Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko ni ina hana shi amsa wayarki ne?"
Ya daga mini hannu yana fad'in." Na ce ya isa haka ko, kada wadda na sake jin ta yi magana."
Ban sake cewa komai ba naja bakina na yi shiru itama ta yi shiru cikin kunyar abinda ta aikata tunda ta fahimci ni dashi duka mun gane ita ta katse mini waya..

Na yun'kura na tashi ina fad'in." Za mu tafi Baba Allah Ya kara sau'ki." Yaran suka tashi gabad'aya Khalil ya d'auki Sultan suka yi gaba k'ananun kuma suka tsaya ni har muka gama sallama da shi, na dube ta babu yabo babu fallasa na ce." Allah Ya ba mu alheri Hauwa."
Ta amsa kanta a kasa domin ta kasa yarda ta dago ta kalle ni.
Biyo bayanmu ya yi wai sai ya rakamu gida muka kuwa jero muna tafiya tare har bakin gate din gidana har da shi muka shiga ciki ya tsaya yana magana da masu gadi. Amma bai biyo mu ciki ba anan dai muka bar shi muka shige ciki ni da yaran gabad'aya.
Washe gari kuwa gari yana yin haske na kira shi bugun farko ya daga na ji muryarsa ta fara bud'ewa ba kamar jiya ba muka gaisa yana gaya mini ya warware tarin ma da yake yi ya sassauta masa sosai.
Ita ya ba ni wai mu gaisa duk a kokarinsa na ganin lallai sai mun samu daidaito ban yi jayayya ba na ce to na ji maganarta a dan sake tana fad'in." Ina kwana ya yaran?"
Na amsa da lafiya lou muke suna can suna shirin makaranta." Ta furta." Allah Ya yi musu albarka."
Na amsa da Amin a tak'aice."
Daga haka ba ta sake cewa komai ba ta bashi wayarsa. Muka dan yi magana kad'an ya kashe tunda a ranar zai dawo gidana.

****
Sati biyu da faruwar hakan. Kawai na ga kiranta na yi mamaki sosai yaushe rabon da mu yi waya ta arziki da Hauwa tun lokacin da ta ajiye Sultan ta tafi garinsu. Haka kawai sai na tsinci kaina cikin fad'uwar gaba domin kuwa zahiri zuciyata ta kasa aminta da ita tun bayan abubuwan da suka shud'e ba ni tunanin zan sake sakin jikina da ita tunda ta gama fito da aninhin abinda yake cikin ranta game da ni.
Na daga cike da tarin zullumi muka gaisa ta yi shiru ba ta ce komai ba na ce." Ina fatan lafiya ko Khalil din za a turo miki ne?." Da yake wasu lukutan takan turo mai yi mata wanki da guga ya kira Khalil ban san sai dalilin da ya sanya take kiransa ba wannan tsakanin d'a da mahaifi ne shima yaron yanzu yana sakewa da ita ba kamar da ba.
Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce." Amina tun ranar da ku ka zo duba maigidan hankalina ya kasa kwanciya ganin Nabila ba ki tunanin akwai wata dangantaka ta soyayya a tsakaninsu kuwa? ko ba ki ji lokacin da yake tambayarta ta dawo ba, hakan na nufin suna da wata ala'ka tunda har yana da masaniyar shige da ficen da take yi kan harkokinta."
Na yi kasa'ke da waya a kunne ina sauraranta har ta kammala maganarta. Zuciyata kwata-kwata bata ta'ba yi mini wannan tunanin ba a ganina shi kuwa me zai yi da Nabila duk nagartattun matan da suke wannan duniya. Kai gaskiya ba na tunanin zai yi soyayya da ita ko ya yi zawarcinta.
Ta ce." Kin yi shiru ba ki ce komai ba, kin ga dacewar ko aure zai kara ya yi da ita. Bayan bada'kalar da ta faru da yayarta."
