Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hade hannunmu wuri d'aya yana fad'in." Kin san wani abu?"
Na girgiza kai ina kallonsa ya ce." Kada ki sake dukan yaran nan ba ni so, a duk lokacin da wani abu ya shiga tsakaninsu ko suka yi abu na rashin kyautawa a zare musu Ido, a yi musu fad'a amma ban da duka ba na so, domin hakan ba tarbiya ce ba don wasu lukutan dukan yakan kangarar da yaro.
Na daidaita yanayina tare da fad'in. " Wai wanene ya gaya maka dukanta na yi? fad'a fa na yi mata na dan murde mata kunne shikkenan duka."
Ya ce." Ta gaya mini kin dake ta a kanta shin kin san illar duka aka kuwa?"
Raina ya b'aci amma na danne na ce." Sai na dake a kanta domin na illatata ko?"
Ya yi shiru yana kallona. Na ce." Ni ban yi mata dukan da zai firgitata ba a gaban Baba Tabawa komai ya faru. Ba ni son cizo domin yana da illa sosai dole a ja mata kunne."
Ya ce." Ni ma ban hana ba, dukan ne kawai na ce ba na so kada a sake?"
A tak'aice na ce." To shikkenan." Domin maganar ta mutu kawai amma ba yadda za a yi Ina raye kuma ina gani su yi abinda ba shikkenan ba na zauna ina yi musu lako-lako ni kaina ba a yi mini irin wannan tarbiyar ba, ba kuma zan yi wa yarana ita ba.
Na ce." Ina Hauwa na d'auka tare za ku taho?''
Ya ce." Tana can gidansu wai ba zata dawo ba"
Da mamaki na ce." Ba zata dawo ba?"
Ya ce." Kwarai kuwa haka ta fad'a, na ce to shikkenan Allah Ya hada kowa da rabonsa."
Kawai sai na zuba masa ido da mamakin maganarsa wai Allah Ya hada kowa da rabonsa ya fadi hakan cikin kwanciyar hankali tabbacin abin bai dame shi ba. Ni Kam sam lamarin bai yi mini sugar ba. Na ce." Don girman Allah ka yi hakuri."
Ya dube ni da mamaki kafin ya ce." Ha'kuri ai na yi tunda har na mayar da ita amma ta ce a a, kuma ta yi mana shegantaka sai ta sha zamanta abinda ga matan nan da yawa me zai dame ni Amina."
Na ce." Amma dai ba kamar ita ba."
Ya ce." To yanzu ya za ayi?"
Kai tsaye na ce." Ta dawo dakinta don Allah."
Sai ya yi murmushi a hankali ya ce." To ki kira wayarta sai ki roke ta Ina ga haka zai fi."
Daga haka sai ya tashi ya nufi gado yana fad'in." Zo mu yi wata magana."
Na yi jim kafin na tashi na bi shi gadon ya janyo ni na kwanta a gefensa sai ya sanya hannu ya rungume ni sosai a jikinsa yana fad'in."Alhamdulillahi. Sai na rasa godiyar Allahn ta mecece haka dai muka raya daran cikin shau'ki da sakwarkwcewa. Da asuba yana fita salla ni ma sauka k'asa cikin gajiya da bacci a idona.
Sai da na yi wanka tukkuna na yi sallah na nemi gado na kwanta domin mugun bacci ne a idona wanda zai iya zame mini ciwo muddin ban yi shi ba.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
🌲🌳🌿☘️

