Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

godiya.
Wani dogari ke ta amsawa.

Ba su daɗe a fadan ba Mai Martaba ya ba da Umarnin Hakimin Daura ya raka Yarima zuwa bangarensa domin ya huta.
Bangaren Yarima in da yake sauka in ya zo Daura. Shashe ne mai girma a cikin masarautan.

Har kofar shashin Saleem ya raka shi.
"A fito lafiya Ranka ya daɗe."
Kai ya jinjina masa kafin su rabu shi ya juya shi kuma ya shige ciki tuni falon ya cika da hadimai mata wasu na jera abinci wasu na shigowa da shi.

"Barka da sauka Yarima. Barka da isowa ranka ya daɗe."
Magajiyar hadiman Fada ta faɗa cikin ladabi bayan ta zube kasa, haka ma sauran hadimai mata suka yi suna mai zubewa a gaban shi.

"Yauwa na same ku lafiya?
Ya faɗa a iya fatar bakinsa sannan ya shige wani korido.
Ba wacce ta sake motsi sai da ya nisa da in da suke sannan Magajiyar hadimai ta miƙe tana ba su umarnin su yi sauri su jera komai Yarima ya shigo.

Dattijuwa ce ita ce shugaban hadimai mata na gidan Sarki gabaɗaya, sannan amintataciya ce a wajen Uwargidan Maimartaba Gimbiya Shahida da umarninta ne ta ce ta yi jagoranci a tanadar ma Yarima da iyalansa duk abin da za su nema.
Cikin lokaci suka gama shirya komai suka bar shashen gabaɗaya.

Shi ko Lamiɗo ɗakin shi na musamman ya shige ya yi wanka ya ɗan kwanta. Shashen na da girma ga dakunan barci ne ba adadi shi ya sa har ya yi barcinsa ya samu natsuwa ya tashi kafin La'asar bai ji ko motsin Balkisu da yara ba suna wani shashe a cikin bangaren na dabam ita da su Sabuwa.
Alwala ya yi ya fita sanye da jallabiya fara wannan karon sai ya dora rigar sarauta mai ruwan zuma haka ma hulan kansa ta sakin gidan sarauta ne haka ma takalmin kafarsa na irin takalman da yayan sarakunan kan saka ne, ga kaya nan birjit a cikin clothset dinsa na bangaren gidan Sarki sai wanda ya zaba sai saka.
Yana fita suka haɗe da Saleem shima da shirin zuwa masallacin.

"Barka da fitowa Ranka ya daɗe."
Lamido bai yi magana ba amma ya jinjina kai.
Yana daga cikin shaidar da ya samu, Lamido mutum ne mai daraja lokacin salla bai taba zuwa garin Daura ya yi fashin salla cikin jam'i ba.
Tare suka yi salla da Mai martaba a sahun gaba sai karamin kanin su Mujahid(Amir) ɗan shekara goma sha shidda , Mai martaba ransa fes ga shi zagaye da yaran shi maza yamma da kudu.

Bayan an idar da salla limamin masallacin ya yi ɗan tunsarwa akan zumunci da falalar nasu sada shi, daga nan Lamido da Saleem suka koma bangaren shi duk da jama'a na son ganin shi amma Hakimin Daura ya ce Yarima na hutawa ne sai zuwa gobe.

Tare suka ci abinci a bangaren Lamiɗo  kamar yadda suke yi in ya zo garin tare da Mujaheed da suka taho tare da shi, ita Balkisu sun riga sun ci na su abincin tuni har an raka ta shashen ɗakunan matan gidan daga ƙarshe ta ci burgi a bangaren Fulanin Daura.

Bayan sun gama cin abincin sun ɗan natsa Lamido ya sauya kaya farar shadda har da babban riga, kayan da in ba a Daura ba, ba ya mu'alama da su.
Da rakiyar Salem da Muhajeed ya fara isa bangaren Uwar gidan Mai martaba yar kuma tsohon wazirin Daura.
Gimbiya Shahida, ita ce mahaifiyar Saleem kuma ita ce Fulani ta aura ma Mai martaba lokacin yana tare da Fatima.

