Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nufi."
Ya mutsa fuskata na yi ban ce komai ba. Ya gama cikin kifin na tattara kayan abincin na sauka da su k'asa na wanko hannuna tsaf na sake komawa saman na same shi zaune a wajen bai tashi ba.
Na dube shi sosai ina fad'in" Yau bacci ne a idona sosai za a shafa maganin yanzu ko sai na kwanta."
Ya lumshe idonsa tare da bud'e su a kaina yana fad'in.'' E, amma mu dan yi wani abu kafin wannan ."
Na gane abinda yake nufi na dan 'bata fuskata kadan ban shirya kwanan tashin hankali da damuwa da kewa ba domin dai tsakani da Allah duk yadda yake ko'karin ganin ya samar mini da nutsuwa ba ta gamsar da ni ha'kuri nake yi kawai sai nake ganin idan bai ta'ba ni ya tsokano ni ba hankalina zai fi kwanciya.
Cikin rarrashi da kwantar da kai har sai da ya ba ni tausayi ya samu ya hillace ni a daran muka yi soyayya sosai ya samu biyan buk'atarta kwarai daga nawa bangaran kuwa abin sai a hankali har sai da na yi kukan b'akinciki a toilet anya rayuwa za ta tafi a haka kuwa gashi maganin da malamin nan ya bayar ya kusa k'arewa saura na kwana biyu kacal babu wani canji.

Sai da na yi kwana uku ban sanya Hauwa a idona ba tana d'aki a kwance na fi tunanin sai ta ji sahu ya d'auke take fitowa ta yi abinda za ta yi a kicin din ta dibi abinda take so ta koma. Ai dole kunya ma yanzu ta fara har in dai ba za ta daidaita tunaninta ba ta zauna lafiya da kowa.

Kuma har yanzu duk ranar girkinta wajena yake kwana idan na shafa masa magani sai ya yi kwanciyarsa idan ina yi masa nasiha da rarrashi kamar da kurma nake magana sai ya juya mini baya kawai sai na zubawa sarautar Allah ido. Tunda duk abinda ya kamata na yi na yi wannan shine alkawarin dana daukawarwa mahaifiyarsa.
Yau ne zai je bunkure kamar yadda muka gama maganar jiya magungunansa sun kare malamin ya ce ya je ya same shi gobe Kuma Hajiya Maryam za ta cika kwana arba'in da rasuwa mun yi waya da Nusaiba kan cewa tana so ta zo gidan su yi aikin funkaso da fanke duk na gaya masa bai ce kada ta zo ba.
Da assubaha ya fita daga d'akina don haka gari yana d'an yi haske kad'an na bi shi nasan ya dawo daga massalaci yana shirin tafiya tunda ya ce su biyu kadai za su tafi da Sukairaju kuma ta jirgi ce yau din yake so su je su dawo idan lokaci ya bada damar hakan.
Na ji maganganunsu tun kafin na murda kofar d'akin sai na yi saurin cire hannuna daga handline din. Ina jinta cikin kuka mai ta'ba zuciya da 'kas'kantar da kanta tana cewa." Hajja cewa ta yi na zo na cigaba da kula da yarana to me zai sanya ka had'a kai da matarka har da masu aiki ku dasa musu tsoro da k'yamata. Tun da kuka dawo nake bin ka ina baka ha'kuri don girman Allah ka yafe mini na yi kuskure ba zan kara ba amma ka daina tozarta ni da nuna mini iyakata a gaban Amina, ban cancanci wannan wulakancin daga wurinka ba tun da ka aure ni kake nuna fifiko akan matayenka Maryam da Amina idan ka amince da cewa Hajiya Maryam tana yi maka asiri akan ta samu soyayya da d'aukaka a wajenka to wallahi ya zama dole ka amince da cewa Amina ma tana yi maka asiri domin ko makaho ne ya duba ya san kana yi mata makauniyar soyayya irin wadda hankali ba zai d'auka ba sai an bi mutum ta k'arkashin kasa. Ni da kai iyayenmu daya cikinsu daya ba zan ta'ba cutar da kai ba domin kai dan uwana ne mijina kuma uban yarana b'acin rai ne kawai ya sanya ni ajiye yaron nan na tafi gidanmu saboda jingine ni da ka yi baka kula ni naga ai babu amfanin zamana a gidan. Amma don girman Allah ka yi hakuri ka yafe mini kuma yarana su dawo hannuna don gaskiya ban yarda da tarbiyar da ake ba su ba.