Na furta." Ki daina wannan maganar don Allah Hauwa, ba ni tunanin haka gaskiya Nabila dai kamar yadda ya gaya mini tana zaune ne domin ta zama garkuwa ga yaran 'yar uwarta, cikinsu babu wanda ya ta'ba kawo korafi a kanta hakan ya nuna suna buk'atar zamanta a tare da su. Maganar kuma mijinki yana zawarcinta ai shi ba mahaukaci ba ne a zahiri da suffa Nabila ba macen da ta kamace shi bace balle ga abubuwan da suka faru a baya. Dole za su gaisa watarana kuma suna da lambar juna hakan kuma ba zai sanya mu ce soyayya suke yi ba."
Ta ce." Jikina ne yake ba ni akwai matsala Amina wallahi ko shi baya sonta to ita tana zawarcinsa ai akace idan kaga kare yana shanshana takalmi d'auka zai yi. Sun gaji asiri fa wallahi kada ta juyar masa da tunani mu rasa gane kansa kamar yadda 'yar uwarta ta yi.''
Na ce." Ki daina tunanin haka don Allah." Abinda na iya ce mata kenan domin ni lokacin ma wani matsanancin ciwon kwankwanso ne ya ri'ke ni.
Na ja kafafu na zauna gefan gado ina jin ta sama-sama a haka muka yi sallama. Tunda na ji ciwon ya tsananta sosai na tabbatar da cewa haihuwa ce. Wannan karon kuma abin ya canza mini kenan ba ni haihuwa tara sai na goma ya kama amma watannan kwanansa goma sha bakwai Allah Ya kawo mini ita.
Na tashi na fito da duk abinda ya kamata mussaman kayan baby ina da su akwati guda manyan set na kayan sanyi da towels Na kira
Dr Sailuba lokacin da sauran k'warina bayan ita ko shi ban gayawa ba balle masu aikin yara kuma duka suna skull minti talatin ta iso lokacin ciwon ya sake k'arfi da kayan aikinta ta taho ta gyara wajen tare da shimfid'a mini wata leda babba ta yi mini shimfid'a a kai na kwanta ta duba ni. Da saura haka na cigaba da fafatawa sai da na k'ara minti talatin da zuwanta tukkuna Allah Ya kawo ta da gaggawa babu jinkiri na farkon
yana fitowa d'an uwansa ya biyo shi jim kad'an mahaifarsu ta biyo baya. Ina kiran sunan Allah itama tana yi bakinta ya k'i rufuwa. Da yake gwanace ta yi komai cikin k'warewa kowanne ta nad'e shi cikin towol fadi take kin iya haihuwa wallahi dubi yara 'kosassu na jima ban ga biyu masu wannan girman ba alhamdulillahi."
Ta shiga toilet dina ta had'a mini ruwan d'umi lokacin na tashi da kaina don ba ni jin komai na canza zani na sanya audiga na kuma tafi da wata toilet din.
Ina fitowa na tarar ta tattare kayan dana haihu a kai babu abinda ya 'baci a d'akin kamar ma ba a yi wata sabga ta jini ba.
Na fito da kayana da kaina na sanya da kanta ta wanke yaran suna ta kusur-kusur kuka wannan idan ya dire sai wannan ya d'auka. Muka fara jin bugu muryar Baba Tabawa tana kiran sunana. Hajiya Amina. Taburni tana fad'in." Haihuwa ta yi wallahi tallahi ga kukan jariri nan.
Na tashi ina murmushi a nutse na je na bud'e musu d'akin suka shigo gabad'aya su uku har da Mairo.
Dr dai sai dariya take yi musu tana aikinta. Baba Tabawa fadi take yi." Ba ku kyauta mana ba amma."
Gabad'aya bakinsu ya'ki rufuwa. Mairo tana dariya take ce wa." Shikkenan biyu sun samu 'yan uwa Allah mun gode maka, Ubangiji Allah Ya yara mana."
