Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida

"Yo ku meye naku ne bayan kowannenku yana nashi gidan da iyalinsa?,ku jiyemin yara da sanabe?" Hajja kakarsu ta fadi tana kama haba

"Gidan ne ba kowa fa,daga maama sai masu aiki" tajuddeen ya fada

"Sai kuma kayita yi,amma tabbas jikina ya bani nijer saita janye hamdiyya" ta fadi saboda yadda taga tana sha'awar qasar sosai da son zuwa tare da son zama a cikinta.

Kai tsaye qanin mahaifiyarta ya soma mata cuku cuku sanda aka fara diban dalibai a matakin karatu na gaba da secondry. A tsarin jami'ar hamdiyya bata da wani aibu ko nakasu da zaya hanata samun gurbi. Results dinta sunyi kyau har abun ya dinga basu mamaki,saidai kuma ba abun mamaki bane,saboda baiwar wata budaddiyar kwanya Allah ya bawa ita hamdiyya din,abun kuma sai ya hadu da nacin son karatu da take dashi.

Sanda ta shiga makarantar hamidou(aba) yana aji uku,kuma shine president na makarantar gaba daya. Ranar data fara zuwa ranar ta fara ganin aba din, saboda a ranar sun gudanar da zanga zangar lumana cikin makarantar. Tana zaune daga qasan bishiya tana jiran driver ya iso ya dauketa,tanata zumbura baki irin na yaran da gata ya yiwa yawa,tana jin yadda zafin rana ya bude a sararin makarantar ya hadu da rairayin yashi yake bada wani hucin zafi har saman fatarta,daidai sanda dandazon matasan makarantar suke yowa ta area din da take.

Tsaki taja me qarfi tana qorafi cikin ranta na yadda ko zafin ranar sukam basuji?. Tana zaune har suka qaraso inda take suna wucewa da ifce ifcensu wanda yake cikin tsari ne ba hauka bare sauka daga tsari.

Da idanu take binsu kawai bakinta a tabe daya bayan daya,tanason gano waye shugaban wannan wahalar?,sukam me suka rasa da zasu damu kansu da surutai haka da rally cikin makaranta?. Caraf idanunta ya sauka saman fuskar kyakkyawan matashin buzun. Sanye yake da wasu jajayen kaya da baqar p cap wadda duk da ta dan rufe fuskarsa kadan amma hakan bai hanata hango gumi da yadan jiqa goshinsa ba,ya kuma bada damshi saman kyakkyawar fuskarsa dake da wani irin sassanyan kyau me matuqar jan hankali.

Kaf yawun bakinta ya katse,ta qifta idanunta ta sake budesu duka lokaci guda tana hadiye busashen miyau din da yayi saura a bakinta. Tunda take zata iya cewa idanuwanta basu taba tozali da namiji me kyan aba ba.

Bata cika buri cikin rayuwa ba,bata da wulaqanci sai son jama'a da take dashi,bata da daukan rayuwa da zafi saboda ta fito daga gidan wadata,amma kuma tana da wani buri qwaya daya da kaf gidansu hatta da abbanta da wasu makusantanta na kurkusa sunsan dashi,wato tana son KYAKKYAWAN NAMIJI. Ba wai abu bane data tsireshi bayan ta girma ba,ko kuma bayan ta fahimci ita dinma me kyau ce ajin farko, a'ah tun tana qanqanuwarta take da wannan dabi'ar. Mama mahaifiyarta bata zafafa mata ba tun daga quruciyar,saidai ta zafafa wajen addu'ar idan ta isa munzali qaddarar aure ta zowa diyartata ubangiji ya hadata da nagartaccen miji salihi kuma managarci. Tun su abdulhakeem suna tsokanarta har suka fahimci da gasken gaske a jininta ne kuma raayinta ne hakan,sai suka daina tsokanar suma sai lokaci bayan lokaci.

Akwai tarin maza da suka amsa sunansu,masu kyau irin kyan nan abun kwatance da suke maqurar qaunarta da neman soyayyarta,to amma sai Allah ya sanya mata wani irin hali na shariya da miskilanci. Duk son jama'arta da haba haba dinta miskilar kanta ce idan taso.

