Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba to ku daina kallonmu, ko mun yi kama da tibi ne.''
Matashiyar mai aikin da take jigila da su tana dariya ta furta." Ke Hassana ku zo ku gaisa Mama ce fa."
Na ce." A'a rabu da ita kada ta zo mu gaisa ta tsaya." Usaina ta fito daga kicin da shafceciyar wuk'a a hannunta tana fad'in." Mairo ga wukar ki yanka mana." Shiru ta yi tana kallonmu yayin da mai aikin ta je ta da sauri ta kar'bi wukar tana fad'in." A can sama fa na d'orata yanzu Usai sai da ki ka d'aukota."
Ba ta ce mata komai ba ta nufo wurin da muke zaune tana zuwa sai ta dora kanta a cinyata tare da zura yatsanta babba a baki tana tsotsa. Na yi shiru ina sauke ajiyar zuciya yayin da na d'ora hannuna a saman kanta.
Ganin haka ya sanya Hassana da sauri itama ta zo ta yi yadda Usainar ta yi dama tuntuni Kamalu ya gaya mini kishi ne da su, duk abinda daya tayi to babu shakka yar uwata ma sai ta yi. Da hannu na yi wa Minal alama ta zo wurina. Ta kuwa taho kataf-kataf domin yanzu itace take tashen ki'ba a cikinsu. Na ri'keta sosai Ina fad'in." Ina Khalil yake?" Cikin yanayin maganarta ta furta." yana can gidan anti Nusaiba."
Baba Tabawa sai murmushi take yi tana jan su da wasa. Hassana da Usaina iyayen miskilanci ne, Minal din ta fi su sakin fuska da son mutane. Tunda suka dora kawunansu saman cinyata babu wadda ta dago sai da suka ji muryar Babansu tukkuna.
Tare suka fito da Momin kallo daya na yi mata gabobin jikina suka shika wata irin rama ta yi mai ban tsoro kanta yana nema ya rinjayi gangar jikinta abinka dama da siririya idanuwanta sun yi kuru-kuru ta d'ashe k'warai da gaske ta yi fau, babu shakka babu k'arya a cikin lalurarta yadda mijinta ya dinga jadadda ciwon ya ci karfinta yanzu na sake gazgata kammaninta duka sun canza ta hadu da ciwuka masu hatsarin gaske sugar da hawan jini.
Ta zauna tare da taimakonsa suka zauna kujera d'aya yana dan gyara mata 'kafafunta ko daga inda nake zaune Ina kallon yadda jikinta yake rawa.
Ban ji haushinsa ba ko kad'an domin a yanzu dai babu maganar kishi ga matar da take cikin irin wannan yanayin na halin ciwo mai tsanani. Ta dinga fara'a a zahiri tana nuna jin dadinta. Muka gaisa cikin kulawa da mutunci. Na yi mata sannu da jiki haka zalika ma baba Tabawa ta dubata sosai. Ta dinga dariya ganin yadda twin's suka yi mini farincikinta ya kasa 'boyuwa ta ce." Ai maigidan yake gaya mini ba ku ji labarin na kwanta a asibiti ba, ku yi hakuri don Allah da yake ni kaina lokacin ba ni hayyacina sai da na kwana na yini tukkuna na fara gane wanda yake kaina. Ko da na tambayi Nusaiba da Nabila shin an sanar daku suka ce mini eh sun sanar daku halin da ake ciki, na gode sosai Amina Allah Ya bar zumunci."
Cikin nutsuwa da kulawa na ce." Allah Ya sawwa'ke yasa kaffara ne amma maganar gaskiya babu wanda ya gaya mana cewa baki da lafiya balle mu ji cewa kin kwanta a asibiti na tsayin wannan kwanakin." Na yi shiru Ina mayar da numfashi kafin na cigaba da cewa." Tabbas da mun sani me zai hana mu zuwa asibiti mu duba ki, babu niyyar wulakanci ko kuma nuna wariya a tsakaninmu dake kuma ciwo ake ce kin ga kuwa lalura ta kori komai, Ubangiji Allah Ya sawwa'ke, Hauwa ta ce a duba ki da kyau kuma tana yi miki sannu da jiki itama kwana biyu da yake ta yi nauyi sosai ba ta jin dad'i ne."
Yanayinta ya nuna alhini da damuwa a zahiri abinda ta nuna kenan. Sai ta gyad'a kanta a hankali ta ce." Babu komai Amina komai ya wuce kuma na ji sau'ki sosai wallahi sai dai rashin 'kwarin jikin da yake d'an damuna yanzu, a cewa da Hauwa ina amsawa Allah Ya raba lafiya."