Taburni ta d'an zauna gefena tana fad'in." Sannu Ubangiji Allah Ya kara lafiya Hajiya Allah Ya hore miki arziki domin wannan baiwa ce daga wurin Ubangiji Allah Ya inganta lafiya."
Na amsa da Amin suma Amin."
Baba Tabawa ta kwashi kayan da suka 'baci ta fita da su. Ta burni ta bi bayanta da sauri.
Ita kuma Mairo muna tare tana zubar da ruwan wankan yaran tare da had'a wani a haka Dr Sailuba ta shiryasu tsaf cikin kayan sanyi kowane da towel dinsa abin dai gwanin burgewa, ni kam tunda na zauna gefan gado nake tasbihi tare da jaddada godiyata ga Allah ganin yadda ya yi mini wannan baiwa ta haihuwa lafiya ba ni jin komai a jikina ina kuma addu'a a gare shi ya sanya ko da an auna yaran a tabbatar mana da sahihancin lafiyarsu.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*160*
Wannan haihuwa ta yi silar wanke zuk'atan bayin Allah da yawa. Tun daga kan masu gadin gidansa da yaransa na jiki irinsu Sukairaju da masu hidima da kai kawo na gidan muka kasance gabad'aya da su cikin
murna tamkar a daran sallah. Ita dai Dr Sailuba ta samu tukwicin kujarar umara da mota. Masu aikin kuwa Baba Tabawa Mairo Taburni kowacce da alk'awarin zuwa umara ta azimi kuma tunda daf muke da shiga watan. Ya rasa inda zai sanya ransa ya ji dad'i da ya dawo ya same ni da yaran lafiya lau kuma Dr Sailuba tana gaya masa cewa ita dai a yadda take ganin yanayin kuzarin yaran bata tsammanin suna d'auke da wani ciwo mai karya garkuwar jiki mussaman irin wanda muke hasashe amma domin dai a sake tabbatar da lafiyarsu lau ya ce mata za mu je asibitinsu tare da ni dashi wajan Dr Iliyas a bincikesu sosai don mu sake samun nutsuwa da kwanciyar hankali.
Sujudur Shakur ya yi a gabana ya jima kuwa goshinsa a kasa da ya d'ago sai ya kama ni
ya rungume ni tsam-tsam a jikinsa yana ta furta mini kalmar godiya tare da jadadda mini so da k'aunar da bata da abin misali.

Yara suka dawo daga makaranta tsalle suke yi Mama ta haihu abinda suke ta fad'i kenan sun kewayemu da Babansu. Ya ce su je su cire uniform suka 'ki lallai sai an ba su sun d'auka.
Kowacce ta tan'kwashe k'afa ya dinga bin su d'aya bayan d'aya yana dora musu a cinya. Usaina sai dariya take yi tana kallonsa ta ce." Baba ka ga hancin wannan irin nawa ko? dama Mairo ta ce da ni suke kama?''
Hassana kamar wata shashasha ta ce." Ni zan dinga goya d'aya kema ki goya daya ko?"
Minal ta ta'be fuska za ta yi kuka tana ce wa." Baba ni fa? ni ma ina nawa wanda zan goya."
Sai kuka hawaye share-share suka shiga kasa tsare a kumatunta. Ya janyota da saurin gaske ya d'ora saman cinyarsa yana share mata hawaye. Ta rike shi tana kuka tana fad'in." Ina nawa yake Baba." Na kar'bi Usainin daga hannun Hassana na ce." Ga naki nan shine Usaini na bar miki."
Ta fara ko'karin ri'ke shi nasa mata a jikinta ya tare da hannunsa. Ta saki dariya tana ta'ba kumatunsa ya d'an bud'e ido d'aya sai kuma ya rufe tasa dariya tana cewa." Baba ka ga ya bud'e idonsa nan d'insa ya yi ja ko ciwo ya ji." Ta nuna kumatunsa da wani tabo a wurin wanda ya yi jaa sosai ya bambamta da fatarsa. Da wannan alamar Allah Ya bambamta mana su Amma kamanninsu daya shi Usainin ne mai wannan tabon.
