Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta da rigan jikinta sanyi take ji shi ya sa duk tsigan jikinta ya tashi ga shi jikin na ta ya ɗau zafi amma Habib bai lura da wannan ba. Haka ya iza ta zuwa cikin bedroom ɗin su ya mora jikin Ummu fiye da yadda ya saba mora tana ji ana ta sallar isha'i a masallatan kusa da su amma Habib bai saurara mata ba, ta gaji ba za ta iya ba amma bai fahimta ba, lamarin na shi babu tausayi da ya kawo kamar zai sauka sai ya koma tun Ummu na kuka a ɓoye har ta dawo tana yi a sarari babu in da jikinta ba ya rawa, sai ta ji kamar ba Habib ba sai ta ji yau ba ta ji daɗin abin ba kwata kwata ta ji wani haushi na sukan zuciyarta amma bai saurara mata ba sai da ya gaji domin kan shi ya kuma tsallake ta ya shiga tiolet domin tsarkake kan shi.

Kanta ta tusa cikin bargo tana kuka amma  ta rufe bakin ta kar ya yi sauti, tana jin shi ya fito yana ce mata ta tashi ta yi wanka su ci abinci yana jin yunwa, ko tsayawa bi ta kanta bai yi ba ya fice ya bar ta nan kwance tana kuka. Da kyar ta iya rarrafawa ta shiga tiolet mene ne ya sa Habib ya yi mata haka! Ko yana so da karfin tsiya sai ya yi ajalin cikin jikin ta ne, Allah ya fi shi domin tun da ta gano manufarsa ta ke saka shi cikin addu'o'in ta na Allah ya tsare ta ita da cikin ta daga sharrin Habib, amma me ya sa har yanzu ba ta daina jin ta daina son Habib ba, tana son shi tana son cikin jikinta sannan tana son auransu shi ya sa yau ɗin ma ta kasa yi masa gaddama.

Jikinta zazzaɓi ne rau haka ta rarrafa ta fito ta sauya kaya ga shi kanta ya jike kuma ciwo yake yi mata ba ta ko samu damar busar da shi ba Habib ya zo ya dame ta da cewa yana jin yunwa haka ta fita daga ita sai wata riga doguwa ta wani yadin material ita ce a farkon wardrope shi ya sa ta saka ta. saman dinning suka zauna ta yi serving ɗin shi ganin ita ba ta saka ma kanta ba ya sa ya tambayeta a sanyaye ta ce ba ta ci ko ta ci sai ta yi amai.
Sai ya ɗauko mata balangun da ya siyo ya ce ta ci ko kaɗan ne.

"Ba zan iya ci ba."

Ta faɗa a sanyaye ajiye spoon ɗin hannun shi ya yi yana kallon ta hannunta guda ɗaya ya kama yana faɗin" Sannu Sorry ki ci ko kaɗan ne sai ki sha wannan lemun in sha Allahu ba zaki yi Amai ba"
Tana cewa ba za ta ci ba yana ɗaukowa ya nufi bakinta da shi tana kauda kai amma sai da ya saka mata shi a cikin bakin ta da ta tauna sai ta ji daɗin shi, shi ya sa sai ta sake ɗauka ta kai bakinta tana taunawa lokaci ɗaya tana kallon shi.

"Kin gani, ba za ki yi amai ba"

Ya faɗa yana yi mata mirmishi, yake ta yi masa ba ta yi mgana ba, abin da ya ba ta mamaki da ya sa ta sake jin a ran ta cewa Habib ba shi da gaskiya, lemun exotic guda biyu ya siyo da zai tsiyaya mata na ta dabam ne, na shi ma na dabam sai ta fara tunanin tunda sha za su yi me ya sa sai ya buɗe har guda biyu, kawai sai ta ji ba ta aminta da cewa Habib ba yana wannan abin don Allah ba ne. Yana yi ne ba domin komai ba sai domin cimma manufar da ya so ta biye mishi ya aiwatar. Ita kuma ta shirya masa da sanin ta ba za ta taɓa bari ya yi galaba akan ta ba.

