Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dalilin gudun abinda ka iya zuwa ya dawo tunda mugun nufi ne fal a zuciyarta game da ni.


Na kudi ne littafin nan kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Yammacin litinin ya dawo kamar yadda ya gaya mini da muka yi waya shekaran jiya daga d'akina ya fita ranar da zai tafi don haka ina yi masa sannu da zuwa na sau'ko k'asa. Ita kuma ta hau ba ta sauko ba sai gefin magriba shi ma ya sauko da shirin massalaci sai da ya dawo tukkuna ya zauna a falon yaran suka taru a wajensa yana ta wasa da su. Ka'ida ne idan yana falon masu aikin basa fitowa sai ya kasance ni da Hauwa ne kadai a zaune da yaran ana ta wasa da dariya. Hauwa ta ci ado da jins da 'yar k'aramar riga sai ta yafe wani bakin mayafi a kanta. Wallahi tausayi ta ba ni ainun ganin wanda ta yi wa kwalliyar ba ya yi mata irin kallon k'aunar yake yi mini. Yana dai amsa mata magana idan ta yi amma ban hangi wani shau'ki da jin dad'in kin burgeni ba abinda yake yi mata ya sanya ni jin kunya da nauyi ta tashi ta shiga d'akinta ya kai sau uku ta fito ta zauna amma ban ce ya san abinda take yi ba.
Ya dube ni yana fad'in." Yarinyar nan Hajara ta sake ba ni sa'ko wajenki yana mota."
Jin haka ya sanya Hauwa yin kicin-kicin da fuska domin yanayin yadda yake sako ni a maganarsa ya fara bata haushi gashi kuma ta ji an ce an bada sa'ko a kawo mini."
Na furta.'' Aikuwa na gode sosai a sanya a kawo nasan abin motsa baki ne."
Na fadi hakane domin ko menene a bud'e shi a gabanta kada ta zargi wani abin tunda ita dabi'arta ce."
Ya d'auki wayarsa kuwa da sauri ya kira Sukairaju ya ce ya duba cikin mota zai ga wata leda mai zane-zane ya d'auko masa ita.
Muna zaune kafin Sukairaju ya shigo ya miko mini wayarsa yana fad'in." Duba gidan Malam D'aha an fara aiki."
Na kar'ba da sauri da fara'a ina fadin." Alhamdulillahi na fara dubawa an rushe gidan gabad'aya aiki ma ya fara nisa.
Na mik'a mata wayar ina fad'in." Gidan Malam D'aha ne za a sabunta shi."
Ta kar'ba da d'an murmushi irin na saman lebe tana dubawa na dube shi ina cewa." To suna ina yanzu?"
Ya ce." Na sanya su a wani gidan daga zarar an kammala aikin an gyara musu ko'ina za su koma."
Na ce." Na yi musu murna sosai Allah ya saka maka da alheri."
Ya amsa da Amin a takaice."
A maimakon ta miko mini wayar kamar yadda na bata sai ta tashi tsam! ta nufe shi da wayar a hannunta. Na bita da kallo cike da mamaki da tausayi da dariya wai ita dole sai ya ga kwalliyar k'ananun kayan da ta yi.
Koda ta bashi wayar sai ta zauna a gefansa tana dan janyo hannun Sultan da yake kusa dashi a tsaye ya dafa gwiwarsa yana dabo (ta-ta-ta) Ya kuwa fad'i timm! ya tsalla kuka da kar'fi tunda daman sai da ya dafa kujera ya tashi.
Aikuwa ya juya yana kallonta da harara yana ce wa." Menene haka? kina zaune can kin zo kin sanya yaro kuka yarinya ce ke?"
Ba ta ce masa komai ba ta d'auki yaron domin rarrashinsa ya dinga zille-zille yana kuka shi kuma sai tsaki yake ja tabbacin haushinta yake ji dangane da kukan yaron
tana jijjigashi ya'ki yin shiru sai ta dubi Khalil cikin muzanta da jin kunyar abinda yake yi mata ta ce." Kira Baba Tabawa ta zo ta d'auke shi."
Ya furta" D'auke shi kai maza kai mata shi ta goya shi."
Ya d'auke shi da sauri tare da nufar d'akin su Baba Tabawa da shi yana ihu shima yana son kasancewa da uban da 'yan uwansa.
Sukairaju ya shigo da leda mai zane-zane a hannunsa. Mu ka gaisa cikin mutuntawa na ce." Ni za ka bawa ai."
