Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ake ciki."
Na ce." Alhamdulillahi babu matsala ina ganin zan ci nasara akan abinda nake so in sha Allahu dama dalilin da ya sanya na kira ki wata shawara nake so mu yi shin ya ki ka ga ni?"
Duka na kwashe abinda yake faruwa na gaya mata. Ta ce." To ai wannan ba matsala ba ce Amina alheri fa ki ke niyyar k'ullawa ban ga dalilin da zai sanya mahaifiyarsa ta nuna rashin amincewarta akan hakan ba ke din Yar uwasa ce kuma ba za ki had'a shi aure da yarinyar da ba ki tabbatar da tarbiyarta ba. Bayan dangantaka ta jini ke uwar dakinsa ce a karkashinki yake idan tana da kunya ai ba zata kalubance ki ba."
Na ce." Hakane anti Yagana amma a cire maganar uwar d'akin nan na dai zauna a matsayina na 'yar uwarsa dalili anan shine ba ni so shi da mahaifiyarsa suga don yana karkashina zan juya masa rayuwa a yanzu ma idan ya zo zan fara tambayarsa shin yana da budurwa tsayayyiya idan ya ce bashi da ita sai na gaya masa shirina. Ina da tabbacin ba zai bijire mini ba."
Ta ce." Misali na yi miki ai idan ta yi tsalle ta nuna d'anta sai a nuna mata ke kuma uwar dakinsa ce a kasuwa sanadinki har yake saya mata atama super ta daura ta yafa mayafi mai tsada ."
Dariya ta kama ni ina fad'in." Anti Yagana kenan, to kin ji dama dalilin da ya sanya nace bari na gaya miki kafin na yanke hukunci Babanmu bashi da matsala hakan zai yi masa dad'i."
Ta ce." Ni ma na baki goyon baya amma kafin nan ki fara tambayarsa genotype dinsa da blood group idan ya sani shikkenan idan kuma bai san matsayin jininsa ba sai ya yi maza yaje a yi masa

Na ce." To shikkenan haka za a yi in sha Allahu anti Yagana a gaishe mini da masu jegon."
Ta ce." Gasu nan suna bacci gabad'aya tunda aka yi wankan safe suka kwanta." Na yi dariya ina fad'in." Fadila manya a shafa mini kan Shahida." Sunan anti Yagana aka sanyawa yarinyar sai uwar tace tana so a dinga kiranta da Shahida a lokacin da ta fad'i hakan na ce wata shekarar sai ki haifo Shahid. Kunya kuwa ta kamata na ce to idan ba rashin kunya ba duk muna zaune ita zata za'bawa 'yarta suna ai ta yi kara ta bari a samu sunan da za a dinga kiran yarinyar tunda ai dole a sakaye dalilin sunan uwarta ne.
Goma da sha biyu ya kira ni a waya ya shigo gate amma maigadi ya hana shi shigowa. Na sanya hijabina na fita harbar gidan suna daga can bakin gate har da Ayuba direba.
Ganin fitowata ya sanya ya kafe babur dinsa Yana kallon Ayuba yake cewa." Idan shi zai ce bai gane ni ba ai kai za ka sheda fuskata ko ba kai ba ne direban da ka dinga zurga-zurgar kai su asibiti a lokacin da Babanmu ya kwana rashin lafiya."
Ayuba ya dinga fad'in." Tabbas ni ne yanzu na sheda fuskarka ka yi hakuri wallahi d'ayan muka fi ganewa." Yana nufin Hamusu. Shi kuma Usaini haushi ya ji yadda suka tsayar dashi a bakin gate suna tuhumarsa domin ba mu yi kama ba ko daya gashi kuma ya ce musu shi kanina ne kuma zuwansa daya gidan shiyasa suke yi masa wanna titsiyar Hamusu suka fi shedawa."
