Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji mamakin jin maganar cikin Ummu a bakin shi, faɗa ya yi masa kaca kaca da cewa bai isa ya sa a zubar da cikin ba. Tunda ya bari aka samu cikin sai an haife shi
Kuma kar ya sake jin wata magana nan da nan Habib ya ce shi bai tilasta mata sai  ta zubar da ciki ba. Shi kuma Baffa Umaru ya ce Habib ɗin ya turtusa ma Ummu akan ta zubar da ciki, jin haka ya sa Alhaji Sheriff ya kira Baffa Umaru ya ce ya zo garin su haɗu a gidan Baffa tare da su Habibun a yi magana gabaɗaya.
 
Shi kuma ya bashi tabbacin, zai zo cikin satin in sha Allahu.
Habibu dai ya san matsayar mganar tun da Alhaji Sheriff ya faɗa masa ga matsayar da aka tsaya. Ita dai Ummu ce ba ta sani ba sai ana gobe zaman Baffa ya kira ta a waya ya faɗa mata ba domin shi ba da ba za ta sani ba. Tunda Habib ba ya magana da ita ballanta ya sanar da ita.

Kuma adaran ta fito shan ruwa suka haɗe da Habib ya fito daga tiolet tana ganin shi sai da gaban ta ya faɗi tunda yanzu ganin sa ba alheri ba ne a wajen ta.
Ta yi saurin faɗawa Kitchen tana sauke numfashi, ta ɗan jima kafin ta fito bayan ta sha ruwan sai dai me tana fitowa ta ga Habib na zaune a falon abin da ya daina yi tun bayan lalacewar zaman su, sun haɗa ido ya yi mata wani kallo gabanta na faɗuwa ta dukar da kai za ta wuce ta ji maganar sa a sama.

"In da kike tunanin kin kaini da niyar na fasa ƙudirina to kin yi kuskure domin nan duniya ba wanda ya isa ya sauya mini ra'ayi na "

Ummu ta ɗago tana kallon shi cikin mamakin kalaman shi..
Ido ya zare mata sannan ya gyaɗa mata kai alamun tabbatarwa.

"Haka na faɗa, saboda haka kin yi kuskure kuma sai kin yi nadama."

Yana gama faɗin haka ya yi tsaki, ba domin ta matsa ba da ya ture ta, in kuma ta faɗi ba shi da asara. Da kallo ta bishi na tsantsan mamaki da al'ajabin maganganunsa yana nufin iyayen ta da iyayen shi, ba su isa da shi ba kenan.

Ta tabbata Habib da gaske yake yi tun tana tunanin lamarin shi wasa ne har dai ta amince da cewa Habib ya sauya duk abin da ya faɗa akan ta gaskiya ne tunda ga shi nan yana aikatawa a aikace.


*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t

*08*

Asabar.
*8:30am*

Washegari ta kama asabar ɗin karshen mako ne, tun ƙarfe takwas da rabi na safe Alhaji Sheriff ya kira Habib da umarnin ya zo gida yanzu-yanzu yana son ganin shi, yana barci ne ma ya tashe shi haka nan yana tura baki da ƙunƙuni ko wanka bai tsaya yi ba ya sauya kaya ya fita.

A tunanin shi ma ko ya kira shi daga can su wuce gidan su Ummu Salma ne, sai kuma ya ji akasin haka. Domin ɗaki Baffan na shi ya saka shi yana ta yi masa faɗa da jan kunne.

"An juma za mu haɗu acan gidan su iyalin naka. Habibu kai da kanka ka zo ka same ni cikin girma da arziƙi, ka ce kun daidaita da wannan yarinya mu je a nema maka auran ta, ga shi iyayenta masu mutumci da dattako ne. Ba za ka dawo daga baya ka kunyata kanka sannan mu ma iyayenka ka kunya tamu ba, don Allah in mun je ka ba ma iyayenta haƙuri maganar ciki kuma tunda har ka ɗiga shi to sai dai ka yi haƙuri bayan ya fito duniya daga baya in har kun gama daidaitawa da matarka to wannan ruwan ku ne, ku tsayar da haihuwa har na tsawon shekarun da kuke so ba ruwan mu a aciki. Amma yanzu maganar zubar da ciki ka janye ta Habibu."

