Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dosa ba......baisan me gobensa ke tanadar masa ba,kuma har yanzu baisan da fuskar da zai kalli ama ba,ta bibi me sauqi ciki cikin sauqi ma......amma aba fa?. Yafi kowa sanin waye din aba,ya sanshi tamkar yunwar cikinsa,shekara biyar ba wasa bace.....ya sani aba bazai taba aminta da cewa ba GUDUN K'ADDARA yayi ba.....bazai taba yarda cewa SHIKE BIBIYAR QADDARAR BA.....cikin kowacce dama daya samu.....daidai da second daya bai taba daga qafa ba saidai idan DAMAR ta kubce masa.

Yadda ta tashi da zazzabi me zafi haka ya tashi da mugun ciwon kai,saidai ko sau daya bai matsa daga bakin tafekeken window din dake dakin ba me kamanceceniya da qofa,idanunsa dukka cikin sashen harami,shine abu guda daya dake sanya masa nutsuwa da kuma juriya.

Kiran sallar azahar daga masallacin haram shine abinda ya tasheta. Ta bude idanunta a hankali tana qarewa dakin kallo. Ta tabbatar cikin dakinsu take na hotel din,abinda ya bayyana mata inda ta ganta a yanzun mafarki tayi.

Shareren fili ne dake dauke da wani irin farin yashi iya ganinka,ba kowa cikin filin daga ita sai maina din. Wasu fararen kaya ne a jikinsa farare qal matuqa da sukayi kusanci da yashin dake shimfide qasan qafafunsu. Sutura ce irin ta asalin buzaye,ya kuma qawata shigar tasa da nadi irin na asalin ba'abzine,nadin farin rawani shima tas dashi wanda ya sake qarawa fuskarsa wani madaukakin kyau da kwarjini. Tsakaninsu duka duka taku ne baifi biyar ba,ita dinma kuma cikin shigen shigarsa take na fararen kaya,kanta babu dankwali sai iska dake wasa da gashinta daga hagu zuwa dama. Suna tsaye carko carko,kallon kallo sukema juna su duka,a duk sanda maina yadan motsa sai ta matsa baya,sunyi hakan ya kusa sau goma,daga qarshe ta jita caraf a hannunsa,kafin kuma tayi kowanne yunquri ya lullubeta da faffadan qirjinsa. Mutsu mutsun qwatar kanta ta dinga yi amma hakan ya gagara,yanason rada mata wani abu a kunne ne amma taqi bashi dama,daga qarshe ta soma cizonsa tana yakushinsa amma tamkar ba jikinsa takema haka ba........sai muryar benazeer ta bayyana tana qwala mata kira,kiran nata da tayi shi ya sanyata farkawa daga baccin ya kuma yanke mata mafarkin.

Sai data tattara nutsuwarta sannan ta miqe a hankali,ta zauna sosai tana duban jikinta da kyau. Haka kawai ta dinga jin kamar qamshinsa ne cikin jikinta,wannan ya sanya kanta yaso sarawa,ta saka dukka hannuwan nata ta dafe kan nata bacin rai yana ratsa zuciyarta.

Ta tabbatar kuma jikinta yana bata masaukinsa yana a wahen,ko cikin hotel din ko kuma wajen hotel din,muddin kuwa haka ne ya zame mata dole tayi takatsantsan ta kuma kula da kyau harsu kammala kwanaki hudun da suka rage musu subar qasar. Ba zata taba bari wani yaji labarin wai ta ganshi ba,hakanan zatayi duk me yiwuwa ta tabbatar baiga yaranta ba. Wannan tunanin ma ya sanya ta janyo wayarta ta kira number ama.

Bugu daya ta daga, muryarta adan dakushe tayi sallama

"Kin tashi kenan?,mun dan fita siyayya kina bacci,zazzabin ya sauka?" Boyayyar ajiyar zuciya ta ya sauke

"Ya sauka ama,batoul suna tare dake?" Tayi mata tambayar dake qasan ranta

"Eh muna tare....." Ta bata amsa matuqar mamakin tambayar sultanar tana kama ama,saboda abune da bata taba yinsa ba

"Akwai wani abu ne?" Ama ta kasa shuru ta tambayeta,da sauri ta girgiza kai kaman tana wajen

"Ba komai,kawai jiya sai da na fita nemosu ne ama,suna nisan kiwo sosai" mamaki ya sake kama ama,yau sultana ke magana haka akansu batoul kai tsaye?.