Ya ce." Ba ciwo ya ji ba haka Allah ya yi masa baiwa."
Ta ce." Mama kin bar mini shi ko?" Na d'aga kaina. Yarinyar bakinta ya'ki rufuwa tasa yatsanta a cikin hannunsa ya kuwa d'amke ta dinga k'yalkyala dariya tana duban 'yan uwan "kin gani ko ya rike ni, Usaina kin ga ya rike mini hannu."
Su dai dariya kawai suke yi mata. Khalil ya shigo bakinsa har kunne da yake sun riga shi dawowa shi yana cikin yaran da za su yi saukar al'kur'ani sun bambamta musu lokacin tashi mahukunta makarantar.
A nutse na ce." Shigo sosai mana." Ya shigo yana ta washe baki ya ce." Masa'udu ne ya gaya mini Mama ta haihu kuma guda biyu Irina."
Uban ya kama yi masa dariya. Ya matsa kusa da shi yana ta duba fuskar yaran ya kar'bi na hannun Usaina yana cewa." Wannan shine a babban mama." Na ce." Shine na hannun Minal kuma Usaini." Abinda ya yi gabad'aya sai da ya ba mu mamaki har uban ya rungume shi a kirjinsa ya rintse idonsa kimanin minti biyu ya bud'e cike da kwalla ya dinga fad'in." Allah Ya raya ku, Allah Ya sa mu yi zumunci domin Allah mu so junanmu domin Allah, Ubangiji Allah Ya yi wa Babanmu tsayin rai."
Na yi saurin sunkuyar da kaina kasa jin k'walla ta cika mini ido. Yaron nan yana da kaifin basira da tunani. Yasan shekarun girma sun cimma Babansu gasu k'ananu shine yake wannan addu'ar yana so su girma tare dashi
Shi kansa jikinsa sai da ya mutu. Amma da yake namiji ne bai nuna rauninsa ba yaron ma yana addu'a amsa masa yake yi. Sai da ya gama tukkuna ya ce." Za mu je umara bayan mun yi bikin suna ni da kai ko Babana." Ya gyad'a kansa cikin dauriya da ko'karin hana 'kwallar idonsa zuba." Ya furta." Akwai wurin da zan nuna maka jikin d'akin Allah sai ka tsaya sosai ka roke Allah Ubangiji Ya raya ni cikinku na ga girmanku ko?"
Shiru ya yi bai ce komai ba 'kwallar dai da yake ko'karin hana ta zuba ita ta fara d'igowa saman towel din jaririn da yake hannunsa.
Ya ce." Menene haka kuma Baban masu gida, a gaban 'kananka za su yi maka dariya."
Ya d'an share hawayen ya fakaice ya dube ni yana cewa." Mama."
Na amsa Ina kallonsa da wani irin yanayi gabad'aya duk ya dakusar mana da walwalarmu."
Ya cigaba da cewa." Mama ta ji kin haihu ko na je na gaya mata?"
Na ce." A a bata ji ba dama jira nake ku dawo daga makaranta."
Ya tashi tsaye da yaron a hannunsa Usaina na mik'a hannu ya bata ya k'i ya mi'ko mini uana fad'in." Zan je yanzu na gaya mata."
Na kar'be shi a hankali na ce." To hakan ya yi."
Fita ya yi daga d'akin da d'an sauri.
Muka dubi juna ni da shi bai ce komai ba haka zalika ni ma haka. Na dube su a nutse na ce. "Ku je ku cire kayan makaranta a yi alwalar magriba sannan a samu nutsuwa a ci abinci."