Bada umarnin da aba yayi wajen dakatawa aje a bada faralin sallah ya sake fusgar hankalinta,tana nan a zaune taron ya watse,ya nufi hanyar masallacin makarantar bangaren maza yana zare pcap din kansa shi da 'yan tawagarsa suna tattaunawa,cire hular kuma da ya sake bayyanar mata da asalin kyansa.

Tun daga ranar bata sake ganinsa ba,hakanan zuciyarta bata huta da tunanin waccan ranar ba. Bata kuma sake ganin nasa ba sai bayan watanni shida,karatunta ya soma yin nisa,ana shirye shiryen fara exams da tafiya hutu. A sannan ne dalibai suka qirqiri wasu programs da sukan gabatar a lokuta irin wadannan,ciki harda zaben sarauniyar kyau ta makarantar.

A lokacin sai kawai gani tayi sunanta ya fita cikin list din wadanda zasu tsaya a matsayin. Ranta ya baci hankalinta kuma ya tashi. Tana da qawaye tunda ita din macace me kirki,bata raba dayan biyun a cikinsunne wata ta bada sunanta,kuma tunaninta ya tafi kan mutum daya data tabbatar bazata wuce ita bace wato ummuhani mammadou. Koda ta tuhumeta din kuwa ita dince. Fada ta balbaleta dashi akan ba zata shiga ba,tace kuma tun wuri su zame sunanta don ba abinda tazo yi ba kenan.

Lokacin aba na zaune cikin 'yan kwamitin tsare tsare ummahani ta shaidawa hafeez wanda shi ya qirqiri abun cewa hamdiyya na buqatar a zame sunanta,ta kuma baiwa hafeez haquri,wanda koda bayan ummahani ta wuce bai fasa qorafi ba

"Ita daya ce zata sanya makarantarmu taci wannan competition din,yanzun wace zata maye mana gurbinta?"

"A soke wannan cikin tsare tsarenmu hafeez, banason irin wadannan abubuwan" shine kawai abinda aba yace.

Bai taba ganinta ko lura da wanzuwarta ba sai ranar da aka fara programs din. Sai kuma a ranar program din da aba yace a soke yaji basu soke din ba,don a wajen aka fara neman 'yammatan da suka shiga suzo su fara rehearsal.

Ko motsi hamdiyya batayiba sanda aka kira sunanta saboda tasan tuni ta bada sanarwar fita daga lamarin. Aka dinga maimaita kiran sunanta amma ko motsi,abinda ya sanya MC pointing dinta don shi ya hangota,take kuwa idanu sukayi caaa a kanta. Adadin idanuwan ya sanya kanta sarawa,sai kawai ta miqe tsam ta dinga ratsawa ta cikin jama'a har ta fice daga hall din.

Haka kawai aba yaji ranshi yayi matuqar baci,bai wata wata ba ya karbi mic daga hannun mc din ya fara bada sanarwa dakatar da shirin. Sanarwar data hargitsa hall din qananun maganganu suka dinga tashi,shidai a matsayinsa na shugaba ya riga ya zartar da hukunci,ya tabbatar kuma dukka mataimakansa ba wanda zaija da hakan saboda zuwan halayensu kusan iri daya,sai kawai ya saka kai shima yana barin hall din.

Baisan tana ta wajejen ba sai daya isa ya tsaya yana furzar da iska sai yaji sautin sheshsheqar kuka kuma ana waya

"Kice musu su qaraso su daukeni gida zan koma" idanu ya zuba mata cikin mamakin yadda qatuwar budurwa irin haka ke kuka shabe shabe da hawaye,jajayen labbanta sun sakeyin ja haka bakinta. Taku biyu tayi Don gyara tsaiwarta santsin wajen ya kwasheta zata fadi. Da hanzari yakai mata taimako Allah ya taqaita kafin ya isa gareta ta samu ta dafa wata qaramar bishiya ta tsaya

"Ki ding kula mana" ya fada cikin nuna damuwa. Kai ta daga da sauri,idanunsu suka gauraya waje guda,wani irin abu me qarfi ya sauka zuciya da gangar jikin kowannensu,sai kowa cikinsu yayi hanzarin janyewa da baya,yayin da ciwon kan hamdiyya ya qaru har sai data saka hannu tadan riqe kan

"Baki da lafiya?" Ya tambayeta yana qoqarin kallon qwayar idanunta. Idonta ta lumshe tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugu da bata taba yi ba ta gyada masa kai

"Saiki tafi gida ko ki wuce hostel ki nema magani Kisha" ya fadi yana janyewa baya saboda shi din ba gwanin kula mata bane.

