Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi mini ta kuma farkar da ni. Ba zai zama abin damuwa wurin Mama ba in haihu ta ki yi mini abin da ya kamata, har wanda yan'uwa suka hada ta hada ta rike.
To ina mafita? Na tambayi kaina, "Allah ka ba ni mafita."
Na furta a hankali.



Da gari ya waye ranar zan fita girki, tun da na fito da safe Fauza ke ta kai da kawo tana kalkale falonta ga kamshi na musamman ta sanya, girki ma tun a sannan ta fara da na tabbatar shi ma na musamman za ta yi. Kirjina ya cushe ina lissafin da garin mu nake in tafi gidanmu ko gidan yan'uwa.
Hamid da ya shirya fita da wuri na tambaye shi zuwa gidan Innar su Aminu, ya ce A'a bai son yawan fita.
Komai ban ce ba ballantana ta kai ni ga magiyar ya bar ni, na gyara na kwanta.

A dakin na wuni ko abinci ban fita na nema ba. Na idar da sallar la'asar ina zaune kan sallayar wayata ta dauki kara na juya inda take sai na dauko ta, sunan Aminu ke yawo saman Screen din na daga bakina dauke da sallama ya ce "Aunty ina waje na zo gaishe ki."
Na dan yi murmushi "An shigo garin kenan? Ina zuwa."
Na yunkura sai na mayar da mayafin doguwar rigar da ke jikina na taka na fita dakin.

Kamshin girkin Fauza da kamshin turaren falon ya hadu ya ba da kamshi na musamman, ba kowa falon na koma dakina na ciro plastic chair da na saya guda biyu ko da zan yi bakon da dole sai na zaunar da shi a falon sai na sanya mishi.
Na fita har zuwa zauren gidan inda na tsinkaye shi, da fara'a nake yi masa sannu da zuwa tare da yi masa jagora muka shiga ciki, a saman daya daga cikin kujerun na yi masa tayin zama, na wuce kitchen na kawo masa ruwa, sannan na zauna a daya kujerar muna gaisawa na ce "Ina amarya? Ba ka kawo mani ita ba, sai wani za shi daga gidan Inna, in bi shi na gano ta."
Ya yi murmushi "Zan ma kawo miki ita Aunty."
Daidai nan Fauza ta fito daga dakinta ta dube mu, muka dube ta, ganin ta yi hanyar kitchen ya ce mata "Ina wuni?
Lafiya kawai ta ce ba tare da ta waiwayo ba.
Hira muka yi da ba ta wuce ta mintuna biyar ba ya mike bayan ya ajiye mini Envelope a kujerar da ya tashi.
Na bi shi ina mai godiya a gare shi, sai da na dan taka masa sai na juyo na koma dakina na bude envelope din rapper guda ce ta yan dari biyar"Dubu hamsin." Na fadi wani tunani na shiga kwanya ta.
Na janyo wayata na yi ma Hajara flashing don ba kudi a tawa wayar. Ba bata lokaci ta biyo tana mini tsiyar na shige Karfi na yi shiru.
Na tambaye ta yaranta da mai gidanta da can wurin Inna ta kuyanbana sai da muka tattauna har kan Haj Iya da ciwon kafarta ya motsa sannan na gangaro kan dalilin da ya sa ni kiran ta.
"Wasu kudi na samu Hajara, shi ne nake so na turo miki ki samu wani abu da ya danganci masu haihuwa ki saya mini."
Kamar ya ban fahimce ki ba."
"Ina nufin abin da ake kawo ma mace idan ta haihu daga gidansu."
"Lallai ma Halima mu duk yawan mu aikin me muke da ba za mu yi miki ba har sai kin kawo kudinki?
Na ce "Ba haka ba ne, ki dai yi hakuri zan dinga turo miki da na samu, kin san sha'anin gidan yawa, ga kishin sauri, ga uwar miji, ga kishiya a gefe."
Ta ce "Na fahimce ki. Allah ya raba ku lafiya."
Sai kuma ta fara mini iya shege "Iyee ta Hamid din ba, Karfi ta amshe ki har kin fara tara kudi? Na yi yar dariya na katse kiran ina tunanin wanda zan ba kudin ya kai mini wurin masu POS, shigowar sako daga wayata ya sa na dubi wayar Hajara ce ta sanya mini Credit na 500 na ji dadi na tura mata sakon godiya sai na kira Haj Iya na tambaye ta kafa na kashe na kira kanwata Bilkisu, muryar Naana na fara ji cikin kukan shagwaba tana fadin a kai ta wuri na.