Na ce." Za ta ji in sha Allahu rabbi."
Tun kafin mu yi sallama take yi mini godiya har sai da jikina ya mutu tsabar tausayin halin da take ciki. Mairo ita ta janye yaran ta tafi dasu tana yayyanka masu mangwaron da tun farkon shigowarmu suke he rigima a kansa....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *2k ON TALGRAM*
*VIA 0542382124... BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*V-VIP AREWAPEN*
*Wsp Gruop 1k*
*103*
Duk abinda muke yi bai ce mana komai ba, mun dai gaisa amma tun bayan gaisuwar bai sake magana ba, sa'i da lokaci dai yakan amsa waya idan an kira shi.
Misalin takwas da wani abu muka fito daga gidan tun a hanya muke alhinin yanayin da muka risketa Baba Tabawa dai kasa daurewa ta yi a hanyarmu ta shiga gida ta fashe da kuka da sauri tasa gefan jihabinta ta rufe fuskarta . To ni ma dai kukan zucci nake yi domin na shiga rud'ani ba karami ba ganin yadda Allah Ya mayar da baiwarsa. Idan kudi na sayan lafiya nasan da ba wannan maganar ake yi ba. Wannan da duniya ta yi mata sheda cewa mutuniyar kirki ce wadda tun a duniya mijinta ya ce ya yafe mata itace cikin irin wannan yanayi to ina ga wanda ya shure umarnin Ubangiji kuma, Ubangiji Allah kasa mu dace Amin.
A haka muka shiga gidan Hauwa na kwance saman kujera 3str tana kallo abinta. Ganinmu sukuku ya sanya ta tashi zaune tana tambayar lafiya.
A takaice na ce." Lafiya lau." Na shige d'aki domin yadda kafafuna ke rawa ba zan iya tsayuwa a wurin ba. Na zauna gefan gado tare da rafka tagumi wani abu ne ya zo ya tsaya mini a wuya na tsananin fargaba da tashin hankali mace ta koma sai kace mai cutar kanjamau! ko mai farfadiya sai an rirriketa. Hawaye suka fara sauka a kumatuna. Haka kawai na ji duniyar ta fice mini daga raina gabad'aya.
Shigowarta ya sanya na daga kaina na dube ta. Ta zauna gefana babu babu fallasa ta ce." Ashe kema kukan ki ke yi Amina." Sai ta sa dariya kafin ta cigaba da cewa." ga Baba Tabawa can ma tana yin nata, ni kam matar nan ko dame take yawo wallahil-azim kurwata tafi tata d'aci, wallahi ni zan yi maganinta."
Na gyada kaina ina ko'karin ture kutittiran abinda ya tsaya mini a wuya na ce." Hauwa k'ullaci da tsananta gaba da k'iyayya wallahi babu inda zai kai ki sai tashar dana sani. Matar nan dai duk rashin Imanin mutum ya ga halin da take ciki sai ya tausayata mata don Allah mu dinga sassautawa kanmu Hauwa."
Ta ja tsaki tare da furta."lalura fa kowa yin ta yake yi, wallahi na fita jin jiki, ni mai yasa ban lanjare ba, saboda ba ni da hakkin kowa a kaina, ita kuwa bari na gaya miki abinda ta shuka ne take girba tun a duniya hakkin mutane ne wallahi."

Na jima ina kallonta tare da auna maganganunta. Yadda take tabbatar da abinda ba ta da tabbas akai shine abinda ya fi daga mini hankali da lamarinta. Wace irin kiyayyace wannan. A ganina wannan abin da take yi jahilci ne tsantsa da rashin sanin abinda ya dace. To ba ni da bakin magana domin kuwa yadda ta yi nisa irin haka babu wani kalami da zan yi mata ya sanya ta sassauto daga irin kiyayyar da take yi wa matar nan wadda alherenta suke dabaibaye damu bakidaya.
Ganin ban ce mata komai ba ya sanya ta tashi tana fad'in." Matsantawa kai ne kawai kowa ya kashe wutar gabansa. Shi kuma ai hakkin rai tun a duniya Ubangiji yake fitar da shi wallahi tallahi yanzu ta fara gani.

Sai kawai na saki bakina ina kallonta har ta fice daga d'akin ban d'auke idona ba.
