Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kada nan gaba a yi mini gori."
Ya yi shiru bai tanka mini ba can kuma ya ce." Yanzu za ki ba ni ha'kkina ko kuwa?"
Na ce." Wane hakki?" don har ga Allah ban zanci hakkin kwanciya yake nufi ba ."
Ya d'ora duka hannuwansa biyu saman kirjina yana fad'in." Wannan dai mallakina ne ke kan ki ba ki da karfin ikon da nake da shi a kansa. Idan na d'ora hannu a kai ki tankwa'be kina neman rahamar Allah kuwa?"
Ya fad'a yana dam'kar d'aya da k'arfi cikin mugunta gasu tubarkallq sun sake kumburi dalilin abinda nake d'auke dashi sun cika sosai.
Na sake tankwa'be hannun ina fad'in." Allah Ya hallice ni da abina a jiki ka ce ka fi ni iko da shi abincin yarana ne masu zuwa."
Ya kuwa gigice yana fad'in." Abincin mu dai, wallahi ba ki isa ba, abincinmu ne da ni da su."
Na juya da kaina gefe ya matso ni sosai yana yi mini magana. Na girgiza kaina tare da cewa." Ba zai yiwu ba sai Hauwa ta tafi ka yi hakuri ni tunda cikin nan ma ya tsufa na daina jin wani abu
Ya ce." Ni kuwa a cikinta nake koyaushe kin matse ni da yawa Amina ba kya gudun hakkina ya kama ki uhum! mu d'an yi soyayya kad'an kafin Hauwa ta shigo sai mu kwana tare kada ta ce ba a yi mata daidai ba."
Na ce." To bari kawai idan ta shigo sai ku yi soyayyar gabad'aya."
Ya sake rikicewa yana cewa." Ya ki ka tsara yanda zai kasance."
Na rasa da wane mizani zan auna maganarsa. Ya na tsara yanda zai kasance me yake nufi. Na gane kawai a rikice yake maganarma ya fad'e ta ne cikin rashin hayyaci.
Ina sane na 'kyale shi ya dinga abinda yake so ba don komai ba sai don na nuna mata cewa kowace mace da irin tata kissar. Gidana kuma ta zo sai abinda ta gani.
Wajan sha biyu da wani abu muka sauko kasan ni da shi bayan ya samu gamsuwa da abinda ya buk'ata. Yaran sun yi bacci duka a saman kujera tana zaune zuru da tibi a kunne duk ta muzanta ganin sakkowarmu ta yi kasa da kanta fuskata a had'e kamar ma kuka ta yi.
Na wuce d'akina ban tsaya a falon ba na ji yana cawa da ita." Tashi yaran su je su kwanta. Amina bude musu daya d'akin, shi Khalil ya zo mu kwana tare a d'akina."
Dakinsu Baba Tabawa da Yusra kenan anan suke kwana na bud'e kamar yadda ya buk'ata. Ita da shi suka fara tashin yaran. Na yi shigewata d'aki a raina ina fad'in." Ki zauna da ni a gida daya ki zama 'yar aikina Hauwa, zan kuma ga abinda gobe za ta haifar ni daku ne gabad'aya.
Na rufe kofa tare da cire kayan jiki na sanya na bacci na yi kwanciyata ban sake sanin wainar da suka toya ba ba. Da asuba gari ya d'an fara haske ina saman dadduma ya shigo ya jira na kammala muka shafa addu'a a tare. Na gaishe shi babu sakewa na ce." Zan je gidanmu idan an jima zan kuma tafi da yara."
Ya yi d'an jim kafin ya ce." Babu damuwa amma ya za a yi da abin kari kada su tashi a bacci ko."
Na ce." Za ka iya bayarwa a sayo abinda za su ci ba ni jin zan shiga kicin gaskiya wanka zan yi na shirya."
Ya ce." Wace banzar magana ce wannan Amina ni zan sayi abinci bayan ina da shi a gidana, ban yi wannan lalacewar ba."
A takaice na ce." To sai ka shiga kicin din ka yi da kanka kada dai ta shigar mini kicin."
Ya dinga kallona cike da takaici ya ce." Jiya ba na gaya miki cewa zan raba muku gidan ba me yasa kike da neman fitina ne Amina. Ya kamata duk abinda ki ke ji a ranki ki ajiye a gefe mu fahimci juna gabad'aya mu gyara kuskuranmu Hauwa bakuwa ce anan gidan."
Na ce." Bakuwarka dai ai ni ban gayyace ta ba."
