Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hadin idan na yi shi yana bala'in saukar mini da ni'ima sosai gefe guda kuma ga ruwan kaninfarin da nake yaiwata sha shiyasa kusan koyaushe a jike nake don ba ni da matsalar bushewa balle matsi da koyaushe idan wata mu'amula za ta kasance sai ya yi kiki-kaka kafin ya samu damar ratsa jikina.

Idan ki ka karanta ba ki biya ni hakkina ba ina bin ki bashi.


Sai wajan takwas da rabi ya kira ni a waya yana gaya mini suna airport saukarsu kenan. Cike da kulawa na ce." To, shikkenan Allah Ya kawo ku gida lafiya."
Ya amsa da kulawa kafin ya datse kiran. Na ajiye wayata ni ma na fita falon shiru Baba na dakinta.
Zamana a falon da kamar minti goma ta fito har yanzu yaron yana goye a bayanta na ce." Wai Baba har sallah ma da yaron nan ki ke yi a goye?"
Tana ko'karin zama kusa da ni take fad'in." Wataran ba, amma dai idan na ga baccinsa ya yi nisa ina sauke shi sai dai fa kafin na idar da sallar ya tashi, ai ya tsani kwanciya sai dai goyo."
Ina dariya na ce." Dama ai duk abinda aka sabawa da yaro shikkenan sai ya tasirantu da shi ki dinga kwantar da shi ko zai saba."
Ta furta." Ai rik'on hannu ga yaro irin wannan shine matsala Hajiya amma goyo daidai kenan, kuma idan dare ya yi sosai na kwantar da shi baccin mu muke sosai sai da asuba yake farkawa.
Aikuwa kamar yana ji sai ya fara motsi ta ce." Af kin ji shi ko? shi fa baya so a goya shi a zauna zai kama tsalla ihu."
Na ce."Sakko shi mu gaisa." Ta kwanto shi daga bayanta tsaf dashi a cikin kayan sanyi masu d'umi yana ta k'amshi ni kaina sheda ce yaron yana samun kulawa wurin Baba Tabawa tamkar yana rayuwa a hannun uwarshi. Na kar'be shi Ina d'an jijjigashi da fad'in." Yau za ka ga babanka yaro."
Ta mike tare da fad'in."Bari na d'auko masa abincinsa." Ta nufi dakinta da saurin gaske.
A kafadata na sanya shi ina d'an jijjigashi maigidan ya shigo tare da Sukairaju a bayanshi. Yana cikin suit ya zanzare sosai ya yi kyau da kayan dukda bai fiye tu'ammuli da su ba amma duk ranar da ya sanya irinsu ni kaina yana burge ni. Farin gilashinsa na ka'ida yana sakaye da idanuwansa na mike tsaye da yaron a kafadata yayin da shi kuma ya juya yana kar'bar yar wasu takardu daga hannun Sukairajun ya ba shi umarnin tafiya.
Baba Tabawa ta fito hannunta ri'ke da fida cike da madara ta washe bakinta tana fad'in." Sannu da zuwa sannu da hanya ranka ya dad'e fatan an dawo lafiya?"
Ya amsa da kulawa. yana fad'in." Lafiya lau Baba mun same ku lafiya? Ya kokari kuma na gode sosai Allah Ya saka da miki da alheri."
Ta d'an sunkuyar da kanta tana fad'in ." Babu komai wallahi, ai babu buk'atar godiya Alhaji."
Bai ce komai ba ya dubi wurin da nake tsaye na saki fuskata sosai Ina fad'in." Barka da zuwa."
"Barkanmu dai Allah Ya taimake ki." Ya fadi hakan cikin sigar tsokana kafin ya fara ko'karin haurawa samansa. Na kar'bi fidar yaron dake hannun Baba Tabawa na bi bayansa.
Na same shi yana ta ko'karin cire safar dake kafafunshi. Ya dago yana kallona kafin ya furta." Amarya."
Ban ce komai ba na zauna gefanshi ya miko mini hannu yana fad'in. Ba ni abokina mu gaisa."