Ta qasa qasa take kallonsa,qafafunsa sake cikin wasu Black sneakers na motsawa da alama wajen zaya bari

"Ka taimakeni ka miqani gida,bazan iya tuqi ba,bani da nisa daga nan" dukka ta bashi maganar lokaci daya. Dan jim yayi yana kallonta duk da baya iya ganin zahirin fuskarta. Kamar zai musanta sai kuma ya tuna da maganar da Bibi ke yawan gaya masu

"Su mata ababen tausayi ne,a duk sanda suke cikin taimako ku taimaka musu gwargwadon iyawarku" wannan maganar ta sanya ya koma ya amshi key din a hannunta yana satar kallonta,haka kawai zuciyarsa ke bugawa a kanta tun ganin farko da yayi mata dazun. Ya zagaya ya bude mata ta shiga sannan ya rufe ya dawo ya shiga shima ya tayar da motar yana godewa Allah da ya sanya ya koyi mota da yau baisan yadda zaiyi ba.

Yadda yake tafiya a hankali da motar,da alama kuma yana yin hakanne dukka don ciwon kan nata sai ya sake narkar mata da zuciya a kansa,sai take ganin yaa tajuddeen da yaa abdulhakeem tattare dashi,haka suke mata irin wannan riritawar. Zuciyarta nata mata saqe saqe akansa,yayin da shi kuma yayi nisa wajen satar kallonta ta cikin madubin gaban motar yana tsarkake ubangiji da irin kyawun halittar da ya bata.

Ita ta dinga kwatanta masa hanya har suka iso gidan,a LOKACIN sai da jininsa yadan daskare na wucin gadi,tsoro kuma ya kamashi na ganin yarinyar da ya rako

"Yanzun idan tayi maka wani qazafin fa?" Abinda ya bashi fargaba kenan,amma da yake namijin duniya ne sai ya daure ya cusa hancin motar har zuwa farfajiyar gidan.

Sanda dukkansu suka fito a motar sai kowa ya rasa bakin magana,ita tana tauna abinda zatace ne kada ta zubda ajinta da kimarta na mace,shi kuma yana dari d'arin ya kawo kansa gidan dafa kansa.

Muryar hajja ta katsesu ta qaraso tare da uncle din hamdiyya. Cikin nuna matuqar kulawa take dubanta kamar tana neman gurin da aka gutsireta tana tambayarta

"Ya akayi kika iya dawowa da kanki?,ke da nace ki jira su soja sun tafi dauko mato daga airport suna kusa daku saisu daukoki?" Hamidou ta nunawa hajja tana mata bayanin shine ya taimaketa. Abinda ya daure masa kai harda qarawa abun gishiri da armashi.

Kaman hajja ta goyashi haka ta dinga zuba masa godiya tamkar wanda ya qwato mata jika daga wajen kidnappers. Hanashi tafiya hajja tayi,cikin lokaci kadan sai gashi ta sanyashi ta dole ya sake cikin gidan. Cikin mintuna kadan yaga kamanceceniyar halaye tsakaninta da granny nadeeya dinsu da har yau basu manta da ita ba. Ya kusa awa daya tana jansa da hira,sannan ta cika masa gaba da kayan ciye ciye. Koda ya tashi tafiya amana me nauyi ta aza masa,wato amanar kula da jikarta

"Ka taimaka.ka karbi wannan aikin,duk da nasan na aza maka nauyi,don Allah,saboda kowacce makaranta akwai bata gari na sani,to amma zasu kiyaye idan sunsan akwai wani namiji a tare da ita,nayi nayi a sama mata masu tsaron lafiya koda mutum biyu ne amma ta qiya,ita wai sam batason irin wannan rayuwar" dan satar kallonta aba yayi,daga yanayinta kawai da yadda yazo ya samu family dinta yasan lallai tana da sauqin kai da rashin daukar rayuwa da zafi,a arziqin da Allah yayi musu yayi imanin inda watace ma sam tabar rayuwa a Nigeria.

