Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suyi hirar masu aikin gidajen nasu,zuwansu makarantar ya sanya suka qara ganin kima da matsayinsu da kuma girman hidimar da suke musu.

Hannu kawai sultana ta sanya ta dafe goshinta,itama tanja ce ta fara fado mata,sau daya kuma koda wasa bata taba daga tsintsiya da sunan share dakinta ba,hatta suturarta idan ta cire tanja ke killace mata,me taci?,me zataci,dukka suna wuyan tanja,hatta panties nata washing machine ke hidimat wanke mata su,yau gata cikin rayuwar yiwa kai komai,ba kuma cikakken 'yancin lokaci,sai iya abinda aka qayyade maka.

"Ya Allah" karon farko ta furta sunan ubangiji da a lokacin zuciyarta ke ayyana mata shine zai dafa mata,ta waiwaya ta sake kallon gadon tana mamakin yadda fateeman ta gyarashi tsaf,ita dinma kamarta kenan take ada?,dole ta sanyata koya?,ta yaya ta kuma ina ita zata fara nata koyon?.

A masallacin sukayi magariba,suka sake komawa kitchen sukaci abincin dare,sukayi isha'i sukayi tilawar litattafan addini sannan suka wuce makwanci.

Kamar jiya din,yauma da farko juyi ta dinga yi,gaba daya yininta na yau take nanatawa cikin ranta. Wata irin rayuwa data banbanta da rayuwarta,ta banbanta da rayuwar data saba yi,yau gata tsundum cikin makaranta, makarantar da babu abinda ta tsana sama da ita,yau sai gashi ba jeka ka dawo bama makarantar kwana ce. A Hankali tunaninta ya gangaro kan yadda rayuwar karatunsu take. Kowa kusan gwanine za'a ce cikin daliban,tana hangen yadda kowa ke zagewa ya kuma dage don ganin ya kai maqurar iya karatunsa,ta tuna yadda a kowanne darasi ta dinga baza idanu,nan da wani lokaci idan batayi da gaske ba zata zama cikin sahun dalibai na kashin baya,wadanda kowa zai fahimci qarancin ganewarsu. Wannan tunanin ya sanyata hantsilowa daga gadonta,wani abu yana dasa mata qaimi cikin zuciyarta,tana jin ba zata lamunci faduwa ko rashin iyawa ba. Ta saka hannu gefan gadonta inda qaramar locker dinta take ta fidda jakar makarantarta,ta zazzage dukka litattafan da a yau sukayisu,ta soma budesu daya bayan daya tana dubawa.

Da qur'ani ta fara,ta dinga hada baqin yana guduwa,ta dinga qoqarin maimaita shafukan daidai,a haka ta kashe awa daya kusan da rabi kafin taji ta fara kama hanyar karatunta bisa qa'ida. Bata sare ba bata kuma gaji ba,tayita nacin maimaitawa har sai da taji ya zauna mata a harshenta,ta tabbatar zuwa gobe koda za'a ci gyaranta kadanne. Kowanne subject sai da tayi maimaicinsa,tun bata fahimtar abinda take ta faman karantawar har sai da taji kamar qwaqwalwarta tana budewa ne a hankali. Sanda ta duba agogo awa uku kacal ya rage lokacin tashinsu dsga bacci yayi. Sai ta zauna tsakiyar gadon tana son tuna addu'a daya daga cikin tarin addu'o'in da taji suna yi,yayin tashi a bacci,kwanciya bacci,cin abinci,shiga bandaki,shiga aji da komai ma na rayuwar daliban makarantar. Ba wani abu guda da taga wani dalibi yayi bs tare da yayi addu'a ba,tamkar ma ta shiga jinin jikinsu ne sun kuma saba. Duk sallolin da akayi yau din cikin jam'i abinda bata taba yi ba tsahon rayuwarta......duk sanda aka idar suka hada baki duk yawansu suna addu'o'in da akeyi bayan idar da sallah,sai taji wani sanyi dadi da nutsuwa suna shigarta,sai taji wani sukuni yana ratsata,har sai taji kamar ma kada lokaci ya cika, kamar kada su daina addu'ar.

Waiwayawa tayi ta dubi su fatima dake bacci abinsu. Cikin ranta ta ajema kanta zasu zame mata mudubi in sha Allah cikin rayuwar makarantar,zata kuma yi qoqari tayi catching up na dukkan abinda suka tsere mata.