Na mika masa yaron ya kar'ba ya tsira masa ido sosai kafin ya gyad'a kansa yana fad'in." Wallahi Amina Hauwa ba ta da imani ko kad'an."
Na yi shiru Ina kallonsa ya sanya bakinsa a kunnan yaron hagu da dama ya jima a haka kafin ya sake duban fuskarsa ya ce." Amadu shine sunanka, ina ro'kon wanda ya ba ni kai ya rayaka tafarkin addinin Islama, ya raya mini ku bakidaya."
Na amsa da "Amin Ya Allah."
Ya miko mini shi yana fad'in." Ina can hankalina yana nan Amina Amma alhamdulillahi na ji dadin ganinku cikin nutsuwa da kwanciyar hankali lallai Allah Ya azurtani da matar rufin asiri kuma Mar'atussaliha, na godewa Allah na kuma gode mini bisa abinda ki ka yi mini."
Maganganunsa sun sanya mini mutuwar jiki, na dube shi karon farko da na ji tausayinsa ya tsirga mini. Na janye idona daga kansa can kasan zuciyata ina ji tana fad'in cewa ba matausaya ba ne ba fa.
Na danne dai tare da furta." Ya mai jikin, koda yake alamar karfi tana ga mai 'kiba wai ka gan ka kuwa yadda ka wani zanzare wai kuma jinyya ka tafi gaskiya ka fi kama da wanda ya tafi yawon sha'katawa."
A sakarce ya kalleni yana ko'karin cire gilashin idonsa ya ce." Wane sha'katawa bayan babu babbar sha'katawata a kusa da ni, ai ke ce karshen sha'katawa Amina."
Murmushi na yi ina kallonsa. Ya ce "Da gaske nake gaya miki kece sha'katawata, na ga kin yi kama da amarya yau tunda na kalle ki nake ganin kamar sabuwar amarya na yi."
A gajarce na ce." Wani Abu ya canza a jikina ne?"
Ya furta." Kwarai kuwa ga lalle an ranga'da mini, an yi mini kwalliya na yaba sosai sai a fadi nawa ne kudin lallan na biya."
Na furta." Ai ba zaka iya biya ba."
"Me yasa?" Ya fad'a yana ko'karin mi'kewa tsaye.''
Ban ce komai ba ni ma na tashi ina fad'in." Bari na mik'a yaron nan wurin Baba ta goyo shi bacci zai koma."
Ya furta." Ya yi, zan yi wanka yanzu na sauko cin abinci sai mu sake gaisawa ko."
Na ce." To shikkenan sai ka sauko." Hanyar fita na nufa ina d'an jijjigashi yana ta motsin kuka.
A falon ya same ni muka nufi wurin cin abincin tare yana fad'in." Hauwa ta kai k'arata wurin Hajja Amina, don Allah tsakanin ni da ita wanene mai gaskiya."
Na gyara masa kujera ya zauna yana ta kallona.
Ban tanka masa ba wai don ba ni da abin fad'a kawai maganar ce ta ishe ni haka, na ma daina sanya musu baki abinda ya shafe su ne wannan tunda shi har yanzu gani yake yi yafi ta gaskiya.
Duk yadda ya so da mu yi maganar Hauwa akan abinda ta yi ban biye masa ba, ya gaji da takalo maganar ya bari ya shiga wata ina d'an taya shi kafin a kira wayarsa. Momi ce ban san me ta gaya masa ba na ji dai yana fad'in." Subahanallahi, bari gani nan zuwa kada ki sake tashi tunda jiri na dibanki bari na zo yanzu."
Ya kashe wayar yana kallona ni ma shi din nake kallo da 'yar damuwa yake fad'in." Bari na sake dubo mai jiki na dawo Amina." A tak'aice na ce." A ce ina yi mata sannu.
Ya mike ba tare da ya kwashi wayoyinsa ba ya nufi hanyar fita yana fad'in." Yanzu zan dawo in sha Allahu."
Ban ce masa komai ba illa ido da na bi shi da shi har ya fice, ina d'an mamaki jiri kuma? Allah dai ya kawo mata sau'ki shine abinda za a ce.