Guda huɗu ta ci balangun sai ta cire hannunta da sauri ya kalle ta." Kin ƙoshi kenan?
Sai ta jinjina masa kai, da sauri ya miƙo mata lemun da ya saka kofin tangaran yana faɗin" Sha wannan sai naman ya kwanta miki yadda ba za ki yi amai ba."

Kallon shi ta ke yi kafin ta ce ta ƙoshi.

"Sha mana."

Ya sake faɗa yana tura mata kofin a bakinta da sauri ta kauda kai, maimakon Habib ya bar ta haka sai ga shi har yana miƙewa ƙoƙarin sa ya tura mata wannan lemun na dole sai ta sha ganin haka kawai ya ba ta tabbacin koma mene ne yana cikin wannan lemun na hannun Habib.

Ganin ta yi Habib na neman yi mata ɗure, tunda ya tashi daga zaune ya matso kusa da ita, ya rike kanta yana tura mata kofin zuwa bakin ta yana faɗin ta sha.

"Ki sha mana."

Ya faɗa yana kallonta.

"Na ƙoshi, zan yi amai in na sha."

Ran shi ya fara ɓaci ko ta fahimci akwai wani abu a cikin lemun ne

" Ki sha na ce miki ba za ki yi Amai ba."

"Ba na so na sha."

Ummu ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙokarin miƙewa zaune shi kuma bai sani ba ya kawo hannun shi sai ta kaɓe kofin da lemun suka tarwatse a saman dinning ɗin.
Jikin Ummu na rawa take kallon shi, shi kuma lemun da fashasshan kofin ya ke bi da kallo ran shi na ɓaci.

"Ka yi haƙuri."

Bai ce mata komai ba ya wuce kitchen ya sake ɗauko wani kofin ya zuba mata yana faɗin" Wannan ki sha, ki sha na ce Ummu Salma kafin ki ɓata mini rai."
Ai kafin ya nufota ta bar wajen Dinning ɗin zuwa falo sai ya yi tsaye da lemu a hannun shi yana kallon ta.

"Ke me ye haka?

Ya faɗa ganin Ummu ta nufi bakin ƙofa ta tsaya.

"Dawo nan malama."

Ya faɗa yana takowa tsakiyar falon.
Ummu ta sake matsawa jikin kofa ta saka hannu ta murza key ɗin ta buɗe ƙofar lokaci ɗaya tana faɗin" Na ce ba zan sha ba dole ne."
"Dole ne, dole ki sha wannan lemun domin cikin jikin ki ya zube."
Ya faɗa cikin tsawa har yana zare mata idanuwansa

Da man ta san za a rina hawaye suka kece mata cikin rauni ta ce" Me ya sa Habib? Wai me ya sa kake son raba ni da gudun jinina ne?
"Saboda bana so ki haihu. Ban shirya hakan tare da ke ba."
"To me ya sa?
Ummu ta katse shi a tsawa ce da karfi sai kawai ya tsaya yana kallonta ga ƙofa a buɗe kar saboda hayaniyarta ta tara musu jama'a da ya shiga uku.

"Ki dawo cikin falo mu yi mgana."

Ya faɗa yana ɗan kwantar da murya har lokacin kuma lemun na hanmun shi dama yake so ya samu ya yi mata ɗuren shi chemist ɗin da ya siya mganin mai wajen ya ba shi tabbacin in ya saka mata guda biyu a cikin lemu ya tabbatar ta sha ko kaɗan ne cikin nan ba zai kwana ba zai zube, hankalin shi da natsuwar kawai yanzu ya ga cikin nan ya zube, idanuwansa sun rufe kawai cikar burin sa ya ke nema ko ta halin ƙaƙa ne.

"Ummu-Salma ki rufe ƙofar nan ki dawo nan ki zauna ki karɓi lemun nan ki sha tun kafin raina ya ɓaci."

