Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amayar da shi, tana cikin yiin aman ne Ammah ta shigo ɗakin har sai da ta leƙo ta.

"Sannu."

Ta ce mata sannan kumavta shiga ta kama ta bayan ta ɗauraye bakin ta, sai ta ce ta fita bari ta wanke wajen, kan gadon Ammah, Ummu ta faɗa tana ma yar da numfashi tas Ammah ta wanke tiolet ɗin sannan ta fito tana kallon Ummu da ke kwance kamar ruwa ba ta sake yin mgana ba ta kaɗa kai ta fice daga ɗakin. Ita kuma Ummu aman da ta yi duk ya sake sakar mata da jiki, kasalan da ta ke ji daga farko ya sake zuwa ya rufe ta da take jin ta kasa tashi sai kawai ta sake naɗewa a kan gadon Ammah ta jawo filo ta rumgume ta lumshe ido tana sauke numfashi sama-sama.

Daga nan sai barci ashe ta daɗe tana barci ba ta sani ba. Sai bayan azahar ta farka. A lokacin ta iya tashi sai dai ta ji yanayin jikin na ta ya ɗan saki tiolet ta shiga ta sake ɗauro alwala ta yi salla ta idar kenan tana kan darduma Amma ta shigo.

"Kin tashi?

"E Amma sannu da aiki "

"Yauwa, ga Baffan can ya dawo "

Amma ta faɗa lokaci ɗaya tana kallon Ummu.

"Ki ci abinci tukunna shima abincin yake ci."

Sai ta gyaɗa mata kai ba tare da ta yi mgana ba.

"Bari na yi wanka."

Haka Amma ta faɗa, lokaci ɗaya kuma tana tura kofar tiolet ɗin ta shiga. Shuru Ummu ta yi kafin ta yi saurin mikewa gwara ta je ta samu Baffa da maganar kafin Ammah ta fito daga wanka. Tana fita falo sanye da hijabin Ammah ta iske ta zuɓo mata abinci a kula da ruwa tana dubawa sai ta ga Dambun shinkafa ne da zogale. Allah sarki Ammah ta ɗauka har yanzu tana son dambun shinkafa da zogale ba ta san yanzu duk wani abu da take so a baya yanzu ya fita ran ta ba, amma ƙamshin gyaɗan da ke tashi a dambun ya sa miyan ta ya tsinke ba ta ci ba sai ta rufe da niyyar sai sun gama mgana da Baffa tukunna. Ta gode ma Allah da Hamma Abdullahi bai biyo ta gidan ba, ba ta son kowa ya san mganar nan sai Baffa ta fi amin ta da tunanin shi akan na kowa.

Sallama ta yi a ɗakin Baffa ba ta shiga ba sai da ya amsa mata.
Yana zaune a ƙasa a saman darduma yana cin dambun da Amma ta yi, gefe ɗaya da kunu da ruwa a saman wani faranti
Tana shigowa ya ɗago yana kallonta nan da nan ya faɗaɗa mirmishin sa.

"Autan Baffa"

Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai cire hannun shi a filet ɗin Dambun.
Itama cikin fara'a da farinciki ta zauna a gaban shi lokaci ɗaya tana faɗin.
"Baffa."
Ta faɗa cikin yar shagwaɓa, Baffa na dariya ya ce" Na dawo Amman ki ta ce kin zo kina tambaya na "
"To Baffa na yi kewarka ne. Ba ni da lafiya daga kai har Ammah ba wanda ya zo ya duba ni"

Da man ƙiris take jira sai hawaye, shi kuma ya shiga aikin lallashin ta da cewa suna shirin zuwa ne sai ga shi ta zo amma in ta koma zai matsa ma Ammah ta shirya su je su duba ta.

"Da gaske Baffa?

Ta faɗa tana kallon shi, shi dai ya je ɗakin ta sau ɗaya ɓarin da ta yi amma Ammah ba ta taɓa zuwa ba, shi ya sa take mamaki da ya ce mata za su zo.

"In sha Allahu."

