Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaina cikin nishadi da annashuwa suka fara gaishe ni ina amsawa tare da tsokanar Minal yau sai makaranta.
Falon muka fito tare na ce." Mairo ta kira mini Masa'udu. Kamar yadda suka bar gidan Maryam ba ni son abinda zai sake dangantasu da gidan duk kuwa da cewa direban da yake jigila dasu yana nan tare da masu gadin amma ba ni son abinda zai sake kai yaran gidan ina so su fara gina sabuwar rayuwa mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Ya shigo tare da risinawa yana gaishe ni na amsa na ce.'' Daga yau za ka cigaba da kai yara makaranta kafin Babansu ya samar musu da sabon direba."
Ya amsa da "To shikkenan in sha Allahu Hajiya."
Ya tasa kan su gabad'aya har Khalil suka fita suna yi mini bye-bye Mairo ta bi su da jakkunansu da kayan abincinsu.
Na leka d'akinsu Baba Tabawa muka gaisa sosai suna tare da Taburni da alama ta su ta zo daya tunda duk dattijai ne. Sultan na ta bacci cikin net din shi sun shirya shi tsaf.
Har na juya zan fita Baba Tabawa ta ce." Hajiya Amina kina jin mu da Taburni ko wai tafiya gida za ta yi."
Na juyo da sauri ina fad'in." Me yasa Taburni ko an yi miki wani abin ne? ko kuma ba ki jin dadin zama da mu."
Ta girgiza kanta tana fad'in." Ko daya wallahi Hajiya ina so na je na ga yarana da iyalinsu idan hali ya yi zan dawo suna can suna jirana tunda sun san uwar rikon nawa ta rasu wasu daga cikin iyalina ma sun zo gaisuwa."
Na ce." A a gaskiya ba za ki saki aikinki ba Taburni za ki zauna da mu in sha Allahu a madadin marigayya kuma za mu ninka miki albashinki, zuwa ganin gida wannan ba lefi ba ne, amma ina jin dad'in ganinku a tare ga yara sun saba daku."
Kwalla ta cika kwarmin idonta tana fad'in." Shikkenan Hajiya Amina na gode sosai Ubangiji Allah ya saka muku da alheri cikin satin nan zan je na dawo."
Na ce." Zan sanar da maigidan in sha Allahu nasan zai sanya a aiki kuma aje a dauko ki."
Na fita daga d'akin cikin nazari. Idan Taburni ta tafi baba Tabawa ba zata ji dad'i ba sun saba ga yaran ma idan Mairo na wani uzuri wajanta suke zuwa kuma macace mai hankali.
da kaina na shirya masa abinda zai ci farfensun kifin na sake yi masa tunda na ga ya yi masa dadi kwanaki na hada masa da funkaso da tea wanda nasan dole zai bukace shi domin dumama cikinsa.
Ya kuwa ji dad'i sosai kuma ya ci da yawa ya dinga yi mini godiya ina jin dadi a raina ganinsa ya fara nutsuwa har ma yana ta rage ayyukan da ya jima bai yi ba.
To shi din ma da na gaya masa cewa Taburni za ta koma garinsu bai bada goyon baya ba ya ce yara sun saba da ita sosai idan har ba a takura mata ba to na gaya mata ta zauna zai dinga biyanta fiye da yadda tsohuwar uward'akinta take biyanta.
Yinin ranar haka na yi shi babu komai a cikina domin duk abinda na tunkara da zumar kaiwa bakina zan ji zuciyata na tashi abu mai tsami tsami shi na fi sha'awa tun da na fara jin haka kuwa akwai matsala daf nake da yin al'ada idan ba ta zo ba kuwa ciki ne.
Duk yadda na kai ga daurewa kuwa kasawa na yi domin da daddare amai na dinga kyalayawa Allah ya sa a d'akina ne na yi na gama na gyara toilet din na fito na kwanta lamo cikin kasala sallar Isha'i ma a zaune nayi ta saboda yadda jikina ya mace lokaci k'an'kani.
Sai wajan goma da arba'in na dare na iya fitowa falon shiru yaran duk sun shiga sun kwanta. Na nufi saman abin mamaki hawa daya biyu zuwa uku sai da na zauna na huta. A haka na kàrasa hayewa zuwa d'akin nasa.
A bud'e yake tunda dama yana tsammanin shigowata na same shi yana waya da harshen larabaci karo na biyu kenan da na ji shi yana magana da harshen. Ranar da aka d'aura auranmu a makka da kuma yau. Ban jima da zama a gefansa ba ya gama wayar ya dube ni yana fad'in." Hajiya yau mantawa ki ka yi da ni ne?"
