Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a yi shi ta fannin da Allah da annabi ba za a iya samun rabon ta hanyar da Allah Ya haramta.
Sosai jikinta ya yi sanyi a wannan karon ba ta yi jayayya da maganata ba kuma da alama ta d'auki shawarar da na ba ta.
Sai daf da magriba muka yi sallama ta tafi. ban yi niyyar girki ba mun dai yi waya da Hamusu tun jiya da rana ya ce mini zai zo mu yi lissafi sai na ce masa ya taho mini da towo daga gidan Gwaggo shiyasa ban shiga kicin ba ko da rana ma Sahura wainar fulawa ta soya mana kayan manja da yaji muka ci cikin marmari.
Sai da na yi sallar isha'i tukkuna na kunna wayata.
A hankali ina duba wayar kimanin minti goma sha biyar ya kira na bari sai da ta katse ya sake kira tukkuna na daga nasa a kunnena na ji ya sauke ajiyar zuciya cikin taushin kalami ya kira sunana ." Na amsa da "Na'am."
Ya furta." Kina lafiya ko ya gajiya?"
Na ce." Kalau nake ina
yara?''
Ya sake sauke ajiyar zuciyar da nake jin saukarta a kunnena kamar yana gabana. Ya ce." Suna lafiya Amina me yasa ki ka kashe wayarki ne?"
A takaice na ce." Na huta gajiya ne shine dalili?"
Ya yi shiru na dan wani lokaci kafin ya ce." To shikkenan sai da safe ko na kira ne domin na ji ya ki ke."
Har zai kashe na ce." Ina son zuwa gidan Gwaggo gobe ko jibi."
Ya furta." Allah Ya tsare."
Na amsa da Amin jikina a d'an mace ganin duk abinda na ce zai amsa babu korafi."
Ya ce." Ba dai wata matsala ko?"
"Umm!" Na ce saboda na ji haushi da bai tambayeni yaushe zan koma ba.
Ya sake fad'in." Sai da safe?"
Na ce." Allah Ya ba mu alheri."
Ya kashe wayar ni ma na kashe tawa jikina gabad'aya ya mutu da abinda ya tsiro da shi wato tunda na ce sai na haihu zan koma ya daina takura mini. Sai na ji hakan bai yi mini dadi ba.
Ko da hamusu ya zo ma a daddafe mu kayi lissafin towon da ya kawo mini kad'an na ci na ajiye ragowa da safe na dumama.
Na kwanta da takaicin abinda yake faruwa. haka na tashi sukuku babu kuzari. Ruwan shayi kawai na sha sai da rana ta yi tukkuna na dumama towon. Zuwan Kamalu da Yusi shi ya d'an warwarar da ni na samu walwala ganinsu cikin tsabta da nutsuwa da kamala. Na dinga godiya ga sarki Allah da ya yi mini wannan tagomashi kowa ya dogara da k'afafunsa sai a lokacin ma nasan da abinda yake faruwa shirye shirye ya gama kammala karshen watan da muke ciki na musulunci yaron zai ta fi jami'ar musulunci ta madina bisa sahalewar uban rik'on nasu shine ya yi masa jagoranci ya kuma shirya masa tafiyar. Ban nunawa yaron cewa ban sani ba muka tafi kan cewa ai na san da tafiyar na kuma yi masa addu'a kwarai da gaske da fatan alheri.
Yini muka yi tare suka ce daga nan gidan Gwaggo suka nufa na ce su gaishe da ita sannan su sanar da ita ina tafe ni ma.
To abinda ya dinga faruwa kenan a tsakaninmu. Zai kira ni a waya kullum mu gaisa da kulawa amma fa ba ya yi mini maganar komawa sbuja zai dai ce mini yara suna kewata amma shi ba zan tantance halin da yake ciki ba tunda yana ko'karin daurewa ya nuna mini bashi da damuwa. Ni kuma takaicin abinda yake yi ya hana ni gaya masa ga ranar da zan dawo amma zahiri hankalina gabad'aya ya koma can da tunanin kada Hauwa ta samu damar yi mini dariya ko wata kafar da mutuncina zai zube.
Sati uku da bikin Usaini ya kawo mini amarya tun safe ya har yamma muna tare Hajara ta zama 'yar gari yarinya ta murmure ta kara kyau kuma ta fara koyar kwalliya irin ta 'yan birni sosai na ji dadin wannan lamari.
