Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ta sake faruwa yanzu kusan wata shida kenan cikina na da wata bakwai lafiyar Allah nake gudanar da hurd'odina babu nauyi irin nasu Hassan sannan laulayin da na yi ma takaitaccene a farkon samun cikin ne.
Babu wanda ya san ina sa juna biyu tsakanin anti Yagana da Sahura tunda ban gaya musu ba muna dai yin waya sa'i da lokaci.
Sai da Hadiza ta haihu tukkuna da su anti Yagana suka zo yan gidanmu suka fahimta lokacin ma ni kadai nake jin abinda nake ji nakuda ce nake yin ta a tsaitsaye Hadiza ta haifi namiji yaro lafiyayye mai kama da babansa sai ta dinga ba ni sha'awa wallahi ganinta ri'ke da jaririnta lafiya lau tiriri ya kare.
Kayan da Nabila ta had'awa su Hassan a lokacin haihuwarsu sama suna saman maigidan don haka ya ce da Sukairaju ya zo ya kwashe su suyi amfani da shi ya samu takwara domin kuwa kwana biyu da haihuwarsa ubansa ya yi masa hud'uba da Tajuden.
Yan gidanmu kaf sun halarci taron sunan Hadiza da yamma sai ga Hauwa da leda cike da kayan baby wai ai ta ji an ce yaro ya ci sunan maigidanta. Ta sake ana ta wasa da dariya da ita babu kuma wanda ya nuna mata komai ni kaina janta nake yi da hira yadda ta saki jikinta sosai ya tabbatar mini da cewa ba ta fahimci halin da nake ciki ba ni ma, ko da yake a zaune nake ba lallai ne ta gane komai ba.
Sai daf da magriba ta yi mana sallama ta tafi anti Yagana ta ce da Fati ta zazzage kayan da ta kawo a duba tsaf kada ta kunso wata jarabar ne. Na dinga dariya ina fad'in anti Yagana kenan.
Set din kayan jariri ne uku da turaruka masu tsada da wani takalmi mai ban sha'awa bayan mun gama gani Fati ta had'a kayan ta mayar da su cikin leda.
Sati biyu suka ce za su yi kafin su tafi anti Yagana kuma ta ce kwana biyu kacal za ta kara ta kama hanyar gidanta na yi na yi da ita itama ta zauna ta huta sosai kamar yadda su Fati suka zauna ta ce ai ita babba ce da kunya kada lalacewar ta yi yawa mazajenmu su daina ganin girmanta. Na ci dariyata kuwa na 'koshi mussaman da na tuna yadda suke yin wasan 'buya da maigidan tun musayar yawun da suka yi akan kamfani shi yana jin kunyanta itama tana jin nauyinsa.


Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biyani hakkina ba.

Aikuwa bayan tafiyarta da kwana biyar ciwon nakuda ya kama ni a gida ranar juma'a kaf kowa yana nan har yaran kuma da safe ciwon ya tashi ban fito daga d'aki ba na kira Dr Sailuba saboda dama tuntuni na yi nak'udata a tsaitsaya don haka zuwanta da minti ashirin da biyar na haihu lafiya lau yarinya mace ta dinga tsalla ihu da ya fargar da kowa Yara suka ki'dime suna murna Mama ta haihu Khalil ne ya ruga gidan Mamansa twin's kuma suka hau sama wajan Babansu bacci yake yi suka tashe shi da ihun murna Mama ta haihu.
Dr Sailuba ba ta bud'e d'aki ba kuwa sai da ta kammala komai ta gyara ko'ina amma still kusan awa guda da haihuwar yarinyar kuka take tsalawa har dai abin ya fara ta'ba ni na fara tambayarta anya lafiya ta ce mini lafiya lau don karon farko bata tsammaci matsala ba.
Tana bude d'akin suka dinga shigowa yan gidanmu su Fati da Hauwa da take jan kafa tsabar k'aduwa da tashin hankali kamar wadda ta yi targad'e a kafarta kallon farko da na yi mata na gane lallai akwai matsala domin duk yadda ta kai ga ganin ta gayyato dariya da annashuwa tasirin damuwar da ta tsinci a kanta a ciki ya danne abinda take kokarin gayyotowa duk wanda ya lura da ita zai gane cewa lallai a rikice take domin kayan bacci ne a jikinta da hijabin sallah.
