Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sako waliyin shi a ciki nan aka kira shi ya ce ya bar mganar in sha Allahu ashe yaudaran mu ya yi, ya koma ya sauya wani tsarin to Jibo horon yunwa fa? Kashe mana Auta yake son yi ko mene ne manufarsa?

Baffa ya faɗa yana kallon Hamma Jibo cikin damuwa muraranta da ya bayyana a saman fuskar shi.

"Mene ne mafita Baffa?

Baffa ya yi shuru yana tunani kafin ya ce" Wannan karon ba zan jira ma Baffan ku Umaru ya zo ba, zan kira shi na ce ya tura mini lambar shi waliyin Habibun zan kira shi na ce masa ina son mu haɗu ni da kaina zan warware masa komai sannan na faɗa masa ya sanar da ɗan shi in har ba ya son Ummu ne ya dawo mini da ita gida ni ina da abincin da zan ciyar da ita ba wai ya gagare ni ba ne"

Yadda Baffa ke magana kaɗai ya isa ka fahimci ya kai makura a takaicin Habibu, ba abin da ya fi ƙona masa rai  a ciki irin horan yunwa ga ciki a jikinta amma ya barta tana wahala saboda wata manufarsa ta banza da wofi. To shi ba zai ɗauka ka ba, ba a dole ya sako masa yarsa in ba zai iya rike amana kamar yadda ya ɗau yaƙini ba.

"Baffa na lura Auta na son mijinta. Kar a yi gaggawan raba su a tsaya dai a sake samun masalaha."

Baffa ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce" To son banza Jibo? Me son ya tsinana mata balle mu iyayenta! Kuma ni na ma fara tamtama in har yanzu yaron nan Habibu na son Auta. Domin mai son ka zai so haɗa zuru'a da kai, sannan ba zai taba wulaƙanta ka ba, ballanta har yana da shi da gangan ya yi maka horo da yunwa."

"Haka ne Baffa"

Hamma Jibo ya faɗa cikin gamsuwa da mganar Baffa amma yadda Ummu ke kuka har yanzu hoton ya kasa ɓace masa.

"Ko tana son shi, in shi ya nuna baya ra'ayin ta ai dole ta haƙura."

Hamma Jibo ya yi shuru duk jikinsa ya yi sanyi. Nan take Baffa ya kira ɗan'uwansa Baffa Umaru bayan sun gaisa ya ce masa yana son ya tura masa lambar waliyin Habibu mijin Auta Ummu Salama.

"Hadi lafiya kuwa?

Baffa Umru ya tambaya daga can bangaren cikin mamaki, domin shi a tunanin shi an samu masalaha tsakanin Auta da mijinta tun bayan zaman da suka yi.

"Zan sanar da kai daga baya. Yanzu dai ka turo mini lambar ina jira.'

Sai bai matsa masa ba ya amsa masa da to zai tura masa, suna yanke wayar mintina biyar tsakani ya turo masa lambar, Hamma Jibo ya ba ma wayar ta sa ya ciro masa lambar ya saka a cikin wayar sannan ya ce ya kira ya ba shi zai yi mgana da shi.

Kira ɗaya ba ta ko daɗe tana kara ba Alhaji Sheriff ya ɗaga wayar da sallama Baffa ya amsa bayan gaisuwa sai Baffa ya gabatar da kansa.

"Sunana Alhaji Hadi Baba ni ne mahaifin Ummu Salma, matar yaron wajen ku Habibu."

Nan da Alhaji Sherif ya washe baki kamar yana ganin shi, suka sake gaisawa tunda ba su da lambar juna, daman da Baffa Umaru ne suke magana tun neman auren.

"Alhaji lafiya kuwa? Ina fatan ba wata matsala ce ta sake tasowa daga bangaren yaran ba?

Alhaji Sheriff ya tambaya daga can bangaren, domin ya ji mamakin kiran na sirikin Habibu a wannan lokacin.

"Lafiya lau, in ba damuwa adireshin gidan ka za ka turo mini zan zo har gida da safe na same ka, akwai mganganun da za mu tattauna ne."

Baffa ya faɗa cikin dattaƙon sa.

"Haba Alhaji ai ba sai ka zo ba. Ni zan zo na same ka a gobe da safen in sha Allahu."

