Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa security lokacin da yake kan sharafin kishinsa. Fadi take yi lallai Hadiza ta yi miji kwarai da gaske abin godiya ga Allah ne. Ban katse ta ba sai da na bari ta gama murna da adduarta tukkuna na gaya mata matsalar da take damun Hadizan. Jikinta ya yi sanyi sosai cikin kasala da sanyin murya ta furta." Har kin sanya jikina ya mutu Amina wannan matsalar ai babba ce kuma ba zai yiwu a rufe ta ba akan son ranmu amma tasan bata da lafiya mai yasa tun farkon dawowarta ba ta yi magana ba wannan ai rashin hankali ne, domin da ta yi magana tun farko da tuni yanzu an ci karfin magani.
Na ce." Ni ma abinda na ce kenan wallahi anti Yagana Hadiza fa sai da na yi da gaske sosai amma duk ta susuce wallahi idan tana yin wasu abubuwan sai ki dauka ta samu matsalar kwakwalwa."
Ta ce." Dole hakan na iya faruwa domin can inda ta zauna din wani darasi ta koyo mai zaman kansa gida ne da idan Allah ya sa mutum ya shiga a sa'a yake fitowa da raunin zuciya da jin tsoro tare da nadama. Idan kuma mutum bai shiga a sa'a ba sai ki ga ya fito da bushewar zuciya tare da koyo wasu dabi'un marasa kyau wanda suka fi na da muni! Mu dai godiyar da za mu yi wa Allah yadda ta fito da kyawawan halaye."
Na ce." Hakane yanzu dai mun yi magana da maigidan ya ce a nema mata magani ko na asibiti ko na hausa zai saya."
Ta ce." Ubangiji Allah Ya saka masa da alheri ki yi masa godiya sosai mun gode Allah Ya jikan mahaifa."
Na ce." In sha Allahu zan sanar masa bayan kwanaki biyu duk yadda ake ciki zan sanar dake in Allah Ya yarda."
Muna yin sallama na kira GARKUWAR MATA. ita ce mai maganin da na tabbatar da inganci da sahihancinsa duk eanda ya san ni da ita ya san ni domin kuwa tunda na fara amfani da magunguñanta ban kuma marmarin amfani da wani wanda ba na ta ba. 08089965176
Duk halin da Hadiza take ciki na gaya mata a take a lokacin ta ce sanyi ne amma bai riga ya girmama ba kuma idan har an dage da magani za ta rabu dashi.
Na ce ta had'a mini mai kyau ta aiko mini dashi har da set din kayan mata irin wanda nake saye. Ta ba ni tabbacin za ta sanya a mota da sassafe. Muka yi sallama cikin amince sannan na duba details dinta na tura mata kudi har da karin dubu goma akai ta kira ni tana yi mini godiya taga dubu goma ita kuma me nake buk'ata na ce ta sayawa yara sweet domin yadda nake jin dad'in magunguñanta sai nake ganin babu abinda zan bata wanda zan biyata.
To wata'kila shi ma da abin ya yini duk da ba girkina ba ne da daddare da ya shigo yi mini sallama sai da ya sake tuntubata ya muka yi da mai magani har yana gaya mini anti Yagana ta kira shi a waya tana yi masa godiya. Na ce eh na gaya mata halin da ake ciki ne, mai magani kuma mun gama magana da ita ya ce nawa ne kudin. Shiru na yi ban iya bashi amsa ba sai nake ganin da kunya ace na bari ya biya tunda ina da halin biya shima ya san haka yau da asibiti ne babu yadda zan yi tunda likitocin da suke duba mu shi yake sallamarsu. Ya dinga tambayata na share shi har abin ya bashi haushi ya shiga fad'a na ce." Kudin fa ba su da yawa ka bar shi na biya gobe za ta aiko da shi."
"Tunda dai na ce a gaya mini ai sai a gaya mini komai k'ankatarsu ai ni na yi niyya ko ke ki ka sanya ni ne da zan ta yi miki magana kina ji ki yi banza da ni."
Na ce." Allah Ya ba ka ha'kuri dubu hamsin ne."
Ya gyad'a kansa ba tare da ya sake cewa komai ba ya d'auki wayarsa ya kunna sai kuma ya sake dubana cikin had'e gira ya ce." Na 'karfin mazan fa? tunda duk inda aka samu maganin sanyi ko na basir ba za a rasa na maza dana mata ba."