Ayuba ya biyo shi a baya yana dan bashi ha'kuri na ce ya je kawai babu komai suma suna kan aikinsu ne babu lefi don sun ga bak'uwar fuska sun nemi dalili.
Da yake safiya ce ko ruwan da na ajiye masa bai sha ba muka gaisa sosai da bayan rabuwa zafin nemansa ya sanya shima ko gidana na Abuja bai taba zuwa ba kullum yana kasuwa a sanin da na yi masa tun Yana yaro manemi ne baya zama duk wasu lissafe-lissafe da za mu yi ta waya muke yin komai kamar dai yadda muke yi da Hamusu abinda ya gaya mini shima Usaini haka zai gaya mini sun yi bala'in cirar tuta a wajena dalili kuwa anan shine ni kaina sai dai na ce dukiyar itace tawa ta farko kenan da na zuba domin gudanar da kasuwancin abinda zai ru'banya daga baya kuwa duk kokarinsu ne kuma duk inda suka hango cigaba da sauri za su gaya mini a jarraba ko za a samu nasara. Shekara na yi kuwa za a yi lissafi a fitar da riba da uwar kudi a sallami kowa hakkinsa. Usaini yana tura kayanmu gari-gari ta hanyar yanar gizo an san shi sosai kamar dai yanzu da yake gaya mini ba'ki sun zo daga nijar domin sayan kaya ba ni tamtama a online suka had'u."
Ya dinga jan Minal da wasa tana janyewa na rashin sabo har sai da ya samu nutsuwa tukkuna na dube shi a tsanake na ce."kasan dalilin kiran ka da na yi?"
Ya girgiza kansa a hankali yana fad'in. A a anti amina Allah ya sa lafiya."
Na ce." Lafiya lau kuma alheri ne."
Sai ya saki fuskarsa sosai har da gyara zama yana fad'in." To Ina jinki anti ko za mu sake bude wani shagon ne?"
Na ce." A a matar aure na yi maka."
Saranda ya yi ya zare ido yana fad'in." Matar aure anti a ina take kuma? ban gama gini na ba dalilin da ya sanya kenan na janye idona daga kan 'yan mata domin ba ni so na fara soyayya da budurwa iyayenta su ce na fito. Ni kuma nafiso sai na kammala komai a tsanake sai na nemi mai hankali daidai da ni na aura."
Murmushi na yi Ina kallonsa yana ta jero mini bayani wanda na tabbatar da cewa gaskiya ce tsantsa kuma duk maganar da ya furta tana fitowa ne da can kasan zuciyarsa.
Na ce." Maganar gini mai sau'ki ne Usaini don ma dai ka d'auki irin na zamani da kyale-kyale ai da tuni ka gama ko ba shine wanda ka ta'ba turo mini ta waya ba kwanaki."
Ya ce." Eh shine gidan anti amma yanzu aiki ya kara nisa."
Na ce." To alhamdulillahi Usaini wata yarinya ce na yi maka sha'awarta nutsatstsiya kuma 'yar Malamai idan har Usaini ya samu nasarar mallakar yarinyar nan ina yi masa albishir da cewa ya gama dacewa da ma'aratussaliha."
Ya yi murmushi yana fad'in.'' Kai anti Amina wannan yarinyar a ina take yadda na ji kina kwarzantata wallahi har kin kwadaita mini ita a cikin raina."
Nasa dariya ina cewa." Ka ji d'an gari ko, sai ma ka ganta doguwa chocolate color ga ka farar fata yaranku za su zama wata kala masu kyau."
Ya sunkuyar da kansa yana murmushi."
Na ce." Ka amince kuma ka bar mini wuka da nama a hannuna?"
Ya gyada kansa yana fad'in." Na amince anti Amina wallahi ba ni da ja kuma ba ni da haufi a kan ki na yi farinciki da wannan zabin da ki ka yi mini tun banga yarinyar nan ba har ta zauna a zuciyata.
