Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar gilmawar wani abu daga sannan ban sake gane komai ba sai dana farka tukkuna na tabbatar da cewar suma na yi lokacin har an kaita makwancinta an dawo. Anti Yagana sun iso tare da Inna Uwani. Ban yi mamakin ganin yanayinsu ba domin akwai d'imuwa da tashin hankali na rasuwar da aka kwantsama. Ko baka da ji'bi da mutum fad'in Annabi ne mutuwarsa dole ta nasheka balle wannan matar da alherinta kowa yake gani.
Hajja ta shigo d'akin da muke tana fad'in." To alhamdulillahi tunda ta tashi da ji da ganinta da kuma lafiya mun gode Allah Yagana taimaka mata sai mu koma can gidan nasu mu yi namu zaman domin nan din zaman zai zame mana fitina.
Gwaggo da fitowarta daga bandaki kenan d'aure da alwala ta ce." Ni ma shawarar da na yanke kenan hakan zai fi alheri."
Anti Yagana ta dube ni a d'an sanyaye kafin ta ce." Sannu ba dai kya jin komai a jikinki ko?"
Kaina na gyad'a mata a nutse na ce." Ashe kun zo?"
Ta ce." Mun zo mun tarar an d'auki gawar gidan a kacame ana ta hayaniya ke kuma gaki a sheme sai da likitanku ta zo ta dubaki fa dogon suma ki ka yi."
Shiru na yi ina nazarin maganarta kafin na ce." Anti Yagana mai ya faru ne?"
Ta'be bakinta ta yi ba ce mini komai ba. Na daga kaina na kalli Hajja dake tsaye jikin bango rumgume da hannunta a k'irji nan take na karanci damuwa da b'acin rai a saman fuskata.
Ban sake wata magana ba na tashi zaune hijabi na da yake gefe anti Yagana ta miko mini na zura a jikina tana taimaka mini na yun'kura na tashi ta ri'ke ni. Na ce." Ki cika ni zan iya tafiya da kafafuna. Inna Uwani ta ce." Da dai kin bari ta rike ki jikin naki ai har yanzu bai gama daidaita ba.
Hajja da Gwaggo suka yi gaba.
Wani irin kallo dangin marigayiyar suke mini na tsana da kyama. Anti Yagana ta juyar da kanta ba ta ce komai ba. Ni ma ban ce musu komai ba na ji ita wannan matar mai suna Yabi tana fad'in." Kun kai ta kasa kun ji dad'i, sai ku jirayi hakki domin wallahi ba mu yafe muku ba, duk abinda za ki nuna a banza a wofi Maryam dai karshenta ya yi kyau ku kam in sha Allahu mutuwar wulakanci za ku yi."
Maganganunta ne suka dinga yi mini amsa kuwawa! a kunne gabana ya dinga bugawa da karfi da karfi. Wannan babban kalubalen ban shirya tararsa ba a yanzu domin ba ni da hujjar da zan kare kaina Allah shine shahidi.
Muka fita tun daga haraba cike da jama'a har zuwa waje mutane cike cikin manya manyan rumfunan da aka kafa.
Kafafuna suka dinga hard'ewa gabad'aya sai na tsargu domin maganganun da matar nan ta yi sun sake dakusar da duk wani karsashi da kwarin gwiwata. Shin wane irin kallo jama'a suke yi mini a yanzu dana fito cikinsu. Cikin dubara na janyo saman hijabina na rufe fuskata dashi dama rike nake a hannun anti Yagana. Ina jin sanda Hajja ta tsaya suna gaisawa da ire-iren abokanan Yallabai din na ce da anti Yagana ta yi sauri mu wuce domin ba ni da wani k'umaji da nutsuwar da zan iya tsayuwa a gaban jama'a domin kar'bar ta'azziya. Muka yi gaba muka bar su ita da Gwaggo suna gaisawa.
K'uryar d'akina anti Yagana ta dangane da ni na zauna kan gado kamar wata sabuwar amarya na yaye hijabin da ya katange fuskata. Muka had'a Ido nan take na rushe da kuka na ri'ke hannunta katamau! Jikina na kyarma na furta." Anti Yagana Hajiya Maryam ta mutu sanadiyar lalure-laluren da suka yi mata hijabi, ina tsoron kada 'yan uwanta da jama'a su jinginta rasuwarta da ni da Hauwa, ai kin ji abinda daya daga cikin 'yan uwanta take fad'a ko?"