Na ji shi yana fad'in." Ke a ganinki tarbiya ce dake Hauwa. Ko kin d'auka wata fitacciya ce ke a zuciyata ne? ki kiyaye ni wallahi idan za ki yi sakarcinki kada na kiara jin kin ambaci sunan Amina. Idan kin danganta Maryam dake bai dame ni ba, amma Amina ba ta da zunubi na itace matar da take rufa mini asiri cikin kowane yanayi. Babu ke a cikin zuciyata Hauwa kuma ba na tsammanin za ki ta'ba samun gurbi a cikinta. Kin yi abinda ya kamata ace hukunciki ya fi haka muni amma arzikin yara da zumunci ya hana hakan don haka ni ban ri'ke ki ba idan kin ga ba za ki iya zama ba ki tafi kawai hankalina ma zai fi kwanciya yara kuwa ai za su rayu tunda ba ke ce mai rayawa ba."
Tana kuka take fad'in." Idan kuwa aka yi mini haka ba a yi min adalci ba anzalince ni kuma wallahi sai Allah Ya
saka mini."

gudun aure littafin kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina bam

Ya furta." Ki ka zalinci kanki dai Hajiya hakkin Sultan kadai ba zai bari ki samu sau'kin zuciya ba, ni dai ba zan sake rayuwar aure dake ba balle ki samu ciki ki haihu ki ajiye mini yaro ki tafi. Ki zauna dai a gida gashinan babu wannan alak'ar a tsakanina dake yanzu."
Da tashin hankali mai tsanani na ji tana fad'in ." Wallahi abinda ba zai yiwu ba kenan ai zalinci ne wannan kuma ni mutum ce ina da bukata a koyaushe me yasa za ka yi mini haka ina kallo kana mu'amula da matarka ni kuma ka ce ba za ka yi da ni ba, zan gayawa Hajja domin wannan abin ya ishe ni ko da can ma ai sai na nema kake kula ni ba ka zuwa wajena don ra'ayin kanka sai na yi ta bin ka, da haka duka muka tara wannan yaran da ake yi mini gadara a kansu, wallahi ba zan iya jurar wannan wulakancin ba."
Ya ce." Kada Allah Ya sa ki jure din ko ni ne na ce miki ki dawo da zan damu kaina tafiyarki kwanciyar hankali da nutsuwa ta haifar mini a gidana ai ke ce ba ki sani ba."
Da gunjin kuka da jan hanci na ji tana cewa." Shikkenan na ji to ka rubuta takardata ka ba ni zan tafi har abada kuma ba zan sake sha'awar sake zama da kai ba ai ko Allah ma ana yi masa lefi ya yafe."
Hankalinsa a kwance ya furta." Idan na sake sakin ki a yanzu na zama sakarai kenan. Ki zauna dai ki ga ikon Allah aure ma zan k'ara bayan Aminata na yi rayuwata da iyalina cikin hayyaci da samun nutsuwa. Na fi ki mugunta da d'anyan kai Hauwa ko kin d'auka cewa ke kadai ce mara ji ne?"
Ta yi shiru tana jan hanci.
A hankali na ri'ke karfen baranda gabana na dokawa na fara sauka maganarsa na yi mini kud'a a tsakiyar kunnena 'aure ma zan k'ara na yi rayuwa da iyalina.' Shin da gaske ne ko kuma barazana ce kawai yake yi mata domin ya gigitata. Zuciyata take rada mini aure a ina mutumin da ba shi da lafiya babu karfi irin na jarumar maza. Daya sashen ta na ce mini duk da haka ai akwai da dama mazan da ba su gama kawar da matsalar iyalinsu ba amma suke rakito auran.
Na zauna jigum da mamaki a cikin raina. A
amma dai bari mu gani lokaci shi zai nuna.
Ina kwance ya shigo ya shirya tsaf cikin manyan kaya ya kuma yi kyau ainun kamshinsa yana ta sirnanowa hancina muka gaisa dama na ware kayan da nake so ya tafi da su turmin atamafa ne biyu da mayafi sai takalma guda biyu duka sawa ta daya sun yi mini tsayi duk da nake gajeriya ba kasafai nake son takalmi mai tudu ba na ce masa sa'kon Hajara ne a ce mata na gode da abin arzi'ki.
tare muka fito falon shiru yaran ba su fito ba suna ciki ana shirin skull.