Dama kusan tare muka ci abincin don haka ko minti biyar ban kara a wurin ba ni ma na tashi tare da diban wayoyinsa da ya bari na
shige d'aki wanka na sake yi na shirya da kayan bacci na zauna jiran sa.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*2K Complete a TALGRAM WHAT'S APP GRUOP 1K VIA 0542382124.... BINTA UMAR GTBANK.*
*V-VIP AREWA PEN*
*07084653262*
*111*
Wayata na d'auka ina dubawa amma hankalina gabad'aya yana wani wuri. A k'alla yanzu da fitarsa kimanin minti talatin kenan, a ganina idan ba wata gagarimar matsalar ba ce ya ci ace ya dawo kuma idan kuma ba acan din zai kwana ba. Zuciyata ta dinga yi mini sake-sake abubuwa da yawa ina dojewa ba ni so na aminta da sashenta ya zamana kuma ba hakan ba ne, uzuri akan ciwo abu ne mai kyau wanda hakan yake da tabbacin kai ma ba ka wuce a jarrabe ka ba. Amma tabbas zai dawo komai dare tunda duka ga wayoyinsa a hannuna.
Sahura na ga ta turo mini voice note na shiga da sauri na kunna ina saurara. Ni sai abin ma ya ba ni dariya wallahi.. Cikin jajantawa kanta da alhini take gaya mini wai Idiris an yi musu rabon gado wata tsohuwar gonar mahaifinsu aka gano a wani k'auye shekarun kusan talatin da biyu da ya sayi wurin ya jefar abinka da mutanan da tunda ya sayi wurin babu wanda ya ta'ba d'auka a cikin manyan yaransa ya nunawa ko 'yan uwansa ba su sani ba tun a wancan lokacin ya kai takardun wani tsohon banki da ya daina aiki a yanzu da yake dukiyar ta halak ce bincike dai har mahukunta suka tabbatar da gonar mahaifinsu ce tunda da sunansa a rubuce a takardun da aka binkito takardun gonar a bankin Yanzu dai tana gaya mini an sayar da gonar miliyar sittin da biyar Idiris ya samu miliyan takwas shine wai ta ga alamar wai yana neman aure.
Na ci dariyata na k'oshi cikin zuciyata ina fad'in." Idan ban da tarangahuma ta da namiji fisabilillahi nawa miliyar takawas take da har za a rakito aure a kanta. Matsalar Malam bahaushe kenan daga zarar ya dan samu fargaba ko yaya ne sai ya ce aure zai kara. A tunanina wannan dama ce da idiris ya samu da zai juya kudin domin dogaro da kansa. Ba a ce masa kada ya yi aure ba amma ya bari ya tsaya sosai da k'afafunsa tunda zahirin gaskiya Sahura tana kokari sosai kusan ita dashi rabi da rabi suke yi kan harkar karatun yaran ma ta fi shi kokari sosai da sosai ni kaina duk wata na kan tura mata abinda ya sawwaka tunda nasan tana da d'awainiya sosai. Wannan dalilin ne fa ya sanya wasu matan cire tausayi da imani akan mazajensu domin wallahi duk namijin da ka nunawa soyayya daga karshe yana samun dama zai yi kokarin jefa ka a rana.
Ganin ban bata amsa ba sai kawai ta kira na dubi agogo goma da ashirin da biyar na dare. Lallai abin yana damunta tunda ta gaza ha'kurin bari gari ya waye
Na daga ina fad'in." Sahura." Ta ce." Shine don wulakanci na turo miki sa'ko kin bade kin saurara kimanin minti goma ina ganinki a online din amma ki gagara ba ni amsa." Muryarta na d'an rawa ta kai k'arshen maganar. Ta d'an ba ni tausayi na danne dariya da nake so na yi na ce." Wallahi na saurara Sahura kaina ne kawai ya daure shiyasa ki ka ji na yi shiru mamaki ne ya ishe ni, in banda abin Idirs nawa miliyan takwas take da zai rakito aure maimakon ya juya kudin su ninku ba mu hana shi ba amma ai sai ya bari mu murmure tukkuna."