Shuru kawai ya yi yana sauraran shi, amma ba ya jin zai iya aikata abin da ya ke so bai shirya ba. Ko ma ya shirya to ba da Ummu ba amma sanin ko ya zauna yana yi ma Baffan na shi bayani ba zai gane ba shi ya sa kawai ya yi musu shuru, sai dai maganar zubar da ciki ba gudu ba ja da baya.

"To Abba in sha Allahu"

Haka Habib ya faɗa ba wai domin ya saduda ba yana nan akan bakan shi.

"Allah ya yi maka albarka."

Ya amsa da amin kansa na ƙasa.

"Abba ko za ka shirya ne sai mu je daga nan?

Habib ya tambaya nan take ya ce masa aa ya koma gida ya ɗau matarsa su haɗu acan ƙarfe goma ne kar su makara. Habib ba haka ya so ba domin shi ba ya ƙaunar ma Ummu Salma ta sake zama a kusa da shi, yadda ba ya son ta haka ya tsani ya gan ta a kusa da shi amma saboda kar ya yi masa gaddama a yanzu anan gaba ya ƙi yi masa amfanin da yake so shi ya sa ya amsa masa da to.

Yana fita daga gidan ƙanin mahaifin na sa, ya shiga mota ya bar anguwa yana hanya ya ɗau waya ya lalubo lambar wayar Ummu Salma da tuni ya daɗe da blooking ɗin ta shi ya sa ko ta kira shi ba ta samun shi, wayar tana ta ringing gabda za ta yanke ta ɗauka murya a cunkushe ta yi masa sallama da mamaki a muryanta na dalilin me ya sa Habib ya kira ta kuma yau?

"Kar ki fita ki jira ni gani nan zuwa."

Haka kawai ya faɗa lokaci ɗaya ya yanke kiran yana mai sakin tsaki shi kaɗai, ba domin yana da wata manufa anan gaba ba, da ba wanda ya isa ya saka shi zuwa gidan su Ummu shi fa ya daɗe da gamawa da ita, sai dai in ya yi gaddama nan gaba ƙwaɓarsa za ta iya yin ruwa shi ya sa yake bi a hankali a yanzu.

***

Kiran da Habib ya yi mata a waya ya ɗaure mata kai. Yaushe rabon da ya kira ta a waya har ta manta. Da man tana ɗan share falon ne ganin ya yi ƙura ta ɗan jima ba ta share ba tana fama da kanta ta ji ana kiran wayarta a ciki tana zuwa ta ga shi ne, tunda ya ce ta jira shi gabanta ya yanke ya faɗi ta kasa sukuni domin ba ta san da abin da zai zo da shi ba.

A haka ta gama sharan ta yi wanka tana cikin shiryawa ya shigo gidan bai neme ta ba ya shiga ciki sama da mintina talatin ya fito sannan tana jin ya sake fita amma bai neme ta ba, tana zaune gefen gado ta yi tagumi ya sake kiran ta a waya.

"Malama ki fito ina waje"

Haka ya faɗa a fusace kamar zai kai mata duka ta cikin wayar, jikin ta a sanyaye ta ɗau hijabin da ta fito da shi dogo jalbab, ta zura lokaci ɗaya tana rataya baƙar jakarta haka ma takalmin kafanta ma baƙi ne keys ɗin gidan ta ɗauka sannan ta fita ta kulle ƙofar baya cikin haraban gidan a can wajen get ta gan  shi yana jiran ta a cikin mota.
Tana zuwa ta buɗe ta shiga a sanyaye ko kafin ta gama ma rufe ƙofar motar ya fizgi motar a guje sai da ta firgita.

