Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kadai ta kasa,duk yadda take tunanin babu soyayyarsa ko digo a zuciyarta a yau din ta qaryata kanta sau babu adadi.....a yau kuma ta tabbatarwa kanta tarin TSANA DA QIYAYYAR da take tunanin tanayi masa ba komai bace face zallar soyayya fara sol mara sofane.......wajen waye zataje taji dadi?,waye zai rage mata abinda takeji a ranta?.

Idanunta a rurrufe ta zura slippers a inda suke aje slippers nasu ta nufi hanyar fita,saita samu kanta da wucewa zuwa sassan bibi kai tsaye,tana jin itace dama me tallafar damuwarta,a yanzun ma ita zata taya idaniya da zuciyarta kokawa.

Aba oncle issofou da oncle umar harda oncle bashar da shi kansa maina dinne zaune a falon,sun kammala karin kumallo suna yin sallama da ama da sauran dan maganganu da suka shafi yan uwa. Daga gefe su aminata ne da yasmine suke tsaye atta da saddi suna musu gyaran daya daga cikin freezer din bibi suna kwashe ruwa da lemukan ciki don sunaso suyi snacks su ajjiyeshu fresh,don dukkansu basu kadai bane,kuma kamar sultana suma basa iya jure yunwa,a nan sassan bibi ne kawai kuma suke da tabbacin zai tsira.

Yadda ta shigo din kusan yaja hankalin kowa a falon,banda bibi daketa faman mita wa maina. Ita dinma idanunta basu gane mata kowa ba,ba wanda ta gani sai bibi kadai wadda hankalin da tunanin dama zuciyar gaba daya dama sun taho ne dominta.

"Yauwa yaki nan" bibi ta fada tana yafitota. Dukka hankalinta ba abinda ya bata sai bibi ta kirata ne ta qara jaddada mata batun auren ayana da laila da maina zaiyi tare da bikinsu najma

"Wai ke kika bawa wannan ja'irin damar tafiya Nigeria zuwa........."


"Wallahi bani bace bibi........bani bace,bibi don Allah ki hanashi......ki gaya masa kada yaje.......inasonsa wallahi......ina qaunarsa bibi.......zuciyata ba zata iya jurar ganinsa da kowa ba......ina sonsa......kice masa nace ina sonsa,ina mutuwar sonshi fiye da yadda yake sona.....nafi sonshi bibi akan son da yakeyimin......yace aure zai qara.......laila da ayana yakeso yanzu......zaije Nigeria neman auren laila bayan ayana kuma...... wallahi bibi bazan iya jurewa ba" ta qarasa fadi hawaye yana sauko mata.

Dif wajen yayi,kunya ta kama aba qwarai da gaske har ya kasa motsi,yayin da bibi mamaki ya kamata,sai kuma a sannan ta fahimci lallai hankalin sultana yayi gaba,bata kula da kowa a cikin falon ba sai ita.

"Zo nan ja'iri,don qaniyarka abinda ka gaya mata dama kenan?,baka ko lura da ba'a gayawa masu juna biyu tashin hankali irin haka ba.?" Zancan bibi ya sanya aba zare jikinsa cikin dabara ya lalubi hanyar barin falon tun kafin sultana ta watsatsake ta sameshi a wajen.

Wani irin sassanyan abu ya soma ratsa zuciyarsa yana narkar da wannan dunqulallen abun me zafi da quna daya tsaye masa a wuya tun ranar farko data soma ware idanunta ta kalleshi tace

"Bana sonka!,bana qaunarka!,i hate you"

"Dakai nake kaketa fama murmushi kaman wanda aka bawa tallan maclien"

"Bibi" ya kirata a tausashe da wata irin murya da farinciki yake gauraye da ita

"Ni nace mata ina neman auren ayana ma bare laila?......da bakina na taba gaya mata haka?…...sultana" ya kira sunanta yana takowa gabanta

"Yau da zan fita na gaya miki ni zan nemawa kaina auren laila?......bibi kaman bakisan zancan suhail da sardauna akeyi ba kin manta?" Dif wuta ta dauke mata,a hankali idanunta suka fara washewa daga rufewar da sukayi,ta fara hango uncle bashar da yayi qasa da kansa,gefe oncle issofou ga kuma oncle umar.........*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 143



Dukkansu suka lula wata duniya......duniyar da basa gane kowa sai kawunansu,duniyar da a lokacin suka manta da kowa da kuma komai. Sirrikan zuciya ne kawai ke tona kawunansu cikin wani irin jirkitaccen yanayi wanda dukkansu su biyun basu taba fuskantarsa ba. Gigicewar qwaqwalwa da dimaucewar tunani.....ba abinda ke tasiri sai QAUNA me wani irin matuqar qarfi dake wanke laifuka ga zukata,ta kuma goge kowanne irin tabo bacin rai da kuma quncin zuciya.