Suka tashi a tare har ita Minal din da take saman cinyarsa ya kar'bi yaron dama kusan rabi a hannunsa yake ta dira kasa tana kallona ." Mama za ki goya mini shi idan an jima ko?"
Na gyad'a kaina alamar E ta juya da niyyar fita tana d'an tsalle.
Shiru na wani lokaci kafin na ji sautin numfashinsa." Ko yanzu Ubangiji Allah Ya d'auki raina Amina kin gama biyana hakika alherin da yake tattare da tarayyata dake ba zan k'idaya shi babu abu mafi girma da arziki face wannan. Allah Ya saka da alheri, ba zan boye miki ba na jima ban tsinci kaina cikin yanayi na farinciki kamar wannan rana ba. Sai dai jikina ya yi sanyi ainun da lamarin yaron nan Khalil ko lokacina ya kusa ne zan tafi na bar ku."
Hararsa na yi ina fad'in." Kai ma abinda za ka yi kenan wace irin magana ce wannan don Allah."
Ya dubi fuskar yaron da yake hannunsa a tsanake ya ce." Sai dai shekarun girma suka cimmani Ubangiji Allah Ya azurta ni da 'yan baiwa gasu nan kin san dai ba zan maimaita shekarun da na yi a baya ba ko Annabi Muhammadu s a w ya ce sittuna au saba'una. Yanzu hamsin da takwas nake."
Shiru na yi ban ce masa komai saboda takaici mutuwa dole ce amma a ganina bai kamata a kawota a yanzu da muke cikin annashuwa ba.


Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Wayarsa aka kira ya canza harshe larabci yake yi sosai. Na tsinci wasu daga cikin abinda yake fad'a wasu kuma ban fahimta ba yana dai ta fad'in sunan Sukairaju a maganarsa ya gama ya dube ni yana fadin." Ba'ki na yi daga madina akan wani lamari ina barar addu'a."
Na ce." A cikinta nake kullum Allah Ya yi riko da hannayenka, ni ma na gode sosai Allah Ya saka da alheri."
Ya tsare ni da ido yana fad'in." Me na yi na godiya Amina?"
A takaice na ce." Abubuwa da yawa. " Ya yi shiru bai ce komai yana dai ta kallona ina kici-kicin gyara rigata ya taimaka mini Hasan din ne yake mamulan baki da neman abinci ya d'ora mini shi saman cinyata na tallafe shi sosai nasa masa nonon a baki. Ya kuwa kama yana sha yaran yanzu duka da wayonsu ake haifarsu amma dai duk da haka na d'an taimaka masa wajan ganin ya rike a bakinsa.
Ya ce." Idan Allah Ya kaimu za mu je asibiti tare kamar yadda na fadi da farko domin a duba mini su."
Na ce." Allah Ya kaimu." Ya duba agogon dake d'aure a hannunsa magriba ta yi ya shiga toilet dina ya dauro alwala ya fita zuwa massalaci.
Duka su biyun na shayar. Baba Tabawa ta shigo tana fad'in.'' ko akwai abinda nake buk'ata wanda zan ci. Na ce ta dama mini kunun gyada kawai na fara dumama cikina an jima idan na yanke shawara akan abinda zan ci zan gaya mata.
Ta dubi yaran suna kwance a gado bacci suke yi ta furta." Ko za a goya su ne Hajiya?"
Na yi dariya tare da fad'in." Sultan din fa?"
Itama tana dariya ta ce." Ai ya girma shi ya zama saurayi."
Na ce." Mu bari zuwa gobe tukkuna Babansu zai dawo."
Ta gyadq kai tare da juyawa da sauri ta fita.