Gimbiya Shahida ya'yanta huɗu ne uku mata namiji ɗaya. Sakeena ce babba tana auran jakadan nageria a England.
Tana can tare da iyalanta(ita ce kuma ke da sarautan Magiyar Gah mata na garin Daura)
Sai Munnira(Magajiyar Hah matan garin Daura) auren zumunci aka yi mata tana auren yaron Hajiya kilishi yayar Mai matarba Sarki Nasiru. Sai Saleem Hakimin Daura, sai auta Badi'atu wacce ba ta daɗe da yin aure ba.

Ba su wani jima a shaahenta ba bayan gaisuwa da yi masa maraba ya yi mata sallama sai kuma bangaren Gimbiya Hadiza wacce ke bin ta.
Ita kuma ya'yanta uku. Ita ɗin jikar sarkin Kano ce.
Hajiya Sadiya(Bata tuman Daura) tana auren yaron Wambai ne, suna kasar portugal da zama.
Sai Hajiya Zainab(magajiyar Jah mata)
Tana aure anan cikin garin Daura, sai Hajiya Safiyya(Yakumon Daura) tana aure a masarautar Gusau. Itama bayan gaisuwa suka bar nan zuwa shashen mai bi mata.
Gimbiya Maimuna ɗiyar marigayi sarkin katsina da ya rasu.
Ya'yanta uku
Yazeed(ɗan ruwatan Daura hakimin Babban mutum) yana can kasar waje yana karatu. Sai Sagir(ɗan burum ɗin Daura) shima yana can kasar wajen yana karatun lauya. Sai Auta Hafsat tana sakandiri.

Sai shashen ta karshe Gimbiya Amratu.
Ita kuma kakanta ƙani yake wajen marigayi Mai martaba Sarki Muhammad shitu kenan kakkani suka haɗa da Mai martaba sarki na yanzu, ita ɗin yar Daura ce kuma yar masarauta.

Yaranta biyu ƙanana ne Mujaheed(Amir) da Mujadala(Amira)
Nan ma gaishe ta suka yi suka fice, lamarin mulki da saurata sai wanda aka haifa a cikin shi ko gaisuwan ma ba wani mai yawa ba ne, shike nan an yi an gama.

Daga nan sai suka ci burki suma a katon bangaren yar Sarki jikan Sarki, matar Sarki sannan uwar Sarki.
Hajiya Raƙayya(Fulani Daura).

Fulani na da mayan ya'ya mata amma namijinta kwara ɗaya ne Mai martaba Muhammad Nasiru Daura, duk da a wancan lokacin maigidanta Marigayi mai martaba tsohon Sarki yana da wata matar kafin ita mai suna Hajiya Rakiya.
Tana da ɗa namiji babba amma an haife shi ba shi da lafiya daga karshe ma ya rasu bayan mahaifiyarsa ta rasu ba daɗewa.

Akwai yaranta biyu yayyen Mai martaba ne da Fulanin Daura ta riƙe su.
Hajiya Kilishi ita ce babba kuma tana da sarautan(Magajiyar garin Daura) Tana kuma auren shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin katsina ne.

Sai Hajiya Balaraba(Magajiyar zama Daura) Tana auren wani babban general ne a hafsan sojan ƙasa tana zaune a garin Abuja da iyalanta.
Sai ya'yan Fulani ƙannen Mai martaba mata
Wacce ke bi ma Mai martaba Hajiya Zaliha wacce Lamiɗo ke kira da Mahma ita ce(Magajiyar sanda mata)
Kuma tana auren madakin masarautar Zazzau ne tana can garin Zariya.
Ita ce kamar 5 and 6 na Mai martaba Sarki komai zai yi sai ya yi shawara da ita ga shi ba ta taɓa haihuwa ba shi ya sa take son Lamiɗo kamar ran ta.

Sai mai bi mata, Hajiya Zeenatu(Magajiyar Gabas)
Tana auren shugaban yan sandan na ƙasa gabaɗaya.
Sai Hajiya Zannura,(Magajiyar Yamma)
Tana auren ɗan sarkin Katsina. Sai ta ƙarshe Hajiya Binta(Magajiyar sha wata Daura)
Tana auren ɗan sarkin muslmin garin sokoto ne can take zaune da iyalanta.

