Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah Ya sa shi din ne, domin a jikina nake ji hakan!"
Na dube shi ganin yadda ya zura mini idonsa ya sanya na ce ." Amin Allah Ya sa shine."
Ya kuwa sauke ajiyar zuciya yana fad'in." Na gode miki sosai Allah Ya yi albarka."
Na amsa da Amin a takaice kafin ya sake kallona a karon da babu adadi.
"A game da abinda muka sanya a gaba ni dake a yanzu nake so na ji a ina aka kwana ina so mu wuce wannan wurin ne zan je Legos ina da uzuri a can din amma ni kad'ai nake son tafiya."
Na ce." Business din da nake yi cikin garin kano na zannuwa takalma da huluna nake so na kawo shi nan din kamar yadda na gaya maka da farko amma ina so shaguna biyu na zuba supplements ina so na jarraba ana samun alheri."
Ya d'an yi jim kafin ya ce."Supplements kayan gyaran jiki na mata da kwalliya ko?"
Na gyad'a kaina idona a kansa ya ce ." Hakan ya yi Allah Ya ba ki sa'a, amma ba ki sha'awar sayar da kayan maza ina nufin irin wanda muke sanyawa tunda harkar huluna ta kar'be ki sai ki sa hannu anan din domin mu ga abinda Allah zai yi."
Na ce." Hakan kuwa ya yi sosai na gode da shawara Allah Ya saka da alheri zan yi ko nan gaba don ba ni tsammanin abinda yake hannuna a yanzu zai ishe ni yin duk abinda nake buk'ata.
Ya ce." Ni zan yi miki order domin shirya shagunan tunda na bada shawarar yin hakan amma har yanzu ba ki fitar da sunan shops din na'ki ba. Ita kanta plazar akwai buk'atar a samar mata da suna na mussaman ko?"

Nan fa d'aya wallahi na manta shaf kuma dai da kunya na ce masa sauran shagunana suna d'auke da AminatuAminu collocation ne. Tun lokacin da na fara bud'e shagon d'inki na sanya masa A-A fashion designer hakan na nufin AminatuAminu sai Kuma da na bud'e shaguna tukkuna na bud'a sunan kowa ya gane abinda nake nufi kuma har zuwa yanzu wannan tambarin ne a jikin duka shops dina sai dai a sabunta idan ana so a sake 'kawata lamarin. Ina so a ko'ina ya cigaba da tafiya a haka domin cirewa customer's d'inmu shakku da kokwanto.......

Masu karatu ku ba mu sunan da ya kamata a kira shop's din Amina na Abuja don Allah kada a yi rashin adalci.......😃
Plazar dai na yi mata suna da (GIWA PLAZA) shin ta cigaba da amfani da AminatuAminu tunda da shi a kasanta.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP #700 VIA 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*173*
Har yanzu idanuwansa na tsaye a kaina jikina ya k'ara yin sanyi kasala ta mamayeni bakina ya mini nauyin da na kasa ce masa ga yadda nake so komai ya tafi daidai da abinda na gina shekara da shekaru ai da kunya da nauyi duk da yanzu babu shi a raye a duniya amma mafiakasari mazan mu na yanzu ba sa rasa abin kishi koda ga wanda ya mutu ne mussaman da na riga na fi kowa sanin halinsa mutum ne shi mai zazzafan kishin tsiya. Kawai sai na tsinkayi maganarsa yana fad'in." Za mu cigaba da kiran shops din da AminatuAminu ne ranki ya dad'e?" Ya fad'a yana dago fuskata da tafin hannunsa.
Na dube shi cikin wani irin yanayi ya aka yi ya san abinda yake d'auke kenan a jikin banner da logon shugunana tunda ban ta'ba daukarsa na kai shi ba kuma ban ta'ba nuna masa bidiyon abinda ya danganci harkokina ba.