Muna tare har dare domin cewa ya yi sai ya taso daga kasuwa tukkuna zai zo ya d'auketa su tafi da muka yi waya ya ce mini yana gidanmu amma gashinan akan hanya.
muna hira a falo ni da ita maigidan ya shigo wannan karon tare da Ade suke. Haka kawai na tsinci kaina cikin faduwar gaba domin ban tsammaci zuwansa ba don bai gaya mini ba duk da da safe mun waya bai ce yana hanya ba.
Daga bakin kofa Ade ya gaishe ni ya juya ya fita da saurin gaske.
Ita kuwa Hajara tun kafin ya shigo cikin falon sosai ta zame daga kan kujera gwiwarta a kasa ta fara gaishe shi. Ya d'an yi jim yana kallonta kafin ya amsa ya dube ni a tsanake ya ce." Amarya ce ko?" Yadda ya fadi maganar ya tabbatar mini da cewa bai ma gama sheda ta sosai ba duk kuwa da cewa a lokacin da ake tirka-tirka auransa da ita da hotonta daya a wayarsa wanda shi ya nunawa Hajja wata'kila ya d'auketa hotone a lokacin domin ya kare mata kallo ya ga ko ta dace da abinda ake buk'ata Allah ne dai masanin dalilin hakan.
Na saki fuskata sosai Ina fad'in." Itace ta zo gaisuwa da ban gajiya."
Ya gyada kansa da d'an murmushi a tare da shi ya ce." Ya yi kyau, ina angon naki yake?"
Ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi kunya take ji."
Na ce." Yanzu aka yi waya da shi yana zuwa su tafi."
Rufe bakina ke da wahala kuwa Usaini ya shigo. Ganinsa ya sanya ya risina yana fad'in." Barka da dare ya kuwa sanya hannu ya dago shi ganin yana ko'karin tsugunawa ya dinga mika masa hannu domin su yi musabaha yaron yana nok'ewa ya'ki kar'bar hannun cikin girmamawa sai sinne kai yake shi kuma yana yi masa dariya tare da tsokanarsa ango na amarya."
Ya rike hannunsa sosai Yana fad'in." Allah Ya sanya alheri ka ji ko, ka kula na so na samu zama da kai kafin d'aurin auran Allah bai nufa ba, yanzu gashi mun had'u na yi maka murna kwarai domin ka yi dace da yarinyar arziki ka kula da amana da kuma hakkinta Ubangiji Allah Ya taya ka riko."
Ya dinga amsawa da Amin ya rabbi na gode ranka ya dad'e Allah ya saka muku da alheri Ubangiji Allah Ya biya bukatu."
Ya amsa da Amin Ya Allah babu buk'atar godiya Malam Usaini ai kai dan'uwana ne?"
Ya fad'a tare da kallona Yana cewa." Ko ba haka ba ne?"
Na gyad'a kaina jikina a d'an sanyaye na ce." Tabbas."
Usaini ya dube ni yana cewa." Anti za mu tafi sai mun yi waya Allah Ya saka da alheri."
Na yun'kura na tashi a hankali itama ta tashi na rika hannunta ina fad'in." Na gode da ziyara Hajara a gaida gida ki kuma kula da shawarwarin da na baki."
Ta ce." In sha Allahu rabbi anti."
Suka juya wajan da yake tsaye yana murmushi shima suka yi masa sallama. Ya fara laluban aljihunsa ya fito da kudi yan dubu sabbi kar da su ba su dai da yawa ba su wuce dubu ashirin ba ya mi'kawa mata yana fad'in." Ga shi a sayi jan baki da hoda." Ta'ki kar'ba da sauri ta bi bayan mijinta sai ni na kar'bi kudin na bi bayansu da sauri.
Koda na dawo cikin falon baya nan ya hau saman don haka sai na bi shi a daddafe na kàrasa hawa na same ya cire rigar jikinsa yana zaune da singeliti da dogon wando agogon hannunsa yake ko'karin cirewa.
Ya zuba mini ido har na kàrasa kusa da shi na zauna ya furta." Hajiya Giwa manya."
'Dan juyar da kaina na yi a gajarce na furta." Ya hanya amma ba ka gaya mini kana tafe ba."
Ya ce." Hakane tafiyar ta same ni bagatatan ai kin san Alhaji sammani ko mutumin nan da ya cutar da ni shekarun baya."
Na ce." Na dai ji labarinsa. Ya ce." Mahaifiyarsa ce ta rasu kin san mutanan Dambatta ne kuma tare suke da Hajja kawaye ne tun lokacin k'uruciya ni da shi kuma abokai ne na unguwa an tashi tare har dai ya zama amintaccena a wancen lokacin kafin ha'inci da son zuciya ya shiga."