Fulani an tsufa amma jinin mulki na nan a jikinta ko da suka shiga tana kishigiɗe Sultan da Beena na jikinta kamar za ta mai da su cikin ta saboda so.
sun iske su suna ta hira da Balkisu, wacce Saleem ya rankwafa shi da Amir suka gaisheta ta amsa cikin sakewa.

"Maraba da Yarima. Maraba da Muhammadu Lamiɗo."
Fulani take faɗa cikin farincikin da ya saka ɓoyuwa a saman fuskarta.

"Ranki ya daɗe ga Yariman Daura nan na kawo miki mene ne tukwaici na?
Saleem ya faɗa yana zama a shimfidar da take zaune.

"Na baka farin doki na Hakimin Daura."
Ta faɗa cikin fara'a shi ko sai ya washe baki yana faɗin" Hakimin Daura yana godiya. Allah ya kara tsawon kwana Fulanin Daura."
Tana son farin dokin nan ta ce gadon shi ta yi wajen babanta ba ta bari kowa ya hau in ba Mai martaba ba, amma yau ta yi masa kyautarsa saboda zuwan Yarima Lamido.

"Barka da hutawa ranki ya daɗe."
Lamido ya faɗa yana mai zama a gefenta cikin ladabi.
"Papa."
Sultan da Beena suka faɗa a tare ganin babansu, Saleem ne ya amsa musu yana mai jawo su jikinsu sun san shi tunda ai suna yawan zuwa in Lamido bai zo ba Balkisu na zuwa in ta samu dama.

"Lafiya lau Yarima, ya wajen su Baffan naka?
Ya amsa mata duk suna lafiya cikin girmawawa.
"Barka da zuwa Muhammadu Lamiɗo. Masarauta ta ji daɗin zuwan ka"

Mirmishi kawai ya yi bai yi magana ba
Bilkisu tafiya ta yi ta bar su tare da Fulanin Daura.
Da yaran nan fa ta shiga abin da ta saba tana ta ba su labaran tarihin masarautan Daura da ya shude shi dai Lamiɗo zaune yake amma ba ya ma jin ta, kanshi har ya fara ciwo Saleem kuma yana ta su Sultan ne Amir ne ke mata tambayoyi.
Kiran mangariba ya fitar da su daga shashen Fulani.
Da suka fita salla har wajen tara na dare Lamido na waje yana gaisawa da mutanen fada.

Goma saura na dare Lamiɗo ya shiga keɓantattacen ɗakin Mai mairtaba na cikin turakansa a shashensa.
In da za su yi ganawar da suka saba daga shi sai shi sai Allah in dai ya zo garin.

Bayan sake gaisuwa.
"Ya wajen iyayen naka na Adamawa?
Maimartaba ya tambaya yana zaune a saman wata darduman dake cikin ɗakin barcinsa.
Sanye yake da jallibiya ba rawani a jikimsa sai fuskarsa ta bayyana kamar ta Lamiɗo, sai dai ya nuna masa yarinta da cikar maza amma har yanayin maganarsu ma iri daya ne, sai dai shi Lamido fari ne yayin da Mai martaba yake da duhu amma ba baki ba ne sosai.

"Duk suna lafiya sun ce a gaishe ku."

"Muna amsawa. '
Daga nan ɗakin ya yi shuru na wani lokaci.
Sai da Maimartaba ya kira sunan shi sannan ya dago.

"Muhammad Lamido."

''Allah ya taimake ka."

"Don Allah ka dinga zuwa gida akai- akai.  Kar ka manta kai ne Yarima mai jiran gado, ka zo gida domin ka koyi sarauta tun kafin ta Allah ta kasance a kaina."
Mai martaba ya faɗa cikin wani irin amo.

Kan Lamido na kasa bai yi magana ba

"Shekaru sun gangara Lamido. Ya kamata ka yi tunani."

"Allah ya kara maka yawancin rai,"

Lamiɗo ya faɗa kafin ya ɗan yi shuru.

"Zan din ga zuwa"
" in sha Allahu."
Ya sake faɗa a rabe,
Jinjina kai Mai martaba ya yi kafin ya ce" Na ji daɗin haka. Allah ya yi ma rayuwarka albarka."