Amma Baffa ya ce aa shi ya yi niyar zuwa saboda haka ya bar shi kawai ya zo, dole ya amince suna gama waya da Baffa nan take ya tura masa adireshin gidan shi da ke At Unit cikin gari, ya yi zuru shi kaɗai yana tunanin me kuma ya sake faruwa? Amma jikinsa ya ba shi koma me zai kawo surukin Habibu wajen sa to ba zuwan lafiya ba ne, in ko haka ne Habibu ya gama kunyata shi da girman shi.

Bangaren Baffa kuma, da shi da Hamma Jibo suka shirya za su je gidan Alhaji Sheriif da safe Baffa ya ce kar Hamma Jibo ya sanar ma da Ammah komai sai zuwa nan gaba har sua ga abin da zai je ya dawo. Shi ya sa ya yi shuru bai faɗa mata ba shima Baffa ko a fuska bai nuna mata wani abu ba, tausayin Ummu ya dame shi
shi ya sa ko a waya ya kasa kiran ta, baya so ya ji muryanta sai ta saka shi kuka.

Ammah ko ba ta san abin da ke faruwa ba, da ta tambayi Nauwara yadda suka baro Ummu sai ta ce tana nan lafiya Hamma Jibo ma haka ya ce mata su Saudat kuma Allah ya sa yan surutun ba sa kusa da ta ce ta ga Anni na kuka kamar Allah ya rufe mata baki ita da Ammi ba su yi surutun ba.

Baffa kwana ya yi bai yi barci ba. Ba kan Ummu farau zawarci ba ya san shi take tsoro, shi ko da ya bar yarsa ta mutu a gidan wanda ba shi da asara gwara duniya ta zage shi , zai ajiye wani fillanci ya tsaya mata. Shi me ye bai gani ba? Nan ƙanwarsa Fatima ta dawo masa da yaro a cikin jinin haihuwa da takardan saki kuma ya karɓeta ya riƙe ta gam, to ba wani sabon abu ba ne in Ummu ta dawo masa da ciki gida, a wannan karon ma godiya zai yi ma Allah ya karba duka kaddaransa, daga karshe da ya gaji da juye juye sai ya tashi ya shiga tiolet ya ɗauro alwala ya yi nafilfilu, tare da addu'o'i ma su yawa akan in har babu alheri a auren Auta da mijinta Allah ya sauƙaƙa mata kaddaranta.

Da Ammah ta farka ta gan shi yana ta salla, sai itama ta mike ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ta zo ta jera a gefen shi, ta tayar da salla ba su suka koma suka kwanta ba sai wajen uku na dare, asuba na yi Baffa ya ta da Ammah shi kuma ya yi alwala zuwa masallaci.

Nauwara da yara suna bangaren Ammah, Hamma Jibo na can bangaren haraba, Baffa na fita sai ga shi ya fito tare suka fita zuwa masallaci.

Wajen shidda na safe suka dawo tunda sun ɗan tsaya liman ya yi tunatarwa kan riƙo da zumunci da yaƙana ko da suka dawo Nauwara ta share gidan tas ta gyara ɗakin Ammah sannan ta yi ma yaran wanka Amma kuma na kitchen tana sama musu abin ƙaryawa.

Fanke ta soya sai ta dama kunun tsamiya, ta dafa indomie saboda yan biyu da dafaffen ƙwai, kawai sai Ammi ta saka rigiman sai an soya mata ƙwai, Amma ta ce ta yi abin da za ta iya  uwarta ta fito ta soya mata Baffa da Hamma Jibo suna ta dariya Ammah ko ta haɗe rai tana faɗin yara sai iyayin tsiya.

Suna gama karyawa Baffa ya yi wanka shima Hamma tuni ya shirya. Jibi yake so su koma saboda aikin sa shi ya sa yau ya ce Nauwara da yara su shirya su je su gaishe da Ummin ikki, da gidajen su Hamma Abdullahi da Abdulrrahman
har Mubi ya so su je su gaishe da su Ummu Balki, amma ba lokaci watakila sai hutun karshen shekara.

Ammah ta ɗan yi mamakin ganin Baffa da Hamma Jibo za su fita tare amma sai Baffa ya ce mata fitan na shi ne Jibon zai tuƙa sa ne, ba daɗewa za su yi ba sai ta yi musu fatan dawowa lafiya.

Hamma Jibo na fitowa da mota waje Baffa na shirin shiga sai ga Hamma Abdullahi ya kariso a mashin ɗin da ya siya, yana da mota amma in ba tafiya mai nisa ba ya fi yawo a mashin.

