Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na ta ba, ba ta damu ba Ammah ce ta damu saboda sun yi mgana ya ce mata zai zo, a cewarsa ya ɗauka za su iso bakin gaba ne ana gobe ɗaurin aure sai kuma tafiyar ta su ta sauya tsari shi ya sa bai samu zuwa ba. Duk fa Ammah ce ke ta yawo da wannan mganar shi gogan ba wanda ya ji haka daga bakin shi. To wai wanda ko ɗaurin auran shi bai samu zuwa ba to na waye zai je? Shi ya sa ma wanda ya damu in bai gan shi a sha'aninsa ba, shi ke da kaico shi dai bai ma san kana yi ba, shi fa mutumin nan dabam yake, ɗauka yake kuɗi sune muhimmi a rayuwar nan daga naira ɗaya har miliyan goma zai iya tura maka amma kuma ba zai iya zuwa ya yi maka murna ko jaje ba shi ya sa har gobe bata taɓa saka Hamma Lamiɗo a jerin mutane masu karamci ba, ta fi saka shi a jerin mutane masu girman kai da ɗagawa.
 
Tana cigaba da cin doughnuts ɗin ta, tana kuma kurɓan tea a lokaci ɗaya amma sai taɓe baki take yi ita kaɗai daga gani hakan yana daga cikin ɗabi'arta.
Ita fa tun wancan satin da ta je gida Ammah ta dame ta da labarin bikin nan na Daura ta ji ba za ta sake komawa ba sai bayan an gama bikin nan, domin hankalin Ammah ba a kwance yake ba yanzu sai ta ga ta je Daura an gama biki lafiya ta dawo tukunna. Baffa dai ba ruwan shi ba lalle ne ma yaje ɗaurin auran ba Ammah kuma ba wanda ya isa ya ce ba za ta je ba ai sai ranar gidan ya kwana ba lafiya. Baffa ma yasan halin kayan shi, shi ya sa ba ya ma gigin shige mata na shi addu'a ne da fatan alheri, domin in dai akan sha'anin abin da ya shafi Hamma Lamiɗo ne ko Baffa bai da ta cewa, da jikinta da zuciyarta take hidimtama wannan bawan Allah da Ubangiji ne ya haɗa wannan ƙaunar da tana tunanin ko su ƴa'ƴan cikinta ba ta nuna musu ƙauna da kula da alamuransu da muhimmanci kamar yadda take kafa-kafa da duk wani al'amarin da ya shafi Hamma Lamiɗo.

  Shi ma kuma ba ya iya tsallake umarninta komai tsaurin shi a gare shi. Da Amma kaɗai yake iya doguwar hira cikin nishaɗi, ita ce kawai take iya ganin dariyan shi har da haƙora a waje. In ba za ta manta ba lokacin tana aji biyu a matakin babban sakandiri aka yi bikin Hamma Lamiɗo, auran da a farko cewa ya yi ba ya so tunda haɗin daga kakarsa ce Fulanin Daura, Mai martaba kuma ya ce ba zai matsa masa ba, Mami kuma ta ce ina ruwanta da sha'anin Lamiɗo? A nemi uwar sa Ammah ita ce za ta iya saka baki akan mganar,
Hamma Lamiɗo da bayan gaisuwa magana ta mintina biyar ba ta taɓa haɗa shi da Mami a matsayinta na mahaifiyarsa ba, ko da za su yini waje ɗaya su kwana. Ba ma ita ba, Hamma Lamiɗo zai yi rayuwa da mutum na tsawon kwanaki amma ban da gaisuwa magana ta fatar baki ba zai yarda ta haɗa su ba. In ko ka matsa ka yi hira da shi kai ne da haushi, domin a ginshiƙe zai din ga tafiyar da kai da har sai ka yi zuciya ka ƙyale shi.