Ya faɗa yana kallonta ita ko sai ta sake matsawa kamar za ta fita tana faɗin" Wallahi ba zan sha ba, kuma kana cewa za ka matso ni zan fita na yi maka ihu."

Ta faɗa cikin kuka yadda ta yi ɗin ya san za ta aikata haka, shi kuma ba zai so mutane su taru akan sa ba, kowa ya ji ga abin da ke faruwa za a ba ma rashin gaskiya.
Kansa ya dafe da hannu ɗaya da yake jin yana sara masa lemun ya koma ya ajiye a saman dinning sannan ya dawo tsakiyar falon yana faɗin.

"Ki dawo nan mu yi mgana "

"Ba zan dawo ba,"

Ummu ta mayar masa da amsa  da iya gaskiyan ta domin tana da tabbacin in har ta bari Habib ya kama ta to ba cikin jikinta ba har ita zai iya yi ma lahani tun da alamomin sa sun nuna duka abin da ya faɗa gaskiya ne.
Ba ya son ta sannan ba ya son haɗa zuru'a da ita, ya faɗa ya kuma nuna shi a aikace kamar yadda yake nunawa yanzu.

Habib ya fara rasa control ɗin shi, ya nufi Ummu da sauri ita kuma ta fita waje ya fito sai ga megidan flat ɗin gefen su, yadda ya gan su kamar zakaru ne ya sa ya ɗan tsaya ganin shi ya sa Habib ya yi saurin wayancewa da cewa" Baby mu yi wasan a ɗaki mana kin ga nan saboda dare"
Jin haka yasa magidanci ya yi mirmishi ya wuce yana shigewa shashen shi Habib ya kalli Ummu cikin tsana da baƙin ciki ya ce.

"Ke wata irin daƙiƙiya ce, komai sai an yi miki bayani ne za ki gane?

Ya faɗa a fusace har jijiyon kansa sun miƙe saboda yanayin da ya ke ciki.

"Sau nawa zan faɗa bana son ki, ba kuma don ki haihu na auro ki ba."

Ya faɗa yana yarfa hannnuwansa yarinyar nan tana so ta bashi matsala tana so ta rusa duka shirin sa.

"To in ba ka sona ba ka son ka haihu da ni me ya sa ka aure ni.? Sannan me ya sa ka yi mini ciki? Ai ka san ba ni na ba ma kaina cikin ba."

Ummu ta sake tambayan shi cikin kuka hawaye na kece mata

Kallon ta ya yi, tabbas ya yarda ita daƙiƙiiya ce sai ya yi mata bayani? Sai ya furta mata dalilin da ya sa ya aureta sannan za ta gane lalle ya yarda dakikiya ce Ummu ba ta da lissafi.

Tsaki ya ja kafin ya ce" Lalle na yarda rashin ilimin boko mai zurfi ya cuce ki, tunda har yanzu tunanin ki bai faɗa miki dalilin da ya sa na aure ki ba."

Yana gama faɗin haka ya juya ya koma cikin ɗaki, ya bar Ummu na tsiyayan hawaye.
Hamma Kabiru da Hamma Abdulrrahaman sun sha nuna mata akwai ranar da za a iya goran ta mata rashin karatun ta mai zurfi a bangaren boko, ɗauka ta ke yi suna faɗa ne saboda ta yi zuciya ta ce za ta yi, sai yau da Habib ya goran ta mata ta sake aminta da maganar su, sai dai har a lokacin ba ta yi nadamar haka ba, ba ta son karatu har kuma gobe ba ta so iya sakandirin da ta gama ya ishe ta zaman duniya tunda tana da na muhammadiyan fiye da yadda ta samu na bokon, Hamma Saddam ya taɓa faɗa mata wata rana tana ji tana gani za a yi mata gorin ilimi sai ga shi yau Habib ya yi mata, hawaye ke kwaranyo mata ga jikinta ya sake ɗaukan zafi saboda sanyin da ta sha, tana son komawa ciki amma tana tsoron ka da Habib ya shirya mata wani gadan zaren, ba ta koma ciki ba sai da ta tabbatar da ba shi a falon sannan ta lallaɓa ta shige ɗakin ta ta rufe ta kwanta a saman gado ta fashe da kuka.

