Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin ya ɗan cije baki kafin ya yi mgana Ummu ta zuɓe a kasa a kan gwiwoyinta tana sake faɗin.

"Me ya sa Habib? Me ya sa haka? Me ya sa ka je ka nemi aurena a hannun iyayena in dai har ka san ba ka taɓa sona ba? Sannan ka san ba ka san haihuwa da ni me ya sa ka yi mini cikin?

Kuka take kamar ranta zai fita amma bai sa Habib ya ji tausayin Ummu ba, bala'in jin haushin ta ya ke ji, domin taurin kanta adadin ɓacin ran masoyiyar shi, shi kuma duk abin da zai ɓata mata rai yana gudun shi.

"Za ki san dalilin anan kusa."

Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin har yana bango ƙofa yana jin ƙaran Ummu da sanda ta sake fashewa da kuka mai cike da sauti.

Falo ya fito ya kasa zaune ya kasa tsaye me ya sa Ummu za ta yi masa haka? Bai taɓa tunanin za ta ba shi matsala haka ba, ƙaran shigowan saƙo daga wayarsa ne ya dakatar da shi daga tunanin mafitan da ya ke yi.

"Ya ake ciki? Ta amince?

Wannan lambar dai da ya yi ma saving da M.S ita ne aka sake turo masa saƙo da ita.

Jikinsa na rawa shima ya ma yar da amsa.

"Ba ta amince ba."

Ya tura ba daɗewa sai ga shi an dawo masa da amsa.

"Duk da ka faɗa mata cewa ba ka taɓa son ta ba?
Shi ya sa ba za ka so haɗa zuru'a da ita ba?

"Na faɗa mata."

"Me ya kamata ka yi a yanzu?

"Na kasa samun mafita."

"Ka sake ta Habib."

Shuru ya yi kafin ya rubuta amsa.

"Zan sake ta. Amma sai na nuna mata kuskurenta sai na saka ta yi nadaman sanina a rayuwarta. Sai na saka ta ji dama ba ta yi mini gaddama ba tun fari. Sannan daga karshe na yi mata sakin wulaƙanci da ƙasƙancin da ba ma ita ba dangin ta ma  ba za su taɓa mantawa da ni ba"

"Good Job.. Cikin jikin ta fa?

"Zai fita ko tana so ko ba ta so."

"Ka aiwatar da hakan da gaggawa domin ka san ba mu da lokaci"

"Ki yarda da ni."

"Na daɗe da Aminta da kai Masoyi na"

Saƙon ƙarshe ya saka shi farinciki har sai da ya murmusa, wayarsa ya ma yar cikin aljihun wandon jikin shi, ya fara safa da marwa yana tunanin yadda zai yi sanadiyar zubar cikin jikin Ummu Salma ko ta karfin tsiya, yana jiyo kukanta a cikin ɗaki amma ko a jikinsa tunanimsa kawai ta ina zai samar masa da kansa mafitar zubar da cikin nan? Domin bai shirya ba, kuma ba akan Ummu Salma ba.

Abin da bai sani ba, wannan gudun jinin sai an busa masa rai kuma sai ya shaƙi iskar duniya, duk abin da zai yi Ubangiji ya riga da ya gama na shi.


*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"


https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t

*05*

Ummu-Salma ta sha jin wata hausa a bakin hausawa. Da sukan ce wai yadda na ga rana haka na dare,  ta ɗauka wata mgana ce kawai ta shaɗi faɗi, wacce ba ta da tushe ballanta makama, ita a da in aka ce mutum ya kwana bai yi barci sai ta yi ta mamakin me zai hana shi barci? ta ɗauka sai in an yi maka mutuwa ta uwa ko ta uba, ko ciwo ita bai hana ta barci. Sannan Ammah da Baffa duk suna raye kuma duka yayyenta ba wanda ta taɓa rasawa. Sannan tun tasowarta take cikin farinciki da gata. Har haɗuwarta da Habib da yadda ya shafe wattani takwas ya na nuna mata fassaran so da ƙauna a baki da aikace.

Ba ta taɓa riskan kanta a yanayin da ta kwana a ciki ba ranar. Har aka kira sallar asuba idanuwanta biyu suna kuma masu zubar da ƙwalla ko sun gaji sun haƙura da zubar ƙwalla ba a ɗaukan lokaci za su dawo suna kwarara kamar an buɗe famfo.