Bakin kowa kamar audiga tun daga kan maigidan zuwa kan masu aiki yaran da 'yan uwanana sai murna da sambara suke yi don ma dai kukan da yarinyar ke tsalawa ya d'an rage karsashi da annashuwar shi ma ya fara tambayar Dr Sailuba babu matsala da confidence d'inta ta ce masa babu wata matsala lafiya ce. Hauwa ta kar'bi babyn hannunsa tana juyyata can kuma ta dan daga mata idanuwanta tana gwalesu sosai ta dubi ta d'aga rigar jikinta tana tatta'ba jikinta da hannunta sai ta dubi
Dr Sailuba tana fad'in." Ki duba sosai Dr kada ki dinga yin abu daka yarinyar nan bata da lafiya."
A d'an sanyaye ta kar'beta daga hannunta har zuwa lokacin kukan take tsalawa ta dan jima tana jujjuyata
Kafin ta dube ni da sanyi jiki ta furta." Za mu je asibiti domin dubata sosai kukan ya d'an so ya yi yawa sannan jikinta ya d'auki zafi akwai abinda nake zargi."
Gabad'aya ni da shi sai jikinmu ya yi sanyi muka dubi juna.
Ya yi saurin kar'be babyn tana tsala ihu ya d'an dubi Hauwa dake tsaye a gefansa itama shi take kallo karaf ta ce." Ku je asibitin sai a dubata gaskiya bata da lafiya." Na ga sanda ya wurga mata wata muguwar harara ya kawar da kansa cikin wani masifaffan yanayi da tashin hankali.
A takaice dai a ranar a asibiti muka kwana domin dai gado aka ba mu babban likita ya bincike mana ita tsaf sikila ce dole akwai buk'atar zamanmu a asibiti na wani lokaci domin kula da ita.
Tashin hankali wanda ba a sa masa rana. A daran ni da shi kuka domin dai da farko har na fi shi dauriya na dinga tausarsa da kawo masa misalai tare da gaya masa kada ya butulcewa Allah kada kuma ya nuna Allah bai yi masa daidai ba. Ya kasa jurewa hawaye yake d'igarwa domin dai bayanin da likitan ya yi mata babyn sikila ce sosai. Hauwa kuwa ta kira shi a daran sm da kyar na bashi baki ya d'auka don gabad'aya ba shi cikin hayyacinsa ban ji me take gaya masa ba sai gani na yi ya tashi tsaye jikinsa na wani irin kyarma yana ce wa." Ba ki kunya da nauyin gaya mini wannan maganar ba Hauwa." Itama na ji ta cikin 'karaji tana fad'in." In sha Allahu rabbi sai ta mutu da izinin Allah hakkina ba zai barka ba wallahi ba zan daina mi'ka kukana ga Ubangiji ba ai ba cikin haihuwar ne ba ni dashi ba ni ma, yarinya kuma nafad'a maririciya kuma mutuwa suke yi kada ma ku sanya rai a kanta domin mun ga haka ya fi sau d'ari.
Jikinsa ya cigaba kyarma da wata kaurarriyar muryar da ban san shi da ita ba ya furta." Ina ce sai ina auranki tukkuna zan kwanta dake ki samu cikin da za ki haihu shikkenan na sake ki Hauwa saki biyu babu wata dangantaka ta aure a tsakanina dake yanzu na sake ki saki biyu.........
Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

*A kar'ba da ha'kuri don Allah hakan tana iya faruwa da rayuwarsu ina fatan dai ba ku mance tushen labari ba. Sakon littafin gudun aure ya isa saura k'arashe in sha Allahu Ina mutukar godiya....*
*GARKUWAR MATA.✍️*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*176*
Na ji komai da kunne na babu buk'atar neman karin bayani ni gabad'aya ma abinda yake gabana lafiyar yarinyarta akwai tsananin damuwa da fargaba a ce ka gama goyon ciki da wahalhalunsa ka haife ka fuskanci wani k'alubalan na mussaman sai yanzu gane wannan shine babban dalilin da ya sanya likitoci suke iyakacin bakin kokarinsa wurin ganin sun dakile yawaitar haihuwar yaran da suke d'auke da wannan lalura. Doke ce a yanzu waliyya da mahukunta basa d'aura aure sai da shedar daidaituwar jini mussaman ga saurayi da budurwar da ba su ta'ba haihuwa ba akansu dai wannan dokar ta fi tsananta akwai sau'ki akan namijin da yake da iyali da kuma bazawarar da ta haihu a wani wajen tana da yara maslaha ce a tsakaninsu ko da suñ yi aure sai su d'auki matakin gujewa samun ciki. Duk da yake duk tsumi da dabara ba a isa a yi wa Allah wayo ba wahalar dai da tiri-tirin shine abin gudu. Na haihu ina murna ban ta'ba tunanin zan sake haihuwar sikila ba ganin na jera haihuwa har sau biyu lafiyarsu lau gabad'aya ni da shi tunda aka samu cikin yarinyar nan ba mu ta'ba zama mun tattauna mas'alar da za ta iya kasancewa a rayuwarmu ba saboda duka tunaninmu daya wata'kila Allah ya d'auke mana tunda mun yi sau biyu a jere dukkaninsu lafiya lau. Sanin gaibu sai Allah kuma duk abinda ya tsara shine daidai kuma dole a yi godiya gare shi. Lamarin Hauwa kuwa gabad'aya kaina ya kulle na gaza kuma na yi rauni akanta domin duk kaifin tunanina k'wakwalwata ta kasa hakaito mini a wane mizani zan ajiyeta a bayyane komai yake bata da abokiyar gaba sai ni kuma a duk lokacin da sarki Allah ya bata sa'a a kaina don ta d'auki makami ba wani abu ne.
Asibitin na mussaman ne don haka da gari waye Baba Tabawa kawai na ce masa a kawo mini na kuma kira Fati a waya na ce ta had'a mini kaya da duk abinda zan buk'ata tunda ba su tafi ba suna nan likitan dake tsaye kan yarinyar ya bada tabbacin kan cewa a k'alla mu yi sati ko kwana goma kuma alhamdulillahi kwana daya kacal da muka yi yarinyar ta sassauta kukan da take yi zafin da jikinta yake d'auka ma ya yi sau'ki ta kuma samu bacci. Hakan ya sanya shi tafiya gida domin yin wanka tunda tare muka kwana cikin tararrabi da zullumin abubuwa masu yawa ya dinga ba ni tausayi daga zarar na daga kaina na dube shi hakika Allah ba yadda baya aiwatar da ikonsa a kan bayinsa. Ya yi addu'a akan samun haihuwa kuma diya mace wadda ya nema a wurin Allah Ya amsa masa sai kuma ta zo a maririya mai rangwamin lafiya wannan ma jarabawa ce me zaman kanta amma godiya ga Allah itake nuna cikar munini tunda ai akwai ma'auranta da duka yaran nasu suke kasancewa da cutuka mabambamta kuma daya bayan d'aya ya d'aukesu su koma gare shi bayan iyayen sun sanya rai kuma ba su gaza ba wurin nemo musu magani da kudi da lafiyar jikinsu. Ubangiji ta kowace suffa ya kan jarrabi bayinsa wanda yake so domin auna imaninsu. Da wad'annan nasihun na d'an samu kansa amma ko bayan wannan nasan damuwar ai tana jika dalilin abinda Hauwa ta yi tamkar ba jininsa ba k'iyayyar ta munana ta kuma tsananta Allah ne mai rayawa kuma shine mai kashewa shi ya ba mu don ya kar'ba ai ba mu da abinda za mu yi tunda mu da muke zaune a duniyar zaman jiranta muke yi. Wannan shine kawai abinda na bari a zuciyata maganganun Hauwa akan yarinyata ba su razanar da ni ba, musulmace ni dole kuma na yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau. Haihuwa ya ba ni ya sake ba ni ya ba ni ta mussaman wadda ba kowa ke da baiwar ba har sau biyu masu lafiya rayayyu guda shida yana kuma raya mini su cikin aminci da kulawarsa da kuma tarbiyarsa babu abinda zan ce da shi sai godiya kuma duk abinda ya zartar daidai ne.
Da Baba Tabawa muka kasance a asibitin tunda gaskiya akwai tsaro sosai ba su barin wannan shige da ficen itama saboda maigidan sananne ne yana kuma da alfarma ya sanya suka barta ta zauna. Alhamdulillahi cikin kwanaki hud'u abubuwa sun yi sau'ki ta daina duk abinda take yi tana kuma kama nono ta sha cikin nutsuwa ta yi baccinta da kwanciyar hankali. Muka samu nutsuwa ni da shi mussaman da likitan yake jaddada mana cewa muddin an kula an kiyaye komai kan ka'ida ciwon ba zai dinga motsa mata ba a kai-kai.