Fuskata ta kara yalwata da annashuwa na ce." Aikuwa na gode sosai na ji dadin wannan alfarma da ka yi mini amma yau din nan nake so ka sanar da Ummanku duk abinda yake faruwa kuma ina son sanin matsayin jininka."
Ya ce." Zan gaya mata a yau din in sha Allah. Matsayin jinina kuwa( O) ne genotype (AA)"
Wani irin sanyi ya sauka a zuciyata shikkenan an samu yadda ake buk'ata ta wannan bangaran akwai dacewa da cancanta wancan bangaran ne kuma ban san wainar da suke toya ba. Gabana ya fadi na daga kai na dubi agogo sha daya saura kuma yadda suka tsara jadawalin d'aurin auran bayan an yi sallar Juma'a ne.
Na saki ajiyar zuciya ina fad'in ." Ma sha Allah ta kowane bangare an samu daidaito idan har Allah Ya kaddara wannan auran Usaini ina yi maka murna sosai domin ka yi mata."
Ya ce." Na gode sosai anti Allah Ya saka da alheri ya kuma kara girma abinda ki ke yi mana na zumunci Ubangiji Allah sanya miki a mizani Allah Ya jikan iyaye da kakanni."
Na dinga amsawa da Amin Amin Allah Ya taimake mu gabad'aya."
Muka yi sallama kafin kafin ya tashi na gaya masa zuwa dare zan kira shi domin karin bayani.
Ya kama hanya ya tafi na zauna cike da nazari da zullumi hankalina kuma yanzu ya yi can garin bunkure ko a wane hali ake yanzu bai kira ni ba nasan kuma tuntuni ya isa garin tunda babu wata nisa.
Na d'auki wayata gabana na d'an fad'uwa na lalubi lambarwa wayar na shiga sai dai har ta katse bai daga ba. Na sake kira a karo na biyu nan ma bai daga ba jikina ya mutu na ajiye wayar da rashin kuzari."

BUNKURE.
Cike gidan yake zuri'ar Malam D'aha 'ya'ya da jikoki kadai sun isa gayya ba sai sun gayyatowa kowa ba. Amma da yake wannan sha'anin na mussaman ne a gare shi gidan cike yake da nau'in ba'ki daga gari gari nasa da na matayensa mussaman uwar bikin uwargidansa mahaifiyar amarya wato Inno.
An gama towon d'aurin aure suna ta malmale shi a leda ana zuba shi a manyan kuloli gefa guda kuma kirigar tukuwanan miya ne guda biyu kan murhu suke ta cin wuta suna zab'abbaka da tashin kamshi mai shanana a saman miyar.
Yaran mata surukan gidan suna can bakin turgijejiyar bishiyar darbejiya da ba a samu nasarar tun'buketa ba a lokacin da aka sabunta gidan suna ta d'aura zobo a leda suna zuba shi a wani mazubi mai girma. Kowa ka gani cike yake da annashuwa da farinciki daka kan iyayen 'ya'yansu da jikokinsu da surakansu.
Zaure malamin kuwa daga can bayan gidan akwai kofar da aka yi masa ta mussaman domin ba'kinsa wanda Malam Rabi'u ya buk'aci da a yi hakan dalilin gidan akwai matansu babu cancanta maza ma bambamta na shiga gidan kai tsaye duk da sashen malamin daban yake amma dai tilas ta tsakargidan za a bi kafin a isa zauran nasa kuma wasu lukutan iyalansu na fitowa.
Ta wannan kofar suka shiga zauran malamin shi da Dr Iliyas ba kowane ya san da zuwan na su ba.
Malam D'aha na sanye da manya kaya babbar riga da 'yar ciki shadda mai kyau daidai gwargwado da d'inki manya cike yake da Kamala da nutsuwa amma kana duban fuskarsa za ka gane cewa lallai yana cikin farinciki dalilin wanzuwar wani lamari da wata'kila ya jima da shi a zuciyarsa.
