Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

misalai."
Ya furta." Ba ni da nutsuwa fa Amina tun sanda ya ba ni kyautar yarinyar na rasa sukuni gabad'aya domin ni kaina ba ni son auran irin k'ananu haka koda da k'addarar sake wani auran a tare da ni wadda ta fita shekaru zan aura amma wannan tayi yarinyata da yawa."
Na ce." Hakan kuma bai hana ka nemi shawara wajan gwajin jini ba ko duk da ta yi yarinyata ai ka shirya takarta ko ba haka ba ne."
Shiru ya yi bai ba ni amsa ba.
Wai ni zai yi wa kalaman yaudara na janye jikina ya sake rukunkume ni yana tatta'ba wasu sassa na jikina tare da sauke ajiyar zuciya.
Gabad'aya nema yake yi ya daga mini hankali a halin kuma da nake ciki ba ni buk'atarsa ko kad'an jikin dai yana so walwala da annashuwar da zata bari a tari lamarin ne babu.
Babu yadda bai yi da ni ba a daran a kan dole sai ya kwanta da ni na ce a a gajiye nake ba zan iya ba.
Dole ya ha'kura da asuba ya sake nemana da rarrashi da kwantar da kai ya fara ko'karin gaya mini wasu maganganu wanda suka danganci Hauwa na katse shi da sauri na nuna ba ni so ban san yaushe ya zama munafikin namiji ba ina ruwana Hauwa tana gamsar da shi bata gamsar da shi ba abinda ya dame ni ba ne.
Na ci da kulafuci kamar dambun kuturu ya ma'kale ni na kasa motsi babu yadda na iya haka nan na kyaleshi ya yi abinda yake so kamar zai shid'e saboda gigita lissafinsa gabad'aya ya kwance.
Da kaina na shiga kicin tunda ya sanya an kawo mini komai na bukata. Na soya doya da kwai da tea sannan na dafawa kaina indomee.
Nan d'akina muka yi breakfast din babu yabo babu fallasa amma dai na kasa sakin jikina duk zantukan da yake akan auran nan da zai yi kawai ina jinsa ne da kunne dalili nema yake yi ya rainawa mutane hankali tunda yadda yake nunawa ko jininsa dana yarinyar bai daidaita ba zai iya yin jayayya da malamin ba yadda tun farko ya amince masa to abu ne mai wahala daga baya ya je ya ce masa ga matsala wadda daga baya turawa suka bijiro da ita tunda ai ko a zamanin annabawa ba a san da wani gwajin jini kafin aure ba haka kuma duka iyaye da kakanni suka ta so.
Da haka dai ya yi wanka ya kintsa ya fita yana gaya mini ya yi baki daga kamaru idan ya gama dashi da wuri zanje bunkure a takaice na yi masa addu'ar dawowa lafiya
Sai wajan daya da rabi Sahura ta zo lokacin ne ta taso daga aiki. Sai bayan da muka ci abinci muka yi sallah tukkuna muka fara aikin gyaran gidan wanda kusan zan iya cewa itace karfin aikin ta shasshare mini ko'ina tas aka yi mopping gidan ya dawo hayyacinsa.
Sannan fa muka zauna ina zolayarta ta yi ki'ba tana ta'be baki kuma da gasken ta yi kiba wallahi alamu sun nuna bata da damuwa tana cin gashin kanta. Idan farko akwai damuwar yanzu makomar auran Idiris ta bayyana ya sanya mata nutsuwa da kwanciyar hankali domin dai alkali ya tilasta shi sakin yarinyar kamar yadda iyayenta suka buk'ata dalili shedu sun shaida babu abinci ingantacce a gidansa sannan kuma alamu na nuna cewa shi din yafi karfinta ta fannin auratayya. Ya kuma yanke masa kudin da zai dinga aikawa yarinyar na goyon ciki har sai ta haihu ta shayar masa da abinda ta haifa kafin ta yaye ya kar'bi d'ansa a bisa adalci.
A wannan matsayar aka tsaya da shi. Tana gaya mini da gumu ta yi gumu ya rasa yadda zai yi ya gaya mata halin da ake ciki.
Na ce." To Sahura tunda dai ya yi nadama sai ki yi hakuri don Allah kada dukan ya yi masa yawa ki kaddara cewa rabon haihuwa ne ya sanya shi rakito auran yarinyar nan."