Ya miko mini ledar yana murmushi ya juya ya fita. Ko da na bud'e sai na ga dangin su goruba ne da kad'anya gauta da yalo da d'ata har da alawar madara a cikin wata farar Leda.
Ina dariya na daga kaina na kalleshi tare da cewa." Yarinyar nan ta iya bada sa'ko fa."
Bai ce komai ba hankalinsa na kan k'aramar wayarsa. Minal ta zo tana le'ka kanta cikin ledar "Mama menene?'' tana fad'a tana k'ara zura kanta ciki. Na ce" Zo mu je kicin a wanke kayan dadi ne."
Ta kuwa biyo ni da saurinta twins suna zaune da wayarsa a hannunsa game ya kamo musu.
Na cire ledar alawar madarar na jika musu gorubar domin ba za su iya cinta a bushe ba. Abu ne da ba su saba dashi ba sosai sai ya zame musu kamar nama. Yalo da d'ata da kad'anya duka na gyara musu suka kewaye ni muna ci Hauwa ta ce ba ta yi sha'awa ba wanda na tabbatar da cewa ta fadi hakane kawai saboda zuciyata tana yi mata zafi babu wata maccan da ko babu uzuri na juna biyu ta ce bata marmarin irin wad'annan kayan gonar. Ganin yadda muke ci da yaran ya ce shi ma a bashi daya.
Usai ta d'auki yalo 'kato ta kai masa.
Ta d'auki wani ta tafi wajan Hauwa tana mika mata. Ta kar'ba amma sai ta ajiye shi saman cinyata ta yi shiru duk ta yi sanyi abin gwanin ban haushi da tausayi domin dai Hauwa ko kana jin tausayinta idan ta kuntuka maka wani takaicin sai ka ji kamar ka rufe ta da duka saboda haushi.....

Daga karshe ma sai kawai ta tashi ta shiga d'akinta ina hankalce da shi bai bita da kallo ba balle ya shiga damuwa don ta bar wajen.
Ta gama kwanaki biyunta ban san wainar da suke toyawa ba. Na kar'bi girki na kasance cikin walwala da farinciki kamar yadda shima ya kasance duk wata hanyar da zata kara mini mutunci da soyayya ita nake bi a yanzu muddin bai shigo mini da son zuciya ba kalau muke zaune a yanzu kuma idan zai nemi ni sau nawa ba na nuna gajiyawata jikina ya horu kwarai da dabi'arsa sai aka yi katari da wannan cikin da nake d'auke shi ba mai k'yamatar lamarin ba ne.
Na kwana biyu ban ji daga Sahura ba ina jin tun bayan wayar da muka yi take gaya mini Idiris ya buge kwado ya shiga gidanta babu yawunta sau biyu muka kara yin waya kuma idan na soko mata da maganar abinda yake faruwa a tsakaninsu ba ta saurarata fadi take yi ta daina gaya mini matsalarta tunda ni ma goyon bayansa na ke yi.
Katsam yau ta kira ni tana gaya mini tana zargin fa auran da Idiris ya k'ara ya gurgud'e. Na tambayeta dalili ta ce mini kullum a gidanta yake kwana tsayin sati uku kenan kuma neman shiri yake yi da ita.
Jikina ya yi sanyi sosai Idiris bai shirya ri'ke musu yarinya ba ya aura aure duka bai fi wata hud'u ba an fara cin karo da matsala. Ta ce mini ai tana zargin ma yarinyar tana da juna biyu ta ji Yayarsu wato uwar mijin Yusura tana fad'a a wata had'uwa da suka yi a gidan sunan k'aninsu amma dai ba su fito sun fad'a mata cewa sun rabu ba ta ji dai suna fad'in saura amaryar Idiris a jerin masu haihuwa domin itama ciki ne da ita.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*142*
Na cika da mamaki 'kwarai da gaske da jin wannan lamari
ni babban takaicina ma yadda yake ko'karin mayar musu da yarinya k'aramar bazawara tunda a yadda take ba ni labari duka bata fi shekara ashirin ba idan hakane kuwa ai da kadan ta girmi Yusura. shari'ar aure ba a yanke ta kai tsaye amma jikina yana ba ni cewa matsalar daga wajansa take wanda itama Sahura take zargin hakan domin ta ce har yanzu ya'ki yi mata bayanin komai sai kame-kame ya yi da kuma neman shiri da ita to kuwa duk yadda ya kai ga b'oyewa dole watarana kowa ya ji dalili mussaman a nasa b'angaran tunda har tana da juna biyu Allah kyauta ya kuma rufa asiri shine kawai abinda za a ce.