Ya d'an yi murmushi yana fad'in." An gaya miki shashashan namiji kike aure Amina. Bari ki ji abinda ba ki sani ba tunda na aure ki idona akan harkokinki yake da cigaba da fad'uwa duk ina samun labari mussaman na samu lokaci Hamusu ya jagorance ni ya nuna mini shagunanki a cikin kasuwar kwari yana kuma gaya mini irin yadda nauyi da hidima suka yi yawa akan ki akwai abin mamaki ne a anan don miji ya bibiyi sha'anin matarsa. Tunda kina shakkar ki nuna mini ciki da wajenki ni na bibiya domin samun nutsuwa kuma na yi miki murna da farinciki kin zama mace mai kamar maza a cikin maza kashi dari kin take hamsin sauran sakarkarun su d'auki hamsin domin jajurcewarki akan neman halak ba kowane namiji ne zai iya abinda ki ke yi ba a yanzu kuma ina yi miki fatan alheri tare da addu'ar Allah Ya sa ki fi haka."
Tun da ya fara maganar kaina yake a sunkuye d'agowar da zan yi sai ta yi daidai da zubowar hawayen da ya taru a cikin kwarmin idona suka fara sauka saman kumatuna bakina ya dinga rawa magana nake so na yi amma gabad'aya ya gama d'aure ni da jijiyar jikina na rasa shin godiya zan yi masa ko kuma rungume shi zan yi."
Ya d'an 'bata fuska yana fad'in." Kina ba ni mamaki wasu lukutan Amina shin ni din kuwa ina da abinda zan biya ki bisa abubuwan da na samu ta dalilinki. Kada ki manta da cewa babu wani arziki madaukaki anan duniya mai sanya farinciki da annashuwa face na haihuwa tabbas Allah ne yake bada ita bayan na yi godiya a wajensa wajibi ne kema na yi miki bisa samun sanyi idaniya da kuka ba ni. Babu buk'atar godiyarki ko zubar hawaye ina so ni ma na shiga cikin ladan da kike samu don haka don na sanya miki hannu cikin lamarinki kaina na yi wa taimako babu wanda ya san gawar fari sai Allah ko bayan babu raina ina da tabbacin yarana kaf da naki da ba naki ba ba za su wulakanta ba.''
Hannuna na sanya na sar'kafo wuyansa ina kuka sosai wanda yake fitowa daga can karkashin zuciyata. Ya d'ora hannuwansa biyu a gadon bayana yana d'an bubbugawa kafin ya dago fuskata muka dubi juna da wani irin murmushi a fuskarsa ya furta." Kukan sam bai yi miki kyau ba giwa na hango muninki." Ya sanya yatsu yana ta'be mini hanci da kumatu haka dai na dinga daurewa ina cire hannunsa yana mayarwa dole dai sai da ya sanya ni dariya ya cika mini kumatu yana fad'in ." To ko kefa kuka ko mutuwa na yi kada ki yi mini kuka domin abin sai ya zai zame mini biyu na tafi na barki wata'kila shekaru kad'an ki manta da ni wasu mazan su fara zawarcinki."
Na ce." Don Allah wace irin magana ce wannan ka daina ba ni son jinta."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Gaskiya ne ai Amina idan na rasu mazan zamanin nan ba za su iya d'auke ido a kan ki ba."
"Idan ka riga ni rasuwa babu yadda zan yi ba kuma zan kalubalanci Ubangiji ba domin ni ma ita nake jira amma ka sani wallahi ko shugaban kasa ne zai fito neman aurena ba zan aure shi ba na gama aure har abada zan zo na riskeka a aljanna mu cigaba da rayuwa."
Yana dariya sosai ya ce."Shugaban kasa fa Amina?' Na tare shi da saurin gaske ina cewa." Ko da sarki ne wallahi ai na gama yin rashin mijin da babu wanda ya isa ya maye mini gurbinsa to me nake nema a duniya komai ka yi mini fa."
Fuskarsa ta yawalta da wani 'kasaitancen murmushi yana ta 'kan'kance idonsa a tsakiyar nawa idon dad'in kalamaina sun sanya shi cikin wani irin shau'ki ya rasa ma abinda zai ce mini duk bakinsa da iya maganarsa na kashe shi a zaune sai murmushi.
Na cigaba da cewa." Kamar yadda ka kawo shawara hakan za a yi Plaza ta cigaba da amsa sunanta na (GIWA PLAZA) Shops din kuma AminatuAminu na amince da hakan na kuma gode bisa wannan kara da ka yi mini Ubangiji Allah Ya bar mu tare."
Ya rike hannuna na dama ya had'e yatsun waje d'aya ya d'amke sosai." Za a yi hakan in sha Allahu amma sauran shagunan ai ba ki da hurumi tunda hayarsu za ki bayar dole masu kar'ba sune suke da zabin abinda za su sayar a ciki kin gane abinda nake nufi ko?"