Ya sake had'e rai yana fad'in." Kina yin abubuwan da suke nema su wuce gona da iri fa. Ko babu

Na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

dangantaka ta aure a tsakanina da yarinyar akwai dangantaka ta jini sannan uwar yarana ce kiyayyar ki a kanta ta tsananta."
"Humm kawai na ce tare da tashi na bar shi zaune bandaki na shiga. Koda na fito baya d'akin na yi tsaki cikin raina na fara shirya jikina zuciyata cike da abubuwa ma su yawa.
Wajan takwas na fito falon yaran sun shirya ko ita ta yi musu wanka oho suna zaune a falo gabad'aya har da Baban nasu ita tana kicin domin fitowata na ji kamshin k'wai na tashi raina ya baci sosai. amma sai na daure na cigaba da amsa gaisuwar da suke jero mini. Shi kuma ya zura mini ido da alamar na gaji da wannan abubuwan da suke faruwa. Kai tsaye kicin din na nufa na same ta tana soya dankali da k'wai ta d'ora ruwan tea yana ta k'amshi citta da kaninfari.
Na cika da mamakin karfin halinta. Kai tsaye gas din na kashe ta yi sakato tana kallona. Na furta." Ba ki da hurumin yi mini yadda ki ke so a gidana Hauwa ko ni na gayyato ki ne, me ya sa za ki shigo mini kicin har ki saki jiki kina soye-soye."
Ta d'an yi murmushi tana fad'in." Amina manya ai kya bari mu gaisa ko?"
Na ce." Dube ni nan Hauwa ba ni buk'atar gaisuwar na ce miki tambayarki nake dalilin da ya sanya ki shigo mini kicin."
Ta yi 'yar dariya cikin raini ta ce. " To Hajiya masu gida ki goya ki kai gidanku."
Ta ajiye cokalin hannunta ta kama hanyar fita zalo-zalo na ce." Sakarai kawai."
Ta juyo a fusace tana cewa." Amina ai ba a sakarai d'aya sai dai sakarkaru biyu."
Na ce." Hakane da ke da ta Bauchi ko?"
Ta zura mini ido da matsanancin mamaki tasan dai inna Uwani nake nufi
Sai ta rushe da kuka mai karfi." Amina ni ke zagi, inna Uwani ce sakarai mahaifiyata." Ta fadi maganar a daidai lokacin da ya shigo kicin din ta dinga wani irin kuka hawaye na kasa tsere a kumatunta.
Yana tambayarta ta yi shiru ta kasa magana ta jingina jikin wardrobe. Can ya juyo kaina ganin yadda fuskata take ya sanya shi fad'in." Me ya faru ke ba kya jin magana da rarrashi ko?"
Na ce." Ni na ce Hauwa ta zo gidana?" Na katse shi ta hanyar yi masa wannan tambayar.
Ya ce." Gidanki ne ko nawa?"
"Gidanka ne amma kaima na fi ka iko dashi wallahi duk zan iya da ku."
Ya gyad'a kansa kamar zai rushe da ihu ya ja hannunta suka fita bata sake tanka mini ba tunda ya shigo sai ta yi shiru kawai tana kuka. Wai na goya gidan na kai shi gidanmu. Magana ta gaya mini a fakaice ashe babu dadi. Ita da uwarta duka sakarkaru ne na fad'in su yi yadda za su yi da ni.
Na same su gabad'aya har yaran sun tsuru-tsuru na wuce daki ban sake kallonsu ba.
Muna waya da Usaini ya shigo da wani irin b'acin rai a tare da shi ya cire wayar daga kunnena ya sanya a aljihunsa. Na zuba masa ido babu fargaba domin nasan ta gaya masa na ce da mahaifiyarta sakarya.

"Tunda ki ka iya zagin Inna Uwani Amina za ki iya zagin mahaifiyata yanzu kin kyauta kenan abinda ki ka yi daidai ne mace ta zo gidanki ki yi mata irin wannan cin zarafin iyaye fa aka ce miki duk iyashegen da ki ke ji da shi ina fa da yadda zan yi a kanki na kyale ki ne ganin kina da juna biyu ba ni tsoron kowa mace ni nan da ki ka gan ni sai mahaifiyata."
Ya fad'i maganar kamar gaske da 'kumaji har da zare mini ido. A raina na ce a banza ai ba zaka iya fad'an ba Alhaji.