Na ce." Allah sarki Ubangiji Allah Ya gafarta mata."
Ya amsa da "Amin a takaice. D'akin ya d'auki shiru na d'an wani lokaci kafin ya dube ni ya ce." Ya yara na ina fatan suna lafiya." Ya fad'a idonsa kan cikina.
Na ce." Suna nan kalau sun ce a gaisheka."
Ya saki fuska kuwa yana cewa." Ina amsawa amma ai gaisuwar iri-iri ce ko?"
Na yi shiru ban ce masa komai ba illa ido dana sanya masa ganin yadda ya kara haske fatar jikinsa ta yi kar har kumari ya yi a cikin wannan satikan da ban gan shi ba idan ba gizo idona yake yi mini ba, ban hangi wata kewa da damuwa a tare da shi ba ban sani ba ko wata ga'ba ya d'auka domin daina nuna mini so da rawar jiki. Jikina duk ya yi sanyi na kasa janye idona daga kansa iina Jin wani bala'in kishi a cikin raina sabon gida sabuwar soyayya tunda nake da shi ban ta'ba zama a gefansa bai ta'ba ni ba hannuwana suna shan mutsika idan ya rike haka zalika ya dinga sumbatar wuyana kenan yana shishshige mini yanzu da muka yi kusan sati biyu bamu ga juna ba babu wani abu na kewa da marari dana hanga a tattare da shi.
Ya furta." Bari watsa ruwa ki ba ni abinci ko?"
A takaice na ce." Ban yi girki ba." Na yi na yi na ha'kura kada na nuna jin haushin abinda yake yi na kasa jurewa. Ya ce." Ba ki yi girki ba kamar Yaya da me ki ka ciyar da ba'kin da ki ka yi?"
Na ce." Na dare ne ban yi ba dama daga gidan Gwaggo Hamusu ke kawo mini towo ba kasafai nake girkin dare ba."
Ya d'an yi jim yana kallona na wani lokaci kafin ya ce." Ko ni zan yi miki girkin ne Hajiyata."
"Idan za ka yi zan ci."
Ya ce." Zan yi kuwa yanzu jira ni na yi wanka."
Ban ce masa uffan ba ya tashi ya nufi toilet na bi shi da kallon takaici da b'acin rai.
Daidai lokacin da ya fito kira ya shiga wayarsa ya zo ya zauna da babban towel a jikinsa ya d'auki wayar sai da ya kalle ni kafin ya d'aga a sake ya amsa sallama.
Sai kuma ya yi shiru na wani lokaci kafin ya ce." To Allah Ya sawwa'ke ki samu bacci sosai ciwon kan zai yi sau'ki maganar masu aikin nan kuma ki ajiyeta yanzu abinda za a yi shine zan yi magana da Hajja anan Dambatta ba za a rasa wadda za ta taimaka miki ba, da safe idan Allah ya kai mu zamu tattaunar maganar sosai, ki kula da kan ki, Allah Ya sawwa'ke."

na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Shiru na d'an wani lokaci yana sauraranta kafin ya sauke ajiyar zuciya ya furta ." To babu damuwa sai na dawo." Daga haka sai ya kashe wayar ya ajiye saman dirowar gefan gado...
Ya sake tashi dai ya je ya d'auko basiline ya zauna da shi a hannunsa yana fad'in." Hauwa ce bata jin dadi tana mura da ciwon kai na dai fi tunanin ciki ta samu itama haka take zargi." Ya fad'i maganar yana d'an kallona.
A takaice na ce." Allah Ya sawwa'ke." Ya amsa daga haka sai d'akin ya d'auki shiru Ina kallonsa ya gama shafa basiline din ya shirya cikin jallabiya mai yankakken hannu ya dube ni yana fad'in." Wane aikin zan yi miki a kicin Hajiya."
Da mamaki nake kallonsa ya gyad'a kansa yana cewa." Menene a ciki manzon rahama ma ya taimakawa iyalinsa ni kuma wanene ko dakan sakwara ki ka ce na yi miki a wannan dare na shirya ke ce fa."
Murmushi na yi a hankali na girgiza kaina tare da cewa." A a ka huta kawai to wai ma ka iya girkin ne?"
Ya furta." K'warai kuwa mu je kicin din naki ki ga yadda ake yi wani abin ma zan koya miki wanda ba ki iya ba."
Na ce." Lallai naga alama amma mu je din indomi kacal za ka dafa mini."