Tunanin ta guda ɗaya ne, yanzu duk wannan soyayya da ƙaunar da Habib ya nuna mata duk na ƙarya ce? In tana so ta aminta da mganar shi sai ta ji ta kasa ta fi gasgata da gaske Habib na son ta ɓacin rai ne ya sa ya faɗi wannan mganar, amma in yana son ta me ya sa ba ya son haɗa zuru'a da ita? Ta kwana a ƙasan cafet jingine da wardrope ba ta damu da komai ba, ita kawai fatan ta, ta buɗe ido ta ga komai a mafarki ne in kuma da gaske ne to ya kasance Habib ya zo ya ɗuka yana ba ta haƙuri ya ce duka mganganun da ya faɗa ba gaskiya ba ne, sai hakan bai faru ba har garin Allah ya waye ba ta sake ganin Habib ba, ba a ɗakin barcin su ya kwana ba sannan ko da ta rarrafa ta fita da safe ta iske shi ya bar gidan. Kukan da ta kwana yi ya taimaka wajen sake sakar mata zazzaɓi mai zafi, tana kwance tana hawaye in ta gaji ta yi kuka salla ne kawai ke ta yar da ita tun jiya ta kasa saka komai a cikin ta sai dare da ta ga za ta mutu ta sulala indomie da ruwan tea ta ci shima ɗin bai zauna ba ta amayar da shi, ruwan zafin ta sake sha shi ne ya samu zama a cikinta.

Yadda ya bar ta da ajiyan da daddare haka ya sake dawowa ya iske ta kwance a falo tana rawan sanyi. Yadda bai ce mata sannu ba itama ta yi alƙawarin ba za ta sake yi masa mgana ba sai shi da kan shi ya gano ya yi mata laifi ya ba ta haƙuri, tunanin Ummu-Salma Habib na son ta kuma zai dawo gare ta domin ya ba ta hakuri su daidaita kansu har a wannan lokacin yardan da ta yi ma Habib bai samu nakasu ba.

Tsayin kwana biyu ba ta da lafiya sannan ta warware tun da ta na shan pracetamol amai kuma da man laulayi ne ba shi da magani, a kuma kwanakin nan magana ta fatar baki ba ta sake haɗa Ummu da Habib ba, ya sauya akalan zaman su gabaɗaya. Ba ta sanin fitan shi ba ta sanin dawowar shi, sannan ya daina kwana ɗaki ɗaya da ita, ya koma yana kwana a ɗayan bedroom ɗin da daman na shi yawancin ma kayan sa suna ciki ne, kawai shi ya ce ya fi son na ta ne saboda yana da tiolet a cikin ɗakin saɓanin ɗayan sai an fito yana tsakiya shi ya raba bedrooms ɗin su guda biyu.

Da ta ji sauƙi ta fara yin abinci ta jera a saman dinning da beakfast kamar yadda ta saba sai dai yadda ta ijiye haka take ɗauka, sun kwashe sama da sati a haka tun Ummu na tunanin nadamar Habib har ta fara sarewa, ta dawo tana gaishe shi in sun haɗu da safe amma bai taɓa amsata ba, yadda ya ke yi ma a cikin gidan kamar bai taɓa sanin ta ba. Saboda in ya dawo ba ya neman ta ballanta ya san a wani hali take ciki, abin da ya faɗa ne yake aiwatar wa da man  ya ce sai ta yi nadaman ƙin bin umarninsa tun kuma tafiya ba ta yi nisa ba Ummu ta fara nadama sai dai ba ta jin za ta iya zubar da cikin jikinta, abin da ke damunta ta kasa jin haushi Habib a cikin zuciyarta da duk da irin yadda zaman auran su ya sauya. Ta kwana kuka ta yini kuka duk ta rame ta lalace ta kuma ta kasa tattauna mganar da kowa, tunanin ta da hangen ta Habib zai dawo ya ba ta hakuri ba za ta yi saurin fallasa sirrin auran ta ba, sannan tana son shi har gobe Habib na nan da wannan matsayin a cikin zuciyarta ta kasa jin haushin shi ko kaɗan a cikin zuciyarta.

