Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wai kudin zance.
Na taya murna sosai a lokacin na kuma bata sharwari akan ta dage da addu'a domin duk lamarin da Babanmu ya kar'be shi da hannu biyu to tabbas ya yi istahara a kai ya gano alherinsa don haka idan tace zata tayar da fitina za ta fita zakka a cikinmu tunda ba ita kadai aka ta'ba yi wa irin haka ba.
Sannu hankali soyayyar Alhaji Amadu ta kar'bu a zuciyar Halisa yadda shi ma yake hidima da ita da gidanmu na tabbatar da cewa da gaske lallai auranta zai yi domin duk bayan sati biyu ko kwana goma yake zuwa wurinta har aka tsayar da maganar daurin auransu wata shida farkon watan maulidi.

Abinda ya fi tsaya mini a raina dangane da al'amarin shine yadda mu'amulata da Maryam bata raunana ba na shiga mamaki sosai jikina kuma ya yi sanyi k'warai na tabbatar da cewar duk wannan abinda yake faruwa Maryam bata sani ba domin kuwa da ta sani dole zan ga canji daga wurinta dalili kuwa shine na fi kowa sanin abinda tafi kyama kenan kishiya. Na gayawa Babansu Madina cewa ni fa hankalina gabad'aya bai kwanta da neman auran nan ba, domin kuwa ina zargin abokinsa da munafurtar uwargidansa. Da ya tambayeni mai yasa nake zargin hakan na ce masa naga ko kad'an ban ga canji a wurinta ba muna zumunci sosai domin ma a satin da aka sanya ranar daurin auran ta aikowa da yara kaya kowanne set biyu da muka yi waya ta ce mini sabuwar order ce shine ta d'ibar musu.
Shi kansa ya jinjina al'amarin sosai amma daga lokacin bai kara tayar da maganar ba ni ce dai abin ya dame ni a zuciyata domin sai nake ganin kamar duk ranar da ta san abinda yake faruwa za ta yi mini kallon munafuka ko kuma mai sonta kanta, ba kuma zata ta'ba yarda da cewa mijinta ne ya ga Halisa yace yana so ba za ta yi zargin cewa ni ce na had'a su.
Wallahi na shiga damuwa sosai da sosai domin kuwa ga'barar da Alhaji Amadu ya d'auka ta neman auransa ba mai kyau ba ce a ganina yafi alheri ya fito ya gaya mata akan ya 'boye mata.
Na kasance cikin zullumi da tunani a koyaushe nazarin da nake yi shine idan har Maryam ta samu labarin mijinta zai auri k'anwata wane kallo za ta yi mini.
Katsam watarana na ga text message d'inta ina dubawa na ga ta rubuto mini Aziza na gode sosai ashe tsakanina dake ba zaman amana, kema kin boye mini abinda yake faruwa, na d'auka ni dake yanzu mun zama 'yan uwana na ji don kin gaya mini mijina na neman auran k'anwarki Halisa menene ko kin d'auka zan tsananta kishi a kanta, ai abin gudu a kishiya shine a d'auko maka kwarkwasa wadda ba ka san ni ba, amma ni kam na sheda halinki kuma ina fatan haka Halisa take da kyawawan halaye idan har da akwai alheri a zamana da ita Ubangiji Allah Ya kawota cikin gidana, ke kuma na gode da 'boye mini da ki ka yi."
Jikina ya yi sanyi sosai da na gama karanta sakon data turo mini na zauna ina ta tunani da mamaki. Dama nasan tuntuni ba ta san abinda yake faruwa ba sai yanzu da daurin auran bai wuce wata biyu da kwanaki ba sannan ta samu labari. Hakika kowacce aka yi wa haka dole zuciyarta ta sosu Amma sai na dinga mamakin yadda ta sadada har ta samu damar yi mini text kuma cikin nutsuwa bata kalubance ni akan had'a baki muka yi da mijinta ba.