Na ce." Yanzu fisabillahi sai na ce mata mijina yana son maganin karfin maza ai sai ta raina ni wane irin kallo kake so ta yi maka ko a jikin jarida da kafafan sadarwa idan ta ga hotonka za ta tuna ashe lusari ne na taba saya maka maganin k'arfin maza a wurinta ba zan iya ba."
Ya dinga dariya yana kallona kafin ya tsagaita still idonsa na tsaye a kaina ya ce." To menene abinda ba ni kad'ai ba ne muna nan da yawa a gari fa, gwara ni ma akan wasu."
"Ni dai mijina gwarzo ne tunda har ya iya bada biyu sau biyu a jera aikuwa ba shi buk'atar wani maganin mazantaka gaskiya ba ka yi wannan lalacewar ba tukkuna ai baka wani tsufa ba."
Ya lumshe idonsa ya bud'e tare da k'ankance su a hankali ya ce.'' Ba ki ji an ce idan da kyau a kara da wanka ba Giwa, ai ba ni nake bada bibbiyu ba Allah ne da damar a hannuna take da tuni na sallami Hauwa itama na bata nata biyun ko na huta da mita."
Ta'be bakina na yi ban ce komai ba domin ba ni so idan muna magana yana yi mini maganarta tunda yanzu sun samu daidaito a tsakaninsu shikkenan kowa ya yi zamansa amma bai fahimci hakan ba sau tari idan muna magana sai ya kira sunanta a ciki. Ganin yadda na kawar da kaina da kallonsa ya sanya shi sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce." Kin sanya mini wani shauki da buk'atar kasancewa dake a wannan dare. Kin yaba ni kin kuma nuna bajintata har kina tabbatar da gwarzontakata na tabbatar da cewa har cikin ranki haka maganar take da gaske da za ki ba ni dama a wannan dare da na sake nuna miki jarumtata na kuma roki Allah bisa k'wanjin da zan zage domin raya sunnarsa ya azurta ni da mai sunan mahaifiyata."

na kudi ne littafin kada ki karanta ba tare da kin biyani hakkina ba

A sanyaye na dube shi. da gaske fa yake shi so yake yi na sake haihuwa kuma ciki yake jajibo mini yara ko shekara d'aya ba su cika ba. Yanzu kuma na yi wata magana cibi ya zama k'ari sannan da yake wannan maganar yau da ba girkina ba ne ta hanyar satar kwana za a samu cikin mai sunan mahaifiyar tasa kenan.
Ya ri'ko hannuwana yana dora bakinsa a wuyana yayin da hucin numfashinsa ke sauka a hankali. Tsigar jikina ta shiga tashi na d'an janye daga jikinsa ya kara riko ni a d'an rikice yana bin jikina yana sansanawa kamar muzurun da ya samu nama bayan ya d'auki shekaru bai yi arangama da shi ba.
Na sake janyewa a karo na biyu ina fad'in." Ya kamata ka tafi wata'kila a can idan rabon ya rantse sai ka ga an samu abinda ake muradi tunda ai ka ga ba zai yiwu ba a cikin hakkin wata ka dinga ikirarin samun mai sunan Hajja idan fa muna neman albarka da kwanciyar hankali.
Ya sake riko ni yana fad'in." Hakan ba haramun ba ne Amina, ki dan ba ni dama mana a cikin wani yanayi nake kwarai da gaske duk da kin nuna ba ki son maganar Hauwa ya kamata ki lura da yanayina ba ni da wata nutsuwa a ranakun girkinta ina kwanciya da ita ne domin hakkinta amma abinda ba ki sani ba shine ba ni gamsuwa irin yadda nake buk'ata. kuma ban fad'i maki haka don na tozartata ba ke ma kada ki yi mata kallon wadda ta gaza a wurin miji Amina ba ni tunanin ko budurwa na kawo ta wadatu da baiwa tare da tarin ni'imar da Allah ya yi miki kin fita daban a cikin mata koyaushe ina alfahari da wannan kyauta da Ubangiji ya yi mini."