Kwana bakwai da dawowarsa guda yake gaya mini na shirya satin da za mu shiga juma'a kenan za mu je jigawa d'aurin auran Alhaji Sulaiman mijinsu Hajiya Aziza. Idan an daura za mu kwana d'aya sai mu dawo gida. Na ce masa to shikkenan, cikin zuciyata ina ta mamaki ashe auran da na ji kwanaki yana fad'a da gaske ne. Kuma wata'kila budurwar zai aura lallai tsufa ya yi gardama an kuma shigo da son zuciya iyayen yara da su kansu masu auran yara k'ananu. To Ashe tana jika a cikin gidana ni ma. Ni dai bayan dawowarmu daga d'aurin auran Alhaji Sulaiman kamar yadda ya fad'a sai nake ganinsa wani sukuku babu irin sa'ke-sa'ken da zuciyata ba ta yi mini ba akan ganin ya canza na d'an ta'kin lokaci. Zuciyata na kawo mini ko shima ya yi sha'awar budurci ne tunda mafiakasarinsu abinda sukewa kulafuci kenan ya sanya suke ture kunya da kawaici su auro 'ya'yan cikinsu su kwanta gado daya da su.
Na zura masa ido kawai yanayin yadda ya fara tafiyar da al'amuransa na rashin walwala da yin shiru da nazari ni ma sai na tsiri yin hakan muka cigaba da tafiya a haka bai gaya mini damuwarsa ba ni ma ban nemi da na ji ba. A d'ayan biyu ne ko matsalar kasuwanci ko kuma shi ma auran yake nema amma kuma yana cike da zullumi da damuwa ga yawan kallona da yake yi daga zarar mun had'a ido sai ya wayance ya tsiri yin wani abin. Yanayin da ya 'kir'kirarwa kansa bai hana shi yin mu'amula da ni a duk lokacin kwanan aurena ba. Hauwa dai har yanzu jiya iyau domin ga dukkanin alamu cutar damuwa(Depression )ddaf take da ta kamata abin gwanin ban tausayi da takaici.
Ana haka Sahura ta kira ni take gaya mini Idiris suna kotu da amarya iyayanta sun buk'aci ya saketa ya ce sai an biya shi abinda ya kashe kafin auranta.
Alkali da ya nemi jin dalili kaf aka gaya masa. Duk wata hidima ta gida ya gaza sai masifar kwanciya da yake yi da yarinyar mutane babu dare babu rana ga rashin k'oshi tunda ya yi na amarci ya jingine k'aramin buhun shinkafa da rabin kwalin taliya da makaroni da kwalbar manja da mangyad'a da had'in maggi. Da suka 'kare sai ya shiga auno mata wake yace ta dinga yi fate-fate yana 'kara jini tunda tana da juna biyu sai ta fi sati daya tana cin wake fate ko 'kulu da mai da yaji da safe ya sayo mata kunnu da awara. Yadda yarinyar take fad'a tana kuka sai ya shigo da leda cike da abin dadi ya zauna ya ci a gabanta ya bar ta da tsotse 'kashin da ya sale masa tsoka. Ya kuma isheta da bala'in kwanciya da daddare ga rashin abinci mai kyau. Da ta ce ta gaji da cin wake sai ya auno mata tsakin masara mai yawa da barkono da farin maggi da manja wai ta dinga yin d'anmalale.
Yarinya mai garin jiki duk ta tsotse gashi baya dawowa da wuri sai sha biyu na dare wataran har da rabi tukkuna zai sanya mukkuli ya bud'eta tunda idan zai fita kulleta yake yi ta ciki
yau da gobe ta'ki wasa har dai iyayenta suka gane wuya yake bata yaran shago ma suka bada shedar kulleta yake yi kuma wataran akan idonsu yake dawowa tunda suma suna kaiwa sha biyu na dare ba su tashi daga aiki ba.
Sosai na tausayawa yarinyar. Ita kuma Sahura sai na lura kamar murna take yi tana fad'in hakkinta ne domin duk auran da aka gina shi akan zalinci da kwadayi k'arshensa kenan wallahi ba zata rike masa d'an ko wace shegiya ba.
