka. Ta amsa ta yi godiya. Inna ma ta yi masa godiya. Asiya ta na kwance tana tunani ko da ba gaskiya bane abinda Sulaiman ya fada ta ji sanyi da farin ciki. Allah ya sa su koma zaman su da mijinta tana sonshi sosai.

Asiya da Sadiyan su Maman Annur suka tafi Asibiti tun a gida suke ta shawara suje Asibitin Unguwa ne ko kuwa suje Murtala. Karshe dai suka tafi wani Asibitin kudi amma ba shi da tsada wata mata da suka hau kekenapep ta basu shawara tace ga kula sosai.Sun isa Asibitin nan suka fada mata cewar dubu ishirin ne zata biya har ta haihu, saidai hoton ciki ko magani su siya zata yi. Tace zata fara ba su dubu goma kafin ta haihu sai ta cika, suka ce babu damuwa.

An tabbatar mata ita da abinda ke cikin nata duk suna lafiya domin bugun zuciyar sa daidai, amma an bata takardar da zata yi hoto domin aga yanayi zaman sa. Sadiya ce ta bata kudin hoton domin anyi mata albashinta ba jimawa. Sunce cikin nata watan shi Hudu da sati uku kuma sun saka mata ranar
haihuwa.


Hajiya Talatu da Anty suka shiga duba katuna sun samu masu suna Asiya guda biyu saidai ba za su gane wacce ce ba saboda Anty bata san sunan Baban Asiya ba. Likitan yace ku duba shekarun mana, inhar baku gane nata shekarun ba sai ku bincika sunan Babanta. Sun samu Asiya daya shekaru Talatin dayar sha takwas, dan haka suka gano yar sha takwas din nan dai ita ce suka zo akan ta.
Hajiya Talatu itace ta sanar da Likitan abinda suke bukata suna son a zubda cikin Asiya suna son ya fadi abinda za su bashi.

Ya dan jima yana Nazari Sannan yace "To da farko dai ina mijinta domin bana son in shiga abinda zai bada matsala. Anty tace bata da miji sun rabu sakamakon kamata da ya yi tirmi da tabar ya da wani, to sai ta zo da wannan cikin tace nasa ne, nasan in anje kotun musulinci shi za a bawa cikin nan, ni kuma gaskiya bazan yarda a bashi ciki da ba nasa ba, shine kawai zamu raba gaddamar.

Likitan yace to ba damuwa miliyan daya zaki bani. Anty ta mike tsaye a gigice haba dai kai kuwa milinyan fa da yawa gaskiya yace to baki duba girman laifin da kike son a aikata wadda ta saba da Dokar likitanci akan wannan aikin naki sai a rufe asibitin tare da kwace lasisin Asibitina, ya dan yi shiru gaskiya nama fasa domin aikin yana da hadari sosai.
Hajiya Talatu tace "Kinji matsalar ki ke baki son fidda kudi kuma kina son ayi miki aikin kudi. " Anty tace ke bazaki gane bane, nifa ba nice me kudin ba Halifa ne me kudin rigar alfamar sa ce ke nuna ni ake min kallon kudi. Hajiya Talatu ta kyakyace da dariyar keta, sannan tace To sai ki ta shi mu tunda ba kudi. Anty ta danyi tsai tana tunanin inda zata samar da wannan kudin kai tsaye.

In kawo miki mai sayen ragowar kayan Lefen nan ku karasar da su har akwatunan ki biya bukatar gabanki. Anty ta danyi shiru tana tunanin Anya kuwa Halifa zai yafe mata ta saida masa kayan masu tsada ta hanyar karyar da su kuma ta yi amfani da kudin gurin zubar masa da ciki dan sa. Ta saki murmushin mugunta tare da fadin hakuri zai yi kawai. Ta kalli Talatu shikenan zanje in nemo rabi aiki yana kammala zan cika maka saura.

Asiya taga Anty da Hajiya Talatu sun biyo ta da gudu tana ta boyewa kuma a cikin Asibitin da taje awo. Ta labe a wani daki suna ta neman ta sai taga wani likita ya shigo yace karki damu zan boye ki biyoni. Bayan ta bishi ya boye ta sai kuma ta hango shi ta windor yana magana da su suna tuntsira dariya. Firgugit ta farka ta tashi zaune tana addu"a, tayi hamdala da ta ga mafarki ne, Asiya tana da girmama mafarki, bata yawan yin sa, amma kuma duk lokacin da zata yi shi sai ya zame mata kamar ishara ko nuni zuwa ga wani abu.
Suna karyawa da safe tace wa Maman Annur nifa ina zargin kamar Anty tana bibiyata domin na yi wani mafarki da ya bani tsoro abin ya shafi cikin jikina domin harda Asibitin da mukaje. ta bata labarin mafarkin. "Karki baiwa mafarki muhimmanci. Da Yawan mafarkai shedan ne ki kyautata zato kiyi addua khairan insha Allah.