Ya ce." Ai ni ba ni cin indomi Amina da gaske kuma yunwa nake ji na d'auka zan samu abinci."
Jin ya fadi haka sai na gazgata gaskiyarsa babban abinda ya tsana zuwa gidan abinci ya jima yana fad'in tozarta kai ne ga maigidancin da yake sayan abinci a waje.
Na tashi tsaye da kyar ina fad'in." To me za ka ci sai na yi maka yanzu.'' Ya riko hannuna yana cewa." A a mu je dai kicin din tare sai mu yi aikin ko?"
Na gyad'a kaina ban sake cewa komai ba muka sauka kasan tare yana yi mini labarin yara da yadda suke hira kullum da masu aiki su Baba Tabawa. Na gama gane so yake yi mu yi maganar komawata can amma ya'ki yarda ya fito kai tsaye ya fad'a sai kame-kame yake yi.
Muka tsaya akan dafa jallof din taliya na kunna masa gas din ya d'auki tunkuya zai tari ruwa ni kuma na d'ebo kayan miya domin marka'dawa ya ciko tukunyar taf da ruwa ya d'ora kan gas din. Ina kallonsa ya rufe da murfi yana fad'in." Sai me za a yi?"
Na ce." Da wannan kurmemen ruwan za a dafa rabin taliya? Ya ce." Ya yi yawa ne?"
"Sosai kuwa kuma mai ake fara soyayya tukkuna a zuba kayan miya a soya tunda za mu yi amfani da busashen kifi idan mun gyara shi mun wanke sai mu zuba mu d'an soya tare da kayan miya nan sannan mu tsayar da ruwan sanwa."
Ya sauke tukunuwar tare da zubar da ruwan da ya mayar da ita kan gas din ya d'auki mai ya tsiya mai mugun yawa don wanda ya zuba zai yi gwangwani biyu ko fiye da haka."
Na ce." Kenan da mai za mu tsayar da ruwan taliyar ko soyayyiya za mu yi ne Allah Ya taimake ka."
Ya ce." Ana yin soyayyiya ne dama?"
Ina dariya na ce." E, amma ba ita za mu yi yanzu ba kuma mangyad'ar da ka zuba ya yi yawa.
Gabagad'i kuwa ya kai hannunsa zai sauke tukunyar da ta d'auki zafi man yana suyuwa. Ya cire a zabure ya matsa har sai da murfin tukunyar ya fadi kasan k'afafunsa. Ya rikice sosai yana duba yatsunsa.
Dariya kamar cikina zai yi ciwo na kashe gas din na jingina jikin wardrobe Ina kallonsa ina dariya sai zare ido yake yi.
Ya nuna mini yatsun yana fad'in sun toye Amina kin ga yadda suka yi jaaa ashe haka abin yake dama?"
Na ce." To kai wanene ya ce ka kama tukunya haka kawai, kuma ka ce ka iya girki ashe baka iya ba."
Ya ce." Idan hakane bayin Allah nan suna aiki Amina wanene yasan iya adadin yadda suka 'kone garin sauke tukunya."
Na d'an 'bata rai cikin shagwaba na ce." Su kadai kenan, ni ma ai ina yi maka girki."
Ya rikice kuwa ganin yanayin yadda na yi masa magana a sangarce da shagwaba ya matso ni yana cewa." Har dake mana kuna kokari gaskiya Allah Ya saka da alheri."
Na amsa da Amin a takaice tare da d'an zame jikina ina cewa." To zo ka ga yadda ake yi ko don gaba.
Ya kuwa taho ya tsaya a bayana yana murmushi na fara gudanar da aikin cikin nutsuwa yana yaba mini har da addu'a da tukwici sumba a wuya da kumatu a haka na yi masa jallof din taliya da dankali da kuma bushshen kifi ya ce a yi masa da manja ta yi kyau sosai tana k'amshi mai dad'i.
Kusan tare muka ci amma dai shine karfin cin kuma yadda ya zage ya ci da yawa ya tabbatar mini da cewa yunwa ce mai yawa a tare da shi.
Ban zaci zai iya d'auke kansa daga kaina ba a daran salin alin muka kwana bai nemi yin wata mu'amula da ni ba. Sai washe gari da rana gatse-gatse ya fara kame-kame da ya ga na'ki nuna na gane abinda yake nufi ya kamo ni wai na yi masa dabaru ta yadda zai gamsu yana tsoron ya kusance ni a haka na yi nauyi a cewarsa tausayina yake ji.