Na jima a zaune Ina tufkewa da warwarewa kafin na tashi jiki a sabule na shiga bandaki domin watsa ruwa a jikina. Gabad'aya cikina ya cushe babu dandano a bakina ko kad'an yunwar ma sam ba na jin ta, daga zarar na tuna halin da muka riski matar nan a ciki sai hankalina ya tashi.
A haka na shirya cikin kayan bacci ina tsaye gaban madubi ina busar da gashin kaina. Ya turo kofar d'akin ya shigo. Ban yi zaton shigowarsa ba. Muka had'a Ido ya nufo wurin da nake tsaye daf da ni ya tsaya na gama abinda nake yi yana ta kallona ta madubi na juyo kirjinmu ya hadu waje daya. Kusan a tare muka sauke ajiyar zuciya. Ya riko hannuna muka zauna gefan gado. Yanayin fuskarsa kadai shi ya nuna mini cewar ya ji dadin abinda na yi. Ya furta." Kin kyauta sosai kuma na ji dadin abinda ki ka yi, idan haka kuke yi mini kara akan abinda nake so mai zai sanya ni ma na 'bata muku ai babu abinda ya fi zaman lafiya dadi ko."
Kanzil ban ce masa ba. amma maganarsa ta d'an dake ni wato shi baya jin nauyin gaya mana irin son da yake yi wa matar nan tasa.
Ya d'ora hannunsa a tudun kirjina wanda tun zaman da muke yi a wurin hankalinsa yake kai. Ya nisa kafin a kasalance ya furta." Momi ba ta da lafiya Amina cikinta da wajenta wallahi, tausayinta nake ji sosai domin lalurai sun gama dabaibayeta."
A nutse na furta." Allah Ya yaye mata, da sauran al'ummar musulmi."
Ya amsa da Amin kafin ya dora da cewar." Kin san yanzu wani result din ya sake fitowa bayan gwajin da aka yi mata satin da ya wuce cancer bakin mahaifa."
Da saurin gaske na dube shi. Ya gyada kansa "Wallahi ni kaina na kad'u Amina na tausaya mata k'warai da aniya yanzu haka za mu yi booking domin zuwa india akwai kwararrun likitoci a can da za su caje mini ita sosai."
Jiki a masifar sanyaye na furta." Tabbas Ubangiji shi yake saukar da ciwo ya kuma saukar da maganinsa, ina yi mata fatan alheri tare da addu'ar samun lafiya madawamiya, kai kuma Allah Ya baka ladan jinya."
Ya sake amsa da "Amin Ya Allah." D'akin ya d'auki shiru har yanzu hannunsa na saman kirjina yana dan tattabawa. Ban hana shi ba kawai dai ina mamakinsa ne a ganina yanayin alhinin da yake ciki da damuwa akan rashin lafiyar maid'akinsa bai kamata a ce wani abu na jin dad'in duniya yana bijiro masa ba, to mai ma zai fahimta bayan yana cikin tashin hankali a haukana fa kenan
Na dube shi yana lumshe idonsa kamar wanda ya samu audiga na dan ture hannun nasa muka kalli juna a sa'rke na ce." Dama ina son magana da kai."
Kai tsaye ya furta." Idan har akan zuwa maiduguri ne to kada ki bata bakinki babu inda zakije....

Na kudi ne littafin don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na ce." To saboda me, kafi kowa sanin matsayin anti Yagana a wurina ko?"
Ya gyad'a kansa a tsanake ya ce." Da dai ban rantse ba ne sai na bari ki je, amma wallahi na riga na rantse ki yi hakuri bayan bikin sai ki je ki ga d'akin amarya."
Zuciyata ta dinga tiriri na dinga danne abinda yake yun'kuro mini domin ba ni son na nuna masa damuwata a kan haka a gaba ya samu abinda zai k'untata mini idan wata matsalar ta faru a tsakaninmu. Na gyada kaina tare da furta." Shikkenan mu ajiye wannan maganar ina so ka gaya mini matsayin zamanka da Hauwa a gidan nan, domin ni har yanzu na kasa gane abinda kuke nufi da kai da ita."
Ya dube ni sosai kafin ya ce." Ke ina ruwanki kuma?"
Na ce." Ni ce kuwa nake da ruwa tunda duk wata mas'ala da kuka samu da kai da ita a kaina ne, yanzu a matsayinka na babba mai hankali da jagoranci abinda kuke aikatawa daidai ne."
Ya ce." Ai taki ta amince da cewar ta yi lefi, sannan taki ta bi umarinina idan tana so magana ta shige mai yasa bata biyo ki zuwa duba Momi ba. Ta cigaba da zama a haka duk ranar da ta gaji sai ta nemawa kanta mafita."