Da a ce wani ɗan'uwanta zai gan ta a yanayin da ta ke ciki sai ya yi gaggawan tambayan ta ko wani abu na damun ta ne, saboda yadda
Ummu-Salma ta koma, ta sake yin fari ta ɗashe ga shi tana laulayi mai zafi ba ta iya cin komai sai ruwan lipton in dai ta ci abinci sai ta amayar da shi, yini take yi a kwance kamar ruwa amma babu ruwan Habib, tana jin shi zai shigo da daddare sosai tun da zaman su ya sauya sai ya kai sha ɗaya na dare a waje bai dawo ba in ko ya dawo yana ɗayan ɗakin sai dai ta ji shi yana ta waya ba kuma za ta iya gane da wanda yake yin wayar ba. Wani lokacin sai in ta ji zai fita ne da sassafe sai ta rarrafa ta fita falo in ya fito ta gaishe shi amma bai taɓa amsawa ba har ya saka kai ya fita ba zai sake kallon ta ba.

Duniyar duk ta yi mata ƙunci ba abin da ke yi mata daɗi, kowa sai ya ji ta ɗif kamar ba ta nan Ammah duk rashin nuna kulawanta ga Ummu sai da ta kira ta, an ci sa'a ma ranar wayar na kusa da ita domin kwana biyu nan sai a hankali ko iya amfani da wayar ba ta yi saboda kasala da zazzaɓin da ta ke fama da shi.

"Ummu kwana biyu daga ke har megidan na ki mun ji ku shuru ina fatan dai kuna lafiya?

Haka Ammah ta faɗa bayan Ummu ta ɗaga wayar. Lokacin da ta amsa mata da lafiya sai da ta danne bakin ta saboda kuka take yi hawaye sun kece mata amma ta kasa iya faɗa ma Ammah wani abu. Tunanin ta Habib zai dawo zai yi nadama sannan zaman auren su zai gyaru bai kamata ta yi gaggawan fallasa sirrin gidan auran ta ba shi ya sa ta daure ta ce ma Ammah zazzaɓi suka yi ta yi ita da Habib kwana biyu shi ya sa a ka ji su shuru amma duk sun samu sauƙi.
Ammah ta yi fatan ƙara samun sauƙin su sannan suka yi sallama to shi ma Baffa haka ya kira ta yana tambayan ko tana lafiya.

"Lafiya ta ƙalau Baffa."

Ta ba shi amsa da fillanci, shima ba ta faɗa masa komai ba sannan ba ta bar shi ya fahimci wani abu ba. Mami ma da ta ji ta shuru sai da ta kira ta, itama ce ma ta ta yi zazzaɓi suka yi ta fama da shi a kwana biyu nan. Baɗɗo ma sai da ta kira ta, ta ce a online kwana biyu ba ta ga ta hau ba itama dai ƙaryan ta yi mata na zazzaɓin sai ta ce satin nan za su gama jarabawa za ta zo ta duba ta daga haka suka rabu. Abin da ya ba ta mamaki yadda Bestie ba ta kira ta ba sai da ta kunna Data sai ta ga ta yi mata mgana ta faɗa mata za ta kashe wayarta sai dai lokaci bayan lokaci za ta dinga kunnawa har su gama jarabawa, shi ya sa ba ta san ta yi kwana biyu ba ta online ba. Sannan dalilin da ya sa ba ta kira ta ba kenan.

Sun shafe wajen sati uku a haka ita da Habib ba abin da ya canza, ba ta sake tsinkewa da lamarin Habib ba sai da ta kama shi yana saka mata wani abu a cikin zoɓon da ke cikin frezer ɗin ta. Abin da bai sani ba ita yanzu ko ruwa ba ta sha ya zauna mata ballanta wani zoɓo tun wanda ta haɗa ne kafin zaman su ya lalace ta ma manta da shi. Da daddare cikin ta na ta juya mata saboda yunwa domin yini ta yi ba ta ci abinci ba, ba ta san shigowar Habib gidan ba tun da ta samu barci ya ɗauke ta sai a lokacin ta farka da agogon wayarta ta yi amfani ta duba lokaci. Ƙarfe 2:43am na dare, tana fitowa sai ta ga kitchen da ɗan hasken fitila ita da farko ma ta tsorata shi ya sa ta yi tsam, ta fara takawa salaf-salaf ta leƙa kitchen ɗin tun da ƙofar a buɗe ne daidai ya na saka wani abu a cikin zoɓon da ba za ta iya tantance mene ne ba, amma koma mene ne ba abu ba ne mai kyau tana da tabbacin haka, ba abin da zai ta da mutum cikin dare yana zuba wani abu a cikin abin sha kuma ace alheri ne.

