Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Khalil ya bi shi a baya da sauri.
Kaina na girgiza kawai na shige d'akina domin gabatar da tawa ibadar.


***
To ranar sadakar bakwai din kamar yadda ya fad'a abinda ya faru kenan bai ma zauna balle a zo a taya shi zaman. Addu'a kawai ya sanya aka yi mata a massalatai. Nusaiba anan wurina ta kwana duk da Nabila tana can gidansu ita bata tafi tana tare da su Salim don bala'i har da kukanta tana fad'in ba zata iya tafiya ta bar su su kadai ba, kuma mamansu kafin ta rasu ta ce ko bayan ranta ta tsaya ta kula mata da yaranta. Haka suka ha'kura suka kyaleta shima Yallabai din da ya ji cewar ba ta tafi ba sai da abin ya bashi haushi sosai ya k:yaleta ne kawai domin ya ga iya gudun ruwanta. Duk da Nusaiba ta san tana gidan hakan bai sanya ta shiga ba nan su Salim din suka same ta. Ta shiga cikinsu Mairo suka yi aikin funkaso da fanke manyan kuloli aka fita da su domin sadaka.
Tun bayan azahar ya shirya ya fita. Muka kasance da Nusaiba da yaranta har bayan la'asar kafin ta yi shirin tafiya gidanta.

Yana shigowa estate din Sukairaju da 'Dahuru suka yi ram da shi Malam Isiyaku ne Malamin Hajiya Maryam da ya zo kar'bar kudinsa kamar yadda aka al'kawaranta masa.
A mota suka zura shi tare da zuge gilashin motar sai ya fara zare ido na k'aduwa da tashin hankali. Sukairaju ya ce." Maigidanmu ne ya ce mu kai masa kai can gidan hutawarsa za ku tattauna wasu batutuwa ko ba kaine malam Isiyaku ba."
Ya gyad'a kansa da saurin baki ya furta." E, ni ne, Malam Isiyaku."
D'ahuru da yake driving ya ce." To kada ka damu lafiya za ka fito in sha Allahu."
Ya yi shiru yana zazzare Ido. To ai shi ba haka ake yi da shi ba me yasa za a yi masa kamun kazar kuku magana aka yi akan mai hakki ya fito ya fadi hakkinsa a ganinsa hakan da aka yi masa tozarci ne tunda shi ba 'barawo ba ne.

Gabansa suka dire Malam Isiyaku da tunda suka isa guesthouse din suka sanya shi a tsakiya babu wata hanya da zai samu ya fece..
Suka fita cike da bin umarni.
Ya dube shi a nutse Yana fad'in." Nutsu sosai ka kwantar da hankalinka. Na buk'aci ke'bewa da kai anan ne saboda muhimmanan batutuwan da zamu tattauna da kai, ai komai yana buk'atar sirri ko."
Ya gyad'a kansa kamar k'adangare kana ganinsa za ka gane a tsorace yake ko ina aljanun nasa suke oho. Wato ashe duk karyar banza ce."
Ya gyara zamansa a gabansa kamar wani mai d'aukar darasi ba malamin da yake da 'kumaji da dulmiyar da al'ummar annabi ba."

Ya ce.'' Tun sanda ka ba ni labarin abinda yake tsakaninka da Maryam mai rasuwa na gaza samun nutsuwa da kwanciyar hankali, a takaice nake sanar da kai har ciwo na kwanta saboda tsananin tashin hankali da damuwa. Malam Isiyaku shin za ka gaya mini irin bak'aken ayyukan da aka yi wa Maryam domin zalinci. Kada ka kuskura ka 'boye mini komai nasan ni ma da nake zaune nan a gabanka ka yi aikina ai asiri da tsafi gaskiya ne tunda ya ci annabinmu fad'in gaskiya shine abinda zai k'waceka bayan haka kuma ina so muje da ni da kai a gabana duk inda kayi binne a kaina ko akan wani na ka tone shi da hannunka."
Ya ki'dime sosai da sosai ya kasa zama Yana fad'in." Yallabai Wani aikin kaikayi ne wallahi idan na karya shi zai dawo kaina, zan iya kwanciya ciwo ko abin ya shafi iyalina don girman Allah ka gafarce ni."