Ya d'an tsaya yana kallona kafin ya janyo ni ya matse tsam a kirjinsa na dan wani lokaci ya cika ni tare da juyawa da sauri ya kama hanyar fita na sauke ajiyar zuciya a kasalance na ce." A gaishe mini da Hajja sosai Allah Ya tsare." Ya amsa da "Amin kafin ya fita.
Ina juyawa da zummar komawa d'aki na ga Hauwa a tsaye a bakin kofar dakinta. Na yi kasa da kaina ba tare da na sake kallonta ba na wuce sai ta zo ta sha gabana muka dubi juna.
Murya a dashe alamun ta ci kuka ta k'oshi ta furta." Kin yi nasara a kan Hajiya Maryam Amina kin dawo kaina ko, kin rantse dai sai kin rayu ke kadai a gidan nan to bari ki ji abinda ba ki sani ba ko kin yi nasarar fitar da ni daga cikin yarana tana jika domin da bakinsa ya fadi cewa aure yake nema kuma in sha Allahu rabbi duk wadda za ta shigo itace za ta karya alkadarinki."
Na jima ina kallonta sosai ina kuma tunano irin zaman da muka yi da ita a baya a lokacin da ta dinga nuna mini k'auna da kara akan rigingimun da suka dinga faruwa. Har ga Allah a lokacin na ya ba da kokarinta kwarai duk da ina cikin kokwanto tunda bata buda mini zuciyarta na ga zahiri ba a aikace take yi komai da ita muka dinga ya'ki a gidan nan akan Maryam da d'anta Salim ta yi mini mubaya'a domin jajanta mini abubuwan da suke faruwa. Wannan shine dalilin da ya sanya ni nake iyakacin bakin kokarina akan lamarinta an ce duk dan halak baya manta alheri a lokacin tare muka dinga fafutukar kwatar 'yancinmu a wajan gidan
Amma cikin wad'an nan kwanakin gabad'aya kaina ya kulle a kanta na rasa da wane ma'auni zan auna al'amuranta. Hakan ya nuna mini cewa dama can tana ya'ki ne a kan kanta domin ta cimma wata manufa tata. Lallai Ubangiji baya bacci kuma yana tare da mai gaskiya.
Na dube ta sosai ina fad'in." In ban da abinki Hauwa ai ni ban isa na kore ki a gidan nan ba. Ni a suwa kuma ke da ki ka d'auki tudu biyu ai ke ya kamata a ce kin yi nasara a kaina na fita na bar miki gidan. Amma bari ji ki sirrin nasarata a kanki da zuciya daya nake zaune dake kuma ban zalinceki ba, ban nemi kai ki kasa ta k'arkashin 'kasa ba sai ko'karin ma ganin mijinki ya duba halin da ki ke ciki na kad'aici da damuwa. Amma idan kina ganin za ki iya had'a kafadarki da tawa to bisimillah sai mu fara buga wasan daga yau ni dake. Amarya kuma ai a shirye nake da zuwanta ko kin d'auka ina tsoro ne? ta shigo mu zauna namiji mijin mace hud'u ne a ciki kuwa dole daya ta yi zarra nasan kuma na cinye wasan tuntuni. Don haka tunda kin biyo ta wannan hanyar mu zuba ni dake shege ka fasa.''
Na wuce a gaggauce na shige d'akina domin bana buk'atar sake jin komai daga bakinta. Tunda ta ce za ta iya to mu zuba daga yau na daina d'aga mata 'kafa wallahi........✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*V-VIP AREWAPEN*

*136*
Zama na yi gefan gado tare da d'umbun mamaki da al'ajabi wai yau Hauwa ce take jingina mutuwar Hajiya Maryam da ni saboda tsananin kishina da yake damunta. Kafin kowa ya san da cewa Maryam mashirika ce ita ta fara fad'in haka a bakinta na ji har nake nuna mata kuskuranta akan tabbatar da abinda ba ta gani da idonta ba. Yanzu da rasuwarta ta tona duka ayyukanta na sa'bon Allah kowa ya sheda hakan amma a yau saboda sharri da k'iyayya tana alak'anta mutuwarta da ni. Wani irin sanyi (d'ari) ya mamaye ni a take a lokacin tsabar k'aduwa da mamaki da kuma tsoron duniya. Ni dai duk yadda na kai ga kishi da nuna k'iyayyata akan kishiya ba zan iya neman hanyar da zan halakar da ita ba kamar dai yadda Maryam ta yi ba kuma zan 'kir'kiri karya ko da sharri na ya'ba mata ba. Ina da kishi sosai mussaman akan abinda nake so amma a duk lokacin da ya taso mini nakan iya sarrafa kaina zuciyata bata ta'ba kissima mini na bi wata hanyar domin cutar da kowa ba.