"Gaskiya hakan ba daidai ba."
Ya 'bata rai yana fad'in." To nuna mini daidai Amina."
Shiru na yi ban sake magana ba. Ya ja tsaki yana fad'in." Na yabe ki sallah za ki kasa alwala, Hauwa ai ba yarinya ba ce idan tana son zama da ni ta ba ni ha'kuri ta kuma bi umarina."
Na ce." To ai kaine babba ha'kurinka shine zai fi rinjaye."
"Na yi iya wanda naga zan iya yi a kanta Amina, wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe, kada ki sake titsiyeni akan lamarin Hauwa ko ni din sa'anki ne?"
Shiru kawai na yi Ina kallonsa. Ya cigaba da ce wa." Dangane da maganar kwanan aure kin ga Momi bata da lafiya ya kike ganin za a yi?"
Na ce." Yadda muke yi mana."
Sai ya yi shiru yana tunani kafin daga bisani ya furta." Shikkenan sai a cigaba da tafiya a hakan, zan kwana biyu ban koma legos ba, domin idan na kai ta asibitin na dawo zan dan jinyaceta."
Uffan ban ce masa ba, ya tashi tsaye yana kallona cikin sigar kulawa ya furta." Ki same ni a sama zan shiga in yi wanka." Ban iya ce masa komai ba har ya fita daga d'akin Ina zaune zuciyata ta kasa tsayuwa wuri d'aya.
A daran na gurzu a hannunsa k'warai da gaske kamar wata sabuwar amarya sai da na yi ruwan d'umi domin kusan sau uku ya yi mu'amula da ni. Farkon dare da asuba bayan ya dawo daga sallah. Still Yana gama breakfast nan ma ya sake yin wani haka na sauko daga saman a galabaice. Na yini ciye ciyen kayan da zasu saukar mini da ni'ima domin na tabbatar da cewar a wannan daran ma ba zai daga mini kafa ba..

***
Bayan kwana biyu da misalin biyar na yammar ranar talata muka yi ba'kuwa a gidan. Hajiya Aziza sunanta matar abokinsu ce Alhaji Sulaiman duk dai abotar tafi karfi tsakaninsa da Alhaji Amadu mai rasuwa dalili shi da girmansu suka hadu ba abotar kuruciya ba ce. Sai bayan rasuwarsa tukkuna abotar ta maye gurbi akan shi da yake ba ni labari. Uwargidansa ce kuma tare suke da maigidan sun zo duba jikin Momi ne tunda ko bayan rasuwar Alhaji Amadun suna yin zumunci dalilin da ya sanya ma kenan Alhaji Sulaiman din yake binbinin abotartasu ta yi karko kamar yadda ta yi da Alhaji Amadun. Shigowarta kenan ya kira wayata ya yi mini wannan bayanin wai ta ce za ta shigo ta gaishe mu kafin su tafi yanzu shi suna tare da maigidan nata a can gidan Momin.
Na ce masa in sha Allahu babu matsala. Sosai na marabceta na sanya Baba Tabawa ta kawo mata abinci tana fad'in a 'koshe take ta ci abinci kafin ta fito nace ta daure ta sanya mini albarka.
Hauwa ta fito suka gaisa sama-sama cikin rashin sakewa ta koma dakinta. Na kira Baba Tabawa domin ta zo ta kwashe kayan abincin da ta jera wanda kad'an ta ci daga ciki. Duk da babu sabo a tsakaninmu amma na lura tana da kirki kuma ta girme mu gaskiya zata iya yin sa'a da Momin ina tambayarta yara ta ce suna nan lafiya biyu suna d'akin mazajensu kenan ta auran da yara biyu akwai hud'u a gida uku maza sai 'yar autarsu mace. Su uku ne a wurin maigidan ita ce Uwargida.
Ta ce." Ai na ga yaran a can gidan Hajiya Maryam twins sun yi wayo sosai sun zama 'yan mata, Ubangiji Allah Ya yi musu albarka."
Na amsa da amin Ya Allah, ai kam duk sun yi wayo."
Ta gyada kanta da d'an murmushi a fuskarta kamar wadda aka tsikara ta ce." Allah dai ya sawwa'ke abinda ba zai shige ba ni Hajiya Aziza."