Kallon shi ta yi ya haɗe fuskar nan kamar hadari, da sauri da kauda kanta saboda hawaye sun kawo mata sai ta yi saurin shanye su.

"Ina kwana."

Ta faɗa muryan ta a sanyaye, yau da ta ga Habib sai ta ji ba za ta iya ɗaukan kaddaran rasa shi ba, tana son shi kuma tana son ta ƙarishe sauran rayuwanta da shi har abada.

Da ta gaishe shi da farko bai amsa ba sai ta sake gaishe shi nan ma sai ya yi mata banza kamar bai san tana ma cikin motar ba, ita kuma tana ce sai ta gaishe shi ya amsa.

"Ina kwana Noori?

Ta sake faɗa cikin marairaicewa.

Wani kallo ya yi mata na tsana da takaici ita wai ba ta da zuciya ne haka ya faɗa a cikin zuciyarsa? Duk yadda ya ke share ta da nuna mata ba ta da wani muhimmanci a rayuwarsa bai sa har yanzu ta fahimci da gaske yake yi ba, watakila sai ya sake nuna mata matsayinta sosai wataƙila a lokacin za ta fi gane matsayin ta.

Kallon da ya yi mata ne ya sa ta kama bakinta ta yi shuru, har suka isa gidan su dake anguwan Zone 3, da suka iso ta ga bai fito daga motar ba ya dai yi parking a bakin get ɗin su, itama ganin bai fito ba sai ta zauna shi kuma ya ɗauko wayarsa yana dubawa shuru ya ji ba ta fita daga motar ba sai ya juya yana mata wani kallo cikin mamakin ta.

"Sai na ce ki fita za ki fita?

Ya faɗa yana ware mata idanuwanta da sauri Ummu Salma ta buɗe motar ta fita tana kallon shi, kauda kansa ya yi lokaci fuskar nan kamar bai taɓa dariya ba. Jikinta a sanyaye ta taka ta nufi get ɗin su, ta tura ta shiga ciki amma sai da ta tsaya a haraba ta daidaita kanta sannan ta shiga cikin gidan. Ammah da Baffa tare da Baffa Umaru suna cikin ɗakin Baffa suna ta hira can ta nufa ta shiga da sallama ta duka a gaban su tana gaishe shi.

"Auta kin iso?

Baffa ya faɗa, sai ta gyaɗa masa kai, ba su daɗe da gama karyawa ba tunda ga kayan karyawan nan a gaban su Ammah ba ta ɗauke ba. Sannan tun wajen tara  na safe Baffa Umaru ya iso Jimeta.

"Sannu Ummu Salama."

Baffa Umaru ya faɗa yana kallon ta ganin yadda ta ɗan rame,  yana shigowa Jimeta
Harkokinsa sosai kuma yana zuwa gidan ɗan'uwan na shi, kuma duk abin da ya danganci yaran Baffa na ba shi girman shi yana saka shi a ciki.

Kan Ummu na ƙasa ta amsa ta kasa mgana, Ammah ta kalle ta ta gefen ido kafin ta ce" Ke kaɗai kika zo? Ina shi Habibun?

"Yana waje."

"Bai shigo ba kuma?

In ji Ammah sai ta gyaɗa kanta kafin ta ce" Zai shigo daga baya."
Ammah ba ta sake magana ba ta miƙe ta kwashi farantin kwanukan da su Baffa suka yi amfani da shi ta fita zuwa kitchen.
Baffa Umaru ya sake tambayan Ummu Salma abin da ke faruwa ta sake warware mishi kamar yadda ta warware ma Baffa a farkon maganar.

"Wannan ai ba mgana ba ne, shi ma bai taki gaskiya ba."