"Amin."

Lamiɗo ya amsa a kasan lebensa.

"Ya wajen aikin naka?
"Alhamdulillah."
Lamiɗo ya sake faɗa.
"Madallah. Ina ita iyalin naka? Ina takwara na? Ina jiran shi zan yi masa hakimi dawakin Daura nan gaba in ya sake girma."

"Allah ya taimake ka."

"Suna cikin gida,"

"Za su zo gaishe ka da safe in sha Allahu."

"Allah ya tashe mu lafiya."

Maimartaba ya faɗa cikin ɗan mirmishi.

Sai kuma ya yi shuru.
Dakin ya yi wani tsit kamar ba kowa a ciki.

"Sultan har yanzu yaro ne"

Mirmishi Mai martaba ya yi na manya da masu sarauta yana kallon ɗan na shi.

"Na ce in ya kara girma Lamiɗo."

Ya faɗa yana kallon sa.

"Tuba na ke yi ranka ya daɗe."

"Ba ka yi laifi ba Lamiɗo."
Ya sake faɗa yana kallonsa. Fuskar Batula na gilma masa.

"Ya wajen Batula?

Lamiɗo ya dago yana kallon mahaifin na shi.
Ya san wace ce ya ke kira Batula ba kuma mamaki ya yi ba domin in dai suna magana da Mai martaba sai ya yi hiran Batula.

"Ka je wajen ta?

Ya tambaye shi cikin kulawa.

"Ban samu zuwa ba ranka ya daɗe."

Ya faɗa yana ɗan sosa giran shi.

"Lamiɗo."

Ya kira shi ya amsa.

"Allah ya ba ka nasara."

"Muhammadu."

Ya sake kiran shi a karo na biyu.

"Allah ya ba ka yawan rai."

Lamiɗo ya sake faɗa cikin rusunawa.

"Ka bi Batula. Ka yi ta bin ta domin ita ɗin mahaifiyarka ce."

"To in sha Allahu."

"Duk yadda za ta nuna ma duniya ba ta damu da kai da abin da ya shafe ka ba. To ka sani tana sonka. Ta fi kowa sonka."

Lamiɗo ya yi shuru bai yi magana ba amma a zuciyarsa sai dai ya ce ba ta kai Ammah sona ba.

"Saboda ita ta haifeka. Cikin ka ta ɗauka na wata tara ta yi nagudar ka ta haifeka ta kuma rene ka."

"Ammah dai ta rene ni Allah ya ba ka nasara."

Ya yi saurin katse Mai martaba.
Domin shi dai da yawon sa Ammah ya sani a komai na shi ba Mami ba.

Mirmishi Ma imartaba ya yi har tana fidda sauti.

"Saboda tana sonka ne, ta ji zafin abin da aka yi mata shi ya sa ta cire ka daga rayuwarta. Amma Batula tana sonka Lamiɗo wata rana ko bayan raina za ka ga hakan."

"Allah ya taimake ka,.'"
Lamiɗo ya faɗa sannan ya cigaba da faɗin.
"Ammah ce uwata ranka ya daɗe ita ce ba ta taɓa wofantar da sha'anina ba har gobe."

Shurun ya sake yi kansa na kasa kafin ya cigaba da fadin.
"Amma ban musa cewa Mami ce ta haifeni ba. Amma ni Ammah ce na sani a mahaifiyata."
Mai martaba ya sake yin mirmishi cikin kasaita kafin ya ce" Ba shakka duka uwayenka ne Lamiɗo amma Batula ce ta haife ka "

"Tuba na ke yi ranka ya daɗe, in na faɗi wata magana ba daidai ba."

Mai martaba ya sake ɗan yin mirmishi kafin ya ce" Ba ka yi laifi ba Lamiɗo "
Sai ta sake kallon shi kafin ya ce" Magana ta shi ne kar don ba ta shiga sha'aninka kai ma ka daina shiga nata. Hakki ne a kanka, ka bita ka yi mata biyayya."

"In sha Allahu ranka ya daɗe."