Ta ce." Ai ban hana shi kwana a gidana ba Amina kwanciya da ni ne na ce ba zai yi ba. Kuma gidan da ki ka ba ni ya balle ni kwado ya sanya matarsa sun kwashe kaya sati biyu da suka wuce na sanya a zuba mini 'yan haya a ciki. Abincin dai ina ba shi idan na yi ga waje nan ya kwanta ya tashi amma babu mu'amula ta aure.
Na ce." To kin sake bashi lasisin yawon dare kenan?"
Ta'be bakinta ta yi ba tace komai ba. A daidai lokacin kira ya shigo wayata ina dubawa na ga maigidan ne na ajiye ta katse ya sake kira na d'auka tare da daidaita maganata. Na ji yana fad'in." Na fasa zuwa bunkuren nan Amina gani nan dawowa gida."
A tak'aice na ce." To.'' na riga shi kashe wayar na ajiye a gefana ina tsaki
Ta bata rai tana fad'in." Menene haka don Allah."
Na ce." Da aka yi me?"
Ta gyad'a kanta tana cewa." Wallahi tallahi ki ji tsoron Allah akan mutumin nan Amina."
Sosai na zuba mata Ido da mamakin maganarta haka kawai ba ta san irin zaman da nake yi dashi ba tana cewa na ji tsoron Allah akan sa. Ko da yake dama can ita 'yar dakinsa ce bata ta'ba ganin lefinsa. To mai baka kuma ya ninke munanan halaye ya bayyana kyakykyawan ya za a yi ta fahimci aibunsa tunda ba tare take rayuwa da shi ba.
Ta cigaba da cewa." Menene abin tsaki don ya gaya miki cewa zai dawo gidansa ne fa."
Na ce." Hajiya kamata ya yi ki tambaye ni dalilin dawowata nan ba kawai kai tsaye ki fara tuhumata ba ke matsalata dake kenan ba kya taba ganin lefinsa.
A d'an sanyaye ta ce." Menene to?"
Duk abinda yake faruwa na gaya mata tun daga kan matsaltsalun da yake tsakani na da Hauwa da auran da aka bashi a bunkure.
Ta yi sakato da baki tana kallona gabad'aya bakinta ya mutu da kyar ta ce ni haukan da Hauwa take yi bai dame ni ba Amina sai maganar auran nan da ki ka ce zai yi ai na gane yarinyar da ki ke gaya mini ko ba itace ta kawo mini abinci a lokacin da naje ba."
Na ce." E ita ce.''
Ta zura mini ido tana kallo kafin ta ce." Ai ko nono ba ta dashi wannan yarinyar ba ta isa aure ba don bata da 'barage ba na tsammanin ba ta fara jinin haila."
Na ce." To ya kar'bi dai auranta sai ya cigaba da raino amma dai da kamar wuya tunda d'azu yake gaya mini wai za su yi gwajin gyonotype kin ga kuwa da sha'awar sabon waje a cikin ransa mussaman budurcin k'aramar yarinya irin wannan ba na tunanin zai zura mata tsayin wasu shekaru."
Ta ce." Don Allah ki daina fad'in haka Amina kunya ma nake ji wallahi yanzu shi sai ya iya tu'bewa a gaban wannan tatsitsiyar?"
Na ce." To me ye a ciki Amina wallahi ki daina mamaki da sha'anin maza abu ne mai sau'ki a wajansa."
Ta yi zugum tana dubana kafin ta ce." Lallai mutumin nan ya ba ni haushi wallahi gaskiya abin bai yi mini ba ya kuma shirya cinye muku fuska yarinyar 'yar cikinku ta kalleku a banzance tunda ai duk ranar da ya kwanta da ita to gabad'aya ba ku da bambanci wallahi.
Na yi shiru Ina nazarin maganarta tabbas hakane ranar da ya kwanta da Hajara to itama daga lokacin za ta ji kanta a matsayin matar gida daidai da kowa. Ba ni fargaba akan tarbiyar yarinyar amma yau da gobe idan zama ya yi zama dole wasu daga cikin d'abiunta su canza dalili itama tana ji kanta cewa matar gida ce."
Sahura bakinta ya mutu duk kaud'in nan nata a kansa bakinta murus ya yi tana jin haushin haka ta yi la'asar ta yi mini sallama ta tafi. Ba ta jima da barin gidan ba ya dawo. Ya yi wanka a dakinsa na sama ya canza ya kaya na shan iska ya sauko kasan ya same ni zaune a kujera Ina kallo ya zauna kusa da ni yayin da kamshin turaransa ya game wajan gabad'aya.