" 'Karamin tsaki ta yi kafin ta ce."Amina duk wanda zai alak'anta rasuwar matar nan daku to dama can ba masoyinta ba ne. Su kansu 'yan uwan nata da suke ko'karin tashin husuma ba kaunarta suke yi ba tunda har suke jingina rasuwarta da wani abu daban. Kishi halak ne kuma duk gidan da aka had'a mace fiye da biyu ana samun irin wad'annan matsaltsalun. A ganina wannan ba wani abun damuwa ba ne, rigima ce suke nema kuma in sha Allah rabbi har a share makoki ba za mu tanka musu ba. Ni gidan ma ba zan sake shiga ba tunda na lura duk yawansu babu mai dattako a cikinsu. Rashi kam ba su kadai suka yi ba mutane da yawa ne domin Hajiya Maryam bango ce majingina kuma uwar marayu har ma da masu uban. Don haka iyakacin k'aunar da za su nuna mata su bita da addu'a tare da rungumar abinda ta bari shine kawai sakamakon da za su yi mata bayan rayuwarta. Don haka ki samu nutsuwa ki kuma daina tunanin kina da hannu lokacinta ne kawai ya yi kuma babu wanda ya isa ya tsalle rana da sa'in komawarsa ga Allah."

Maganganun anti Yagana sun d'an sanya ni mini nutsuwa kad'an amma har yanzu zuciyata ba ta daina yin tsalle akan abinda na ji yana fitowa daga bakin 'yar uwar marigayiyar ba.
Babanmu suka iso tare da baba Sule da Ummansu Hadiza kamar yadda ya fad'a. Baban Saude ne har yanzu bai shigo inda nake ba, anti Yagana kuma ta gaya mini tare suke da Babansu Fadila har da Baba Madu wanda ya kasance babban yayansu Mamanmu, mahaifin Babandi.


Kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Sai wajan biyar saura tukkuna suka shigo da d'an yawansu duk muna zaune a babban falo. Maigidan tare da iyayenshi biyu 'yan uwan mahaifinsa da kuma Baban Saude Baba Madu da Babansu Fadila. Falon ya cika da sabuwar gaisuwa tare da yi wa juna ta'aziya. Ta mussaman suka yi mini gaisuwar na amsa yayin da nake jin cikowar ruwan hawaye idona. Ina jin Hajja tana tambayar Alhaji Sa'idu Hajiya saratu ya ce tana can gidan mai rasuwar tunda koda suka sauka nan ta shiga ba ta fito ba kuma har yanzu. Suna ta tattauna hirar marigayiyar yayin da maigidan ke sake basu labarin irin wahalar da ta sha na jinyya farkon zuwansu asibitin a yayin da aka dora ta akan magani an ga sauyi sosai yanayin yadda yake magana da alhini shi yake nuna mutuwar ta dake shi kwarai da gaske kwarmin idonsa ya zurma fatar lebanshi ta bushe kamar wanda ya yi azimin shekara bai sha ruwa ba. Irin wannan yanayin ya shiga a lokacin rasuwar tsohon mijinta Alhaji Amadu da kyar ya dinga cin abinci. Yanzu ma ba na raba daya da biyu rabonsa da abinci tun da aka yi rasuwar kwana da yini kenan.
Gabad'aya sun jajanta sosai kuma kafin tafiyarsu sai da Baban Saude ya jagorancemu gabad'aya muka yi mata doguwar addu'a wadda take d'auke da surorin da ake karantawa mamaci. Yamma likis suka yi mana sallama gabad'ayansu har da Hamusu da Babanmu domin cewa ya yi shi ma ba zai zauna ba tafiya za su yi tunda sun yi abinda ya kawo su. Shi kansa maigidan ya so su kwana ko daya ne amma gabad'aya suka ki har da kawunan nasa. Hajiya saratu ce kawai ta zauna ta ce sai an yi sadakar ukku tukkuna.