Ya dube shi cike da tsantsar mamaki ya ce." Abin zalinci ne kenan, me yasa gabad'ayanku baku da imani ne, kai kanka kana gudun kada abinda ka yi ya shafi iyalinka to me yasa ka yi. Okey shikkenan tunda duk ina da bayanai a kan ka zan had'a ka da hukuma su za su yi maka tonan asiri duniya ta sheda wannan rawanin daka nad'a a kanka na zalinci ne furfurar dake gemunka kuma ta banza ce, daga nan 'yayanka da kake gudun su damu lahani su yi tur da kai da nadamar fitowa daga tsatsonka."
Ya ce." Duk ba za mu kai ga haka ba ranka ya dad'e za mu je duk inda na yi haka da binne a kanka zan tone da hannuna in sha Allahu ko da hakan zai zama barazana ga rayuwata."
Ya gyad'a kansa yana kallonsa cikin nazari kafin ya ce." Maryam ta yi aiki a kaina da iyalina kenan.''
Ya rusanar da kansa yana fad'in." K'warai kuwa na yi mata aiki akanka da kuma tsohon mijinta Alhaji Amadu akwai wanda na yi binne a kasan bishiyar kuka akwai wanda na yi a bishiyar tsamiya da kuma d'aurin baki da aka yi maka shima yana can za mu je ka gani domin laya ce aka 'dora mata gungumen dutse a can cikin wani daji.......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *Gudun aure paid book 2k complete on telegram what'sapp Gruop 1k via 0542382124...... Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*123*
Wato a duk lokacin da Ubangiji ya so bawansa da rahama ya kan wanke shi ya daidaita tunani da tafarkinsa zuwa hanyar tsira ya kuma yafe dukkunanin kuraransa. Allah," Ya ce kada ku hada ni da wani bawa na wurin neman biyan buk'ata ni ne da Ubangijin talikai mai jin kai, mai kuma bayarwa da hanawa. Ni ne d'aya wanda ba ni da farko da kuma k'arshe. Ku ro'ke ni da kowane irin yare ina jinku zan kuma amsa muku.
Had'a Ubangiji da waninsa babban zunubi ne da yake tabbatar da cewa babu afuwa da yafiya daga wajensa. Domin Allah yakan iya yafe kowane irin zunubi ne mutukar bawa ya yi tabbaccen tuba.
'Kwarai da gaske ya girgiza ya kuma shiga razani da nadamar rayuwa a lokacin da suka dinga haurawa kan dutse tare da Malam Isiyaku da yaransa biyu Sukairaju da D'ahuru. Duk gwagwarmayar rayuwar da ya yi ta duniya k'afarsa bata zuwa ire iren wannan wurin ba. Karamin gari ne a cikin jos din kuma mafi akasarinsu maguzawane. A wannan 'kauyen da mahukunta suka manta dashi nan Malam Isiyaku ke zuwa ya gudanar da ayyukansa. Tunda a bayan gari yake kuma gari ne da ba su san menene addini ba.
Suka dinga tsallake koguna da dutsina suna wuce manyan bishiyun kuka masu tsananin firgitarwa da bada tsoro.
Wata narkekiyar bishiyar kuka suka nufi mai manyan koguna kuma babu ganye a jikinta.
Suka tsaye gabad'aya wurin tsit sai kukan tsinye-tsinye ne ke tashi. Da alama bishiyar ta zama sansani wurin ajiye kayan asiri domin ga layu nan birjiki wasu a cikin kwalabe wasu kuma an nad'e su da jan zare da kwalaban tururukan da iska ke so.
Ya tsuguna ya fara wasu zantuka kimanin minti goma ya gama can daga gefe ya fara hak'a da zurfi sosai ya d'auko wata doguwar kwalba da ta fara rinewa cikinta cike da allurai da bakin yadi mai kama da likkafani a ciki. Daga 'kasan wurin da ya yi hak'an ya cire yadin likkafani shima ya dan rine da kasar wajan Amma hakan bai hana ganin sa'kandamin da yake zane ba.
Ya taso da kayan a hannunsa yana fad'in." Na ha'ko nan."
Ya tambaye shi nasa ne ko na Alhaji Amadu. Cike da nadama da tsoron abinda zai biyo baya ya ce." Na ka ne Yallabai."