Halifa ya sauka a filin jirgin sama na Kano da karfe shidda na safe, mota ya dauka kai tsaye ta kai shi gidan sa, sai da yayi bacci ya huta yunwa ta fito dashi, yaje gidan ci abinci ya ci sannan ya sake daukan mai a daidaita sahu zuwa gida. Kiran Baffan sa ya shigo wayarsa, mamaki ya kama shi tunda ya shigo ya maida layinsa yake jin saukar sakwanni tunda ya duba daya biyu babu na Asiya kawai ya fita sabgar su. Ba wanda ya kira shi dan bai fadawa kowa cewar ya dawo ba.
Ya daga cike da girmamawa suka gaisa Baffa yace ashe ka dawo? Halifa yace na dawo tun sassafiya da yake gidana na wuce ko su Anty ba su san na dawo ba. Baffa yace to idan babu damuwa ina son kazo yanzu. To ganinan Insha Allah. Ya saka me a daidaita suka kama hanyar gidan Baffa. Cike da sake sake.

Bayan sun gama gaisawa Baffa yace Ina son ka fada min abinda ke faruwa a gidanka da bakin ka. Domin na samu labarai marasa dadi daga bakuna daban daban. Nan dai Halifa ya zanyyane wa Baffa iya abinda ya faru na zuwan kwarto gidan sa abinda ya biyo baya na dorawa a waya. Baffa yace to kai ina matsayar ka da yarinyar domin kayi kuskuren rashin rike kwarton kuma kai baka shiga ba dan haka babu wani labari da zaka bada shara a ta karba. Sannan Antyn ka taje da ƴan sanda gidan su matar ka za a kama Uwar yarinyar yan Unguwa suka hana. Kasan da wannan?

Tsaye Halifa ya mike,. Anty ce ta kira wa Inna yansanda to akan me? Baffa yace zauna ka kwantar da hankalin ka. Kamar yadda na fada maka munyi magana da abokina Baban Abokin ka. Gaba daya suna zargin Antynka da yunkurin kashe auren ku, ta hanyar kulla abubuwa. Dan sunce har guba ta bata da sauran zantuka su na mata. Ina son ka kwantar da hankalin ka ka sanar dani kai me ke ranka game da matar ka? Halifa yace gaskiya Baffa bana zargin matata har zuwa yanzu kawai naji haushi tafiyar da ta yi gida ne bayan na hana ta, kuma tafiyar ta ta ce ta bawa masu yada maganar damar bin diddigi da kuma kaga wasu zantuka, da tana gidanta karya ne wani dan jarida ko dan tiktok koma waye ya tinkare ni ko ita tunda dai irin wannan abin ace ya faru da gaske kuma muna tare ai bazai yiwu ba. To da ta tafi ma daga gidan su sai ta kuma tafiya kauyen su duk ba yarda ta. Dan haka sai na barta ta gama yin yadda take so. Amma game da aurena ko cikin ta wannan duk baani da wata damuwa. Sannan ni kaina ina zargin Antyna da wasu abubuwan saidai bana fata zargin ya zama gaskiya shiyasa nake ta gocewa kuma ina ta bata uzri. Domin idan har Anty zata cutar da ni to kuwa Mahaifiya zata cutar da danta.

In Anty bata sona meyasa bata kashe ni tun ina tsumman goyo ba? In Anty tana son kashe ni me yasa ta tsaya ta bani tarbiyya da ilimi bata taba nuna min wani banbancin ba? Wace riba zata samu in ta hana ni zama da mata ta?
Wadannan sune tambayoyina Baffa kuma inka duba zaka ga haka ne. Amma Na fadawa Allah ya kawo min mafita ya bayyana shedanin da ke son hanani zama lafiya da matata da kuma Anty na.

Baffa yace to Allah ya bayyana gaskiya amma ka samu ka dawo da matar ka dakinta ita kuma Antyn taka ka bata hakuri matsalar iyali ba a sako jami an tsaro.
Halifa yace Insha Allah zan tashi in koma can gidana ne kawai maganin fitinar Baffa yace haka ya yi. Halifa ya nufi gida. Anty ta kira mai sayen akwatuna ta zube su a falo suna ta ciniki Hajiya Talatu ma tana son biyu a ciki amma fa Anty tace sai ta zube mata kudi ko kuma idan taga alat sannan zata bada. Halifa ya yi sallama a kofar falo sannan ya shigo kai tsaye....


*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*


*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[9/7, 11:02] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w

Kallo ya bisu da shi fuskarshi cike da alamun tambayoyi Anty ta diririce tamike tana fadin oyoyo Halifa Oyoyo Uban masu gida oyoyo uban masu kudi kinsan fa duk yan gidan su masu kudi ne. Har lokacin idanun shi suna kan akwatunan Anty cike da in ina tace "Am dama wannan ne ya wannan irin akwatunan ka ya kawo za a siya kasan baka nan an saka ranar danka Baban su Nihal shine ka ga ina wayata ma ko ina ya jefa ta, wallahi sai kiranta nake yi bai daga ba. Halifa ya kai kallon shi kan Hajiya Talatu wadda ta ke ta kokarin rufe wasu jajayen kayan bacci wadan da yasiye su a wata tafiya da ya yi Chaina lokacin yana kan hada lefe. Nuna wasu ta kalma da aka tura kasan kujera yace, "Harda wadan can takalaman da kayan baccin can duk zai saida? Ba jira amsa ba ya ci gaba da fadin Ni zuwa anjima zan amshi nawa akwatunan da kayan ciki zan kai su sabon gida." To ai suna ciki ko zaka dauka yanzu? Anty ta fada da sauri tare da share zufar data keto mata a goshi. Ta ci gaba da fadin ka zauna mana bari a kawo maka abinci ka sha hanya. Zata yi hanyar kicin Halifa ya ce " A koshe nake Anty karki manta bayan magriba zan kwashi kayan". Ya Juya ba tare da ya jira amsa ba.