Mamaki ya kama shi na ganin Baffa sun fita da Hamma Jibo saboda kafin ya kariso da mashin ɗin kofar gida har Baffa ya shiga mota sun bar wajen agogon hannun shi ya duba tara ta gota shi kaɗai yana mamakin ina za su je da safen nan haka?
Ya shanye mamakinsa ya ƙarisa cikin gida bayan ya shiga da mashin ɗin sa har haraba.

Tun kafin ma Ammah ta ce masa Baffa baya nan ya ce mata ya gan su za su fita tare da Hamma jibo a ƙofar gida.

"Ammah ina su Baffa za su je ne?

"Bai faɗa mini ba Baba "

Da yake yana da sunan mahaifin Baffa shi ya sa Amma ba ta iya faɗin sunan shi har gwara ma Baffa yana kiran shi da Abdullahi wani lokacin.

Ta ba shi amsa da harshen fillanci, bai sake tambaya ba, yana cikin falon ne zaune su Saudat na ta yi masa hira yana biye musu Nauwaran ma ta fito sun gaisa Ammah ta ce ai duk yau za ta leƙa gidajensu shi  Abdulrrahman.

"Itama yau take yi mini mganar tana so ta zo su gaisa."

Ya faɗa yana kallon Ammah.

"To ai ta yi zaman ta yau Jibon ya ce duk ta leƙa ku."

Sun ɗan taba hira ya so ya jira su Baffa ne sai aka kira shi a waya wani abokin shi ya zo gida nemansa sai ya yi ma Ammah sallama da cewa zai tafi.

"Ba za ka jira Baffan ba?

"Amma na yi baƙo a gida. Zan dawo zuwa anjuma da man magana za mu yi kan injinan mu da zan je kwatano na taho da su."

"To ko Nauwara za ta taho ka sauke su tun da gida za ka koma?

Da sauri ya ce" Da mashin na zo Ammah ba da mota ba."
Sai Ammah ta yi shuru, har su Hassan suna rigiman sai sun bi shi.

"To ku jira baban ku wannan uban na ku bai zo da mota ba"

Yara sai suka fara kuka suna sai sun bi Bobo, haka yaran Hamma Jibo ke kiran duka ƙannen ubansu maza.

"Bari kawai Ammah na tafi da su Hassan sauran Mamansu sai ta taho da su."

Haka ko aka yi yan biyun ya ɗauka a mashin, da Isma'il a gaba domin shima rigima ya saka sai ya je, ga shi karami ɗan shekara 4 amma ya iya rigima Ammah ta yi ta tsaki tana faɗin iyayensu sun sangarta su.
Saudat aka bari da Ammi za su taho tare da Nauwara da ta ce in ta ga Hamma Jibo ya daɗe za su hau kekepep ne su tafi.

**

Gidan Akhaji Sherif bai da wuyar ganewa suna shiga anguwar tambaya ɗaya suka yi aka kawo su tunda sananne a anguwa sakamakon fitattacen ɗan kasuwa ne, suna zuwa ƙofar gidan Baffa ya kira shi ya ce sun ƙariso da man shi yake jira ba daɗewa sai ga shi ya fito ya tarbi Baffa.

Hamma Jibo ma ya gaishe shi ya amsa cikin sakewa yana kallon shi

"Jibril jibo kenan babban yaro na ne, yana aiki Abuja."

Nan da nan Alhaji Sheriff ya washe baki suka yi musabaha da Hamma lokaci ɗaya yana cewa' Ai na ga kama "

Da ya yi ma Baffa ta yin shiga cikin gida cewa ya yi ba zai shiga ba sai da ya yi masa magiya sannan ya amince suka shiga falon gidan Alhaji Sherif an kawo musu ruwa Baffa ne kaɗai ya sha ban da Hamma Jibo.

"Alhaji ina fatan lafiya ko? Duk da dai lafiya ba za ta saka ka taso da kan ka zuwa wajena ba."

"Wannan gaskiya ne."

Baffa ya faɗa kafin ya gyara zama yana faɗin" Alhaji a matsayin ka na waliyin Habibu kai muka sani a matsayin wakilinshi shi ya sa da lamarin zubar da ciki ya taso muka neme ka, domin ka tsawatar masa."

"Gaskiya ne wannan."

Alhaji Sheriff ya fafa cikin gamsuwa da kalaman Baffa.

"To a wannan karon ma shi ya sa na sake neman ka."

"To. Me ya faru?

Ya tambaya cikin son ya ji  kuma wani abu Habibu ya sake fitowa da shi.

