Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawar nata gardama ba .
Yadda ta kyale mijin nasu bata yi mai magana ba shima haka ya shareta bai fada mata cewa sunje wajen salma ba ai saima mamaki da duk sukeyi da junansu.
Inda ita tana mamakin yadda ya iya zuwa gidan sulaiman din to yace mashi me yaya zai gabatar mashi da kansu a lokacin matsayinshi na mijinta a wajenshi.
Tsuki taja tana rayawa a ranta cewa sai dai in salma zata fada mashi ba ji yadda ya koma yanzu daya talauce dinnan ita kanta yanzu haushi yake bata sosai wallahi kamar bashi bane dan kwalisa a baya da kake so dagani amma yanzu duk ya koma wani jagal dashi haka babu dadin gani ai sai yasa sulaiman din jin dadin hakan a yanzu.
Shikan Alh Rufa,i cefane yayo da kudinsa yakaiwa mahaifiyarshi nata ya kawo gidanshi dama ranan Naimace zata karbi girki ta shige kitchen ta shiga dahuwa abinta tana daki duk haushi ya kumeta a lokacin.
Bayan mun gama wayan dashi ya bugo min yana ta zabga min godiya nan nake tunane ta zan taimakawa bawan Allah nan nima.
Don bani manta alherinshi akan mu a baya ya taimaki rayuwan mu a lokacin da muke cikin bukatan a taimake mu din don banda shi da kawu hassan da kanzo dubamu ya kawo muna abu wanda a karshe baba zaisa mu fito da abjn yace a raba dukka gida muda matanshi wanan yasa yaya fadila ta soma dabaran boye wani abin idan an bamu a lokacin don ya dan wadace mu.
Ban fadawa kowa shawaran dana yanke ba amma nayi alkawarin zan taimaka mashi din hakan yasa na shawarci mijina kan zance kada yazo yaji daga baya hakan bai mai dadi ba.
Lokacin dana fada mai shawaran dana yanke din sai cewa yayi kin rigani ke nan nima nayi tunanen a taimaka mai ko ya dan farfado ya kama iyalinshi ko don saboda ita hindatu din da yake aure ?.
To kuma sai naga kada yayi tunanen mun raina mashi ga hakan da muka ganshi ba laifi zan kara maki wani abu idan yazo din kunyi shawara dashi .
Mai karatu ban tabo maki bangaren jamila ba don mun hadu ranan da naje gaida hjy inna gidanta ina jin wani ya fada mata cewa gani gidan ai.
Sai gata ta shawo kwalliya ta shigo tana fadin wai inna tana da dan goro ta bata zuciyarta ke tashi tun safe ?
Goro jamila yaushe rabona da goro ai tunda likita ya hanani ci na kiyayeshi ko an ban kyautarwa nakeyi don ma kada in gani a kusa dani inci.
Ta juya inna din ke fadin baki ga bakin ku bane sunzo gaudamu jamila ga yarki can a hannun zarah ke miko mata ita ta ganta mana ?
Baki suwaye kuma ta fada tana wani abu kamar irin manta nan yan dandi inna tace jam salma din ne abokiyar zamanki baki gane ba ga yarki nan ai bakutu da ita.
Humm inna ke nan kina son wani zance aini banda wata abokiyar zama kema kin sani saidai in nashi abokiyar zaman zan yarda.
To haka abin yake lokacin na dakatar da wayan da nakeyi nace haka zalika don bansan da wata shara a gidan mijina ba irin haka ?
Banda surutu amma kuma bani barin kota kwana ga duk wanda yaso kawo min raini a take nake mayar da martani ga mutum haka halina yake.
Ta zata zatayi min iskancinsu da fitsara irin da nasan su gwaggo dashi tun a baya sunawa mutane na cin fuska shine itama ta yafa tazo zatayi min a lokacin.
Sai na fahinci idan na biye mata a wajen yadda take haukan nan zamu zamo daya da ita a lokacin mu bamuzo wajenki ba gurin uwata nazo don ke baki da matsayin da zan tako zuwa wajenki dama.
Na kara fada mata daga haka nayi shiru ina dakilan wayata itako sai abinda ta manra yake fitowa bakinta zagi harda iyayye da duk wani shakikina take hada min a lokacin.
Ita ko inna sai fadi take da nasan rashin mutuncin da zakuyi ke nan da ban furta hakan ba a gabanki ?