Zazzabi ne mai zafi ya rufe ni da ciwon kai abubuwa da yawa sun yi mini dabaibayi haka na yi wani irin bacci mara dad'i da mafarkai irin na mai mashashshara. Biyu da minti ashirin na tashi kaina ya tsananta da ciwo na daddafa na shiga toilet alwala na yi na fito na yi salla kafin na fita falon. Shiru na d'an harari kofar d'akinta a garkame kamar koyaushe tsaki na yi na wuce dakin su Baba Tabawa nan na tarar da Nusaiba ashe tun d'azu ta zo tana cikinsu suna ta hira muka gaisa sosai na tambayeta yara tace mini suna can gidan kakarsu da ta haifi Babansu. Kamar wancan lokacin ranar addu'ar uku yau ma da shirin kwana ta zo. Na ce hakan ya yi ka fi na dubi Baba Tabawa da take ta fama da Sultan yana ta rigima ta ce tana tsammanin zazza'bi ne a jikinsa don ya yi zafi. Na shiga d'akin sosai na sunkuya na ta'ba wuyansa rau zazza'bi yake da gaske kamar ni dole ne kam Dr Sailuba ta zo gidan nan ta duba mu.
Goya shi ta yi tana jijjigashi har ya yi bacci muka fito falon ni da ita ta shiga kicin ni kuma na zauna saman kujera cikin nauyin kai da bugawa.
Abiñci ta kawo mini alkubus suka yi da rana da miyar agushi ya yi mini dadi sosai na ci hud'u nasha ruwa na sake komawa d'aki na kwanta ashe tana hankalce da ni ta biyo ni dakin tana fad'in.'' Hajiya ba kya jin dadi ne tunda ki ka fito na karanci yanayinki."
Na ce." Wallahi zazzabi ni ma nake yi Baba har ma da ciwon kai."
Ta dinga yi mini sannu cikin damuwa. Na daure na tashi zaune tare da d'aukar wayata na lalubi number Dr Sailuba bugun farko ta daga muka gaisa na ce mata idan babu damuwa ko za ki zo gida ki duba ni da yaron nan Sultan nasan yau babu aiki gashi weakened muke babu matsala ko."
Ta ce." Babu komai zan shigo bayan la'asar maigidan ma baya gari ai."
A tak'aice na ce." Na gode sosai." Na kashe wayar na ajiye Baba Tabawa ta ce." Ko da akwai abinda ki ke buk'ata na game da abinci tun da naga baki ciki alkubus din nan da yawa ba."
Na ce." Da daddare ku yi mana towo a yi kuka maigidan ita yake so amma a yi mini miyata daban ta d'an yi yaji."
Ta ce." An gama in sha Allahu ta juya ta fita da sauri.''
Ledar kayan motsa bakin da Hajara ta ba ni na d'auko na tsinci tsamiyar biri na sanya a bakina saboda galmi-galmi nake jinsa na sake kwanciya da wayata a hannu. Na rasa wanda zan kira na gayawa tsakanin anti Yagana da Sahura abinda yake damuna a game da abinda Hauwa ta ce mini d'azu abin ya tsaya mini a raina. Anti Yagana na kira muka gaisa jin maganata da kasala ya sanya ta fara jero mini tambayoyi na ce."lafiyata lau amma ina zargin ciki ne da ni.'
Ta ce." Ba ki na zargi ba kin tabbatar kuma kin gayawa mai shi ko?"
Yar dariya na yi domin nasan dalilin da ya sanyata ta fad'i haka tunda artabun da aka sha a baya na ce.'' Na tabbatar gaskiya shi din ne smma yanayi bai barni na sanar masa ba amma zan gaya masa yau idan ya dawo ya je bunkure wajan Malam D'aha."
Babu tsammanin kawai na ji ta rufe ni da fad'a. Sai da na bari ta gama na ce." Lokacin da na samu cikin nan fa yana kwance anti Yagana bai ma san a inda yake ba yanzu ne ya dan fara dawowa hayyacinsa babu abinda zai faru in sha Allahu."