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa

*PAID BOOK 2K COMPLETE ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA 1K VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
Kirana da aka yi a waya shi ya tashe ni wajejan goma da ashirin da biyar na safe. Koda na duba lambace babu suna na daga tare da sallama sai na ji muryar Idiris mijin Sahura nan da nan na daidaita yanayina. Domin zahirin gaskiya ni ma haushinsa nake ji dangane da abinda yake ahirin aikatawa. Tabbas nasan kiran nasa baya rasa nasaba da matsalarsu. Muka gaisa jikinsa a sanyaye ya fara yi mini bayanin halin da ake ciki Sahura ta rufe gida sannan ta tattara yara da kayansu ta kaiwa mahaifiyarsa bayan tasan bata da k'oshin lafiya. Yanzu haka sai a shagon dake jikin gidan ya kwanta shagon da yarana suke d'inki kenan yana jadadda mini a cikinsu ya kwanta cike da alhini da damuwa. Ban katse shi ba har sai da ya kammala tukkuna na ce." To wallahi ni dai Idiris ba ni da tacewa akan wannan lamari. Ina ganin ka kyaleta kawai tunda tafi buk'atar rabuwar sai ka je ka yi rayuwarka da sabuwar amaryarka yara kuma ai duk sun girma babu wanda za a yi wa wahala a cikinsu."
Da damuwa ya ce." Saboda fa kusancin da yake tsakaninku ya sanya na kira ki Amina, me yasa za ki gaya mini haka ke don Allah idan na ce zan rabu da Sahura ba za ki yi mamaki ba?"
Na d'an yi murmushi babu nisha'di na ce." Babu mamakin da zan yi Idiris abinda aure na mutum biyu ne idan ka gaji da ita zaka sawwa'ke mata mana ko kuma ka nemi hanyar da za ka k'untata mata."
Ya ce." Yanzu dai don Allah ki rarrasheta wallahi ba wai don na wulakantata zan yi auran nan ba. Ina son Sahura ina kuma buk'atar cigaba da zama da ita ki rarrasheta ki bata ha'kuri ta dawo mu cigaba da zama in sha Allahu babu abinda zai faru domin itama yarinyar da zan aura bata da matsala 'yar gidan tarbiya ce wallahi bata da fitina."
Na yi dariya ina mamakin maganarsa tun bai zauna da yarinyar ba yana shedar halayenta tabbaci kenan ba zai janye ba. Na ce." To shikkenan zan yi magana da ita zuwa an jima in sha Allahu."
Da sauri ya furta." Zan kira ki domin na ji abinda ku ka yanke amma don girman ki tausheta ta dawo na ware mata turmi biyu daga cikin lefen da nake had'awa sannan zan bata dubu hamsin sai ta sayi kayan kwalliya."
Na ce." To shikkenan. Da takaici na katse wayar ban tsaya na kàrasa sauraran karshen maganarsa ba. A tunana ai Sahura tafi karfin turmin atamfa biyu da dubu hamsin, ita wahalar nawa ta yi masa tunda suka yi aure har yanzu ma cikin yi masa hidima take.

Da yammacin ranar muka yi waya da ita na gaya mata Idiris ya kira ni a waya akan abinda yake faruwa. Kamar yadda ya buk'ata din na fara rarrashinta da kawo mata misalai ta yi shiru tana saurarena don har ina murna ina cewa ta sauko a zuciyata sai da na gama maganata tukkuna ta ce ." Ba ni buk'atar atamfofinsa ya ri'ke har da k'udin ya k'arawa amarya Amina, takarda zai aiko mini da ita yanzu zaman da nake yi kenan."
Na ce" Sahura akan kishiya dai idan ki ka kashe auranki na kusan shekara ashirin da wani abu wallahi kin ba ni kunya kuma na raina wayonki, ki bari ta shigo mana ki ga kamun ludayin zaman. Haba don Allah ki jure mana."
Kashe mini wayata ta yi ta barni ri'ke da tawa a kunne da mamaki.