Yallabai din ya bada umarnin mayar dasu Babanmu gida. su Baban Saude kuma dama a motarsa suke tafe. Sai bayan sun tafi tukkuna Hajja ta dinga fad'a wai mai yasa anti Yagana ba ta jagoranci Ummansu Hadiza zuwa gidan mai rasuwar ba.
Anti Yagana ta ce mata mantawa ta yi shiyasa ni kuma nasan ba haka ba ne ita da kanta ta gaya mini k'afarta ba zata sake taka gidan ba. Gaisuwar da ta yi wa maigidan ma ta isa ba sai ta je ta yi wa 'yan uwanta ba tunda dukkaninsu taron tsintsinya ba share ne.
Sai bayan magariba Hajiya Saratu ta shigo. Ina d'aki lokacin na idar da sallah ban ka ga tashi daga kan daddauma ba ta shigo.
Na saki fuskata sosai Ina fad'in." Mai sunan Mamana ina yini?"
Ta zauna gefan gadona a nutse tana fad'in." Lafiya lau Yayata kuma diyata."
Na yi murmushi a hankali na ce." Ai tun d'azu aka ce kina can gidan marigiyar ina nan ina ta zuba idon ganin Mamana"
Ta dafa kafadata tana fad'in." Ga ni na shigo ai Amina ya muka ji da hakurin Maryam lokaci ya yi Ubangiji Allah Ya gafarta."
Na amsa da "Amin Ya Allah." Cikin wata iriyar murya.
D'akin ya d'an yi shiru wanda ya yi daidai da lokacin da anti Yagana ta fito daga bandaki daure da alwala. Ta saki fuska tana fad'in." Hajiya kin shigo kenan?"
Ta ce." E wallahi Yagana ya gida ya yaran, ya muka ji da hakuri?"
Anti Yagana ta ce." Ha'kuri da godiya Hajiya Allah dai ya jikinta da rahama."
Da Amin ta amsa yayin da take sake dora hannunta a kafad'ata.
Anti Yagana ta d'auki daddauma da hijabi ta koma can gefe domin gabatar da sallar magriba.
Ta ce." Ai ni ban fito ba daga gidan ba sai da na gabatar da sallata tukkun." Na yi murmushi kad'an ban ce komai ba.
Sai ta ce." Amina akwai maganganun da nake so mu tattauna dake idan babu damuwa."
Cikin nutsuwa na ce." Babu damuwa Hajiya Ina sauraranki."
Ta sauke ajiyar zuciya a tsanake ta ce." Duk abubuwan da suke faruwa a zamantakewar gidan nan ina da labari. Da har Ina cewa tunda matsalar ta'ki ta'ki cinyewa zan wanko kafata takasan na zo naji komai daga gare ki nasan ke ba za ki yi mini karya ba, ba kuma za ki goyu da bayan mijinki ko ki goyu da bayan Hauwa ba, idan har kema kina da lefi za ki gaya mini gaskiya sanin da na yi miki tun farkon fari.
Ta nisa kafin ta cigaba da cewa. Sai gashi kuma
rasuwar Hajiya Maryam ta ratsa hakan sai ya kara ba ni k'warin gwiwar zuwa domin na ji komai daga gare ki, Amina da hankalinki za ki biyewa Hauwa da har yanzu ba ta san rayuwa ba, mai yasa kuka kasa bawa mijinku k'warin gwiwa da taimako wurin ganin ya rike amanar abokinsa. Jimawata gidan marigayiya Maryam tana da dalili domin 'yan uwanta ne suka zaunar da ni suna wassafa mini irin zaman da kuka yi da ita da irin abubuwan da kuka dinga yi mata na rashin kyautatawa, idan har hakan gaskiya ne Amina ban tsammata daga wurinki ba domin kallon da nake yi miki kin wuce a ce a yanzu an zauna a nuna miki abinda ya dace idan Hauwa ta yi hakan ba zan yi jayayya ba dama na san halinta da na ji sunanki a ciki ne sai hakan bai yi mini dadi ba, mai ake gudu ne a zaman tare irin wannan fa, yanzu ina Maryam din take ta mutu ta bar duniya to mai zai sanya ba za mu yi hakuri da rayuwa ba. Gashi Hauwa har sai da ta yi sanadin da Tajo ya saketa saboda kuma bata da hankali ta tafi ta bar yaro jinjiri fisabillahi ina hankali da tunaninku yake?"