Kwananmu takwas muka dawo gida. Ya zama kamar kufai shiru babu hada-hada ta yara duk suna ma makaranta masu aiki Mairo da Taburni na kicin Hassan da Usaini na bacci bayan wankan da aka yi musu shi kuma Sultan na tare da su a kicin.
Na kira Hadiza a waya na gaya mata na dawo cikin kasa da minti ashirin sai gasu gabad'ayansu suka kewayeni duk babu wata annashuwa a tare da su babyn tana ta bacci babu halin d'aukarta domin dai likitanta ya bada umarni hakan kada a yawaita jagwalgwala mata jiki sai dai ido kawai Fati take tambayata da wane suna za a dinga kiranta tunda wai Sukairaju ya gaya musu sunan Hajja ne da ita na ce Mufida haka babanta ya ce a kira ta.
Yini muka yi tare da su har yaran suka dawo daga makaranta ganina a gidan ya sanya su shiga tsananin murna hankalinsu gabad'aya nakan babyn sai sun d'auketa Minal har da kuka sai da na kira Mairo tukkuna na ce ta ja ta su fita domin wani irin ciwon kai nake yi kukan da take yi kuma yana sa'bata da yanayin yadda duk na gansu cikin damuwa mussaman Khalil duk jikinsa ya yi sanyi na kasa gane shin akan menene ba ni tsammanin ubansa ya gaya masa ya saki uwarsa sai dai idan ita za ta gaya masa kuma ba na tsammanin ta tafi tana gidanta tunda na ji lokacin da yake magana da Mairo yana gaya mata sakon Ladidi tunda k'awarta ce idan Hauwan ta aikota sukan dan jima suna hira akwai wani k'aramin gari a cikin bauchi mai suna giayade anan cibiyar iyayensu take duk da ba su had'a wata dangantaka ba hirar yau da gobe ta sanya suka fahimci garinsu daya.
Washe garin ranar da muka fito Hajja da yayarsa suka dira dama ya gaya mini shine ya dakatar da su tunda ko sun zo muna asibiti ganin hakan ya sanya ni ma na hana anti Yagana zuwa tukkuna can gidanmu ma haka na gayawa Babanmu a waya cewa su bari sai mun fito Sahura kuwa kusan kullum sai mun yi waya.
Sai dare tukkuna muka samu ke'bewa Hajja fadi take yi Hauwa abinda ta yi muku Amina Allah Ya yi mata ba zan yi mata baki ba ba kuma zan nunawa duniya Tajo ne nawa ba amma da wahala ta sake yin katari da namiji da abokiyar zama kamarki zahiri kin yi iyakacin bakin kokarinki wurin ganin kin kawo daidaito a tsakaninku kin yi bajinta kwarai kuma kin yi da jiki da aljihunki a tarihi ban ta'ba ganin kishiya irinki ba Allah ya biya ki da aljanna Ubangiji Allah Ya dubi rayuwarki. Wad'annan yara kuma ina yi miki addu'a akan Allah Ya ba ki wuyan d'auka Allah Ya raya mana su.
Na dinga amsawa da Amin Amin amma bayan haka ban iya furta komai ba akan abinda suke tattaunawa Hajiya Saratu tana ta fad'a akan zaman da take yi tunda an yi ta ta kare babu wata sauran igiya zaman me take yi kuma har tana fad'in da safe za ta je gidan ta ji dalili babu sauran wani mutunci da zumunci a tsakaninsu tunda har ta iya rufe idonta ta yi wa dan uwanta wannan cin fuskarsa. Gaskiya ne a wannan ga'bar takai-takai kawai ake yi kowa nasa ya sani domin kuwa abinda ita Inna Uwanin ta nuna kenan. Wannan karon Hajja ta saki ragamar hannun yaranta ai kuma magana ta 'kare babu sauran gyara babu amfanin zamanta a gidan ta kama hanya ta tafi yara kuma ta bar su a gidan ubansu.
Da wannan suka rufe maganar ni dai magana akan Hauwa ta k'are a bakina domin ban san abinda zan ce ba ta gama goge mini hadda ta tilawa.