Bayan magriba Idiris din ya dinga kira wayata ina kan daddauma ina jan carki kamar yadda na saba. Koda na duba na ga shine na ajiye wayar kawai na cigaba da abinda nake yi shi kuma bai fasa kira ba. Hakan ya yi daidai da shigowar maigidan wanda shi ma tunda ya fita da asubahi bai sake shigowa ba.
Ya d'auki wayar yana dubawa sai ya kalle ni kaina a sunkuye kawai sai ya daga tare da sanyata a kunnansa jin muryar namiji na ji yana fad'in." Wanene?" ban ji abinda Idiris din ya ce masa. Na ji yana fad'in." Mijin Sahura ne to bari ta kammala tana azkar ne zuwa an jima sai ka kira."
Ya yi shiru na d'an wani lokacin kafin na ji yana fad'in." Amin Ya Allah, ma sha Allah, ka kira zuwa an jima kadan." Daga haka sai ya kashe wayar ya ajiye har na kammala na juyo ina dubansa ya ce." Mijin Sahura ne ya kira ki a waya ina fatan lafiya?"
A tak'aice na ce." Lafiya ba lafiya."
Ya dube ni sosai yana fad'in." Suna da matsala ne?"
Ina ko'karin cire hijabin jikina na furta." Aure zai ka'ra shine take bore har ta tafi gida."
Ya yi d'an jim kafin ya furta." Na kan rasa inda tunaninku yake tafiya wataran Amina, daga zai kara aure domin raya sunna sai ta ta tafi ta bar dakinta menene amfanin hakan."
Cike da takaici na ce." Ai ba a ce kada ya kara ba, ya bari ya tsaya da k'afafunsa tukkuna bashi fa da cikakkiyar
sana'a, wallahi Sahura wahala take sha a hannunsa kuma ta yi masa hallaci tunda suka faru a gidan haya suke shekara kusan ashirin da uku da auransu buge-buge yake yi itace karfin kula da gidan tun kafin ma ta samu aiki a kamfaninka haka take gwagwarmaya. Amma shine daka kawai an yi musu rabon gado ya samu miliyan takwas ko wata biyu fa ba a yi da raba musu kudin ba ya fara yun'kurin karin aure har yana tara lefe a dakinta. Ita kuwa ta kulle gidan ta gudu ta kai masa yaransa wurin Babarsa."
Dariya ce ta sub'ce masa ya dinga yi har ina mamakinsa na d'auka ai zai cigaba da goya masa baya. Ya ce." A lallai bai kyauta ba kuma da gaske bai yi adalci ba. Yadda ki ka gaya mini yanzu ai ita ta yi masa hidimar da ta zarce ta miliyan takwas to me yasa tunaninsa bai kai ya saka mata da alheri ba sai da kishiya. Bai kyauta bai kuma yi daidai ba, in banda rashin tsinkaye ai ba aure ya kamata ya yi ba a yanzu ko?"
Da sauri na ce." Kwarai kuwa abinda itama take ji wa haushi kenan zai bata turmin atamfa biyu da dubu hamsin abinda ya kara ba ni haushi dashi kenan."
Ya ce." Kin ga kira mini Sahurar yanzu na yi magana da ita."
Na zauna gefansa ya miko wayata na lalubi lambata bugun farko ta daga cikin bala'i ta fara fad'in." Amina ki kyale ni don Allah idan har kin san ba maganar arziki za ki gaya mini ba, na gaya miki na gama yanke hukunci, idan kema za ki goyu da bayan Idiris din sai nasan a wani aji zan ajiye ki."