Ya ce ya warware a wurin. Sukairaju da ba shi da tsoro ya kar'bi likkafanin da sa'kandamin yake hannunsa suka fara dubuwa.
Zanen hotonsa ne tsaf kowace ga'ba da kusurwa ta jikinsa rubuce da sunan Allah da kuma wani irin jagwalgwalon rubutu mai ri'ke ta kwakwalwa. Abin mamaki yadin likkafin yana ta 'kamshin wani irin turare mai masifar karfi.
Ya dube shi yana fad'in." Menene makarin aikin."
Ya ce." An karya ai tunda an ha'ko."
Suka yi gaba bishiyar tsamiya ce itama turgijejeya kana kallon wannan bishiyasa zaka tan ta tara 'kwan'kwamai masu illa gashinan ma da kanta take kamawa da wuta tsabar sansanin bak'aken aljanune.
Itama dai kamar daya bishiyar kukan aikin mutane ne birjik a k'asanta da sassan reshenta tunda akwai ragowar ganye a jikinta ga layu nan murtuka murtuka suna ta reto wasu daban wasu a cikin kwalabe."
Ya shiga mamaki sosai da ya ga ya d'ane bishiyasar can k'ololuwa ya kamo wani reshe ya d'auko wata doguwar kwalba da aka d'aureta sosai a jikin reshen an nannad'eta da jan yadi ya daddafo ya sauko da ita a hannunsa.
Sukairaju ya mika masa babbar rigarsa yasa yana fad'in." Wannan shine na alhaj Amadu mai rasuwa."
Ya buda kwalbar a wurin ta fashe. Layu k'ananu ne soke da allurai suka fito da wani irin warin turare mai gigitarwa..
A wurin ya sanya shi ya warware layun gabad'aya sunan Allah ne gashinan muraran Maliki yaumiddin mimun din da sunan Alhaji Amadu da Hajiya Ayya babarsa da kuma mahaifinsa. Duk ya warware guda ukun.
Ya bawa Sukairaju umarnin tattarawa ya zuba a leda domin babu damar barin su a wurin da sunan Ubangiji.
Suka yi gaba sosai suka riski wani shuri zungurere ya tsaya a sanyaye yana fad'in" Sati uku da suka wuce na zo na yi aikin wata mata a nan itama akan abokiyar zamanta ne farra'ku zan cire." Ya fad'a a sanyaye da alamar nadama a tare da shi.
Suka tsaya kuwa ya tsuguna ga rana ta kwalle a wurin tururuwai masu yawa sun fito har suna bin kafafunsu. Ko alama bai sare ba, kuma bai tsorota duk da akwai razanarwa saboda ya san jahadi ya yi shiyasa ya fi yarda su je ya gani da idonsa domin tabbatar da duk ya warware kullin da ya yi."
Ya haka gefen shurin inda ya san ya yi ajiyar ya d'auko wata yar tukunya ta 'kasa nan nad'e da likkafani ya kwance layu ne uku masu kauri ya warware cikinsu gashi ne da barkono tsidigu a hade da kuma d'anyan nama wanda kwance layun ke da wuya wari ya game hancinsu. Daga kansa ya yi musu bayani cewar naman na ja'ba ne sai gashin matar da aka yi wa asirin tsidigun (barkono) kuma shi zai dinga zafafawa ma'auratan zuciyoyinsu su ji sun tsani kansu da zama da juna.
Suka gama da wannan suka sake nausawa sosai wannan karon tafiyar da suka yi tafi ta baya can suka riski murgujejen dutsan. Suka tsaya cikin ransa yana raya da wannan aka danne masa baki kenan.


Gudun aure paid book ne kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba

Daga can gefe Malam Isiyakun ya tsaya ya takarkare yana ture dutsen D'ahuru ya taimaka masa. Aikuwa sai ga wata laya mai fad'i a kwance tsabar nauyin dutsin ya sanya ta tamushe duk tudunta da nannad'ar da aka yi mata.