Cikin kwanaki biyu da haihuwa dangina da nasa babu wanda bai ji ba. A kuma yau da suke da kwanaki uku a duniya Hajja da yayarsa Hajiya Saratu suka sauka a garin da abin arzikinsu akwati biyu cike da kayan yara kowanne da tasa
Anti Yagana kuma ta ce mini itama dai tana tafe da muka yi waya da ita. Baban Saude kuwa kwana d'aya da haihuwar ya zo bakinsa kamar zai yage ganina kalau yaran ma haka domin ni da shi baban nasu mun sake samun nutsuwa da kwanciyar hankali a lokacin da aka tabbatar mana da ingancin lafiyarsu sai farinkinmu ya sake hauhawa. Kwana ya yi da safe bayan ya karya kummalo ya yi mana sallama ya wuce wajan sana'arsa har yana yi mini alkawarin zuwan iyalinsa tunda mun ce da taron suna ko dai ba su zo gabad'aya ba Anti Saude da Mamansu za su zo idan mun tsayar da ranar da za mu yi bikin sunan ya ce na gaya masa.
Na yi ta murna kuwa ina yi masa godiya kafin ya tafi.
Shud'ewar wannan kwanakin babu Hauwa babu dalilinta. Khalil ya gaya mata ranar dana haihu haka zalika ma mijinta ya gaya mata da bakinsa ya gaya mini ta sani. A yadda na fahimta yana tunanin ta zo tunda ba yini yake yi a gida ba tunda ya yi ba'kin nan bai zauna ba sai da daddare yake shigowa kuma kwana daya da haihuwar ta kar'bi girki. Yau da su Hajja su ka zo ya dawo gidana.
Zuwa yanzu ni ma na fito falo cikinsu amma ta ko'ina jikina a rufe yake kafafuna ma koyaushe suna cikin safa. Tunda na haihu Allah ya hore mini lafiya ba ni jin ciwon irin na gigita bayan haihuwa kuma babu abinda ba na gudanarwa na abinda ya shafe ni. Wannan kad'ai ya isa na godewa Ubangiji.
Rashin zuwan Hauwa ya ta'ba mini rai ainun na kuma yi mamaki ba kad'an ba.
Masu aiki na hidima da yara ta kowace siga kowa k'auna da kulawa yake nuna mini me zan ce da Ubangiji. Salim baya garin yana Legos amma Nusaiba zuwanta biyu Adam ma tunda na haihu yake shigowa haka zalika ma Nabila ta shigo mini kwana daya da haihuwa ta yi mini barka sosai ta fita...
Kwanansu Hajja biyu ranar biyar kenan suka fahimci akwai matsala daga bangaran Hauwa dalili da ni da maigidan da masu yi masa hidima daga waje har zuwa cikin gidan kowa cikin annashuwa yake yi. Hakan ya ta'ba ran Hajja sosai ina d'aki ta same ni, ganin yanayinta ya sanya na nutsu ta zauna a gefena tana duba fuskar Usaini ta ce." Wannan tabon kamar sake rinuwa yake yi a fuskarsa Amina."
Na ce." Ni ma na lura da hakan, amma dai Dr Iliyas ya ce babu matsala in sha Allahu."
Ta sauke ajiyar zuciya a hankali kafin ta dube ni ta ce.'' Menene a tsakaninku da Hauwa, Amina kada ki b'oye mini komai wannan lamarin naku ya fara damuna ya kamata a ce kun girma tunda duka babu yaro a cikinku."
A hankali na furta." Babu komai sai alheri Hajja ranar da zan haihu ma mun yi wa da ita a sanina dai babu wata hatsaniya da ta ratsa tsakaninmu."
Ta yi shiru na d'an wani lokaci kafin ta ce." Ki gaya mini gaskiya ta shigo gidan nan tunda ki ka haihu?"
Na girgiza kaina ina fad'in." Ba ta shigo ba."
Ta furta." Ki ce kuma babu komai Amina haihuwa irin wannan akwai dai wani abu da kuke b'oye mini?'
Na ce." Hajja babu komai wallahi ni dai a nawa b'angaran ban san nata b'angaran ba."