Ina binki bashi idan kin karanta ba ki biya ni hakkina ba

Na ce." Yi ha'kuri mai da wukar sis, Yallabai ne zai yi magana dake." Ta yi shiru ba ta ce komai ba sai na mik'a masa wayar da sauri ya kar'ba a nutse ya kira sunanta "Sahura."
Ina ji ta amsa cikin ladabi." Na'am ranka ya dad'e ina yini?"
Ya ce." Lafiya lau ya kuke ina yara?"
Ta ce." Kowa lafiya lau Sir."
Shiru ya d'an biyo baya kafin ya yi gyaran murya ya ce." Kin san abinda nake so dake?" Ta ce." A'a. "
Ya ce." Amina ta yi mini bayanin duk abinda yake faruwa, ki yi hakuri ki koma dakin mijinki ki cigaba da kula da yaranki, shi kuma ki kyale shi idan har kina da hakki sannu a hankali Allah zai saka miki. Ni kuma zan yi miki alheri domin ki zauna a wadace cikin walwala zan canza miki gida mai kyau sannan zan baki kudi ki dinga wata sana'ar a gefe sannan ki cigaba da zuwa aikinki kina taimakon yaranki da 'yan uwa, kada don mijinki zai kara aure ki yi fushi ki dasawa kan ki k'unci yaranki su shiga damuwa ki daure na wani lokaci komai zai wuce ."
A sanyaye ta ce." Na gode ranka ya dad'e, Allah Ya saka da alheri, shikkenan in sha Allahu zan koma kamar yadda ka buk'ata."
Cike da jin dadi kuwa ya furta." Ni ma na gode sosai Sahura, zan yi magana da Jamilu sakatare na nan kamfanin naku duk abinda yake da akwai zai yi miki bayani in sha Allahu maganar abinda na ce zan baki kuma za ki gani a daran nan."
Ta dinga godiya har muryarta tana rawa. Ya mik'o mini wayar na kar'ba a d'an sanyaye na ji dad'i sosai da ya shiga lamarin gashi har da alherinsa ko babu komai yana da lada a wurin Ubangiji.
Muka yi sallama da ita tana fad'in." Na kara yi masa godiya. Na dube shi a hankali na ce." Mun gode sosai Ubangiji Allah Ya saka da alheri."
Bai kalle ni ba ya ce." Ba ni details dinta yanzu ."
Ya miko mini wayarsa na kar'ba na sanya masa kamar yadda ya ce.
Ya ce." Ke nawa ki ka bata gudummuwa?"
Na ce." Gudumawa kuma?"
." Dannar kirji kuke cewa ko?"
Dariya na yi na ce." Ban bata komai ba wallahi."
Ya d'an Harare ni yana fad'in." To yaushe kuwa za ta saurari rarrashinki irin wannan ana had'awa da hasafi sai ki ga an shawo kan matsalar."
Na dinga gyada kaina ina dariya lallai ne kudi suna iya sayan komai amma ban da rai da rayuwa.
Miliyar biyar ya tura mata bai gaya mini ba amma yana tura mata da kamar minti goma ta kira ni a ki'dime har da rawar murya "Amina don girman Allah ki kara yi mini godiya yanzu nan na ga sa'ko 5m na gode na gode na gode Allah Ya saka da alheri ga sabon gida an ce za a ba ni."
Dariya ta kama ni na ce." Sahura yanzu don Allah ina rantse-rantsen da ki ka dinga yi, Idiris fa aure zai ka'ra ko kin manta."
Ta ja tsaki tana fad'in." Wallahi tallahi Amina saboda Yallabai ya saka ba ki a maganar nan zan koma zaman aure da Idiris amma wallahi ba don haka ba sai dai ya aiko mini da takardata."
Ta kashe wayar ba tare da ta jira ta ji abinda zan ce ba."
Ya dube ni yana fad'in." Ba ki kyauta ba Amina." Ina dariya sosai na ce." Don ba ka ji rantsuwar da ta dinga yi ba shine abinda ya ba ni dariya da mamaki."
Ya gyad'a kansa Shima da d'an murmushi a saman fuskarsa ya ce." Ai tace saboda na sanya ba ki zata koma. Kuma wallahi na ji dad'i sosai tuntuni na fahimci cewa ai tana da kirki da saukin hali."
A tak'aice na ce." Hakane kam Sahura mutum ce har da rabin mutum mun gode sosai ta ce na sake godiya ina yi akan kaina da ita Ubangiji Allah Ya sa kafi haka."
Ya amsa da Amin suma Amin yana kallona.
Na dan sauke ajiyar zuciya kafin na ce." Sai mu yi maganar Hauwa tunda mun sasanta wannan auran."
Ya bata rai yana fad'in." Za ki bata mini rai kenan ko?"
Na ce." B'acin rai kamar yaya?"
Cikin 'kosawa ya ce." Maganar Hauwa ta ishe ni a gidan nan Amina, ya kamata ke ma ki bar ta kamar yadda na bar ta ba na son abinda zai rikita mini gida dama can itace husumiya yanzu da bata nan ba gashi kuna zaune kalau da Maryam ba."
Haka kawai sai na ji rashin jin dadin maganarsa. A ganina kamar Hauwa bata cancanci haka daga wurinsa ba duk da bai gaya mini abinda ya faru ba a wajan sulhunsu amma na lura haushinta da yake ji ya sake ninkuwa. Zaman da na yi da ita na fahimci macace mai taurin kai da girman kai har shi eanda ya ajiyeta yi masa take kuma a cikin ayyukan da ta dinga yi a gidan nan da gadara da iko take gudanar da komai dalili tana ganin kamar ta fi kowa dangantaka mai karfi bayan ta aure duka na fahimceta. To amma ni wannan baya damuna tunda nasan matsayina a zuciyar mijina ko bai fito ya fad'a ba. Ba na sha'awar a ce sun rabu gabad'aya ga zuria a tsakaninsu mai k'arfi kamata ya yi a ce sun sulhunta junansu sun yi hakuri sun cigaba da zama.
Ganin yadda ya had'e rai da nuna baya buk'atar sake maganar Hauwa sai na shigo da maganar zuwa maiduguri tunda shi ya yi mini alkawari ya ce za mu je a karshen wata amma daga mun dawo za mu tafi legos tunda Alhmdullhi jikin matar tasa ya yi sau'ki.

***
Abinda ya faru kenan kamar yadda ya yi mini al'kawari cikin karamci da kara da kulawa muka je maiduguri tare. Ya bi dangin Mamana da alheri mai yawa. Baban Saude bayan gari a lokacin da muke je garin. Da yawa wad'anda ba su ta'ba ganinsa a zahiri ba suka yi tozali da shi tare da alherinsa. Ni kuma na sayawa Fadila sabuwar freezer 'katuwa da kenan d'inki domin yin sana'ar sayar da ruwa da 'kan'kara.
Kwananmu biyu kacal a maiduguri muka yi sallama da su.