"Wayyo ni Ummu-Salma Ubangiji ka kawo mini agaji"

Ta faɗa a fili tana mai dafe kanta da ta ji yana sara mata, me ya kamata ta yi? Zama tare da Habib yana neman yi mata illa da karfin cin tuwo ba nata ba ne, ya kamata ta sanar da wani abin da ke faruwa. Ta daɗe kwance tana kuka amma ta rasa mafita, kunya ta ke ji da nauyi yadda kowa a dangi da ƙawaye suke yi mata kallon wacce ta yi dacen miji yanzu kuma ta je da wannan mganar? Amma in ba ta faɗa ba akwai yuyuwar ko ta ƙarfin tsiya sai Habib ya cimma burin sa na raba ta da cikin nan ita kuma ba za ta bar shi ya cika wannan burin ba, har ta rarrafa ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ba ta samu mafita ba tana salla tana kuka bayan ta idar ta ɗaga hannu sama tana roƙon Allah ya tsare ta daga sharrin Habib ya kuma tsare cikin jikin ta.

Haushin kanta take ji da har a lokacin ba ta ji ko da son Habib ya ragu daga cikin zuciyarta ba, sai ma ta ji kamar ana ƙara hura wutar ƙaunar sa ne a cikin zuciyanta. A saman darduman da ta yi sallan ta kwana cikin matsanan cin ciwon jiki da kai, sanna ga zazzaɓi mai zafi sallar asuba ma sai da safe lokacin akwai hasken rana sannan ta samu damar yi,  shima a zaune saboda jiri take gani in da ta idar nan ta sake sulalewa ta kwanta numfashinta na sarƙewa ga zafin zazzaɓi kamar za ta mutu, ganin ta yi in ta cigaba da zama a cikin ɗaki za ta iya mutuwa Habib ba shi da asara ya sa ta rarrafa zuwa saman drowers ɗin gefen gadon ta lalubo wayarta Ummin ikki take da niyar kira amma dishi dishi ta ke gani tsabar zafin zazzaɓi.

Wayar na hannunta kira ya shigo ba ta iya gane sunan saboda yanayin da ta ke ciki ta samu dai ta yi ƙarfin halin ɗaga kiran sai ta ji muryan Baɗɗo.

"Sisna gani a ƙofar bangaren ki, ina ta knooking shuru ko bakwa nan ne?

Jin muryan Baɗɗo da abin da ta ce ne ya sa ta ji kamar an buɗe mata idanuwanta wani karfi ta ji ya zo mata da ya sa muryatan a dishe ta ce.

"Ga ni nan zuwa."

Sai ta sauke wayar a saman gado da taimakon gadon ta iya miƙewa tsaye tana dafa bango har ta buɗe kofar Bedroom ɗin ta fita falo tana dafe da bango, ƙofar ma a buɗe take Habib ya fita ita kuma ba ta san ma fitan shi ba, ballatana ta taso ta rufe.
Ita kuma Baɗɗo ba ta murɗa handel ɗin ba a tunanin ta ƙofar na rufe ne kamar yadda Ummu ta saba rufewa sai an yi knooking take zuwa ta buɗe ma wanda ya zo.

Tana buɗe ƙofar suka yi arba da Baɗɗo wacce sai da ta tsorata da ganin yadda Ummu Salma ta koma.

"Ummu lafiya.?

Ta faɗa cikin fizgo mganar, ita kuma Ummu jiri ya kwashe ta sai kawai ta faɗa ma Baɗɗo a jiki, da sai da ta saka ƙarfi ta iya riƙe ta suka shiga cikin falon da kafa ta rufe ƙofar lokaci ɗaya tana sake faɗin.

"Innalillahi Ummu lafiya?