"Ko maganar zubar da cikin ne bai barta ba har yanzu?

Alhaji Sheriff ya sake tambaya yana mai kallon Baffa.

"Ba shi ba ne, amma kuma ya fito da wani tsarin ne, ya fara yi mata horo da yunwa a takaice dai ya bar ta, tana ci da kanta jiya ɗan'uwanta ga shi nan ya je gidanta ya dawo mini hankali tashe. Ya rantse mini har ga Allah bai ji daɗin ganin Auta a cikin yanayin da ya gan ta ba."

"Horon yunwa kuma? Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.

Alhaji Sheriff ya faɗa cikin tashin hankali Baffa kuma ya cigaba da warware masa duka halin da ake ciki.

"Habibu bai sauya ba, duk abin da ya faɗa a gaban mu a gaban ka duk yaudara ce ya san tana da ciki kuma yana mata horon yunwa in yana tunanin wahala zai iya sanadin ciki ba ya tunanin halin da Ummu za ta shiga! Tsakani ga Allah Alhaji na kasa haƙuri da wannan rashin imanin horon yunwa ga mai juna biyu hatsari ne, bai rasa abin da zai ba ta ta ci ba, sai na fahimci kawai mugunta ne da son zuciya irin na ɗan adam "

Alhaji Sheriff ya ji zufa na keto mai saboda nauyi da kunya.

"Assha wannan lamarin bai yi daɗi ba Alhaji."

Ya faɗa cikin takaici da baƙin ciki.

"Wallahi bayan mun zauna da ku, ni da kaina na sake kiran shi na yi masa faɗa ya ce mini komai ya wuce, ko shekaranjiya mun haɗu a gidan su a gaban mahaifin shi na tambaye shi komai lafiya ya amsa mini da lafiya lau ashe ya yaudare mu ne ba mu sani ba"

Baffa ya jinjina kai kafin ya ce" Tabbas ya yaudare mu, bai saduda ba."

"Kai, amma Habibu ya ba ni mamaki,."

"Mu ma duk ya shayar da mu  mamakin sa."

Baffa ya faɗa yana kallon Alhaji Sherif da Habibu ya gama kunyatawa a idanuwan su Baffa.

"Ka yi hakuri Alhaji bari na kira shi yanzu."

Da sauri Baffa ya ce" A'a ba sai ka kira shi yanzu ba. Ga dai saƙo na a gare shi in ya zo ka faɗa masa."

Shuru Baffa ya yi na ɗan lokaci kafin ya cigaba da faɗin"
Ka sanar da shi in ya gaji da Ummu Salma ne to ya dawo mini da ita gida ni ban gaji da ita ba. Da ita da cikin jikinta duka suna da kyakyawan gurɓi a gidana."

Alhaji Sheriff ya ce" Aa ba za a yi haka ba Alhaji."

"Haka za a yi, sannan daga ƙarshe ka sanar da shi cewa lokacin da na aura masa Ummu Salma bai ganta cikin yunwa ba, saboda haka ba shi da hurumin yi mata horon yunwa a na shi gidan."

Baffa na gama faɗin haka ya miƙe yana gyara babban rigan shadda faran dake jikinsa.

"Jibo ta shi mu tafi."

Ya yi gaba Alhaji Sherif ya biyo bayan shi yana ta bashi haƙuri har waje.

"Don Allah Alhaji ka yi haƙuri. Wallahi ba da yawun mu Habibu ke yin wasu abubuwan ba tabbas ba san me ya sa ya koma haka ba."

"Ba komai,  ba a dole in ba ya son ta babu matsala in ya dawo mini da ita."

Alhaji Sheriff ya yi ta ban haƙuri Baffa ya nuna masa ba komai amma in har Habib ya gaji to ya dawo da Ummu gida.
Sallama suka yi cikin girma kafin Baffa ya shiga mota Hamma Jibo ya tada motar suka bar layin.

Sai da suka hau titi sannan Hamma Jibo ya kalli Baffa da ya yi shuru yana faɗin" Baffa kana ganin Auta ba ta yi ƙanƙanta da zaawarci ba?

"In abin da Allah ya kaddaro mata kenan ai ba mu da yadda za mu yi Jibo amma tabbas yaron nan ya gaji da zama da Auta duk ya nuna alamun haka a bayyyane."

Hamma Jibo ya yi shuru bai yi magana ba sai dai yana ta furzar da iska daga bakin shi alamun lamarin ya dame shi.