A tak'aice na ce." A a gani na yi ka ji sauki ai."
Ya ce." Sai ba ni da lafiya za ki zo wajena har ki d'ora kaina anan." Ya fad'a tare da dora hannunsa saman kirjina.
Murmushi kawai na yi ban ce masa komai ba kaina ne ma yake yi mini ciwo.
Ya ce." Tunda magriba da ki ka kawo mini abinci ki ka sauka ba ki dawo ba ko na yi wani abin ne?"
Ya fad'a cikin rausayar da kai."
Na ce." Babu abinda ka yi kawai na ga kana aiki ne shine na ce bari na dan baka wuri ka kammala."
Kira ya shigo wayarsa ya d'auka na ji yana fad'in." Lafiya ya kike ina Uwani." Daga nan na fahimci Hauwa ce. Sai na juyar da kaina gefe to da yake hands free wayar take na ji tana fad'in." Yau kwana uku Ina neman wayoyinka bata shiga."
A tak'aice ya ce."
"Ba ki da number Amina?" Ya bata amsa da haka.
Ta ce." Itama ba ta shiga."
Da mamaki na kalle shi wayata kullum a kunne take wannan ba gaskiya ba ne ba ta kira ni ba.
Ya ce mata." Ok
Ina fatan lafiya ko?"
"Ba ni da lafiya ne?" Ta fad'a cikin 'yar k'aramar murya."
Babu wani gigita a tare da shi ya ce. Sannu idan kin je asibiti sai ki sanar da ni abinda ya kasance na sayan magani zan sa miki."
Daga haka bai jira jin abinda za ta sake cewa ba ya datse wayarsa ya ajiye.
Ya dube ni muka had'a Ido sai ya kanne mini idonsa yana fad'in." Ina labari?"



Gudun aure paid book ne yar uwa kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Na ce." Kai zan tambaya domin cikin kwanakin nan ka jefa ni cikin rudani"
Ya sauke ajiyar zuciya bai ce komai ba sai ya d'ora kansa saman tudun kirjina. Ni ma da taya 'bera 'bari na tallafe masa kan ina shafa shi. Ai sai na kunna shi ya sake ma'kale ni tare da zura hannuwansa duka biyun ya kewaye 'kuguna. Mun jima haka Ina ta shafa saman kansa a hankali yana ta sauke ajiyar zuciya babu wanda ya sake yin magana a cikinmu. Hauwa ta sake kiran waya a karo na biyu ba tare da ya d'auke kansa daga kirjina ba ya d'auki wayar yasa a kunnansa. Ta fara maganar da karamin sauti ban ji komai ba, ni kuma daman ban so na jin ba na ji yana fad'in." Babu halin hakan."
A tak'aice ya gaya mata haka duk kuwa da cewa doguwar magana ta yi masa ya sake dai kashe mata wayar a karo na biyu na ji shi can kasa yana fadin." Na d'auka mutuwa zan yi a cikin kwanakin nan ban zaci zan sake moruwa ba wallahi saboda tsabar yadda ga'bobin jikina suka mutu."
Na ce." Ni ma na tsorata gaskiya amma dai duk da haka yana da kyau likitanka ya dubaka sosai baka da lafiya."
Ya ce." Hakan za a yi in sha Allahu." Ya d'auke yana gyara zamansa na ce.'' Kasan yaran nan sun koma makaranta yau ko?''
Ya ce." K'warai kuwa mun yi magana da Masa'udu d'azu dana fita sallar la'asar zai maye gurbin Dauda direbansu na can gidan Maryam."
Na ce." Hakan ya fi."
A daran ranar ma sai da ya yi auratayya da ni, na dinga daurewa domin akwai buk'atar hutu da samun bacci a tare da ni ga jikin babu kuzari. Sai da ya gane kuwa ya d'an saurara mini da asuba da yawo daga massalaci bai sake nema na ba.
Nima tunda na koma bacci bayan sallar asubahin ban tashi ba sai wajan sha biyu da kwata sai da na yi wanka tsaf na kintsa jikina sannan na fito yaran suna makaranta a falon na samu Mairo da Nusaiba suna hira Taburni da Baba Tabawa suna kicin suna aiki.