Ba ta amsa mata saboda shaƙan turaran Baɗɗo da ta yi ya ta yar mata da zuciya Amai ta ji yana taso mata shi ya sa ta sake ta, da dafe bango ta isa tiolet ɗin falon nan ta fara kwara Amai, a su kwane Baɗɗo ta bita har ciki ta riƙe ta, tana yi mata sannu aman ba komai sai ruwa ruwa sai naman da ta ci jiya da daddare, a galabai ce ta gama aman Baɗɗo ce ma ta taimaka mata ta wanke bakin sannan ta kama ta suka dawo falo.

Ummu a kan kujera ta zube ta na mayar da numfashi Baɗɗo ta zauna gefen ta tana faɗin.

"Subhanalla  jikin ki ya yi zafi ne haka ne Ummu? Habib ya fita ne?

Shuru ta yi ba ta yi mgana ba tana ma yar da numfashi kawai sai Baɗɗo ta jawo jakarta ta fiddo wayarta lokaci ɗaya tana faɗin.

"Bari na kira shi ko asibiti sai mu je amma barin ki a gida ke kaɗai a yanayin ki ai akwai matsala Sisna."

Da sauri Ummu ta riƙe hannun Baɗɗo cikin mamaki ta kalle ta sai ta hau girgiza mata kai.

"Wai kar na kira Habib ɗin?

Baɗɗo ta tambaya cikin mamaki.

Sai Ummu ta gyaɗa mata kai tana mai lumshe idanuwanta sai ga hawaye ta gefe da gefen kumatun ta.

"Sabo da mene ne! Ko ba ya garin ne?

Baɗɗo ta sake tambaya cikin mamaki.

"Baɗɗo."

Ummu ta kira ta a raunane ta amsa da sauri.

" Naam."

"Ina da ciki."

Ta faɗa tana numfashi da sauri da sauri.

Sai Baɗɗo ta washe baki kafin ta ce" Da man a yadda na gan ki na yi tunanin cikin ne. Congratulations Sisna"

Ta faɗa da duka haƙoran ta a waje.

"Amma Habib."

Sai ta kasa ƙarisawa Baɗɗo ta kalle ta kafin ta ce.

"Amma Habib me ne? Me ya faru da shi?

Ummu ta miƙa ma Baɗdo hannu ita ta taimaka mata ta tashi zaune ta jingina da jikin kujera jin yadda jikinta ya yi zafi ne ya sa Baɗɗo ta ce.

"Sannu Zazzaɓi ne ma a jikin ki Ummu."

Shuru ta yi mata ba ta yi mgana ba.

"Kun je asibiti?

Sai Ummu ta girgiza mata kai cikin mamaki Baɗɗo ta ce.

"To saboda mene ne, Habib bai san ba ki da lafiya ba ne?

Ummu ta runtse idanuwanta sai hawaye suka kece mata.

Ganin haka ya sa sai jikin Baɗɗo ya yi sanyi.

"Sisna wani abu ne ya faru da Habib ɗin ne?

Ta sake faɗa tana riƙe hannayenta ganin yadda take hawaye wasu na ganganrowa wasu na sake kwaranya.

"Me ke faruwa ne Ummu Salma?

Ta sake tambayan ta cikin damuwa da ya bayyana har a muryan ta.

"Baɗɗo."

Ummu ta sake kiran sunan ta wannan karon bata ba ta damar amsawa bq ta cigaba da faɗin.

"Habib ya ce ba ya sona sannan kuma ba ya son haɗa zuru'a da ni."

Baɗɗo ta zaro ido, tana kallon Ummu da ta fashe da kuka har yana fidda sauti.

"Me ne kika ce?

Baɗɗo ta faɗa da sauri lokaci ɗaya tana zaro idanuwanta waje.

"Haka ya ce Baɗɗo. Yanzu ma ƙoƙarinsa na zubar da cikin dake jikina."