Na kwana da tunanin hakan a raina sai da gari ya waye tukkuna na kira ta a waya ta daga babu jinkiri muka gaisa sosai cikin ko'karin kare kaina na fara yi mata bayanin abubuwan da suka faru tun farkon neman auran har zuwa yanzu. Ta dinga fad'in ai na d'auka ni dake babu rufi Aziza babban abinda ya ba ni haushi kenan yadda kike biye masa kema ki ka yi mini shiru wato sai dai kawai na ji an d'aura auran kenan kun yi mini adalci.
Na shiga bata ha'kuri da tausarta Ina nuna mata cewar ban san ta yadda za a yi na iya tunkararta da maganar ba domin ni duk a tunani na mijinta ya gaya mata.
Ta ce mini bai gaya mata ba ita ta fahimta da kanta yana neman aure da kuma ta yi bincike ta gane Halisa ce k'anwata.
Yadda muka fahimci juna sosai a wayar ya sanya mini kwanciyar hankali da nutsuwa a zuciyata na amince da cewa Maryam ta sakko ta kuma yi na'am da cewa kishiya abokiyar zama ce kuma hukuncin ne na Allah....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: 🌲🌳🌿☘️
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*2K ON TALGRAM.*
*VIA 0542382124... BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWA PEN*
*07084653262*

*105*
Ta yi d'an murmushi tana fad'in." Kina mamakina daga zuwa na ishe ki da surutu ko Amina?"
Ni ma murmushin na yi wanda babu nisha'di a cikinsa kuma cike nake da fargabar sauraran karshen labarinta dalili yanzu ni gabad'aya ba kasafai nake son abinda zai daga mini hankalina ba. Ta nisa kafin ta sauke zazzafar ajiyar zuciya ta sunkuyar da kanta kasa tana dan yi wani murmushi irin mai ciwon nan ta cigaba da cewa." Muka cigaba da mu'amula da Maryam cikin fahimtar juna tunda ni tsakanina da Allah ban d'auka cewa ta 'kullaci wani abun a cikin ranta ba ganin yadda ta nuna mini a lokacin da ta samu labari.
Sai da bikin ya rage sati bakwai daga bangaranmu nuna ta shirye-shirye. Halisa ta zo tana gaya mini cewa Alhaji Amadu ya kwana biyu bai zo ba kuma kiran wayar ma da yake yi ya jima bai yi ba.
Sai nace mata wata'kila akwai dalili domin mutum ne shi mai sabgogi kada ta damu zai kira ta a waya kuma zai zo ai tunda bikin ma ya matso dole abubuwa su yi masa yawa.
Da wannan na kwantar mata da hankali ta tafi gida.
Abubuwa suka 'kara mikawa mu nan mun dage da shirin biki ango ya d'auke kafarsa ya daina zuwa ko ta kira wayarsa bata shiga. A lokacin ne hankalina ya fara tashi abubuwa da yawa suka fara dawo mini na farko yadda a can garin namu da sauran wad'anda ba su son auran ke ta surutun cewa Babanmu kudi ya duba ya d'auki Halisa ya bayar da ita ga tsoho bayan ga saurayinta da suka jima suna soyayya dan bashi da kudi aka hana shi. Na biyu kuma yadda lamarin auran yake kwan gaba kwan baya ta bangaran angon. Na sanar da Babansu Madina halin da yake ciki, sai yake gaya mini ai baya ma k'asar tsayin sati uku ya yi tafiya zuwa chaina. Na ce ai da sai ya gaya mata tunda ya san halin da ake ciki Muna nan muna shiri. Sai ya ce mini kada mu damu domin sun yi magana dashi kafin ya tafi daga zarar ya dawo za a kawo lefe da sadaki a dauran aure.