Suna tsakiyar wannan yanayin wayarsa ta fasa qara. Cikin zafin nama ya miqa hannu da zummar kasheta don baya buqatar komai da zai katse masa wannan yanayi me matuqar tsada a gareshi...... yanayi mafi soyuwa a gareshi fiye da dararen farko ga angwaye. Akayi rashin sa'a ya daga kiran a maimakon kashewa harda guzurin shigar da wayar handsfree.

Muryar suhail ta fito fes ta cika dakin,cikin wata muguwar kasala ya zare jikinsa daga gareta a hankali yana sauke numfashi a jejjere kaman wanda yayi tseren gudu da dawakai

"Zamuyi missing flight fa......kana duba time kuwa?" Lion eyes dinsa da suka qara girma suka kuma sauya kala ya lumshe yana furzar da iska,qoqarinsa ya daidaita numfashinsa kada yayi magana suhail ya fahimci yanayin da yake ciki

"Hello.....maina"

"Ina jinka" yayi qoqarin fadi

"Wulaqancin naka ne ya motsa?,don baqinciki saida layi yazo kaina sannan zaka tsiri mugun halinka?"

"Ni kake gayawa haka?" Ya furta calmly yana nuna qirjinsa da yatsarsa.

"An gaya maka waye kai?" Ya fada da sautin dariyar da ake qoqarin boyewa.

"Alright......to na fasa zuwa bazanje ba......kayi duk abinda zakayi,Allah yasa su hanaka lailan muga ta tsiya...."

"Mugu saboda kai ka samu?....." Bai tsaya ya gama jin abinda zaice ba ya katse kiran gaba daya ya kuma kife wayar. Bai taba kawowa dukkansu zasu amshi batun laila da ayana haka da muhimmanci ba,koda yake ya sani wani abu ne kawai da ubangiji ya shiga cikinsa, bayan dimbin tarin addu'a daya dinga yi dare sur akan ubangiji ya kawo daidaito a tsakaninsu.

Already an bashi laila,amma kuma madaurin aurensu yana Nigeria,sai suka yanke zuwa gaidashi hade da nemawa sardauna ayana. To amma shi suhail dinma yafi sardauna matsuwa da damuwa,kamar wanda akace an fasa bashi lailan.

Da wani irin narkakken kallo ya waiwaya gareta,bai samu ganin fuskarta ba don ta duqunqune waje guda,ya sanya hannu ya birkitota,daidai sannan aka soma knocking qofar.

Wani wawan tsaki ya saki yana sake adanata a qirjinsa da kyau,tana jin yadda zuciyarsa ke fat fat fat,ta lumshe ido tana jin sautin cikin kunnenta

"Sulthana" ya kirayeta da wannan salon kiran da tayi imani duk duniya babu wanda ya kaishi iyawa

"Anya zan iya ci gaba da zama cikin gidannan?,.a tabbatar bazasu barmu mu mori amarcinmu ba?" Kunyace ta kamata da abinda ya fada,wanne irin amarci da yara biyu ga tsarabar wani cikin ma?.

Kafin wani a cikinsu ya sake magana aka sake knocking qofar sosai. Wani dogon tsakin da yaf na dazu ya kuma saki,jikinsa a matuqar mace ya miqe yana maida bottom na rigar shaddarsa da tuni tayi squeezing sosai,ya taka a hankali ya fita yana mita a fili.

Numfashi taja sosai tana qanqame pillow tana jin yadda mararta ta daure sosai. Har ga Allah itama an shiga nata haqqin,kowanne bangare a jikinta yana buqatarsa,batasan haka tayi mahaukacin kewarsa ba sai yanzu,batasan haka ta zama addicted to him ba sai yanzu.

A zafafe ya bude qofar,almu yaja da baya yana rabewa,ya sani ko ada ba mutum bane meson a yawaita masa knocking ba.

Jirkitattun idanunsa ya kafeshi dasu,har sai shakka da tsoronsa suka saukarwa almu.