"Kar ka damu, Fatima ta dawo hannuna a bazawara tana da shekaru sha bakwai ne, yau ina take? Tana can tana rayuwarta da mijinta da ya'yanta bai wuce ba, ya wuce Jibo sai dai mu tuna kawai. To itama Auta in hakan ta kasance da ita na san za ta ji ba daɗi amma in ta yi hakuri komai zai wuce ya zama wata rana sai labari."

Hamma Jibo ya jinjina kai yana mai gamsuwa da maganganun Baffa tabbas gaskiya ya faɗa duk kaddaran da ta same ka, in ka yi haƙuri wata rana za ka tuna har ka yi dariya.
Baffa ya yi ƙokari sosai ya san Baffa na da kara sosai amma akan ya'yan shi ko yan'uwan shi ba shi da wannan karan zai yi kawaici na farko na biyu ana uku kuma zai shiga gaba, sau tari in Baffa ya yi wani abun kamar ba jinin fulani a jikin shi, yana da kunya amma bai cika bari kunya na cutar da shi ba, Ammah ce mai kara da kunya kan ƴa'ƴan ta komai na su kuma da man Ummin ikki ne ke shigewa gaba. Ita in an ganta a gaba-gaba Lamiɗo ne da duk abin da ya shafe shi, in ko ba shi ba, ba ruwanta da sha'anin kowa ballatana ma ta shiga.

Da suka koma gida Amma ta faɗa ma Baffa Abdullahi ya zo neman shi ba ya nan, nan da nan ya ɗaga waya ya kira shi ya ce ya zo gida ya same shi ya dawo.

Hamma Jibo kuma Nauwara ya ɗauka a mota tare da su Saudat zuwa gidan Ummin ikki daga can zai wuce da su gidan Abdullahi.
Ko da wasa Baffa bai sanar da Ammah abin da ke faruwa ba, duk da ya san ta da kawaici amma yana da tabbacin yadda ya iya shanye damuwarsa ita ba za ta iya shanyewa ba, za ta shiga damuwa sosai ko da ba za ta yi magana ba.

***

Alhaji Sheriff tun fitan su Baffa daga gidansa yake kiran lambar wayar Habib amma ba ya samun shi har dare kuma bai same shi ba sai ya kira Malam Usman, ƙani yake gare shi, kuma shi ke bi ma mahaifin Habibu a haihuwa nan ya warware mishi komai, shi da yake ba shi da hali sosai Alhaji Sheriff duk a cikin su ya fi su rufin asiri.

"Assha Habibu bai yi tunani ba ya ɓata wayon sa sam."

Malam Usman ya faɗa cikin mamakin Habibu har da shi a cikin maganar auran nan na Habibu iyayen matarsa masu mutumci da ƙima ne.

"Wallahi Usman Habibu ya gama zubar mana da mutumci, na yi ta kiran wayarsa ban samu ba in na same shi zan ce gobe goben nan mu haɗu gaban mahaifinsa da uwar riƙon sa, na maimaita masa saƙon uban matarsa a gabansa sannan na zare hannuna a sha'aninsa ya je can ya yi duk abin da ya ga dama tun da ba ya jin shawara."

"Aa ba za a yi haka ba Yaya Sheriff. In ka ce masa haka ai sai ya sake lalacewa. Gwara dai mu taru mu sake jan kunnen sa, in ka same shi a waya ka sanar da ni, sai mu haɗu gabaɗaya mu sake jan kunnen sa."

"Allah ya sa ya ji to. "

Alhaji Sheriff ya faɗa cikin takaici sun cigaba da tattaunawa duk da dai akan mganar kafin su rabu da juna akan sai Alhajin Sheriff ɗin ya kira shi in ya samu Habib a waya.

A ranar dai bai same shi ba sai a washegari, sai dai ya sanar da shi ba ya Jimeta yana Abuja a wajen aiki an tura su wata Seminar, kuma ba za su dawo ba sai gobe lahadi da yamma, nan take Alhaji Sheriff ya ce masa in ya dawo a daran su haɗu a gidan su bayan isha'i ya kashe wayarsa  ba tare da ya jira cewar Habib ɗin ba, ya bar shi cikin tunanin abin da ya faru, ya san abin da ya yi shi ya sa ya kawo tunanin maganar Ummu Salma ce.

"Kai wannan yarinyar kamar mayya wai sai na ce mata na sake ta ne za ta gane na gaji da ita ne?