Ya faɗa yana dariya, in ban da rigiman Ummu me zai kai su gidan ta, amma saboda ya san halin ta ya sa ya lallaɓata da za su zo, abincin ya ce ta zo su ci sai ta ce nata na ɗakin Amma, shima kaɗan ya ƙara ya ce ya ƙoshi. Ummu ta ɗauko masa wata roba ta zuba masa ruwa ya wanke hannunsa sannan ta kwashe kwanukan da ya yi amfani da su ta mayar kitchen ita saurin ta kafin Ammah ta fito ta sanar ma da Baffa abin da ke faruwa shi ya sa tana dawowa ta sake tankwashe kafafu a gaban shi tana kallon shi, yana kurɓan kunun sa lokaci ɗaya yana nazarin Ummu.
Tambayanta jikinta ya yi ta ce da sauƙi.

"Ya wajen shi Habibun? Fatan yana nan lafiya ko?

Habibin da ya ambata kamar ya yi mata fami ne, sai ta fara marairaicewa kafin Baffa ya sake mgana Ummu ta kece masa da kuka cikin tashin hankali ya ajiye kofin hannun shi yana kallon Ummu.

"Kuka Ummu? Me ke faruwa ne? Wani abu ne ya samu Habibun?

Ya faɗa duka a jere, kai ta girgiza masa kafin ta kira sunan shi.

"Baffa."

"Naam Ummu Salma."

Kukan ta ya ki tsayawa hawayenta suna zuba tana saka gefen hijabin jikinta tana gogewa.

"Me ke faruwa ne?

Baffa ya sake tambayan ta cikin kyakyawan lafazi.

"Baffa."

Kafin ya amsa ta cigaba da faɗin" Da ma, da ma ina da ciki ne."
Sai kawai Baffa ya washe baki yana faɗin" Ma sha Allah. Wannan ai abun murna ne ba na kuka ba Autan Baffa."
Kallon sa ta yi kafin ta ce" Baffa Habib ya ce ba ya son cikin fa"
Baffa ya zuru yana kallonta cikin mamaki kafin ya ce" Ban gane ba ya son cikin ba kamar ya ya?

Ummu-Salma ta sake fashe masa da kuka ƙasa-ƙasa ta kasa mgana.

"Kukan kuma dai Auta! In ba ki bar kukan nan ba ta ya ya za ki yi mini bayanin da zan fahimce ki?

Ya faɗa cikin damuwa saboda tunaninsa ya tsaya a dalilin kukan Ummu saboda mijinta Habib ne kuma ya shafi cikin jikin ta.

"Baffa kai kaɗai ne za ka iya taimako na. Shi ya sa na zo wajen ka."

Kai ya gyaɗa mata kafin ya ce" In sha Allahu Auta sai dai abin da ya gagare ni, sai na bar ma Allah ya yi na shi ikon."

"Baffa ina son Habib."

"Na sani."

Baffa ya ba ta amsa a ɗokance domin ya ƙosa ya ji dalilin Habibu na cewa ba ya son ciki.

"Ba na so na rasa shi, ko na rasa aurena."

"In sha Allahu alheri ne zai biyo baya Ummu-Salma.".
Ya kira sunanta, suna mai darajan da ba ya iya kira saboda sunan mahaifiyar shi ce sai dai ya ce Ummu ko Autan Amma ko Autan Baffa amma tun da ta ji ya kira sunan ta tasan wasa kuma ya ƙare.

"In ba ki yi mini bayanin abin da ke faruwa ba, ai ba zan iya taimaka miki ba Auta"

Tana kuka tana shessheƙa ta labartama Baffa abin da ke faruwa amma ta ɓoye maganganun Habib a kan ta na cewa ba ya son ta auren sha'awa ya yi da ita sannan ta ɓoye hanyoyin da ya bi wajen mata barazanar ta zubar da cikin, ta dai  faɗa ma Baffa zaman su ya lalace domin Habib ya ce in har ba ta bi umarninsa ba, yanzu suka fara yar tsama a tsakanin su.

