Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana da yara tana kuma da hakki."
Ta ce." Lokacin da zai yi mata kyauta kin sani ne Yagana? ke dai ba yar uwarki ki ka sani ba me yasa ba za ki goya mata baya ba bisa abin alherin da ta samu kin ga kenan anan gaba zaki sanya masa shakku idan ya yi niyyar yi mata wani alherin."
Ta yi shiru bata ce komai ba. Na gane dalilinta na magana kuma tana da hujja amma yanzu tunda ya fito ya fad'i da bakinsa ni ya bawa ba yara ba shikkenan.
Na ce." Ya ji haushi har yana ta fad'a wai babu wanda zai nuna masa yadda zai yi da abinsa. Ya gaya mini dalilai masu muhimmancin da ya sanya shi ba ni kyautar wannan kamfani. Na kar'ba kuma na gode amma abinda na yanke shine ya sanya mini shi a kasuwa a kar'bi kudin domin idan har zai cigaba da aiki da sunana akwai matsala babba a tashe shi daga aiki idan ya so na nemi plaza na saya na fad'ad'a harkokina na kuma sanya haya a wasu wuraran."
Ya Falmata da annashuwa ta furta." Wannan tunanin naki ya yi Amina. Ya kike gani Yagana hakan ya yi ko?"
Ta furta." Ya yi sosai Ubangiji Allah Ya dafa miki amma ta wace sigar za ki tunkare shi har ki gaya masa ya sa a kasuwa ya baki kudin."
Na furta." Ni ma ban san ta sigar da zan gaya masa ba wallahi tunda yanzu fad'a yake ta yi kan cewa ba ya yi mini gwaninta duk abinda ya yi mini na alheri sai na gwasile na ce ga yadda nake so."
Sahura da ta gama sanya kayanta kuma tunda muka fara maganar ba ta ce komai ba sai yanzu ta furta." Sister na taya ki murna sosai Ubangiji Allah Ya yi ri'ko da hannunki lallai kin cancanta da fiye da abinda ya fi haka ma, an yi gwagwarmaya kuma an tari kalubale mabambamta amma ni a shawarce ki bari a kwana biyu lokacin da kuke dad'i da shi sai ki gaya masa tunaninki idan kin ci sa'a zai amince tunda gaskiya yana da sau'kin kai a wasu lukutan."
Anti Yagana ta ce." Ni ma tunanin da na yi kenan ki bari a kwana biyu kun samu nutsuwa dake da shi cikin lumana sai ki gaya masa abinda ki ke so."
Na sauke ajiyar zuciya a hankali na furta.''In sha Allah."
Yusura ta tashi daga bacci ta shiga toilet ta fito na ce ta janyo mana akwatinan kayan nan.
Ta d'auko su d'aya bayan d'aya aka bud'e kaya ne masu kyau da kud'i kuma ta duba quality sosai babu wani k'aramin abu a ciki ko na son zuciya ban san dai iya adadin kud'in da ya bata ba amma ta yi kokari kuma sun yi kyau kayan kwarai
Muka gani gabad'aya Ya Falmata 'yar gayu mai son abu mai kyau sai yabawa take yi da kayan. Muka gama gani yarinyar ta mayar da su inda suke. Gaza ha'kuri na yi na sauke ajiyar zuciya ina duban anti Yagana na ce." Nabila ce fa ta had'o kayan nan."
Ta yi kasa'ke da alama ba ta gane Nabilar da nake magana akai ba Sahura ta yi caraf tana ce wa." Nabila wadda na sani 'kanwar Hajiya Maryam mai rasuwa."
Na gyad'a kaina ina kallonta. Anti Yagana da sauri ta ce." Kamar Yaya dama ba shine ya sayowa yaran ba?"
Na ce." Kudi ya bata ta sayo musu anti Yagana mu zube lamarin nan a fefe mu kuma aunashi da ma'auni na hankali da adalci shin me kuka fahimta don Allah?"
Ya Falmata ta yi shiru domin bata san bada'kalar da ta faru ba fadi take yi aikuwa kaya dai sun yi kyau Amina ina ganin ko ke ce abinda za ki sayo kenan domin dai babu abinda babu kuma kowacece wannan ba ta yi cuta da almundahana ba
Anti Yagana ta ce." Ba ki gane ba ne, ita wadda ya bawa kudin kayan k'anwar wannan matar tasa ce fa Maryam da ta rasu mahaifiyar yaron nan Adamu da suka kawo kayan tare da Yusi."