Ta furta." Wallahi da ni yake zancen Amina muddin ya ce zai yi aure a irin wannan yanayin sai dai ya sake ni domin ba zan iya zama da butulu ba."
Na ce." Ki saurare ni Sahura, ki bi komai a hankali dan Allah, kin san yanzu idonsa a rufe yake yana ganinsa da 'yan canji zai iya aikata komai. Kada fushi ya sanya ki zo kina nadama daga baya, ki yi hakuri ki bi a sannu ba ni son wata matsala ta faru dake."
Sai kawai ta fashe da kuka tana fad'in." Wallahi Amina ban ta'ba tsammanin Idiris zai mini haka ba, ki duba ki ga fa irin wahalar da nasha da yawon haya da ba don kin ba ni wannan gidan ba da tuni fa muna can zaune a wannan tsukakken gidan da masu shi suke yi mana wulakancin duk lokacin da suka zo kar'bar kudinsu. Kin dai sani ke kanki kin sha cika mana kudi idan lokacin biya ya yi. Yanzu yana ganin bashi da matsalar biyar kudin haya. An aurar da Yusura kuma ina d'aukar albashi tare da samun kayan abinci sa'i da lokaci a wurin aiki shine ya sakar mini wahalar gida ta sauran yaran da ya samu kudinsa bai yi tunanin komai ba sai na aure yanzu don Allah Amina idiris ya yi mini adalci."

Na ce." Bai yi ba wallahi, kuma ya yi butulci, ai shine na ce miki ba mu hana shi ya kara aure ba amma ya bari ya tsaya da k'afafunsa sosai yanzu ba lokacin da zai rakito wata ba ne. Amma kin san yawanci tunaninsu daban ne da namu kuma idan idon su ya rufe akan mace suna aikata komai a yanzu Sahura ba fata nake yi ba don Idiris ya rabu dake ba wani abin ba ne wallahi tunda baya hankalinsa."
Cikin dusashewar murya ta ce." Na gaya miki wallahi duk ranar da ya daura aure da wata to ni kuma na gama zama da shi har abada kuwa."
Bata bari na yi magana ba ta datse waya. Na yi sororo da tawa a hannu Ina mamakin al'amarin. Gaskiya Idiris bai kyauta mana ba wallahi.

Ina binki bashi domin littafin nan na kudi ne.

"Wallahi jiri ne ya d'ebe ta ta fad'i, Allah ma yasa ina d'akin da ban san abinda zai faru ba." Nabila ce take yin wannan maganar yayin da take zaune kusa da 'yar uwarta dake kwance a sambal a gado sai kace matacciya.
Ya ce." Dama ai kamata ya yi ki kasance tare da ita a koyaushe saboda jikin nata babu kwari har yanzu, sai kin kula sosai." Ya kai karshen maganar yana duban dirowar da take gefan gadon da Momin take kwance wata madaidaiciyar jarka ce cike da rubutu da kofin gilas a ajiye.
Ya dubi Nabilan yana fad'in." Ta ci abinci?" Ta ce." Yanzu dai zan kawo mata?" Ta mike da sauri tare da kama hanyar fita.
Ya zauna kusa da ita a hankali ya kira sunanta "Maryam." Ta bude idonta tana ko'karin tashi zaune ya sanya hannu ya dago kafadunta ta tashi." Me yake damunki yanzu?"
"Ba ni jin komai sai jirin fa, daga zarar na mike zan ji hajijiya baya ga haka kuwa sai dai nace alhamdulillahi."
Ya gyad'a kansa cikin kulawa ya furta." Za ki daina ji in sha Allahu daga zarar kin ci abinci kin sha magani yanzu, amma menene a wannan a gefanki."
Ta dubi wurin da yake kallo a hankali ta ce." Sanyawa na yi aka rubuce mini al'kur'ani mai girma. Ya d'an jima yana dubanta kafin ya ce." Hakan yana da kyau, kina ji ko dole fa sai kin rage yawan tunani da damuwa, ba ke kad'ai ce ke d'auke da wannan cutar ba kuna da yawa ko a asibitin ma ai kin ga wad'anda suka fi ki jin jiki, cuta ba mutuwa ba ce za ki samu sau'ki in sha Allahu, ki dinga sanya hakan a ranki."