Tsohuwar ta masa kwarjini da yawa dole ya karbi amanar hamdiyya ba don ya shirya ba. Wanda hakan ya fara kawo alaqa tsakaninsu me qarfi,ta dauke tamkar yayanta,shima kuma kaman qanwarsa,wani lokaci ma tare suke tafiya makaranta cikin motarta,donma yana goggocewa kasancewarsa mutum da ya iya kamun kansa yasan kuma kimar martaba da darajarsa. Duk da haka komai nata saita tsomashi a ciki,idan yaqi ma takan hadashi da tsohuwar dole saboda girmamawa yayi din.

Shi da ita dukkansu soyayya tayi musu mugun kamun da basu zata ba,ga hamdiyya dai tasan tabbas ta fada dumu dumu cikin soyyayar hamidou,amma kuma ba zata taba yin abinda zai watsa mutunci da darajarta ta diya mace ba. Abinda bata sani ha hamidou ya fita shiga garari,domin kuwa kusan har walwalarsa abun yaso.tabawa,daga bibi har hamma mohmoud ba wanda bai Kula ba,tambayar duniya ya kasa basu amsa,saboda shi kansa yasan bai daukowa kansa da su turba me bullewa ba,su da suke ririta rayuwarsu ta yaya zai dauko wannan babban aiki?.

A yanzun yana tsaka da karatunsa kuma nauyinsa yana wuyan wani mutum ne wato mohmoud,mohmoud din da ya kashe tasa rayuwar saboda ya raya tasa rayuwar?,ta yaya zai iya duban qwayar idanunsu yace ya fada soyayya?.



**_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 05
_______________________________
*_Shin kin isa mace?,don magana akeyi ta ISASSUN MATA_*

*_SUTURA ABAR TUNQAHO_*

*_Ado da kwalliya shine cikar 'YA MACE_*

_Magana akeyi ta_

*UMMU MAHNOOR LUXURIES*

*UMMU MAHNOOR LUXURIES*

_GIDAN QAWA ADO NA KECE RAINI_

*_INA AL'UMMAR KADUNA ABUJA SULEJA DAMA NIGER......HAR MA FADIN NIJERIA GABA DAYA_*

*_KIN SHIRYA FITA KUNYA?_*

*_MAZA HANZARTA KI LALUBI KALOLIN SUTURAR DA TA DACE DAKE,KAYAN ADO MASU_*

*KYAU*

*QUALITY DA DAUKAN HANKALI*

*LACES NE,SHADDA CE,ATAMFOFI NA 'YAN QWALISA*
*GA KUMA DESIGNERS TAKALMA DA JAKANKUNA NA ALFARMA DA FITA KUNYA*

*_ZAKU IYA SAMUN MAMALLAKIYAR KAMFANIN KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_*

08135142610

*INSTAGRAM* UMMU_MAHNOOR_LUXURIES

*FACEBOOK* MUSA GARBA SHIFA

*_Ga wadanda ke cikin garin abuja kuma zasu sameta kai tsaye a_*

*_system property Nefelix estate,near amasco,galadimawa roundabout_*

*_KARKI BARI A BAKI LABARI,KARKI KUSKURA KI ZAMA 'YAR KALLO_*

*TASTED AND TRUSTED*πŸ‘ŒπŸ‘ŒπŸ‘Œ
__________________________________


".............ya fada soyayya?,yana nufin kenan aure yake da buqatar yi?,bama fadawa soyayyar ba,wadda ya fada soyayyar da ita, yarinyar dake da gatan da ya kerewa nasa,suke da dukiya da tarin gatan da ya yiwa hankali nisan tazara,kai koda ma ace ya kammala karatunsa ya kama aiki ina yaga kudin auren hamdiyya abdu me kano?,ko yana da kudin aurenta dinmma sakayyar da zai yiwa bibi da mohmoud dake tsaye a kansa ba dare ba rana?,ya tattara 'yan kudinsa yayi aure ba tare da sun mori komai daga gareshi na wahalar da suka sha dashi ba?. Kansa ya girgiza yana bawa kansa amsa da A'AH,ya zama dole ya sake nisanta kansa da zuciyarsa daga soyayyar hamdiyya,hatta da mohmoud sai yanzun yaga an fara tada zancan aurenshi,idan bai manta ba wancan satin yaga ya fara shigo da akwati guda uku bibi na mata wajen ajiya,ta yaya shi da yaie sanya ran zai zamesu musu sanyin idaniya ya buge da wannan zancan?. Dama bai bari ko kadan zancan hamdiyya ya fasu cikin gidansu ba saboda gudun tashin hankalin bibi da kullum tsaronta akansu ne,sai kawai ya yanke shawarar fara janye jiki daga gareta da kuma dukkan al'amuranta.