Ta sauke ajiyar zuciya kad'an tana fad'in.'' Duk da haka dai Amina tunda kin san halin mijinki da zargi mussaman idan kin samu ciki kamata ya yi ace yanzu ya sani tunda ai ya jima da dawowa nutsuwa ba ki da wata hujja anan."
Na ce." Ki yi hakuri zan gaya masa in sha Allahu anti Yagana ni akwai dalilin da ya sanya ma na kira ki yanzu."
Ta ce." Menene kuma?''
Hanci na dan ja a sanyaye na furta." Hauwa ce take jingina rasuwar Hajiya Maryam da ni." Duk na kwashe sa'insar da muka yi da ita na gaya mata .
Ta ja tsaki tana fad'in." Ta dawo ashe?''
Na ce.''kwarai ta dawo amma ta ki yadda mu zauna lafiya fitinar yau daban ta gobe ma daban tana daga mini hankali wallahi domin ni yanzu anti Yagana babu abinda na fi buk'ata face zaman lafiya duniyar nan tsoro take ba ni."
Ta furta." Kin ga Amina idan za ki kwantar da hankalinki ki kwantar ina abin yake me yasa Hauwa zata razanaki har ki dinga jin fargaba a kanta. Ban yarda ki zalinceta ta kowace siga ba amma ki daina raga mata balle ta hangi lagonki ta raina ki tunda ita Yar iska ce mara mutunci to sai kema ki sanya rigar rashin mutuncin ku buga aga wanda zai ci riba ina dalilin wannan masifar."
Na ce." Anti Yagana ai na riga na yi wa Hajja alkawari ba na so na biye mata wata matsalar ta faru wadda Hajja za ta ji haka kawai dattijiwar take ba ni tausayi wallahi a ganina idan nima na biyewa Hauwa kin ga mun zama sakarkaru gabad'aya kuma maigidan ba zai samu nutsuwa ba.''
Ta ce." Ai ba cewa na yi ki biye mata ba Amina ki fita daga harkarta ki daina raga mata ko ki nuna mata kina son zaman lafiya da ita. Kuma ki yi duk yadda za ki yi wajan ganin kin sake samun gurbi a zuciyar mijinki abinda nake nufi kenan."
Na ce." Ni ma shawarar dana yanke kenan wallahi."
Ta furta." Dada kuwa ba ta da lafiya sosai Amina har sai da ta kwanta a asibiti kwananta biyu jiya aka sallamota."
Da damuwa mai yawa na furta." Mai yake damunta ne?"
Ta ce." Lalura ce kawai irin ta girma da shekarun yau ta ce kafafunta na ciwo gobe ta ce bayanta ya 'kage abinda dai ya tsananta a ciwon har ta kwanta a asibiti ciwon wuya da ta yi eanda ta kai ta kawo ma ba ta iya motsa wuyan ya 'kage amma yanzu alhamdulillahi da sauki."
Cike da tausayinta na ce.'" Allah Ya sawwa'ke idan ya dawo zan gaya masa wata'kila mu zo dubata. Anti Yagana ina labarin Ya falmata ne ko a Whasap na jima ban gan ta ba kuma mun jima ba mu yi waya ba.
Ta ce." Ai Ya falmata tana saudia neman kud'i Baban Saude ya shige mata gaba wajan mahukunta sai da Alhaji Bana ya sake ta."
Na ce.'' To kin ga wannan shine adalci ai ko banza ana samun jajurtatun iyaye a family kamar irinsu Baban Saude da yawa mazan da suke zalintar matayensu za su shiga hankalinsu.
Abinda ya faru shine kowa ya san da cewar Ya falmata macace mai zafin nema domin ni kaina itace madubina kuma sai da na takata tukkuna na tashi. Harkokinta sun bukasa sosai a lokacin da muka had'a karfi da k'arfe domin gina gobenmu muka tashi a tare. Tun bayan da na yi auran nan sai kasuwancin da muka yi da ita ya raunana dalili duka ta nuna mini hanyoyin yadda zan dogara da kaina da kuma yadda kayana za su cigaba da zaga 'kasashen waje irinsu sinigal nijar mali kamaru da chadi har ma da saudiya dama kusan sune suke sayan kayanmu a lokacin da muke fafutar ganin mun tashi manyan matan abuja ma suna saye amma duka ta hanyarta tunda ni ce mai aikin dinkawa na yi mata odarsu zuwa maiduguri ta rarraba a sassasa daban-daban.