"Kinfi kowa sani muddin cikin haram ne ba abinda zai faru,just relax....." Aman ta fada murmushi yana subuce mata. Sautin murmushin ama din ya sanya kunya tadan kamata,saita wayance dayi musu adawo lafiya,ta maida wayar ta ajjiye gefanta tana sauke ajiyar zuciya.

Har yanzun kallon kallon da suka yima junansu a daren jiya ya kasa barin idanu da kwanyarta,hakanan kallonsa na cikin mafarkin me kama dana jiya. Qatuwar tsaki taja,wani irin tsanarsa yana ratsata,ba abinda fuskarsa ke tuna mata sai zallar azaba qunci da jarrabawar daya afka rayuwarta a ciki.

*_Masu karatu......marabanmu da isowa gaba😂😂😂.......wasan zaya fara,sai nace Allah ya hadamu ranar litinin muji_*

*Waye zaiyi nasara?"

*Waye zaiyi giving up?*

*Ta yaya maina zai fuskanci mutum hudu zuwa biyar?*

*Ama*
*Aba*
*Bibi*
*Benazeer batoul*

*Me gayya me aiki SULTANA?*

_ASHA HUTUN QARSHEN MAKO LAFIYA_


*HUGUMANKU CE*🥰*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 47



A nutse ya rufe mas hafin qur'anin dake hannunsa,yayi addu'o'i na wasu sakanni sannan ya maidashi ya ajiye. Wayarsa ya jawo ya bude,makeken hoton benazeer da batoul dake saman screen din wayarsa ya bayyana. Sunyi matuqar kyau cikin wasu pink gown,komai dake jikinsu pink ne,hatta ribbon da aka musu adon ka dashi da qananun dan kunnayen azurfa masu pink din duwatsu ne.

Ajiyar zuciya ya sauke karo na babu adadi,fuskoki ukun wunin yau duka su suka hanashi kuzari ko wani karsashi. Fuskokin yaran da baisan meye hadinsa dasu ba yakejinsu da wani irin qauna me zurfi a zuciyarsa,da kuma fuskar sultana.

Yes,sultana ce,ba wani abu ba kuma wasu shekaru yanayi ko zamani da zai iya hanashi ganeta,halittar daya raina da hannunsa ya bata dukkan kulawa. Ko ina yaronsa?,da waye yake kama?,ya girmansa yanzu?,duk bai sani ba,yana kuma daya daga cikin burikansa a yanzun. Yayi zirga zirga yau din tsakanin haram zuwa cikin hotel tsakanin kowacce sallah amma baiga wani abu da yayi kamanceceniya da ita ba. Ciwon kan da yake fama dashi duka yau bai barshi zama a masallacin ba,dole idan ya idar da sallah yake dawowa daki ya kwanta,amma yanzun da ake shirye shiryen kiran sallar isha'i sai yaji yana da muradin sake fitan. Yanason sake ganin yaran,ko suma sun nemeshi oho?,ko a wanne hotel suka sauka?,duka bai sani ba.

Alwala ya sake duk da wancan bai baci ba,ya feshe jikinsa da turarensa ya sanya qaramar hular da bahaushe ke kira tashi ka fiya naci saman kansa sai gashi ya fita a balarabe sak,ya sanya takalmansa ya fito a dakin.

Yana takawa har zuwa cikin haramin zuciyarsa na masa saqe saqe iri iri,bakinsa da kuma zuciyar tasa duka ambaton Allah sukeyi. Zuwa yanzu yanajin kamar ya rufe ido ya bude ya ganshi a nijer,yana jin ya shirya facing duk wani challenge.....duk wani tuhuma da kuma kowanne hawa da sauka bore da kuma bijirewa daga gurin koma waye.

Cikin tsantsan sawa kai nutsuwa da kushu'i akayi sallan isha'i da shi,ya kammala dukka addu'o'insa,sai ya samu kansa da zama a hanyar da sukayi clashing da yaran jiya,saman wata concrete chair.

Yana lazumi a hankali iskar wajen kuma tana ratsashi, cikin ruhinsa kuma yana jin kewar yaran,sai ya dinga hango fuskokinsu a jiya,daga shi har cikin yaran a cikin nishadi suke,dukka moment da sukayi spending tare ya zame masa memorable.