Ba ta bari ya lura da ita ba bakin ta alaikum ta koma ɗakinta ta faɗa kan gado ta na mai fashewa da kuka matsananci, kuka take yi kamar ranta zai fita ta yi ta tunanin mene ne dalilin Habib na aikata haka? Sai wata zuciyar ta bata amsa da cikin jikin ki, tabbas ko ta amince ko kar ta amince cikin jikin ta ne Habib ya yi alwashin sai ya fidda shi ko ta ƙarfin tsiya.
Ita kuma yanzu ta ji ma tana sake ƙaunar cikin ta, ta yi alƙawarin komai zai same ta sai ta kare shi ta zame masa garkuwan yadda Habib bai isa ya matso kusa da shi ba.

washegari Habib na fita ta je ta kwarara wannan zoɓon a tiolet ta zuba masa ruwa ya wuce. In da ta sake tabbatar da zargin ta a daran da ya dawo har ɗakin sai da ya leƙa ta ya ɗauka zai gan ta a galabai ce wata ƙila cikin ya zube amma bai fahimci komai ba a fusace ya buga mata ƙofa ya fice ya bar Ummu da hawaye a fili tana tambayan kanta.

"Me ya sa Habib? Me ya sa haka?

Tana mai ƙara kecewa da kuka da ƙarfi har yana fidda Sauti a cikin zuciyarta ta ke jin wani zafi da radaɗi, gani ta ke yi kamar ba rayuwarta ba ce, ita fa ce Ummu-Salma wacce Habib ya nuna duk duniya ba shi da kamarta amma kalle ta a cikin gidansa kashi ma ya fita daraja, duk da ya ce bai shirya zama uba ba, sannan ba ya son ta shi ya sa ba zai iya haɗa zuru'a da ita ba. Ita tana son shi har kuma gobe ba ta ji ta cikin nadaman auren shi ba wallahi tana son Habib kuma za ta yi komai domin ta ga ta tsira da mijinta da auran ta.

**

*3:45am*

Habib ne a cikin ɗakin sa ya kasa zaune ya kasa tsaye,  kansa har sara masa yake yi saboda damuwa da tunanin mafita? Wani amsa zai ba ma Masoyiyar shi in ta tambaye shi labarin cikin da ke jikin Umma-Salma? Ya faɗa mata cikin na nan bai zube ba, ya saɓa alƙawari domin ba haka suka yi ba, shi kuma duk wata hanya da zai bi domin Ummu ta saduda ya bi amma taurin kanta ya wuce tunanin shi, ya ɗauka matakin da ya fara ɗauka akanta zai yi tasirin da za ta neme shi ta bashi hakuri, salim alim a zubar da cikin nan ya gama more sadakin sa sannan ya kaɗa ta amma ta nuna masa ita ɗin mai taurin kai ne, saboda rasa mafita ya sa ya je ya siyo mganin barci sleeping pills ya saka mata da yawa a cikin zoɓon da ya san tana so sosai amma ya fahimci kamar ko ta sha bai yi mata komai ba. Sannan ya duba bai ga roban zoɓan ba in da a ce tasha yana da tabbacin ba a gida zai gan ta  ba sai dai a kira shi a ce tana asibiti amma yanayin da ya ganta ya ba shi tabbacin wannan karon bai samu mafita ba.

Hannun shi guda ɗaya ya buga a ɗayan, lokaci ɗaya yana mai dafe kan shi cikin matsanancin damuwa na rashin mafita,  me ya sa Ummu-Salma ta kasa gane wa ne?  Ita duk maganganun da ya faɗa mata ba ta yarda ba ya son ta ba? Ba ta yarda ba ita ce zaɓin sa ba, ko kuwa sai ya zauna ya yi mata gwari-gwari ne sannan za ta  gane manufar auran shi da ita, yana cikin wannan tunanin wayarsa dake yashe saman gado ta fara vibration yana kai idanuwan shi wajen sai da gaban shi ya faɗi.

"M.S..!

