Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin ˜awayenta da duk suka bi shi da ido yuuu tayi tambayar.
"Ryan Khamis kike ji da gani, sojan da ko a cikin sojoji ake ji dashi, likitan da ko a cikin likitoci babu kamarsa... Ga sanyi ga zafi, ganin dariyar shi ko murmushinshi sai ka yanki tikiti"
"Wow shi ne Surgeon General Ryan Khamis? Da gaske don Allah? Dama yana zuwa gidanku haka a bati?"
Sadiqa ta saki murmushi
"Abokin yayana ne, yana zuwa sossai ma musamman idan suka samu saukin aiki saleem na gida don ba'a raba su, mahaifiyarshi ma na zuwa har gidan nan, shine dai Ryan Khamis"
No 1 matashi ne da ake ji dashi mata suke rububinshi don duk inda ya shiga akwai masu kyasawa amma fa shi duk basa gabanshi, yana flatforms sai dai babu wanda ya san handle nashi don akwai handles dayawa da sunayenshi na ™arya ana yaudarar 'yan mata, shi dai kam kaman dutse yake mace bayan mahaifiyarshi duk a maza ³an uwanshi ya Wauke su.

Da zancen shi suka shiga parlor nan aka baje ana cigaba da hiranshi kala kala da kyar suka saki suka kama wata.

Shi kam Rayyan yana tada motar shi ya danna ™iran Salim
"Don iskanci ko godiya ba za ka min ba ko?"
"Afuwan Ryan ka san ina gani printing kawai nayi na tafi presenting don ana jirana, yanzu kenan fitowa ta ko wayan ban fitar ba na ji ™iran ka"
Driving yake slowly duk zantukan Salim Win bai tanka ba sai ya daka tsalle ya kama wani zancen da ya kasa bari a ranshi sai yake jin kaman shima Allah zai kamashi da laifin wulakanta dan Adam tunda ya gani bai yi magana ba

"I saw someone familiar kaman na san fuskan but i cant recall"
Salim ya Wan tafi nazari kan ya ce
"A gidan mu kuma?"
Kai Ryan ya gyaWa sai kuma ya tuna voice call ne suke yi a hankali yace
"Yeah, choculate tall young lady haka"
"Afeefah ka gani?"
Salim yayi saurin katse shi, a ranshi ya maimaita sunan 'Afeefah' ba tare da yayi magana ba, Salim ya cigaba da magana

"Ka santa mana Rayyan, yarinyar da ka ceta wacce ta taSa shan poison a Anchau?"
Sai lokacin ya tuna inda ya san fuskar but Meyasa take aikatau gidan su salim? Ina iyayenta da family Winta? Kaman salim ya shiga Ranshi wai aka ce sanin hali ya fi sanin kama bai wuce magana ne a bakinshi ya kasa fitarwa ba don haka ya shiga bashi labarin yadda ya mayar da ita da irin wulakancin da suka sha yadda ta bashi labarinta daga farko har karshe sai da ya gama tsaf Ryan dake parking tsakar gidansu ya ce
"Hmmm"
Ya ™arasa yana dan taSe jajazir Win laSSanshi ba tare da ya ce komai ba bayan nan, har salim ya zaci ya katse kiran sai ya ji Ryan Win ya watsa mishi tambayar
"Then taimakonta kenan ka yi to be lowly house help?"
"No! No!! Wallahi ba hakan bane a raina Rayyan na rasa yadda zan yi ne, mommy ta katange min duk wata ™ofa da zan iya inganta rayuwarta, abin is hurting me badly... Ka kuwa san akwai Allah ya isa a kaina muddin na yi magana da ita na fatar baki na sama da minti Waya?"
Šan zare shanyayyun idanunshi Rayyan yayi
"Wow! Why?"

"Saboda kawai sun yarda da champin mutane da ™agen da ake yi mata" nan ya shiga bashi labarin gumurzun da suka sha da mommy a kanta kan ma aka barta a house help Win.
Rayyan ya Wan lumshe idanu ya buWe a ranshi mamakin mutane yake yi, Sai ji salim yayi yana cewa

"Idan bata kashe ku ba ku ai kun Wauki hanyar kasheta!"
Yana kai nan ya yanke wayar don ya gaji da magana, Salle murfin motar yayi ya nufi cikin gidan cikin natsuwa da takunshi na ™asaita haWe da izza.