Ya faɗa cikin ɓacin rai Baffa na gefe ya kaɗa kai kafin ya ce" Kuma tunda har an samu cikin maganar a zubar da shi ai bai ma taso ba."
"Sosai, bari Baban na shi ya ƙariso a zauna zan faɗa masa ba mu yadda da wannan tsarin ba."

Ita dai kanta na ƙasa ba ta yi magana ba ganin sun faɗa wata hiran ya sa Baffa ya ce ta je  wajen Ammah kafin waliyin Habib ya iso, sai ta tashi a sanyaye ta koma ɗakin Ammah ta isketa tana shara, ta yi saurin ijiye jaka za ta karɓa da sauri Amma ta ce" Ke bar shi, ba ki jin daɗi je ki kwanta ki huta"
Fir Ammah ta ƙi sakar mata sharan dole ta haƙura ta koma ta zauna a saman kujera ta yi tagumi.

"Kin ci wani abu kafin ki fito?

Sai ta girgiza ma Ammah kai amma ba ta yi magana ba.

"Akwai kunun gyaɗa da kosai za ki ci?

Da sauri ta ce" Zan sha Ammah."
Saboda tana son ƙosai ta daɗe ma ba ta ci ba kunun ɠyaɗan ma tana son shi har ƙamshin ɠyaɗan take ji yanzu a hancin ta.

Ammah da kanta ta ajiye sharan da take yi ta je Kitchen ta zubo ma Ummu kunun sannan ta zuɓo mata ƙosan a wani faranti, ta kawo mata har ɗaki aiko ta zauna ta shan kunun tana cin ƙosan har wani lumshe idanuwanta take yi saboda da daɗi addu'a take yi a cikin zuciyarta Allah ya sa kar ta yi amai, Ammah na ta kallonta ta gefen ido. Tana sake tausaya ma rayuwar Ummu ta sake ramewa bisa ranar da ta zo har a cikin zuciyarta ta ke jin tausayin Autar nata kuma tun da ta ji wannan lamarin ba ta sake barci   tun daga dare har safe ba, addua'a take yi ba dare ba rana, tana roƙon Ubangiji da kar ya kaddara ma Ummu zawarci da kaddaran aure, domin kaddaran tana da nauyi Ummu Salma ta yi ƙanƙanta da fuskanta hakan.

Allah ya taimaki Ummu har ta gama shan kunun ta da ƙosai ba ta ji amai ba Ammah kuma ta gama sharan ta ta shiga wanka kafin ta fito har Alhaji Sheriff ya iso ashe shi Habib ya jira daga waje su Baffa suka fito sai suka shigo da su, ba daɗewa sai ga Hamma Abdullahi, Ummu ba ta ji wani fargaban zuwan shi ba tunda shi ɗan ba ruwan mu ne ɗakin Ammah ya leƙo duk da sun daɗe ba su haɗu ba, ko a fuska bai yi mamakin ganin ba, ballatana ya fahimci tana cikin wani hali.

"Ina kwana Hamma"

Ummu ta faɗa tana gyara zamanta kallonta ya yi kafin ya ce" Aa Ummu ke ce?
Sai ta gyaɗa mata kai.
Gaisawa suka yi sannan ya tambayi Amma sai ta ce tana wanka ficewa ya yi duk da ya yi mamakin ganin Ummu da mijinta tare da ƙanin mahaifinsa ya san da matsala amma bai tsaya tambayan matsalan ba, mgana ya zo su yi da Baffa amma ganin sa da ɓaki ya sa kawai ya bar gidan, ƙarin mamakin shi ganin har da Baffa Umaru ya ta so daga Mubi lamarin ya girmama a cikin zuciyarsa dai ya yi fatan koma mene ne Allah ya daidaita.

Kafin Amma ta fito wanka Baffa da kansa ya leƙo falon Ammah ya kira Ummu, hijabin ta sanya sannan ta bi bayan Baffa zuwa cikin ɗakin sa. Kan ta a ƙasa ta shiga cikin ɗakin a gefen su Baffa daga hannun dama ta zauna a saman cafet sannan ta ɗan ɗago kanta tana gaishe da Alhaji Sheriff wanda ke zaune shima a ƙasan cafet gefen shi kuma Habib ne ƙansa na ƙasa kamar na gari.