Na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Ta d'an yi shiru na wani lokaci sai ta ce." Ba ta da aure ne?''
Ta gyad'a kanta tana fad'in." Bazawara ce tana zaune gidan yayarta tana business da kuma kula da yaran. Shi babban ma Salim baya gari ita kuma Nusaiba tun iyayansu na raye suka yi mata aure sai shi wannan karamin Adamu."
Na ce." Yana ta jaddada mini cewa business d'in da take yi kenan kuma da a sayi kaya a waje gwara a saya a wurinta. Ke anti Yagana kin san wuya da masifar da muka shiga dalilin Maryam ko, me kike tunanin zai faru yanzu tunda shi ba shi da tunani bai gane cewa sonsa take yi ba."
Ta dinga girgiza kanta tana fad'in." Lallai mutumin nan to ina ruwansa da ita idan ba yana so ya d'auka ba shi yanzu don girman Allah sai ya yi zawarcinta duk matan da suke duniya."
Ya Falmata ta yi shiru fuskarta ta canza da wani yanayi ta ce." Wata'kila wannan kyautar da ya yi miki yana so ne ya kashe miki baki kin ga ai idan ya yun'kuro domin auranta baki da bakin magana to mutumin da aka bawa kamfani na miliyoyin kud'i. Ai ya jefi tsuntsu da dutse biyu ne.
Zuru na yi ina kallonta Ya Falmata macace mai tsinkaye sosai ni ban ma ta'ba yin wannan tunanin ba, amma har yanzu zuciyata bata gama aminta da cewa zai iya yin zawarcin Nabila ba idan an yi duba da irin muguwar wahalar da muka ci domin dai ba shi kad'ai ya shiga tasku ba har da mu gabad'aya Allah ne ya sa da kwanansa a gaba.
Anti Yagana ta ce." Hakan za ta iya kasancewa ya yi da wannan niyyar ne, amma abin ya ba ni mamaki wallahi, wai me yasa wasu mazan ba su da tunani ne?"
Sahura ta furta." Sai ki tsananta da addu'a Amina ni kaina wallahi na tsorata wad'annan mutanan sai kace mayu ita ta yi ta gama ita kuma wannan zata kutso kanta ba wani abu ta hange ba sai dukiya ce sun zama annoba wallahi.
Anti Yagana ta dubi Ya Falmata da mataccen jiki ta shiga bata labarin irin abubuwan da suka faru baya kafin rasuwar Hajiya Maryam din.
Ta dube ni tana fad'in." Ki ajiye kayan kada ki yi wa yaranki amfani da su. Ya bada wasu kudin kafin mu tafi mu sayo musu sannan ko ya ba ki takardun kamfanin nan kada ki kar'ba har sai ya gaya miki abinda yake tsakaninsa da ita irin wannan fa sai dai ki ji an d'aura tunda haka ya yi lokacin auran 'yar uwarta."
Shiru kawai na yi ban iya cewa komai ba. muka yini muna tattauna lamarin shima tun jiya da daddare da ya fita bai sake shigowa ba. Sai bayan la'asar duk muna falo yaran suka sake shigowa a karo na biyu wannan karon har da Masa'udu kowanne kafad'arsa sa'be da dilar atamfa suka jibge dila biyar a gefe sai wasu manyan kwalaye hud'u da suka shigo da shi suka tattara kayan waje daya.
Suka fita jim kad'an Hauwa da inna Uwani har da yaran gabad'aya suka shigo a gidanta suka yini, alamu sun nuna itama Inna Uwanin bata jima da sauka ba kuma kai tsaye gidan yarta ta sauka. Hakan kuwa ya bawa Hajja haushi domin a takaice ta amsa gaisuwarta yayin da ita kuma take ta washe baki da Hasan a hannunta tana yi mini sannu da barka da arziki ina amsawa tare da kallonsu daga ita har Hauwan nema suke yi su mayar da mutane shashasai
Jim kan da zamansu shima ya shigo ganinsa sanye da kayan shan iska irin wanda ya saba sanyawa idan yana gida
ya tabbatar mini da cewa bai fita ba gabad'aya amma bai shigo ba sai yanzu. Ya zauna a ka shiga gaisawa nan na ji yana gayawa Hajja bacci ya yi tun safe shiyasa bai shigo da wuri ba. Ya Falmata ta fara tashi ta shiga d'akina. Da kamar minti goma anti Yagana ta bi bayanta Sahura da Yusura dama suna ciki ba su fito ba. Sauran kuwa suna can sashen ba'ki tun safe da muka gaisa na ce su koma can su yi zamansu sai sun fi sakewa.