Na gyad'a kaina a nutse na ce.'' Na gane ni dai wurina sunansa GIWA PLAZA saboda suna ne na mussaman da babylove ya sanya mini kuma ina alfahari da sunan ya fito daga bakinsa."
Ya sa dariya har sai da duka hakoransa suka bayyana." Me yasa ba ki ta'ba nuna mini sunan na yi miki dadi ba uhumm?"
Ina murmushi na ce." Wallahi da gaske sunan dadi yake yi mini har wani tunkaho nake yi fa?"

littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Aikuwa dadi ya ishe shi ya kwanta saman gado yana ta dariya sai kace wani shashasha ni ma ina ta ya shi yau na gama kashe masa karsashin jiki da 'yan kalaman da ba su wani sun kai sun kawo ba abin har ya ba ni tausayi wato ita soyayya jahilar mahaukaciya ce babu talaka babu mai kudi haka zalika babu sarakai babu attajirai duk lokacin da ta so illatarwarta sauka take yi a duk inda ta so ta yi sharafinta amma idan ba ita ba din ba ai ban ga wani dalilin da zai sanya mutumin nan yin wannan dariyar ba wallahi.
****
Lamarin da ya kara dakusar mini da jiki akan sha'aninsa yadda da kansa yake yi mini tallah status d'insa da kuma babban pege dinsa na facebook da Instagram bayan an gama shirya duka shagunan shidan kowanne d'ankare da kayan masu inganci da quality shaguna biyu da ya yi alkawari sai da ya shirye mini su da lates Textiles yaduka na manya da shaddodi d'ankare kowace kanta abin gwanin burgewa shagon cosmetics d'aya na supplements d'aya d'ayan kuma na zannuwa leces atamfofi kowane nau'in da b'angaran abaya (dogayen riguna) d'ayan kuma ya zama na takalman mata da maza da kuma b'angaran huluna iri daban daban. Mussaman ya sanya masu shirya advert da muryar da lallai dole ta isar da sa'ko aka yi bidiyon na mussaman tun daga kan shagunana na kwari market har zuwa wad'annan sabbin da aka bud'e. To sanya hotonan wajan a peges din sa na sadarwa ya sanya jama'arsa yin shearing kafin ki ce me messages na 'yan uwa sun fara cika inbox dina mussaman daga maiduguri mutum kusan shida na buk'atar samun gurbi daga cikin dole ne a cikinsu zan duba wad'anda suka dace daga cikinsu.

Rasa abinda zance masa na yi tunda ya ce ba shi buk'atar godiya sai dai daga zarar na kalleshi sai na ji tausayinsa ya tsirga mini har ina jin taruwar hawaye a idona da kansa yake ta yi mini tallah ya cire girman kai ya cire son a sani ya kuma cire k'yashi irin na wasu mazan ya kuma nuna shi din duk arzikinsa me nema ne ya kuma tabbatar mini da cewar abinda ya yi shine kasuwanci domin kuwa shi arziki ai ba a nemansa da sau'ki. Ban yi gangancin kwatanta abinda ya yi ba a ganina yadda jama'arsa ma suke sharing ya isa gefe guda kuma daga can kano Hamusu da Usaini suma sun dage sosai da tallah ta kowace kafar sadarwa abin ya yi ta ba ni mamaki.
A daran na amsa wayar Baban Saude addu'a ce dai da fatan alheri anti Yagana Sahura Hadiza ma ta kira ni Ya Falmata kuwa kamar ma ta fi ni farinciki fadi take yi na jima da gaya miki cewa akwai haske cikin rayuwarki domin kina da nasibi gaba kad'an za ki zama abar kwantace.