Ya fad'i hakane kawai don ya kare kansa amma shi kansa ya san babu wata dubara da take kwantar masa da buk'atarsa face sai wannan abin ya faru.
ban ma yi nisa wajan yin dabarun ba ya fice daga hayyacinsa maganar tausayi kuma sai ta kau ya fara ko'karin ganin ya samu hanyar zai mutunta kansa sai da na dinga ankarar da shi halin da nake ciki tukkuna a haka lamarin ya faru kamar wani sabon tuburarran mara hankali......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
*ZA MU KAMMALA A CIKIN SATIN SALLAH IN SHA ALLAHU*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*158*
Haka muka kasance cikin kula da juna mussaman daga b'angaransa wata sabuwar kulawa na dinga samu a wurinsa bini bini sai ya ce tausayina yake ji amma hakan ba ya hana shi da daddare ko kuma dai duk lokacin da lambarin ya bijiro masa ya kwanta da ni, a wannan gefen sai ya manta da tausayi girki kuwa bai sake cewa zai yi ba dalili ya ji babu sugar domin yatsunsa da ya kama tukunya sai da suka ruruce suka ja ruwa. Sai dai duk lokacin da zan shiga kicin zai bi bayana ina aiki yana damuna da runguma da ta'be-ta'be lamarin nasa dai kamar na sabon ango ko kuma wanda ya koyo wani sabon darasi ai soyayya ya iya babu karya kamar sabuwar balaga ba dattijo mai yawan shekaru ba.
Ranar sadakar uku ya ce na shirya mu je ya kai ni gaisuwa. Na shirya kamar yadda ya buk'ata din muka nufi dambatta a mota Ade direbansa ya ja mu.
A gidan rasuwar na samu Hajja tare da jama'a tunda shi daga waje ya tsaya sai daga baya tukkuna ya shigo gidan. Hajja ta dinga nuna ni ga jama'arta wasu sun san fuskata wasu kuma ba su san ni ba dama fadi take itace uwargidan nasa ai Amina sunanta, itace wadda aka dauro auransu a saudiya. Sai na zama abin kallo na dinga jin nauyi da kunya domin na kasa tantance kallon da yawancin jama'ar wajen ke yi mini.
Da la'asar muka fito daga gidan a kafa muka taka zuwa gidan Hajjan tunda babu nisa.
Ta sanya Iyami mai aikinta yi mini towon shinkafa miyar zogale domin dai ko kad'an na kasa cin abincin da aka ajiye mini a gidan rasuwar dafadukan shinkafa ce amma sun yi amfani da wani irin curry ya yi rabad'au dashi 'kamshin babu dad'i.
Wajan biyar iyami ta gama aiki ta kawo mini sannan Hajja ta ce ta zuba mini wani a fulas sai mu tafi dashi na huta girki.
Na kuwa ji dadin hakan sosai. Sai da na yi sallar magriba tukkuna ta fito daga cikin dakinta da turaman atamfofi guda uku manya ta miko mini tana fad'in.'' Kada na manta kar'bi wannan Amina bari na nemo leda."
Ya juya da sauri ta koma d'akin ta bar ni ina juya atamfofin tsala-tsala masu tsada.
Ta dawo da leda viva mai zurfi tana fad'in wannan ai zata d'auke kayan ko?"
Na kar'ba Ina fad'in." Eh za ta isa."
Ta zauna saman kujera tana cewa." A kar'ba da hakuri ban samu zuwa biki ba amma wannan a bawa amarya Hajara idan na sanya rana Yusi zai kai ni gidan na yini in sha Allahu."
Na sa dariya ina fad'in." Kai Hajja an yi abu ya wuce fa don Allah da kin bar atamfofinki ki dinka abinki."
Ta girgiza kanta tana murmushi ta ce." A a dama na yi niyya Amina sai ki sanya Ayuba direbanki ya kai mata ko kuma angonta ya zo ya kar'ba a ce babu yawa kuma ina yi musu fatan alheri."
Na ce." To shikkenan Hajja Allah Ya saka da alheri ya kara girma Ubangiji Allah Ya sa a fi haka, mun gode sosai."
Ta amsa da kulawa tana kallona kafin ta ce." Ya gaya miki Kamalu zai tafi karatu can Madina ko?"
Eh ya gaya mini." Na fadi haka duk da har yanzu bai ce mini komai ba.
Sai ta gyada kanta tana cewa." Ki kara yi wa yaron nan addu'a akwai alamun haske a cikin al'amarinsa in sha Allahu za a amfana dashi."