Ni dai banyi magana ba ban kuma san wanda ya kirashi ba na daiji muryanshi ya shigo yana fadin dama na fada maki duk kikai min haka a gida ba zan kyale ko waye ba yanzu meya kawo ki nan wajensu ko sun shiga bangarekine ?
Kazo ka shigar matane na taba yar gwal ko toka shigar mata din mugani ai ina iyawa daku duka dama kai ka ja min raini har take gani kamar tafi kowa a yanzu ?
Duk wanan abin nice na jawoshi ko jamila nidana nuna maki yarku shine kika mayar da abjn fita inna ke fadin hakan a cikin damuwa lokacin.
Ki fice nan ki basu waje ko yanzu ranki ya baci dake da duk wani na tare dake kuwa a garin nan meye haka son Allah kin koma kamar mahaukaciya saboda kishin banza da wofi ?
Dama ai iyaka kace zaka sakeni sanoda ita ko ka sake din ita kuma ta samo zani ta goya ka dashi ta kewaye garin nan tasa ka sakeni taji dadi ?
Inns sai kolarin fitar dashi waje takeyi nikan hankalina yana a waya ban kula da haukanta ba don na zuba mata dafi a lokacin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *2K Complete ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP 1K...0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*109*
Kai tsaye ya furta." Na kai Hajiya k'arama tasha zata bi mota zuwa bauchi don haka na ji tana fad'a a waya kafin mu isa."
Ba tare da na sake cewa komai ba na kad'a kaina na koma ciki gidan raina a masifar b'ace. Anya kuwa Hauwa tana da hankali ta haihu kwana biyu kacal saboda mugun abu ta gudu ta bar jaririn da ta sha dawainiya da wahala a kansa kafin ya zo duniya ta kuma ci kwakwa duk a kansa tare da tsallake siradi. Ga kuma d'aita irin ta haihuwa da rashin kwari a jiki, wannan ba tunani ba ne gaskiyar magana a wannan karon ba ta kyauta ba, shi jariri ina ruwansa kuma hakkinsa kad'ai ba zai bari ta samu nutsuwa ba a duk inda take.
Baba Tabawa ta dinga sallallami tana fad'in." Wannan wane irin sakarci ne Hajiya Amina, to shi wannan din da ta tafi ta bar shi ai hakkinsa ba zai bar ta, ina ruwansa da abinda ya faru."
Ban ce mata komai ba na shige na je na d'auko wayata layinta na dingi kira wayar a kashe na kira ya kai sau goma amma is switch off. Na zube saman kujera ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un, wace irin masifa ce wannan ne?
Na jima cikin wannan yanayin kafin na d'auki wayata dake saman cinyata kai tsaye lambar Dr Sailuba na nemo itace tsayayyiyar likitan da take duba ni a duk lokacin da na samu ciki mussaman cikin baby Nana ta taka muhimmiyar rawa kwarai da gaske. Abu na farko da zan yi shine samarwa da yaron abinci matsalar raino wannan mai sau'ki ne. Bayani na yi mata sosai amma ban sanar da ita cewa uwar yaron ce ta ajiye shi ba.
Ba mu yi sallama da ita ba sai da ta tabbatar mini da cewa da kanta za ta shigo ta kawo mini duk abinda ya dace.
Na kashe wayar tare da zubawa Baba Tabawa idanu tana ta faman safa da marwa a katafaran falon duk domin hillatar yaron da yake ta kusurkusur da alamun kuka.
Sai da bacci ya d'auke shi tukkuna ta zo ta zauna a gefana tana fad'in." Ko a tarihi ban ta'ba ganin shashashar uwa irin Hauwa ba Hajiya Amina lallai ta gwadawa wannan yaro rashin Imani."
Shiru na yi Ina nazari kafin daga bisani na furta." Tana so ta huce fushin abinda ubansa ya yi mata shine ta dire shi ta yi tafiyarta. Abin mamaki kuma ita da mijin nata jini guda ne mamansa ta cika nono ta bawa Mamanta wace irin zuciyace wannan."
Kai tsaye ta ce." Zuciyar kafurai ce."
Muka yi shiru cikin alhini kafin ta cigaba da cewa." Ita kanta na tabbatar da cewa wallahi hankalinta ba zai ta'ba kwanciya ba ciwon jiki da ciwon nono ma ya isheta.