Suka d'auko tare da fara kiciniyar kwanceta yana tsaye yana kallonsu jikinsa duk ya yi sanyi wato nan aka kawo bakinsa aka daure to akan me wai? Annabi ya yi gaskiya da yake cewa mata za su kasance da yawa a wuta, shi kam bai ga abinda ya yi wa Maryam ba da za ta yi masa haka.
Aka warware laya itama mai cike da sa'kandamai guda uku daga kowane sashe sunan da labaraci ya fito radau Tajudden!.
Suka had'a kan komai suka juya da baya domin fita cikin gari.
Sukairaju da D'ahuru suna bayansu shi da Malam Isiyaku suna gaba.
Ya d'an dube shi da gefan Ido gabad'aya ya yi sanyi mutumin fargaba ta mamaye shi. Tausayi ya bashi kad'an domin dai babu yadda za a yi ya sake shi ba tare da ya sanya hukuma a ciki ba. Mutumin banza ne wanda zuwansa duniya bai amfanar da kowa ba. Abin jajantawa da tausayawa iyalinsa da ya jefa rayuwarsa cikin gagari da 'kyama ta jama'a duk da akwai ire-irensa da yawa a gari masu ci da addini da halakar da mutane amma a ganinsa wannan nasa ya yi muni sosai.
Ya ce." Ranar da ka fara yi mini bayani akan za ka yi aiki akan matata Hauwa ita dayar ba ka ta'ba wani aiki a kanta ba?''
Ya yi shiru na d'an wani lokaci kafin ya furta." Idan itace Amina gaskiya marigayiya bata ta'ba sanya ni aiki a kanta ba, abinda na sani shine ta ta'ba ce mini tana so a had'a taurarinta dana Amina din saboda nata suna da haske sosai kuma iyayen makarai ne a tare da ita tana da jalabi sosai bayan haka ma ba kasafai jifa ya ke kaita kasa ba tunda ba raguwa ba ce wurin addu'a. Taurarinta suna da tsananin haske dalilin da ya sanya kenan itama ta buk'aci da su yi musharaka wurin haduwar taurarin.
Ya jima yana girgiza kansa da mamakin abin. Ya jima da sanin cewa ana iya amfani da haske da taurarin mutum domin cimma wata manufa wasu lukutan mutum na zaune kaf sai a kwashe masa taurari bai sani ba. Wato malam ka ji tsoron Malaman yanzu da suka kwashe kayansu daga gaban ma'aki.

Kwana da yini suka yi a garin jos duk yadda Malam Isiyaku yake karyar da kai da nuna ya yi nadama bai saurare shi ba. Yana da jama'a sosai duk da wata mu'amula ba ta ta'ba had'a shi da shugaban jami'an tsoron garin ba. Dalilin suna da shahararsa a duniya ya sanya a daran ya gana da commissioner yan'sanda suka cika hannu da Malam Isiyaku zuwa sansaninsu.
Gajiya kam sun kwaso ta daga shi har yaran nasa ga tafiyar mota sai gefen asubahi suka shiga garin abuja ana ta kiran sallar farko.

Ban san ya dawo ba sai da gari ya waye tukkuna na fito na same shi da yaran gabad'aya a falo a zaune. Sun zagaye shi yana ta sauraransu yana murmushi Minal yar lelanshi tana kan cinyarsa. Twins kuma na gefansa a tsaye suna ta tsalle Khalil na saman kujera a zaune. Dukkaninsu cikin tsafta Mairo ta kintsa su. Suna ta 'kamshi.
Na yi murmushi ina kallonsu gwanin ban sha'awa na ce." Cikin dare ka dawo ne?"
Suka juyo gabad'aya suna kallona har da shi ba su lura da fitowata ba sai da na yi magana.
Ya gyad'a kansa a nutse ya ce." Gefin asuba na shigo Amina. Ya kuke na same ku lafiya."
Na ce." Alhamdulillahi ya su Hajja?" Domin ni ce mini yayi kano za shi kuma zai kwana daya."
A tak'aice ya furta suna gaishe ku."
Ya sauke Minal kasa Yana fadin." Zan kwanta zuwa an jima ki tashe ni."
Na ce." To shikkenan."
Ya haye sama da dan sauri.