A ranar da muka dawo a gidan Momi ya kwana washe gari ya shigo mini a hargitse yana gaya mini jikinta ne ya sake tashi jiya ba su yi wani baccin kirki ba suma ta yi sai gefan asubahi ta dawo.
Ya ba ni tausayi sosai itama haka domin da gaske ne duk mai zuciyar imani idan ya ga halin da take ciki zuciyarsa sai ta motsa. Dole shiryin tafiyarmu Legos ya rushe yadda hankalinsa ya tashi da ciwon komai nasa tsayawa ya yi

Kwana biyu a tsakani ya sake kwasarta suka sake koma can kasar hindu din asibitin da suka kula da ita a wancan karon domin sake duba lafiyarta.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
🌲🌳🌿☘️

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*PAID BOOK 2K COMPLETE ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA 1K VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
A tsanake ta ce." A a ai tare duk muke tafe tun a waje ya ce Garba ya ajiye shi yana can tare da Adamu."
Na gyada kaina ba tare da na sake cewa komai ba. Baba Tabawa ta kawo tire uku masu girma cike da abinci na taimaka mata wurin zubawa kowa Hajja ta ce ." Hajiya Saratu tana tafe in sha Allahu mun yi waya da Alhaji Sa'idu shi da d'an uwansa Alhaji Dahiru sun ce za su yi kokarin samun jana'iza." 'Yan uwan mahaifin maigidan ne wanda a yanzu su kadai ne suka rage musu a family din. Na gyada kaina a sanyaye na ce." Allah Ya kawo su lafiya.

Kai na jima ban shiga tashin hankali da nadamar rayuwa ba sai a rasuwar baiwar Allah nan. Tunda gawar ta iso gabad'aya estate din namu ya cika da motoci jama'a daga kowace kusurwa abokanan maigidan dama wasu daga ciki abokan tsohon mijinta ne. Cikin gidanta cike da 'yan uwanta da zuriarsu tare da abokanan arziki da yaranta masu yi mata hidima na shagunanta. Ana ta koke koke masu dauriyar daga ciki kad'ane. Babbar yarinyata Nusaiba sumanta biyu har yanzu ba ta gane wanda yake kanta ba. Nabila kuma tana ta iskokai a wani d'aki da 'yan uwansu sun kulle-kulle kofa don kada ta fito daga inda muke a zaune muna jin ihunta. Cikin masu yi wa Momi wankan gawa har da Baba Tabawa lallai na yaba k'warai da aniya wurin jajuecewarta da dauriyarta koda yake yadda take ba ni labari a gaban idonta mahaifiyarta ta rasu kuma itace ta wanke ta. Wannan ya kara tabbatar mini da cewa Baba Tabawa tana daya daga cikin salihan matan da Ubangiji ya ce lallai yana jin kunyarsu a gidan duniya da lahira dalilin rashin haihuwa.
Ban tashi tabbatar da cewa d'an adam ba a bakin komai yake ba sai da aka gama had'a Maryam tsaf cikin likkafani a mike cikin makara ta zama 'yar mitsitsiya a tsakiyar makarar tsabar ciwo ya cinyata
ana ta lallabata sunanta gabad'aya ya shafe daga jiya zuwa yau din wasu na kiran ta da gawa wasu na kiranta da marigayiya. Yaranta da mijinta tare da yan uwanta sun kewaye makarar yayin da masu aikinta mata da muke tare da su a gidan suke gefe sun cure kansu wuri d'aya sai shar'bar kuka suke yi. Adamu dake tare da Yusi ya can gefe daya kuka yake yi sosai yana fad'in." Momi kin mutu da wa ki ka bar mu a duniya, ba mu da uwa ba mu da uba. Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!.
Sambatun da yaron yake yi ya kidima ni sosai ya kuma ba ni tausayi ainun na yi saurin d'auke kaina daga kansu Yusi yana ta rirrike shi sun kasa zuwa gaban gawar ma gabad'aya.
Hajja da Gwaggo suka nufi bakin makarar. Na yi na yi na ja kafata domin bin bayansu na kasa don wata irin juwa da Hajijiya nake ji idona na ganinsu garagara,
Bayan haka kuma gabad'aya a tsarge nake ga yanayin kallon da na ga wata mata da na ji suna kiranta da suna Yabi take yi mini irin na wulakanci da neman fitina.
Hawaye masu d'umi suka silalo kumatuna wanda ya yi daidai da lokacin da na yi hu'bbasa wurin sarrafa 'kafafuna amma suka doje ban san yadda aka yi ba kawai na ji ni a k'asa na zube a lokacin ne kuma naga

Please Login or Register in order to submit comment