Na lallashe ta na ce ta bari a yi hutu kasan zuciyata kuma zullumi ya rufe ni, Naana ta zo a wannan hali da ake ciki akwai kura, yaro bai san babu ba, ina kudin da za mu yi mata yadda ta saba?
Bilkisu ta karbi wayar tana fadin "Allah Aunty yar nan taki tana ba ni ciwon kai." Na ce "Me take miki Aunty Billy? Ta ce "Na kusa fara zane ta." Na ce "A'a ba a yi haka ba me take yi?
Ta ce "Sangarta mana. Yanzu haka ta sa na fara tunanin da zan samu aiki."
Na ce "Aiki kuma ko karatun ba a kammala ba?
Don Hamid ya nema mata gurbin karatu a ABU Zaria ya roki Baba ya bar ta ci gaba da karatu ita kanta ba kananan kudade ya kashe mata ba duk don tana kula masa da Naana.
Ta ce "Hmm ba za ki gane ba Aunty. Yau tun da ta dawo Sch ta sanya ni gaba sai na fita da ita ta sha Ice cream, Uncle dinta Abdullah ya ba mu 2000 na samu na aika aka kawo mana Ice cream din.
Ta kwanta tana kuka sai na kai ta Smart kick ina na ga kudin motar zuwa KD da abin da za mu kashe?
Na ja ajiyar zuciya "Zan turo 7k Aunty Bilkisu, ki rike ku lallaba kina saya mata abin da take so."
Shi kenan Aunty mun gode. Amma Naana ba ta san a lallaba ba. Teddy dinta yaron Aunty Sakina ya taba daga zuwa ta birkice ba ta so yanzu ita zan samu na saya mata kullum sai ta yi mini kukan banza
Na ce "A yi hakuri Aunty Billy. Ina jiyo muryar Mama tana sababin hidimar Naana da muka sakar musu.
Naana ta karbe wayar tana ba ni labari, duk wani abu da aka yi mata sai ta fada mini, da kyar na samu ta bar ni ba ta cinye kudaden wayar ba.
Na ajiye ta ina son fita in nemi abin da zan sanya ma cikina amma ba na son haduwa da Fauza, na daure har sai da na yi sallar magrib ina kan sallaya Hamid ya shigo wanda tun fitar shi da safe sai yanzu ya dawo na gaishe shi ya tambaye ni gobe zan koma Hospital na ce E ya ciro kudade ya ba ni na karba da godiya tare da ba shi labarin zuwan Aminu, ya fita ya ce mini zai je ya ci abinci.
Na tashi daga inda nake na hau katifa amma cikina ya ki ba ni hadin kai, da gasken gaske yunwa nake ji.
Na mike kamar mai tafiya kan kwai na fita dakin, ba kowa falon na shiga kitchen, ina da sauran Indomie ita na dafa cikin sauri na juye a flate na dauki ruwa na hada na fito, idona ya yi kyauyawan gani Hamid da Fauza suna cin abinci ta sheka ado cikin wani kankararren leshi wuya da hannu suna ta shekin sarka da yan kunne, na kawar da fuskata na wuce daki.

Na zauna ina cin indomie a hankali zuciyata na can ga tunanin kwalliyar da Fauza ta caba, ji na yi zuciyata na nadamar suturuna da na kyautar, yanzu sai dai na yi kallon Fauza na cancada kwalliya yayin da nake fama da suturu masu rangwamen kudi.
Na yi nisa cikin nadamar sai na ji kamar an mintsine ni, take na dawo cikin nutsuwa ta, istigfari na shiga kirgawa da yatsun hannuna.
Ba karshen nadama da ta wuce ka tashi gaban Ubangiji ka rayu da cin haram, suturar haram.
"Zan jure komai ya Ubangiji." Na fadi kamar mai magana da wani.
A daddafe na cinye Indomie na sha ruwa sai na yi shirin kwanciya.
Wayata na dauka ina dannawa sai na ji bugun kofa da na san Hamid ne na kasa motsawa don wani sake-saken daga zuciyata har ya gaji ya tafi na gyara kwanciyata ina jiran gari ya waye a yi wacce za a yi.