Murmushi na yi tare da cewa." Ciwon nono mai sau'ki ne a wurinta tunda likita ce tana da hanyoyin da zata magance abinta ciwon jiki kam zata sha ai haihuwa ba wasa ba ce."
Haka muka kasance cikin zullumi da tararrabi har Dr Sailuba ta zo ta tafi muna zaune a falon cikin wani irin yanayi na mamaki da takaici.
Ba ni da niyyar sanar da kowa wannan lamarin amma dole maigidan ya sani domin duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubar da ruwa, domin duk abinda yake faruwa shine sanadi me ake yi da zuciya irin tasa ta riko da ba'kar gaba, ita dashi duka kanwar ja ce shi ba'kar zuciya da gaba ita girman kai da rashin tsinkaye.
Sai da daddare tukkuna yaron ya gama kiciniyar kukansa Baba Tabawa ta goya shi ya yi bacci sannan na samu sararin bude data.
Na duba shi ta What'sapp din bai jima da sauka ba. Sallama na yi masa tare da barin datar a bud'e na ajiyar wayar na tashi na je na leka d'akin Baba Tabawa tana zagaye a d'akin bayanta goyo da yaron. Tausayinta ya kama ni haka kawai sun sanya tsohuwa wahala lokacin da suka jiyar da junansu dadi har suka samu 'karuwa bata sani ba, yanzu kuma sun haihu sun barwa wasu da raino.
Ta juyo tana kallona a dan sanyaye na ce." Ya yi baccin ne?'
Ta gyada kanta a hankali ta furta." Ya yi da farko dana kwantar da shi shine fa ya tashi na sake mayar dashi na goya."
Na sauke ajiyar zuciya tare da fad'in." Ki yi hakuri Baba an tashe ki a tsaye."
Sai ta yi dariya tana fad'in." To menene a ciki ni na kar'bi ladan Amina duk da ban ta'ba haihuwa ba ai na iya raino an sha kawo mini yara na yaye su ki tambayi Hajiya Sahura ni ce na yaye Yasir kanin Yusura."
Da d'an murmushi na furta." Ai na ga alama duk da haka dai idan ya yi bacci sai ki kwantar da shi kema ki huta da tsayuwa."
Ta furta." Haka za a yi in sha Allahu."
Na juya na fita zuwa d'akina.
Ina d'aukar wayar na duba naga sakon shi voice note ne na buda na saurara yana gaya mini Momi ta samu sau'ki sosai ta ce tana so mu gaisa.
Ban mayar masa ta hanyar murya ba na rubuta masa a rubuce
"Hauwa ta ajiye maka jaririnka ta tafi."
Yana karantawa kuwa sai ya kira ta What'sapp din na daga.
Ya ce." Me ki ka ce?" Na ce." Hauwa ce ta tafi Bauchi ta bar jaririn a gida."
Cike da wani irin yanayi na rikita ya ce." Ta tafi Bauchi ta bar jariri bisa umarnin wa? Me yasa ba ku da hankali ne Amina?"
Da mamaki a tare da ni na ce." Ba mu da hankali kamar yaya? Ni kuma ina ruwa don na gaya maka sai hakan ya zama lefi idan na yi shiru kuma nan ma ya zama lefi."
Ya ce." Da zata ta tafi mai yasa ba ki hana ta ba, ashe ba za ki iya tsaya mini a gidana ba idan ba na nan?"
Dan murmushin takaici na yi kafin na furta." Wallahi ni kaina ban san lokacin da ta tafi ba, kuma tunda ta haihu ban ga alamun fitina a tare da ita ba, sannan da kake cewa na hana ta ni na isa? zaman idda take yi fa tunda duk cikinmu babu wanda ka gayawa ka mayar da ita don ta haihu ta ajiye maka d'anka lefi ne, tun kafin ta haihu kake da dama a hannunka ba ka yi amfani da ita ba."
A d'an raunana ya furta." Ba ki ga lefinta ba kenan Amina tare da hadin bakin ki Hauwa ta yi mini wannan wulakancin."
Na furta." Kada ka d'auki hakkina wallahi ban sani ba, bata kyauta ba ai ko babu komai ta duba yaron ta tafi dashi idan ma ba zata zauna ba."