Haka ko aka yi  tawagar Fulanin Daura har cikin falon Ammah, ta zauna ta roƙe ta da ta sanya baki Lamiɗo ya karɓi auran nan, da suka je suka karɓo masa ƙafa da ƙafa har wajen Mai martaba Sarkin Kano a lokacin Balkisu ba ta daɗe da dawowa daga ƙasar Spain ba, a can ta yi duka karatun ta na likitan ci. Ammah ta yi ma Fulanin Daura alƙawarin za'a yi auran nan kuma maganarta ya tabbata. Tana cema Hamma Lamiɗo in har ya ɗauke ta a matsayin uwa to ya karɓi wannan auran da cewarta da auran ko wata biyu ba a yi ba. Abin mamaki sun rufe shekara da wattani ne da aure matar Hamma Lamiɗo ta haihu,  har yau Ummu-Salma na mamakin wannan abu, ka ce ba ka son aure amma kuma ana yi sai shuru, kuma ko zuwa suka yi tare ba mai gane yanayin shi. Ba za ka ce yana son ta ba, ba kuma za ka ce baya son ta ko da wani lokaci yana nan a ginshiƙen sa. Shi fa ba ka iya gane ma yanayinsa kwata-kwata, fuskarsa ba ta bayyana farincikinsa ko bakincikinsa.

Ammah kuma al'amarin ƴa'yanta kuwa sai dai Ummi ikki ta yi gaba ita tana baya, amma in dai lamarin Hamma Lamiɗo ne ba ta jira ba ta kuma sakawa a yi mata, ita ce da kanta take yi masa komai, tun tana ƙarama ta shaida Ammah ta fi hidimtama Hamma Lamiɗo fiye da su ƴa'ƴanta na cikinta tun tana damuwa har ta saduda ta sare. Ta taɓa tambayan Baffa me ya sa Ammah ta fi son Hamma Lamiɗo akan kowa a gidan nan?

"Sabo da shima ɗan ta ne Ummu Salma. Nima ba ki ga ta fi son shi a kaina ba?

A lokacin dariya ta yi, kuma gaskiya ya faɗa ko Baffa bai isa ya ce wani abu akan Hamma Lamiɗo ba, ko yana nan ko baya nan Ammah mai tsaya ma yau ɗin sa ne har da jiyansa ma sannan za ta tsaya ma gobensa ma. Ba ta san Habib ya dawo ba domin ba ta ji motsin ko shigowar motarsa haraban gidan ba hankalin ta na kan Tv tana hakaito soyayyar Ammah ga Hamma Lamiɗo gefe ɗaya tana kallon drama ɗin Rayya da Avm Adnan, haka kurum take son film ɗin sabo da su, soyayyarsu na matukar birge ta Kamar ita da Noorin ta.
Su suka sanya ta mantawa da Komai ta ma yar da hankalinta kan kallon gabaɗaya.

Kamar daga sama ta ji ana murza ƙofa alamun an saka key za a buɗe, ƙurama ƙofar ido ta yi ba ta yi ko motsi ba. Ya saba ina tana dirin shigowar motarsa ta ke kamewa a tsakiyar falo yana shigowa za ta tafi da gudu ta naɗe a jikin shi, shi kuma kamar ko yaushe ya fara juyi da ita a tsakiyar falon cikin soyayya da muradi.
Amma yau sai ta ji kasala ya rufe ta ta kasa tashi, ko mararin ganin shi a lokacin ba ta ji ba wataƙila da ba ta gan shi ba ne ya sake ta ba ta dai sani ba. Tana nan zaune ya shigo falon ɗauke da karamar jakarsa ya ɗan jiƙe domin ga alamun yayyafi nan a jikin baƙaken suit ɗin da ke jikinsa.

Wataƙila ya ɗauka ba ta falon ne, shi ya sa ya tuɓe takalmansa ya ƙariso ciki sai dai me! Sai ya gan ta zaune tana mai kallon shi da manyan idanuwan ta.
Waro ido ya yi kafin ya ce.

"Baby da man kina jina?

Ya faɗa yana mai sauke jakar hannunsa a saman kujera mai zaman mutum ukun dake kusa da shi, ware ma ta hannuwa ya yi lokaci ɗaya yana sake faɗin.

"Baby na i miss you."

Ya faɗa yana yi mata murmishi, wannan murmishin na shi mai tsada da ya kan narkar ma ta da zuciya a lokuta da dama in ya kalle ta ya yi mata.