Na dube su Usai ta yi saurin janye idonta daga kaina. Na sassauta fuska tare da mika mata hannuna ina fad'in." Zo." Tun ranar da na mur'de mata kunne take ja baya dani. Hassana ce ke iya zuwa kusa da ni har ta yi mini hira. Minal kuwa yar d'akina ce tunda ita dama can akwai ta da saurin sabo."
Ta zo din kamar yadda na buk'ata amma bata kalle ni ba.
"Na ce." Menene?"
"Babu komai."
Na ri'ko hannunta a nutse na furta." Kina jin tsorona ne?"
Ta girgiza kanta. Na d'ora ta saman cinyata ta ai kuwa sai tasa dariya tana kallona abin ya zo mata daban.
Hassana ta taho itama tana bata rai. Na dauketa na sanya a daya gefan suka dinga dariya suna yi wa Minal gwalo ita kuwa mai neman jiran kiris ta fashe da kuka. Khalil yana yin dariya ya ce ni zo na goya ki."
Na ce." Zo nan goyo kike so ko?"
Ta daga kanta. Na ce." To ta kwana gidan sau'ki je ki ce Mairo ta bada abin goyo."
Ta kuwa ta fi da sauri.
Na dire su a kasa ina fad'in." Idan ba ku sanyata kuka ba bakwa jin dadi, kun yi girman banza."
Ina shiga d'aki ta shigo da towel din Sultan tana mika mini na ce." Aiki ya same ni kenan, gashi wanka zan yi yanzu Minal amma muje."
Ta biyo bayana na samu Taburni da yaran tana had'a musu tea na ce." To zauna ki ci abinci idan na yi wanka na fito zan goya ki."
Mairo da ke goge musu kayan makaranta ta ce." ashe da gaske goyon za a yi Hajiya."
Na ce." K'warai kuwa Mairo na juya na fita daga d'akin ina jinsu suna yi mata dariya.
Na sami Adam a falon a tsaye wanda shigowarsa kenan. Muka gaisa yana tambayata Baba ya dawo?"
Na ce masa ya dawo amma ya kwanta sai zuwa an jima ya dawo lokacin ya tashi.
Ya ce to cikin sanyin jiki kafin ya juya ya fita na bi shi da kallo gwanin ban tausayi.
Wajan daya da rabi na tashe shi domin yin sallah.
Ya tashi zaune yana kallona goye da Minal a baya. Ya ce "Wacece a bayanki?"
A tak'aice na ce." Name sake dina ce."
Sai ya yi murmushi ya ta shi ya shiga bandaki ina zaune ya fito d'aure da alwala na ce." Adam kuwa ya shigo nemanka d'azu."
Ya ce." Zuwa an jima zan nema shi. Sallah zan yi yanzu ki kawo mini abinci.".
Na tashi na sauka kasa na had'o masa abincin da abinda zai buk'ata na koma na same shi ya idar amma yana gyangyadi a saman daddumar hakan kuma ba dabi'arsa ba ce.
Na ajiye tiran ina tashinsa ya tashi ya nufi bed yana fad'in." Baccin zan sake komawa.
Da mamaki na ce." Abincin fa.''
Ya rufa da bargo yana fad'in." Sai na tashi tukkuna.
To wasa-wasa haka ya wanzu tsayin kwanaki hud'u yana wannan baccin gabad'aya yin ibada ne kawai yake tashinsa idan ya gabatar ya ce zai koma ya kwanta da rigima sosai yake cikin abinci ya zama kamar wani sususu jikinsa babu kuzari sai bacci sai kace wani rik'akken d'an 'kwaya.
Hankalina ya fara tashi domin na ce masa ya kira likitansa ya duba shi bashi da lafiya ya ce na kyale shi a hankali zai warware kawai dai na cigaba da kunnansa karatun al'kurani. Ganin abin nasa ya'ki sau'ki na fara kuka domin tunda ya yi tafiyar nan ya dawo bai kwanta da ni mun yi sunna ba kwana biyar yanzu wanda a tarihin rayuwarmu hakan bai ta'ba faruwa ba.