Ya ce." Yanzu ina yaron yake?"
Kai tsaye na ce." Na aikawa da Nabila shi."
''Kin aikawa da Nabila shi?''
Ya maimaita amsar dana bashi cike da mamaki.
Na ce." Kwarai kuwa sai ta had'a gabad'aya ta ri'ke da 'yan uwansa ko ba haka ba ne tsarinka."
"Ke ba za ki iya ri'ke shi ba kafin na dawo na yanke hukunci.''
Ya fad'a cikin sanyi murya tabbacin ya ji ciwon abin."
Na ce." To ai gani na yi ba ni da nonon da zan ba shi, kuma ban iya raino ba da kula ba shiyasa na aikata mata dashi ta had'a shi ta ri'ke."
Ya furta." Kin so kema ki tozarta ni Amina, na gode bisa wannan abu da kuka hadu ku ka yi mini Allah Ya saka mini."
Bai jira jin abinda zan ce ba ya datse kiran ya ma sauka daga Whasap din gabad'aya.
Na yi kasa'ke da waya hannuna ina dariya wai Allah Ya saka masa ashe da ciwo kenan. Hauwa ta kyauta bata kyauta ba, lallai abinda ta yi ya ta'ba shi ainun ganin bakinsa ya mutu ya rasa abinda zai ce.
Kafin na kwanta sai da na sake zuwa na leka d'akin baba Tabawa yaron ya yi bacci cikin net din sa, itama ta kwanta amma ba ta yi baccin ba tukkuna na tsaya muka d'an yi maganar kad'an kafin mu yi sallama na je na yi shirin kwanciya.
Da safe ina bud'e data sakon shi ya shigo yana gaya mini jiya ya tambayi Nabila ta ce ita yaron baya hannunta. Ina muka kai masa d'ansa.
Dariya na yi kafin na rubuta masa cewa." Gidan marayu muka kai shi."
Yana dubawa kuwa ya kira bidiyo call.
Bai bari ma mun gaisa ba ya fara fadin." Kin ga ki gaya mini gaskiya don Allah ba ni son abinda zai daga mini hankali jiya ban yi baccin kirki ba Amina ban san ba ku da Imani ba sai yanzu."

Idan ki ka karanta ba ki biya ni hakkina ba ina binki bashi.

Ina kallonsa da gaske din a rikice yake yanayinsa ya nuna alamun damuwa da tashin hankali. Daki ne na mussaman shi da matar tasa don ina hangenta a can wani gado a kwance irin na marasa lafiya shi kuma yana wata kujera.
Na ce." Ba mu da imani fa ka ce?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Kwarai kuwa ba ku da shi wallahi, kin ga yanzu yadda za a yi tunda ita ta gudu ta bar shi ke ki yanke abinda ki ke so na biya ki ki kula mini da shi kafin na dawo."
Na ce." A a daka bar shi a hannun Nabila zai fi alheri, idan zan kula da shi har sai na kar'bi kudi a hannunka mai ka mayar da ni."
Ya ce." Nasan ki da alheri ai, don girman Allah idan yaron nan yana wurinki ki sanar da ni hankalina zai kwanta jiya na gaya miki mun yi magana da Nabila ta ce mini ba ki kai mata shi ba."
Ganin yadda yake had'a ni da Allah ya sanya ni cewa." Yana hannunmu ni da Baba Tabawa cikin kulawa da koshin lafiya kuma tun jiya na kira Dr Sailuba ta had'a mishi duk abinda aka buk'ata."
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Na gode sosai my love life Allah Ya yi miki albarka.
A dan sanyaye na ce." Babu komai." Ina hangen Momin ta tashi zaune daga can wurin dake tana kallonshi shi ya juyo mata baya ya dage sai kalamai yake yi mini na dadin baki.
Na ce." Ka juya ka ga ta tashi fa."
Ya d'an juya a hankali yana fad'in." Ok jiya na ce miki tana so ku gaisa ko, amma bari mu bari zuwa yamma zan sake ta'bo ki sai ku gaisa."
Na ce." To shikkenan a ma sha Allah na ga jikin ya yi kyau Allah Ya kara sau'ki."
Ya amsa da Amin Amin mun gode giwa Allah Ya yi miki albarka." Na ce." Amin a takaice. Ni na fara datse wayar saboda ganin kamar tana buk'atar magana da shi.