"Allah ya yi maka albarka. Allah albarkaci zuru'anka Muhammadu Lamiɗo "

"Amin Allah ya kara maka lafiya da yawancin kwana ranka ya daɗe."
Shi kan shi Lamiɗo ba ya sanin a ina ya koyo wasu abubuwan na sarauta sai dai kawai ya samu kanshi cikin aikatawa.
Sun daɗe suna tattaunawa sai sha ɗaya da rabi Mai martaba ya sallamesa ya koma bangarensa.

Duk ya gaji ga ciwon kai da rashin natsuwa wanka ya yi ya sha tea kawai ya kwanta ko Balkisu bai nema ba saboda gajiyar dake jikinsa rabon shi da ita tun a falon Fulani.

Washe gari ma bai samu zama ba da shi aka yi zaman fada sannan da yamma kuma ya fita cikin gari shawagi a saman doki shi da Saleem da Amir.
Ya yi ta kuma ganawa da mutane, kuɗi ne bai san adadin su ba ya fita da su amma duk sun kare tun daga ma'aikatan gidan da dogarai haka ya yi ta musu alheri. Lamido is a giver duk da ba shi da fara'a amma yana da kirki da kyauta.

Tun da suka zo Daura bai zauna ba, kullum yana fada ko sun fita gari gabaɗaya ya gaji ya takura amma ba shi da mafita ranar da suka yi kwana huɗu ya fita shi da Saleem da wasu dogarai a dawakai ya sha rawani da kayan sarauta yana ta gaisawa da mutane.

Washe gari kuma Balkisu da yara tare da hadimanta suka koma Lagos.
Da shi da Saleem da wasu dogarai suka kai ta filin jirgin katsina.
Ta na so ta rumgumi mijinta saboda ta yi kewarsa amma ba hali yana cikin mutane kuma a halin Lamiɗo in ta rike sa a nan shi ne kunyanta shi na farko da ta taɓa yi a rayuwarsa.

Tunda suka zo bai samu lokacinta ba sai jiya da daddare da za su yi sallama.
Mamah ma ta zo daga zaria, ba ta kwana ba ta juya sannan shi kuma ya je katsina gidan Hajiya Kilishi shi da Saleem da wasu hakiman Mai martaba daga nan suka karisa masarautar Katsina suka yi gaisuwa Hajjya Zannura ba ta kasar ta raka mijinta domin a duba lafiyansa.

Ya ji maganar Mai martaba ya nemi Mami, da man kuma Ammah ta matsa masa ya je Kaduna ya gaisheta.
Sai dai ko da ya kira ta sai ta ce ba sa nan suna Zamfara ita da megidan da ya ce ya zo ne zai zo ya gaisheta kafin ya koma sai ta ce ta yafe masa gaisuwan

Bai damu ba domin ta ma hutar da shi, sai da ya shafe kwanaki goma a Daura sannan ya samu ya komawa Jimeta.

Gabaɗaya tunda ya je Daura bai huta ba, da ya dawo Jimeta ya yi hutu sosai domin akwai ranar da tun safe har dare bai zo gida ba Ammh ta ɗaga hankalinta gashi ana ta kiran wayarsa ba ya ɗauka.  Ta kira Hamma Abdullahi sai da ya je gidan ya gano mata, lafiyansa lau kawai yana barcin gajiya ne. Sannan hankalinta ya kwanta.

Bai koma Lagos ba sai da ya yi hutun wata ɗaya cur duka a haɗe da zuwa Jimeta da Daura.
Washegarin ranar da ya koma Hamma Abdullahi ya kawo atamfofi guda hamsi cur daga Lamiɗo Ammah ta raba ma yan'uwa da dangi sannan an cika store din Baffa da kayan abinci sannan an siya masa sabuwar mota camry, Amma kuma ya siya mata waya sabuwar kiran samsumg sannan ya ce ta shirya za ta je Umra.

Ammah sai kuka kukan farinciki, da man in zai yi musu abu sai ya bar garin a cewarsa ba ya son godiya.
Da Ammah ta kira shi a waya tana ta masa addu'a.
Ya dinga amawa da Amin yana faɗin" Ammah ki je Madina ki yi addua'a sannan ki samu natsuwa."
Shi duk ƙokarinsa tana cikin damuwa ta tafi can ta samu natsuwa.