Da na tashi da asuba na yi sallah ban fita neman abin da zan karya ba kamar yadda na saba yi a cikin yan kwanakin nan, na dai bude kofa sai na koma na kwanta, kamar jira Hamid ya shigo sanye da jallabiya mai yankakken hannu.
Ta kasan ido na dube shi sai na lumshe ido, ya iso ya zauna "Lafiya ba ki tashi ba?
Na bude ido "Na tashi." "Lafiya kike? Na daga masa kai.
"Amma ba ki tashi kin fara shirin asibitin ba?
Na ce "Za ni, ina son yin magana da kai." "Ok ina jin ki."
Na ja ajiyar zuciya "Gaskiya ban aminta da kayan Fauza a falo ba."
Ya dube ni da alamar rashin fahimta "Ban gane ba to ina za ta kai su?
"Ko'ina. Amma ina son filin falon ni da ita kowa ya yi amfani da shi, ba ta gaje ita kadai ba, ni ina rabe."
Why Lima me zai sa ki yi haka? Tun kafin ta sanya kayan za ki yi magana ba sai yanzu ba.". Na ce "Ta kwashe ban amince ba."
"Hakuri za ki yi daga ba ki yi magana a farko ba."
"Ba zan yi ba." Na fadi ina tashi zaune "Wai me kike ji ne haka ina taro ki kina fada mini magana? Wuri dai nawa ne ba na wani ba da za a sanya mini doka."
Na mike tsaye. Tabbas naka ne. Amma ni ma ba za a tilasta mini zama da kayan ba, daga na ce ba ni da bukata."
"Me kike nufi?
"Komai ma." Daga haka na fara tube kayan jikina ya bi ni da kallo har na shiga wanka, ban tunanin zan fito na same shi ba sai na same shi zaune, na tsane jikina na fara shiri, kwalliyar doguwar rigar atamfa na yi na sanya farin hijab da farin takalmi na dauki jakata na kama hanyar kofa ya kira sunana ba tare da na waiwayo ba na taaya "Ina za ki? Ban amsa ba na kama hanya, ban san yana biye da ni ba sai da na fito Fauza na tsaye da alama cikin bacin rai mai yawa take "Aikina ka shiga dakinta tun asuba wallahi ba zan yarda ba."
Na wuce shi ma bai tanka ta ba ya bi ni "Ba ki rufe dakinki ba Halima."
Ya fadi daidai kunnena "Daki ai naka ne kamar yadda ka tabbatar mini."
"To ina za ki hospital?
Na yi mishi shiru ya juya cikin sauri na ci gaba da tafiya ta cikin sa'a na samu abin hawa ba bata lokaci ya haye titi.
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: A cikin kwanaki biyun da suka kasance na girkina mun yi abin arzi'ki sosai ni da shi ya dinga lalla'ba ni tare da ko'karin ganin wata matsala bata faru ba wadda zata janyo mana k'ananun maganganu . Washe garin ranar da girki ya bar hannuna kafin na sauko daga saman na sake tuntu'barsa maganar zuwa maiduguri ganin d'akin Fadila ya ce ai ya riga ya rantse na yi hakuri har su je su dawo daga asibitin da za su je shi da Momi tunda yanzu abinda ya sanya a gaba kenan idan ya dawo sai ya raka ni mu je maidugurin tare, shima sai ya gaishe da su Dada da sauran 'yan uwana,
Na ce amma maganar yara fa kai tsaye ya ce mini suna tare da Nabila a gidan domin ta d'an kwana biyu da zuwa wurin 'yar uwata, amma ba da ita za a yi tafiyar ba zata zauna ta kula da yaran gabad'aya har da su Salim da Adamu.
Rashin abin fad'a ya sanya ni kawai zuba masa ido, wace irin masifa ce ne wannan jama'a, shin yaushe yaranmu za su dawo hannunmu ne ni Aminatu?"
Ina zaune har ya gama kintsa jikinsa muka sauko tare babu kowa a falon Baba Tabawa ta gama aiki tun da wuri ta shige dakinta. Hauwa ba ta fito ba. Har zai fita sai ya tsaya yana kallona kafin ya ce." Ina Hauwa ne?"
Kai tsaye na ce." Ba kasan inda take ba?"
Ya zura mini ido na 'yan sakkoni kafin ya gyad'a kansa ya kama hanyar fita yana fad'in.'' idan ba ki yi tsiwa ba ai ba sunanki Amina ba."
Ya fice a gaggauce don da alama yana da wani babban uzurin da ya hana shi tsayuwa ma ya karya kummalo.