"Innalillahi wa'innna ilaihirraju'un"

Baffa ya dire salatinsa cikin mamaki yana kallon Ummu yadda take kuka kamar ran ta zai fita.

"Baffa don Allah ka kira Habib ka yi masa faɗa na san yana jin maganarka. Ka faɗa masa ina son cikin nan ba zan iya zubar da shi ba"

Ta sake faɗa cikin kuka Baffa ya yi shuru lamarin na ɗaure masa kai , ina aka taɓa haka? Ka yi ciki da kan ka sannan ka dawo ka ce ba ka so sai an zubar.

"Don Allah Baffa."

Ta sake roƙon shi, tausayi ta ba shi Ummu ta faɗa cikin kaddaran aure tun tana da ƙananun shekaru.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Abin da ban gane ba, me ya sa ba ya son ciki? Mene ne dalilin shi na cewa sai an zubar?

"Baffa wai ba yanzu ya tashi haihuwa ba."

"Ka ji wani shirmen banza. Da man shi ke da wannan tsarin ba na Ubangji ba ne? Habibu ya ba ni mamaki ina ɗaukan sa mai hankali ashe kallon kitse na ke yi ma rogo ban sani ba?

Baffa ya faɗa cikin bayyana mamakinsa domin abin da ya yi, aikin jahilai ne mara sa ilimi da tarbiya.

"Tun yaushe ne kuka cikin wannan yanayin?

"An fi wata fa Baffa."

Ta faɗa tana cikin dashewar murya lokaci ɗaya tana share hawayenta da gefen hijabin jikin ta.

"Me ya sa tun a lokacin ba ki zo kin faɗa mini ko Amman ku ba?

"Baffa na ɗauka za mu iya warware matsalan ne da kan mu."

Baffa ya jinjina kai kafin ya ce" Ni lamarin ne ya ɗaure mini kai. Ban taba zaton haka daga Habibu ba."

"Nima ban yi zato ba Baffa."

Ta faɗa cikin sanyin murya.

"Ki yi hakuri Auta. Amma ba ni ne zan yi ma Habib mgana ba. Ta in da aka hau ta nan za a sauka."

Ya faɗa yana kallon ta, kafin ta yi mgana ya rigata da cewa." maganar ki zubar da ciki ma bai taso ba tun da lafiyan ki lau, saboda haka waliyin shi wanda ya karɓan masa auran ki za a yi ma mgana su za su kira shi su yi masa magana."

"Baffa me ya sa kai ba za ka yi masa da kan ka ba?

Kai tsaye Baffa ya ce" Maganar ba ta ni kaɗai ba ne, dole a sako waliyin shi a ciki "

Ummu ta yi shuru kanta na ƙasa Baffa bai fahimci abin da take tsoro ba. Kamar ya san abin da take tunani ya kalle ta yana faɗin" Ki kwantar da hankalin ki, Baffan ki Umaru zan yi ma waya shi zai kira waliyin na shi mu ji me zai ce."

"Baffa ina son Habib, ba na so a raba mu "

Ummu ta faɗa cikin karyewan sauti kamar za ta sake fashewa da kuka.

Baffa na shirin mgana su ka ji sallama, gaban Ummu ya amsa domin ta ji muryan Hamma Abdurrahaman.

"Ammah ko ba ta nan ne?

Ya faɗa daga tsakar gida, kafin kuma ya kariso ɗakin Baffa tun da ya ga motarsa ya san yana gida, balle ma ya yi waya da Ammah da safe ta ce ya fita tare da Abdullahi amma ba za su daɗe ba.

  Jikin Ummu ya fara rawa lokacin da Hamma Abdulrrahaman ya shigo ɗakin Baffa da sallama ta kasa iya ɗago idanuwana ma ta kalle shi, fatan ta ka da Baffa ya sanar da shi abin da ke faruwa.

"Abdulrrahman lale sannu da zuwa."