"Ama tace na gaya maka aunty sultana ta shirya,ga dr noor nan zata shigo ta dubata" idanunsa ya maida ya lumshe yana dora hannunsa saman goshinsa. Bayajin zamansu cikin gidan zaici gaba da dorewa gaskiya,yasan muddin suna zaune ko iya kulawar ama garesu ba zata basu cikakken lokaci ba. Qofar ya tura kadan sannan ya taka yana komawa ciki. Yadda yayin. Ya ishi almu amsa,don haka ya juya yana barin wajen gami da sakin ajiyar zuciya

"Allah ya soni". Ya fada a fili yana yiwa kanshi dariya qasa qasa.

Cak ya dagota yana kallon qwayar idanunta ita kuma tana qoqarin boyewa,ya saki dariya a hankali yana tura fuskarshi cikin fuskarta yana laluben kunnenta

"Baby yayi missing daddynshi?...." Riqeshi tayi da kyau kunya tana dawainiya da ita tana kuma boye fuskarta a jikinsa

"Wait....." Ya furta yana qoqarin dagota,saita hanashi,wannan ya sanya hankali kwance ya sauketa gami da zaunar da ita saman sofa. Tana qoqarin kwanciya ya tallabota ta zauna sosai,sai ya sulale a gabanta ya duqa bisa dukka gwiwoyinsa,yasa tattausan tafin hannunsa ya riqe hannuwanta yana kallon tsakiyar qwayar idanunta

"Sulthana" da fararen idanuwanta ta amsa masa,abinda ya sanyashi hadiyar yawu da qyar,ya tarkato sauran nutsuwar data rage masa yaja numfashi sosai sannan yace

"A bedroom...... sulthana nakeso gani zahirinta...kin fahimta?" Wuya ta langabar tana narke masa fuska gami da turo lips dinta na qasa saita girgiza kai kadan

"Ya salammmm" ya fadi da sauri yana runtse idanunshi. Yadda tayi masan gaba daya ta sake tsomoshi,sai yaji yana craving nata qwarai da gaske,kamar ya toshe kowacce qofa da zata sada jama'a dasu

"Exactly wannan sultanar!" Ya fadi da karsashinsa yana nunata da yatsansa idanunsa cikin nata.

"Sultana shagwababbiya....... sulthana sakakkiya........sultana mara jin magana........ sulthana mara kunya.......amma dukka a bedroom dina.......akan gado na......." Sai kuma ya sassauta murya can qasa

"......idan mun fita waje kuma ki zama mummyn twins.......matar aliyyu maina.....the owner of my heart,my life and my breath.....kiyimin alqawari" ya fadi idanunsa yana lullumshewa.

Kai tsaye a yanzun ta kalleshi da fari qal din qwayar idonta.

"Ka fadi ko meye kakeso......ka fadi ko meye kake da buqata daga wajen sulthana......nayi maka alqawarin zaka samu fiye dashi" fuskarsa ya kifa tsakiyar tafin hannunta,hannunsa ya shaqi wani irin launin qamshi daya banbanta da qamshin jikinta,ya daga kansa a hankali yana sake kallonta da narkakkun idanunsa

"Kiyimin alqawarin bani sabon ruhi......kiyi alqawarin bani sabuwar rayuwa......kiyi alqawarin lullube rayuwata da tsaftatacciyar soyayya..... kiyimin alqawarin rayuwa dani har abada..........ki sadaukarmin da raywarki sulthana gaba daya".

Gaba daya kalamansa sun qarasa kashe mata jiki,har taji kaman qwalla zata fito daga idanunta,sai kawai ta zamo daga saman kujerar itama tana riqe da hannuwan nasa

"Rayuwar sulthana naka ne yaa maina......ka manta da wadannan hannuwan ka raineta?,ka manta kaine ka kafa tubalin rayuwarta?,ka manta kaine ka bata dukkan wata rayuwa data dace da ita?,kaine ka bata qwarin gwiwar rayuwa ka kula da komai nata......kaine sulthana......kaine rayuwa da komai na sulthana,kaine numfashinta.....ka manta jininka ke yawo a jikin sulthana?,ka manta jininka aka zubawa sulthana ta miqe taci gaba da rayuwa?...." Idonsa ya sake lumshewa yana jinsa tamkar yana yawo cikin iska.......yana jin wani abu daya zarta farinciki yana dawainiya dashi

"Zan baka fiye da rayuwar daka sanya rai a kanta.....zan baka sama da farincikin da kake mafarkin samu......zan zame maka tamkar uwa.....zan zame maka tamkar 'ya zan kuma zame maka mata......in sha Allah"..