"Na gode Lamido. Ubangiji ya yi maka albarka "
"Amin Ammah ta."
Baffa ma da ya kira shi sai ya ce masa" Na gode Lamiɗo amma ni ba Ammah ba ce godiya zan yi ba sai na yi kuka ba."
Baffa na ta dariya shima sai da ya murmusa.

"Na gode Baffa. Allah ya kara girma."

Kalamansa kenan domin har abada ba zai iya biyan abin da suka yi masa.
Hamma Saddam ma dake makaranta an shaka masa kuɗi tunda Ummu Salma ta ga yana ta yin status yana wasa Hamma Lamido, har su Hamma Abdulrahaman duk sun samu kyautar ban girma Ummu Salma ce ko abin da ba a so bai ma nuna ya san tana gidan ba.
Itama ba ta damu ba, wani abun duniya yanzu duk ba ya gabanta halin data ke ciki kawai ya ishe ta.
Har kuma ya gama zaman shi ya koma ba ta yarda sun sake haɗuwa ba.

Tuni Ammah ta shiga rabon zannuwa, na mutanen Mubi sama da guda ashirin Ummin ikki da yayanta matan su Hamma Jibo duk ta aje musu, har Ummu an ba ta turmi ɗaya ta karba domin in ta ce ba ta so Ammah za ta yi mata masifa shi ya sa ta karɓa ta ajiye.
Addu''oin godiya da fatan alheri kam Hamma Lamiɗo na shan su.

Mami ta aiko ma da Ummu Salma waya sabuwar samsumg iri ɗaya da ta Ammah har da sabon layi.
Da ta fara amfani da wayar amma ban da lambar yayyenta da ta Mami sai ta Baffa da Ammh sai na Baɗdo da shamsiya ba ta da ta kowa, wayar ma da komai duk sun fita kanta ita dai gata nan ne tana dai rayuwa. Ba ta buɗe whatsApp ba balle tiktok wayar ce kawai a hannunta.

Ta fara zuwa awo Hamma Abdullahi ke kai ta tare da Ummin ikki. Karfin addu'a da kulawan mutane ya ke riƙe da Imanin Ummu amna fa zuciya ta raunana, wani rami ne a zuciyarta wawake da Habib ya yi mata haƙon shi, taɓo ne da ba zai taɓa warkewa ba.

Tafiyan Ammah zuwa Umra ya tashi sannan ta Lagos za su tashi ana ta shirye-shirye.
An yanke shawaran Mami za ta zo ta tafi da Ummu, tuni har ta haɗa kayanta tana murnan tafiya Kaduna.

Ana cikin haka ne mijin Mami Alhaji Isa ya yi hatsari  ya samu karaya a kafarsa an ba shi gado a asibitin 44 dake Kaduna. Mami ba ta da natsuwa sai kawai Baffa ya ce Ummu ta yi zamanta duk da Mamin ta so ta je amma Baffa ya hana wannan karon da cewa tana da majinyaci ta zauna ta kula da shi.
Shikenan tafiya Kaduna ta sha ruwa, Ummu ta so ta yi nesa da garin Jimeta amma tunda Allah bai so ba sai ta hakura. Da Hamma Abdulrrahman har cewa ya yi ta koma gidan shi da zama har Ammah ta dawo sai ta yi tunanin ai ga Baffa a gida gwara ta yi zamanta kawai.

Ammah ma ta kawo ƙorafin a asibiti an ce ta huta kar ta yi aikin wahala ita kuma ta dage za ta iya domin tana ganin cewa har zuwa yaushe ne za ta yi ta zama takura da lalura ga yan'uwanta da iyayenta,? Shi ya sa ta ɗau niyyar canzawa domin samar ma da zukatan dake zagayeta da ita salama.

Hamma Abdullahi ne ya raka Ammah har lagos gidan Hamma Lamiɗo ta sauka baya ma nan ya fara aiki da sabon kamfaninsa, amma an gama dukkan komai kwana biyu Hamma Abdullahi ya yi a Lagos sannan ya dawo bayan a safiyar ranar jirgin su Ammah ya daga zuwa Jidda.