Cike da girmamawa duka suka yi mini barka da fitowa na nemi wuri na zauna cikina na hautsinawa yunwa da tashin zuciya bakina salam. Ina fad'in." Yaushe ki ka zo ne?"
Da murmushi a fuskarta take fad'in." Wajan sha daya da rabi Baba ya kira ni yana sama amma bai sauko ba mun dai yi magana a waya ya ce mu jira shi."
Na ce." Allah sarki Ina yaran na gan ki ke kadai."
Ta ce." Suna makaranta anti."
Salim da Adam suka shigo cikin kaya iri daya gabad'aya yaran daga lokacin rasuwar Mamansu zuwa yanzu sun ladabtu sosai ba kamar Salim da yadda yake risina mini ke ba ni mamaki yaron da ya d'auki mummunan gaba da ni. Itama Nusaiban har yanzu bata iya had'a Ido da ni. Adam kuwa dama d'an d'akina ne tunda suna tare da Yusi.
Muka gaisa cikin kulawa na tashi ina fad'in." Bari ina zuwa."
saman na nufa domin sake sanar dashi zuwan yaran. Sai na same shi shi da Sukairaju suna ta kicin-kicin bud'e wannan dirowa da aka shigo da ita kwanakin da suka shige.
Da kyar suka samu nasarar bud'eta da dabaru da kuma wasu mukkulai da na gansu a hannun Sukairaju...
Na ce." Nusaiba da 'yan uwanta sun zo wajenka."
Bai ce mini komai ba sai da Sukairaju ya fita tukkuna ya fura." E, wannan ma'ajiyar ta Mamansu zan bud'e a gabansu.
Ya d'auki wayarsa ya kira Nusaiban ya ce mata su haho saman.
Muna zaune suka shigo gabad'aya suka gaishe shi ya amsa cikin kulawa yana tambayarta yara da yanayin jikinta. Ta nuna masa wuyan nata tana fad'in." Wurin ya warke alhamdulillahi.
Ya ce." To alhamdulillahi kamar yadda na gaya muku cewa idan na samu nutsuwa sosai zan bude wannan ma'ajiyar domin ni daku muga abinda yake ciki ma sha Allah cikin ikon Allah yanzu Sukairaju ya samu nasarar bud'eta don haka ku ba ni hankalinku gabad'aya.
Ya sanya hannu a nutse zai bud'e
na fara ko'karin tashi domin ba su waje ya ce na zauna. Ba don raina ya so ba na zauna din

Tana da d'an zurfi amma ni da nake zaune kusa da shi na gama ganin duk abinda yake ciki. Da saurin gaske na d'auke kaina gabana na wani irin fad'uwa.
Daga b'angaransa ban hangi wani razani ba da hannunsa ma ya shiga fito da abubuwan da suke ciki. Farko dalar amurka ce ta fi bandur ashirin ya gama fito da su sannan ya kwaso tarin akwatinan gold's dinta kusan set biyar manya ba k'ananu ba bayan zobuna na tsayun hannu dake cikin akwatinansu.
Ya debo wasu takardu ya mi'kawa Salim yana fad'in " Duba nan ka ga menene. Ya kar'ba da sauri ya fara dubawa. Abubuwa biyu da suka yi saura cikin dirowar ya d'auko
Mutumin-mutumi ne mai d'auke da suffarsa da suffarta tsirara kammaninsa sak haka zalika itama kammaninta sak an had'e su waje daya an matse sosai da farin likkafani da jan zare aka nannad'e sannan 'kasa da sama duk an kulle da ko'ina da kwa'do. (Key)
Sai wata kwalba doguwa mai kama da ta lemo cike da turare mai maiko da k'ananun layu a ciki kimanin takwas kowacce soke da allura.
Ya dubi Nusaiba da ta gama kidimewa ganin abinda ya biyo bayan dukiyarsu da Mamansu ta boye musu ya nuna mata yana fad'in." Wannan shine abinda ya rage cikin wannan dirowa Nusaiba."
Sai ta rushe da kuka tana 'kunshe bakinta da hannu hawaye suka fara kasa tsere a kumatunta.
Adam kuwa sunkuyar da kansa kasa ya yi yana cike da damuwa mai yawa.
Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un kawai take fad'in tana kuka. Shi kuma Salim sakato kawai ya yi da takardu a hannu ya tsirawa abubuwan ido yana kallo cikin jin nauyi da kunya.