Jin haka daga bakin Babansu Madina sai hankali ya kwanta na kira ta a waya na gaya mata tare da sake kwantar mata da hankali. To bayan kwana shida da maganarmu da Babansu Madina yake gaya mini ai sun yi waya dashi ya gaya masa ya dawo a jira shi zai turo in sha Allahu. Hankalina ya sake kwanciya sosai gefe guda kuma dangantarmu da Maryam na sake yin karfi sosai domin babu wani abu da ya raunana kamar koyaushe sa'i da lokaci idan za ta gudanar da wani abu da ya danganceta mussaman akan kasuwancinta ko 'yan uwanta takan kira ni a waya ta nemi shawarata ni kuma ina bata shawara mai kyau ni ma haka duk abinda ya dame ni ina neman hanyar da zan warware zan gaya mata idan ma har ta fahimci matsalata ta kudi ce ko ta wani abu wallahi sai dai naga ta turo mini ta bankina tunda tsakani da Allah ta fi ni k'arfin dukiya sannan mijinta ya fi Babansu Madina abokai ne dai sai dai kowa da yanayin karfinsa kuma suna taimakawa juna sosai Babansu Madina yana da tasa dukiyar daidai gwargwado amma bai kai Alhaji Amadun ba.
To cikin ikon Allah satikan da suka rage na wa'adin da iyaye suka d'auka a matsayin lokacin daurin aure suka shude babu labarin Alhaji Amadu babu aikensa kamar yadda ya fad'a gabad'aya ya ba'ce bat ya d'auke 'kafarsa baya zuwa haka zalika baya kiran wayarta. Hankalin dangi ya tashi domin a tarihin gidanmu ba a ta'ba sanyawa budurwa rana an d'aga ba. Mahaifinmu ya ce na sanar da abokinsa yana nufin Babansu Madina na gaya masa halin da ake ciki.
Na ce duk abinda yake faruwa ya sani sai dai na sake tuna masa.
Koda na gaya masa sakon Babanmu sai da raina ya baci domin maganar da yaga mini akan lamarin ta 'bata mini rai wai Alhaji Amadu ba yaro ba ne shine ya ga Halisa ya ce yana son auranta idan kuma yanzu ya janye ma'ana ya fasa sai a kyale shi yarinya ta samu wani ta aura. Muka dinga musayar yawu da shi a daran har sai da na yi kuka saboda b'akinciki dalili shi ma na lura yana so ya goyi da bayan abokinsa ne, duk wannan hanya hanyar da suke yi mana suna so su tozartamu ne.
Ana cikin wannan tashin hankalin Halisa ta fara ciwo a tsayayye da farko da ciwon kai ta fara ba zan manta ba ni na kaita asibiti aka bata magani na mayar da ita gida. Kwana biyu Mamanmu ta kira ni da wayar Halisan take gaya mini tunda suka tashi da ita a ranar tana kwance a shimfida ta kasa tashi an yi an yi ta mike tsaye ta kasa amma tana magana. Ban kawo abu mai razanarwa ba a cikin raina na ce ta bata wayar mu yi magana ta kar'ba muka gaisa nake tambayarta yanayin jikinta ta ce mini kan nata da sauki sai dai ta yi ta yi ta tashi tayi tafiya ta kasa taka kafafunta baya ga haka kuwa babu abinda yake yi mata ciwo.
Na ce wa Mamamu su kaita asibiti gobe da safe ta ce mini sai abinda maigidan yace tukkuna tana nufin Babanmu.
Haka muka yi sallama cike da damuwa da tashin hankali. A dai ranar Maryam ta kira ni a waya take ce mini ta saya mana wani swiss lece da za mu yi fitar biki da shi ni da ita za ta bayar dinkw mana a can abujan. Na yi kokari sosai wurin danne damuwata na yi mata godiya ban nuna mata halin da ake ciki ba. Mun d'an ta'ba hira a takaice kafin mu yi sallama.
da Babansu Madina ya dawo na gaya masa cewa Halisa fa babu lafiya domin dai ni yini na yi da abin a raina daga ciwon kai sai ace an kasa tafiya. Ganin shine yake kiran wayar abokin nasa kai tsaye ta shiga ya sanya na ce ya gaya masa Halisa babu lafiya ga abinda yake damunta.