Jikina ya mutu sosai to ko dai ya yi ne domin ya ja hankalina tabbas ya samu nasara domin kuwa jikina lakwas ya yi kwakwalwata na tariyo mini zafafan kalaman da ya furzar da su a yau a kaina duk da shi din namiji ne mara k'waron baki ko a shimfid'a ne idan yana nisha'dantuwa ya kan rasa inda zai tsoma rayuwarsa kalaman soyayya da yabawa ina shansu masu tafe da sheshaka da kuma gurnani mai tafe da d'igar hawaye.
Na kan ajiye wannan akan shau'ki tunda ni ma ina yi a wasu lukutan ni da shi din sakarkaru muke zama amma na yau sun sagar mini da gwiwa jikina ya mutu murus ya samu damar tatta'ba ni son ransa amma ban bari lamarin ya wanzu ba domin sai zuciyata take gaya mini idan har kun yi sunna Amina Allah Ya bada rabo to zai iya jarrabarku ta wata sigar domin hakki kuka take babu ruwanki da abinda yake faruwa a tsakaninsu idan yana gamsuwa da ita ba matsalarki ba ce haka zalika ma idan baya gamsuwa da ita.
Na k'wace da k'yar sai kace wasu k'ananun yara ni da shi yana kamo ni ina dojewa na samu na sauka 'kasa cike da mutuwar jiki da tunanin wannan lamari.
Washe gari da safe kalau ya shigo kamar wani abu bai faru ba a tsakaninmu na dinga tunanin yanayin da na bar shi a jiya amma kuma a wartseke ya shigo babu kasala ko k'ankancewar ido gashi kuma da bakinsa ya furta baya gamsuwa irin yadda yake so da Hauwa hakan ya nuna maleji yake yi.
Bai yarda ya amsa gaisuwata a falon k'asa ba sai ya haye sama Hakan ya nuna mini yana buk'atar na bayansa. Ban kawo cewa ga dalili ba ko bayan da na bi bayan nasa gaisawa kawai muka yi ya ce ga abinda ya shigo dashi tunda Allah Ya sa gari ya waye to ya dawo hannuna
Wallahi ni abin ma dariya ya ba ni na zauna ina ta yi ina kallonsa a yadda tun farko muke ai bai dawo hannun nawa ba tukkuna sai da yamma dare ya shiga sai ya shigo na bashi baccin dare daga nan kuma komai ya faru. Yanzu saboda da rigima ya dage yana fad'in kwana biyunta sun k'are har dariyar da nake yi ta bashi haushi ya fara fad'a yana cewa na mayar da shi wawa kenan yana magana akan hakkinsa ina yi masa dariya saboda rashin tausayi.
Ni dai sauka k'asa kawai na yi na kyale shi. Amma daga zarar abin ya fado mini zan yi murmushi ikon Allah. Baccin dole ya yi daya saura na rana na sake haurawa saman saboda lokacin sallah ya yi na same shi ya tashi daga baccin yana ko'karin sauka daga bed din ko kallona bai yi ba ya tashi ya nufi toilet..

Aikuwa dai a daran na gayawa 'yan garin mu abinda duk fitinarsa baya wuce yi sau biyu yau kam uku ya yi yana ta ko'karin yin na hud'u na rasa inda zan tsumbula rayuwata domin kuwa da gayya yake yi yana fad'in tunda ke uwar mata ce bai kamata a ji tausayinki ba. Na galabaita sosai na dinga gwada 'karfina domin na zame amma ina duk ya taushe mini jiki ko'ina na jikinsa 'kwarin gaske k'yam-k'yam! Ya sossoke ni da k'ashin hannu da gwiwarsa.
Da gari ya waye na dinga galla masa harara yana ta murmushi na ce." Ba maganin k'arfin maza ne ya dace da kai ba zumar ki'ba zan saya maka ka yi zuciya don girman Allah ka yi ki'ba kai ko irin tumbin nan na masu kudi ma baka da shi Allah Ya saka mini."
Duk ciccijewar da yake yi sai da ya fashe da dariya ya kishingida lafiyar lau ya ce." Ai na gaya miki irin wannan hawan zan dinga yi miki abinda ba yarinya ba ce ke, giwa wai har kece me yi mini dariya saboda kin raina ni, namiji nake har yanzu."