Da man da Hamma Saddam na nan ne shi zai rakata to in baya nan Hamma Abdullahi ne komai na gida duk wanda zai yi sako ma ta hannunsa ne. Kafin tafiyar Ammah Ummu ta roke ta da in ta je ta yi mata addua a ka'aba Ammah ta ce tana daga cikin dalilin da ya sa ta yi farinciki da Lamiɗo ya biya mata Umra. Ta tafi da niyar za ta yo ma Ummin addu'an Allah ya ba ta dangana ya sauketa lafiya sannan ya sauya rayuwarta daga kunci zuwa farinciki.

Sannan ta bar ma Ummin ikki amana duk da ga Baffa a gida. Kuma ta karɓa tunda kullum za ta zo ta duba Ummu, Baɗdo ma tana zuwa sosai kuma tana jin daɗin ganin yanayin Ummun na sauyawa.
Makaranta ne ma yasa ba ta kwana tunda bayan ta gama ND Sai wannan shekaran ne ma ta ɗora Degree ɗin ta(HND).

Tun bayan tafiyar Ammah Ummu ce ke da alhakin gyaran gida da yin abincin Baffa na ganin ba za ta iya ba sai ga shi ta ware, kuma sai aikin ya ɗan rage mata damuwa balle ma da take yiin girke-girke kala kala, abin da ba ta gane ba ta ɗau wayarta ta faɗa Youtube ta duba.

In Baffa na gida ya yi ta kambama ta komai ta yi ta bashi ya yi ta santi.
"Auta shi kuma wannan abin da me kika yi shi?
Ita kuma tana jin daɗin in yana santi sai ta zauna ta yi ta faɗa masa yadda ta yi.
Haka ma Hamma Abdullahi in ya zo gidan ta yi wani abin ta zuba masa.

"Ummu da me wai kika yi wannan?
Haka yace ranar da ya zo da safe ta yi musu Naan bread, mai nama a ciki shi da Baffa suna santi ita kuma tana jin daɗi.

Haka ko su Adda Suwaiba suke cewa in suka zo gidan, ita ce yi musu kosan rogo, wainar fulawa, gurasa fanke cake da su samosa tunda duk abubuwan baking ɗinta suna nan ɗakin cikin kayanta kawai buɗewa ta yi ta ɗauko su tana amfani da su.

Cikin wata ɗayan da Ammah ta yi a Saudiya Ummu ta sauya ta ware ta fara maida jikinta ga cikinta ya turo wattani biyar har da wasu kwanaki tana kuma zuwa asibiti in lokacin awonta ya zo.

Zirga-zirgan da take yi da kai da kawo sai ya rage mata tunani, sannan ta dage da addu'a in ta ji damuwa ko tunanin Habib yanzu za ta kunna karatun Qur'ani tana bi tana saurara tana aikinta.
Kowa ya zo ya ganta sai ya ji daɗin ganinta. Haka ma Ammah ranar da ta dawo ta ce Auta ta sauya ta yi kumari kamar ba ita ba.

Ta Lagos din Ammah ta sake sauka, sai da ta huta a gidan Hamma Lamido sannan ta dawo Jimeta. Itama ta yi shar kamar ba ita ba.
Tana cewa me Baffa ke ci da ba ta nan ta ga ya yi kiba ne.
Shi kuma ya ce itama da ɗanta ya biya mata Umra ta tafi ta barshi, to ai shima Auta nan nan na jiyar da shi kayan daɗi ana ta dariya.
Sai bayan Ammah ta dawo ne suka je Kaduna ita da Ummin ikki duba mijin Mami su Baffa tun lokacin da aka yi hatsarin suka je.

Bayan sun dawo Ammah ta ce Ummu ta haɗa kayanta ta je Kaduna. An sallami mijin Mami yana gida.
Lokacin Ummu ta ji ma gwara ta yi zamanta gabansu Baffa sai kawai ta ce ita ba ta son zuwa yanzu watakila sai nan gaba. Mami ta fahimceta ba ta matsa mata ba, suma su Baffa ba su matsa mata ba sun kyaleta ganin ta fara dangana da komawa kamar Ummu Salma farko kafin Habib ya shigo rayuwarta.




*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No. 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supplements wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai

Please Login or Register in order to submit comment