"Lafiya lau, kina lafiya dai ko?

Alhaji Sheriff ya faɗa bayan Ummu ta gaishe shi.
Kanta na ƙasa ta amsa da lafiya lau.
Bayan buɗe taro da addu'a, da Baffa Umaru ya yi sai ya maimaita abin da Baffa ya kira shi ya sanar da shi kan matsalan da ke faruwa tsakanin Ummu da Habib.

"Tabbas haka ka kira ni ka faɗa mini nima, nima na kira shi na yi masa mgana. Saboda ma a samu daidaito shi ya sa na ce gwara mu haɗa su gabaɗaya."

Alhaji Sheriff ya faɗa Baffa Umaru ya amsa da haka ne Baffa dai na gefe bai saka baki ba, Habib kuma kansa na ƙasa bai ɗago ba sai yanzu ya fahimci Ummu ta ɓoye ma iyayenta wasu abubuwan. Sai da ya murmusa lalle ta yi kuskure wataƙila da ta sanar da su duka abin da ke faruwa da sun sauƙaƙa mata wasu abubuwan da suke jiran ta anan gaba.

"Yanzu maganar zubar da ciki ba ta, na yi masa faɗa sosai kuma ya yi mini alƙawarin in sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba"

Alhaji Sheriff ya sake faɗa cikin taushin murya, Ummu ya sake kallo kafin ya cigaba da cewa" Ki yi haƙuri kin ji ko?
Sai ta gyaɗa kanta hawaye na kece mata ta saka gefen hijabin ta share da sauri.

"To Alhamdulillah mun ji daɗin da aka samu masalaha cikin lokaci. Kai Habibu abin da ka yi ba ka yi daidai ba tunda har cikin nan ya shiga ba ku ɗau wani mataki daga farko ba, to sai dai ka yi hakuri Ummu Salama ta haihu, daga baya in kuka zauna kuka samu fahimtan juna za ku iya bari sai a lokacin da kuka sake shiryawa ku sake haihuwa wannan tsarin ku ne, ba ruwan mu a ciki amma mganar a zubar da ciki bai yi daidai ba kuskure ne mu kuma a matsayin mu na iyayen ku ba za mu bari ku kauce ma hanya ba shi ya sa muka shiga ciki domin mu samar muku da masalaha kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu."

Habib ya yi shuru yana sauraran Baffa Umaru har ya gama jawabinsa.
Baffa da ba zai yi mgana ba Baffa Umaru ya ce ya ɗan tofa wani abu mana.

"Ni ba ni da wani abin da zan ce duk abin da zan faɗa kun gama faɗa sai dai ba zan fasa tunsar da su abubuwa guda uku zuwa huɗu ba."

Habib ya kalla sannan ya kira sunan shi.

"Habibu."

Sai da ya ɗago kansa sannan ya amsa da Naam Ummu ma ya juya ya kira sunan ta.

"Auta."

"Naam Baffa."

"Ku sani aure ibada ne, kuma shi da man ibada sai an ɗaure za a samu riba, dukkan ku saboda kun aminta da juna kuke zaune a inuwa ɗaya na aure. To ina so ku sani sai kun yi hakuri kun girmama junan ku , sannan za ku samu fahimtar juna. Ku sani ibadar da kuke yi sakamakon ku na wajen ubangijin ku, saboda haka in kuka yi wani abu saɓanin umarninsa ma duk yana sama yana kallon ku. Daga karshe ina mai sanar da ku da cewa ku ji tsoron Allah. Ku zaauna lafiya ku girmama zamantakewarku Allah ya yi muku albarka ya sake kaɗe fitina a tsakanin ku."