Baffa ya faɗa cikin mirmishi, shima Hamma Abdulrrahaman ɗin cikin fara'a ya amsa yana mai zama kusa da Baffa a saman darduman da ya ke zaune sai a lokacin ya kula da Ummu.

"Ke lafiya?

Ya faɗa yana kallonta kafin ya juya yana kallon Baffa.

"Baffa me ke faruwa ne?

Saboda irin zaman da ta yi ne ya sa ya ji kamar jikinsa bai ba shi ba.
"Lafiya lau. Ya aiki da wajen iyalan naka?
Baffa ya faɗa yana mirmishi, ya amsa da duk suna lafiya yana sake nazarin Ummu da ke dukar da kai kamar munafuka.

"Na zo nan kusa ne kan wata sharia da na kai ne a yanzu."

"Allah ya ba ka nasara."

Ya amsa da Amin.

"Ke jira kike ni na fara gaishe ki?

Hamma Abdurrahaman ya fada a ɗan zafafe.
Baffa ya yi saurin tare shi da faɗin". To sarkin ƙorafi yaushe mu ka gama gaisawar ballanta ma ta samu damar gaishe ka?

"Baffa kar ka kare mata, mintina na nawa da shigowa ɗakin nan?

"A yi haƙuri."

Baffa ya faɗa yana ɗan mirmishi.

"Hamma ina yini."

Ummu ta faɗa muryanta na rawa, lafiya lau ya amsa sannan yana sake kallon ta.

"Kin yi ciwo ne?

Ya faɗa daidai da ta tashi za ta bar ɗakin na Baffa.
Sai ta juyo tana kallon shi duk da ya ɗan kwana biyu bai gan ta amma ta lalace da yawa.

"Ta yi zazzaɓi kwana biyu."

Baffa ya amsa mishi, kallon shi ya yi kafin ya sake kallonta ya ce" Baffa wannan ya wuce zazzaɓi, idanuwanta da fuskarta sun nuna tana cikin damuwa."
Baffa na dariya ya ce" To lauya."
Shima sai da ya yi dariyan da haka Ummu ta so ta sulale Hamma Abdulrrhaman ya tsare ta da cewa ta dawo ta zauna  jikinta na rawa gabanta na faɗi ta koma ta zauna a in da ta tashi.

"Ke kina da wata damuwa ne?

Ya faɗa yana mai tsare ta da ido, har yana sauke jakar hannunsa a ƙasa, sanye yake da suit ya tsuke, da man Hamma Abdulrrahaman in ya ta saka ka gaba ba ka iya ƙwatan kan ka, aikin lauyancin har a gida yana yi, in yafara jefa maka uban tambayoyi sai ka fara zufa ma ba ka sani ba.

"Ko mijin na ki ne ke ba ki wahala! Kin rame sannan fuskarki ba ta cikin walwala."

Ya sake tambaya kanta na kasa ta kasa mgana sai rawan hannu take fama da shi duk yana lura da ita.
Baffa na so ya yi mgana ya katse shi da cewa" Baffa da wani abu ko! Wani abu na damun yarinyar nan kamar mai depression kalli yadda hannayenta ke rawa?

Baffa na dariya ya ce" Kai ne ka saka ta rawan hannu. Daga zuwan ka, ka fara mata tambayoyi sai ka ce a kotu."

Baffa na so ya ɗan shashantar da maganar amma Hamma ya ƙi yarda saboda ya fahimci akwai wani abu.

"Baffa wani abu na faruwa, kai ma fuskar ka ta bayyana damuwa."

Baffa ya kasa mgana, da gaske ne tun da Ummu ta faɗa masa abin da ke faruwa ya rasa abin da ke yi masa daɗi.

"Ya kamata na sani Baffa?

Ya tambayana yana kallon shi, Ummu kuma Baffa take kallo tana girgiza masa kai, karaf ko ya ganta da sauri ta mai da kanta ƙasa tana jin hancin jikinta na ƙalawa saboda tsoro.

"Baffa me ke faruwa?

Ya faɗa cikin  muryan da ba wasa a cikin ta.
Baffa ya yi gyaran murya sannan ya shiga sanar da shi abin da Ummu ta gama faɗa masa.