Washe gari da safe kafin ya fita yake gaya mini akwai wanda suka gama magana da shi gogaggene fannin kasuwanci kuma mutum ne mai kula da amana don haka ya saya mini sabbin layikan waya shi wanda ya kira da Lawan zai zama kamar manager a wajan domin sa ido da kuma kula da yaran da za a sanya a shagunan
sannan akwai buk'atar samar da securities saboda dukiyar da aka zuba shaguna dai tuni an kar'be su domin a yinin ranar da bidiyon ya fita duk guda shidan kyasa da sama aka kama saboda sun yi sau'ki duk kuwa da cewar an kashe kudi an kuma yi komai cikin inganci ga soler ga Ac sannan ko'ina teis kuma akan miliyan shida duk d'aya ga wurin fuskar jama'a daf da titi jama'a na hada-hada a fannin babu cunkoso mai yawa. Wallahi cikin yammacin ranar naga shigowar kud'ina miliyan talatin da shida. Ya kira ni domin ya tabbatar da shigowarsu ya ce kudin shagunana ne yaa katse jin na fara yin godiya abinda baya buk'ata kenan.
Sai da ya dawo yake gaya mini sun yi waya da Baban Saude har da Babanmu ma suna yi ta yi masa godiya na ce nima duk sun kira ni sun yi mini addu'a sosai. Anti Yagana kuma tun abin nan da ya faru a lokacin da ya yi mini kyautar kamfani suke jin kunyar juna ita dashi Ya Falmata ce dai ta kira shi a waya har ta had'a shi da Dada sukai ta yi masa godiya.
Wannan shine abinda ya haddasa mummunan rikici tsakaninsa da Hauwa wanda ya kaita ga tsautsayin kunnawa gidanta wuta tunda tsabar bala'in da tashin hankali a ranar da taga abinda yake faruwa a social media da kuma status dinsa ta d'ora abinci jallop din taliya har sai ta babbake ta yi baki tana can d'aki a kwance ta manta tana ta kuka gidan ya fara canzawa da k'aurin hayaki ga mai aikinta Ladidi bata nan ta je ganin gida. Sulaimanu mai yi mata hidima gidan shi ya ankara domin masu gadi na can nesa abin bai je musu ba ya shiga gidan a gigice hayaki da kauri daga kicin tukunya ta yi jajawur gas na neman yin bindiga da ita da shi Allah ne yasa suna da nisan kwana ya yi namijin kokari sosai domin kuwa shine ya tunkari gas din ya kashe ya toshe hancinsa a gaggauce ya fita sai a lokacin ne ta fito a ki'dime ita da shi suka yi waje Ubangiji Allah Ya ta'kaita k'auri da haya'kin suka gama fita tukkuna ta koma cikin falon. To tundaga ranar suke rikici shi fad'ansa yana so ya ji dalilin da ya sanya take nema ta had'a masa gobara a gida domin dai duk b'oyenta sai da ya gane lallai akwai abinda ya faru a gidan kuma Sulaimanun bai boye masa komai ba. Ta dinga kuka tana fad'in sai ya saketa ita gaji ya ce shi kuma haka kawai ba zai yi saki ba sai da hujja. Rikicin dai har sai da ya kai su gaban Hajja anan ne ta fad'i abinda yake sasakarta Ya gina mini plaza ya ya zuba mini kaya sannan ya kuma bude mini shaguna a kasuwar kwari guda uku ita kuma ya had'a ta da wani lalataccen kamfaninsa da ya tabbatar da cewa shi kansa ya tashi daga aiki don haka wallahi idan har adalci za a yi itama a yi mata plaza sannan a bude mata shaguna. To sai a lokacin ne ya san dalilin tashin hankalinta. Ya ce yadda ya mallaka mata kamafani ba tare da ya cire na'urorin da ake aiki da su ba haka zalika don ya gina mini plaza ya sanya mini kaya a ciki ba lefi ba. Duk abinda yake yi yana sane yana kuma yin aiki da ilimi da koyarwar Annabi domin yin adalci cikin ni da ita babu wadda ta sanya shi ba mu wani abu daga cikin dukiyarsa shi ya yi ra'ayi a lokacin ya jaddadawa Hajjan cewa plaza kad'an ya yi mini a madadin kamfanin da ya bata sauran shagunan da take tunanin shi ya bud'e mini ba shi da hannu tun kafin ya aure ni nake neman kudi ita kanta Hajjan ta san da haka tunda da farko ganin yadda Hauwa ta yi bala'in shiga damuwa ta ce a samu sulhu kawai ya kar'bi kamfanin tunda ita din macace zai wahala ta iya kawo masa cigaba sai ya yi mata yadda take so. Amma jin haka sai jikinta ya kara yin sanyi tuntuni ta fahimceta zafin kishinta da ganin Ido shine zai kai ta ya baro.