Ya faɗa a fili yana dafe kai, a cikin kayattacen ɗakin hotel ɗin da bankin su ta kama musu.
Da man ko ba a kira shi ba ya gama yanke shawaran in har ya koma ya ga yunwa bai saka Ummu tafiya gida ba to zai sallame ta, har ga Allah ya gaji da shiga damuwa akan ta.

**

Hamma Jibo a ranar lahadin da sassafe suka ɗau hanya shi da iyalan shi, da yake tafiyar mota suka yi wannan karon shi ya sa suka fita da wuri, sun rabu da Baffa akan duk halin da ake ciki zai kira shi ya sanar da shi, sannan Ummu ma sun yi waya ya sanar da ita ya faɗa ma Baffa komai amma bai faɗa mata Baffa ya je wajen waliyin Habib ba, shi dai ya jadadda mata ta kula da kanta sannan ta zama jaruma ko da wani abu zai faru ta sani Allah ne ya jarabce ta ba wani ba.

Ta amsa masa da in sha Allahu, domin ita tuni ta san wannan karatun ita da rayuwarta ta yi juyin waina cikin lokaci, Habib ma ba ya kwana a gidan yanzu ba ta san ya yi tafiya ba a tunanin ta tunda yanzu ba ya buƙatar ta shi ya sa ya daina ma kwana a in da take shaƙan numfashi.

Kamar wasa a ranar tana zaune tana cin abinci  da yamma gabda mangariba sai ga Habib ya shigo gidan. Ko kallon ta bai yi ba ballantana ta saka ran cewa zai iya jin tausayinta bayan ya kalle ta, shigewa ciki ya yi ya barta anan tana tsiyayan hawayen da suka zame mata jiki, sai ta ma kasa cin abincin ƙwata-ƙwata sai juya shi cokalin take yi a hannun ta, shinkafa da wake ne da man da dafa sai ta saka allayahu sosai ya ji saboda dokar likita yunwa take ji tana zumuɗin cin abincin amma ganin Habib ya sa komai ya ƙwace mata. Hawaye suka kece mata wasu na gangara wasu na kawowa tana tuna irin rayuwar da suka gudanar ita da Habib tun daga soyayyarsu har zuwa auren su. Ta daɗe tana alfahari da buɗe kafaɗan cewa ba wata macen da ta kai ta dacen miji mai son ta da ƙaunarta. Ba ta taɓa tunanin nan kusa za ta fuskanci kuka da damuwa ba, ba ta taɓa zaton wata rana ita Ummu Salma za ta zama wacce Habib ya tsana ba ya son gani ba sai yanzu da yake faruwa, su Baɗɗo sun daɗe suna fata da ƙwatancen su zama kamar ita domin sun ɗauka tarihin soyayyarta ya kai a ba da labarin shi da zai sa mata da dama su ji suna jin haushi da yadda ta yi dace ta bar su, tabbas za a ba da labarin soyayyarta da na rayuwarta gabaɗaya Habib zai sa ta zama abin nunawa da kwatance a cikin dangi da anguwa gabaɗaya.

Tana nan zaune tana kuka Habib ya sake fitowa, ta kifa kanta a saman hannun kujeran da take zaune tana ta kuka har yana fidda sauti, yadda ya shigo bai kalleta ba haka ya sake fita bai ko kalli in da take ba amma ita ta ɗan ɗago ta kalle shi ya yi wanka ya sauya kaya zuwa manya yana ta tashin ƙamshin turare. A baya in ta kalli Habib wani nishaɗi da alfahari take ji , wani irin son shi ke ƙaruwa in ta kalle shi amma sai ga shi yanzu in ta kalle shi sai ta ji nadama da baƙin ciki yadda in da za a ba da tarihin rayuwarta sai an fara da Habib watakila ma a ƙare da shi tunda Habib ya gama kassara rayuwarta gaba da baya ba ta kuma da sauran wata mamora.

Abincin da ta hakura dashi kenan ba ta ci ba, sai ta mai da shi kitchen ta ajiye ruwa kawai ta iya sha ta koma ciki ta kwanta tana jan casbaha tana kuma kuka lokaci ɗaya. Addu'a take yi ubangiji ya yaye mata ƙunci da damuwar dake cikin zuciyarta Allah ya ba ta ikon cin jarabawanta, cikin da ke jikin ta Allah ya kare shi ta daina ma adduan Allah ya karkato da hankalin Habib kanta, ta yarda kuma ta amince da gaske Habib yake yi bai taɓa son ta ba, shi kuma wanda  ya

Please Login or Register in order to submit comment