Gabaɗaya su Baffa suka amsa da Amin, Ummu ma ta amsa a cikin zuciyarta Habib ne bai amsa ba domin kalaman Baffa sun shiga ne sun kuma fita, domin gani yake yi kamar ba su da amfani a wajen shi, bai so ya yi magana ba sai da Alhaji Sheriff ya ɗan zungure shi sannan ya ɗan yi gyaran murya yana faɗin.

"Ku yi haƙuri Baffa in sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba."

Habib ya fada yana ɗan cije baki, Baffa ya ɗan jinjina kai kafin ya ce" Na ji daɗin haka. Ubangiji  ya zaunar da ku lafiya."
Zaman bai wani ɗau lokaci ba tunda an samu matsaya, Baffa ya ce Ummu ta tashi ta bi mijinta ta koma gidan ta, tun da dalilin da ya kawo su an samu masalaha, Ammah ba ta fito ba kuma Habib bai neme ya shiga ya gaishe ta ba suma su Baffa ba su buƙaci haka ba, Ummu kaɗai ta shiga ta yi ma Ammah sallama.

"Ki kula da kanki kin ji ko?

Sai ta gyaɗa ma Amma kai kafin ta ce" In sha Allahu Ammah"
Daga nan suka yi sallama har ƙofar gida su Baffa suka raka su, Alhaji Sheriff ya shiga motarsa shi ya fara tafiya sannan su daga baya, har sun shiga mota Baffa ya ƙwanƙwasa ma Habib gilashin mota ta bangaren sa, bayan ya zuge gilashin Baffa ya kalle shi lokaci ɗaya yana kallon Ummu kafin ya kira sunan shi.

"Habibu"

Ya amsa ƙansa na ƙasa amma a cikin zuciyarsa faɗi ya ke yi an fa dame ni

"Kai ne da kanka ka zo ka ce kana son Auta na kuma ba ka ita cikin yaƙinin cewa za ka iya riƙe mini ita amana. Ko ba haka ba?

"Haka ne"

"To ina so ka sani amanarta da na baka tun ranar da ta tashi a ƙarƙashin ikona na ke so ka sake tunawa. Habibu kar ka saka na ji na sare bisa yaƙinina akan ka, don Allah ka riƙe mini Ummu bisa amana da gaskiya."

Baffa ya ƙarishe faɗa cikin magiya, Habib ya kalle shi yana masa mirmishin yaudara da bai kai zucci ba kafin ya ce" In sha Allahu Baffa"
Baffa ya ji daɗi har ya miƙa masa hannu suka sake musabaha yana ɗaga musu hannu suka bar ƙofar gidan  Baffa Umaru yana gefe kamar an kira shi a waya ne yana ta mgana.

Suna fita daga kwanar anguwan Habib ya kalli Ummu kafin ya ce" Me ya sa kika ɓoye ma iyayenki gaskiyan manufata a kan aurana da ke?
Ummu ta ɗago tana kallon shi cikin mamaki murna take yi na ganin komai ya daidai ta tsakanin ta da Habib amma kalamsa sai suka ruguza murnan ta da saka ranta.

"Me ya sa ba ki faɗa musu cewa bana son ki ba sannan kin rufe musu ba auran soyayya na yi da ke ba, auren shaa'awa ne. Me ya sa ba ki sanar da su gaskiyan mganar ba?

Ya sake jefo mata tambayoyi, kanta na ƙasa tana wasa da gefen hijabinta ta ce" Saboda ina tunanin ba gaskiya ka faɗa ba, kana dai fadin haka ne saboda na ƙi bi umarnin ka na zubar da cikin jikina."
Habib ya kece da wata dariya kafin ya ce," Har yanzu ke a tunanin ki wasa na ke yi dake Ummu Salma?
Lalle ko ba ki da hankali na kuma yadda ke ɗin shashasha ce."