Na furta." In sha Allahu rabbi Hajja na gode Allah Ya saka da alheri."
Ta yi murmushi ba ta ce komai a daidai lokacin ne kuma ya shigo yana waya ya tsaya tsakiyar falon duk muna kallonsa har sai da ya kammala tukkuna. Ya dube ta yana fad'in." Hauwa ce ta kira waya wai Sultan baya jin dad'i."
Hajja ta ce." Ashsha me yake damunsa?''
Ya gyada kansa da Yar damuwa ya ce." Ciwon ciki abinda dai tace kenan ya kwana biyu bai yi bayan gida ba yana ta kuka uwar rainon nasa ce ta je tana gaya mata halin da yaron yake ciki amma ya sha magani a cewarta."
Hajja ta ce." Wata'kila wani abin ya ci ya dam'ke masa ciki sai an kula da abinda za a dinga ba shi ya ci mussaman abinda ya danganci madara da fulawa."
Ya furta." Sauyi ne kawai tunda yaron ya fara cin abinci bai ta'ba irin wannan ba ko ba haka ba ne?"
Ya fad'a yana kallona na ce." Sosai kuwa kuma Baba Tabawa na kula kwarai da gaske da abincin da zai ci, tana kokari a kansa gaskiya.
Ta ce." To shikkenan Allah Ya sawwa'ke ai tunda ya sha magani da sauki cikin zai saki zuwa dare sai ka kira waya ka tambayi jikin nasa."
Ya ce." Hakan za a yi in sha Allahu, ni ma ai ina tunanin jibi zan koma."
Ta gyad'a kanta tana cewa to babu lefi ai tunda an yi uku sai kowa ya koma bakin aikinsa."
Ya dube ni cikin kulawa yana fad'in." Tashi mu tafi."
Na tashi da bismillah tana fad'in." Sannu ai gwara ki zauna nan din Amina ki haihu ni kaina hankali zai fi kwanciya."
Da sauri ya ce." Ai ba sabuwar haihuwa ba ce Hajja."
Ta ce." In ji wa? au! haihuwa dama akwai sabuwa da tsohuwa ina ce idan ta yi nisa ne ma ake jin jiki, ko makaho ne ya dubi yarinyar nan ya san tana cikin ibada."
Ya yi shiru bai ce komai ba amma gabad'aya jikinsa ya yi sanyi a haka muka yi sallama ta rako ni har farfajiyar gidan lokacin shi tuni ya shige mota.
Ade ya bude mini kusa da shi na zauna da ledar atamfofin Hajara da madaidaicin fulas din towona. Ina zama a gefansa ya kar'bi ledar ya ajiye kasan k'afafunsa saboda kayan sun yi mini yawa a hannu
Ade ya shiga mazauninsa muka d'auki hanya.
Har muka isa gida bai yi magana ba. Ya rage walwala da nishadi ya yi shiru abinsa tabbacin akwai abinda yake damunsa.
Na daure na fara tambayarsa ko ba ya jin dadi ne ya ce dani 'kalau yake gajiya ce kawai.
Ko da na yi masa tayin towon ma kafin mu kwanta ya ce a a shayi kadai zai sha shima cikinsa ya b'aci.
Na kyale shi kawai na zauna na ci towona na koshi na sauka da kayan na dawo na same shi yana waya da Hauwa jikin yaron yake tambayarta ga yanayin fuskarsa amsar da ta ba shi ba mai dadi ba ce.
Raina ya ba ci sosai wai shin ya ma aka yi Hauwa ta san yaron ba shi da lafiya ne abinda ba tare suke ba, ba fa da gaske ba ne karya take yi ta mayar da shi shashasha tana daga masa hankali saboda ta gane lagonsa akan yara yake yau tace wannan gobe tace wancen kwanaki ta bugo waya tace bata da lafiya yau kuma ta kirkiri ciwo ta d'orawa yaro wane irin jahilci ne wannan. Ta gama gane damuwarsa akan yara shiyasa take amfani da wannan dama. Gashi muna cikin farinciki da soyayya da kulawa lallai sai ta rusa hakan ta kira shi ya dawo wajenta shine hankalina zai kwanta.
Na bude baki ina fad'in." Idan ba ka farga da wuri ba wallahi Hauwa daf take da ta mayar da kai sakarai ko ma nace ta mayar da kai tuntuni shashasha take kallonka."
Ya dube ni da b'acin rai yana cewa." Wace irin magana ce wannan

Please Login or Register in order to submit comment