Na ce." Ke abinda yake damunki kenan ko Sahura an ce mijinki yana raba dare a waje shi ba wani business yake yi ba na cin kasuwar dare ba balle a ce ba ki yi tunanin wani abu ba?"
Ta ce." Ba zai wuce yana yawon neman mata da d'an kudin da ya samu ba, ai ki bar d'an iskan namiji Amina kin ga ni ban ci ba haka zalika yarinyar mutane ma da ya auro bata ci ba ya tafi yana kaiwa matan banza shiyasa tunda ya yi auran nan kamar na sani ban sake ba shi kaina ba."
Na ce." Lallai akwai buk'atar ki sanya ido akan Idiris Sahura kada kishi ya sanya nan gaba ki yi nadama idan ya kasance Idiris ya fad'a harkar bariki kina da kamasho tunda ke kin San wanene shi gashi kina ba ni labarin irin durzar da yake wa yarinyar mutane yanzu da babu ita ai zai sake tsunduma tunda ke kin daina ba shi kanki. Haihuwar da ta ratsa tsakaninku ta wuce komai."
Ta ce." Haka kowa yake cewa Amina amma bari kiji wallahi yadda Idiris ya cire kawaici a kaina ya gwada mini rashin Imani babu wani dalili da zai sanya ni don ya shiga matsala a yanzu na damu. Na gaya miki fa yanzu ko ya sake ni ba ni da damuwa Allah ya yi mini rufin asiri ina da matsuguni da 'yan kudi a asusuna zawarci zan buga mai kasafiti Hajiya."
Dariya ta kama ni na ce." Sahura ki dai yi tunani akan maganata ki yi hakuri ku samu daidaito don Allah ko saboda yaranmu babu dad'i Idiris ya lalace dole za a danganshi dake ace tsohon mijinki ne kuma uban yaranki.
Ta furta." Ai ko zamu daidaita ba dai yanzu ba Amina wallahi yadda ya gumami ni ba'kinciki in sha Allahu masifar da zai tsinci kansa sai ta shige wadda ya jefa ni."
Da haka muka yi sallama tunda duk ta inda na biyo sai ta doje ta nuna yanzu ba lokacin da ya dace a ce ta tausaya masa ba ne.

A daran ranar da muka yi wannan tattaunwar da Sahura bayan isha'i muna falon gabad'aya masu aiki da yaran ban da Hauwa da yake girkinta ne tana ta kai wa da kawowa daga kasa zuwa sama. Na ce da Baba Tabawa ta kawo mini abinci. Towon shinkafa suka yi miyar taushe da tantakwashi. Sun jima ba su miyar taushe a gidan ba wannan dalilin ya sanya mini mugun mararin son cin towon. Ina ci muna hira da su jefi-jefi Hauwa ta sakko kai tsaye dakinta ta nufa sai ta d'an tsaya tana kallona kafin ta ce." Maigidan fa baya jin dad'i Amina."
Gabana ya buga da k'arfi a take a lokacin na ji abincin ya fitar mini daga rai Allah ma dai ya sa na ci da yawa. Na daidaita yanayina sosai kafin na ce." Mai yake damunsa?"
Ta d'an ta'be bakinta tana fad'in." Ciwon kai na ji yana gayawa likitansa yanzu tun rana da shi dai ya yini na yanzu ya yi tsanani ko 'daga kansa baya iya yi yana kwance."
Na yi 'kasa da kaina abin har ya kai ga kwanciya irin haka wace irin matsala ce take damunsa da har zai ajiyeta a ransa ta haddasa masa ciwo.
Ta shige dakinta ba ta sake yi wata magana ba.
Kafin na haura saman sai da na sanyo hijabi jin cewa likitansa yana kan hanya
Yana kwance shar'be a gado ya dafe kansa da hannunsa.
Na zauna gefansa jiki a mace ina fad'in." Baba baka da lafiya ashe?"
Ya dube ni da gefan ido ya furta." Ciwon kai ne Amina yanzu nan ya sake tsananta."
Na ce." Kana jin sa ashe a hankali a hankali ba ka yi magana ba sai yanzu da ya kwantar da kai an ta'ba wasa da lafiya ashe."