Ya fada har yana buga sitiyarin mota, Ummu ta kalle shi idanuwanta da hawaye kafin ta ce" Ka kirani da kowani suna ban damu ba. In dai har zan cigaba da zama a ƙarkashin ka, sannan zan tsira da cikin jikina na yarda ka kirani da kowa ni suna har wanda ma ya fi shashasha"

Kallon ba ki da hankali yake yi mata ita kuma kawai sai ta kece masa da kuka.

"Habib ka san ina son ka? Kai ma kana sona me ya ka sauya! Ni ce fa Ummu salman ka?

Ta ƙarishe faɗa cikin kuka, sai ya sake yin dariya kafin ya ce" Lalle ba ki da hankali."
Haka kawai ya ke faɗa lokaci ɗaya yana kallonta kuma yana dariyan haushi da takaici.

"Na ji ba ni da hankali in dai akan ka ne Habib. Na ji ka ma ce na haukace duk na yarda da haka amma don Allah ka saurara mini haka nan na azabatu don Allah Noori."

Yadda take marairaicewa ne ya sake tunzura shi, a fusace ya daka mata tsawa.
"Wallahi bana son ki, bana sha'awan sake wani sauran zama a tsakanina da ke."
ƙasaƙe Ummu ta yi tana kallon shi hawaye na kece mata wasu na zuba wasu na sake tunkuɗowa.
Gefen titi Habib ya gangara ya kashe motan ya gyara zama yana sake kallon Ummu tana kuka kamar ran ta zai fita.

"Ko zuwa gidanku da kike ganin na yi kina jin daɗin watakila na sauka daga kan kudiri na ne, to gwara ki daina murna ki dawo cikin hayyacin ki, sannan ki sake buɗe kunnuwan ki da kyau ki saurare ni."

Ya faɗa yana karkaɗa kunnunsa guda ɗaya sannan ya cigaba da faɗin" Na bi umarnin Abba ne saboda shima nan gaba zai yi mini wani amfani saboda ke kuma ba zan ɓata gobe na ba, amma wallahi tallahi ban sauka daga kan kudirina ba. Bana son ki sannan ba na son cikin dake jikin ki, sai dai ina so ki sani daga yau ba zan sake matsa miki akan zubar da ciki ba da kanki za ki yi nadamar taurin kan da kika yi mini. Ke ba ki ga komai ba yanzu ne za a fara wasan Ummu Salama."

Ya ƙarishe faɗa yana yi mata wani irin kallo har yana kashe mata ido ɗaya.

"Ka san da haka me ya sa ka amsa ma  Baffa da cewa za ka riƙe ni bisa Amanar da ya ba ka?

Ta tambaye shi cikin kuka, ƴar dariya ya yi kafin ya ce" Ummu in kin koma gida ya kamata ki koma makaranta ki yi karatu mai zurfi wataƙila zuwa lokacin za ki fahimci komai."
Kallon ban gane maka ba ta yi masa sai ya girgiza kai lokaci ɗaya ya ta da motar suka fara tafiya.

"Har sai na faɗa miki maganganun babanki da na yayansa ne ma ko ƙaninsa duk sun shiga ne sun fita? Sai na faɗa miki ni da man ban karɓi amanarki tun farko ba, abin da ya sa na aure ki jikin ki, kuma sadaki na biya sannan more komai, ai amanar kenan bayan na gama amfana dake zan mayar masa dake gidansa."

Ummu ta yi ƙuru tana kallon Habib, hawaye suna kwaranya a saman kumatun ta.

"Don Allah kar ka rabu da ni Habib.'

Ta faɗa cikin matsanancin kuka.

"Kar ki damu da sauran lokaci ai ba ki gama yin nadama ba. Sai na tabbatar da kin yi nadaman taurin kan da kika yi mini sannan zan ba ki sakamakonki ki ƙara gaba. Wataƙila a lokacin za ki ji kin tsane ni har ki fahimci da gaske na ke

Please Login or Register in order to submit comment