Tun bayan gaisuwar da suka yi da shi sai jikinsa ya kara mutuwa kwarai da gaske ya ji a ransa baya buk'atar wannan annashuwar da take fuskar malamin ta dusashe domin kuwa lamarin da suka zo dashi gare shi babba ne wanda zai iya rushe duk wata walwalarsa.
Lallai ne akwai buk'atar zama akan wannan mas'alar mai sark'akkiya kamar yadda mai d'akinsa ta gaya masa ya makara a yanzu ba lallai ne malamin ya yarda da uzurinsa ba tunda ai ya jima da bashi yarinyar mai yasa bai kawo tasgaro ba sai yanzu da aski ya zo gaban goshi
Jikinsa ya yi tubis bakinsa ya mutu d'akin ya d'auki shiru bayan gama gaishe-gaishe daga shi har Dr Iliyas din sai zare ido suke yi domin dai malamin bai fito ba sai da shirya Kuma yawanci irin wad'annan malaman masifar kwarjini ne da su da cika ido.
Dr Iliyas duk 'kumaji da karsashinsa na k'wararran likita sai da jikinsa ya mace ganin yadda wanda ya gayyato shima jikinsa ya yi la'asar sai rarraba Ido yake yi yana sinne kai wannan lamari yana da wahalar fahimtarwa a wajen irin wad'annan mutanan da tauhidi ya yi wa k'awanya da kuma rashin samun ilimin boko mai zurfi ga kuma rayuwar karkara abin dai goma da ashirin.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*152*
Suka juya gabad'aya suna kallonsa a lokacin da ya fara magana kamar haka. " Ya kamata a k'ara duba wannan uzurin da suka zo da shi Allah Ya gafarta Malam nasan da wahala Alhaji Tajo ya d'auki aniyyar tozartaka a irin wannan ranar da gabad'aya ta zame mana abar alfahari da farinciki mussaman da muka tabbatar da cewa wanzuwar lamarin shine abinda ka fi buk'ata a yanzu domin sake kulla zumunci mai karfi tsakaninka da abokinka Alhaji Ibrahimu Allah Ya yi masa rahama da gafara."
Suka amsa da "Amin gabad'ayansu kafin ya sake nutsuwa sosai ya cigaba da cewa zahiri wannan lalura da suke magana akanta akwaita kuma har yanzu tana k'ara yaduwa a wasu wuraran da ba su d'auki abinda ya zo a zamanance da muhimmanci ba. Malam ko dai ka manta shekarun baya ashirin da biyu da suka wuce muka dinga dawaniya da mai sunan Inno har Allah Ya d'auki ranta a asibitin Murtala na cikin garin kano wanda sai a lokacin ne gabad'aya muka san ga cutar da ta zama ajalinta."

ABINDA YA FARU.
Shekaru ashirin da bakwai can baya Malam Nuhu ya auri matarsa ta fari Lantana wadda a yanzu ba ta raye ta rasu dalilin farfadiya tunda tana da mutanan b'oye sa'i da lokaci sukan tashi. Auran soyayya suka yi a cikin kauyen nasu kamar yadda al'ada take duk da wannan lalurar tata ta farfadiya hakan ya zauna da ita tunda yana sonta shi kansa mahaifinsa ya bashi gudumuwa kwarai wajan yi mata magani idan ciwon ya tashi. Da ta samu ciki sai wahalar da take sha ta sake ru'banya tunda kowa ya san yadda masu wannan ciwon suke shan ba'kar wahala a duk lokacin da iskar ta buge su a kan titi ne ko a kasuwa ko a gida sun dinga katantanwa kenan da jikinsu suna malkwadewa tare da taune lebensu da kumfa dafara mai hade da jini.
Suka dinga bige ta a kai akai don babu wanda ya tsammaci za ta haife wannan ciki da yake jikinta lafiya saboda yadda take jigata.