Na girgiza kaina ban ce komai ba na kama hanya na fita daga d'akin yanzu lamarinsa ya daina ba ni mamaki tunda kullum sabon darasi nake d'auka a wajensa.......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*171*
To 'kasa da kwanaki goma Hauwa ta fara amfani da maganin infection din Islamic din GARKUWAR MATA kyakykyawan result ya fito domin da bakinta take gaya mini wurin da ya kumbura ya sa'be sannan ruwan da yake fita yana b'ata mata pant da karni karni da wari shi ma ya daina zuba tana dariya sosai take jaddada mini cewa a matsanancin buk'ace take tun lokacin da ta fara amfani da maganin take matse-matsen cinya sha'awar da ta mance ya ake jin ta shekara da shekaru to yanzu itace take bijiro mata. Lamarin ya ba ni dariya sosai da mamaki lallai na yarda da maganar GARKUWAR MATA da tun farkon had'uwarmu take gaya mini cewa babu buk'atar rantsuwa akan duk abinda take sayarwa ni zahiri ce kwarai da gaske gashi yanzu na sake gazgatawa maganin ne ya wanko mata duk dattin mara har ta fara jin sha'awar d'a namiji tunda gashi da bakinta tana fad'in cewa ta mance ma yadda ake jin feeling din sai yanzu da tasirin maganin ya tasirantu a gangan jikinta.
Aikuwa sai ta zama abar tsokanata bini bini da abin ya fado mini sai nasa dariya ina kallonta har dai ta tsargu ta fara kame-kame tana sake jadadda mini da gaske take yi kuma ba ta fad'i domin na yi mata dariya ba tsabar farinciki ne ya sanya ta kasa rufe bakinta. Ni kuwa na ce ai dariya kam yanzu na fara tunda har lafiya ta samu to auren zai tabbata da izinin Allah.
Ban sanar da maigidan ba sai da ta gama shan maganin na tsayin sati uku tukkuna lokacin ta kara kasantuwa cikin jazaba irin ta buk'atar ruhi da gangar jiki kuma ba ta jin kunyar gaya mini yanayin da take ciki ba.
Ranar da girki ya dawo hannuna bayan mun nutsu ni da shi na gaya masa halin da ake ciki. Ya yi murna sosai yana fad'in abu na gaba a tsakaninsu zuwa yin gwaje-gwaje kamar yadda zamani ya zo da shi domin samun nutsuwa da kwanciyar hankali.
Ni ma hankalina zai fi nutsuwa da yin hakan daga kowane bangare a samu daidaito.
Alhamdulillahi kowane irin tes an yi kuma sakamako mai kyau ya fito na genotype ya yi mini dadi sosai Hauwa AS Sukairaju A-A Bangaran blood group ma komai ya daidaita yadda ake so. Tsakanin shi da ita sai na rasa wanene ya fi farinciki kasancewar yanzu na taka tudu biyu sai girman da yake ba ni ya kara tsananta duk da maigidan ya gaya masa yayata ce amma risina mini yake yi kuma ba shi yarda mu had'a ido. Ni dai da muka dawo daga asibitin a mota na bar su shi da ita suna zantawa.
Ina shiga ciki na riski Hauwa tare da Mairo a falo suna hira yaran dama sun tafi skull tun safe.
Na zauna kan kujera cikin hijabi don ban iya cire shi ba ganinta a falon a zaune sai nake tambayar zuciyata dalilin zuwanta.
Muka gaisa sosai da sakakkiyar fuska abin har ya so ya ba ni mamaki amma dai na share ban nuna mata na ji dadin zuwanta ba haka zalika kuma ban nuna mata na ji haushin ganinta ba ta ce mini sallama ta shigo ta yi mini farkon wataran maulid wanda saura kwanaki uku kacal mu shiga za ta tafi umara kasa mai tsarki. Na taya murna sosai da fatan alheri mu kad'an ta'ba hirar yara kad'an kafin ta tashi da zumar tafiya ni ma na mi'ke har bakin kofa na taka mata ta fita tukkuna na dawo falon na ce da Mairo ta shiga kicin ta cewa Baba Tabawa su dafa zogalen nan da Masa'udu ya kawo mana tsaraba daga garinsu domin kafin maigidan ya fita ya ce a yi masa kwadonsa idan ya dawo da yamma zai ci.
Ta tashi da azama kuwa ta nufi kicin goye da Hassan a bayanta. Usaini kuma ina da tabbacin yana bayan Taburni tunda kusan tare suke rainon su biyu wasu lukutan Hadiza da Baba Tabawa na sanya musu hannu.