Aikuwa kamar yadda ta kwana da al'amarin garin Allah Yana waye wa ko karyawa ba ta yi ba ta nufi gidan Hauwa. Ni dai Ina d'aki da yake kofar a bud'e take saboda yaran sun shigo mini kafin su tafi skull na ji fad'anta a falo har ina tsinkayar muryar maigidan. Fadi take yi zaman nata ai bashi da wani amfani ban kuma yarda da abinda ta fad'a ba wai juna biyu gareta ko za ta tafi sai a bari ta haihu tukkuna shin kai ka san cikin ne da ita. Cikin rashin karfin sauti na ji maganarsa amma ban ji abinda yake cewa ba. Na yi zuru ina mamaki cikin da take ta ha'kilo a kansa shin tasan dama tana dashi ta yi wannan rashin mutuncin ko kuma dai karya take yi don kada ta tafi ne. Wani sashi na zuciyata ya dinga gaya mini karya take yi da tana da ciki da kowa ya sani tunda abinda take nema ne kenan kuma ba zata zafafa bakincikinta ba.
Can wajan minti ashirin da biyar a tsakani na dinga jin kuka kasa k'asa da maganganu suna tashi sai da na kasa kunne tukkuna na gane muryar Hauwan ce take wani irin kuka mai cin rai Hajja tana ta yi mata magana akan ta yi shiru amma sai kara karfin kukan take yi. Cikin babban sauti na ji muryar Hajiya Saratu tana cewa kan ki kika tonawa asiri Hauwa ba mu za'bi Amina ba saboda muna 'kin ki. Mun za'bi kyawawan halayenta ne da kuma biyayya amma tunda yanzu magana ta kare babu buk'atar a yi ta maimaitawa sai dai addu'ar Allah Ya fitar da sakamako da gaggawa a tsakaninku wanda ya cuci wani sai Allah ya saka masa ba mu da wata hanyar gyara kuma babu wata mazahaba da za a bi saki ukun ai ba a lokacin daya ya yi miki su ba an yi daya da farko ya zo ya maimaita miki biyu saboda haka baki fara yin nadama ba Hauwa kuma muna nan ba za mu fasa addu'a ba idan shi ya cutar dake kamar yadda kike yawaita fadi Allah Ya saka miki.
Saboda irin bud'e wutar da Hajiya Saratu ta yi a gidan sanya kowa jikinsa ya yi sanyi masu aiki kaf ba su fito ba domin sun jima a falon suna musayar yawu tana ta jaddada mata 15m din da take tunanin maigidan ne ya bata to ba shi ba ne ni ce hakan ya kara tsananta kukanta ina daga d'aki ina Jin gurnaninta cikin tashin hankali kamar wadda ke shirin tayar da sarkin aljannu.
Shi gabad'aya ma bai sauko ba balle ya tanka takaici da b'akinciki ya na ta nukurkusarsa. Babu arziki Hauwa ta kama hanyar garinsu jin zafafan kalamai raddi masu kauri da jefa zuciya cikin rud'ani
da bala'in yanayin da ba zai misaltu ba dama aka ce duk wanda ya ce tukunyar wani ba zata tafasa ba tabbas ta shi ko d'umi ba za ta yi ba.
Washe gari Nusaiba ta zo mini da yaranta kaf muka yini tare su kuma su Fati suna jiran zuwan anti Yagana tukkuna don ba su kai ga tafiya ba.
Kwana biyu a tsakani ta iso da yamma kuma matan gidanmu gabad'ayansu har da Babanmu da Baba Sule suka kwana da yamma suka yi shirin tafiya gabad'aya amma ban da anti Yagana saboda na ce ta bari tukkuna sai nan da sati d'aya
Yaran shop's dina har da securities din dake gadi a wajan Lawan ya jagorancesu a daran da su Fati suka tafi muka jima da suma muna tattauna cigaban da ake samu koyaushe.
Haka na dinga samun baki daga wannan sun tafi wasu za su zo Sahura ita kadai ta zo mini wannan karon Yusura ta sake samun ciki sai kawai na ganta da yarinya jale-jale tana koyar tafiya yarinyar Idiris ce uwarta ta cire ta daga nono lokacinta bai cika ba ta yi aure a cewarta baya kawo kudin abincinta iyayanta suka ce ta cire ta daga nono a kai masa 'yarsa suka kawota suka dire babu Imani uwar ta tafi ta yi aure. Mai shegen k'iwa da rashin yarda saboda tsabar bala'i lallai Sahurar ba zata huta ba ko uban da ya haifeta bata yarda dashi balle danginsa ta ma'kale mata na dinga mamakin wannan lamari kwatankwancin abinda Minal take yi mini yanzu ko wurin aiki da ita take zuwa Hajja kuwa sai 'kara mata karfin gwiwa take yi tana fad'in kada ki sare kada ki gaji wata'kila zata ji kan ki da d'a da dukiya ba a yi musu mugunta.