Hakan bai haifar da komai ba saima sake dagula al'amarin da yayi,ta zube dukkan wautar dan fari da shagwabarta,kwatsam sai kawai gashi ta dauko mahaifinta tun daga Nigeria yayo tattaki ya iskeshi har cikin makaranta wai yazo sasantashi da hamdiyya,tace batasan laifin data yiwa yayanta hamidou ba yake gudunta. A ranar hankalinsa yayi matuqar tashi,ganin babban mutum me girman daraja wai yazo gareshi ban haquri?.

Kame kame ya dinga yiwa abban don baisan ma me zaice masa ba. Daga qarshe kawao abban ya saki murmushi yana dubansu

"Inaga gwara kawai na yanke muku wannan wahalar da kukeyi akan juna,kai yayan hamdiyya,indai ka aminta kanason hamdiyya ka shaidamin zan baka aurenta,ku sasanta kanku bari na baku waje" abinda abba ya fada kenan ya fita daga wajen cin abincin daya kama musu table daya.

Kamar zata hadiye zuciyarta haka ama taji sanda taji furucin bakin mahaifinta,tabbas inda ace ita daya ce a wajen ihu zatayi tayi tsalle tayi shewa,amma.yanzun duk yadda albishiri din yakai ga faranta mata dole ta kame kanta ta kuma zuba masa idanu tana jiran jin ta bakinsa. Kau dakai tayi sanda yayi nufin kallonta,a yanzun yana jin bazai iya boye mata komai ba

"Ina tsananin qaunarki hamdiyya bazan iya boye miki ba,amma kuma bani da halin aurenki saboda a yanxu nidin ba kowa bane,kuma bani da komai ban kuma bawa kowa ajiya ba,idan nace zan aureki hamdiyya na cutar dake,bani da arziqin riqeki,ki bari kiyi aurenki na gata,ki auri dan gata irinki da zai iya baki irin rayuwar data dace dake..."

"Ba wanda yayimin cikin maza babu kuma wanda nakeso saikai, hamidou xan aura ba alatun duniya ba,dukka maganganunka a yanxun ba hujja bane,saidai idan kanaso ka fake ne,ni hamdiyya ban maka ba" ta fadi tasirin sonsa na yawo cikin idanunta da wani irin kaifi.

Duk da ba'a mode da zaiyi dariya suke ba amma sai daya murmusa,bayajin tana masa rabin son da Allah ya jarabceshi dashi nata

"Baya ga bibi da 'yan uwana ban taba jin soyayyar wata halitta a zuciyata ba haka....."

"Indai hakane ka sanya a ranka ni hamdiyya matarka ce,ban kuma fi qarfinka ba" ta tari numfashinsa kai tsaye.

A nan gurin ta lalata masa dukkan wani tunani nasa da zazzafar soyayyarta ta hanyar kalaman bakinta,suka rabu suna kewar juna ainun saboda a yau din dukka wani qulli ya kwance soyayya kuma tayi ambaliya ta bayyana kanta.

Wajen tara na dare yana rungume da littafi yanason yayi karatu amma ya kasa saboda tunaninta,wayar hannu sai me wadata,su dinma ada akwaita cikin gidan,amma yanzun da rayuwar ke neman fin qarfinsu dole suka sakata a kasuwa suka saida.

Yana kwance daga daki yana jiyo hirar bibi da mohmoud,ya dawo daga aiki futu futu da tarin gajiya bibi ta zaunar dashi tace sai ya fara cin abinci kafin yayi wanka. A hankali yaji suna sako batun aurensa da bintou,da yadda za'a yi asiri ya rufu ayi komai a gama,don ma itama bintou din ba yar gidan wani bace,asalima bafulatanar katsina ce,yanayin aiki ya kawosu nan din,saidai kuma suna da tarin rufin asiri daidai gwargwadon yadda dan adam zai iya rayuwa cikin walwala. Yadda yaji suna maganar ya sake sanyayar masa da jiki,sai yaji batun hamdiyya tamkar ya ajeshi a gefe don baiga ta inda zai yiwu ba.