Abunda ya bawa su fatima mamaki a yau ita ta tashesu maimakon jiya da sune suka tasheta,kafin kace meye ta kammala komai da sukeyi kafin fita masallaci sallar asuba. A bakin hostel din suka cimmata tsaye da metron asabe tana gaidata

"Ina fatan baki da wata matsala ko?,idan kun kammala karatu kina da sha'awar wanka kafin ki wuce aji kiyimin magana saiki shiga kiyi"

"Ba komai,zan jira har lokacin da kowa yakeyi,idan ban samu toilet ba zan miki magana sai nayi s gurarenku din" ta amsa mata tana rungume da qur'aninta cikin wata murya me sanyi. Da kallo metron asabe ta bita,bata taba zaton zata sameta da sauqin kai har haka ba,bata taba kawowa cewa zatayi saurin daukan shawararta ba,sai gashi daga jiya zuwa yau kacal tana qoqarin kiyaye dokar makarantar.

Yadda ta dinga nacin bibiyar kowanne harafi da ake qara musu ya sauqaqa mata qwarai. Kafin akai ga tashi sai gashi ta iya karatun fes kamar kowa. Dadi sosai ta dinga ji cikin ranta,har kuma hakan ya nuna a fuskarta,duk da ba murmushi takeyi ba amma fuskarta a washe take sarai.

Gurin sharar compound na hostel dinsu kuwa kamar kowa ta karbi tsintsiya. Metron asabe na cewa ta bari amma tace zata iya. Tana sharar tana mamakin meye dalilin metron asabe nason dauke mata wasu wahalhalu na makarantar ne?,me yasa take kawo mata hanyoyi sauqi da sauqaqawa?,ahalinta ne fa da hannunsu suka danqata a makarantar,komai na ama bisa manufa da tsari yake,ta tabbatar ba a banza ama ta aikata hakan ba,ba shakka akwai dalili,kuma akwai hujja.

Koma meye ita dai ta barma ranta zata rayu kamar kowa,tayi alwashin zatayi irin rayuwar data samu cikin makarantar,zata rungumi kalar sabuwar K'ADDARAR da ta risketa. Can kuma qasan ranta takejin kamar dai ama ta kawota ne don tasan rayuwa?,kamar dai ama ta kawota ne don ta fahimci bayan duniyar da take rayuwa a ciki akwai wata duniyar ta daban?,kamar dai ta kawota ne saboda wasu abubuwa masu yawan da ita kanta bata gama fahimtarsu ba.

Tana ankare da yadda labour prefect huda keta wani fusge fusge da sanya mutane aiki cikin izza da gadara. Duk wanda ta kira ita da team dinta da sassarfa yake isowa ya kuma zube yana kiran

"Aunty gani" ladabi ne wannan na makarantar da dole kowanne dalibi ya koya ya kuma ginu akai,amma batajin zata iya zube musu har haka,hasalima batajin tana da LOKACIN shiga sharafinsu.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 34


Lokacin data sake kame kanta tare da takatsantsan da lamarin huda da sauran maqarrabanta ita kanta sai tayi mamakin kanta,har batasan sanda qaramin murmushi ya subuce mata ba abinda ta jima bata yishi ba,wai yau ita sultana ita ke kaucewa rigima da wasu,ita sultana da batajin tsoron rigima da ko waye,mace ko namiji,yaro ko babba,bata tsoron tunkararka ko qaddamar maka,lallai giwa tayi lafiya ta fadi qasan zuciyarta tana shafar gefan fuskarta,to ko hankali ta soma yi?,ta yiwa kanta tambayar data sanyata sakin wani murmushin.