Ummu ta sake faɗa cikin kuka, lokaci ɗaya tana ma yar da kanta saman cinyar Baɗɗo.

"Baɗɗo Habib ya canza ya tsane ni  bai da mu da ni ba. burin shi kawai cikin dake jikina ya fita. Burin shi kawai na rasa cikin da ke jikina, ya faɗa mini bai aure ni domin ya haihu da ni ba."

Ta ƙarishe faɗa cikin kuka,har da shessheƙa.
Baɗɗo da itama har ta fara hawaayen tausayin yar'uwanta nata ta ce.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un"

"Me na ke ji haka Ummu? Shi Habib ɗin?

Ummu ta kasa mgana ban da kuka ba abin da take yi, kukan baƙinciki da takaici kanta kukan ciwo da zafin zazzaɓin jikinta kukan samun salama tunda ta samu ta iya faɗa ma Baɗɗo damuwarta.


*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"


https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t


*06*

Cikin kuka mai tsanani da shessheƙa Ummu ta sanar ma da Baɗɗo abin da ke faruwa. Lamarin da ya girgiza duniyar Baɗɗo kafin Ummu ta gama ba ta labarin halin da ta ke ciki hawaye sun gama jiƙa ma Baɗɗo gaban doguwar rigar atamfar dake jikinta.

Tana kuka Ummu na kuka suka haɗu suka rumgume juna suna ta kuka a tare, ita Ummu kukan halin da ta tsinci kanta a ciki take yi da tausayin kanta sannan tana kukan takaici na har a yanzu tana yi ma Habib uziri, har yanzu tana tunanin cewa zai dawo gare ta, har a lokacin tana tunanin wasa yake yi yana son ta sannan kuma yana son haɗa zuru'a da ita. Ga gaskiya ƙiri-ƙiri amma soyayyar Habib ta rufe mata ido daga ganin wannan gaskiyn.

  Baɗɗo kuma kukan tausayin Ummu take yi. Tausayi mai yawa ganin irin halin da take ciki, gani ta ke yi kamar a mafarki ba domin Ummu ce da kanta ta e faɗa mata wannan labarin ba sai ta ƙarya ta ko ma waye, Habib ne fa? Ba ta taɓa tunanin zai iya aikata haka ba, ba ta taɓa tunanin Habib jahili ba ne mara ilimi sai da Ummu ke ba ta labarin shi.

"Ya zan yi? Na rasa yadda zan yi Baɗɗo gani na ke yi kamar a mafarki, gani na ke yi kamar ba Habib ba ne."

Ummu Ta sake faɗa tana gunjin kuka kanta a saman cinyar Baɗɗo ya yin da ita kuma take shafa kitson da ke kanta alamun lallashi amma ita ma kukan take yi, hawaye sun kasa tsaya mata saboda tausayin halin da Ummu take ciki? Lalle ta ƙara sarewa da lamarin mazan wannan zamanin masu sauya launi a duk lokacin da suka ga dama, za su kuma iya juya rayuwar wanda ya yarda da su daga sama zuwa ƙasa.

"Ya ce ba ya sona sannan ba ya son haɗa zuru'a da ni. Ƙarya yake yi ko? Ke ma ai kin shaida irin son da ya ke yi mini ko Baɗɗo?

Ta sake faɗa cikin kuka tana mai riƙo hannayen Baɗdo a cikin nata. Baɗɗo ta kalli Ummu kafin ta share hawayenta duk da ta fahimci Ummu na son Habib ba za ta fasa faɗa mata gaskiyan da soyayyarsa ta rufe mata idon da ta kasa fahimtar manufarsa ba.

"Ummu-Salma ta so nan ki saurare ni ki ji."

Ta faɗa lokaci ɗaya tana taimaka mata ta tashi zaune suna fuskantar juna hannayenta Baɗɗo ta riƙe duka biyun kafin ta sake kiran sunan ta.

"Ummu-Salma."

Ta amsa mata cikin shaƙewar murya saboda kuka.