Na dube shi kad'an kafin na janye idona ban ce komai ba.
Sai ya riko hannuna yana cewa." Ta karfi da yaji dai kin zama bebiya giwa wai me ya yi zafi ne uhum?''
Ban ce komai ba na zare hannuna. Ya kamo yatsan da ya sanya mini zoben nan ya sumbuta ya ciro shi daga yatsansa ya sake mayar mini yana fad'in." Ban yi zuciya ba amma ya kamata ki sassauta mini ki yi mini adalci akan duk abubuwan da suke faruwa ke kan ki kin san abinda ki ke yi ba daidai ba ne ko?"
Na ce." Adalci wane iri kake so na yi maka na hana ka kar'bar auran da aka baka ne? A lokacin daka gaya mini addu'a na yi maka kuma dole sai ka yi hakuri a wannan lokacin tunda ni kaina ba jin dad'in jikina nake yi ba."
Ya d'ora hannunsa saman cikina yana fad'in." Na sani amma me yasa ki ka cire duk wani subsidy a kaina kin daina sona ne."
Ban iya kallonsa ba saboda takaici. Ya juyo da fuskata yana cewa." Zan fasa auran nan fa wallahi ba zan iya ba."
Na yi shiru dai ban ce komai ba daidai lokacin ne Hauwa ta kira shi yana d'agawa ta fara kuka tana fad'in." Minal ce ta suma!"
Ya ki'dime sosai hannunsa har yana karkarwa yana tambayarta ya ake ciki yanzu. Yadda take bashi amsa ya sanya na fahimci cewa k'arya take yi wallahi.
Kawai dai za ta fake da ciwon yarinyar ne ta daga masa hankali.
Ya kashe wayar da tsananin tashin hankali yana fad'in." Ki yi wa Allah da annabi ki tashi mu tafi yarinyar nan Minal tana sonki Amina kada hakkinta ya kama ki tunda ta dalilinki komai yana iya faruwa kada mu yi rashinta.
A nutse na ce." Ka je ka kawo mini su nan gabad'aya zan ri'ke su Ina nan akan bakana ba ni sake zama da Hauwa. Idan kuma za ka canza mata gida ni ta bar mini wanda take ciki sai na koma."
Ya ce." Ba ki ji an ce suma take yi ba. Na gaya miki cewa jikinta ya'ki dad'i wallahi tunda ki ka bar gidan nan."
Na ce." Ni da hankalina sarai babu abinda Hauwa za ta k'irkira ya firgita ni. Minal kuwa Ina tsammanin ma uwarta ba ta kaini sonta ba."

wannan littafin dai na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ya yi shiru yana kallona na wani lokaci kafin ya haura samansa. Na dubi agogo biyar da rabi jim kad'an ya sauko cikin manyan kaya babbar riga da 'yar ciki.
Cikin zuciyata na ce." Aiki ya same ka in dai Hauwa ce sharrinta yawa gare shi neman kudi ma wataran sai ka yi da gaske za ka yi."
Ya tsaya gabana yana fad'in." Rarrashi da ban ha'kuri babu irin kalar da ban yi miki ba. Ba a yi maccan da zan dinga kwantar mata da kai tana gara ni kamar gare-gare ba. Ki sani Amina kina da magabata kuma hukuncin saki a hannuna yake sai na ga dama zan yi. Wallahi tallahi zan d'auki mummunan mataki akan abinda ki ke yi mini.
Na ce." Sanar da magabatana halin da muke ciki shi zai kara dagula maka lamari domin wallahi ba zaka taba samun kaina ba. Shekara nawa ina ha'kuri dakai tare da bin umarinnka ina so ko ba ba na so. So kake yi na zauna da Hauwa wataran ta d'auki makami ta farauci rayuwata. Ko za ka gaya mini cewa har yanzu ba ka fahimci irin tsananin kiyayyar da take nuna mini ba. Ka kawo mini yarana na ri'ke a hannuna domin ba zan iya barin su a tare da ita ba za ta iya yi musu lahani ta kowace siga.
Idan ba za ka iya rabuwa da ni ba to bar ni anan din ni wata daula ba damuna ta yi ba. Idan za ka shekara ba ka zo in da nake ba babu damuwa na sahale maka."