"Yanzu nan da ka gan mu, nima ta gama faɗa mini abin da ke faruwa kenan."

Hamma Abdulrrahaman ya yi shuru kafin ya ce.
" No wonder na ga yarinyar nan duk ta lalace, ba ma za ta rasa depression ba."
Baffa ya yi shuru bai yi mgana Hamma Abdulrahaman ya kalli Ummu ya fara faɗin" Shi don uban shi bai shirya haihuwa ba yanzu ya zo ya aure ki? Ya san bai shirya haihuwa ba ya yi aure? Ji wani rashi tunani don uban shi ba a haihuwa shi aka haife shi?

Ya ƙarishe faɗa cikin ɗaga murya jikin Ummu ya fara rawa kafin ma ta samu damar magana Ammah ta faɗo ɗakin tana faɗin" Waye kuma ba ya son haihuwa?
Ta yi turus ganin Ummu zaune tana rawan jiki ga Hamma Abdulrrahaman na ta bala'i Baffa na zaune a gefe bai yi mgana ba.

Ta ji zuwan shi lokacin tana salla ne amma yanayin da ta gan su  a ciki ya sa jikin ta ya yi san yi.
"Baffa me ke faruwa,?
Ta faɗa tana mai zama a gefen Ummu.

"Me aka yi ma wannan ta ke rawan jiki?

Ammah ta sake tambaya tana mai kallon Ummu da har ta fara hawaye.

"Au kema ba ki sani ba?

Hamma Abdurrahaman ya tambaya yana kallon Amma.

"Mene ne? Ban sani ba"

Ta faɗa cikin mamaki, Hamma Abdurrahaman bai tsaya ba ya kwashe komai ya faɗa ma Ammah yana fada mata tana sake kallon Ummu cikin mamaki.

"Na zo na same ta durkushe a gaban Baffa kamar wata marainiya, ba ta so na ji mganar ba ne. Raina ya ɓaci sai da lokacin nan Kabiru ya yi ta cewa an yi gaggawa Baffa ko fa bincikan shi yaron ba a yi ba sosai in da an yi bincike sosai ta ina za a aura mata ɗan iska wanda ba ya son haihuwa. ? Wato in ma wajen zubar da cikin wani abu ya same ta shi ba shi da asara kenan ko?

Ya sake faɗa har yana ta yar da jijiyan wuya.

"Duk binciken da ya kamata a yi an yi Abdurrahaman kuma ba a same shi da wani abu na ashha ba."

"To Baffa wannan dai abin assha ne, jahilci tsantsan da rashin tunani. Tunda cikin ya shiga sai ya bar shi ta haihu can tsakaninsu za su iya tsayar da haihuwa da fahimtar junan su duk ana haka ba matsala ba ne. Amma kawai ya ce sai ta zubar da ciki da karfin tsiya wannan ya saɓa ma doka. In muka yi ƙaran shi sai ya gane ba shi da wayau"

"A'a ba za a yi haka ba."

"To Baffa me ye amfanin zama da mara mutumci? A raba auren kawai."

Da sauri Baffa ya ce" Na ce aa ko,  shi ya sa ban faɗa maka da farko ba sanin halin ka na saurin yanke hukunci."

"To Baffa me kake so a yi?

Hamma Abdurrahaman ya faɗa cikin sarander
Ammah mamaki ne ya sa ta kasa mgana tunani take yi lokacin da Ummu ta yi ɓarin cikinta na farko yadda Ummin ikki ta ce ya damu, to yanzu kuma da ya kamata ya yi murna me ya sa zai ce ba ya so?

"Baffan ku Umaru zan kira, shi zai kira waliyin shi ya faɗa masa sai mu ji abin da ya kamata mu yi nan gaba."

"Baffa ya fa san da waliyin na shi ya ce sai ta zubar da ciki. Ni ina ganin a biyo da shi ta hanyar da ya biyo, ka ji fa ta ce yana azabtar da yarinya yana so ya yi mata dole."