Kasake salim yayi rike da wayan a hannu yana juyawa, jikinshi ne ke bashi ba haka kawai Rayyan yayi maganar Afeefah ba, ya kuma san a yanzu ko ya sake kiranshi ba lallai ya bi ta kan zancen Afeefah ba kuma bare yayi mishi bayanin me yake nufi da za su kasheta? Hankalinshi ne ya ji yana neman tashi. Allah ya sani daga lokacin da tausayinta ya yi tsanani a ranshi ya juye ya zama mishi so ba tare da ya farga ba, har ranshi sonta yake kuma so yake ya aureta saboda ™aunar da yake mata not out of pity, ko da ya ajiye ta kaman yadda mommy ta umurta yayi iya kokarinshi wurin ganin ya manta da rayuwarta ya bar wa mommy Win sai dai hakan ya gagara mishi dole ta sa ya waiwayeta ya dawo ya kawo mata waya don ya dinga jin lafiyarta da bukatun ta, layinta ya lalubo ya zubawa idanu sama da mintuna uku kan ya danna mata ™ira sai da ya jera sama da 10missed calls bata Waga ba sai hankalinshi ya fi na da tashi ya tura mata text message sama da biyar ba reply.

A lokacin tana ™o™arin tattara kwanukan da ta gama wankewa ta kai bakin kitchen, jikinta babu inda ba ya rawa har hakwaranta na haWuwa, bayan ta ajiye ta koma inda ta tashi ta Wauki wayan da karatun ma yau bata samu ta iya kunnawa ba ta nufi Wakin tana tafiya da kyar, hijaban kawai ta zare ta zubar a wurin ta shige bargo tana hawayen tausayin kanta, jin kaman vibration na wayan nata ya sa ko ido bata buWe ba tayi picking tare da ma™alawa a kunnenta, Sheshekarta ne ya fara shiga mishi kunne yaji wani abu ya sauka mishi har cikin zuciyarshi hakan ya rikita masa lissafin kwakwalwa...

"Afeefah menene? Me ya sameki?"
Shiru sai kuka da itama jin muryarshi ya sa ta ™ara karfin kukan, kaman shi ma zai fashe da kukan cikin sanyi ya shiga cewa
"Don Allah ki yi min magana Afeefah, hankalina tashi yake da kukan nan naki talk to me please, menene?"
Sau™e wayan yayi ya kalli time saura seconds goma
"Help me Afeefah ko ta text ne ki rubuta min Meke damun ki? Kar ki yi kisan kai ki taimaka"
Yana kai nan ya sau™e wayan ya kashe tare da jingina kanshi jikin motarshi, ji yake kaman yayi tsuntsuwa ya ganshi Kaduna sautin Muryar kukanta ke ta amsa kuwwa cikin kanshi...



=ؤİGureenjoh=ؤİ

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*014*

Shigowar sa™o wayanshi ne ya sa da wani irin hanzari ya mi™e daga jikin motar yana duba wa.

"Ba ni da lafiya"
Abin da kawai ta iya rubutawa kenan, sai ya ji hankalinshi ya fi na baya tashi don bai san wa zai kira ya taimaka mata ba, idan ma ya ™ira su Samha ya san abin ba zai yi kyau ba mommy kuma za ta iya Waga hankali a kan ya aka yi ya san bata da lafiya yana Maiduguri tana Kaduna?

Wani tunani ne ya faWo mishi, nan ya shiga neman Layin wani friend dinshi da yake nan capital hospital Kaduna Win a kan ya taimake shi da Layin Dr. Sulaiman, cikin mintuna biyu sai ga Layin a take ya shiga ™iran Layin ringing uku aka Waga "Dr Cap. Saleem ne don Allah wani taimako ne nake nema daga gareka please in ba damuwa"
Ya faWa bayan sallama da gaisuwa, Nan ya yi ta mishi godiya bayan sun gama disussing, ko gida bai iya ya je ba yana zaune ne kawai cikin motar shi cike da tsumayin sake ganin ™iran Sulaiman.

A chan Kaduna kuwa sallamar da ake ta doka wa ne ya sa sameera Mi™ewa ta nufi ™ofan, Sadiqa suna dining da ˜awayenta ana cin abinci ana hira, mommy ke karyawa a tsakiyar parlorn, Samha na wani research a system Winta hakan shine ma ya tilastawa sameera da ke danna waya Mi™ewa tana mitar irin uban Sallamar da ake tayi, tana bude kofan ta yi niyyar masifa ne sai idanunta suka sau™a kan Dr. Sulaiman da ke jingine Wan nesa kaWan da jikin motar shi, daga ganinshi ka san responsible matashi ne da yake kan ganiyar samartakarsa daga yanayi shiga da kuma tsarin motar shi zaka san ko shi ba mai kuWi bane daga gidan kuWin ya fito, Baaba jummai ce dake doka Sallamar ta katse ta "Har na fara tunanin babu mutane ne gidan 'yan nan ashe kuna ciki"
Ta Wan harareta a fakaice "eh muna nan, lafiya kam?"
Ta ™arasa tana sake kallon Dr. Sulaiman da har yanzu hankalinshi ke kan wayanshi.