"Uncle haidar....... uncle haidar" ya jiyo muryar dab da shi. Kaf qasar a yanzun yasan su daya ne zasu kirashi da wannan sunan,don su kadai ya gayamawa wannan suna,a ko ina da aliyyu maina yake amfani,idan yaso ya qara da MAYAK'I.

Idanuwansa ya bude yana waiwayawa,dukkansu suna sanye da jilbab daidai jikinsu da yayi matuqar haskasu ya kuma qara musu kwarjini. Daga benazeer me giggiwa har batoul miskila murmushi sukeyi masa,alamun dake nuna sunji dadin ganinsa qwarai da gaske.

"U are highly welcome my BB" kafin ya gama kaiwa qarshen zancan ma benazeer ta zagayo tana neman gurin zama kusa dashi

"Dama na cewa batoul zamu iya ganinka fa,tunda aunty bata kiramu ba mu duba ko zamu ganka kafin lokacin komawa gida yayi" murmushi ya saki yana juyawa wajen batoul,yayi mata alama da hannu kan ta taho. Bata musa din ba ta zauna a daya gefan nasa,ya basu hannu sukayi musabaha dukkansu yana gaidasu da larabci. Ga mamakinsa sai yaji sun responding masa,yadan zaro idanu

"Wanne yare da wanne kukeji?" Dariya benazeer ta bushe dashi tana kallonsa,saita nuna masa yatsa hudu

"Ehnn......wanne da wanne?" Ya tambayeta irin amazingly dinnan yana fidda murmushi

"Hausa,english,arabic....... France small small" dariya sosai ta bashi da yadda ta fadi small small din tana daga qaramin yatsanta.

Kai ya jinjina sosai suna sake burgeshi,da alama sun samu background me kyau ta kowanne fanni na rayuwa

"Za'a yimin magana da kowanne?" Kai suka gyada kusan lokaci guda,sai ya saki murmushi yana gyara zamansa sosai a gaskiyarsu,yana jin zuciyarshi da ruhinsa yana masa wani irin dadi,yana jinsa tamkar a tsakiyar ahalinsa

"Bari na gayawa kowa abinda zaice" yana rufe baki benazeer ta maida masa da arabic,sannan ta sakeyi da sauri ta maida da France,sannan ta sake maida masa da english

"Daman da hausan ka fada" ta qarashe zancan da fadin hakan. Dariya ne ya kamashi,fararen haqoransa dake a jere ras suna sheqi suka bayyana.

"Na yarda....yanzun muje na bada gift na wannan abun" ya furta yana miqewa. Duk sai yaga basu motsa ba,ya waiwaya yana dubansu

"Oya...... muje"

"Aunty zatayi fada uncle" batoul ta fada tana maqale kafada. Dawowa yayi ya zauna ya dafa kansu

"Idan zatayi fada kuce uncle ne ya baku sabeel.....kun gane?"

"Idan mukace haka ba zatayi fada ba?" Kai ya gyada yana murmushi,duk sai suka sauka da karsashinsu suka bisa.

Kaman jiya ya musu siyayya,saidai yau din ya siya musu dai dai daidai yadda zasu iya cinyewa ma a gurin,gudun kada ya sanyawa iyayensu rashin nutsuwa a zuciyarsu da kuma ayar tambaya. Tsakiyarsun ya zauna sunata ciye ciyensu suna qananun fadansu da ba'a raba sako da sako,wani lokaci kuma su sakashi a ciki ya raba ko su jefashi a hirar su har suka gama.

Sanda ya niyyaci rakasu suka fidda idanu,suna tsoron ya hadu da sultana,don ko jiyan susan banda sun iso da wuri data fito nemansun nan saita gansu,sun tabbatar kuma zasusha fada qila harda punishment

"Uncle zamu iya zuwa da kanmu" idanunsa ya lumshe yana gyada kansa

"Goodnight"

"Goodnight uncle" suka maida masa,zukatansu dukkansu cike da shauqi,kowanne a cikinsu yana jin kamar kada ya rabu da dan uwansa.

Sai daya qara wasu awanni a wajen,ya sake addu'a sosai yana neman ubangiji ya shiga lamarinsa. Sai kusan sanda dare ya raba sannan ya wuce masaukinsa.

A dakin kusan abun jiya ya hanashi bacci. Fuskar sultana da a yau yayi mararin su sake ganin juna,da kuma yaran. Baisan wacce jarrabawa ce take bibiyarsa akan yaran ba,amma yana jin wata irin tsaftatacciya kuma tatacciyar qaunarsu cikin zuciya da ruhinsa.