Kwanansa biyu a kano suna buga artabu Hajja ta ce a sayar da kamfanin a bata kudin shi kuma ya ce bai gina shi don ya sayar ba. Adalci d'aya da zai yi mata zai cigaba da kula mata da shi domin ganin ya sake yin shura yanzu ma ba wai aiki ne ba ya yi ba, kawai dai yawaitar massarafuwar kamfanin sabulun da suka yi yawa ya sanya kasuwarsa ta kwanta dama amma a rana akan iya fitar da kwali dubu ko fiye da haka ina lefi. Hajja ta ji dad'in hakan domin sai take ganin ba wani abun bane a ganinta ma wanda aka bawa kamfani guda ai ya fi morewa ta sallame shi ta ce ita Hauwan ta kwana biyu a wurinta domin a ganinta cikin kwanakin da za ta yi zata iya tausarta ta rarrrasheta ta ha'kura amma ina Hauwa ta wuce da tunaninta washe garin ranar da ya tashi Hajja na dyakinta da safe misalin goma da kwata tana sallar walha Hauwa ta bar gidan cikin matsanaciyar damuwa da tashin hankali bauci ta nufa zuciyarta cike da bakinciki da kuma neman hanyar da zata warware damuwarta.......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*174*
To duk yadda ya kai da ko'karin ganin ya b'oye abinda yake damunsa sai da na hankalta cewa lallai a cikin matsanaciyar damuwa yake wadda ma take ko'karin ganin ta ta'ba wasu muhimmanan al'amuransa mussaman da ya d'auki dabi'ar shiru da nazari. Hankalina sai ya rabu biyu daya a kansa daya kuma akan harkokina da suka fara kafuwa wanda shi din ne ya zama sila kuma ma'kasudi domin dai ya taka muhimmiyar rawa wadda ta zama tushe kuma matakin nasara shaguna har mun tsayar da ranar bud'e su wadda muke sanya ran cewa a cikinta za mu yi promo ga customers dinmu na farko mun tallata daga can kano zuwa abujan da sauran jahohi bisa jagorancin mutumin da ya had'a ni dashi Lawan wanda na tabbatar da cewar shi din za'kwakuri ne tuntuni sun yi masayar lambobin waya da su Hamusu. Kuma mun gama magana da Baban Saude kan cewa zai ba ni yaransa biyu duk da acan suna sana'ar huluna da sayar da yaduka mabambamta mussaman na hijabai da ro'ko da magiya ya amince mini domin duk wad'anda suka nemi samun gurbin zama duk da cikin family dinmu suke Ya Falmata ta ce a a daya muka d'auka daga cikinsu Halifa karamin k'aninsu Banandi sai Abahuraira da kaninsa Saifullahi yaran Baban Saude daga can kano kuma gidanmu na ce idan Hamusu da Usaini za su taho sai Ashiru ya biyo su shima tunda shi Saminu suna tare da Yusi a shago daya wanda koyaushe yake sake bunkasa dalilin kokari da cigaban da suke kawo masa a zamanance. Wannan yanayin nasa gabad'aya sai ya dakusar mini da karsashin jikina hidimar dai kawai nake yi amma gabad'aya bana yin ta cikin dadi dalili ko bai gaya mini cewar akwai matsala tsakaninsa da Hauwa ba dole na gane tunda ya fi sati daya yana kwana a gidana sau d'aya da na yi masa magana ya 'bata ransa yana ba ni amsa kamar ba ya so sai ban sake ce masa komai ba na zura masa ido amma dai yau na yi niyyar takureshi akan sanin abinda yake faruwa yanzu abinda na gama fahimta a game dashi Hauwa ce matsalarsa tunda zahiri da bad'ini Allah Ya riga ya gama yi masa komai
Ilai kuwa ita din ce domin dana matsananta masa da tambaya abinda yake zuciyarsa ya furta mini Kai tsaye Amina zan saki Hauwa.
Zahiri na ji fad'uwar gaba da tashin hankali lokacin da maganar ta fito daga bakinsa ban kuma yi mamaki ba domin tsananin tunani da nazarin da yake yi akan lamarin ne shin ya aikata ko kada ya aikata tsayin shekarun zamana da shi na fahimci mutum ne mai nisan tunani kuma bai fiye yanke hukunci cikin fushi ba yakan ta jujjuya lamari yana nazari a kansa kafin ya yi hukunci ga misali nan akan matarsa Hajiya Maryam da ta rasu kafin ya amince da abinda ake magana a kanta sai da aka kai ruwa rana har ya gani da idonsa ya kuma tabbatar.