Ni ma ban yi dogon zama ba na tashi na bar musu yaran gabad'aya. Ina daf da shiga d'akina mai sunan Mamana ta fito Hajiya Saratu kenan da yake d'akin Hauwa na da suka sauka ita da Hajja tunda asali d'akin da suke yada zango idan sun zo Khalil ne a ciki yanzu ta tsaya cikin raha tana fad'in." Uwargida kuma uwar biyu sau biyu." Dariya na yi na ce." Hajajju kenan ina yini." Ta amsa da kulawa tana fad'in." Na ce bari na fito nasan yanzu Falmata tana nan ta fara bada labari."
Ina dariya na furta." Yanzu kuwa ta shiga d'aki yau tun safe bata jin dadin jikinta zazza'bi ne amma ta sha magani da sauki."
Na fad'i mata hakane kawai domin ban san abinda zan ce mata ba bayan haka dalili tunda suka zo ake yin wannan zaman a yi hira a yi wasa da dariya amma tunda na gaya musu abinda yake faruwa jikinsu ya yi sanyi mussaman ita din. Kishi ne da su haka Mamanmu take da wannan kishin da rashin son kishiya yanzu nan duk sai su damu. Gashi dai ba ita za a yi wa ba jin labarin wahalar dana sha a baya ya sanyayyar mata da jiki gabad'aya ma kyautar da take ta murna an yi mini ta daina burgeta don tunaninta yana gaya mata danne mini kirji zai yi kawai sai dai mu ji d'aurin aure.
Na shiga d'akin na samesu suna sake tattaunar maganar Ya Falmata duk ta yi wani kicin-kicin da rai na ji tana fad'in zaman ya isheta yau kwana bakwai tunda yara sun amsa sunansu su yi shirin tafiya kawai.
Na zauna gefanta ina fad'in." Wane irin tafiya kuma Ya Falmata ku bari a kàrasa shagalin sunan mana.
Tsaki ta ja kafin ta ce." Mijinki haushi yake ba ni Amina wallahi sam shekarunsa ba su amfanar da shi komai ba gabad'aya ba shi da tunani da hangen nesa."
Dariya ce ta kama ni ganin yadda ta hak'ikance tana ta fad'a.
Na shiga wanka na fito na shirya jikina sosai d'aya daga cikin sabbin d'inkunan da na yi wanda Sahura ta zo mini da su.
Still dai maganar suke yi anti Yagana tana fad'in." Wata'kila ma ita ya bawa kudin raggon suna tunda yau da ake da kwana bakwai a al'ada ya kamata a ce an yankawa yara rago duk da ba a ce dole yin hakan farilla ba ne.
Waya ta yi kara tana can saman dirowa kusa da Sahura ita ta miko mini don yadda ake ta caccakar ubangidan nata bata iya sanya baki ba yanayinta dai da yar damuwa itama abin ya bata haushi da mamaki.
Na d'aga wayar cikin nutsuwa ya kira yi sunana na amsa ya ce." Ki zo ki same ni mu yi magana ina sama." Na ce." To shikkenan." Ya kashe waya ni ma na kashe tawa.
Suna falon Hajja Inna Uwani da Hauwa da kuma mai sunan Mamana suna ta hira Hajja yanzu ta sake da 'yar uwarta. Sannu na yi musu na d'an tsaya muna magana da ita akan farin kwalli wai ta sanya Magaji ya nemo a can kano din ya kawo had'e da garafuni na ce to shikkenan an gode.
Ina kallon Hauwa tana d'an satar kallona domin ni kaina nasan na yi kyau sosai atamfa ce a jikina amma duk jikinta aiki ne da uban stones ko ta ina dinkin buba ne ya zauna a jikina yadda ake so.
Na haye saman zuciyata sam babu dadi ina kallon tarin kayan da su Adam suka jibge wajan 'kafar benan zan dai ji dalili.
A zaune na same shi yana waya aikin kenan na zauna har ya gama ya juyo tana kallona tare da kiran sunana.