Maƙe kafaɗa ta yi, lokaci ɗaya tana tura baki , sannan ta kauda kanta alamun ta yi fushi, yana ganin haka ya yi saurin isowa kujeran da takwle zaune yana faɗin.

"Baby am sorry, kin ji ni shuru ko?

Ta ƙi yarda ta kalle shi, ganin haka yasa ya ɗauke Bowl ɗin dakw gaban ta da mug ɗin tea ya ɗora bisa table ɗin gaban su da karfin sa ya saka hannu yana ƙokarin juyo da fuskarta ta ki ba shi damar haka.

"Baby ni ne fa? Noori ɗin ki ne yau ba ki son kallon fuskar shi?

Ya faɗa yana kawo mata hannu zai taɓa fuskarta da sauri ta bige hannun shi, cikin shagwaɓa ta ce.

"Noori ka san zan damu ko?

Ta faɗa tana mai kallonsa lokaci ɗaya hawaye suna cika kwarmin idanuwanta  ba ta da wuyar kuka abu kaɗan sai ya saka ta kuka ko kallo ta ke yi ɗan emotion kaɗan sai ta fara hawaye, yanzu ɗin ma ji kawai ta yi tana so ta yi kuka.

Jin muryar ta na rawa ga shi idanuwanta da jwalla ya sa ya ruɗe ya tarairayo ta da hijabin jikinta ya ɗora ta bisa cinyarsa yana tallabe da fuskarta da tafukan hannayensa duka biyu

"Ni ne ko? Sorry Baby Gwaggo ce t kira ni kuma na manta waya ta a mota na saka ta chaji, lokacin da na fito na ga kiran ki sai ban kira ba, tun da lokacin ina kan hanyar dawowa ne"

Ya faɗa yana mai kallon ta itama shi ta ƙura masa ido, tana sake runtse ido sai kawai hawaye suka zubo mata sharr a saman kumatun ta.

"Baby ki daina kuka mana. Bana so kin sani."

Ya sake faɗa bayan ya saka tafin hannunsa yana share mata hawaye.
Buɗe idanuwanta  ta yi  tana kallon shi, gashin idanuwan ta duka biyu ya sumbata kafin ya ɗago yana faɗin.

"Gudu na yi ta yi a mota fa Baby."

"Ba na hana ka ba."

Ta faɗa cikin wata irin shagwaɓaɓbiyar murya.

"Kin hana ni Baby."

Ya ba ta amsa shima cikin ƙaramar murya, lokaci ɗaya yana kwantar da kan shi a saman kirjin ta hannayensa kuma ya tusa su ta ƙasa hijabinta yana shafa mararta zuwa ƙirjin ta banƙarewa ta yi shi kuma sai ya ji daɗin haka zare mata hijabin jikin ta ya yi ya tsaya yana kallon kirjin ta.
Ganin haka ya sa kunya ya kamata sai ta faɗa kan kirjinsa tana masa kukan shagwaɓa.

"Noori ka bari."

"Me zan bari Baby?

"Uhm"

Ya faɗa yana shinshinar wuyanta cikin lokaci ya fara birkicewa, yana bin sasaan jikinta da wasanni ta kasa mgana sannan ta kasa hana shi, duk da yau ɗin tana jin gajiya a jikinta amma Habib ya sabar mata da komai, ƙa'ida ne in ya dawo kafin ya yi wanka ya ci abinci sai ya riban ce ta, kuma a daran ma ba zai bar ta ba kafin asuba ya yi sau uku ko sui huɗu, haka ma bayan asuba, tun Ummu-Salma na ɗaukan hakan a matsayin amarci a farkon auran su har yanzu ta daina ɗauka haka. Sai ta bar shi a matsayin mijinta Habib na daga cikin mabukatan maza ma su yawan buƙata.