Kallonta na yi ban ce komai ba. Ta sake yin murmushi kafin ta ce wani abu kira ya shigo wayarta tana d'agawa na ji tana fad'in." Halisa har na fito ma daga gidan, a alhamdulillahi jikin nata da sauki wallahi, eh na gaya mata sa'konki ta ce ta gode." Ta yi shiru tana sauraranta kafin ta ce." To ya za a yi lalura aka ce fa Halisa kin kyauta ai Allah ma yana son masu wannan zuciyar irin taki Ubangiji Allah Ya sa mu fi karfin zuciyarmu."
Daga can ta amsa da Amin kafin su yi sallama da juna ta dube ni tana fad'in." 'Kanwata ce Halisa.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *2K ON TALGRAM.*
*VIA 0542382124... BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*104*
*Whasap Gruop 1K*
Na ce."Allah sarki a takaice ina d'an wani nazari a zuciyata sai na ji maganarta tana fad'in." Halisa k'anwata ce cikinmu daya ai da da rabo kuma Allah Ya yi wa Alhaji Amadu tsayin rayuwa suna tare da Maryam din domin kuwa sun yi soyayya k'warai kuma har iyaye suka shiga maganar har da yarjejeniyar aure a tsakani domin sadaki ne kawai bai biya ba lamarin ya rushe.
Shiru na yi ban ce mata komai ba. Ganin haka ya sanya ta cigaba da ce wa." Alhaji Amadu ya so Halisa sosai kuma ya yi mata hidima k'warai farko a gidana suka had'u ya nuna yana sonta sanin halin tsananin kishin matarsa ya sanya da maigidanmu yake sanar mini da buk'atar abokinsa na ce a a gaskiya dalili na farko Maryam k'awata ce muna zumunci sosai saboda abotar mazajenmu. Duk da ba mu zaune a gari daya amma muna ziyartar junanmu sa'i da lokaci kuma muna yin zumunci ta waya bayan haka kuma tsaye take a kan yarana kamar yadda ni ma nake tsaye akan yaranta. Shiyasa ban yi mamakin ganin yaranku a gidanta ba domin zahiri macace mai son yara da gaske da hidima su.
Da yake 'yar kasuwa ce mai zafin nema ba zan manta ba tasha yi mini fad'a sosai idan muka hadu tana fad'in ko ba zan nemi kudi don yarana ba dalilin ubansuya tara musu na tashi na nema domin iyaye da 'yan uwa da kuma gajiyayyu.
A duk lokacin da wani abu ya fito na ya yi muddin ta yi odarsa to kamar yadda za ta d'ibarwa Nusaiba kaya haka zata d'ibarwa Asiya da Madina kaya irin na yarinyarta babu bambamci ko kad'an. Sosai take yi mini kara akan komai ni kaina na sheda tana da kyauta da kirki daidai gwargwado Maryam duk wanda ya ra'be ta zai dandali arzikinta. Sai dai kin san an ce d'an Adam tara yake bai cika goma ba nasan dai tuntuni Maryam ba ta son kishiya tasha gaya mini a rayuwarta abinda tafi tsana kenan dalilin da ya sanya lokacin da maigidanmu zai 'kara aure ta dinga ba ni shawarwarin yi masa tutsu da wasu dai shawarwarin da nake ganin za su iya kaini ga halaka. Lokacin na tsananta da addu'a sosai domin mu gaskiya gidanmu gidan malamai ne Amina ba mu ta so mun ga iyayenmu na yawon bin malamai ba. Addu'a dai da yin nafilar tsakiyar dare ita iyayenmu suka koya mana tare da azkar a duk lokacin da wata matsala ta tunkaro mana. Gaskiya ban yarda na bi sharwarin da take ba ni ba na dai dage da addu'a sosai akan idan auran da mijina zai yi akwai alheri ina rokan Allah Ya hada ni da abokiyar zama tagari dalili tunda?a na ta so gidanmu mata hud'u ne a ciki kuma mahaifinmu tsayayye ne da wuya ma a cikinmu wata ta kaso auranta ta dawo masa gida da zumar yin zawarci daidai gwargwado mun samu kula da tarbiya.
Sosai Alhaji Amadu ya makance da soyayyar Halisa ya zama duk bayan sati biyu daga nan abuja sai ya je Jigawa gidanmu hira wurin Halisa a lokacin itama bai kwanta mata a rai ba ta zo tana gaya mini abinda yake faruwa ni lokacin ma ban san yana zuwa zance ba tunda mun gama magana da Babansu Madina akan zai gaya masa cewa ta tsayar da wanda zata zaura kuma gaskiya ne akwai wanda suke soyayya a lokacin sai dai bai kai ga turowa ba, Amma dai gidanmu sun san da maganar mahaifinmu ma sun yi magana da mahaifinsa akan hakan.