*****A hankali A hankali cikin wani irin yanayi sauyi na bazata ke ruskar rayuwarta. Ingatacce kuma gamsashen sauyin da yayi nasarar taba ainihin ruhi da zuciyarta. Cikin ba zatar da ita kanta bata sani ba ta tashi daga SULTANAn bibi,sultanan aba sultana ta nijer zuwa sultanan Nijeria,sultanan hassan Ibrahim gwarzo,sultanan fateema Ahmad da kuma ameena aleeyu. Ba wanda take bari ya huta tsakanin fateema Ahmad da ameena,kowannensu ta samu ta riqeshi to tabbas sai yayi mata qarin dukkan wani kwantan karatu da aka tsere mata,tashin cikin dare ya fara bin jikinta,a lokacin da kowa ya sanya haqarqarinsa yake bacci.....a lokacin take tashi bita da tilawar katatuttukanta. Cikin kowanne mataki na karatunta batajin akwai ya kamar ALQUR'ANI. Tana jinta wani fresh a sanda take karantasa,tana jin wani softness cikin zuciyarta,tana jin kuma nutsuwa tana shigarta,shi ya sanya cikin lokaci qanqani ta kamosu ta kuma hade da izifin baya da suka wurwuceta,abinda ya baiwa kowa mamaki,sauri da kaifin basirarta,duk da a farko sun mata kallon hadarin kaji,kallon dalibar da bazata wani basu matsala ba. Tana da rivals da yawa a ajin,matan da sukaci buri suke ganin sune na gaba gaba wajen samun yarda da amincin malamansu,sai gashi cikin dare daya wata baquwar haure na shirin yi musu shalll. Wata irin murya Allah ya mallaka mata me dadi,sai take sake qawatuwa da sautin karatun qur'ani da wani irin daddadan sauti.

Bata da lokacin kowa,ba wanda take bi ta kansa,bata kuma hulda da kowa idan ka debe fateema da ameena. Muddin kaga hirarta sosai to da sune,idan kaga motsawa kumatu da labbanta to da ameena dinne,sun dinke sun zama kaman wasu 'yan uwa, dabi'a da yanayin sultana din su ke burgesu,suna mata kallon wadda gayu gata da shagwaba suka yiwa yawa shi yasa komai nata ya fita na dabanne.

Kowanne kwanan duniya sai metron asabe ta tambayeta ko tana da wani buqatar?,amsarta daya ce A'ah,a nata tunanin tanason gwadawa ama zata iya rayuwar data zabar mata,zata kuma wanzuwa a kowanne bigire ko muhalli da rayuwa ta gangarata cikinsa.


*_VISITING DAY_*


Tun daren jiya daukacin daliban makarantar ke cikin farinciki da walwalar ganin ahalinsu a goben,kamar yadda fateema da ameena aleeyu suka bi sahun sauran dalibai.

Safiyar yau din kowa shiryawa yakeyi don 'yan gidansu su ganshi fes..... sultana na zaune kusan sai da kowa yayi nisa wajen nashi shirin,wasuma suka soma fita sannan ta shiga tayi nata wankan da yau ta zabi tayi cikin tsaftatattun toilets dinsu ba nasu metron asabe yadda ta saba yi ba.

Komai nata cikin wani sanyi da nutsuwa ya koma,babu sultanan nan ta anihi,haka ta tsaya gaban gadonta ta shirya kanta cikin house wear kaman kowa,bayan ta daure jelar manyan kitson da fateema da ameena sukayi taron dangi sukayi mata,saboda sulbinsa da tsahonsa ya sanya ba kasafai take kitso ba,koda anyim ma baya dogon zango yake warwarewa.

Tayi kyau sosai,don sabbin house wear ta sanka,dinkin kuma ya zauna sosai ya qara fidda tsaho data qara,saidai kuma tadan fada kadan wanda hakan baya rasa nasaba da sabuwar rayuwar da take qoqarin daidaita kanta taga ta hauta bisa tsari.

"Sultana mohmoud mayak'i" aka maimaita kiran sunanta har sau uku. Waiwayawa tayi tana duban me kiran nata,senior dinta ce cikin wadanda zasu fita makarantar a shekarar da ake ciki

"Kina da baqo" ta fadima sultana din tana juyawa. Turarenta ta miqa hannu da sauri ta dauka ta fesa ta maidashi,sannan ta zura house shoe dinta ta soma tattakawa cikin wani irin zumudi tana ratsa hostel din nasu

"Tacan zaki zagaya" dalibar ta fadi tana mata nuni da hannu sannan ta wuce gararin gabanta.

Sosai take takawa da zumudinta shiyyar da ta nuna matan,qasan ranta cike fal da dokin ganin ama da aba,tasan kuma zaiyi wuya ace bibi batazo mata ba,BATOUL da BENAZEER......taji an kira mata sunan yaran daga can qasan zuciyarta,ta lumshe idanunta murmushi na subuce mata,wata irin mahaukaciyar kewar yaran ta taso ta lullubeta,karon farko daga can qasan ranta taji wani irin tausayinsu ya saukar mata.