Na dube shi sosai tare da fad'in." Da farko daka tambaye ni maganar abin kari ban munafurceka ba na ce a a ba zan yi ba, akwai masu yin abinci a gari ka bada kudi a sayo musu mai yasa za ka ce ta shige mini kicin ko ajiya ta yi mini ne?"
Ya rasa abinda zai ce mini can kuma ya gyad'a kansa yana fad'in." Tunda kuke rashin hankalinku ban ta'ba jin lokacin da Hauwa ta zagi wani naki ba abin ya wuce kaina ya tsallaka iyaye kuma duk lalacewar inna Uwani ai idan da mutunci da sanin daraja uwace a wajenki."
Na ce." Tunda haka ta gaya maka na zage ta mu tafi a haka kawai idan kalmar sakarai ce zagi to zan sake maimaitawa ai iyaye ba su fi iyaye ba."
Jikinsa ya yi sanyi sosai ya juya ya fita bai sake yin wata magana ba.
Na d'auki kusan minti ashirin kafin na fito cikin shiri na same su still a falon suna shan tea har da bread tare da dankalin da ta soya musu. Minal ta ta so a guje ta rike ni tunda ta ga alamar fita zan yi. Twins din suka biyota.
Ba ni son d'aukar musu yarinya nawa biyu kadai zan yi gaba da su ba kuma zan dawo cikin gidan ba muddin Hauwa na cikinsa.
Ya yi mana shiru bai ce komai ba.
Na ce da Minal din ta je ta d'auko mini bread din da take ci. Wayo na yi mata ta kuwa juya baya da sauri nan na ri'ke hannun Usai Hassana ta biyo bayana muka fita na ja kofar da k'arfi daidai lokacin da na ji ta fasa ihu da karfin gaske.
Ayuba ya fito da mota muna ko'karin shiga ya fito da yarinyar ta yi wurjajan da kuka da majina yana goge mata da tissue.
Kamar kurma ya saka ta a cikin mota kusa da 'yan uwanta ya juya bai ce mini komai ba. Sai da na shiga motar tukkuna na tuna da wayata a hannunsa na ce Hassana ta je ta kar'bo mini jim kad'an sai ga ta da wayar a hannunta, ta shigo ta zauna suna cike da murna za su fita Ayuba ya ja motar muka fita daga gate din gidan.
Ashiru k'aramin kaninmu yana ko'karin bud'e kwantenarsa ya tsaya yana kallon fitowarmu daga mota da yake har kofar gida Ayuba ya ajiyemu
Ya taho daa sauri kuwa yana washe baki "anti Amina sannu da zuwa."
Na amsa a tak'aice ina bawa Ayuba amsa yana tambayata da kamar k'arfe nawa zai dawo ya dauke ni na ce." Ya bari zan kira shi tukkuna.
Muka nufi gidan tare da shi yana ri'ke da hannun Usaina yana fad'in." Anti sun girma sosai ban taba ganinsu ba sai a hoto."
Na ce." Kai ma ai ka girma Ashiru ka zama saurayi ina rigimar abincin hantsi.?"
Da yake yana yaro dan rigima ne idan an sha koko da safe wajan goma zai dasa rigima abinci ka'ida ne ko ba a ajiyewa kowa dumame ba shi sai an ajiye masa idan ma ba su dashi ni nake bashi ko na yi masa sabo. Idan sun dawo daga makarantar allo ba a gama na rana ba ya yi ta kuka har sai an sauke na rana sannan gidan za a samu lafiya.
Ya yi ta dariya kuwa domin ko ya mance wasu abubuwan da ya dinga yi tabbas ba zai mance wasu ba. Ya bude mini kwantenar tasa cike da kayan masarufi awo ne kadai ba ya yi ina ta dubawa ina jin dadi ganin yadda yaro ya zama manemi shi bai yi fitinar su Kamalu da Saminu ba sai da kukan kuruciya. Na ce." Aikuwa ni ma zan sanya hannuna a ciki Ashiru ya kamata a ce harkar nan an fad'ad'ata."
Ya dinga washe baki yana fad'in." Wallahi kuwa anti Amina Babanmu ne ya fara ba ni dubu dari da hamsin na fara a hankali a hankali Yayanmu Usaini ya sake ba ni dubu dari." Na ce." Ya yi daidai Hakan ni ma zan bada gudumuwata in sha Allahu."
Muka shiga ciki shiru Ina ta sallama. Can Ummansu ta amsa ya ce." Ummansu Hadiza wata'kila bacci take yi domin kwana biyu ta yi fama da mura da zazza'bi.