Baffa ya tare shi da cewa" Duk da haka dai a fara sanar da su, a bi komai a hankali."
Amma ta jinjina kai kafin ta ce" Baffa ya yi gaskiya a fara sanar da su a ji su kuma na su hukuncin. Amma dai Habibu ya ba ni mamaki ban zaci haka daga wajen shi ba."

"Nima haka wallahi."

Baffa ya faɗa shima cikin ɗan damuwa Ummu kuma hawaye ta ke sharewa ta kasa mgana.

"Ni da man na san za a yi haka. Yaro ne fa ƙarami Baffa yarinyar nan da karatunta ta cigaba amma ta na ce ta ce aure za ta yi ai ga shi nan kin fara ganin uwar da ke cikin auren."

Baffa sai da ya yi dariya Amma ta kauda kai ba ta yi magana ba.

"Ba yadda ba mu yi da ke ki cigaba da karatu ba kika ƙi, kika ce ke aure ke yar soyayya to yau duk ina soyayyar! Tun da kin samu ciki ya ce dole sai kin zubar? Kin ga wawancin da muke faɗa miki kin yi ko a wancan lokacin ko? Auran ki ko shekara bai yi a ce su Baffa sun fara sulhu tsakanin ku? Da yau karatun ki kike yi da ba ki yi kuka ba"

Ya sake faɗa yana kallon Ummu yadda take kuka har yana fidda sauti.

"Na so ki cigaba da karatu, na so ki yi karatu. Nawa kike Ummu? Just 24 to 25 kina da sauran damarmaki masu yawa amma kika ƙin jin maganar mu, Baffa da Hamma Jibo suka mara miki baya. Yanzu don Allah ina amfanin a fara kiran su Baffa Umru da magarnar ki? Yaron ma ba shi da mutumci in har ba zai sauke kudirinsa ba ya sake ki kawai "

Ummu ta sake jin kuka ya taso mata, domin ta san  ko giwar wake ta sha ba ta isa ta ce ma Hamma Abdulrrahaman tana son Habib ba ta son rabuwa da shi ba, ta tabbata sai ya yi ball da ita shi ya sa ta yi shuru tana ta kuka shi ko yana ta faɗa da masifa Baffa ne ke tausan shi amma bai haƙura ba.

"Kaddara ta riga fata fa, Abdulrrahaman. Fatan mu dai Allah ya sa lamarin ya zo da sauƙi."

Ammah ta faɗa, ita tausayin Ummu ta ke ji. Ita mace ce sannan ƙarin tausayin ta da fatan ta kar Ummu ta fara fuskanta kaddaran aure da ƙananun shekarunta. Ita ta zauna da Fatima lokacin da kaddaran aure ta faɗa mata da shekarunta sha bakwai a duniya ita kaɗai ta san siraɗan da fatima ta tsallake kafin ta iya tsayuwa da kafafunta. Fatan ta Ubangiji ya zaunar da Ummu a ɗakin auren ta na har abada ya kuma sassauto da zuciyar Habib a kan ta. Kar Allah ya sa ta ɗanɗana zafin zawarci har abada a rayuwarta.

"Fatan da za mu yi kenan tun da mai afkuwa ta faru. Kuma bawa bai isa ya sauya zanen kaddaran sa ba."

Baffa ya faɗa, amma shi fa Hamma Abdulrrahaman bai yarda ba faɗi yake yi har da kuskuran su Baffa.

Amma ta ga Autar ta nata kuka ya sa ta shigar mata.

"Don Allah ka kyale ta Abdurrahaman ba ta ko da cikakkiyar lafiya!. Ke ta shi ki je ki ci abinci"

Ammah ta cece ta, ta samu ta bar ɗakin Baffa tana kuka zuwa falon Ammah ta faɗa saman kujera ta saki kukan ta shike nan abin da take gudu ya faru ya za ta yi ma Hamma bayanin yadda take son Habibu ta ke kuma son cikin jikinta da aurenta. Ta tabbata ba zai taɓa ganewa ba gwara Baffa shi ne zai fahimce ta da halin da ta ke ciki ba amma ba su Hamma Abdulrrahaman ba da daman yana cikin yan adawa da auran ta da Habib.