A nutse na dubeta tare da cewa." Mamana abubuwan da yawa sun faru masu dadi da akasin haka. Amma zan gaya miki wani abu da ba kowa ya san shi ba sai ni sai Ubangijin da ya hallice ni wallahi tallahi ban ta'ba kin Maryam a cikin raina ba. Tabbas akwai kishi kuma kowace mace tana da nata daidai gwargwado amma ni Amina ban zafafa shi akan matar nan ba duk sanda zuciyata za ta kitsa mini mummunan abu akan kanta nakan yi tirr da ita da take bijiro mini mugun nufi akan matar da alherinta ya fara riskata kafin wata mu'amula mai karfi ta ratsa tsakaninmu. Duk abubuwan da suka dinga faruwa yaranmu suka had'a amma ni da ita sa'insa mai muni bata ta'ba hadamu ba, kuma lafiya lau muka yi sallama da juna har ta koma ga Ubangijin talikai. Har yau har gobe ban k'ulleceta ba ban kuma k'ullaci yaranta ba ina jin tausayinsu kuma ina yi musu kallo irin na uwa." D'akin ya shiru bayan ajiye maganata na ja numfashi cikin bushewar ma'kogwaro na cigaba da cewa." Magana akan Hauwa kuma ni ba zan iya ce miki komai ba, abinda dai na sani shine Hauwa ta yi mini kokari kwarai kuma babu kishi da ganin kyashin juna a tsakanina da ita ni fa a tunanina kenan, domin Hauwa 'yar uwa na dauketa ba kishiya ba. Duk hanyoyin na bi domin na nuna mata abubuwan da take ba su da kyau na bi, na yi bakin kokarina amma ba ta ji ba. Dalilin rigimarsu da maigidan tana da ala'ka da ni da ita mai rasuwar da yaranta. Mun daidaita a wattanin baya har na so ni da ita mu je mu dubata a lokacin da ta kwanta a asibiti amma fafur ta'ki sai tare da Baba Tabawa na tafi mai aikinm kenan. Wannan shine abinda zan iya gaya miki Mamana bayan hakan ban san abinda yake tsakanin Hauwa da mijinta ba tunda tun kafin ta aikata haka na yi iyakacin bakin kokarina a kansu ita dashi amma babu wanda ya saurareni a cikinsu."
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
🌲🌳🌿☘️

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*2k COMPLETE ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA 1K VIA 0542382124.... BINTA UMAR GTBANK.*
*07084653262*

Ta jima sosai kafin ta yi magana cikin yanayi na damuwa ta ce." Dangin matar nan dai a ciki suke da ku Amina domin gani suke yi bakincikinku ne ya kashe musu 'yar uwarsu duk wanda ya zauna ya tashi sai sun amayar masa da abinda yake cikinsu.