Ya ce mini shikkenan zai gaya masa. Washe gari na kira waya domin tambayar halin da yarinyar take ciki abun babu dadi domin ihunta ne ma ya fara yi mini sallama a kunnena. Sai da Mamanmu ta bar wurin take gaya mini tun daran jiya take buge-buge tare da ihu! yanzu haka ma kafafunta sun nannad'e jan jiki take yi kuma a yinin ranar ta yi fitsari ya fi sau d'ari abu ne yake zuba daga gabanta kamar fitsari kamar kuma wata najasar. Kuka na kama yi ina kiran sunan Allah. Na kashe wayar ban jira koma ba na zura hijabina na fito daidai lokacin Babansu Madina ya fito daga sashen abokiyar zamana zai fita ganina a hargitse ina kuka ya tayar masa da hankali ya rike ni yana tambayata.
Ina kuka nake gaya masa halin da Halisa take ciki. Shima hankalinsa ya tashi kwarai da gaske ya ce maza na shiga mota muje gidan.
Wallahi Amina na shiga rud'ani da tsananin rikici a lokacin da naga yadda kammanin Halisa suka sauya gurguwa fa ta zama sosai cikin kwana biyu kacal d'akin da take sai zarni yake yi da karni-karni tana bacci a zaune kafafu a shanye ta yi wata iriyar rama.
Kuka dai a gidan namu kamar ana zaman makoki domin ba mu ta'ba ganin irin wannan tashin hankalin ba. Shi kansa Babansu Madina yana ganin haka ya ce shafar aljanu ne abinda kowa yake ta fad'a kenan.
Kaf gidanmu mu ashirin da hud'u Babanmu ya haifa mata da maza babu wanda ya ta'ba nuna alamun iska jinnu tundaga kuruciya har zuwa girma sai yanzu. Kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa wasu na fad'in wata'kila gamo tayi da su, wasu na fad'in ko ture aka yi wa Babanmu tunda yana harkar malunta ko sun dawo masa ne. Shi Kuma ya ce kafin ya fara harkar malunta sai da ya kafe kansa da gidansa da iyalinsa bai yadda akwai wata iska da za ta cutar da shi ba sai dai idan turo ta aka yi.
Amina in takaice miki labari wallahi mun sha wahala sosai da Halisa sai da ta kai ta kawo Babanmu ya had'a da wasu Malaman domin kuwa ba'kar iskar da aka had'a Halisa da ita mugwaye tafiya suke yi su dawo kuma sun ki yadda su yi magana abinda zai tsorataki kuwa shine yadda suke tsotse mata jini a lokacin abinka da mace mai garin jiki wallahi ta komade sai 'kashi da jijiiya duk sun kad'e mata gashin kanta.
Duk abinda aka yi Alhaji Amadu bai zo ba kuma Babansu Madina ya tabbatar mini da cewa ya gaya masa ke da aka tsananta ma sai ya kawai ya fito ya gayawa Babansu Madina cewa ya sanar da Babanmu cewa ya janye duk abinda ya kawo da zummar auran Halisa ya bar mata.
Ni kuka Mamanmu kuka saboda tsabar b'akinciki da takaici. Ya fasa auranta ga matarsa ta yi wa yarinya makaru(asiri) ta had'ata da iskokai masu mugunta sun nakasata. Ni nasan Maryam ce da wannan aikin ban fito na fad'a ba amma da yawa kowa abinda yake cewa kenan Maryam ce ta yi mata asiri saboda kada ta auri mijinta.
Wasu sun gazgata hakan wasu kuma suna fad'in kada a d'auki alhakinta jarrabawa ce kawai daga Allah.
Kuma fa cikin wannan halin babu wata alama da Maryam ta nuna mini daga bangaranta muna yin waya sosai kuma tana yi mini aike kamar yadda ta saba amma ta daina yi mini maganar bikin ni ma kuma ban ce mata komai ba.