Ganin yadda duk suka ki'dime ya sanya ya fara rarrashinsu yana fad'in su nutsu Nusaiba dai fadi take yi don Allah Baba ka rufa mana asiri ka ce ka yafe mata ko zata samu rahama. Anti Amina kuma don Allah ku yafe mata ban sani ba ko ta yi muku wani abin na cutarwa ni dai wallahi ban san Momi tana bin wannan hanyar ba domin kullum idan mun zauna da ita cikin yi mana fad'a da nasiha take bantaba sanin abinda take yi ba."
Ya ce." Babu komai ku nutsu kowane dan Adam yana tare da jarrabawarsa a duniya mai kyau ko mara kyau ni daku duka ba mu san abinda yake lullube ba domin alherinta muka sani shi kuma muka dinga fad'a bayan mutuwarta. Ba ni da masaniyar cewa ta tuba kafin Allah Ya d'auki rayuwarta tunda zuciyarta a kirjinta take kuma ba a bud'e mini na gani ba. Na yafe mata Ina kuma roka mata sasaauci daga mahallicinta. Wannan abin da kuka ga ni zai zama sirri in sha Allahu, abinda nake so daku gabad'aya shine ku samu nutsuwa kada cikinku wani ya sanya damuwa a ransa. Ina nan har yanzu a madadin mahaifinku kamar yadda ya ba ni amanarku in sha Allah......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *Paid book ne 2k complete on telegram WhatsApp Gruop 1k 0542382124.... Binta Umar gtbank*
*07084653262*
Kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba. Mu kiyaye mu kula da hakkin junanmu.
Kukan da Nusaiba take yi shi ya fara ta'ba mini zuciya na ji hawaye ya cika kwarmin mini idona. A hankali na janye idona daga kanta gabana na fad'uwa cikin raina ina ta kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Yadda yaran nan suka ki'dime ganin abinda Mamansu ta mutu ta bari na sa'bawa Allah shine ya tabbatar mini da cewa duk zargin da ake yi mata na cewa mushirikiya ce ba su gazgata ba sai yanzu da mutuwa ta yi mata tonan silili. Babu kama ko d'aya a zahirance da kuma mu'amularta domin ni kaina ban ta'ba gazgata maganar dake yawo a kanta ba saboda ban ga ni da idona ba a wasu lukutan dai idan abin ya yi tsanani nakan ji a raina anya babu k'amshin gaskiya akan abinda ake fadi akanta. Tun farkon neman auranta Sahura ta gaya mini har nake kwa'barta kan tabbatar da abinda baka da sheda a kansa. Na sanya hannu na d'an share guntun hawayen da ya sauka saman kumatuna sun gama karya mini zuciya yaran yayin da tausayinsu ya zauna a zuciyata me ya fi wannan takaici ace ana binciken sirrin uwarka bayan ta rasu a gano wani abu na takaici wanda ta aikata.
Ban ankara ba kawai na ganta a kusa dani gwiwa a kasa ta kamo hannuna tana fad'in." Anti Amina don Allah ku rufa mana asiri don Allah anti Amina."
Na ri'ke hannunta har na ji yana karkarwa na gane akan abinda take yi wa kuka da tashin hankali kada maganar nan ta fita mutane su gazgata zarginsu.
Sosai na ri'ke ta ina fad'in." Ki kwantar da hankalinki Nusaiba, yadda Ubangijin da ya hallice ta ya rufa mata asiri a lokacin da take raye ya amince da jama'a su ambaci alherinta da kyakykyawan fata har ta rasu to ban ga dalilin da zai sanya don ganin wani sirrinta da ya kasance tsakaninta da Allah ya sanya ni fad'i a gari ba. Na yi miki alkawari kan cewa ni dai babu wanda zai ji haka daga b'angarena, muna ro'kon Allah Ya yafe mata, mu kuma rayuwarmu ta yi kyau a duniya da lahira ."
Ta dinga godiya cikin rawar murya da tashin hankali.
Na ji maganar Salim yana fad'in." Wannan takardun gidan da ta saya ne a kano da filaye uku sai na shagunanta biyu dai na san haya ta kar'ba amma watannin baya kafin ta kwanta ciwo ta ce mini sun gama magana tana so ta biya kudin duka su zama mallakinta."
Ya ce." To tunda ka ga baka ga shedar mallaka ba a cikin wannan takardun da suke hannunka wata'kila ba ta biya su ba, amma dai ka bincika mana wanda suka bata hayar wajan mu ji daga gare su kafin nan sai a had'a kan komai a zauna domin sauke mata nauyi."