Ta cigaba da kujiba-kujibarta ni ma na cigaba da yin tawa har Allah ya sanya ta bude katafaran shago ta zuba iyayen kekunan d'inki manyan kai da k'ananu ya yara suna aiki. Shekara daya ta sake bude wani a takaice dai sai da shagunanta na d'inki suka kai biyar kuma shago bai wai karami ba wanda yake iya cin sama da keken d'inki goma sha biyu.
Mijinta Alhaji Bana shine silar karyata domin had'a ba ki ya yi wasu daga cikin yaranta suka dinga kwashe mata kaya cikin dare suna fita da su a baggo. Idan suka sayar su raba kudin kashi uku shi ya d'auki kashi biyu yaran su d'auki kashi daya. Wataran rigima ta shiga tsakanin yaran nata da suke aikata mata haka har da makami abinda ya assasa musu zuwa gaban hukuma kenan daga nan sai suka fara tonawa junansu asiri dama kuma gefe guda ta sanya Malamai ana ta yi mata ro'kon Allah itama ta tsananta da addu'a. Suka fadi mijinta ne me sanya su da ya ji duka da matsa ya tabbatar da sanya hannunsa wanda da da farko ya fara gardama da jayayya yana fad'in yaushe zai kai matarsa k'asa uwar yaransu har biyu. Daga lokacin ne ta yi tsalle ta dire ta ce sai ya saketa har suka shiga kotu alkali ya yanke musu hukunci daidai da abinda suka aikata ya kuma tilastashi sakinta tunda gaskiya ba namijin da kowace mace za ta yi sha'awar zama da shi ba ne.
Anti Yagana ta cigaba da cewa." Ai tana fita idda ta lallaba Dada ta tafi makka wata shida fa yanzu tun bikin Fadila
Na ce." Allah sarki Ya falmata zuciyarta a tsaye take irin ta Baban Saude ba ta son zama koyaushe tunaninta ya za a yi ta juya biyar ta koma goma. Amma ni da ta yi shawara da ni zan ce mata ta yi zamanta anan ta cigaba da sana'arta kamar zai fi alheri."
Ta ce." To ta dai ce shekara uku kacal za ta yi ta dawo sai dai mu yi mata fatan alheri kawai."
Na ce." Ubangiji Allah Ya taimake mu bakidaya anti Yagana ke kuma me ki ke sayarwa?" Na tambayeta cikin sigar tsokana."
Ta ce." Babu komai hankalinta a kwance har sai da na yi dariya na furta.'' Babansu Fadila ne ya tsaya miki anti Yagana shiyasa kike wanke goma ki tsoma biyar ba ki da matsala."
Ta ja tsaki tana fad'in." Amina ai sai mutum ma ya rasa wace sana'ar zai yi wallahi maza daga waje duk sun k'wace mana abin yi."

Na kudi ne littafin don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na ce." Anti Yagana ba ni so ki kasance daya daga cikin matan nan da barmani coge take yi wa wa'ka (Sakarai baki da wayo) na yi dariya ina fad'in." Ki yi nazarin abinda za ki sayar na baki jari don Allah."
A tak'aice ta furta."Aikuwa na gode sosai ai ba ki ga yadda Fadila take cinikin ruwan sanyi ba cikin nan da take d'auke da shi ya hanata fara zuwa koyan d'inki don har mijin nata ya sayo mata form na makarantar."
Na ce." Ai ni ya burge ni sosai da ya ke so ta yi Sana'a dalili kuwa rayuwa juyawa take yi ga kuma yadda duniyar ta zama komai ya yi tsada tunda karamin ma'aikaci ne za su taimake ki kan su anan gaba"
Ta ce." K'warai kuwa hakane ni ma in sha Allahu zan yi nazarin abinda zan sayar idan na yanke shawara zan sanar da ke."
Da jin dad'i sosai na furta.'' Yawwa anti Yaganata ko ke fa" Dariya ta yi kawai muka yi sallama cike da barkwanci da k'aunar juna irin ta jini.
Wayar mu da anti Yagana ta kara mini karsashi da kuzari na tashi na je na dauro alwalar

Please Login or Register in order to submit comment