Cikin ikon Allah da lokacin ya zo ta haihu kalau aka samu 'ya mace wadda ta ci sunan Inno Ramatu suke kiranta da Rahma. Tun tana yarinya jinjira ta fara nuna alamun rashin lafiya ido ya jirkice daga fari zuwa yellow cikinta ya yi kurcici sai siraran kafafu da hannu. Da masifar kukan tsiya da zafin jiki domin koyaushe idan aka ta'ba jikinta radau ake jikinsa. Da yake kauyene a wancan lokacin da babu wayewa sosai kamar wadda suke ciki a yanzu sai duka daga can b'angaran iyayenta dana shi Malam Nuhu suka alak'anta lalurar da yarinyar take yi akan shafar aljanu dalili uwarta tana da su kuma sun tashi sosai a lokacin da take d'auke da cikinta a jikinta..
Suka dukufa wajen yi mata jike-jike na maganin gargajiya daga can b'angaran malamin kuwa yana yi mata rubutu da tofi ana bata tun tana jaririya ta saba da shan sassaken magani mai d'auke da ruwan rubutun da kakanta yake yi mata. Har hayaki sukeyi wa yarinyar saboda duhun kai har rukiya sai da Malam D'aha ya yi mata da abin ya ci tura duk a tunaninsu aljanu ne suke tsotse ta kuma suke hana ta bacci da daddare suke firgitata tana kwanan kuka. Duk wannan wuyar da yarinyar take ci Allah bai amshi abarsa ba sai da ta yi shekaru hud'u tukkuna cikin halin rai da rayuwa domin a duk lokacin da ciwon nata ya tashi hayaki ake yi mata aka dingi bata sassake da saiwa wadda aka dafa da jar kanwa.
Wajan cirani can Katsina uban suke hira da abokinsa yana gaya masa halin da yake ciki da yarinyarsa wannan mutumin a irin bayanin da ya yi masa ya gane cewa babu maganar iska sai dai idan wata lalurar ce shine ya ba shi shawara kan cewa ya kaita asibitin cikin gari na kano general ne na kowa da kowa domin yawanci ma mutanan kauyen sun fi morarsa har ya ta'ba bashi labari shima daga nan k'atsina garinsu ya ta'ba kai mahaifiyarsa asibitin na Murtala aka dubata har ta kwanta na tsayin sati hud'u kuma ta samu kulawa kwarai ya ce masa su jarraba yin na asibiti ko za a dace.
Koda ya dawo gida ya sanar da Malam D'aha da kyar ya amince da a d'auki yarinyar a tafi da ita a ganinsa abinda yake damunta bai had'a hanya da asibiti ba domin duka sun d'auka cewa lalurar uwarta ce ta shafe ta.
Ba a tafi da uwar ba tunda tana halin ciwo Inno kakarta ita ta goyata suka tafi dawowar da yarinyar ba ta yi ba kenan domin kwanansu daya a asibitin ciwon ya tashi da masifar k'arfi likitoci suka dinga kai kawo a kanta inaaa babu jini ya kone ta rasu.
A wannan lokacin ne likitan da yake tsaye a kan yarinyar ya zauna ya dinga yi musu bayanin musabbabin abinda ya yi ajalinta babu iska sai tsananin ciwon da Allah ne kadai yasan maganinsa.
Duka ba su gazgata hakan ba a lokacin suka dawo gida da gawar yarinyar daga lokacin ne Malamin ya ce kada a sake daukar wani daga cikin zuria'arsa a kai asibiti duk cuta akwai maganinta cikin al'kur'ani mai girma.
Shekara biyu bayan rasuwar yarinyar uwar ma Allah Ya d'auki rayuwarta sakamakon wata fad'uwa da ta yi iskokai da suke tare da ita suka bugeta a bakin kofar bandaki daga lokacin jikin nata ya'ki dad'i har dai rai ya yi halinsa.