Duk dauriyarsa ta qare,babu wani sauran juriya ko dagiya tattare dashi ya jawota yayi mata wata wawiyar runguma. Sai digar hawayensa taji kawai tsakiyar kanta daya ratsa sassalkan gashinta dake tarwatse a gadon bayanta.

Zuciyarta tayi wani irin laushi,jikinta ya mutu murus. Ya haidar da babu wani abu da za'a ce ya taba sanyashi kuka a iya tsahon sanin da akayi masa?,yau shine yake kuka a kanta har karo na biyu?,ya haidar me kafiya da tsaiwa akan raayi,me kuma tsatstsauran ra'ayin da baya canzawa yau shine duqe a gabanta yake kuka?.

"Ba GUDUN QADDARA nayi ba sulthana.......ki yafemin......please......bansan da wanne idanu bane zan kalli su aba da bibi......na taba marainiyarsu......na taba ajiyar da suke riritawa......na taba halittar da sukewa masifaffen so......muddin na zauna a lokacin fushin aba zai iya lalata rayuwata,don bansan da wanne furuci zai jefeni ba......motsa zuciyar ama da nayi a sannan sannan kuma tana ci gaba da kallona zai iya saukar da fushinta a kaina......na tafi ne da zummar sai kowa ya huce sannan na dawo,ashe wata QADDARAR tana biye da dukanmu.....ashe ke din nabar mikia ajiyar bayin Allah cikinki......ni kuma qaddarar mutanen da zasu kamaji su nemi shigar dani kalar aikinsu yana bibiyata.....da qyar na kubuta daga hannunsu,sunmin daurin talala,sun barni inje dui inda zani,amma duk takuna qwaya daya tak suna biye dashi.....ashe bazanga girman daddyn sardauna ba?,me yasa bazan girmama musu laila ba?,shine silar kubutata daga hannunsu,ya daukeni ya bani kalar rayuwar da nake buri,duk kuwa da cewa......daga ranar dana aikata miki abinda ya farun duk wani buri na na zama soja ya zagwanye ya fita a kaina......na kalli kaina a madubi yafi sau shurin masaki ina gayawa kaina tabbas bani da imani......aikin soja bai dace dani ba.....tunda har na iya haikewa wannan 'yar qaramar babyn ta bibi......na iya sauke mata huqatuna masu girma da nauyi na shekara da shekaru ba tare dana duba qanqantarta ba......ashe dai wannan babyn itace rayuwata.....mabudin farinciki na...... wannan babyn ita zata zama mummy..... Mummyn twins da upcoming triples in sha Allah......." Ya qarasa fadi murmushin farinciki da nasara yana kubce masa.

Duka idanunta ta zaro waje tana kallonsa,sai kuma ta shagwabe masa kwatankwacin yadda take masa a baya

"Do you know how i survived yaa maina.....na kusa mutuwa fa kafin na haif......." Yatsansa ya dora mata saman lips dinta yana fadin

"Shshshsh......." A tausashe

"Nasan komai sulthana..... kowanne motsi na rayuwarki ina da information akai har zuwa rana ta qarshe a hassan gwarzo.....kina cikin depression da anxiety a lokacin...... yanzu kuma ga beloved person a gefanki.....Likitanki,duk da ba bangarena bane amma na miki alqawarin baki kalar kulawar data banbanta data kowa.......ke kika dasamin son twins sulthana......daga ranar dana fara ganin hotunansu benazeer suka zama jarrabawar rayuwata.....Allah ya jarabceni da soyayyarsu irin wadda bayan ke ban taba jin irinta akan kowa ba idan kika cire ama........ashe su din nawa ne......daga randa kuma nasan cewa nawa ne......a ranar burikana suka ninninku....Wallahi,Allah sulthana burina a duniya kiyita haifa min uku uku bibbiyu" hannunsa ta kama tana dariya ta aza saman goshinta,ta buda baki zatayi magana sautin wayarsa ya katsesu.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 144



Sunan ama ke yawo saman screen din wayar,ya saki sultana yana daga wayar.

"Me kakeyi haka ne aliyyu?,ban gaya maka ga Dr Noor nan ba?"

"Afwan ama....." Ya fada. A tausashe,bata sake cewa komai ba ta katse wayar,shima sai ya kashe yana ajjiyeta a gefen sa.