Anti Yagana ta ja tsaki tana fad'in." To, abinda ya fi sai kawai su d'auki lasifika su fara bi sa'ko da loko suna shela tunda ba su da hankali, wannan ba k'auna ba ce abinda suke nunawa tsantsar jahilci ne kuma za su hana yar uwarsu kwanciyar lafiya a kabarinta muddin suka ce za su tashi rigima abubuwa da yawa ne za su faru. Dama zaman tare ai ya gaji haka dole a samu matsaltsalu ma bambamta sai dai kawai Allah Ya kyauta, ta wace hanya kike ganin za su hade mata kai ko su ware ta. Matar da ta samu soyayyar miji fiye da su, Hajiya Saratu ki duba maganar nan don Allah kaf fa yaransu suna hannunta basu da iko akan komai kina kwance kina jina Allah Ya jikanki, idan sun yi magana akan nuna rashin yarda ya goyu da bayanta. Ai ma sun yi hakuri da ita wallahi kuma son su ta da zaman lafiya domin da wahala a ce wata uwa an yi mata fin karfin a kan yaranta ta iya dannewa sun yi namijin kokari anan kuma na yana musu. Mu dama tsakaninmu da ita alheri ne, wallahi koyaushe Amina ta gaya mini halin da take ciki na damuwa akan zamantakewar gidanta akan tausheta tare da nuna mata cewa haka auran yake gabad'ayansa jarabawa ce a ciki jin dadinsa kad'an ne kuma ibada ne, kokarinmu ta yi hakuri ta zauna a yau ba wai don yar uwata ba ce ina yabonta sosai dalilin abubuwa da yawa da ta dinga cin karo na b'akinciki da b'acin rai amma ta yi hakuri ta jure. Don haka idan 'yan uwan Maryam sun zargi Amina da Hauwa wajen gumawa Maryam takaici har ta rasu to sun so kansu kuma zahiri ba su bukataci zaman lafiya ba domin dai duk mai hankali ya san matar nan ta sha jinyya kafin ta rasu. "

Ta girgiza kanta tana fad'in." Hakane amma Yagana daidai ne Hauwa ta ajiye jariri sabuwar haihuwa ta shilla wata duniya ko a waje Tajo ya je ya auri yarinyar nan ya kamata ta aikata mana wannan rashin mutuncin. Jininmu ce fa ciki daya fa ba wasa ba ne Hakan ne ma ya sanya duk muka ture komai da jin zafin abinda ta yi Hajja ta ce mu je a bata ha'kuri bisa bin umarinta muke je can bauchi Hauwa ta rufe idonta ta yi mini dibar albarka zagi na ne kawai ba ta yi ba, hakan ya sanya na yi alkawarin cewa muddin da yawuna da shawarata Tajo ya gama zama da ita har abada tunda ta za'bi ta tozartamu shikkenan sai dai zumuncin ya lalace ."
Anti Yagana ta ce." A a ba za a yi haka ba Hajiya, ai ko babu dangantaka ta jini an riga an zama daya tunda har yara suka ratsa tsakani. Don kyautawa Hauwa ba ta kyauta ba. A dai nuna mata kuskuran abinda ta yi a gyara ta dawo dakinta a ganina shine abinda ya fi dacewa."
Ta gyada kanta ba tace komai ba tabbacin maganar anti Yagana ba ta gamsar da ita ba.
Na ce." Anti Yagana idan Hauwa tana da lefi shima yana da lefi fa. Domin ya yi abubuwa sosai wanda ya kamata a ce ya gane kuskure ne a zamantakewa amma bai gane ba, ni na yi kokarin dannewa dalili nasan babu wani abun da yake dawwama sai ikon Allah wanda shi muka gani yanzu. Na yi ta ko'karin bata shawara kan cewa ta kawar da kanta ta kasa jimirin yin hakan har sai da bacin rai ya ratsa tsakaninsu. Ya kamata gaskiya a tsage Mamana. Shi kansa maigidan akwai tashi matsalar sai dai ace ta Hauwa ta rinjayi tasa."
Ta ce." Ni dai da yawuna ba zan bashi umarnin dawo da ita ba duk hukuncin da ya yanke daidai ne."
Tana fad'in haka ta tashi tana cewa." Zan je na watsa ruwa can wurin su Hajja jikina duk ciwo yake yi mini na samu nasa wani abu a cikina."
Na ce." To shikkenan Mamana dama na ce da Baba Tabawa ta tu'ka mana towo don zai fi manà dadin ci akan tsabar shinkafar nan."
Ta ce."Aikuwa kin yi shawara mai kyau Amina don tunda aka sanar da ni rasuwar nan wallahi ko na sanya abinci a gabana sai dai na kalle shi ba na iya ci. Kai rasuwar baiwar Allah nan ta ta'ba ni wallahi."
Anti Yagana ta ce." Ba ke kadai ba wallahi ni kaina na gigita kwarai da aniya Ubangiji Allah Ya yi mata rahama."