Na sake amsawa ni ma idonsa a kaina. Ya cigaba da cewa." Ki yi hakuri yau tun safe ban shigo ba kin san Allah bacci ne ya shammace ni mai nauyi na ce da Hauwa ta tashe ni kafin azuhur wai ta manta sai uku da wani abu na tashi sallah sai a lokacin na yi."
Na yi shiru ban ce komai.
Ya ce." Na so yau a yi wa yaran nan yanka hakan bai yiwu ba amma gobe idan Allah ya kaimu za a yi da wuri akwai shanu biyu wannan na jama'ar da suke kewaye damu ne ku d'iba Hajja ma ku bata nata ku bawa Hauwa da duk wanda yake da hakki. Ragona hud'u ne wannan naki sai kin ga dama za ki ba ni."
Ya fad'a yana kallona na daure zuciyata na ce." To an gode Allah Ya saka da alheri da budi."
Ya ce.'' Ni ne da godiya ranar juma'a mai zuwa kuma za mu yi walima kamar dai yadda na saba abokaina da Malamai za su halarta in sha Allahu rabbi za a yi adduoi kamar yadda annabin rahama ya koyar da mu. Ubangiji Allah Ya raya mana zuria."
Na sake amsawa da Amin Ya Allah.
Ya yi shiru na d'an wani lokaci kafin ya cigaba da cewa." Duk abinda za a buk'ata fannin ci da sha za a yi order babu buk'atar a wahalar da wani sai dai akwai turaman atamfofi da Nabila ta yi mini tallansu gasunan na saya miki ki rabawa jama'arki."
Na sake godiya a ta'kaice kafin na ce.'' To abinda yake cikin kwalayen fa."
Ya d'an yi shiru kafin ya furta.'' Zannuwa kawai na saya a wurinta amma bari mu gani."
Ya fara neman lambarta tunda wayarsa dama tana hannunsa bugu d'aya ta shiga ta d'aga na ji suna gaisawa ya ce." Bayan zannuwan da na saya menene ki ka aiko yara da shi a akwali?"
Shiru ya yi yana sauraranta da yake can k'asa take magana ban ji komai ba. Sai da suka yi sallama tukkuna ya dube ni yana fad'in." Kin ji gudumuwa ta yi mana wai abin rabo ne duk wanda a ka bawa zani sai a sa masa cikin jaka mun gode ko?"
Na ce." Ka gode dai ai kai ta yi wa ba Amina ba. Ya yi shiru yana kallona na cigaba da cewa." Ka ce da ni soyayya kuke yi ba wai ka zaunar da ni kana kwantar mini da kai ba. Soyayya kuke yi a fakaice ka yi mata alheri ta yi maka zaka maye gurbin Maryam da ita ko ba haka ba ne."
Ya gyad'a kansa yana cewa.'' Sai ta iya kasancewa hakan ne amma ana ta 'bangaran fa wata'kila sona take yi."
"Kai kuma da ka gane hakan sai ka cigaba da biye mata tunda kana hangen jin dadi da nagarta a tattare da ita ko?"
Ya yi banza da ni kawai ya mike 'kafarsa ya kwanta tare da lumshe idonsa.
Na ce." Wallahi tallahi wannan abin ya ba ni mamaki da tsoro yanzu kai ba ka jin wani iri a jikinka.
Ya bude ido yana dubana kafin ya furta." Ba ni jin komai, kuma ba zan yi rigima dake ba a cikin mutane Nabila dai idan za ta sare kanta ta ba ni shi saboda so wallahi ba zan aureta ba. Idan kun ce tana sona ba zance a a ba, amma ni fa ba ni sonta ba kuma ni da niyyar auranta. Wannan maganar idan ba ku daina yi mini ita ba daga ke har ita Hauwa wallahi sai ranku ya 'baci tunda babu wadda ta haife ni a cikinku ina dalili ne za ku dame ni da wata Nabila."
Na ce." Kai zaka daina idan har kana so a daina yi maka maganarta cikinmu babu yaro k'arami da za ka yi wa wasa da hankali."