A farko-farkon auran su ta sha tambayan ta kanta da man wanne ne daɗin auran? Ba hutu sam, lokacin ba ta yi kiban amarci ba sai rama saboda kwazzaban Habib saboda ba ta cikin jinsin mata fitannanu, amma saboda Habib ta koya, har in bai neme ta ba sai ta ji ta a takure, da farko ta ɗauka illa ne hakan sai da ta ga wani rubutu a faceebook wanda ke nuni da cewa yawan mu'amalar aure ga mace nuna soyayya ce makura daga mijinta shike nan ta daina fargaba ta saki jikinta duk lokacin da Habib ya marabanceta za ta ba shi cikakken goyon baya, amma tunda ta yi ɓarin cikinta wattani biyu baya da suka wuce ta daina jin shauƙin abin, kwana biyu kamar lamarin ya yi sauƙi yanzu kuma ya dawo mata, sai ta rika jin ta gaji sannan ba ta son a sakar mata wata gajiyan bayan wacce take muƙurƙusan kashin ta a lokacin, sai dai ta kasa mgana ta na ji tana gani Habib ya ɗaga ta sama yana nishi zuwa bedroom ɗin su, kan gado suka faɗa ya cigaba da abin da ya fara.

Ta yi ƙokarin ta bashi dukkan haɗin kai har ya samu natsuwa, bayan ya shiga wanka ko ɗan yatsan ta ba ta iya motsawa tsabar yadda take jin jikinta a mace. Tana kwance ta rufe rabin jikinta da blanket saboda Habib ya yi fatali da kayan jikinta tun a farkon yaƙin. Tana kwance ya fito ɗaure da towel a ƙugun shi karamin kuma yana goge ruwan da ke gashin kansa.

Tana daga kwance take ƙare ma Habib kallo, in dai ana neman cikar zati da mazantaka Habib ya kai a namiji, fari ne tas shima sannan dogo amma ba shi da tsaho sosai yana da faɗin jiki daga sama kaɗan kyakyawa asalin bafullatanin Yola ne na uwa da na uba, hancinsa har baka sumar kansa tana nannaɗe irin ta fulani, ko ta ko'ina Habib ya kai za kuma a nuna shi daga nan har Saudiya a matsayin namijin da ya ƙera sa'a ga ilmi ga martaba ga sanin ya kamata ga iya soyayya, a kalla a shekarunsa ba zai gaza talatin da biyu ba 32. Shi ya sa yana cikin jerin layin matasa masu jini a jika, ma'aikacin banki ne shi ya sa ya zama ɗan gayu na karshe da kwatance.
Habib Idris Mai imani ya kai  ya haɗu ya gaji da haɗuwa da duk macen da ta mallake shi zai zama abin alfarinta.

"Baby ki tashi mana."

Ya faɗa bayan ya yarfa mata ruwan dake gashin kansa.
Mirmshi ta yi masa shima ya mayar mata da martanin mirmishin nata.

"Tashi ki yi wanka ki ba ni abinci yunwa na ke ji Baby."

Ya sake faɗa cikin yar shagwaɓa, hannunta guda ɗaya ta mika masa lokaci ɗaya tana faɗin" Noori ka ɗaga ni."
Ta faɗa tana mele masa baki.

"Baby me ke damun ki yau? Kin gaji ne da yawa?

Ya faɗa yana rike hannunta da taimakon shi ta miƙe zaune.

"Baby are you sick?

Ya faɗa yana kallonta ganin ta lamgwaɓe kai.

"Ban sani ba Noori amma jikina ya yi weak"

Da sauri ya matso gabanta ya dafa goshinta kafin ya ce" Kuma tempereture ɗin ki is Normal."
Shagwaɓa fuska ta yi kafin ta ce" Ni ma ban san meke damuna ba Noor."
Kallonta ya yi kafin ya kashe mata ido ɗaya yana sake faɗin.
"Ko ni ne Baby?
Ture shi na yi ina faɗin" Yau ne farkon mu?
"Baby to amma ai yau na kai farmaki na da kyau ko?