Muka amsa da amin gabad'ayanmu kafin ta yi mana sallama ta fita daga d'akin, anti Yagana ta dube ni tana fad'in." Na so na tambayi Ummansu Hadiza labarinta amma na sha'afa wallahi, kuma don dai Babanmu ya ce sai sun tafi amma da ko kwana daya sai su yi tunda yanzu dole ne su kwana a hanya
ina so mu sake samun lokoci mu je mu sake dubata ko ya ki ka ce."
Na ce." Hakane anti Yagana ni kaina Hadiza tana raina wallahi, dalilin da ya sanya kenan na ce da Hamusu duk k'arshen wata ya dinga yi mata siyayya yana kai mata, zuwan namu yana da amfani ai hannunka baya rubewa ka yanke ka yar."
Ta furta." Ni har fargabar ganinta nake yi wallahi saboda ina tuna irin kukan da ta dinga shirga a ranar da muke je kin san da kyar aka tura ciki muka fito, na jima ina kukan zucci duk sanda na tuna da halin da take ciki nakan shiga yanayi na damuwa mace a irin wannan wurin a ajiye Amina duniyar nan ta baci duk da ba ita kadai ba ce, amma su kansu ma'aikatan wurin wallahi wasu daga ciki ba su tsoron Allah."
Cike da damuwa na ce." Anti Yagana lefin Hadiza na kisa ne ta kuma tabbatarwa da kotu gaskiyarta ba mu da wani yun'kuri da zamu yi domin ceto ta. Hakkin rai ba abin banza ne. Idan Allah Ya kar'bi tubanta kuma tana da ragowar rayuwa sai ki ga ta fito ta hanyar da ba mu yi tsammani ba. Idan kuma sun kasheta shikkenan sai ta riski Ubangijinta a wankakkiya. Ubangiji Allah Ya kare mu daga fadawa jarabawa da mummunar kaddara."
Ta amsa da Amin Ya Allah da yanayi na damuwa da nadama.

Misalin goma da rabi maigidan ya shigo tare suke da Kamalu ban yi mamakin ganinsu su biyu babu Yusi ba domin sai na ce ganina da Yusi daya kafin a d'auki gawar marigayiyar na hange shi tare da Adam a rakube a bayan kujera yana rarrashisa yanzu ma su Hajja da Gwaggo sai tambayarsa suke yi ina jin Kamalu na basu amsa da cewa yana can tare da Adam. Maigidan bai tsaya ba suna gaisawa ya haye sama hankalina gabad'aya yana kansa don haka ban yi jinkirin bin bayansa ba.
Na same shi zai shiga wanka da babban towel a jikinsa.
Muka zubawa juna ido. Na isa dab da shi na tsaye a sanyaye na ce." Ya karin hakuri tun d'azu nake ta so na yi maka gaisuwa ban samu dama ba, Ubangiji Allah Ya gafarta mata, kai kuma Allah Ya baka hakurin jure rashinta, Allah Ya albarkaci abinda ta bari."
Ya dinga amsa da "Amin Ya Allah cikin jin dadi. Ya nufi bandakin na bi bayan shi na taimaka masa wurin had'a ruwan wanka. Kallo yake ta bi na dashi babu yabo babu fallasa, amma kallon ya fara sa'bata sai na tsargu na fara tunanin ko shima ya fara yarda da abinda 'yan uwanta suke fad'a akanmu wato da bakincikinmu ta rasu. Da na tuna kallon nasa babu harara da k'yama a ciki sai na d'an samu sassauci, na fito na bar shi a bandakin domin ya yi wankan. Na zauna jigum cikin zullumi.
Ya fito yana tsane jikinsa na tashi da sauri na bude wardrobe dinshi jallabiya na fito masa da ita da gajeran wando. Na mika masa ya kar'ba na koma na zauna yana kintsa jikinsa ya ce." Ki kawo mini abinci Amina."
Da sauri na mike ina fadin." Dama abinda zan tambayeka kenan, tun yamma na ce da Baba Tabawa ta yi towo zai fi dadin tafiya."
A takaice ya ce." Kin kyauta kuwa."
Ya d'auki turare yana fesawa a jikinsa. Na sauka kasa cikin nazarin abinda ya yi a ganina wane turare zai fesa a cikin wannan yanayin da matarsa ta rasu ko kwana daya ba ta yi a

Please Login or Register in order to submit comment