Ido ya zubawa sultana kaman bazai dauke idanun nasa ba sai kuma yace

"Get ready......yau ko gobe zamu bar gidan nan......zamu tare a namu gidan sulthana bazan iya zama a nan kusa ba" dubansa tayi,tana mamakin hakan da yace,don tayi tsammanin zai rayu cikin gidanne kamar sauran kawunnansu. Kai ya jinjina mata yana miqewa ya nufi toilet.

Tsarki yayi yayi alwala sannan ya fito itama yace taje tayi,ya zare shaddar jikinsa data gama yamutsewa ya sauyasu da wani tattausan yadin vicuna me asalin tsada da aka yiwa aikin kufta na zamani. Ita kanta data fito sai daya dauki hankalinta,ta fahimci gayunshi ya ninka sosai,idan batayi da gaske ba da alama zai nuna mata feleqe da iya ado.

Jawota yayi ya karata da jikinsa yana murmushi

"Idan baki gaji da kallona ba mu zauna,sai na bawa Dr Noor haquri,mu shanye fadan ama tare dake" rau rau tayi da idonta. Duk sanda taga Dr noor sai ta tuna wahalan da tasha cikinsu benazeer,bata tunanin akwai wani guri dake daukan allura a jikinta da ba'a bulashi ba

"Don Allah yaa maina......kace mata kada tayimin allura,ko magunguna kadan don Allah"ta fadi tana narke fuska.

Murmushi ya qwace masa,ya saka tafukan hannayensa biyun duka ya kamo fuskarta tsakiyarsu yana matso da fuskarta dai dai tasa

"Ki yarda dani....duk cikin da za'a raineshi cikin soyyaya da kwanciyar hankali daban yake da wanda ba'a raineshi ta haka ba,zakiyi lafiyayyen ciki fiye dana baya......ba allura ba tarin magunguna ba kwanciya asibiti........in sha Allah" da iya kalaman bakinsa kadai sun saukar mata da nutsuwa,ya sanya mata hijab ya kama hannunta suna wucewa falon.

Bata tashi jin kunya ba sai da suka hada ido da Dr Noor. Ta tuna abubuwa da dama da suka wuce lokacin cikinsu benazeer,wai yau sai gata zaune gaban dr noor din da wani cikin.

Ta dubata sosai ta kuma tabbatar da komai lafiya,amma tace

"A kula da ita sosai,don cikin kamar wancan ne nake tunani" sai ya tuna maganar Dr Camille,satin da tace su koma tahowarsu nijer ya tashi basu koma ba,ya barshi ne da zummar zasu je din idan sun koma paris.

"Wannan karon kamar kinfi jarumta ma.....kamar 'yan uku nake hasashe......" Dr Noor ta fadi cikin salon tsokanar nan nata

"Amma sir maina yaci gari......don ba haka mukayi dake ba......"

"Please don Allah Dr Noor" sultana ta fada tana qunshe bakinta cikin matsananciyar kunya,ta tabbatar tsiya Dr noor zatayi mata,zata tuna mata maganganun data dinga fada ne cikin quruciya da kuma damuwar da ta ninkawa kanta saboda cikinsu batoul.

"Wani abu ne Dr?" Maina dake son ya samu abun tsonakarta ya tambayi Dr noor

"A'ah sir.....abar kaza cikin gashinta" Dr noor ta fadi tana dariya dariya

"Zan iya siyan labarin?" Ya tambayi Dr noor yana duban sultana data marairaice masa dariya nason zuwa masa,ya tabbatar ta sheqa quruciya me yawa shi yasa bataso aji.

"Idan farashin yayi mani sai na siyar" Dr noor ta kuma fadi bayan ta gama hade komai nata

"Dollar dari uku yayi?"

"Ma sha Allah labari yayi tsada......tace ba zata sake ma aure ba bare ta haihu,ta gama haihuwa har abada.....su wadannan ma ita ba ita tayi cikinsu ba su sukazo suka shiga cikinta bata sani ba......kana zaman zamanka abu ya shige maka ciki yayita hura maka ciki cikinka yana zama qato don mugunta bayan kai ko abinci baka iya ci?.......at last kuma ta fashe da kuka......na shiga tausayinta a ranar irin tausayin da ban taba yiwa wani patient nawa ba".