Ya furta." Zan daina amma ba zan wula'kantata kamar yadda kuke so ba wallahi, idan zan nemi aure a cikinku akwai wadda ta isa na yi wasa da hankalita, abinda Allah da Annabinsa suka halasta mini me yasa zan ji tsoron wata hallita wadda take da rauni kuma take a k'arkashin ikona........✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK.*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*163*
Share shi na yi ban 'kara tanka masa ba ba kuma don ba ni da abinda zan ce ba. Na tashi na sauka k'asa jikina babu wani karsashi ya rantse da Allah ya kara rantsuwa ba zai iya auranta ba to yaudararta zai yi kenan tunda shi ma zuwa yanzu ya gane sonsa take yi muddin bai fito fili ya nuna mata baya ra'ayinta ba za ta cigaba da bibiyarsa da zaman saurare daga gare shi tunda yana sayan kayanta yana kuma bata kudi yawanci mu mata wayayene shi yanzu ga abinda yake cikin zuciyarsa a game da ita duk da ba wai ya bankad'a mini zuciyar tasa ya yi na gani ba amma dai akwai k'amshin gaskiya a maganarsa don da ya na sonta da niyyar aure ba zai yi rantsuwa da Ubangiji ba tunda ya san girmansa. Shirunsa da yanayin yadda yake mu'amulantarta shine abinda zai k'ara mata kwarin gwiwa ta ji a ranta kamar buk'atarta za ta biya domin samun nasarar mallakarsa duk abinda take yi a kansa da wanda ya dangance shi sone ba wani abu ba.
Bandir din atamfofin irin mai sha biyu ce bandir shida kuma mabambamta ba duka iri daya ba ne, sun yi kyau sosai duka cotton irin 'yan dubu goma nan ne da ake ya yi idan za a yi ankon biki.
Duk abinda ya kamata da a yi na al'ada da fita hakki su anti Yagana sun yi hatta da atamfofin sai da suka d'ibarwa Hajja nata duk da ba ta yi wata gayya ba amma ai tana da jama'a a can garin Dambatta idan ta koma gida sai ta raba. Nama kuwa da aka soya zallar tsoka da yawa suka zuba mata cikin fanteka tace ya yi yawa Hajiya Saratu ma kad'an ta d'iba yayin da inna Uwani ta yi kamar ta dora hannu aka ta dinga rusa ihu ganin yadda Hajja ta ce da masu aikin su kwashe nama ta d'ibi daidai gwargwado. Hauwa d'anye ta kar'ba ba ta bari an soya ba ita kuma Inna Uwani koda anti Yagana ta nuna mini wanda ta zuba mata na ce ya yi kad'an ta 'kara ashe duk da haka ba a yi mata gwaninta ba ta ji haushi sosai saboda Hajja bata kar'bi naman da yawa ba ta bawa masu aiki.
Su kansu su anti Yagana sun samu soyayyan nama sosai fatar shanun na sanya aka gyara musu (Ganda) da kawunan suka d'iba Sahura ma ta d'ibi daidai gwargwado sannan sauran na sanya baba Tabawa zubawa a buhu biyu yan gidanmu Ummansu Hadiza gabad'ayansu dai da suka zo tare na ce idan sun je sai su yi rabon a tsanake a tamfofi kuwa kowacce sai da ta tsira da turmi shida duka cikin kowane bandir sai da kowa ya samu har da ragowar wasu. A ranar da muka yi walima k'warai na samu alherai masu yawan gaske daga wurin manyan mutane daga cikin abokanansa da suka samu. Kud'i kaman sai godiya yara sun samu kaya masu yawa. Babu shakka kowace haihuwa da goshinta don haka ni dai ba ni da bakin magana sai dai godiya ga Allah.
Washe gari masu aiki na ta hidimar gyara gidan ciki da wajensa. Su anti Yagana na ta had'a kaya don 'yan gidanmu ma su Ummansu Hadiza da sassafe suka d'auki hanya bisa bin umarnin Babanmu ya ce su taho lallai shi kuma maigidan ya yi musu shirin tafiya cikin mutunci da rufin asiri don da ya ji a motar haya suka zo ya yi fad'a sosai har yana cewa lefina ne nasan za su zo mai yasa ban gaya masa ba tun daga can ya sanya a kawo su ya fi nutsuwa.
Sahura na ta gyara mini wardrobe ita kuma Yusra na shiryawa yaran kayansu. Hauwa ta aiko Khalil wai na bata atamfa turmi bakwai jin haka Ya Falmata ta fara fad'in ba a d'ibar mata ba dama."