Wannan shine abinda ya shud'e a shakarun baya kuma a iya gwagwarmayar da yake da sauraran redio hurd'a da mutane bambamta tunda a can katsina wajan da yake gudanar da sana'arsa birni ne ba kauye ba ya tabbatar da cewa duk bayanin da ake yi akan wannan lalura gaskiya ne ya gazgata itace silar yarinyarsa ta fari Rahma wanda ada can suke d'auka shafar aljanune.

Malaman D'aha ya yi shiru jikinsa ya d'an shika kadan a lokacin da yaron nasa ya tariyo masa abinda ya shud'e a cikin wasu shekaru da suka gabata. To amma shi a ganinsa wannan kadai ba zai hana k'ulla aure ba domin a zamanin baya wanene ya san da yin wani gwajin kafin a yi auran kuma cutar ba ta yawaita ba."
Malam Rabi'u da jikinsa ya gama mutuwa saboda wannan lamari ya furta." Ya Malam a duba wannan lamari a kawo sasanci a cikinsa domin kada a zo a yi abu anan gaba a koka tun yanzu ya kamata a ce an magance matsalar nan domin ana yin aure ne domin samun zuri'a wadatattu kuma masu lafiya muna neman alfarma a duba a kuma yi adalci ta kowane bangare."
A dan sanyaye ya furta." Rabi'u ba na 'ki ba ne zuwa yanzu ni ma jikina ya yi sanyi tunda zamani aka ce, Annabi Muhammadu S.a.w shi kansa ya yi magana akan zamani duk yadda muka kai ga ta'kawa da gudun sa'bawa Ubangiji idan abu na zamani babu yadda muka iya amma abin lura anan shine mu yi yaya da jama'ar da muka tara domin taya mu murna wannan shine abinda ya fi damuna a yanzu."
Malam Nuhu ya furta." Abu ne mai sau'ki Ya Malam kana da almajira da suka 'yantu da yawa wasu sun shiga cikin gari neman arziki kamar yadda ka saba duba nagarta da cancanta a cikinsu ka bashi auran Hajara a daura da duk wanda ka zab'a mata in sha Allahu ba za a samu wata matsala ba daga kowane bangare."


na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Daga can b'angaransa kuwa ya kira sunan Ubangiji babu adadi ya yi tahamidi tare da jaddada godiyarsa a gare shi ganin yadda aka samu kan malamin cikin k'ankanin lokaci ya magantu cikin kwarin gwiwa ya furta." Idan babu matsala an kuma ba ni wu'ka da nama ina nemawa wani aminttaccen yarona auran yarinyar zan kuma zame musu Uba gabad'aya."
Malam Nuhu ya washe bakinsa Yana fad'in." Ka ji wani iko Allah ko Malam ina ganin duk wanda zai fito daga wajen Alhaji Tajo za a samu nagarta da sasihancin abinda ake buk'ata an samu mafita cikin sau'ki sai a juya d'aurin auran zuwa gare shi.""
Malam D'aha ya dube shi cike da damuwa ya furta." Na so tabbatuwar auran nan da raina ya kwadaitu da shi Alhaji Tajuden amma ga yadda Allah Ya juya lamarin muna fatan hakan ya zama alheri da samun abinda ake buk'ata na kuma baka wu'ka da nama akan Hajara."
Ya dinga godiya kuwa kamar wanda ya yi masa gagarimar kyauta Malam Nuhu fadi yake yi mu ne za mu yi godiya fa Alhaji Tajo mune muke da godiya a wurinka.
Ya tashi ya fita tare da fad'in su jira shi lokacin rana ta yi sosai sha biyu da rabi ana ta haramar tafiya massalaci kai tsaye mota ya nufa Sukairaju ya hango shi ya fito da sauri ya bude masa ya shiga ya mayar da kofar ya rufe ya tsaya daga waje tare da harde hannunsa a k'irji.