Ya cire gilashin idonsa ya sanya hankici ya goge ya mayar dashi idon nasa. A d'an rikice ya sake cirewa ya goge kafin ya sake mayar dashi. Na d'auke kaina a raina ina fad'in zautuwa yanzu ka fara yin ta ka wani binjimo babbar riga. Gaskiya na karyawa Hauwa d'ankwali a wannan ga'bar da alama ta d'auki hanyar rama kashin da ya bata. Na yarda Minal bata da lafiya amma haka kawai zuciyata ba ta amince mini da cewa da gaske ne ta suma ba
Na juya ina kallonsa a lokacin da ya kama hanyar fita kenan abujan ya nufa saboda an ce masa yarinya ta suma. Aikuwa dai ga dukkanin alamu mutumin nan so yake yi ya yi mutuwar tsaye.
Kwana uku da tafiyarsa bai kira ni a waya ba ni ma ban kira shi ba ana hudun ne ya zo tare da yarinyar da akwatin kayanta. Ta ma'kalkale ni tana dariya da shafa fuskata duk garin jikin nan nata sai da ya rairaye ta yi d'an wuya. Ko da na gaishe shi sama-sama ya amsa ya bar wajen. Na ri'ke hannunta muka haura saman a tare yana wanka da ya fito ya gan ni a zaune ya sake d'aure fuska ya d'auki basiline ya zauna can nesa da ni yana shafawa a jikinsa. Yarinyar ta fara zagaye d'akin tana neman abin wasa.
Ni abinda yake yi ma dariya yake ba ni abinda ba zai iya ba. Duk tsananin gabar sa ban san me ya sanya yanzu ta daina tasiri a kan kansa ba domin daga ya fara ma yake bari kwana daya biyu zuwa uku ya fara neman hanyar da za a shirya.
Na ce." Ina 'yan biyu na ga Minal ita kadai ai ba haka muka yi da kai ba."
Ya ce." Tunda kin haife ni Amina ai ya zame mini dole na bi umarininki kada na lalace ko?"
Na danne dariyar da nake ji tana yun'kuro mini na ce." Ban haife ka ba amma abinda yake a hakkina nake tambayarka ni 'yan biyu na ce ka kawo mini."
Ya furta." Wannan din da na kawo miki sai ki yi cilli da ita tunda ai ba gidan ubanta ba ne."
Na ce." Mu yi magana wadda take daidai kuma ta fahimta mu kuma cire son zuciya. Ban ce ba zan ri'ke yarinyar nan ba tunda har ka kawo mini ita amma ba ni son tashin hankali daga kowane 'bangare. Idan har da sanin uwarta ka daukota ta amince da hakan babu damuwa a wajena. Amma ya zama dole a kawo mini yarana."
Ya ce." Wannan ne kuma ba ki isa ba. Ba za ki dinga gindaya mini sharadai ba. Hauwa ta da ba ta yanzu ba ce domin duk yadda ki ke tunanin tana 'kin ki na tabbatar da cewa ba zata zalinci yara ba, kuma sanin da ki ka yi mata ta canza sosai ta kuma kar'bi dukkanin kuskuranta."
Na ce." Babu ruwana wannan matsalarka ce kai da ita. Ni dai Hauwa ko za ta had'iyi al'kur'ani don tsoron Allah da gaskiya ba zan yarda da ita ba domin ita din mutuniyar banza ce mara tsoron Allah."
Ya ce." Cin fuska ne ki dinga kiranta da irin wannan kalaman Amina kwanakin baya kin mare ta a fuska duka ta yi hakuri saboda tana jin maganata."
Na ce." Me yasa baka rama mata ba a lokacin ba, ai da ka sani kawai ka d'aukar mata fansa kuma yanzu ma ai bata 'baci ba ga ni zaune kusa dakai ka rama mata kawai......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700.....0542382124. BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*148*
Share ni ya yi ya tafi ya je ya d'auko rigarsa jallabiya mai yankakken hannu ya sanya a jikinsa ya fesa turare sosai sannan ya sauka kasa ya bar ni da yarinyar a d'akin. Na tashi tare da kama hannunta muka sauka baya falon k'asa da alama fita ya yi.
Kai tsaye kicin na nufa na d'ora sanwar dare gefe guda kuma kasan marata na d'an yi mini ciwo kadan da cijewar kafa gobe alhamis asibiti zan yi sammakon zuwa domin duba lafiyata da abinda yake cikina a auna abinda yake cikin domin tabbatar da lafiya yake kwance.