*******Dukka kwanakin da suka rage musu cikin makka din a darare take,kowanne motsi sai take ganin kamar zata ganshi a masaukinsu kowanne fita da yaran zasuyi sai taji kaman zasu hadu,kaman zai kwashe yaran a nemesu a rasa,kowanne fita tata cikin kaffa kaffa takeyi da lura da duk inda zata gifta din. Tun daga rabar bata sake bin elevator ba ta gwammace tayita bin stairs har takai qasa,wanda idan ta fita din sai tayi zamanta cikin masallaci,idan ta dawo ciki kuma ta dawo din kenan sai kuma washegari. Duk sanda tayi hanyar elevator sai taga kamar zasu sake haduwa,kaman zata sake ganinsa irin yadda ta ganshi rannan.

Kwana hudu kacal da suka rage subar makka su wuce nijer sukayi wani irin sabo dashi,hakanan shima yayi wani sabo dasu ta yadda har bai tuna haduwa sukayi kuma kowanne lokaci shi ko kuma su wani zai iya tafiya yabar wani. A jikinsa yake jin kamar gurin zamansu daya,kamar wani family ne shi dasu dake rayuwa cikin gida daya,kamar a nan zasu dawwama da yaran. A kullum bayan sallar isha'i sai ya zauna ya jirayesu. Duk irin yadda yake girmama lokaci......duk irin yadda ya tsani jira cikin rayuwarsa,duk kamewa irin tasa da rashin shiga sharafin kowa.......duk uban miskilanci da tsananin ginshira irin nashi amma bayan sallar isha'i saiya bata wananna awa daya zuwa biyun. Ko yana zama su iso,ko yazo ya samesu zaune a wajen suma suna jiransa. Ice cream da chocolate sun sha har babu iyaka,masu tsada ya koma siya musu irin wanda canjin da ama ke sanya musu cikin jaka bazai isa su siya ba,babu kuma me biyewa ciye ciyensu a cikinsu bare ya bisu ya siya musu da nasa kudin,don dukkansu sunsan girman wajen,zaman masallacin yafi komai cinye lokacinsu a wuni guda.

Tunda benazeer ta fahimci a ranar zuwa azahar jirginsu zai bar makka hankalinta ya soma dagawa,tasan dai ba zasu kai lokacin da suka saba haduwa da uncle ba bare suyi sallama,ta kuma gaya masa zasu tafin. Gaba daya sai ta kasa sukuni,tana cikin kujera a kwance tana ta kallon batoul dake cin chips da fork,tana ta son ta kalleta suyi shawarar yadda zasu ga uncle su gaya masa zasu tafi,shima yaushe zai tafi?,yaushe kuma zasu sake ganinsa?.

Yawan surutu kuzari da karsashin batoul ya sanya kusan kowa ma ya fahimci tana da damuwa. Tuni sultana ta fahimta,amma saboda kawaici da batason fiya zaqewa cikin lamuran yaran bayan ga qashin bayansu nan jigonsu a gurin saita kauda kai,saidai kuma tanata monitoring komai nata,ta kuma karanci tsaf akwai abinda yake damunta ya kuma hana mata sukuni.

Qaramar akwatinsu da ama ta shirya musu tsaraba a ciki tazo ta ajjiye,saita juya kadan tana kallon benazeer

"B....me yake damunki yau?" Tayi tambayar cikin salon nuna muhimmancin tambayar saman fuskarta. Zamewa tayi ya sakeyin lamo cikin kujera,sannan ta motsa qaramin bakinta

"Ba komai"

" Da gaske?" Kai ta gyada a hankali

"Ko kuma kayan shaye shayen sanyin nasu takeso ba,tunda na fahimci duk sun zama shazumamu,sunma fi uwarsu son shan jarabbaben zaqin nan ai" Dariya ama ta danyi,ta jawo purse dinta data shigo da ita ta fidda riyals tana cewa

"Su kenan suka ragemin dama......aje a siyo na bankwana" ta furta tana murmushi. Idanu sultana ta dauke gefe zuciyarta na motsawa,zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba ganin soyayya tsakanin kaka da jikokinta ba irin ta ama da su batoul. Haqiqa bibi ta sota,ta qaunaceta,ta kuma nuna mata soyayya me yawan gaske.....amma akwai wasu kusakurai da ramuka masu yawa a hanyar,wadanda tasan ta tsallakesu ne kawai saboda qilan taci albarkaci ko darajar wani ne.