Ta dago labule ganina sai ta kama dariya. Na sauke ajiyar zuciya ganin yadda ta marabceta ni dama ina ta tararrabin kada ta kawo mana tangard'a a cikin lamarin nan amma yanzu yadda na hangi sukuni da annashuwa a fuskarta ya sanya na kori shakkun da nake yi. Ta fara fadin." Maraba lale Hajiya Amina sannu da zuwa ashe tare kike tafe da yaran bakid'aya yanzu nan mutumin naki ya fita kasuwa amma ya ce idan ya gama d'aure wasu kayan da zai tura Ghana zai dawo ."
Na ce." Allah sarki babu damuwa dama ai zuwan na ki ne bari na shiga mu gaisa da Ummansu Hadiza na fito."
Tana cike da matsanancin farinciki ta ce." To shikkenan."

Na same ta a kwance a katifa shiru kamar ta rushe da ihu domin yanayin fuskata kadai ka duba za ka gane a cikin damuwa da take da b'acin rai.
Ta tashi zaune tana yar dariya "Amina maraba lale marhabun ai jiya babanku yake gaya mana kina tafe maraba." Ta sake fad'in haka tana janyo hannun Usaina tana cewa." Biyu sun girma sun zama 'yan mata."
Na zauna saman daddumar da ta shimfida mini ita kuma ta janyo yaran suka hau katifar da take zaune suna jereran gaisheta. Ta dubi Minal tana cewa " 'Kanwarsu ce wanann ko don na ga hangi kama."
Na ce." Eh mai sunana ba Amina ce muna kiranta da Minal."
Ta ce." Ma sha Allah duka gasunan sun yi wayo sosai wallahi."
Na yi murmushi ina nazartata ta d'an rame gaskiya ba kamar lokacin da suka je gaisuwar Hajiya Maryam ba ramar da ta yi yanzu ta fi muni domin kallo daya na yi mata da na shigo na tabbatar da cewa." depression yana damunta.......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700...0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*155*
Ta ba ni tausayi sosai to ya za a yi ne shiyasa ake fad'in idan kasan farkon ka baka san karshenka ba. Kuma duk wanda ya shuka alheri shi zai gani kuma idan sharri ma ka shuka to tabbas shi za ka girba da wayo na ba zan manta da irin azabar da matar nan ta gana mini ba. Na ci wahala ainun a hannunta wankin yaranta ni ce girki da cefane shara da wanke-wanke duk ni ce ba ni da sabulun wanka a gidan balle na wanki haka za ta tura Hadiza gidan kisto da kudi a yi mata ni nawa kan ya yi sama da sati hud'u ban tsefe ba idan zan ari kibiya a wajenta na dinga ra'be-ra'be kenan har sai da Gwaggo ta fahimta. Wando pant da siket kuwa sai da ya kasance biyu gare ni duk sun yayyage haka nake sanyawa a jikina nan ma gwaggon ta ankara ta sayo mini ita da Yaya Aminu da Sahura sun taimaka mini k'warai a wancan lokacin. Na yi girki da hannuna ta zo ta raba ta cikawa yaranta kwano ni ta bar mini 'kasan tunkuya duk ranar da ta tauna tsakuwa a shinkafa kuwa ina shan zagi a gidan. Sai da Ummansu Saminu ta zo gidan na fara samun sau'ki amma zahiri Ummansu Hadiza ta wahalar da rayuwata babu abinda yake bibiyarta sai hakki.
Ta dinga kuka haka kawai tana kallona na yi na yi da ita ta yi shiru ta yi mini bayanin abinda yake damunta da kyar cikin dashewar murya ta furta."Hankalina ya'ki kwanciya Amina kullum Hadiza tana raina da wannan zaman da take a wannan waje gwara su yanke mata hukuncin ta san matsayinta, ni ma hankalina zai fi kwanciya. Da yawa mutane sai su dinga fad'in na kwantar da hankalina wallahi ba zan iya ba domin ko bacci bana iya yi sai ciwon kai."
Na ce." Ai ha'kuri da tawakalli ya zama dole Umma ki bar wa Allah lamarinsa domin Ubangiji yana so ya jarrabeka ka yi hakuri ki dinga yi mata addu'a idan da rabon za ta fito ta sake wata rayuwar sai ki ga dalilin wani lamari ta fito mun cigaba da rayuwa tare. Idan kin tsananta ciwo zai iya kama ki, kuma yana da kyau mu sake komawa asibiti tunda kin ce kina fama da ciwon kai."