Amina mun ci ba'kar wahala da Halisa kafin Allah Ya kawo k'arshen masifar a ka yi nasarar magana dasu dukansu arna ne su dari da d'aya. Ki ga aljanu arna dari har da daya aka d'ora su akan yarinya kamar Halisa. Sun fita da suka ji wahala sun ce yanka aka yi musu domin su shiga jikinta su wahalar da ita. Ba su fadi suna ba amma sun ce macace ta sanya su aikin.
Aka ce wai ba a yadda da maganar jinnu ni dai kam Amina a wannan karon na yarda da maganarsu domin kuwa ko kaffara ba zan yi ba Maryam ce ta yi wa Halisa wannan turan.
Tsayin wattani shida Halisa ta d'auka cikin jinyya sai da ta sake yin sama da wata shida kafin ta dawo hayyacinta domin kuwa ko da aka samu nasarar raba ta da su wallahi mun ci ba'kar wahala kafin ta daina firgita tafiya kuwa sai da aka dinga koya mata har yanzu kafarta ta hagu bata dawo daidai yadda take ba tana d'an janta a 'kasa. Da 'kyar ta mayar da jikinta gabad'aya dabi'unta kamar an canza mata su ta dawo shiru shiru mara son hayaniya da surutu kullum tana kwance a d'aki kana dai kallonta zaka tabbatar da cewa bata da ishshiyar lafiya. To alhamdulillahi tunda an yi nasarar rabata da su tana tafiya da k'afafunta tana kuma ibada ruwan najasar da suka sakar mata ya d'auke sai dai ta zama kamar kurma don sai ta yini ba ta yi magana muddin ba a yi mata ba hakan ba damuwarta ba ne.
Allah ba yadda baya shirya lamarinsa kuma mun gode masa amma tun daga lokacin na janye jikina da Maryam kuma na tsorata sosai da abinda ta aikata akan umarnin Ubangiji tabbas za ta iya aikata komai akan abinda ranta baya so ashe duk alherinta da nake gani jama'a suke gani zata iya aikata wannan mummunan aikin akan son rai.
Murtala ya sake dawo wa a karo na biyu domin auran Halisa Babanmu duk ya gaya masa abinda ya faru da halin da take ciki a yanzu ya ce ya ji ya gani zai aureta hakan mahafinsa ma ya ce dama matarsa ce shiyasa Allah Ya shirya hakan don haka a shirye suke wata uku kacal a ka sanya daidai gwargwado suka yi abinda al'ada ta ce a yi aka daura auran. Wallahi Amina washe garin ranar da muka kai Halisa gidan mijinta Murtala sai ga Hajiya Maryam a gidana da kaya kiriga guda wai gummuwa ce ta kawowa Halisa tunda ban gaya mata bikin ba ta ji labari ta zo yi mini Allah Ya sanya alheri.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *07084653262*
Wallahi Amina duk yadda na so da ganin na sakar mata jiki kasawa na yi duk tsananin sabon kuwa da yake tsakaninmu sai ta dinga ba ni tsoro daga zarar na kalleta sai na tuna irin mawuyacin halin da Halisa ta shiga. Duk da zato zunubi ne amma tsakani da Allah kenan na fi gazgata cewa itace ta jefi Halisa ta kuma juyar da hankalin mijinta akan lamarin gabad'aya. Haka nan muka yini da ita kadaran kadahan domin hausawa suna cewa idan ba ka iya kama b'arawo ba shi sai ya kama ka shiyasa kawai na kyaleta ban iya ce mata komai akan lamarin ba tunda ai a duniya muke akwai kuma ranar tsayuwa idan har ita ta cutar da Halisa ta d'ora mata muguwar jinyya mai wahala ubangiji zai fitar da hakki.
Muka rabu kowa zuciyarsa cike da tunani domin kuwa ko bata fito ta fad'a tabbas ta fahimci na canza mata ba kamar yadda muke a da can baya.