Ta ce." Ke ai na yarda dake Amina kuma na gazgataki domin da da akwai matsala za ki gaya mini, Hauwa ba ta jin maganar kowa, ta raina ni ta raina uwarta kuma ba ta jin shawara."
Na yi shiru ban ce komai ba.
Ta girgiza kanta da damuwa a tare da ita ta tashi ta fita. Sai ta d'an ba ni tausayi domin na gane duk fafutukar da take yi akan gidan d'anta ya gyaru da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa Hauwa ta bari hassada ta yi mata illah a rayuwarta.
Da daddare muka yi waya da anti Yagana cewa suna tafe ita da Ya Falmata ta dawo sati biyu da suka wuce. Na yi musu addu'ar isowa lafiya.
A daran dai da ya dawo wajan goma da wani abin ban jima da yin sallama da su Hajja ba na shiga d'aki domin gasa jikina na kwanta na fito daga toilet na same shi rungume da Hassan yana kafadarsa ya tashi daga bacci yaran suna da tsotso mussaman da daddare Usainin na goye a bayan Taburni yana bacci.
Na sanya kayan bacci a gurguje na kar'be shi domin kuka yake yi sosai na zauna nasa masa nono ya kama. D'akin ya d'auki shiru na wani lokacin kafin ya ce." Gobe ba'kin nan da na yi za su tafi amma jin labarin k'aruwar dana samu suka ce za su zo yi miki barka wasu labarawan Madina ne sharifai ne jinin Annabi Muhammadu S.a.w suka ce wai na tambaye ki za ki ba su yaran?"
Na dube shi cikin rashin gane inda maganarsa ta dosa na basu yara kamar Yaya?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Sun ji irin jikokin Annabi Muhammadu S.a.W ki ke haifa kin san akwai su da kara da karamci da tsantsar ha'din kai
sun ta ya ni murna sosai da abin alheri suka ce a baki."
Dariya na yi na ce." Aikuwa na gode sosai amma dai su yi hakuri ba zan ba su ba."
Yana dariyar shima ya furta." Kai tsaye abinda na gaya musu kenan, sun ce wai ke y'ar baiwa ce ta mussaman kina haihuwar yara masu daraja da albarka."
Murmushi kawai na yi
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa akwai kud'i da na bawa Nabila za ta had'o musu kaya akwati hud'u Hasan biyu Usaini biyu idan kin duba abinda bai yi ba ko ake buk'ata sai ki yi magana ko?"
Na dube shi sosai ina fadin." Akan me za ka bata kudi kace ta had'o mini kaya, me yasa ba ka yi shawara da ni ba ko ni ban san abinda ya dace da su ba?"
Ya ce." Hajiya sassauta mana ita ta nema ba ni naga dacewar bata kudi ta sayowa yarana kaya ba business d'in ta ne da take yi kenan da aje waje a sayo sai a saya a wajenta ko?''
Shiru na yi ban ce komai ba. Ba zan yarda da wannan shishshigi ba duk abinda yake tsakaninsu ba ni buk'atar ji, jiki magayi ne duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan doka. Ba ha'ka mai ya kawo rami, idan ta yi wari sai mu ji ai!
Ya cigaba da cewa." 'Kiyasin kud'in nan da mutanan nan suka ba ki a matsayin alheri na haihuwar yaran nan sun haura miliyan saba'in. Ni kuma na ba ki tukwucin 'karamin kamfanina na soap (sarrafa sabulun wanka) wanda yake mariri."
Da wani irin mamaki na dago ina kallonsa miliyan saba'in!
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Kad'an kenan daga irin alherinsu ba wani abu ba ne, kin cancanci fiye da haka Allah Ya yi miki albarka."
Na ce." Me yasa za ka ba ni kamfani guda?''
Kai tsaye ya furta." Saboda ina shirye-shiryen bud'e wani zuwan da suka yi kenan!''
Na girgiza kaina a hankali na ce." A

Please Login or Register in order to submit comment