Tsaiwa tayi cak ganin tana ta cusa kai area din da babu motsin kowa babu kai kawon kowa. Ta tayi ta tsaya cak,wai mema dalibar tace mata ne

"Kinyi baqo" ta tuna da abinda tace

"Baqo......baqi...." Sai taji kwanyarta ta rikice. To ko aba ne shi daya ya samu zuwa?,idan hakane ai ba za'a barshi ya qaraso har gate na biyu na sashen mata ba,akwai askar da basa bari maza su wuce gurin,kuma bata nan ya kamata ya tsaya ganin nata ba.

Wani mummunar bugawa zuciyarta tayi. Cikin jini tsoka da jikinta taji kamar ana fusgar hankali da kuma numfashinta sakamakon shaqar wannan qamshin.......wannan qamshin dai da hanci zuw qwaqwalwa ba zasu iya gaza fayyaceshi ba,wannan qamshin dai da yake da taushi dadi da laushi......amma a nata hancin kama yakeyi mata da qamshin MUTUWA.....Tabbas inda mutuwa tana da wani qamshi na daban......wannan qamshin shi ya dace a baiwa wannan sunan.

Waige waige ta fara yi jikinta yanason fara rawa, hankalinta kuma nason yin qaura daga gangar jikinta

"Ki nutsu,ba kowa a wajen nan,ba shi daya aka qerowa turaren ba,bashi daya kaf duniya yake siyan turaren ba......ki nutsu kada ki ruda kanki sultana" zuciyarta ta fara rada mata cikin kunnuwanta yayin da qirjinta ke wani irin bugawa da tsananin qarfi har numfashinta yana rarrabewa.

"Sultana mohmoud mayak'i" ta sake ji an kirata,kiran sunan da ya hautsinata gaba daya ta waiwayo da wani irin sauri. Wata dalibar ce cikin daliban da suke ajin farko wato J.s one ke nufota. Hannunta riqe da wani babban abu da ya yima sultana zubi da kwali. Har ta iso gabanta sultana na dubanta qirjinta kuma bai fasa dagawa ba,sai ta miqa mata kwalin tana kallonta bayan ta rusunawa sultana din kamar yadda yake doka ne na makarantar dole na qasa ya rusunawa babba

"Wai gashi" bin kwalin dake hannun yarinyar tayi da kallo sannan ta maida dubanta ga fuskarta tana tattaro ragowar miyau din bakinta,da qyar ta tambayeta

"Wai inji wa?" Kai ta karkada yarinyar

"Ban sani ba,nima wata daliba ce ta bani tace itama wata ce ta bata tace a baki" fuska tadan motsa kadan,abun yadan daure mata kai,tayi kaman ba zata karba ba,to amma yadda yarinyar ke rusune sai taga bai kamata ta barta a haka ba

"Ya sunan wadda ko wanda ya bada?"

"Nima na tambaya tace bata sani ba,wancan din tace me bada saqon sunanki kawai ya kama yace a baki"

"Kodai aba ne yake sauri bazai iya tsaiwa ba ya bayar a kawo?" Wannan tunanin ya sanyata miqa hannu ta karba,yarinyar ta juya da sauri sauri tana barin gurin don kada azo mata ba'a sameta ba,sai itama sultana din ta soma takawa tana riqe da kwalin tana barin wajen zuwa nana aisha hostel,har a sannan hancinta yana jin qamshin nan data yiwa maqurar tsana*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 35


Tana tafe a hanya tana juya kwalin,ba qato bane hakanan ba qarami ba,yana da matsakaicin girma,amma kuma yana da dan nauyi. Kai tsaye ta koma hostel dinsu,sanda ta isa dakin da yawa an yoye,kowa ya fita waje,wasu gurin family dinsu,wasu kuma suna jiran tsammanin isowar 'yan uwan nasu.

Gefan gadonta ta zauna a nutse,ta aza kwalin saman cinyarta ta fara budeshi.

Sannu a hankali ta kammala yage takardar jiki tsaf,wani irin kwali ne na musamman tamkar qaramin akwati,sai daukan idanu yakeyi da wani irin santsi da tambarin dolce and Gabbana ko ina a manne a jiki.

Doki ya kamata,muddin wannan kyautar daga hannun aba take to ko shakka batayi tafiya yayi ya kuma tuna da ita

"Allah sarki ubana,maganin kukana" ta furta hawayen qaunar aba na cika mata idanu.