Ita ce ke kira, a kuma yanzu ba shi da amsar da zai ba ta, ya na ta falling ɗin ta yana ta gazawa. Me ya sa ya yi wannan wawancin tun farko bai kai Ummu Salma an cire mata cikin nan ba tare da ta sani ba? Ba ya bukatar barin wani abu na shi a rayuwar Ummu Salma, bukatar shi in ya gama biyan buƙatar shi da ita ya sake ta shike nan babu wani sauran alaqa, sannan ba haka suka yi da Masoyiyar shi ba ya riga ya yi mata alƙawarin ba wata macen da za ta fara haifa masa zuru'a sai ita, kuma ba ya son saɓa wannan alƙawarin a matsayin shi na namiji, kwata-kwata ya rasa mafita duk yadda ya ɗau lamarin kamar wasa ba wasa ba ne, lamarin na bukatar ya yi aiki tukari akan haka in ba haka ba daga baya zai zo ya yi fargar jaji alhalin lokaci ya riga ya ƙure masa.

Ganin ba za'a daina kiran ba ne, ya san halin mai kiran da saka damuwa , kuma so ta ke ta ji yadda labarin cikin jikin Umma ya tsaya shi kuma ba shi da wata amsa mai daɗin da zai iya sanar da ita.
Kiran na ƙarshe da ya katse ba a sake kira ba sai can ba daɗewa sai ya ji ƙaran shigowan saƙo hannunsa na rawa ya jawo wayar ya buɗe saƙon

"Habib ko ka ɗaga kirana ko gobe na zo gidan ka, koma me zai faru sai da ya faru. Ka amsa kirana."

Haka aka rubuta a jikin saƙon, jikinsa na rawa yana ƙokarin kiran lambar sai ga shi an sake kira a sanyaye ya ɗaga amma bai yi mgana ba.

"Habib me ya faru ne?

Aka tambaye shi, daga can cikin sanyin murya kuma muryan ta mace ce.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"  Ina tunanin cikin yana nan"
Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai shafa kansa cikin damuwa.

"Kana ma tunani ne ba ka da tabbaci Habib?

Aka sake faɗa wannan karon cikin ɗaga murya.

"Walahi na saka mata kamar yadda na faɗa miki. Sai dai..."

"Sai dai me?

Ta katse shi a fusace.

"Ina tunanin ba ta sha ba."

Wani ɗan ihu aka saki acikin wayar daga can bangaren.

"Ki yi hakuri zan samo wata mafitar."

"Wata mafitar! Ai ka daɗe da rasa damar ka Habib. Tun farko kai ka jawo mana wannan matsalan tun farkon auran ku na ce ka sa a yi mata planning yadda wanzuwar ciki a jikinta ba zai ba mu matsala ba, ba ka aminta da shawarana ba ka zauna a tunanin shekara ɗaya ya yi kaɗan ɗin da za ta samu ciki, ka manta da yanzu aure ma ba a shekara ake haihuwa, cikin ta na farko ba domin Allah ya yi zubewar shi da shi ma ya bamu matsala wannan ma Habib ka kasa yin wani tunani? Sai da na ce maka kar ka sanar da ita komai ka ɗauke ta ka kai ta asibiti a zubar da cikin ka kuma sake ta daga can amma ka ce ba haka ba na ka tsarin za a bi yanzu ga in da na ka tsarin ya kai mu. Haba Habib ina jin kamar na haukace in na tuna jakar yarinyar ce ta riga ni aje ƙwan haihuwarka a mahaifarta ji na ke yi kamar zan suma saboda baƙin ciki."

Ta karishe faɗa cikin ƙaraji, jikinsa har rawa yake yi wajen zayyano mata kalaman ban haƙuri da rarrashi.

"My love kin ga kwantar da hankalin ki, ni na yi miki alƙawarin bayan ke babu wata macen da ita isa ta fara haɗa zuru'a da ni. Ki kwantar da hankalin ki dole cikin nan ya zube a goben nan in sha Allahu."

Ya faɗa cikin sigan lallashi, daƙyar har yana ɗan ɗaga hannu kamar tana ganin shi.
Shuru na wani lokaci daga can bangaren kafin ta sauke numfashi ta ce" Habib ka san ina son ka shi ya sa na ba ka damar yin abin da kake so ko?

"Na sani."

"To kar ka ba ni kunya. Kar ka saka na cire yaƙini na a kan ka."

"In sha Allahu, gobe zan ɗauke ta mu je asibiti a cire cikin nan ko tana so ba ta so."