To yaro dai na d'auka tunda ta tafi ta bar shi zan yi iyakar bakin kokarina. Bayan ubansa babu wanda nake jin zan gayawa ko Hajja kuwa amma tabbas nasan Hauwa rikici da gangami ta shiryawa kanta, dalili kuwa shine yadda abin nan da ta yi ya kidima shi ba zai kyaleta ba, to ma ji ma gani dai Allah Ya kyauta.
Sai bayan sallar azuhur tukkuna na samu Hauwa a waya. Ta daga hankalinta a kwance domin ban ji alamun nadama da danasani a muryarta ba.
Jikina ya mutu sosai da kyar na furta." Kina ina Hauwa?"
Kai tsaye ta ce." Ina nan Bauchi."
Na danne takaicina tare da cewa." Ashe kin shirya hakan tuntuni to hakan da ki ka yi a ganinki daidai ne ko?"
Da d'an murmushi ta ce." Shine daidai Amina, domin wa'adin zamana ya kare a gidan tunda na haihu yaro kuma ai gidan ubansa ne tunda ba dashi na zo ba, mai zai sanya na d'auko shi na kawo shi inda babu tarbiya ba Amina sunan Amadu fa ya fi sunan ubana an ce mini ubana ba komai ba ne a lokacin da na nuna shi din wani abu ne, tuntuni na gaya miki dama ba zan jure wannan rashin mutuncin ba."
Cike da takaici na furta." Amadu fa aka ce shine Mahmudu Muhammadu. Ki tuna mai wannan sunan shine wanda aka yi duniya dominsa Annabi Muhammadu S.a.w a ganina wannan abin alfahari ne a wurinki."
Ta yi murmushi tana cewa." A a ba da wannan niyyar ya sanya sunan Amadu ba. Abokinsa mai rasuwa fa shi yayi wa takwara na ce masa ina son sunan mahaifina tunda na farko ya sanya sunan mahaifinsa daga fad'in haka ya fara gaya mini magana tabbacin dama haushina yake ji to menene saura a tsakaninmu na fita daga iddarsa da dama."
Na gyada kaina ina danne abinda nake ji a raina na ce." To kina ganin Allah ba zai kama ki da hakkin yaron ba shine ina ruwansa."
Ta yi dariya tare da furta." Allah Ya yafe mini shi kuma idan rayayyene Allah Ya raya shi."
Na yi shiru domin kamar kalaman bakina sun kare da kyar na ce." Yanzu mai ki ka gayawa inna Uwani."
Da sauri ta furta." Tun daga farko a har karshe wallahi ban boye mata komai ba, Amina ai na yi hakuri na yi kuma biyayya, ke kan ki ban shure shawararki ba, na yi ta ha'kuri tsayin wattanin dana d'auka a matsayin sakakkiya mutumin nan baya kula ni kuma bai furta ya mayar da ni ba, duk wata dama ya samu bai yi magana ba yanzu kuma ai komai ya zo karshe na gaya mata komai haka zalika ma babu wanda bai sani na a family din Babanmu."
"Kenan Hajja ta ji komai?"
Na tambayata cikin zullumi.
Ta furta." Kwarai kuwa d'azu nan suka gama waya da Inna." Na yi shiru Ina nazari kafin daga bisani na furta." Hauwa idan zu'kata sun huce a daidaita don Allah kuma yaron nan da kaina zan kawo miki shi gobe in sha Allahu rabbi, ki yi hakuri don girman Allah ki kar'bi d'anki kada ki wulakantashi domin bakisan baiwar da take tare dashi ba."
"Na rantse da girman Allah a yanzu dai Amina ko kin zo da yaron nan sai dai ki koma dashi don wallahi tallahi ba zan karbe shi ba sai ubansa ya zo da k'afafunsa ya nuna nadama akan abinda ya yi mini, idan har ke za ki iya jure wulakancinsa ni kam ba zan iya ba. Ki ri'ke shi kawai na bar miki."