Na dinga mamaki sosai sai dana tambayi Babansu Madina akan mai yasa bai gaya masa ba sai yace ya gaya masa ya'ki ha'kura ya ce tunda har yanzu shi wancan din bai fito ba shi ba zai janye ba.
Na kira ta zo na ce da ita duk lokacin da ya sake zuwa kada ta fito ta yi masa kora da hali domin a gaskiya ba ni son abinda za a yi shi daga baya rai yana b'aci Muna mu'amula da Maryam sosai a tsukin na tabbatar da cewar ba ta san abinda yake faruwa ba, kuma ba na son abinda zai ta'ba zumuncinmu. Idan lallai ya zama dole mijinta ya kara aure to ya nema a wani wurin amma ba daga b'angarena ba.
Sati uku da yin wannan maganar ta sake zuwa gidana tana kuka sosai ta ce mini ya sake zuwa kuma Babanmu ya saurare shi. Wata dabi'a ce ta mahaifinmu son bawa mai aure d'ansa. Ni kaina don dai lokacin da maigidan nan ya fito da niyyar aurena da gaske yake domin gabad'aya ya shigo da na tabbatar da cewa mai mata Babanmu zai bawa ni. tana gaya mini sun yi magana sosai da Babanmu har ya ce ya jira shi zai yi magana da iyayen Murtala saurayin da suke soyayya idan har da gaske yake yi to ya fito a cewarsa masu son auran da gaske suna fitowa ba za a ce za a zauna jiran wani lokaci ba. A lokacin shi Murtala din baya gari ya tafi can kudu Benin suna harkar gwangwani. Amma ya ce mata yana dawowa zai yi magana domin a zo a kawo kudin aure. Da ta gayawa Baban namu haka ya ce sai ya ji ta bakin mahaifin Murtala din tukkuna zai yanke hukunci.
Dole ta ha'kura ta tsaya sauraransa. Lokacin Malam Shu'aibu bai rufe komai ba ya gayawa Babanmu cewa. Har yanzu Murtala ba shi da taku daya wanda idan ya yi aure zai ajiye iyalinsa. Can kudu (Benin) da yake zuwa tare da abokansa sana'a suke yi ta inada da 'karafuna da robobi, wannan shine amma tunda manemi ne arziki na Allah ne. Shi ba zai hana idan mijin aure ya fitowa yarinya ta yi auranta ba domin tauye hakki ne a ce mace ta zauna jiran namijin da bai zama lallai ya yi mata adalci a gaba ba, tunda da yawa hakan ta faru samari su yi alkawarin aure da budurwa su tafi neman kudi idan sun samo sun dawo gida sai su ga ai sun fi karfin ajin wannan budurwa da suka bari a gida.
Wannan maganganun na Malam Shu'aibu maihaifin Murtala ya zaburar da Babanmu a cikin satin da Alhaji Amadu ya je gidan namu suka yi magana ya ce idan har da gaske yake kuma ya shirya auran ya turo magabantasa. A tak'aice dai Amina na gaya miki da ni da Halisa sai ji muka yi an kawo kudin auran dubu dari biyun shekarun baya mai d'anko. Kuka sosai Halisa ta zo gidana ta na yi mini kamar ranta zai fita tana fad'in ita kwata kwata bai yi mata ba tsoho ne. A lokacin da take wannan koke-koken babu abinda nake tunani sai yadda za ta zauna da Maryam domin na fi kowa sanin yadda ta k'yamaci kishiya a rayuwarta.
Sosai na tausheta da rarrashi da ban baki har Babansu Madina ma da ya dawo ya sanya bakinsa yana ta kwarzanta mata nagartar abokin nasa yana fad'in ta kwantar da hankalinta ta yi mijin da za ta yi alfahari da shi. Muka rarrasheta sosai ta ha'kura kwanta uku a gidan namu da yake duk gari daya muke gidan iyayenmu na kazaure gidana kuma a dutse a kwana na hudun Alhaji Amadu ya zo gidan wata'kila ya je can gidanmu aka ce masa tana nan
lokacin da rarrashi da ban baki na tursasa Halisa sauraran Alhaji Amadu suka dan jima a d'akin bakin maigidan suna hira kafin su yi sallama ya tafi ta shigo mini da kwalin waya sabuwa dal black berry mai kyau da tsada da kudi dubu hamsin

Please Login or Register in order to submit comment