Lokacin da na gayawa Babansu Madina zuwanta da kayan da ta kawowa Halisa da yara ya yi godiya kawai daga haka bai sake cewa komai ba Amina kin san su maza ba su yarda da irin wannan muddin ba gani suke yi a zahiri ba domin da farko da na gaya masa nuna zargin Maryam akan ciwon dake damun Halisa ya dinga fad'a yana cewa shikkenan lalura ba zata samu bawa sai a jingina hakan da wani mutuniyar kirki ce wadda ba ta da abokin fad'a sam baya tsammanin za ta aikata haka.
Duk yadda na so na fahimtar da shi ya kasa fahimta nagartatta kawai yake fadi shi ma ya sheda ayyukan alherinta a zahiri.
To sai kawai na kyale shi domin ba zai yarda ba zai ce muna neman tayar da fitina ko mu had'a shi da abokinsa.
Tun daga ranar da ta zo taga sauyi a tare da ni sai ta janye jikinta itama. Amma ba gabad'aya sa'i da lokaci tana kirana a waya mu gaisa ko kuma na ga aike mussaman idan zata turo kaya garin nan to za ta had'o da sakon yara mai delivery ya kawo mini har gida. Duk shekara kuwa idan ta fitar da zakka tana turo mini ta ce na duba family din mu wanda suke da k'aramar sana'a na ba su domin su tashi da kafarsu. Wannan shine zan fad'a akan Maryam Amina amma ban ta'ba zarginta akan dukiyarta ba dalili nasan macace mai zafin nema mussaman a lokacin da iyayensu suka rasu ya kasance girma ya hau kanta duk itace take tsaye a kan 'yan uwanta kuma mijinta ya tsaya mata sosai har ta kafu kwarai ta tsaya da k'afafunta ko a lokacin da muke mu'amula sosai nasan tana da manyan shaguna uku daya a garinsu biyu a garin Abuja. Amma yanzu labarin da nake ji a tsakanin matan abokan mijinmu ta mallaki wurare da yawa a rassa daban daban da ake mata hurd'a ta kasuwanci. Lokacin da na samu labarin auranta da Alhaji Tajo na yi mamaki sosai ya aka yi ta amince da zama dashi a matsayin ma'aurata bayan yana da iyali ita kuma da bata son kishiya. Sai babansu Madina yake gaya mini wasiyyar da Alhaji Amadu ya bari kenan amma ba zan boye miki ba wallahi na shiga tashin hankali ganin da na yi mata a yau sai na ji gabad'aya duniyar ta fice mini daga rai lallai d'an Adam ba a bakin komai yake ba. Dama na sanar da Halisa kafin mu zo shine fa ta ce idan har na zo na ce tana gaisheta da sannu da jiki wallahi lokacin da nake gaya mata sakon Halisan sai hawaye shaaa suka sauka a kumatunta har na yi danasanin gaya mata ta ba ni tausayi sosai lallai Allah ya jarrabeta da ciwo mai wahala muna ro'kon Allah Ya bata lafiya ya kuma yafe mata kuskuranta."
Ajiyar zuciya na saki a hankali na ce." Amin suma Amin, muna nema mata afuwa da sasaauci wurin Allah, ai d'an adam sai dai idan ba hallice shi a duniya ba Hajiya amma tunda annabawan Allah suka kuskurewa Ubangiji kowane bawa ba zai tsallake ba, sai dai mu yi addu'a akan Allah Ya sa kada son zuciya ya sanya mu cutar da wani tabbas ban so jin wannan labarin ba wallahi ba zan boye miki ba hankalina ya tashi amma komai dalili yake yi. Momi ta aikata abu mafi muni shirka shine had'a Allah da waninsa cutar da wanda bai ji ba kuma bai gani ba. Idan na ce miki ta yi mana wani abu mai razanarwa na yi mata sharri domin ni dai a zamana da ita ban hangi wani babban lamari kwatankwancin na Halisa ba. Kamar yadda kika fad'a macace mai alheri domin ta ri'ke mini yarana da ubansu ya rasu don 'karamin ma ya fi shekara shida a hannunta babban ne bai wani

Please Login or Register in order to submit comment