Jikina ya shika sosai na zuba masa idanuwana shima ya zuba mini nasa ido babu annuri ko kad'an a saman fuskarsa ya cigaba da cewa rabuwata da yarinyar nan shine kwanciyar hankalinmu gabad'aya domin kuwa Hauwa ba ta shirya zama ta gyara mini gidana ba har ta ba ni nutsuwa da kwanciyar hankali irin wadda nake samu a wurinki. Ni ba sakaran namiji ba ne don haka ban ga dalilin da zai sanya a ce wata mace na raba mini hankali ba. Abu biyu suke ri'ke da Hauwa a hannuna a yanzu kuma su nake dubawa shiyasa duk abubuwan da take yi nake kawar da kaina a kanta ba wai tsoron rabuwa nake da ita ba kamar yadda take nuna hakan. Ko yau na rabu da ita gobe ina iya auro wata a madadinta idan har ina da ra'ayin hakan don haka tunda kin nemi da lallai sai kin ji matsalata to wannan ce."
A kasalance na ce." Ko zan iya sanin dalili, ai dai ka san haka kawai ba a sakin mace sai da dalili, gaskiya ka yi hakuri abin kunya ne a tsakaninku dukkaninku kun girma fa."
Ya gyad'a kansa ." Dalili akan ki ne domin duk zargi da tashin hankalin da ta shiga ganin kasuwancinki tana ganin ni na kafa ki na ce mata a a ni ma cikin nema na gan ki muka yi aure kina neman ki, bata yarda ba ta kai kara wurin Hajja wai kamar ni Hauwa ke yawon kaini k'ara saboda ba ta da mutunci tana ganin na fifitaki ina kashe miki kudi ita na bata tsohon kamfani sai dai a canza mata da abinda na yi miki shin a cikinku ko akwai wadda ta sanya ni d'aukar dukiyata na baku, alheri ne kawaii na yi muku ganin tare duka aka nemi dukiyar daku tana ganin abinda na yi miki ya fi wanda na yi mata akan hakan kuwa lallai ranta zai b'aci don ban ga dalilin da zai sanya ta tsananta k'yashi a kan ki ba, kema Allah ne ya yi miki daidai gwargwado kuma kin nema ni hannu kawai nasa miki kuma sai daga karshe ko ba haka ba ne?"
Na gyad'a kaina ina fad'in." Hakane amma akan hakan ka ke cewa za ka saketa ai ba hujja ba ce wannan kuma abinda ta nema ka fi karfinsa don ta tsananta kishi da k'yashi a kaina babu lefi ko ka manta kishi ne a tsakaninmu kowa fa da irin zuciyarsa, wallahi ban ji komai ba amma don girman Allah in dai zan baka shawara ka d'auka to ka yi mata yadda take so tunda kana da iko ka daidaita tsakaninmu itama ka bude mata plazar sai ka kar'bi kamfanin ka kawai tunda dama wahalarsa yawa gareta."
Ya girgiza kansa." Idan na yi mata plaza sauran shops din na kwari market kuma wa zai yi mata? tana cewa ai duk ni na yi miki"
Yar dariya na yi kad'an na ce sai ka yi mata menene a ciki ai Allah Ya hore maka?"
Ya girgiza kansa a nutse ya furta." Babu wanda zai karya mini rantsuwa Giwa ai na ce ta bar shi a hannuna zan a cigaba da aiki da shi a madadinta kuma abinda take han'koro za ta samu rashin yarda ne kawai da ci da zucci. Ba zan yi wata plaza ba yanzu wannan shine karshen magana."
"To kasan halinta da rashin yarda da kuma taurin kai kenan idan kai da kake matsayin jagora baka yi yun'kurin ganin ka nemo mafita ba lamarin zai lalace ai."
"Ai na nemi mafita tuntuni aiwatarwa zan yi kawai ko kin ga na yi miki kama da namijin da mace za ta juya ne Amina. Wasu lukatan Kawai ina biye muku ne domin ba

Please Login or Register in order to submit comment