Ina juyawa da zummar shiga d'akina Hauwa ta fito cikin kayan bacci da alamar ba ta jima da tashi ba hankalinta na wurin cin abinci. Tana hamma ta furta." Wata mashahuriyar yunwa ce ta tashe ni Amina."
Na ce." Ai fa wannan abinda yake cikin naki acici za mu sanya masa Hauwa."
Dariya ta yi tana fad'in." Na dai kusa saukewa na sha ibada wallahi."
Cike da kulawa na ce." Ubangiji Allah Ya sauke ki lafiya, yanzu nan kuwa maigidan da zai fita yake tambayarki."
Ta yi sororo tana kallona. Na gyad'a kaina ina fad'in." A shawarce Hauwa tun kafin manya su ji wannan abin ku shirya tsakaninku don Allah ke ce 'kasa dashi dole ki sauke girman kan ki."
Ta ce." To so ki ke yi na je na ce masa ya yi hakuri ya janye sakin da ya yi mini Amina?"
Na ce." E, mana menene a ciki idan kin ce masa ka yi hakuri."
Ta'be bakinta ta yi ba ta ce komai ba ta nufi wurin da abin kari yake a shirye tana fad'in." Zancen ki ke so Amina."
Na bita da kallon mamaki kafin na girgiza kai na wuce d'akina da tunanin abin a raina. Da alama shi ya fara sakkowa tunda har ya tambayeta na tabbatar da cewa yanzu ya fara neman zaman lafiya a gidansa.

Ranar da za su tafi
har gida ya yi mata jagora domin ta yi mana sallama. Zamanta ke da wuya Hauwa ta yun'kura ta tashi ta shige dakinta. Hakan kuwa bai yi mata dad'i ba, amma dai ba ta ce komai ba, muka d'an ta'ba hira sama-sama kafin ya sauko daga saman suka fita tare. Sosai na yi mata addu'a da fatan alheri ta dinga godiya da murmushin nan nata wanda duk rintsi baya ta'ba d'aukewa daga saman fuskarta.

Bayan tafiyar su da kwana ashirin da shida Hauwa ta haihu. Cikin ikon Allah ta haifi d'anta namiji kama da ubanshi har ta 'baci duk abinda ya kamaci ta yi wa kanta ta yi tunda haihuwar gida ta yi kuma lafiya lau ita da yaron da ta haifa, a matsayinta na ma'aikaciyar lafiya taimakon da muka yi mata kad'an ne. Sai bayan da muka samu nutsuwa gabad'ayanmu ni da ita tukkuna na nemi maigidan da yake koda suka tafi ba kasafai yake kiran waya ba sai dai mu had'u ta whasap to baya jurar typing sai da vedio call. Sai na ajiye masa sa'ko ta whasap din tare da hoton yaron nasan daga zarar ya hau zai gani. Ina idar da sallar la'asar na bud'e sakonshi ya shigo yana online din muka sake gaisawa na tambaye shi mai jiki ya ba ni amsa mai dadi jiki yayi kyau domin a karshen watan da muke ciki ma za su dawo domin an d'orata akan maganguna kuma alhamdulillahi an samu cigaba. Sai ya d'ora da fad'in wai na yi wa yaron hud'uba da sunan Ahmadu domin shine sunan da ya rad'a masa. Rashin abin cewa ya sanya ni yi masa shiru kawai domin tunda Hauwa ta haihu take kiran yaron da sunan mahaifinta wato Ishak, ban san kuma mai zan ce mata ba gaskiyar magana kenan.
Ganin na yi shiru ban ce komai ba ya sanya shi kiran sunana na kalle shi tunda bidiyo call ne ya furta." Ko akwai wata matsala ne domin na karanci damuwa a cikin kwayar Idonki."
Na girgiza kaina a nutse na ce." Babu matsala amma gaskiya ba zan iya gaya Hauwa ga abinda ka yanke ba, mai zai hana kai ka gaya mata naga tare kuka samar da yaron nan ku biyu mai zai sanya ni ka saka ni a tsakiya. Hauwa tunda ta haihu take kiran yaron nan da sunan babanta, to ni mai kake so na ce kuma."
Ya yi shiru yana kallona kafin daga bisani ya ce." Shikkenan zan gaya mata hukuncin dana yanke hakan ya yi ko."