Ummu ba ta sake fitowa daga falon Amma ba har sai da Hamma Abdulrrahaman ya tafi, la'asar na yi ta yi salla ta ce ma Ammah za ta tafi da ta ce mata tun yanzu sai ta ce za ta biya gidan Ummin ikki, dambun ma ba ta ci ba ta ɗauka ta ce sai ta je gida Baffa ma ya fita masallaci bai dawo ba ta tafi, Amma dai ta faɗa mata an kira Baffa Umaru ba a same shi ba amma Baffa ya ce zai sake kiran shi. Har haraba Amma ta raka ta, tana ta sake jadadda mata ta kula da kanta.

Gida ta koma da man dai ta ce ma Ammah za ta je gidan su Baɗɗo ne saboda kar ta ce ta tafi da wuri, nan ko hankalinta ne ke tashe ba ta san yadda Habib zai yi in ya ji mgana ta kai wajen waliyin shi ba, tsoro ta ke ji shi ya sa ta kasa zaman gidan sannan da fargaban kar wani ya sake zuwa Baffa ya sanar da shi abin da ke faruwa a sake sauke mata wani masifan. A waya kawai ta kira Baɗɗo suka yi mgana ta sanar da ita ta je gida ta faɗa ma Baffa.

"Gwara hakan, in manya suka shiga ciki sai asan mafita."

Ita dai ba ta ce komai ba ta ma kasa ba ta labarin karon ta da Hamma Abdulrrahaman
Ranar da Habib ya dawo tana ta jiran ko za ta ji ya yi mata wata mgana ba ta ji ba, yadda ya saba mata haka ya yi na mantawa ma da wata hallita a gidan.
Washegari Shamsiya ta kira ta, tana tambayanta yadda ake ciki , tana kuka ta sanar da ita halin da ake ciki.

"Kash. Bestie kin yi kuskure na so ki yi amfani da shawara ta kafin maganar ta kai wajen su Baffa."

Ummu ta rantse mata da cewa bata san cewa haka lamarin zai koma ba, sannan ita dai tana son cikin jikinta ba za ta iya rabuwa da shi ba.
Shamsiya dai ita tana ganin laifin Ummu ne Habib ne ke da gaskiya. Ita a ganin ta ahakan ba wani abu ba ne, normal ne. Tunda yanzu yin tsarin iyali domin taƙaita haihuwa ya zama ruwan dare.

***

A ranar Baffa bai samu Baffa Umaru a waya ba sai a washegari ya same shi sannan ya sanar da shi abin da ke faruwa.
Shi kan shi Baffa Umaru faɗa ya hau yi yana cewa ai wannan shirme ne.
Suna gama waya da Baffa nan take ya lalubo lambar waliyin Habibu kanin mahaifinsa Alhaji Sheriff, tun lokacin neman aure suke da lambar juna.

Yana kiran shi bayan gaisuwa da tambayan iyalan juna. Sannan Baffa Umaru ya zayyane masa halin da ake ciki.

"Wani shirme ne haka Habibu ya aikata? Shi ba a haihuwa iyayen shi suka haife shi? Kuma ya san ba ya son haihuwan yanzu bai ɗau mataki ba sai da cikin ya samu? Ai ko bai isa ba "

Sun yi sallama da juna akan cewa zai yi ma Habibun waya ya ce ya zo gida ya same shi. Yadda suka yi zai kira shi, nan take ya kira Baffa ya faɗa masa yadda suka yi da waliyin Habibu shima suka rabu da cewa sai yadda ta yuyu in ya kira shi zai sake kiran shi.

Habibu kuma bai san abin da ke faruwa ba kiran Alhaji Shariff kawai ya samu da cewa ya zo gida yana son ganin shi, a ranar ya je bayan ya taso daga wajen aiki ya

Please Login or Register in order to submit comment