Ta gyad'a kanta tana fad'in." Shine abinda ya fi damuna yanzu."
Na ce." To shikkenan in sha Allahu da kaina ma zan kai ki asibitin."
Ta ce." Na gode sosai Amina."
Shiru ya d'an ratsa wurin na dubi agogon da yake daure a hannuna sha daya saura na yun'kura da kyar na tashi sai a lokacin ta lura da cikin jikina ta ce." Ashe da sai dai mu ji haihuwa Amina haka ki ka yi nauyi."
Yar dariya na yi kawai dama sai mai kurrula ne zai gane akwai ciki a jikina dalili duk ya bi kirjina daga 'kasa ya sake bud'e ni na yi fadi sosai sai dai yayi mini mugun nauyi a mara sosai.
Ta ce."Allah Ya sauke lafiya." Na amsa da Amin a takaice. Hanyar fita na kama ina fad'in" Bari na shiga wajan Ummansu Saminu. " Ta yi shiru ba ta ce komai ba yaran suka biyo bayana na ji tana fad'in." Ba za ku zauna anan ba."
Babu wanda ya waiwayeta suka biyo ni. Ummansu Saminu na zaune cikin annashuwa har da sanya sabon d'inki ta cokala d'aurin d'ankwali tana tauna cigum cike da nishadi. Mamaki ya kama ni kamar an fara hidimar bikin ita tun yau ta fara kwalliya kenan. Na zauna ina nazarinta dama d'akin gabad'aya
Rumfarta makad'e da kafet mai taushi da sabbin labulaye da sabon agogon bango sakamakon na Ummansu Hadiza da ba a sabunta shi da komai ba. Wala'ala ita ta yi gyaranta ko kuma shi Usainin ya yi mata saboda taron bikin da zai gudana. Jikina ya yi sanyi sosai wato ita duniyar nan juyawa take yi amma kuma ga dukkanin alamu zaman ha'kuri Ummansu Hadiza take yi a gidan alamu sun nuna Ummansu Saminu itace mai hutawa dalilin yaranta duka maza ne kuma sun tashi suna nema ita kuma Ummansu Hadiza ga yadda rayuwa ta juya mata shiyasa ake so mutum ya shuka alheri domin ba a san inda rayuwa za ta juya ba. Ban yarda mun yi wata magana da ta shafi abinda ya kawo ni ba sai da na kira Ummansu Hadiza domin kada abin ya yi mata yawa kuma lallai idan Usaini ne ya yi wa mahaifiyarsa wannan gyaran bai had'a da Ummansu Hadiza ba to bai kyauta ba. Gabad'aya ma gidan zan sanya a yi masa fenti da sabon simitin tsakargida a canza musu kofofi da tagogi dole ne abin ya yi mata yawa ta auri zaman d'aki kunci da damuwar yadda rayuwa ta juya mata ya janyo mata ciwon kai.
Ta kuwa ji dadin yadda na sanyota cikin lamarin hakan ya nuna mini cewa Ummansu Saminu iyakarta take nuna mata akan sabgar.
Ban yadda na gaya musu ga yadda al'amarin ya kasance har auran ya juya kan Usaini ba bayanin da na yi Babanmu haka suma na yi musu cewa yarinyar a can k'auyensu mijina take wato bunkure kuma na je naga gidansu da mahaifinta fitaccen malamin addinin musulunci ne.
Ummansu Hadiza ta saki jikinta sosai muna ta hira yayin da ita kuma Ummansu Saminu na fahimci hakan bai yi mata dadi ba sai ma ta tashi tana fad'in bari ta d'ora abinci.
Ta shigo bayan fitarta da kamar minti goma tana fad'in." Hadari ne a garin nan fa wata'kila yau mu samu ruwa." Ummansu Hadiza da sauri ta ce." Allah Ya sa ai kwana biyu mun sha zafi."
Ta share ta ba tace komai ba ta d'auki wani dan bokiti ta fita. Na dube ta a sanyaye sai ta ba ni tausayi kad'an wato abinda ta yi wa Mamanmu a can baya ne yanzu take ganin sakamako.
Ban ji dadin irin wannan zaman da suke yi ba ai na d'auka sun girma masu yi wa wasu fad'a ne ni kaina abinda yake faruwa tsakanina da Hauwa baya yi mini dadi ko kad'an don dai babu yadda zan yi ne, amma babu abinda ya fi zaman lafiya dad'i Ubangiji Allah ka ba mu ikon zama da kowa lafiya kada mu cutar da wani domin shi sharri d'an aike ne.