Sake ture shi ta yi sannan ta miƙe ya taimaka mata yana tura ta bakin tiolet.
"Baby yunwa."
Ya sake faɗa da karfi gwiwa ta tura ƙofar toilet ɗin ta shiga tana faɗin" 5 minutes."
Ta faɗa tana mai rufe ƙofar, da kallo ya bita kafin ya yi mirmishi. Wardrope ya buɗe ya ɗauko saukaƙkun kayan barci ya saka riga mai gajeren wando falo ya fita ya sauya tasha zuwa tashar ƙwallo mintina goma tsakani Ummu Salma ta fito itama cikin rigar barci mai shara-shara wacce ba ta wuce gwiwarta ba.

Abinci ta jera bisa dinning, yana daga can a falo ta kira shi.

"Noori Dinner is ready"

Da sauri ya taso, ita ta ja masa kujeran ya zauna yana faɗin" Thank you Baby."
"You are always welcome Noori na."
Mirmishi ya yi mata lokaci ɗaya yana kashe mata ido ɗaya, kau da kai ta yi tana yar dariya.

White rice ne da miyar allayahu, sai zoɓo da tea, tare suka ci abinci suna yi suna hiran su ta masoya.
Bayan sum gama suka shiga tiolet suka wanke bakin su, Ummu-Salma ta kwashe abin da suka ɓata zuwa kitchen sannan ta koma falo wajen Habib da ya rage hasken falon ta naɗe a jikin shi, suna kallo suna hira suna kuma soyayyar su.

****

Duk da yanayin Ummu-Salma da Habib ya gani bai saka ya ɗaga mata kafa ba, kafin su kwanta sai da ya maimaita. Can cikin dare ma sai da ya tashe ta tana so ta ce ya ƙyaleta ba ta jin daɗin jikinta amma ta kasa, yana dawowa daga sallar asuba ma sai da ya yi duk yadda ya ga jikin Ummu-Salma ya yi laushi a cewarsa jarumatarsa ce ta ƙaru, shi ya sa ta makara sai wajen bakwai saura ta iya ƙarfin halin tashi ta shiga kitchen, da ya ke girki Hobby ɗin ta ne garin fulawa ta iya sarrafa wa, cikin lokaci ta kwaɓa fulawa ta sarrafa shi zuwa Naan Bread.
Tun da tana da kayan lambu, nama ne babu sai ta yi amfani da ƙwai.

Ko kafin takwas ta yi ta jera komai a saman dinning. Ta koma bedroom ta tashi ta Habib ta taimaka masa ya yi wanka, ya tsuke cikin suit masu ruwan  baƙi da ruwan toka. Tare suka zauna zaman ƙaryawan Naan bread ɗin suke ci haɗe da tea Habib na gutsira yana yi mata santi.

"Baby ina son wannan abin. Ya ma sunan shi?

Tana dariya ta ce" Naan Bread Noori, amma wannan mai ƙwai ne ba nama ba."

Sai ya jinjina kai kafin ya ce" A online clases ɗin ku aka koya miki?
Bayansa ta dafa kafin ta ce" Noori na santi."
Sai da ya kurɓi tea kafin ya ce" Ba santi ba ne, Allah Baby yana da daɗi, in dai kika yi shi ai ina cewa yana da daɗi ko?

"Yes My Noori."

Hira suke yi, jefi-jefi ita tea ɗin ma kawai ta ke kurɓa saboda zuciyarta ta ji tana tashi tun da safe, shi ya sa ma ba ta ci ba naan bread ɗin ba.

Habib wayarsa ce a hannunsa yana ta dubawa. Lokaci ɗaya kuma yana cin abinci.

"Baby."

"Naam"

"Ashe kuna da biki ban sani ba?

Sai ta kalle shi cikin mamaki.

"Noori Biki kuma?

"Yes"

Ya faɗa yana karkata mata wayar ta leƙo da kanta sai ta yi arba da zafafan hotunan Badia'tu yar sarkin Daura.

"Ba bikin gidanku ba ne?

Ya faɗa  yana sake tura abin da ke hannunsa a baki lokaci ɗaya yana korawa da ruwan tea.

"Oh ai fa."

Ummu-Salma ta faɗa tana kauda kanta.

"Ammah za ta je?

"Za ta je mana. Kai ma ka sani"

"Mami fa? Itama za ta je?

Sai ta kalle shi kafin ta ce.