Bakina ne ya mutu murus na rasa abin cewa tunda har ta riga ta rantse nasan abu ne mai mutukar wahala ko na kai mata yaron ta kar'ba......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *2K ON TALGRAM WHAT'SAPP GRUOP 1k VIA 0542382124... BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*110*
To wannan lamarin na su sai dai na ce Allah ya sawwa'ke har ga Allah ban so rigimar tasu ta yi tsayin da har magabatansu su shiga ba. Saboda daga shi har ita babu yaro duka sun mallaki hankalin kansu su din masu yi wasu gyara ne, duk da mas'ala ta aure akan sameta a kowane gida amma abinda yake cikin gidan nan namu sai dai mu godewa Allah daga wannan sai wannan ashe kalmar hakurin nan da manya suke nanata mana akoyaushe tana da tasiri gabad'aya sha'ani na aure a yanzu ya zama abinda ya zama domin kuwa k'alubalan da ke cikinsa ba kowace macace zata jura ba. Zawarawa sun yaiwata wad'anda mazajensu suka rasu ga 'yan mata nan birjik a gari suna yawo idan ma kana murna ka aurar da d'anka to ka bi shi da addu'a kawai domin kuwa zamani ya zo da mata da yawa suke ganin gwara su rayu babu aura akan yin sa saboda riskar rikici da tashin hankali idan ba a yi dace ba. Abu ne a bayyane ba kowane a yanzu zamu bud'e baki mu gaya masa cewa ba ma cikin nutsuwa ya aminta ba. Dalili ana ganin Ubangiji ai ya yi mana gamnakatar da auran attajiri wanda ba mu rasa komai ba na jin dad'in duniya tabbas ba mu rasa komai na jin dadi ba amma mun rasa kwanciyar hankali domin kuwa idan ana murna an kashe wannan wutar sai ya sake kunno wata da kansa.
Kwanaki biyu ba ni ganinsa a online hankali ya tashi domin tunda suka tafi tsayin sati uku kullum sai mun yi magana. Na shiga damuwa sosai na kuma kasance cikin duba wayata a akai-akai. Misalin goma da rabi na yi shirin kwanciya don ban jima da fitowa daga d'akin Baba Tabawa ba na d'auki wayata na duba sakon voice note din shi ya shigo na bud'e ina saurara yana gaya mini suna kan hanyar dawowa gobe domin sun gama shiri kuma alhamdulillahi ta ji sau'ki."
Jin haka ya sanya hankalina kwanciya domin tsakani da Allah kwana biyun nan na yi sune cikin fargaba da tunanin halin da suke ciki ko kuma na ce yake ciki tunda ta hanyar wayar ne kawai muke magana.
Washe gari da wuri kuwa na kira yarinyar nan da ta yi mini 'kunshi ta zo ta zana mini baki da jaa kafafu da hannayena. Ya yi kyau ainun. Na ce da Baba Tabawa ta shirya masa towon somovita ayi miyar kuka domin duk cikin kayan kad'i ya fi sonta.
Tare muka shiga kicin na taimaka mata tana goye da yaron a bayanta yana bacci muna d'an ta'ba hirar rashin lafiyar Momin har muka kammala tsaf towo semo da farfensun kayan ciki tunda shi ma yana daya daga cikin abinda yake so domin shi kam ya fi kauri ga abincin gida. Lemo kam ba kowanne yake sha ba ya ma fi jin dadin zob'on da Baba Tabawa take yi masa mai cike da kamshin citta da kaninfari.
Na riga ta fitowa daga kicin din wanka na yi a gurguje na d'aura alwala tunda daf ake da kiran sallar magriba na shirya jikina a cikin atamfa java kalar sararin samaniya mai d'auke da adon zaiba da stones a tare fittedgwon ce ta d'an kama ni amma ba sosai ba. Yanzu ina iya sanya matsatstsun kaya dalilin maganin tumbin da na yi amfani da shi wanda ya narkar mini da mugun tumbin da ya yi mini zuguda a ciki. 08089965176 wurin GARKUWAR MATA na sayi maganin yana da kyau sosai kuma harbel ne ba shi da side effect.
Ban yi cikakkiyar kwalliya ba domin can dama ban fiye fenta fuskata ba na dai shafa hoda tare da sanya kwalli na sanya jan janbaki a le'bena. Na gyara gashin kaina sosai kafin na daura d'ankwalin daidai da zamani.
Ni ce har da had'a kankana da zumar mata ta goron tula itama dai duka order ce daga wurin GARKUWAR MATA na hada da madara na cika kofi na shanye wannan

Please Login or Register in order to submit comment