Muna tare da su tsayin kwanaki uku babu irin batutuwan da ba mu tattauna ba abinda Hauwa kuwa ta aikata ya yi bala'in ba su mamaki amma jin irin hukuncin da maigidan ya yanke a kanta ya sanya zuciyoyinsu suka yi sanyi.
A ranar da suka shirya tafiya wasu bakin suka dira Hamusu da Usaini kowanne da iyalinsa sai kuma Yusi da Saminu. Hajja kuwa ta samu 'kawa 'yar gidan Usaini mai sunana kenan itama suna kiranta da Minal ta dinga tsokanarta da faratu haske ne da ita kau har ta so ta fi ubanta haske Hajiya Saratu na tsokanar Hajara kamar ba goyonta ba, ita yarinyar ashe mahaifiyar Ummansu Saminu ta d'auko domin duka hasken fatar ta gada musu duk da ta tsufa amma tana nan kar kar da ita Fulani ne na asali.
Kwana biyu da zuwansu Yusi yake gaya mini Kamalu daf yake da dawowa gida domin sun yi magana da shi a cikin satin da ya wuce na ce bai gaya mini ba duk da kuma mun yi magana da shi kwana hud'u da suka wuce ya dai tabbatar mini da cewa daf yake da ya kammala abinda ya kai shi amma bai fada mini ranar da zai dawo ba, amma ba na mamakin kan cewa ya sanar da maigidan tunda kusan ya fi sakewa da shi fiye da ni.
Kwanaki biyu a tsakani suka tafi Hajiya Saratu ma ta riga Hajja yin gaba domin ta ce ita zata zauna ta kwana biyu tukkuna har na ji Yusi yana tsokanarta wai sai ta taso sun tafi haka yake janta da tsokana irin wadda ma bai yi wa Gwaggo irinta ba tsakanin Yusi da Hajja akwai amana da kuma 'kaunar juna har da rantsuwa wai gidan babu dad'i idan bata nan ta ce masa ba wasu kwanaki za ta yi da masu yawa ba. Shi kam babu halin zama makaranta ga kasuwa ba ma shi da ishashen lokaci na kansa.
Hajja ta sake sosai da jikokinta tana jan su a jiki da wasa da dariya har dai suka sake tunda sun gano cewar kakarsu ce wadda ta haifi Babansu idan suna gidan karad'insu kad'ai ake ji a falo tana ta biye musu Baba Tabawa na yi musu dariya. Minal ce take ma'kale da ni da Mufida suna dawowa daga makaranta a wasu lukutan ko uniform ba ta zuwa ta cire za ta same ni a d'aki ta'ba nan ta'ba can ta yi ta han'koro ita lallai sai na bata k'anwarta. Cikinsu har khalil babu wanda ya taba daukarta sai dai gani daga nesa Babansu ya ce ko za a ba su sai ta kara wayo tunda ga abinda likita ya ce kuma alhamdulillahi ta yi lafiya tana shan nono sosai ta yi baccinta na rana da dare babu kuka mai zaburarwa sai dai tak'aitacce dalili duk wasu sharad'ai ina bi yadda muka yanke ni dashi rainonta yana hannuna duk rintsi babu buk'atar taimakon masu aiki gudun yin abinda zai sa'ba da lafiyarta.
Yau kwananmu talatin da tara ya kama saura kwana daya kacal mu yi arba'in ina toilet na din ga jin kukanta a gaggauce na fito da sauri na riski Minal kane-kane saman gado tana ta cakumarta da wannan rawar kan nata. Tsawa na yi mata irin wadda ban ta'ba yi mata irinta ba ta kuwa zabura da sauri ta juyo tana kallona wanda ya yi daidai da shigowar Khalil na cigaba da Fadin." Ba ki jin magana ko, na ce ki bari zan baki ita ba yanzu ba tukkuna."
Ta cire hannunta da sauri daga kan towel din Khalil da sauri ya dube ni yana fad'in." Mama me ta yi mata?"
Shiru na yi ban ce masa komai saboda kwanaki ya daketa akan haka alokacin da ta taba yun'kurin aikata abinda ta yi a yanzu. Na nufi yarinyar da

Please Login or Register in order to submit comment