"Kai ma ka san Mami ba za ta je ba."

Sai ya jinjina kai yana cigaba da kallon wayarsa kafin ya ce" Baby da kin tambayeni da na bar ki, kin raka Ammah dagaa ganin bikin nan za a sha shagali."

"Uhm"

Ta faɗa ba tare da ta sake mgana ba.

Dariya Habib ya yi kafin ya ce" Am just joking. In kika tafi ni kuma ya za ki yi da ni?
Hararan shi ta yi, yana sake yin wata dariyan ya ce.

"I love you Baby."

Juya masa ido ta yi sannan ta yi masa fari, jinjina kai ya yi kafin ya ce" Ki bari kafin na ce mu shiga daga ciki."
Tana jin haka ta yi saurin gyara zama tana faɗin.

"Za ka makara fa Noori?.

"Ina sane da time fa Baby."

Sai ta jinjina kai, ba ta yi mgana saboda cikinta ne ta ji yana juya mata.

"Baby."

"Noori."

Sai da ya kalleta kafin ya ce.

"Hamma Lamiɗon to zai je can Daura ɗin ne?

"Ban sani ba Noori."

"Serous fa?

"Allah fa ban sani ba."

Ta faɗa tana mai kallon shi.

"Ko Ammah ba ta faɗa miki ba.?

"Ba ta faɗa mini ba Noori."

Ta faɗa cikin gajiya da tambayoyin.

"Noori yau kuma Hamma Lamiɗon kake son gani?

Ta  faɗa tana kallon shi mirmishi ya yi kafin ya ce" Ba laifi ba ne, kin manta sau ɗaya na taɓa ganin shi, shima daga nesa kafin na karisa ya shige cikin mota."

Baki ta taɓe kafin ta ce.

"Uhm"

"Baby ke dai kawai ki ce jininku bai haɗu ba, kuma saboda kin ƙi karatu ne "

Wani kallo ta yi masa da ya sa ya fara dariya kafin ya ce.
"Baby gaskiya na faɗa, nima fa ta shafe ni kamar baya sona saboda ke."

Kai Ummu-Salma ta girgiza kafin ta ce" Shi wannan yana neman dalilin tsanar mutum ne? in dai haka ne kowa ya tsana kenan."

"Me ya sa kika ce haka?

"To ban da Ammah wa ke ganin dariyan mutumin nan! Ko Baffa a ginshiƙe yake masa mgana. To bari ka ji ko su Hamma Jibril a takamance yake yi musu mgana, ballanta irin mu ƙananun ƙwari."

Habib ya kwashe da dariya ganin yadda matar tashi ta haɗe rai, tissue ya ɗauka yana goge bakin shi kafin ya ce.

"Kuma Ammah tafi son shi da ke ba Baby."

"Ta fi son shi da kowa ma Noori. Ni ai na bar masa ita na kama Mami na da Umman ikki."

Ta faɗa tana juya masa baki, miƙewa ya yi yana faɗin" Baby is time."
Itama sai ta mike, bedroom ta koma ta ɗauko masa briefcase ɗin sa ta dawo falon suka rumgume juna sai da ya sumbaci bakin ta kafin ya ce.

"Baby take care kin ji ko."

"In sha Allahu"

Ya hana ta masa rakiya a haraba shi ya sa iyakarta kofar falo ya fita tana ɗaga masa hannu har ta za ta rufe ƙofar sai ga shi ya dawo da sauri yana faɗin.

"Baby key ɗin mota ko a kafa kike son na je wajen aikin yau?

Sai ta juya da sarssarfa ta koma ciki ta ɗauko masa, bayan ta kawo masa sai da ya sumbaci hannun sannan ya wuce yana faɗin

"I love you Baby."

"Love you too Noori na."