Cak ta tsaya tana duban kyaututtukan da aka shirya cikin box din. Tarin tsagwaron chocolates,dukka kalolin wasu chocolate da takesha babu wadda ba'a zuba ba a cikinta. Wani siririn agogo da take da tabbacin zaiyi wuya chain dinsa idan ba gold bane a jiki. Turaren da take amfani dashi sanda tana sultana dinta wanda a yanzun ma tuni ta sauya zuwa wani kalar daban. Biro da wasu qananun notebook masu masifar kyau da tsari,sai wata memo itama daban da zata baka damar tsara komai na rayuwarka da date da komai,sai wani greeting card da duka rubutun jiki layi qwaya daya ne tal

"Best wishes" kadai ke rubuce daga tsakiyansa.

Bin budadden box din kawai takeyi da kallo,cikin jikinta ta dinga jin wannan kyautar ba daga hannun aba ta fito ba,batama dace da ace daga aba din take ba,to anya ba batan suna sukayi ba?,tunda dai daliban makarantar ba suna da yawa qwarai,kuma bazaiyiwu kaf makarantar ace ita daya ce qwallin qwal me suna sultana mahmoud ba. Juya bayan katin tayi,a nan ta samu amsar tambayarta,cikakken sunanta harda na qasarta ne rattabe a bayan,hakan yana nufin me aiken yanason bata tabbacin saqonshi ne.

Wani abu me kama da bacin rai ya biyo bayan mamakinta,ta sake juya katin ko zataga alama koda ta sunan me saqonne amma babu,tsoro da shakka suka kamata,daidai sanda ameena aleeyu ta shigo da sassarfa

"To kizo ga duka 'yan gidanku nan gaba daya,har mun gaisa da aba ma,ama nada maqurar kirki,atta da almu suna yanayi dake" ameena din tace da sultana cikin nuna zallar zumudi.

Da sauri ta tashi hae box din dake saman cinyarta ya watse a wajen,sam batabi ta kansa ba tayi hanyar waje duk da tana jiyo ameena na fadin

"Kinyi barna,wannan agogon me tsada .......Allah yasa baki fasa glass dinshi ba".

Tana tafiya zuciyarta na nanata tambayarta daga ina wannan gift din ya fito?,indai har ga aba yazo to waye ko wace ta aiko da gift din?.

"May be dai still aba dinne" zuciyar dake neman nutsuwarta ta fada tana bata tabbaci.

Tun daga nesa data hangosu murmushi ya subucewa fuskarta,kasa jurewa tayi ta isa garesu a hankali sai ta dan saka da sassarfa,ta qarasa ga ama ya fada jikinta tana riqeta da kyau,bakinta har rawa yakeyi wajen fadin sunanta

"Ama.....sannu da zuwa ama"

"Wato ama dinki kawai kika gani ko?,ni baki ganni ba?" Muryar bibi ta doki kunnenta. Waiwayawa tayi da sauri tana duban bibin,sai ta saki ama ta nufeta itama ta fada jikinta tana qanqameta

"Ban lura da bibi na ba,bibi tun daga nijer kikazo ganina?" Ta fadi tana murmushi. Harara ta balla mata

"Kuma gashi an yanqwanani ko ganina ma ba'a yi ba?" Ta fadi tana yatsina baki,saidai kuma qasan zuciyarta na mata wani irin sanyi saboda sauyi muraran da take gani tattare da sultanarta. Baya taja tana duban bibin

"Ni ya kamata nayi fushi bibi,kina can kina qiba abunki aba yana baki kayan dadi,ina nan kin barni da abinci da horon boarding" ta dan taba tsokanarta wanda abune da kusan dukkaninsu kunnuwansu sun manta rabon da su jishi daga bakinta,sai suka sanya dariya,wanda muryar aba ta fito a ciki,sai a sannan ta ankara dashi shima,abinda ya sanya tadan yi qas da kanta ta kuma nufeshi da hanzari.

Zamewa tayi ta tsugunna a qasa tana gaidashi

"Barka da warhaka aba,ina kwana?" Ba wanda bai dubeta ba yadda take komai cikin nutsuwa da tsantsar girmamawa. Yana dan saki murmushi ya amsa mata

"Lafiya qalau sultana,tashi a qasa kada ki bata uniform dinki,ga abun zama can an shimfida mu qarasa" tanja ce ta riqe hannunta,saita waiwaya tana duban tanja din

"Kina Nigeria ko kina nijer tanja?" Ta tambayeta bayan ta gaida tanjan itama cikin rusunawa,abinda sultana din bata taba mata shi ba koda wasa,kai kwata kwata ma ba zatace ga sanda sultanar ta taba gaidata ba,ba zata iya tunawa ba.