Sai ta sanya kuka tana fad'in. Anya kuwa, ga ni nake yi mutuwa zan yi wallahi, ba fa na jin dad'in duniyar gabad'aya, ciwon nan shi zai kai ni."
Ya ce." A a, mutane nawa ne suka yi jinyya mai tsanani kuma suka tashi ki daina sanya damuwar hakan a ranki za ki ji sau'ki in sha Allahu."
Ta dinga share hawaye tana girgiza kanta har Nabila ta shigo da plate din abinci madaidaici ya kar'ba ita kuma ta juya ta fita. Kusa da ita ya matsa sosai da kansa ya bata abincin da maganganunta ta sha. Ya sanyata a jikinsa sosai yana rarrashinta cikin tausasawa kamar yadda ake yi wa mai ciwo. Kusan sha d'aya da arba'in sha biyu saura kenan ta yi bacci ya fito Nabila na falon tana kallo ya ce ta shiga su kwana tare. Sallama ya yi mata a gurguje ya fita.
Cikin baccin da ya kwashe ni na ji motsin shigowarsa d'akina. Na bude ido ina kallonsa yana zama gefana kamshin turare biyu ya gauraye hancina k'amshinsa daban ne kuma ya zauna a jikinsa tuntuni duka kayansa k'amshin suke yi yanzu hancina na shako mini wani kamshin na daban.
Na tashi zaune ina d'an dubansa na dubi agogo sha biyu saura minti goma sha biyar ya samu kimanin awa uku babu wani abu a can.
Na ce." Ashe za ka dawo?" Ya gyad'a kansa yana fad'in." E, me zai sanya ni na kwana bayan ga amaryata tana jira ko ba ki yi kewa ta ba?"
Ya fad'a yana d'an matsowa kusa da ni. Sai na ji kawai haushinsa ya kama ni, na tsani munafurci wallahi ko bai fad'a mini ba ya rungume matar nan a jikinsa tunda ga k'amshin turaranta nan a jikinsa.
Na ce." Aikuwa da ka sani ka kwanta a can kawai dubi agogo fa ga gani."
Ya rike hannuna yana murzawa ya ce." Kada mu yi wata hatsaniya dake a wannan daran Amina, ki ba ni hadin kai da k'warin gwiwa don Allah kada kishi ya sanya ki zobe lada da albarkar da nake ta shi miki tunda na dawo kike faranta mini rai, ina ta murna Allah ya amshi addu'ata a kanki, ki ru'banya ladanki kafin gari ya waye."
Baki na zum'bura na ce." Me ka ji na fada yanzu, cewa na yi fa da ka sani ka yi kwanciyarka a can shine ya zama lefi bata fa da lafiya."
Ya girgiza kansa yana fad'in." Ba ni da wani dalili da zan kwana a can, ai ta ji sau'ki kuma kwana na nawa a tare da ita, ai kina da hakki a kaina ni ma ina dashi a kanki kamata ya yi mu raya wannan daran ya zama ma mussaman a gare mu har ya fi na ranar amarcinmu daraja."
Shiru na yi ban ce komai ba ya d'an shafa dokin wuyana yana fad'in." D'azu dana shigo na gan ki rungume da yaron nan a kafadarki sai dana na ro'ki Allah subahanahu-wata'ala da ya ba ni namijin ko'karin samar da makamacinsa a daran yau, za ki ba ni hadin kai ko?"
Ya fad'a hucin numfashinsa na sauka a jikina.
Na kalle shi na ga ya wani saki gabad'aya kansa a langa'be ido daya a kanne. Cikin zuciyata na ce." Yaudara da iya kalamai sai ka ce goggagen d'an bariki.
Ya had'e hannunmu waje daya yana sakin ajiyar zuciya tare da d'an sake shigowa jikina. Ya kamo daya hannun na yana duba lallan yasa bakinsa ya sumbuta yana fad'in." Ko wannan da ki ka yi mini na ji dad'i har na ce Allah Ya shi albarka abinda za a ru'banya miki lada ne. Yanzu za ki cika she ladanki ina so ki nuna mini kwanzonki a wannan daran mai albarka."