Hannu ya ɗaga mata, itama ta daga masa sannan ta rufe ƙofar. Dinning ɗin ta koma ta zauna domin ba ta ƙoshi ba sauran Naan bread ɗin da Habib ya rage ta ɗauka ta ci guda ɗaya ta hada da ruwan tea, Allah ne ya sota da ta yi amai saboda zuciyarta ta yi ta tashi sai da ta sha ruwa sai ta ji zuciyarta ta kwanta

Tunani take yi ko dai ciki gare ta? Sai ta fara tunanin yaushen da rabon da ta ga al'adanta? Tun bayan ɗaukewar jinin nan na ɓarin da ta yi ba ta sake wani jini ba, tsalle ta buga ita kaɗai a falo da gudu ta ruga ɗaki ta dauko wayarta Habib ta so kira sai kuma ta fasa kar ta ɗaga masa hankali.
Sai ta mai da alkalan kiran ga Sisna amma ba ta ɗauki wayar ba wata kila ta shiga cikin makaranta ne
Sai ta bar mata saƙo.

"Albishirin ki. Ina tunanin ina da wani cikin SisNa."

Ita kaɗai a gaban madubi tana shafa cikinta tana kallo, farincikinta ya kasa ɓoyuwa wani irin murna Habib zai yi in ya san tana da ciki? Ba ta da tabbaci amma alamominta na kwana biyun nan ya fi kama da na masu juna biyu, sai a lokacin ta kula da nonuwanta sun tasa, kuma da man cikinta na farko kafin ta yi ɓarin shi a Nono ya fara nuna kansa kenan wannan ma anan zai fara bayyana kan shi?

Wata zuciyar na faɗa mata kar ta faɗa ma Habib sai ta je asibiti an tabbatar mata sannan sai ta faɗa masa cikin mamakin da tasan murnan da zai yi ba ƙarama ba ce, saboda lokacin da ta yi ɓari ya shiga damuwa sosai har ta dinga mamakin haka yake son haihuwa? Ko da yake in ta yi duba da gidan da ya fito gidan yawa ne shi ya sa zai so shima ya tara yara kamar mahaifinsa.

*littafin Fargar Jaji na kuɗi ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura Kuɗin karatun ku ta wannan acct ɗin 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waɗannan lambobin kamar haka.*

09069067488.
08032773332.

*Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.*

*Janafty*
*Sat, 05. June 2025.*
5:53pm.
*Posting on 17/04/2026*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*


To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/IF0uPZWtcCOIczsjhdCbIZ?mode=gi_t


https://www.arewapen.com/u/jamilaumarjanafty

*02*
_JIMETA: Zone 3_
*10:30pm.*

Alhaji Hadi Baba na zaune a gefen gadon dake cikin turakan shi, wasu takardu ne a hannun shi yake dubawa sanye yake da jallabiya mai ruwan madara, kansa da tsilintsilin furfura wani siririn farin gilashin ne a idanuwansa wanda in zai karanta wani abu yake amfani da shi saboda raunin ganin sa.

Sallaman matarsa ne ya katse masa nazarin takardun dake hannunsa, ya ɗago kansa lokaci ɗaya yana mai amsa mata cikakkiyar sallaman kamar yadda ta yi.

Dattijo ne mai cikar kamala da haiba, fari ne amma ba shi da haske sosai wataƙila ya yi sirki shekarunsa na haihuwa za su kai 66 amma hutu da jin daɗi sun saka fatarsa da yanayin jikinsa suna ƙaryata shekarunsa
mai ɗakin sa yake kallo dai-dai lokacin da ta ƙariso gaban shi.

"Baffa ba ka kwanta ba?

Ta faɗa da muryanta da ta cakuɗe irin na fulani lokaci ɗaya kuma tana nufar can ƙurar ɗakin in da ta ijiye mganin sauron da ta kunno a hannunta a saman wata kwalba lokaci ɗaya tana sake faɗin" Na manta yau ban yi maka feshin magani ba Baffa."

"Sannu da ƙoƙari. Na gode."

Ya faɗa da cikin harshen fillanci, dawowa ta yi zuwa gefen shi ta zauna tana kallon shi, itama ita ya kalla amma bai yi mgana ba sai ta fara dariya tana faɗin" Baffa me kuma na yi ni Jamila?
Kai ya girgiza kafin ya ce" Ba ki yi komai ba."
Agogon da ke

Please Login or Register in order to submit comment