Sahura ta ce." Ni na d'ibar mata turmi shida cikin kowane bandir na d'auki daya."
Ta ce." To kuma wace atamfa za a bata."
Anti Yagana ta ce." Tunda da akwai a bata mana wata'kila wani zata bawa."
Yaron ya ce." E, na ji suna magana da inna Uwani za ta tafi da su can bauchi ta yi rabo."
Ya Falmata ta dube ni tana ta'be baki ban ce komai ba na ce da Yusura ta d'ebo abinda suka rage saura turmi sha uku gabad'aya na ce a cire bakwai din da suka buk'ata a bashi ya kai mata.
Bayan fitarsa Ya Falmata ta kwashe ragowar kaf katon kwalin da suka shirya kayansu a ciki ta watsa atamfofin tana fad'in." Ke ma kina dangi idan mun je gida za a ba su ke da haihuwa wata da iko da kayanki idan haihuwar biyu banza ne ta yi zuciya ta yi."
Sahura ta dinga dariya tana fad'in." Wallahi baiwar Allah nan Hajja tana burgeni suruka ce tagari babu ruwanta da sa ido akan duk abinda yake faruwa ki ga dai uban naman da a ka bata ta dibi kad'an ta bayar da shi. Hauwa da mamanta sai ka ce mayu ita tsabar rashin yarda ma d'anye ta sanya a ka kai mata gida kamar ita ta haihu."
Anti Yagana ta ce." Abu dai ya wuce alhamdulillahi an tashi lafiya wata matsala dai ba ta faru ba ni na gaji ma da zaman nan wallahi Ya Falmata tunda mun had'a kaya an jima muna yin wanka mu kama hanya."
Na ce." Sai dai gobe tunda ya fita kuma har yanzu bai shigo ba ai ba za ku tafi ba tare da kun yi masa sallama ba."
Ta ce." Bashi muke bin sa da sai mun jira ya dawo Amina."
Na ce." Duk da haka dai anti Yagana a bari ya dawo din ya fi mutunci."
Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba. Itama Ya Falmata din ba ta tanka ba maganar dai da take ta jaddada mini shine kada na yarda ya auri Nabila domin babu haske a cikin al'amarin. Yadda ta zafafa sosai abin har mamaki yake ba ni, kishi take taya ni sosai Hauwa ma don dai tana ciki ne muna tare da yaranta babu yadda za a yi da ita.
Ba su tafin ba kuwa sai da gari ya waye tara na safe sun fito lokacin Masa'udu ya kwashe kayansu tsaf ya kai mota su Hajja na d'aki ba su fito ba muka shiga tare muka same su ashe inna Uwani a gidan ta kwana duka muka gaisa cikin mutunci da raha. Ya Falmata tana fad'in." Bako zai yi halinsa Hajja mun yi shirin tafiya, mun gode sosai Allah Ya kara girma yara kuma Allah Ya raya su."
Ta dinga amsa da "Amin mune da godiya Allah Ya saka da alheri."
Tare da ni su gabad'aya muka yi musu rakiya bakin mota suka shiga Ya Falmata da anti Yagana ita Sahura sai gobe yadda muka yi da ita za su tafi.

****
To sati uku da haihuwa gidan na mu ya daidaita kamar ba a yi wata dabdala ba kowa ya watse an bar ni da yara da masu aiki kamar yadda muke a da. Hassan da Usaini basa zuwa hannuna sai idan yunwa ta kawo su suna can wurin Baba Tabawa da taburni da daddare ne kawai nake kwana tare da su, shima maigidan muddin ranar girkina ne sai dai ya sakko kasa ya same ni a d'akina.
A tsukin suka tafi saudiya umara shi da Khalil kamar yadda ya fadi ranar dana haihu. Sati biyu suka dawo a cikin satin kuma ya sabunta mini komai na gidan tun daga kasa har zuwa sama komai sabo da sabbin kayan kicin abin dai kamar wata sabuwar amarya. Hatta da kayan da yara suke sanyawa sai da aka fitar da su aka yi musu sabbi Taburni da Mairo sune masu iyali a kauye Kuma sune masu wahala da yarab na ce su kwashe suka kuwa cika manyan bacco suka ajiye da jiran lokacin ziyara tunda sun ce sai sallah za su ganin gida yanzu muna daf da shiga wataran Ramadan kuma

Please Login or Register in order to submit comment