Duk inda na ajiye kafata nan yarinyar take ajiye tata tana yi mini hirar 'yan uwan nata biyu can kasan zuciyata kewarsu ta ishe ni haka kawai yanzu nake tsananin jininsu a cikin raina ba kuma na tsammanin zan iya bar wa Hauwa su wallahi sai dai duk rigimar da za mu yi muyi ta a shirye nake gabad'aya na gama dawowa daga rakiyar Hauwa.
Bayan sallah Isha'i ya shigo muna d'aki ni da Minal na bata wayata tana game ya buk'aci abinci ya kama hanya ya fita da jin haushi domin ya'ki sakin fuskarsa tun da ya dawo.
Na shirya masa abinda na dafa na hau saman da tire din a hannuna cikin jan kafa daya ta ri'ke mini cikin ya yi mini nauyi ainun.
Na same shi yana waya na ajiye tiran kusa da shi na juya zan fita ya dakatar da ni.
Na juyo ina kallonsa fuskata a had'e sai kuma ya ce" Je ki kawai."
Na kada kaina ba tare da nace komai ba na sauka yarinyar tana ta game cikin nishadi cikin zuciyata na ce ikon Allah kenan ban haifi yarinyar nan ba Allah Ya jarabbeta da kaunata haka zalika ni ma ina sonta sosai domin ba ta d'auko kamanin uwarta ba fuskar ta ubanta ce garin jikin ni kuma na washeta tunda uwar da uban duka sirira ne.
Ya kwana can shi kadai na kwana da Minal da safe na yi mata wanka na shirya ni ma na kintsa. Ruwan shayi kawai na iya dafawa na soya 'kawai zalla na had'a mata tea din ta karya.
Ina yin nawa karin kummalon ne ya shigo ya shirya shi ma da alama fita zai yi da wuri a haka har yanzu babu nutsuwa da cikakkiyar walwala a tare dashi tana ganinsa ta fara fad'in." Baba ka ga." Tana nuna masa wayata dake ajiye game din dana kamo mata tana yi ban kashe ba. Tana ta maimaita maganar "Baba ka gani."
Ya karaso ciki sosai ya kar'bi wayar yana dubawa ya d'an saki fuska yana cewa." Na gani Minal mu gaisa ko?''
Ta daga kanta sai ya mika hannu ya kamo nata yana fad'in." Haka ake cewa ina kwana."
Ta sake daga kanta tana fad'in." Baba ina kwana."
Ya amsa yana dariya wadda ban ga ya yi ta ba tunda ya shigo jiya.
Ya d'an tsira mini ido na wani lokaci kafin ya ce." Ba za ki gaishe ni ba?"
Na ajiye kofin shayin da yake hannuna na ce." Ina kwana?"
Ya amsa a tak'aice tare da tankwashe kafa a gabana. Sai na yi kasa da kaina ban sake ce masa komai.
Ya furta." Had'a mini tea din ma nasha.
Ya janyo flat din dake gabana da soyayyan kwai fefe uku manya na d'auki kofi na tsiyaya masa ruwan shayin nasa madara kad'an da milo domin wasu lukutan ma ya fi shan tsura shima amma dai shi yana shan madarar amma kadan ba kamar Baban Saude da gabad'aya madarar ce ma ba ya sha.
Yana kurbar ruwan shayin yana kallona kamar wadda ya samu tibi can na ji yana fad'in." Naga duk kin tasa kin kara girma ina fatan lafiya." Ya fad'a yana duba yatsun hannuna da suma suka d'an yi kumburi duk irin na masu ciki.
Na ce." Lafiya lau in sha Allahu amma dai yanzu shirin da na yi asibiti zan je ina so su yi mini awo sannan kafata na ciwo amma dai hakan ba matsala ba ne in sha Allahu idan ciki ya yi nauyi ya shiga watanni shida zuwa bakwai akan ci karo da irin wad'annan matsaltsalun."
Ya gyad'a kansa yana cigaba da yi mini kallon kurulla kafin ya ajiye kofin hannunsa ya furta." Za mu je na kai ki asibitin da kaina idan ya so zan yi magana da magaji direban Hajja idan kin kammala sai ya zo ya d'auke ki ku je da Minal ku gaisa." A tak'aice na ce to shikkenan.