Dariya aka yi daga can bangaren kafin ta ce" Habib kar ma ka fara, in ka yi haka za ka yi nadama. Yadda Ummu ta san manufarka akan cikin jikinta ko Saudiya ne ba za ta sake aminta da kai ba balle har ta haɗa tafiya da kai. Ka samo wata mafitar dai."

Sai da ta faɗa kuma ya fahimci haka yadda ya bayyana munafarsa ba lalle Ummu ta sake aminta da shi ba amma duk da haka ba zai sare ba zai sake jaraba sa'ar shi sun daɗe suna waya yana faɗa mata kalaman soyayya cikin lallashi har sai da ya tabbatar da hankalinta ya kwanta sun rabu da cewa duk yadda zai yi zai yi na ganin cikin nan ya zube a gobe in sha Allahu.

Su sun gama na su tsarin, abin da kuma ba su sani ba Ubangiji shi ya riga ya gama nashi. A cikin zanen kaddaran su Ubangiji ya rubuta cewa Habib da Ummu za su samar da gudan jini, daga gudan jini zuwa rai.

***

Wani abu ya ba ma Ummu mamaki da ya sa kuma ta fara shakku, lamarin Habib yanzu ya zama abin tsoro da taka tsan-tsan a wajen ta.
Shigowa fa ɗakin ta ya yi da safe kafin ya wuce wajen aiki yana tambayan ta ya jikin ta yana fatan ba ta da wata matsala.
Tsabar mamaki sai ta kasa mgana, tana kallon shi yana yi mata mirmishi, mirmishin da har cikin zuciyarta ba ta yarda da shi ba.

"Sannu, Baby zan tafi wajen aiki, amma ina so ki yi mini girki da kwalliya yau in na dawo za mu yi mgana."

Har ya fice daga ɗakin tana bin shi da kallo bakin ta sake ta kasa mgana wata zuciyar na faɗa mata Ko dai ya saduda ne, wata ƙila ya gane kuskuren shi ne zai ba ta haƙuri, da ya ke tana son Habib ta kuma aminta dashi shi ya sa wata zuciyarta ta rinjaye ta da cewa hakuri zai ba ta, ayayin da wata zuciyar a can gefe tana ɗan ɗari-ɗari alamun ba ta aminta da saukowan Habib lokaci ɗaya ba. Sai dai duk da haka ba ta fasa yin abin da ya ce ba, yamma na yi ba ta ko jin daɗin jikinta ta miƙe ta fara aiki Baɗɗo ma ta kira ta a waya ta ce tana tunanin za ta shigo sai ta ce mata ta bari sai gobe, acikin ranta tana murna da farinciki na daidatawar ta da Habib ko da Baɗɗo za ta zo gobe ba za ta fahimci komai ba.

Farar shinkafa ta dafa da miya sai salat. Har da kunun aya ta yi duk da tana yi tana faman hutawa domin sai ta ke jin numfashin ta na yin sama sama kamar zai ɗauke. Ko kafin mangariba ta gama komai sai da ta idar da salla sannan ta rarrafa ta yi wanka tana jin jikinta ya yi zafi zazzaɓin jikinta ya dawo, ammma haka nan ta yi masa kwalliya cikin wata doguwar riga baka mai kwalliyan ja a jikinta shi ya sa ma mayafin rigar ja ne, ta yi kyau duk da ba kwalliya ta yi ba amma fuskarta ta yi mata fayau kamar wacce ta shekara tana jinya.

Da wuri Habib ya dawo tun kafin ma a kira sallar isha'i ya shigo  gidan da niƙi-niƙin ledoji ya siyo balangu da su lemon exotic. Yana ganin ta ya buɗe mata hannuwana ya ce ta taho ita dai ba ta saki jiki ba, ta tafi gare shi ya rumgume ta yana wani shinshina wuyanta cikin sanyaya murya ya ce.

"Na yi kewar ki Baby."

Hawaye suka kece ma Ummu, amma Habib bai bar ta haka ba sai da ya ɗago ta ya saka harshen shi yana lashe mata hawayen fuskarta, daga nan ya fara yamutsa ta, duk da zuciyarta na son ta hana shi amma ta kasa cewa ta ke yi Habib ne, Habib ne fa mijinta masoyinta. Tun a falo ya raba

Please Login or Register in order to submit comment