"Ki kalli gaskiyan dake gaban ki. Da gaske ne duk abin da Habib ya faɗa, domin wanda ke son ka shi ke ƙaunar haɗa zuru'a da kai, kin ce ya faɗa miki da bakin shi sannan ya yi ƙokarin aikata hakan a aikace, kin ga kenan zaman ki tare da shi ma hatsari ne, tun da ya sha alwashi zai iya miki lahani domin ya ga ya cimma burin shi."

Ta ƙarishe faɗa cikin ƙura ma Ummu ido tana so ta ga yadda ta ƙarɓi mganar, tun da ta ce mata tana cikin halin wannan laulayin amma bai damu da ita ba, shi dai burin sa ta zubar da cikin jikinta da kuma  yadda ta faɗa mata matakan da ya bi domin ganin ya cimma manufarsa ta tsoraci Habib da lamarinsa ta kuma tabbatar da yadda yake son cimma burinsa zai iya komai in ta ce komai tana nufin komai domin ya ga cikin jikin Ummu ya fita ko da ita za ta shiga haɗari ne.

"Ya zan yi.! Ina son cikina Baɗɗo sannan ina son Habib."

Baɗɗo ta taɗe tana  kallon ta kafin ta ce" Ni ma ban ba ki goyon bayan ki zubar da cikin nan ba domin ba ki sani ba ko shi ne kaɗai ƙwan ki a duniya ba. Shi ma jahilci ne da rashin tunani sannan da manufarsa ta auran ki, mganar kina son shi duk ki cire shi Ummu tunda da bakin ki kika faɗa mini ya ce shi bai taɓa son ki ba, sannan bai aure ki domin haihuwa ba."

"Habib ne fa Baɗɗo. Habib na sona ke ma kin sani?

Ummu ta katse ta cikin kuka hawaye sun kece mata da ƙarfi kuma tana yin kukan mai fidda sauti. Baɗɗo ta yi mata uziri domin ko ita tantaman Habib ta ke yi, in ta yi nazari duba da tun daga lokacin da suka haɗu da Ummu da irin soyayya da ƙauna da tattali da ya nuna mata suma saboda ita duk ya ƙaunace su, ita kanta ba domin Ummu ce da kanta ta ga zahirin Habib ba za ta iya ƙaryata wannan labarin, Ummu na cikin damuwa ta kasa gasgasta Habib ne zai yi mata haka? Tunani ta ke yi kamar ba zai iya nuna haka ba saboda ya gurɓata rayuwarta cikin so da ƙaunarsa tare da kuma Aminta da shi.

"Mun sani a baya yana son ki ayadda ya nuna mana a aikace Ummu. Yanzu kuma ya fito da zahirin manufarsa a kan ki."

Baɗɗo ta sake faɗa tana jijjiga hannayen Ummu dake cikin na ta.

"To ya san ba ya sona me ya sa ya zo ya nuna mini so da ƙauna har ya aure ni?

"To wannan kuma manufarsa ce tun da bai faɗa ba, ba za mu iya yanke masa hukunci ba. Amma duk namijin da ya ce ya aure ka ba domin  yana son ka ba sannan ya nuna ba zai iya haɗa zuru'a da kai ba to dalili biyu ne, na farko ko ya yi auran fansa dake domin rama wani abu da kika yi masa na biyu kuma ko ya yi auren sha'awa da ke Ummu."

Ummu ta ƙura ma Baɗɗo ido  tana mai tsiyayan hawaye. Ta fi amin ta da auran sha'awan da Baɗɗo ta ce in ta yi duba da yadda Habib ya tsara zamantakewar su ta aure, yadda ya mai da abin cin tuwo ba dare ba rana ko ba ta da lafiya bai damu ba sai ya aikata abin da yake so da ita.

"Ni na fi tunanin auren sha'awa ya yi dake Ummu."

Baɗɗo ta faɗa hawaye na sake kece mata Ummu ma ta sake fashewa da kuka suka sake

Please Login or Register in order to submit comment