Na gyada kaina ina fad'in." Ya yi shine daidai sai ku tsayar da matsaya a tsakaninku, Allah Ya raya mana shi."
Ya amsa da "Amin. Yana mai zuba mini ido."
Ni ma na zuba masa nawa idon nan na fahimci canzawar da ya yi har da wani kumatu fatar nan ta sake yin fresh duk da bidiyo call yana sanya mutum muni da duhu to shi ban ga hakan ba, kamar ba wanda ya tafi jinyya ba ya yi kama da ango wanda ya tafi yawon sha'katawa da amaryarsa.
Ajiyar zuciya na sauke yayin da nake ko'karin kawar da abinda na ji yana yun'kuro mini a game dashi na ce." Na canza kammanni ne Allah Ya taimaka ka."
Sai ya rausayar da kansa yana ce wa." Sosai kuwa, wata na gani anan asibitin da muke mai kama dake duk sanda na yi ido hud'u da ita sai hankalina ya tashi wallahi yanzu ina cikin tsananin damuwa na yi missing d'inki my love dina."
Na dan bata rai tare da cewa." Matar kuma idan tana da aure fa, kana raya abun da bai dace ba akan matar wani daidai kenan a wurinka."
Kansa ya girgiza kamar karamin yaro ya furta." Ba daidai ba ne, amma ba na tsammanin ai tana da aure budurwa ce, wallahi ba zan munafurceki ba Amina ba na iya d'auke kaina daga kanta domin yanayin hallitar jikinku daya 'yar duma-duma ce mai yawaltaccen kirji da tudun mazaunai."
Dariya maganar ta ba ni na danne ban yi ba domin ganin abin nasa yana nema ya wuce makadi da rawa na ce." To sai ka tuntubeta idan ba ta da aure ka aurota ko?"
Ya girgiza kansa yana ce wa." A'a ai ba musluma ba ce addinin hindu ce."
Na ce." To menene a ciki sai ka musuluntar da ita."
Kansa ya girgiza tare da furta." A a, abinda ya sa ki ka ji ina yi miki maganarta kamar da kuke yi da ita ne ya b'aci da gaske
idan na ganta ina shiga yanayi na buk'atuwa sosai."
Shiru na yi ban ce komai ba. Sai ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Ina nan dawowa my love za mu sha soyayya ko?"
Na kashe idona tare da fad'in." Sosai ma irin wadda kake so za mu yi."
Sai ya zuba mini idanuwansa babu kiftawa. Na kama dariya ina fad'in." Ka na ji kamar ka d'auko ni daga cikin wayar ko?"
Ya gyada kansa yana lumshe Ido. Hakan ya sake jefa ni a damuwa da sha'awa na sauke ajiyar zuciya a kasalance na furta." Ni ma na yi missing din Baba Yallabai baban soyayya."
Kafin ya ce wani abu kiran da aka yi masa a wayar ya katse video call din. Na kashe wayar tare da ajiyeta a gefe Ina sauke ajiyar zuciya gabad'aya hirar nan da muka yi ta tayar mini da hankali wani irin nake ji a jikina.
Sai gefin magriba na fito falon daga cikin d'akin Hauwa na ji kukan yaron ya tsananta da saurin gaske na shiga d'akin na same shi kwance cikin net dinshi yana ta wutsil-wutsil towel ya toshe masa hanci. Da azama na zuge net din na d'auko shi fuskarsa ta yi jazur saboda da alama ya jima yana kukan.
Na zauna gefan gadonta ina jijiigashi gabad'aya ya shid'e a tunanina tana bandaki na tashi tsaye dashi a kafad'ata na tsaya kofar band'akin ina kiran sunanta shiru bata amsa ba kuma babu motsin ruwa. Sai kawai na kutsa kaina ciki wayam babu alamunta. Da sauri na fito gabana na dan fad'uwa na tsaya ina rarraba idanuwana a d'akin ban ga alamun komai ba..
Na fita kai tsaye kicin na nufa Baba Tabawa ta kammala abinci dare tana gyara kicin din. Cikin kasala da sagewar gwiwa na furta." Baba ina Hauwa?"
Sai kawai ta tsaya tana kallona kafin daga bisani ta furta." Ba ta dakinta ne Amina?"
Na furta." Kwarai kuwa, fitowata daga d'aki kenan na ji kukan yaron nan koda na shiga d'akinta bata nan."