Washegari jinkirin isowarta makaranta kadai akan lokaci ya hautsinashi,ya gaza shiga aji ya zauna har sai da driver dinta ya ajeta. Ta fito tana masa hararar wasa da fararen idanunta

"Kada kacemin komai,ina shakka akan son da kace kana yimin,tunda har na qara awa daya kusan da rabi amma ka gaza zuwa ka taho dani har sai da driver ya taho dani" murmushi kawai yayi yana jin sassauci cikin qirjinsa tunda ta iso lafiya.

A ranar kafin su rabu ta damqa masa waya me kyau a hannunsa

"Mu dinga communicating,dare yanamin tsaho kafin wayewar gari nazo na ganka" amsa din kawai yayi yana juyata a hannunsa,bayason zaqewa ko zura jiki da yawa,bayason kuma su sake nisa shi da ita abun yazo baiyiwu ba ya zame musu ciwo shi da ita. Baice bazai karba ba bai kuma ce ya karba din ba,yabar wayar a hannunsa dai ya kuma shiga gidansu da ita.

Sam ya manta tana jikinsa har suka gama hira da bibi yaci abincinsa,yana shirin shiga daki ya watsa ruwa kira ya shigo,shi da bibi din duk sukayi sak sai ya ciro wayar yana dubawa. Alarm ne, kasheshi yayi ya matsa gaba ya ajjiye wayar gaban bibi yau yana yankewa a ransa ya shaidawa bibi komai,tunda cikin maganganun da sukayi a yau da hamdiyya ta shaida masa abbanta ya bawa aba din damar fitowa neman aurenta saboda duniya ta shaida shima ya huta da zirya da neman irinta da ake faman zuwan masa.

Yana fara gayama bibi komai sai ga mohmoud shima ya shigo,duk da lokacin shigowarsa baiyi ba,hannunsa biyu dauke da.ledoji niqi niqi yana fadin

"Bibi yau nayi babban samu,nace bazan iya jira lokacin tashi yayi ba banzo na shaida miki addu'arki ta daren jiya ta karbu ba,bibi yau kaji kawai zamuci a gidannan" yanayin da ya gansu ya sassauta karsashinsa,sai bibi ta nuna masa gefanta

"Zauna nan" ba musu ya aje ledojin ya kuma zauna din,aba kuma ya dora da bayaninsa.

Bai boye musu komai ba,komai ya bayyana musu,falon yayi shuru kowa yana juya abun cikin ransa. Tsahon wasu mintuna sannan bibi tace

"Kai yanzun kana ganin hamdiyya kininka ce?" Ta jefa masa tambayar kai tsaye wadda ya kasa amsa mata

"Banason na sake jin wannan zancan,hamdiyya ba tsararka bace,koda ka dage kan zaka aureta ba lallai ka samu abinda kakeso daga matarka ba,cikin abinda akeson miji yafi matarsa akwai dukiya wadda kusan ita ke riqe da auren,kai kuma baka da ita,uwa uba ma yanzun haka dan uwanka ake maganar ya samu ya fara auren,kada na sake jin wannan batun"

"In sha Allah" ya amsa mata cikin matuqar girmamawa,har ransa kuma yakejin ya gamsu da hakan zai kuma yi qoqarin bi iyakacin qarfinsa.



*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 06



Shi da hamdiyya dukka sun dauki abun da wasa,bayan ya shaida mata zai haqura din saboda rashin goyon bayan mahaifiyarsa da bai samu ba,ita dinma zuciyarta tadan tabu,kuka ta amince zata dafa masa baya akan hakan,amma sai su duka zukatansu suja gaza jurewar. Qarewa suka dinga yi suna rama shi da ita harda qananun lalure lalure,at last dai abban hamdiyya ya sake shiha maganar,yayi tattaki da kansa ya iske bibi har gida,ya kuma bata tabbacin amincewarsa shi da hamdiyya din,sannan kuma ya qara mata da albishir din cewa baya buqatar komai daga hannun hamidou illa sadaki. Abban hamdiyya ya barsu da tarin kyautatawa da alkhairinsa wanda baya boyuwa daga cikin kyawawan halayen da yake dasu.



Please Login or Register in order to submit comment