Muka dinga rigima akan na ce zan gayawa Hajja ba shi da lafiya a ganina ai mai matsalar aljanu da farfadiya ya kamata ace ana kunnawa akaratun al'kur'ani a saitin kunne, ga yanayin jikinsa ya nune babu kuzari amma ya ce shi lafiyarsa lau wace irin gajiyace wannan da zata mayar da shi d'an maye kullum bacci....✍️
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
🌲🌳🌿☘️

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*Gudun aure paid book 2k complete on telegram what'sapp Gruop 1k via 0542382124.... Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*124*
A cikin kwanakin da ya kasance cikin wannan yanayin ki'ba ya yi ta fuska sosai ban sani ba ko baccin da yake yi ne ya janyo faruwar hakan oho! tunda gaskiya ba abincin kirki yake ci ba ballantana na ce tun asali ma mutum ne shi da bai fiye tasa abinci a gaba ya yi ta narka ba, kuma ba shi da irin ciye-ciyen nan na masu kudi.
Cikin dare na tashi na yi sallah raka'a biyu na tsananta addu'a sosai domin abin ya fara daga mini hankali yanzu kuma na gano babu shakka akwai abinda ya faru wanda yake b'oye mini.
Gefan kansa na zauna na bud'e alk'uranin izifi sittin din da yake hannuna daga sama na fara a cikin nutsuwa har aka fara kiran sallar farko wanda ya yi daidai da lokacin ya motsa. Ya tashi zaune yana kallona na rufe al'kur'anin muka dubi juna na dan wani lokaci kafin ya kira sunana na amsa.
Sai ya zura k'afafunsa kasa domin sauka yana fad'in." An yi kiran sallah ko?''
Na ce." Za a yi yanzu dai."
Toilet din ya nufa na bishi da kallon nazari kafin na tashi na bi bayansa na ga yana had'a ruwan zafi dana sanyi wanka zai yi ban hana shi ba kawai na ja masa k'ofar na fito na zauna har ya kammala ya fito d'aure da towel ashe ba iya fuska ya murmure ba har jikin gabad'aya.
Ga mamakina da kuzarinsa ya kintsa ya fita massalaci wanda ya d'auki kimanin kwanaki biyar rabon da ya sanya kafarsa a waje duka sallolinsa a gida yake yin su ya koma ya lafke a gado.
Kasa sauka 'kasa na yi har sai da gari ya yi haske ya dawo. Ya gan ni a zaune bai nuna mamaki ba na zuba masa ido har ya zo ya zauna kusa da ni wanda na yi zaton kwanciyar zai sake yi sai naga akasin haka muka gaisa ya ce mini na d'auko masa Loptop dinsa dake ajiye can wurin da yake zama. Cike da jin dad'in ganinsa a haka na tashi da azama na je na d'auko masa har ya bud'e ya kunnanta sai kuma ya kashe ya janyo ni jikinsa.
Ga mamakina na ga yana ko'karin cire mini hijabin dake wuyana. Muka kalli juna ya kanne mini ido cikin wata kalar murya ya ce." Mu 'dan yi wani abu ko."
Kasa ce masa komai na yi domin ni hakan ma jefe ni ya yi a farinciki ganin ya fara dawowa hayyacinsa. Na biye masa kimanin minti talatin muka d'auka kafin komai ya kammala.
Ya riga ni yin wanka ko da na fito sai na same shi yana yin waya na ji yana kiran sunan wani Malam Rabi'u akan zai tura masa da abin sadaka a sake yin saukar al'kur'anin da aka yi a watannin baya.
Sai da suka gama tukkuna na sake gaya masa Adam ya shigo jiya da shekaran jiya wurinsa.
Yana sake ko'karin kunna Loptop din a karo na biyu ya ce." To zan neme shi na ji menene nasan ba zai wuce maganar Nabila ba ita take turo shi wai zata zauna tare da su."
A tak'aice na ce." Hakan yana da kyau ai."
Na tashi na sauka kasa domin had'a masa abin kari.
Kafin na shiga kicin din d'akin yaran na fara dubawa duk sun yi shirin tahafiz yau asabar da lahadi tun takwas na safe suke tafiya sai shida. Ranakun da suke da boko kuma suna shiga k'arfe uku. Dukkaninsu cikin uniform a tsaftace kamar yadda dai suke yi musu hidima a gidan Momin Taburni da Mairo kowanne da lunchbooks dinsa. Ganinsu ya saukar mini da wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali a raina na tsinci

Please Login or Register in order to submit comment