Ya yi shiru bai ce komai ba. Na gyad'a kaina ina fad'in." Ni ba yarinya ba ce duk yanayin da kake ciki ina hankalce ban buk'aci dole ka gaya mini sirrinka ba wata'kila baka son kowa ya sani shiyasa ka yi shiru abin yana cin ranka ya kamata a ce ka sassautawa kanka dalilin gudun faruwar mummunar abu akwai shekaran girma a tare dake kuma idan ban manta ba kana da hawan jini bai kamata a ce ka dinga ajiye wani abu a cikin ranka ba. Amma ina so na gaya maka cewa ko ka fad'a ko baka fad'a lallai kana cikin damuwa domin gabad'aya al'amuranka sun canza a tsukin lokacin nan."
Ya yun'kura ya tashi zaune yana kallona da wani irin yanayi ya ce." Lallai ina cikin damuwa Amina amma ban san yadda zan yi na fitar da kaina daga cikinta ba."
Na ce." Duk abinda ya yi tsanani ai maganinsa Allah kaine ka ke da hanyar fitar da kanka daga cikinta idan ka sanya hakan a ranka."
Ya gyad'a kansa yana kallona amma bai ce komai ba.
Jikina ya sake yin sanyi na d'an riko hannuna a hankali na ce." Idan babu takurawa ka gaya mini damuwar da take damunka ko Allah zai sanya ina da shawarar da zan baka."

na kudi ne wànnan littafin Yar uwa don Allah a duk inda za ki gan shi kada ki karanta sai kin biya ni hakkina.

Ya furta." Malam 'Daha ne ya ba ni 'yarsa amma ban san ko wacece daga ciki ba, kin san dai gidansa cike yake da yara ko?''
Kunnena ne ya yi dumm! kamar irin kumfar sabulu ta shiga ciki na ji ya sake rintse hannuna yana fad'in." Ban zan iya bijire masa ba Amina wallahil-azim ba zan 'ki 'karbar tayinsa ba."
Na zuba masa ido kawai ina kallo bakina ya yi nauyi na rasa ma abinda zan ce saboda zahiri na 'kadu da jin maganar nan gidan Malam D'aha babu wata cikakkiyar budurwa duk matasa ne kuma mafi akasari daga sassan gidan suke fitowa alamu sun nuna wasu daga ciki 'ya'yan yaransa ne irinsu malam Rabi'u. Jikokinsa kenan
Hajara ita ce kadai 'yar budurwar da ta fara tasawa tunda ta fara 'kirgar dangi sun yi cibir-cibir a cikin riga ba ma su kai a sanya musu rigar mama ba.
Na daure na ce." Ai duk babu wata budurwa cikakkiya a gidan Malam D'aha."
Ya ce." Akwai uku da bai aurar da su ba sauran jikokinsa ne a cikin ukun ya ba ni d'aya ban santa ba ni ma."
"Hajara ce abinda zuciyata take raya mini kenan. Muka yi shiru ni dashi muna duban juna Hauwa ta shigo sanye da hijabi a jikinta ta same mu a haka mun k'urawa juna ido ga hannuwanmu a ri'ke
ta kasa jurewa muryarta tana rawa ta ce." Ka ce baka da lafiya maganar duniya na yi maka baka tanka mini ba kana kwance kana jina yanzu gashi kuma yanzu na shigo na gan ku ma'kale da juna wallahi Amina ku ji tsoron Allah hakkina ba zai bar ku ba ba zan ta'ba sahale muku ba a ranar lahira."
Na juya da mataccen jiki ina kallonta. Wata gaud'iya da ita ana ga gabas tana ga yamma. Karamin tsaki kawai na ja ban ce komai ba na cire hannuna daga cikin nasa. Ya sake kamowa yana fad'in." Kin ce akwai shawarar da za ki ba ni ko Amina wallahi ba ni son auran da ake ko'karin ma'kala mini abinda yake zuciyata na gaya miki tunda kin matsanta ki ji kada ki d'auki maganata a matsayin dad'in baki a yanzu dai babu ajandar aure a tare budurwa ko bazawara kin san matsayin Malam D'aha a wajen mahaifina da ni kaina da irin gudumuwar da ya ba ni a rayuwa abu ne mai wahala na yi ja'in'ja akan wannan umarin nasa Amina
ba ni da mafita ne dole na gaya muku halin da ake ciki daga yau zuwa ko wane lokaci za ku iya jin labarin d'aurin aurena domin gidan Malam D'aha ba'a bida'a idan an d'aura aure yarinyar zan je kawai na d'auko."