Ya amsa a sanyaye yana had'a kan takardun ya mik'a masa ya kar'ba ya mayar cikin dirowar da kudin da sarkokin. Sauran biyun da suka zama na karshen fitowa kama bai mayar da su ba. Tsabar fargaba da tashin hankali a duk lokacin da na dubi mutum-mutimin da ya sha d'auri tamau sai gabana ya fad'i lallai bokan da ya sassa'ka suffofinsu ba 'karamin hatsabibi ba ne. Fuskar Baba sak da yanayin jikin itama suffarta sak rai ne kawai babu a tare da su amma an had'e su waje daya an nannad'e da likkafani da jan zare sai da na k'ura ido ma tukkuna na hangi da wasu 'yan mici-micin layu sun saje da jan zaren ne shiyasa ban gansu ba ga wasu manyan mukullai an had'a an kulle.
Ina can cikin tunani na ji maganarta tana fad'in." Anti mun tafi."
Da sauri na daga kaina ina fad'in." Ki gaishe mini da yaran Nusaiba."
Ta amsa da in sha Allahu kafin su fita da sanyin jiki.
D'akin ya kasance shiru bayan fitarsa.
Ya juyo yana kallona muka zubawa juna ido na dan wani lokaci. Ji na yi zuciyata ta tsinke haka kawai sai na ji ina tausayinsa wace irin masifa ce wannan ni Amina matar nan ashe d'aure mutumin nan ta yi sai ta yi aikin akan ga'ba dama aka ce asiri yana tasiri sosai mussaman idan ya tarar da hali.
Ya d'auki abin zai kwance da sauri na ce." Ka ajiye kada ka ta'ba"
Ya kuwa ajiye da sauri a tsorace yana kallona.
Na ji hawaye sun zubo mini wannan d'aurin ba k'arami ba ne tunda har ta yi masa wannan boyon ina jin tsoron duk ranar da aka warware d'aurin ya fadi ya mutu ko kuma ya kwanta jinyyya mai tsanani mafiakasari irin wannan mugun aikin wad'anda suka yi sune suke da makarinsa.
Kuka kawai na dinga yi hankalina ya yi bala'in tashi ainun muna cikin masifa ni da yara Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Ya zo ya rirrike ni hankalinsa a tashe yana fad'in." Menene abin kuka Amina na amince Maryam ta cutar da ni ta mini illah a rayuwata amma godiyar da nake yi ga Allah yadda ya zaunar mini dake ba ki bar ni ba. Har kullum idan na daga kaina na dube ki sai na ce alhamdulillahi a zuciyata na kuma yi alfahari da kasantuwarki matsayin matata abokiyar rayuwata. Na gode Amina, Na gode kin so ni kin zauna da ni a lokacin da mata suka guje ni, kin yi mini biyayya bisa abinda ranki ba ya so, kin daraja mahaifiyata kin kyautata mata a yau ina gaya miki bayan mahaifiyata ke ce ta biyu a cikin matan da nake alfahari da su, ina so mu kasance tare anan gidan duniya da kuma na lahira."
Kuka na ya sake tsananta jin irin zantukan da suke fitowa daga bakinsa. Gabana ya cigaba da bugawa tsigar jikina na tashi na sanya duka hannuwana biyu na matse shi sosai a jikina ina fad'in." Rayuwarmu da ni da yara za ta shiga garari idan babu kai a cikinta Maryam ta illata mu muddin warware wannan d'aurin da yake tsakaninku ya haddasa masa maka mummunan ciwo. Ko ba ka gaya mini ba kwanciya ciwon da ka yi a kwanakin baya yana da ala'ka da irin ayyukan da ta yi a kanka a jikina na ji hakan mutuwarta abubuwa suka fara lalacewa.
Ya ki'dime sosai yana d'an jijjigani da rawar murya yake fad'in." Ba abinda zai faru, na yarda Maryam ta yi mini illah Amina amma bata samu nasarar kai ni k'asa ba, ga ni ina raye tare dake ta jefe ni sosai ta ko'ina ta dabaibayi ni da d'aurin baki domin kada na hangi lefinta amma ni jin dadina da bata nemi hanyar da zata illata mini ke ba Amina kamar yadda ta ci laya akan Hauwa Allah Ya d'auki ranta kudirinta bai cika ba. Ba ki da hakkinmu da ni da ita shiyasa bata ma yi tunanin cutar da ke ba. Tsafi gaskiyar mai shi na gazgata hakan ne a kwanakin nan da suka wuce da muka je da wani malaminta ya warware ayyukan da ta sanya shi ya yi aikana wannan shine dalilin da ya sanya ni wannan kwanciyar na dinga bacci da ciwon jiki. Ban zalinceta ba amma ni ta zalince ni ta hanyar d'addaureni ta ko'ina babu gaira babu dalili tare da haddasa mini rikici da husuma ta karkashin kasa a gidana. Tunda har ki ka ga na tashi yanzu bayan warware wancen makarun da ta yi mini to warware wannan ma ba zai zama cutarwa a gare ni ba in sha Allahu."