Hadiza ta shigo cikin annashuwa sai na fashe da dariya ina kallonta cikin zolaya na ce." Masoya masu kafasiti Hadiza na fahimci Sukairaju ya saye zuciyarki kina sonsa ba."
Ta zauna tana kallona da murmushinta har yanzu ta ce." Sosai kam, kin san lokacin kuruciya sakarci muka dinga yi na zo na za'bi mugun mutumin nan Alhaji Halilu Umma da Baba Sule suka rud'e saboda watsi da kudin da yake mini, lokacin wallahi ban san menene so ba Amina ni ma kudi da jin dad'in kawai nake hange ashe mugu ne azzalimi na ci wahala a hannunsa ba kad'an ba."
Na gyada kaina a tsanake na ce." Kaddara ce ai Allah ya zano shi a matsayin mijin da za ki aura amma shawara anan shine kada ki yarda ki nuna masa tsananin son da kike yi masa maza suna da wani abu a duk lokacin da suka gane mace na mutuwar sonsu to sukan kwatanta rashin adalci a kanta. Amma ba duka ne suke da wannan halin ba. Ban ce kada ki nuna masa k'auna ba amma daidai misali."
Ya gyad'a kanta a hankali tana fad'in." In sha Allahu zan lura amma fa ni kaina yanzu ne nake jin ina soyayya Amina."
Na yi shiru ban ce komai ba sai ta cigaba da cewa yanzu muka gaisa da Hauwa a farfajiya ta tare ni da fara'a sosai abin har ya ba ni mamaki."
Na ce." Ta sauko ai tana neman shiri ta zo yi mini sallama ne wai za ta tafi umara cikin satin nan."
Ta ce." Allah Ya kar'bi ibada ya sa ta je lafiya ta kuma dawo lafiya."
Na amsa da Amin ta d'an yi jim kafin ta cigaba da cewa." Wai tambayata take yi yaushe zan je gidanta mu gaisa sai na ce mata zan zo in sha Allahu. Shine ta wuce tana cewa wai tana saurarena kafin ta tafi umara."
Na ce." Wata gaisuwar kuma za ku yi bayan wadda kuka yi a yau Hadiza?"
Ta ta'be bakinta tana fad'in." To ni ma haka na gani sabon salon makirci ne ai babu inda zan je kuma ni ban yarda da wannan faram-faram din na ta ba, hausawa suka ce ruwan da ya dake ka shine ruwa.
Ban ce komai sai murmushi na saman lebe Hauwa kenan neman mutane take yi yanzu ga shi kuma ba ta iya mu'amula ba. Nusaiba ta sha gaya mini wai tana kiranta a waya ita har tana mamakin a ina ta samun lambarta yarinyar da ta yi wa zagin tsamar nama da cin zarafi shine yanzu take janta a jiki saboda tana kishin yadda yaran ke dabdala a gidana domin ko zuwan Salim hutu nan wurina yake d'aukar abinci kamar yadda d'an uwansa ke zuwa ya d'auki na rana da daddare Adam kwana ne kawai ba ma yi a tare a gidan. A can gidansu yake kwana tun bayan abinda ya faru da Nabila to yanzu kuma sun juya Legos din shi da Salim din domin cigaba da gudanar da abinda zai kawo musu cigaba a rayuwarsu. Lamarin yana yi mata zafi ba tun yau ba na lura da cewa ta tsani duk wanda zai ra'be ni shima sai ta dasa masa k'iyayya. To yanzu kuma taga hakan bai yi ba ta fito da wani salon. Lambar waya ai ba za ta yi mata wahala ba ko a wurin mijinta za ta iya samu.
Kafin ya shigo gidan ya kira ni a waya yana fad'in zogalan nan da Masa'udu ya kawo dama buhu guda ne d'anye sai uwar doya da albasa ya ce a dibarwa Hauwa na ce to ina mamaki shin shine ya gaya mata ko kuwa a takaice dai na ce." Zogalan kad'ai ka gaya mata an kawo ko da sauran abubuwan?''
Na ji shi yana fad'in.'" Shi tace tana buk'ata idan ma aka ajiye shi zai bushe ko ya lalace ku d'ibar mata tunda tace tana buk'ata."
Na ce." Ba wani lalacewa da zai yi ai kana son miyar zogale sai mu busar da shi."