Hadarin ya taso sosai iska ta fara tashi garin ya turnuke farkon damuna muke ciki ga dukkanin alamu za a samu ruwan sama da wuri
Yaran suna tsakargida suna wasa sun samu sake da yake tsakargidanmu akwai yalwa na ji Ummansu Saminu tana fad'in." Ina Gambon taku take ne ko dai ta fita."
Ummansu Hadiza ta leka tsakargidan daidai lokacin da Usaina take k'walawa Minal kira bata gidan da gaske fita ta yi gabad'aya ba mu ankara ba, suma yaran da suke wasa tare ba su lura da lokacin da fice ba.

Na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Na tashi da kiran sunan Allah gabana na fad'uwa hijab dina na zura dalili na cire shi jin abinda jikina ya kasa d'auka zafi sosai da kyaikyayin jiki ban sani ba ko dan na jima ina rayuwa cikin ac ne oho amma dai yau yini guda duk na burkice dalilin hadarin da ya had'o da kuma zafin da ake tsugawa.
Muka fita tare da Ummansu Hadiza ma'kota ta dinga shishshiga ni kuma na fara duba yara da suke wasa a layin ban hangi rigar Minal ba.
Kafafuna suka dinga kyarma. Ashiru ya rufe kwantena ya bazama.
Kasa cire kafata na yi na koma soro na tsaya ina kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Twins kuwa da suka fahimci Minal 'bata ta yi sai kuka Hassana tana fad'in." Kuma bata da lafiya ko Usai."
Ta daga kanta tare da zura yatsa a baki tana tsotsa hawaye na fita.
Na sake karyewa k'warai da gaske tsautsayi ne ya sanya ni taho da yarinyar nan, na tabbatar da cewa idan ba a ganta ba daga nan zuwa dare ubanta da uwarta dole su ji a wannan ga'bar da muke ciki da ni da su na rashin samun daidaito bai zama lallai su yi mini uzuri cewa tsautsayi ne ba. Za a ce me yasa nawa yaran ban sake sun fita sun shiga lungunan da ba su sani ba sun 'bace.
Ina nan tsaye cikin tararrabi kimanin minti ashirin Ummansu Hadiza ta dawo daga yawon shiga makota babu Minal babu dalilinta
Muka koma cikin gidan jikina a mace k'warai da gaske Ummansu Saminu ta sauke abinci ta ce." Ya kamata ki sanar da babanta Hajiya Amina."
Na zauna saman turmi a nutse ina fad'in." Bari mu jira dawowar Ashiru ba ni tsammanin yarinyar nan nisa ta yi. Ina rufe baki kuwa sai muka ji kukanta daga soro na tashi tsaye da sauri.
Ashiru ya shigo da ita a hannunsa ta yi wujiga-wujiga ta ci kuka ta k'oshi har da tabon fad'uwa a goshinta da alamun jini kad'an
Na kar'beta da sauri ina dudduba jikinta gabana na ta fad'uwa ta ri'ke ni tamau tana shasheka ina jin Ummansu Hadiza na tambayarsa a Ina ya same ta ya ce tsallaken titi wani mutum yana yawo da ita a hannu zai nausa da ita titin tudun yola
Na zaunar da ita tare da cire mara riga jikinta da zullumi da fargaba na tube mata wando pant na duba gabanta alhamdulillahi babu wata alama.
Ummansu Saminu ta juye ruwan da yake cikin fulas din shayi na surka na yi mata wanka ta zuba musu abinci suka ci cikin rashin dad'i ta b'ingire ta kama bacci. Na kasa cin komai saboda tashin hankali tabon da yake goshinta shine ya fi d'aga mini hankali kuma har yanzu zabura take yi. alamun a tsorace take har yanzu.
Sai da na yi sallar la'asar tukkuna na ci abincin dafuduka ta shinkafa har da kifi da ruwan pure water. Na d'auki wayata domin kiran Ayuba ya zo ya d'auke mu na mayar musu da 'yar su. Ina laluben lambar direban shi kuma ya kira hannuna ya shiga rawa na daga ban iya cewa komai ba saboda tashin hankali sai nake ganin wata'kila labari ya riske shi abinda zuciyata take raya mini kenan duk da cewar yarinyar ba a san 'yarsa ba ce amma zuciyata ta

Please Login or Register in order to submit comment