Ya sauke ajiyar zuciyar da ba zata lissafu ba godiyar Allah kuwa a cikinta yake yi sai dai yana d'an zullumin saurin yanke hukuncin da ya yi bai kira ta ya ji ya ake ciki ba. Shin wane yaro ne take nemawa aure a yadda yanzu malamin ya karrama shi tare da bashi amana baya tsammanin zai yarda da kowane irin za'bi. Idan wanda take nemawa auran bai yi masa ba zai aurawa Sukairaju yarinyar duk tsiya ya fi shi kuruciya kuma ya tabbatar da cewa zai rike masa ita da amana amma hanzari ba gudu ba shine menene matakin jini tunda dai shi a kan haka ya bijire yana da kyau daga kowane bangare ya samu gamsashen bayani kafin a k'ulla auran.
Jikinsa ya sanyi sosai ya lalubi wayarsa dake cikin aljihu sai a lokacin ma ya lura da kiran da ta yi masa.
Ina zaune jikina duk ya yi la'asar ganin d'aya saura na rana zuciyata na tabbatar mini da cewa wannan auran fa sai an daura shi da mijinki Amina tunda ki ka ga har yanzu bai kira ki ya gaya miki wata matsala ba. Dama fa yana so yaudara ce kawai yake yi miki akwai wani namijin da zai ce baya sha'awar budurci mussaman na yar k'aramar yarinyar irin wannan wadda yanzu take tashi.
Na kwanta a hankali saman gado ina kallon Minal tana yi mini 'buruntu saman madubi yaran dake cikina sai wutsil-wutsil suke yi tabbacin suna buk'atar abinci ba ni kuma da niyyar shiga kicin din babu ma kuzari da karsashin da zan iya gudanar da wani abu.
Na tashi da sauri jin kiran waya na d'auka da sauri shine na sanya a kunnena har muryata na rawa na amsa sallamarsa kafin na ji shi a dake yana fad'in." Wane yaro ne ki ka ce za ki nemawa auran yarinyar nan.''
Jin wannan maganar daga bakinsa na ji sanyi ya cikin zuciyata na daidaita maganata ganin yadda yake furta tasa da isa na ce." 'Kanina ne Usaini dazu na kira shi na gaya masa kuma mu yi maganar genotype domin shine akan gaba kafin komai. (AA) genotype blood group (o)" Duka na zayyano masa wannan bayanin babu hadiyar yawu.
Ya furta.'' Ya kuke da shi Usainin kuma menene sana'arsa kin tabbatar dai da nagartarsa ko domin yanzu amanar yarinyar tana hannuna. Na ji maganar daidaituwar jini amma ina so kada ki rufe mini da son lallai aure ya tashi daga kaina ya koma kan waninki, ki gaya mini halinsa dalili mas'ala irin ta aure mussaman irin wannan da ta zo a jirkice ba a rufi ana fayyace gaskiya daga kowane bangare da ni da ke gabad'aya mun sheda nagarta da tarbiyar yarinyar nan shi wanda ki ke nemawa auran nata nake so na ji bayani na gaskiya a kansa kada ki rufe mini komai a kansa."
Na ji kaina ya wani sara saboda tsananin mamakin maganganun da yake furta mini. Wato da irin abinda zai saka mini kenan. Kwanaki uku da suka wuce ya zama kamar wani mahaukaci saboda tarin damuwa da tashin hankali. Na shiga cikin matsalarsa na bashi shawara domin samun mafita shine yanzu zai juya maganar ta wata siga daban neman mafitata ne ya sanya na ce zan nemawa dan'uwana auranta saboda shi kada ya aureta tunda Ina kishi akan yarinyar. Wannan shine karatun kawai domin duk yadda ya yi maganar a kudindine na fahimta tunda ni ba mahaukaciya ba ce.
Na daure sosai tare da danne tashin hankalin da yake yun'kuro

Please Login or Register in order to submit comment