Ta sanya hannunta ta kar'be shi a sanyaye ta biyo bayana muka tsaya a tsakiyar falon. Ina Hauwa za ta tafi to. Ni nake tambayar zuciyata dalili tunda ta haihu ban ga alamun fitina a tattare da ita ba asalima wani babin annashuwa da farinciki ta bud'e. Baba Tabawa ta sanya babban towel ta goya yaron ni kuma na d'auko hijabina na sanya na fita can harabar gidan. Daga nesa na tsaya ina hangen securitys a bakin gate. Masa'udu ya shigo da mota ya ajiye a wurin da motocin suke ya fito daga motar ganina a tsaye ya sanya shi da sauri ya nufo ni. Ya risina yana gaishe ni na amsa tare da fad'in." Daga ina kake domin kuwa zuciyata ta fara hasashen wani abu......✍️
*2k complete a kan telegram via 0542382124...Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: A cikin kwanaki biyun da suka kasance na girkina mun yi abin arzi'ki sosai ni da shi ya dinga lalla'ba ni tare da ko'karin ganin wata matsala bata faru ba wadda zata janyo mana k'ananun maganganu . Washe garin ranar da girki ya bar hannuna kafin na sauko daga saman na sake tuntu'barsa maganar zuwa maiduguri ganin d'akin Fadila ya ce ai ya riga ya rantse na yi hakuri har su je su dawo daga asibitin da za su je shi da Momi tunda yanzu abinda ya sanya a gaba kenan idan ya dawo sai ya raka ni mu je maidugurin tare, shima sai ya gaishe da su Dada da sauran 'yan uwana,
Na ce amma maganar yara fa kai tsaye ya ce mini suna tare da Nabila a gidan domin ta d'an kwana biyu da zuwa wurin 'yar uwata, amma ba da ita za a yi tafiyar ba zata zauna ta kula da yaran gabad'aya har da su Salim da Adamu.
Rashin abin fad'a ya sanya ni kawai zuba masa ido, wace irin masifa ce ne wannan jama'a, shin yaushe yaranmu za su dawo hannunmu ne ni Aminatu?"
Ina zaune har ya gama kintsa jikinsa muka sauko tare babu kowa a falon Baba Tabawa ta gama aiki tun da wuri ta shige dakinta. Hauwa ba ta fito ba. Har zai fita sai ya tsaya yana kallona kafin ya ce." Ina Hauwa ne?"
Kai tsaye na ce." Ba kasan inda take ba?"
Ya zura mini ido na 'yan sakkoni kafin ya gyad'a kansa ya kama hanyar fita yana fad'in.'' idan ba ki yi tsiwa ba ai ba sunanki Amina ba."
Ya fice a gaggauce don da alama yana da wani babban uzurin da ya hana shi tsayuwa ma ya karya kummalo.
Ina juyawa da zummar shiga d'akina Hauwa ta fito cikin kayan bacci da alamar ba ta jima da tashi ba hankalinta na wurin cin abinci. Tana hamma ta furta." Wata mashahuriyar yunwa ce ta tashe ni Amina."
Na ce." Ai fa wannan abinda yake cikin naki acici za mu sanya masa Hauwa."
Dariya ta yi tana fad'in." Na dai kusa saukewa na sha ibada wallahi."
Cike da kulawa na ce." Ubangiji Allah Ya sauke ki lafiya, yanzu nan kuwa maigidan da zai fita yake tambayarki."
Ta yi sororo tana kallona. Na gyad'a kaina ina fad'in." A shawarce Hauwa tun kafin manya su ji wannan abin ku shirya tsakaninku don Allah ke ce 'kasa dashi dole ki sauke girman kan ki."
Ta ce." To so ki ke yi na je na ce masa ya yi hakuri ya janye sakin da ya yi mini Amina?"
Na ce." E, mana menene a ciki idan kin ce masa ka yi hakuri."
Ta'be bakinta ta yi ba ta ce komai ba ta nufi wurin da abin kari yake a shirye tana fad'in." Zancen ki ke so Amina."
Na bita da kallon mamaki kafin na girgiza kai na wuce d'akina da tunanin abin a raina. Da alama shi ya fara sakkowa tunda har ya tambayeta na tabbatar da cewa yanzu ya fara neman zaman lafiya a gidansa.

Ranar da za su tafi
har gida ya yi mata jagora domin ta yi mana sallama. Zamanta ke da wuya Hauwa ta yun'kura ta

Please Login or Register in order to submit comment