A mota yake gaya mini daga asibitin bunkure zai nufa domin dai gobe ne za a daura aure bayan an yi sallar Juma'a akwai zai d'auko yarinyar still su dawo asibitin a tare domin akwai likitan da ya yi magana da shi a sirrin ce zai yi mata (genotype) tunda shi dama tuntuni ya san matsayin jininsa.
Na ce." Wane irin a sirrin ce sai kace munafurci me yasa baka so a san za ka yi aure ka bugo kati kana d'ora shi a status dinka menene abin boyewa.
Ya furta." Ni yarinyar ce ba ni so a gani."
Na ce." Kasan abin kunya ne kenan ko?"
Ya yi shiru bai ce komai ba can kuma ya furta." Babu wata kunya fa akan yin koyi da annabin rahama ni dai a yadda nake garau Amina ba na shakkar zamantakewata da mu'amula ta aure da yarinya irin Hajara saboda nasan kaina zan kuma yi mata iyakacin bakin kokarina. Kawai dai har yanzu abin ne bai kwanta mini a rai ba. Maganar buga kati ai ba wani abu ba ne na bugawa bazawara ma balle budurwa."
Na yi shiru ina auna maganarsa. Ni dai lokacin daurin aure na babu wani kati da ya buga tunda abin duka ya zo mana a bazata sai da aka d'aura tukkuna gidajen jaridu suka sani. Yana nufin Hajiya Maryam ne.
Sai na share ban tanka masa ba duk kuwa da cewa na ji zafin maganar da yake akan yarinya ya nuna budurwa ta fi bazawara kenan ita ya kamata ace an bugawa kati.
Duk tsayin rayuwar da muke yi ban ta'ba ganinsa yana tu'ka mota ba sai yau duk da yake ya ce tafiyar sirri ce har da sanya takunkumi da rufe hancinsa da bakinsa da (fecemark)
Haka muka isa asibitin Malam Aminu Kano yana ta yi mini zantukan marasa dadin saurare tunda duka akan auran da zai daura gobe ne ni Ina nake da wata shawara da zan bashi a ce sai da asiki ya zo gaban goshi tukkuna zai yi gwajin jinin ya so wata matsala ta faru idan ba su samu haduwar jini ba fadi yake yi akwai matsala domin dai shi ba zai iya gayawa malam 'Daha ya fasa ba saboda wannan dalili zai bari a d'aura auran amma fa zai bar yarinyar a gidansu kafin ya yankewa kansa hukunci.
Jin haka ya sanya jikina yin sanyi tabbas wannan son rai ne tsagowaronsa babu yadda za a yi na yarda ya lalatawa yarinya kuruciya wane irin wulakanci ne wannan gwara duk yadda za a yi a yau din idan results bai daidaita ba a zauna zama na mussaman da muhukunta domin su fayyacewa Malam D'aha illar hakan.
Yana had'a ni da likitan da zai duba ni ya yi mini sallama a ka yi sa'a cikin asibitin in banda likitan babu wanda ya fahimci shine tunda motar da muke ciki babu tambarinsa kamar sauran motocinsa na zurga-zurga wanda suke tabbatar da zuwansa waje idan an gan su a ajiye.
Scanning ya ba ni naje na yi da result ya fito ya gama dubawa ya dinga washe baki yana fad'in." Hajiya wannan albishirin ni ya kamata na yi wa Yallabai please a yi mini wannan." Na yi murmushi ina fad'in." To shikkenan duk da bai gaya
mini abinda sakamako ya nuna ba a jikina na ji cewa tagwaye zan sake haifa domin yanayin wannan cikin yanayin cikinsu Hassana sai dai wannan din da d'an bambanci kad'an.
Na ji yana fad'in." Yara maza ne biyu yadda sakamako ya nuna dukkaninsu cikin koshin lafiya sun kuma juya yadda ake so nan da sati hud'u sai ki sake zuwa a yi miki awo domin mu sake tabbatar da yanayin kwanciyarsu.
Cikin zuciyata na kira sunan Allah tare da yin godiya a gare shi.
Na ce." In sha Allahu Dr na gade sosai.
Muka fito dare da Minal da takardar result din a hannuna sai sannan na sanyata a jakata can na hangi Magaji zaune a gindin wata bishiya ya taso da sauri ya karaso tare da risinawa yana gaishe ni na amsa da kulawa ya kama hannun Minal muka nufi inda ya ajiye motar a tare.
Hajja ta ji dadin ganinmu su biyu kacal a falo ita da Kamalu suna hira

Please Login or Register in order to submit comment