Ya ce." A d'ibar mata dai na ce." Sai na tare shi da sauri ina fad'in." Ai shine na ce iya zogalan kawai ka gaya mata an kawo ko da sauran tsarabar."
Ya ce." A a ni ban gaya mata ba Giwa mun yi waya ne yanzu take gaya mini ta shigo yi miki sallama bayan ta fita suka gaisa da Masa'udu tasan ya yi tafiya zuwa garinsu shine ya gaya mata abinda ya kawo muku."
Na ce." To tunda hakkinta za ta fitar mata ai kamata ya yi ta buk'aci sauran kuma saboda neman magana ni me yasa ba zata gaya mini ba."
Cikin k'osawa ya furta." Ba ni son 'karamar magana ta zama babba Amina kwana biyu abubuwa sun yi sanyi dalili na fahimci kowacce a tsakaninku kada ki girmama lamarin don ta sanar da ni ba wani abu ba ne, ni kuma ai gashi na gaya miki."
Na ce." Munafurci ne kawai idan da yarda babu wani nufi a zuciyarta ai ni ya kamata ta gayawa tana buk'ata tunda tana da lambar wayata."
Ya datse kiran ba tare da ya ba ni amsa ba.
Kicin din na shiga na ce su raba tsarabar nan kashi biyu daidai a bawa Hauwa.
Hadiza dake gyara alayyahu ta ce." A a ai nan kuke da yawa Amina na yi zaman gidan iyali na gani kin san dai Alhaji Halilu matansa biyu ni ce ta uku ko, to duk abinda ya kawo nawa ne kad'an tunda ba ni da yara. Me zai sanya za a yi haka kuma?"
Ina dariya na ce." To Masa'udu garin kaud'insa ya gaya mata ya kawo tsarabar zogale da albasa tare da doya shine tana zuwa gida ta kira maigidan wai tana son zogale.
Taburni ta ce ." Ban da abin Hajiya Hauwa ai ke da ita duk daya ne sai ta gaya miki tana buk'ata ta shigo ta dibi yadda ranta yake so."
Murmushi kawai na yi ban sake tankawa ba Ina jin su suna ta magana. Hadiza na fad'in." Idan an raba an bata biyu ba a yi miki adalci ba."
Anan ne na ce to wannan tsaraba dai ta Masa'udu na neman ta janyo cecekuce ayi dai yadda na ce din idan ma kyautar da su za ta yi shikkenan a bata zogale ne dama yake yi mana wahala don ta doya da albasa wannan ai ba matsalarmu ba ce ko ku raba daidai a had'a mata cikin buhu sai ta aiko ta d'auka."
Na juya na fita daga kicin ina jin maganganunsa akan lamarin.
Yana kuwa shigowa da abinda ya fara kenan na ce an raba kashi biyu ta aiko ta d'auka ko kai ka d'auka ka kai mata.
Yadda na fadi maganar a harzuke shine abinda ya sanya shi tsirawa fuskata ido yadda ya nuna kamar abin ba na tashin hankali ba ne gashi ina ko'karin girmama shi. Ni abinda ya ba ni haushi yadda ta kasa tambayata sai shi zata tambayata tunda ai Masa'udu direbansa kuma shi ya kawo kayan babu buk'atar ta tambayeni wanda yake zaune dominsa shi za ta tambayata ni ban isa ba. Yanayin yadda ya damu da lallai sai an bata tamkar wadda ta bawa umarni.
Haka dai ya dinga kaucewa neman fitinata domin so na yi ya tanka na fad'i abinda yake raina sai ya'ki biye mini ya kira ta a gabana yana fad'in ta turo Ladidi ko yaron dake bawa shokokin gidanta ruwa ya d'aukar mata.
Ya kashe wayarsa. Ya dinga jana da hira a lokacin da nake zaune a gefansa yana aiki a computer na ki biye masa ni ma. Sai ya ja bakinsa ya yi shiru tsayin minti ashirin da biyar ya gama abinda zai yi ya rufe Loptop din Yana kallona ya ce." In banda dole sai an janyo mini tsiya a gidana ya za a yi rigima akan zogale Amina wai don Allah menene yake damunku ne?"
Na dube shi ina fad'in." Halin tsiya ai yana

Please Login or Register in order to submit comment