Na dube shi duk ya kanainayeni. Na ce." Wane k'wazo zan nuna kuma?"
"Ya dago da sauri yana fad'in." Ki cinye ni a wasan gabad'aya hajiyata."
"Umm" Kawai na iya cewa jikina duka ya shika. A hankali ya mik'a hannunsa ya kashe fitilar gefan gadon da ta d'an haske d'akin. Sai ya yi duhu sosai. Ya rike ni da kyau tare da d'an tura ni na kwanta ya yi mini rumfa shikkenan daga lokacin ni ma na kwarkwace muka zama kamar tuburarrun mahaukata.


Da safe da wayar Hajja ya karya. Ga yanayin yadda yake amsa mata magana ya sanya mini kasala. Suna gamawa ya dube ni yana fad'in." Zan je kano yanzu Amina Amma ina sha Allah zan dawo yau idan kuma wani dalili ya sanya ni kwana zan kira waya na sanar dake in sha Allahu."
Na ce." To shikkenan." Na yi shiru ina kallonsa yana kimtsawa. Na dai kasa daurewa da nace ba zan sake sanya musu baki ba, amma na gaza ha'kuri na ce." Ka ga abinda nake ta guje muku kai da Hauwa ko?"
Ya dube ni yayin da yake sanya links a hannun rigar da take jikinsa ya ce." Ai dole dama za a zo wannan ga'bar na sani, kada ki damu ni babu abinda zai faru sai alheri ni dama ai ban ce ina sonta ba, sune suka dage za kuma ta san ni ta yi wa wannan wulakancin ai."
Na ce." Kenan a ganinka itace mai lefi kafi ta gaskiya, ko da suka dage suna son auranka ka fad'i tsakaninka da Allah da annabi cewa kai ma baka sonta."
Kai tsaye ya furta." Wallahi Samira nake so ba Hauwa ba Amina, ai na gaya miki tuntuni Samira da ita na fara soyayya nasan menene so, Allah Ya k'addara ba mu zauna ba ta rasu. Hauwa kam ba ni yi mata soyayya fitacciya gaskiyar magana"
Na ce." To mai yasa ba zaka maye gurbin soyayyar da kake yi wa Samira zuwa ga 'yar uwarta ba, ka ji tsoron Allah wallahi yanzu da bakinka kake furtawa baka sonta. Amma mai yasa kake rayuwar aure da ita har ku haihu, menene bambacin Samirar da Hauwa tunda duka uwa daya Uba daya suke."
Ya girgiza kansa yana fad'in." Da bambamci Amina, babu dalilin da zai sanya ni maye gurbin son da nake yi wa Samira akan Hauwa, me yasa lokacin da ta rasu ta'ki maye gurbin 'yar uwarta, na fa san komai Amina, don haka ba ki da ruwa akan wannan abinda yake faruwa tsakaninmu. Ba a yi macan da za ta yi mini wannan iskacin ta kwana lafiya ba."
Na ce." To ai zumuncin da yake tsakaninku za ka duba."
Ya furta." Ita ta duba zumuncin ne?"
Na yi shiru ina kallonsa. Ya girgiza kansa kafin ya bud'e ma'adanar da yake ajiye gilasansa ya d'auko daya ya sanya kafin ya kwashi wayoyinsa ya zuba a aljihu. Ya dube ni sai kuma ya kama hanyar zai fita na bi bayansa ina fad'in." Za ka tsaya ka yi breakfast ko?"
Ya ce." A a yanzu wurin Momi zan shiga mu gaisa na wuce kawai zan ci abinci a can gidan Hajja in sha Allahu."
Muka sauko a tare ina fad'in." Shikkenan to don Allah a ce ina gaishe da Hajja da kyau tare da su Kamalu." Ya furta." Za su ji, zan gaya musu sa'konki in sha Allahu sai na dawo." Ya fice da saurin gaske. Na juya na shiga d'akina jikina duk a mace. Ubangiji Allah Ya sa mu ji alheri.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
🌲🌳🌿☘️
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su

Please Login or Register in order to submit comment