Da farko dariya tazo masa,amma maganar Dr noor ta qarshe ta narkar masa da zuciya har ya kasa dauriya ya sanya hannunshi ya lalubi hannun sultana ya riqe sosai cikin nasa. Bashi ba har dr noor din ma data tuna da labarin kana kallon fuskarta zakaga ta sauya. Ita kuwa murmushi kawai takeyi qasa qasa kanta a qasa, quruciya da wautar data tafka ke dawo mata.

Koda ya bawa Dr Noor Dollar din qin karba tayi,amma ya sanya almu yabita da ita har motarta ya saka mata a seat din baya.

Shuru ya ratsa bayan fitar Dr Noor,ya kasa cewa komai sai murza tafin hannunta kawai da yakeyi,yana hango irin jarumtar da tayi duk da quruciyarta,har yanzu ya kasa hasashen abinda zaiyi mata ya biyata

"Am really sorry sulthana.....har yanzu sai naji kamar idan nace miki kiyi haquri bai wadatar ba"

"Sorry for what ya maina?.....qaddararmu ce.....akwai wanda ya isa YA GUJEWA QADDARARSA,gudun qaddara fa guzurin tarar da ita". Kai ya jinjina yana mamakin yadda taji hausa haka,koda yake Nigeria ta zame musu kamar gida kuma uwa.

Yaso zamansu ya dore a falon amma hakan bai yuwu ba,a hankali a hankali sai ga masu dubiya cikin gidan da baqi sunata shigowa. Dole badon yaso ba ya tattare falon yayi qaura yabar musu nan.

Baisan bayanin da Dr noor ta yiwa ama ba,amma wani sabon salon jinya yaga an fiddo dashi. Ama din ta shigo da kanta sunyi maganganu da sultana,baisan me suka tattauna ba,amma ya damu mutane su janye yaji meye ama ta fadi?. Tanja ta aiko sashen ta soma gyaran wani bedroom din daban,da alama kuma umarni tanja ta samu,duk wani motsi na sultana tana kula dashi,sun hanata komai,komai tana daga zaune akeyi mata shi wunin ranar.

Baya falon amma yana bibiye da komai shima ta CCTV camera din dake cikin falon. Yadda sultana din ta sake cikin mutane ya masa dadi,amma kuma yana jin su nesantashi da ita. Yana jin lokacin cin amarcinsa ne amma sunason kawo masa cikas. Wani abu da yayi masa dadi yadda ya fahimci time to time tana duban sashen dakinsa. Hakan ya masa dadi sosai,mutum ne shi me matuqar son a nuna soyyaya a gareshi,musamman ga abinda shima zuciyarsa ke matuqar so din.

Sanda ya idar da sallar la'asar cikin masallacin layinsu sai yayi zamanshi daga gurin da shekarun baya yafi zama cikin gidan. Iskar wajen tana masa dadi qwarai tana kuma saka masa nutsuwa sosai. Kira ya shigo wayarsa,koda ya duba sai yaga sardauna ne.

Sau biyu yana kira bai sameshi ba,don dama bai kira suhail ba,yasan idan ya kira xasu taba rigima yadda suka saba.

"Boss.....sir.....surukina" duka sardauna ya fada lokaci guda. Murmushin nan nasa me sanyi ya qwace masa

"Kaima yau?"

"Ai dole,ba sake tabbatarwa da nayi dacen dan uwa ba irin wannan lokacin,familyn ama akwai karamci da mutunci,na dace da samun ayana......an bani ayana halak malak"

"Alhamdulillah" maina ya furta a fili. Har cikin zuciyarsa yana jin farinciki yana ratsashi. Duk da sun soshi basu sameshi ba,amma kuma ya musu silar samun mazaje tamkarsa,yayi silar danganasu da inda yake tabbacin za'a riqesu kaman yadda zaiyi nasa qoqarin.

"Saika qara masa da bayanin kawu ya karbeni hannu bibbiyu,laila ta zama tawa" ya jiyo muryar suhail daga gefe. Maganar tasa ta saka dole murmushin ya sake kubcewa maina,ya girgiza kai kawai yana fadin

"Zamuyi waya anjima,amma wannan surukin naka ka samu majanyi da kyau ka daure masa wannan kan nashi dake fama rawa" dariya sardauna ya saki shima suka katse wayar a tare.

Wayar ya mayar gefe yana dora idanunsa ga bangaren sashensa. Yana kallon yadda masu dubiya ke shiga suna fita,ya sake ajiyar zuciya. Bazai iya jurewa

Please Login or Register in order to submit comment