Na dago ina dubansa tare da cewa." Da bakinka fa ka ce tare ku ka je da malamin da ya yi aikin ya warware da hannunsa. To shi wannan din kana da makarin warware shi, ka dubi abubuwan da suke jikinku kai da ita kuma likkafani ne ya yi muku sansani da kai da ita. Wata'kila ta yi aikin ne akan idan ta riga ka mutuwa duk ranar da aka kwance d'aurin da yake tsakaninku kaima ka bi bayanta, idan hakan ba ta samu ka kwanta ciwo mai tsananin gaske."
Ya yi shiru yana kallona a d'an tsorace! sai ya sake matseni gam a kirjinsa yana kiran sunan Allah tare da sake duban idan gunkin mutumin-mutumin na su yake ajiye.
Muka kasance cikin shiru da zullumi jikinsa ya yi bala'in mutuwa ya yi mini wata matsa tsam kamar yana jin tsoron a k'wace ni.
Minti goma a haka muka wanzu babu magana ya cika ni tare da zuwa ya d'auko wayarsa. Ya zauna yana fad'in." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Kimanin minti biyar yana waya da Malam Rabi'u kafin su yi sallama ya dube ni yana fad'in." Akwai gaskiya a cikin maganarki Amina. Ba ni da masaniyar akan malamin da ya yi wannan aikin don haka dole zuwa kano ya kama ni can kauyen Bunkure wajan Malam D'aha abokin mahaifina ne in sha Allahu ina da yakinin shi zai warware mini wannan d'aurin kuma babu abinda zai same ni da izinin Allah."
Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." To ita fa waccan kwalbar mai layu a ciki."
Ya ce." Har da ita za mu je gaban Malam din duk abinda yake da akwai Allah zai bayyana shi."

A daran ranar ban iya rintsawa ba har ya ma fi ni tawakkali a wannan ga'bar hawayen idona kuwa ya kasa tsayuwa domin sai nake ganin kwance wannan tsatstsauran d'aurin da yake tsakaninsu zai kassara masa rayuwa idan bai fadi ya mutu ba to ya yi mutuwar tsaye tunda bata raye a duniya to kowace mace ta yi asara. Abinda na ke ji a raina kenan shine kuma ya hana ni sukuni don daga zarar na tuna irin wahalar da ya sha kwanakin da suka wuce sai hankalina ya sake tashi zuciyata tana ta raya mini cewa wannan likkafanin da yake d'aure a jikinsu ita dashi akwai alamar tambaya a kansa tunda duk inda aka ce an yi wa mutum asiri da likkafani ko an binne a makabarta abu ne mai munin gaske. Tsakanin d'azu da safe da yanzu da muke cikin talatanin dare dana juya na kalle shi zan ji wani bala'in tsoro da tausayi da kaunarsa a cikin zuciyata idan ya mutu ni da yara mun shiga masifa wace rayuwa ce za ta biyo bayan faruwar hakan, me zai faru? Maryam ta so zuciyarta ta cuce ni ta cutar mana da yaranmu.
Na jima a sujjada ina kuka ina ro'kon Allah har sheshshekar kukana ya tashe shi ya kira sunana na juya na dube shi yana fad'in." Me yasa wai kike wannan kukan ne? Na gaya miki ba ni so ni shine kadai yafi damuna ki zo ki kwanta babu abinda zai same ni."
Kasa tashi na yi daga saman daddumar na cigaba da jan hanci ina share hawayen da nake ta ko'karin tsayar da shi amma ya'ki yatsuwa.
Ya sauko ya zo ya zauna gabana har da tankwashe kafa. Na kalleshi baccinsa ma yake yi shi kamar abin bai dame shi ba.
Ya ri'ko hannayena cikin kulawa yana fad'in." Ban san haka kike sona da yawa ba Amina, Maryam ashe

Please Login or Register in order to submit comment