Abin ya daki Hauwa k'warai da aniya ta zuba masa ido cikin k'aduwa tana fad'in." Aure da gaske za ka yi to kai yaro ne da za ka ce an ma'kala maka daman can kana so akwai wanda ya isa ya yi maka dole ne? ashe kana da lafiya ta mazantaka da kuzari irin na maza tunda har zaka iya 'karbar auran budurwa 'kan'kanuwar yarinya.
Ya 'kankance ido yana fad'in." Ba ni son hauka da rashin hankali Hauwa ki kiyaye ni wallahi kada ki sake ki fusata ni."
Ta ja tsaki ba ta sake cewa komai ba ta kad'a kanta ta kama hanyar fita.
Ya ja tsaki tare da sake juyowa gare ni yana fad'in." Ya za mu yi ne Amina ta ina kike ganin zan warware wannan mas'alar da na shiga.
Ajiyar zuciya na sauke a nutse na furta." To ai ni ban isa na hana umarinin Ubangiji ba. Na d'auka wata matsalar ce ta daban shiyasa ka ji na ce maka ka gaya mini zan baka shawara. Lamarin aure kuma ai yin Allah ne Amina bata da hurumi anan sai addu'a da fatan alheri."
Ya ri'ke hannuna sosai yana fad'in. " Kin amince a yi? kina ganin babu komai idan an yi din?"
Na gyara kaina gabana na dokawa na ce." Idan ma da matsala ai ban isa na sani ba tunda ni hallitar Allah ce a karan kaina ban san abinda zai same ni daga yanzu zuwa gobe ba kaga kuwa ba ni da abinda zan ce anan kamar yadda na fad'a da farko Allah Ya sanya alheri yasa abokiyar arzikinka ce. Wannan shine kawai addu'ar da zan yi."
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta.'' Ban za ci zan samu ha'din kanki cikin d'an'kankanin lokaci ba Amina. Lallai na yi sa'ar samun mace tagari mai ko'karin ganin ta samar mini da nutsuwa cikin kowane yanayi na gode sosai Allah Ya yi miki albarka."
A tak'aice na amsa da amin ina ta kallonsa ganin ya wartsake idan ma da ciwon kan to a kashi dari hamsin ya sauka sai abinda ba za a rasa ba.
A haka likitansa ya zo ya dudduba shi yana fad'in jininsa ya hau kad'an shine kuma ya haddasa masa tsananin ciwon kai da jirin da yake ji ya zama dole ya daina tsanantawa kansa damuwa.
Ya tashi ya fita minti talatin a tsakani ya dawo da magunguña a leda ya yi bayanin yadda ya kamata a ce an yi amfani da su daga yanzu. Ban sauka ba sai da na tabbatar da cewar ya ci abinci sosai sannan ya sha maganin a gabana tukkuna na yi masa sallama na sauka gwiwata kamar an rad'e da gora saboda mugun sanyin da jikina ya yi jin wannan batu......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*143*
Ni jin wannan batu gabad'aya ya kassara mini dukkanin karsashin jikina. Na yi shiru zuciyata na harbawa tare da tariyo maganganunsa akan auran da yake yi wa lak'abi dana cushe. Ba ni fargabar ya yi aure a gidan nan saboda na riga na san matsayina a zuciyarsa idan ma yana amfani da kalaman yaudare wajen nuna mini soyayya tabbas to akwaita a zuciyarsa ko da kuwa da akwai matsugunin wata. Matsalar dai anan 'kankanuwar yarinyar da zai auro ya kawota cikinmu shine tashin hankali tun lokacin da yake gaya mini zuciyata take hasaso mini Hajara ce domin kaf yaran da suke gidan Malam D'aha itace a samansu ba su kaita girma ba ita zamu kira da budurwa amma a rashinta domin yadda take a tsamure a tsuke sai uban tsayi bana tsammanin ta fara jinin al'ada.
Lallai wannan babban lamari ne da ya tunkaro mu gabad'aya domin idan har Allah Ya kaddara auran nan to sai da ya rainin yarinyar nan duk da matarsa ce ba zan yarda ya haye musu kan d'iya ta had'u da lalaruba. Malamai suna ta wa'azi kan cewa iyaye su daina irin wannan auran na cutarwa to da haka za mu kira shi ma a wannan zamanin domin dai muddin a fake da cewa sunnar manzon rahama ce yin haka to akan jefe yara cikin halin damuwa a gaba. Dalili zamanin Annabi Muhammadu S.a.w daban yake da wanda muke ciki a yanzu idan an fake da cewa za

Please Login or Register in order to submit comment