"Inaaa......ina nan gurin iyayen dakina,in tafi nabar 'yan biyu?,ai bazan iya ba" ta amsa mata tana murmushi. Sai a sannan hankalinta yakai kai,bataga benazeer da batoul ba,idanu ta shiga warewa can qasan zuciyarta tana jin shauqin ganin yaran,amma ko me kama dasu bata gani ba. Duka sai taji zuciyarta ba dadi,ta dinga nacin kallon inda goumar yake amma bataga alamun suna tare ba,har goumar din ya lura da yawan kallon da takeyi,sai ya saki murmushi ya watsa mata hannuwansa,qasa qasa kuma yadda babu wanda zaiji yace da ita

"Me na satar miki ne kuma yau?,mutumin da ko kallon fuskarsa ba'a sonyi yau shi aketa kalla?,ki bude baki kawai ki cewa ama ina 'ya'yanki ko?" Harara ta watsa masa gabanta yana faduwa,salon maganarsa sak yaa maina,kusan wasu abubuwan nasu suna bala'in kamanceceniya da juna,kamannin fuska ne sam Allah bai sanya sunyo daya ba. Qaramin tsaki taja tana dauke kanta ta maida ga sashen su ama daketa bata labarin abubuwan da suke wakana bayan batanan,sai muryar goumar ta motsa cikin dariya

"Allah bibi wannan 'yar jikanyar taki ladabin qarya tayi muku,qanzo ne ya sanyata yin laushi,bata canza hali ba ashe rashin kunyar nan tana nan,yanzun nan ta gama min tsaki harda harara" ya qarasa fadi yana dariya sosai. Harara bibi ta watsa masa

"Qaniyarka sarkin sharri,ta ina ta hararekan dukkanmu muna nan idanunmu suna gani?"

"Wannan idon naki ai ya kusa rubewa,don inda kina gani sosai da a yanxun kinga wani abu da ni kadai nake hangowa" ya furta maganar yana kallon wani guri daban. Ba tare da Bibi din ta waiwayo ba tace

"Kaji dashi ja'iri" saita jawo wani mazubi ta miqawa sultana,wanda ba komai ciki sai kayan ciye ciye da tasan tafiso.

Cikin wata irin sassanyan nutsuwa ya maida wayar tashi me bango biyu ya manneta guri guda ya rufeta. Qirjinsa da zuciyarsa tana masa wani irin nauyi,da gaske goumar yakeyi bazai taba ganin yaran ba?,da gaske yake,yau din rana ce da zata iya sake nesantashi da damar sake ganin kowa da komai da ya shefeshi ko ahalinsa.

Yayi kwadayi qwarai wajen sakasu a idanunsa,yaso ya samu wannan damar koda zata kasance dama ta qarshe a garesa,tunda bai san yaushe ba?,baisan sai wanne lokaci ba.

Wannan babbar dama ce a gareshi da muddin ta gushe masa baisan sai yaushe zai sake samun wata damar makamanciyarta ba,zaiyi komai zaije zai kuma aiwatar dukka domin sa,domin ahalinsa.

A hankali ya isa dab da motar da mutumin da idan baka matso kusa dashi qwarai ba zaka tsammaci mutum mutumi ne. Yana isowar ya sanya hannu ya bude masa bayan motar,ya zura gangar jikinsa cikin wata irin kasala da galabaita tamkar wanda yayi watanni yana aikin kauda duwatsu ba tare da ya huta ba. Wata wawiyar ajiyar zuciya ta subuce masa,ya lumshe kyawawan idanunsa yana jin kamar ajiyar zuciyar zata fita ne tare da zuciyar dake qirjinsa,ya maida bayansa jikin kujerar yayi relax yana jin yadda zuciyarsa ke tsananta bugawa sanda motar ke gangarawa tana barin wajen.

Har ta rako su aba bakin mota,suka kuma fidda komai da komai da suka kawo mata cikin zuciyarta bata kasa juya batun box dinnan ba,daga ina yake?, itace tambayar da taketa nacin nanatawa.

Tana nan tsaye har suka kammala shiga motar. Ama ya sauke glass din bangarenta ta miqa ma sultana

Please Login or Register in order to submit comment