Kai kawo yake yi tunda ya shiga falon sa, ko kaffara ba zai yi ba wadannan kayan sa ne, kwanaki ta fada masa ta taba wani abu a kayan ransa ya baci amma ya nuna mata babu komai. Shine yanzu kuma zata sai da akwatu nan. A fili ya furta Allah ya sa dai ba duka kayan ta salwantar masa ba.
Anty ta kalli Hajiya Talatu tace "Na shiga uku kinga wata masifa to yanzu ina zan samo sauran kayan ni Habiba, ko kuwa dai in kira Malam ya rufe min bakin sa. Hajiya Talatu ta ja tsaki" Dan Allah dubi yadda duk ki ka burkuce kika fita hayyacin ki kamar wani ubanki, dan bai samu kayan ba sai ya dake ki? Anty tace "Baza ki gane irin zuciyar da Halifa yake da ita ba, a haka ma dan na saka Malamai sun min aikin karya zuciyar ta sa, ke da dane ya samu kayan nan wallahi sai ya daga mana hankali a gurin nan ko ya kwashi kayan ya cinna musu wuta."

Hajiya Talatu tace, to hakura zakiyi da wancan aikin kenan na Asibitin? Anty ta kalli mai sayen akwatunan tace Inaga kawai kaje. Yace To zan baki yadda kika ce da farko. Anty tace Kai kuma ana ga koshi kana ga kwanan yunwa, duk fa a gaban ka komai ya faru kuma da Hausa muke magana ba wai da wani yare ba. Me siya akwatuna yace Hajiya in kun canza shawara Dan Allah ku nemeni ta wannan lambar. Hajiya Talatu ta yi karaf tace ina ganin abinda za ayi kawai ka bamu kudi in kurar ta lafa kazo ka kwashi kaya. Anty tace "Tabbas domin na san ganin kayan ne ya sa yace zai dauka domin fa tabbas ya san kayan shi ne ba wai ya yarda da abinda na fada bane. Me Siyan kaya yace ina ce nan gidan ki ne? Anty tace. Ban gane ba, yace" "Ba dai nan ne gidan mijinki ba, ko kuwa zan ba ki kudi ne kawai dan tsoro?
Hajiya Talatu tace gidan ta ne ka bamu miliyan daya daga baya sai muyi magana. Yace ai ba kayan miliyan zan siya ba, akwati catai in bada dari uku nake neman ragi. Hajiya Talatu tace ai zamu baka wasu kayan kalli gidan nan fa, ji kayan da ke falon nan miliyan din banza kawai dai wata bukata ce ta gaggawa. Yabi ko Ina da kallo a zuciyar sa yace zai so ma su ki bashi kayan ko kudinsa domin in har abin ya zama rigima sai ya ci ribar da ta linka abinda zai samu in aka yi sabgar lafiya lafiya. Ya Numfasa
Yace to naji zan bada amma in na bada miliyan daya in kudin za a maido min miliyan da dari biyu da hamsin za a bani ko kuma a bani kayan kudi. Suka ce sun yarda nan take yace sai anyi rubutun yarjejeniya bayan sun gama yace Su bashi account number. Kamar wasa ya saka wa Anty miliyan daya kuma ya tafi.

Halifa bai jima a gidan ba ya dauki motarsa ya kaita gurin wanki yana can ya kira Bros ya sanar da shi ya dawo anan yaake fada masa Maman Nihal ta haihu da namiji. Ya yi masa murna ya kuma tambaye shi batun aure da ya ji Anty tana fada, yace tabbas akwai batun ya sanar da shi komai. Halifa yace Kasan kayan lefen mata ta da Anty tace a jinkirta bata sune na gani sun tasa tare da wannan kawar ta ta suna cinikin su? Bros ya saki salati Sannan yace "Amma ka Karbi kayan ka ko?" Halifa yace Tace ba su bane amma dai na san borin kunya ne da dare zanje in ce ta bani wallahi Bros Anty bata taba bata min rai irin na yau ba, yau ne na yi tunanin dama ace mahaifiyata tana raye domin Uwa ce kawai ta san darajar duk wani abu na danta. na ga iyayen da sune ke hadawa yaran su lefe dan su rufa Asiri. Bros yace "Ina tabbatar maka cewa Anty ko ni din ne hakan zata aikata min dubi yadda ta korar min mata." Halifa yace ta yi haka ne dan tana zargin tun da ka auri maman Nihal kasuwancin ka ya tsaya kaga tana fada ne akan son

Please Login or Register in order to submit comment