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*

*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 48


Da sauri benazeer ta miqawa ama qaramin hijabinta ama din ta sanya mata, batoul ma ta ajjiye abincin tana sanya lausasan wasu rufaffun takalma masu kyau suka sanya kai suna ficewa riqe da hannun juna,ama ta bisu da

"Ayi addu'a"

"In sha Allah" suka hada baki wajen fada.

Sai da benazeer ta tabbatar sun sauka sannan ta kalli batoul

"Nifa uncle zan nemo na gaya masa mun tafi fa" ido batoul ta zaro tana kallonta

"A ina zaki ganshi?"

"A inda muke zama,muje mu siya ice cream sai mu dawo mu wuce ta wajen ko zamu ganshi" dan jim tayi kaman me nazari,sai kuma tayi murmushi

"Muje to".

Shop din da ya saba kaisu suka shiga,suka zabi kowa flavor din da yakeso,har ma'aikatan wajen suna tsokanarsu

"Yau babu fada?,ina uncle din nasu?" Dariya sukayi, benazeer tace

"Baizo ba?,nemansa muke" daya balaraben yace

" Tare kuke zuwa, sai dare yake zuwa tare daku" basu wani fahimta ba,sundai gane kawai baizo ba don haka suka sanya kansu suka fice benazeer na cewa

"Ma'assalama". Suna riqe da ice cream din suna sha suna kuma bin duk hanyar da suke ganin zasu iya ganin uncle haidar amma babu shi babu dalilinshi,har batoul ta gaji,taja tunga sanda aka soma kiran sallar azahar

"Kizo mu tafi gida tunda bamu ganshi ba,kada aunty tayi mana fada,ama ma kuma tace fa mu dawo da wuri" juya idanuwa benazeer tayi kaman me shirin sakin kuka,ta sake waiwayawa bayanta kamar me fatan ta bude idanunta ta ganshi a wajen,saita dawo da kallonta ga batoul wadda itama dinma duk ranta ba dadi

"Muje" ta fadi a sanyaye. Haka suka jera suna komawa hotel din ba um ba um um. Sanda suka isa dakin duk sun fice zuwa sallar azahar,amma kuma kayansun sun gama hadasu tsaf,kowacce saita samu waje tayi lamo ba wani me magana ko kuzari a cikinsu.

Koda suna shirin fita a dakunan saida ama tayi qorafi

"Anya lafiya kuke kuwa.yau dinnan?" Ta fadi tana taba wuyansu,sanyi taji ba alamun zazzabi ba komai,batoul ce tace mata ba komai

"To Allah yasa alkhairi" aman ta furta,saboda tsahon tarenta da yaran bata taba ganin jikinsu ya mutu haka ba.

Nannauyan numfashi ta sauke tana furzar da iska daga bakinta. Cikin ruhinta takejin wani salama da nutsuwa suna saukar mata,zuciyarta kuma tana gaya mata tayi masa nesa ta tsere masa. Ta window din take kallon fadin sararin airport din,tana jin kewar barin qasar kamar yadda ta saba,amma tana jin farinciki idan ta tuna ta tserema idanun maina,sannan nan gaba kadan zata dawo ta sake ziyartar dakin Allah.

Tafiya miqaqqiya daga birnin makka har zuwa qasar nijer. Tafiyan awanni goma sha daya suka sauka a niamy,daga nan wani jirgin suka sake hawa suka wuce marad'i.

Iska ta shaqa sosai ta qasar nijer sanda tayi relax cikin daya daga cikin lafiyayyun motocin mallakin aba da ama. Wasu emotions suna cakuduwa cikin zuciyarta,qamshin qasartata yana motsata tare da tuna mata abubuwa masu yawa,wanda kusan fiye da rabinsu quruciyarta ne......yarinta da zallar wauta da ta tafka a rayuwarta,wani abun ya sanyata murmushi wani ya bata takaicin da shima din dai murmushi ne na dole ke qwace mata.

Tun barinta nijer zuwanta daya kacal......wannan shine zuwa na biyu da tayi,zuwan daya banbanta da zuwanta na farko. A yanzun ta sake dawowa qasarta a matsayin cikakkiyar sultana,me yara har guda biyu,wadda ta mallakin hankalin kanta......sannan masaniya cikakken sani a harkar ilimin jarida. Sultanar da a yanzun kai tsaye zaka iya kiranta da madam. Dukkan wata sura da halitta nata na kyawu ya gama cika,ya kuma cakuda da zallar kwarjini da hasken ilimi. Ta zama classy qwarai,ta banbanta da girman tazara da wancan sultanar me rawan kai yawan surutu fitsara da rashin kunya. Yanzun ta zama wata sultana me yawan shuru shuru,wadda ba shirgin kowa take shiga ba,abinda ya shafeta ma ba kowanne take daga idanu ta kalla ba har ta bashi lokutanta.

Isowarsu qofar makeken gate din mansion house din mallakin MAYAK'I ya sanyata daga tsintsiyar hannunta tana gyara zaman siririn agogon gold din dake hannunta,lokaci ta duba murmushi ya subuce mata sanda hancin motarsu ke shiga harabar gidan. Ba wani abu ta tuna ba illa lokaci irin wannan da take hada dabar hira,sam qawaye mata a sannan ba damuwarta bane,maza ma sunfi mata dadin qawance qwarai,saboda su din zata musu tsiwa tayi musu fitsara kuma su daga mata qafa don suna kallon ita macace kamar sauran mata. Idanunta cikin farfajiyar gidan da ta sake qawatuwa qwarai,anyi mata gyara sosai,da alama kuma dukkan gyaran yana da nasaba da bikinsu aminata ne. Ko ina yayi fes,tamkar sabon gini,tamkar ba wannan tsohon ginin da qarfi d kuma qoqarin NADEEYA ya samar dashi shekarun baya ba. Ko kusa ko alama mamallakan gidan basu taba barin tsufa ko shekaru su cimmasa,saboda kusan koda yaushe cikin aikin gyaransa suke,duk wanda ya samu dama a cikin kawunnan nata saidai kawai mutanen gidan suji ana shelar a kwashe ko za'a yi aiki.

Idanunta ta janye sanda suka sauka a wannan bigiren....muhalli ne da kusan yafi zama a cikinsa akan ko ina cikin gidan,waje ne da yake zama yana kula da shige ficensu yana kuma monitoring motsinsu da tarbiyyarsu. A duk sanda zata kalli wajen koda sau dubu ne sai taji ranta ya baci sau dubun,shi ya sanya zabinta daya kauda kai a irin wannan lokacin.

Motarsu na tsaiwa kusan duk wanda ke wajen ya ankara da isowarsu. Kafin kace meye wannan mutanen dake cikin gida ma sun fara fitowa tarbarsu. Kusan kowa ya fito ta batoul da benazeer yake. Batoul sarkin rashin yarda da shegen miskilanci da taga ama ta kutsa kai cikin jama'a sai ta koma jikin sultana ta lafe. Abun sai ya soma baiwa sultana kunya,saboda idanuwa data ja mata,kowa sai ya matso ya tsokaneta ya kuma tsokani sultanar,wadda a sannan idan kaga batoul dake jikinta zatayi rantsuwa yayarsu ce bawai uwa mahaifiya ba. Ko kusa ko alama duk qwaqwafinka baka isa kaga alamun sultana ta isa ta mallaki tiqa tiqan yara har guda biyu kamar benazeer da batoul ba.

Wata motar ce ta shigo,najma aminata da yasmine ne a ciki amare. Najma ke driving aminata da yasmine da houda cousin dinsu suna baya,a kujerar gaba kuma djamilla ce itama dukka kakanni daya suke dasu sultana.

A gaggauce najma ta tsaida motar,dukkansu cike da farinciki suke qoqarin fitowa,saidai ta rigasu ma qarasowa,fuskarta dauke da nutsatsen murmushin nan nata,da muryartannan me sanyi tace

"An fara yawon amarcinne?,amma ko a jirani?" Junansu suka kalla da dan mamaki,ba wanda ya kawo zata nema sakewa a cikinsu shi yasa wasu abubuwan ma basu tsara da sunanta ba

"Zaki iya yawo a cikinmu?" Houda ta fadi tana 'yar qaramar dariya. Waiwayowa tayi tana dunan houda da murmushin da ya tsaya saman kumatunta tace

"pourquoi pas?(me zai hana?)" Ta fadi tana kallon houda

"Yar jarida ce ke yanzun a qasar France...... kinga dole muyi takatsantsan karmu shiga ajin da ba namu ba" dole ta sanya sultana sakin siririyar dariya,siraran jerarrun haqoranta suna bayyana

"Banason sharri houda.....har yanzun baki sauya

Please Login or Register in order to submit comment