"Wanchan likitan Afeefah ne mun zo duba ta da jiki"
Ta haWe fuska kan tace
"Ina zuwa"
Ciki ta koma kafin mommy ta tambayi waye ta shiga ce mata
"Mommy wai sun zo duba wanchan Mayyar da yaya salim ya kawo wai likitan ta"
Šan shiru mommy tayi tana tunanin Allah ya sa ba salim bane ya aiko su, sai kuma ta tuna ai bai ma san halin da take ciki ba, kila ma ya zuwa yanzu ya mance da ita ko ma bai mance da ita ba ta san ba zai taSa saSawa umarnin ta ba itama kuma hankalinta ya fi kwanciya a yadda yayi uwar watsi da rayuwar yarinyar yake kuma mu'amala da ita da ™annenshi lafiya ™alau.

"Tura Talatuwa ta kai su, su suka sani"
Ta Wan zauna kaWan kan ta mi™e ta nufi Wakin Talatuwa ta tura ta, Baaba jummai har ta gaji da tsayuwa sai ga Talatuwa, suka gaisa kan tace su tafi Wakin Afeefar don yadda ta gantan nan ta tabbatar ba za ta iya fitowa ba, Dr. Sulaiman Baaba ta yiwa magana ya bi bayansu har Wakin da Afeefar take su biyu ya bari suka fara shiga, Baaba jummai na ta sallalamin yadda ta gantan kan ta fito ta kira Sulaiman cikin sauri
"Alhaji ™arami zo ka ga yarinyar nan jiki babu daaWi sam"
Ita kaman uwa take wurinsu don gabanta aka haife shi har ya girma tana gidan su, kuma shine babba a yadda ya Wauke ta kaman uwa haka ™annenshi suka tashi suka gani su ma kuma suka yi following footsteps Win shi a girmama ta, shiga dakin yayi ya isa gabanta ya du™a.

"Afeefah"
Ta amsa da "uhmm" ba tare da ta buWe idanunta ba.
"Menene yake miki ciwo?"
Ta Nuna mishi kanta da kaman zai tsage.
"Akwai amai?"
Ta girgiza kai.
"Jiri fa?"
Ta gyaWa kai.
"Mura fa da tari?"
Nan ma ta gyaWa kai, plate na abincinta na safen da ke rufe a gefe ya buWe ko spoon Waya bata yi ba.
Ledojin da ya shigo dasu a hannunshi ya shiga buWewa babu bukatar zuwa asibiti drip ya haWa ya Waura mata ya haWa allurai yayi wasu a jikin canular wasu kuma jikin ruwan, ya dubi Talatuwa
"Kin san magungunan da suka shafi na mura da zazzabi da sa bacci, bare ma jininta ya yi ™asa sossai tana Wan bu™atar hutu na kwana biyu ba tare da ta yi hulda da ruwa ko abu mai sanyi ba"

"Toh fa, ranka ya daWe ni ma 'yar aiki ce kamar ta ba ni da ikon bata hutu da dai Hajiya da kanta ka yi wa bayanin da sai ya fi"
Ita dai Baaba jummai ta zabga tagumi tana kallon Afeefah dake bacci ji take kaman ta yi mata kuka ashe itama aikatau take yi gidan su Saleem Win? Muryar Sulaiman ne ya katse ta yana cewa Talatuwa
"ko za ki kai ni wurin hajiyar?"

Duk da basu yi haka da Saleem ba amma ba zai iya kau da ido a kan yarinyar ba she's too young and fragile kaman she's having a lot a cikin zuciyarta.
Fitowa suka yi Baaba dai kaman ta tsaya haka take ji Don Allah ya saka mata ™auna da tausayin Afeefah kaman jikar ta.
Talatuwa ta du™a gaban mommy bayan ta bar su a waje "Hajiya da ma wai likitan ne yake son gani ki".
Kan mommy ta yi magana ma sameera tayi saurin cewa
"Ki ce ya shigo, mommy bari na ba ki mayafi"
Samha ta Wago ta kalleta, mommyn bata ce komai ba har sameerah ta kawo mata mayafin daidai Sulaiman ya yi sallama ya shigo.

Kamshinshi ne ya cika parlorn duk yadda mommy ta so ta kame nagartarshi da kwarjininshi ya sa ta shiga mishi sannu da zuwa a dole, gaisheta ya shiga yi cikin girmamawa bayan sun gama Sameerah ta shiga gaishe shi, ya amsa da murmushi saman fuskanshi dole Samha itama ta gaishe shi itama ya amsa mata kan ya dubi mommy
"Da ma akan patient Wi ta Afeefah na nemi ganin ki Hajiya, na zo duba jikinta don ganin lokacin komawarta checkup ya yi ban ganta ba sai na samu ashe tana kwance rip da zazzabi mura da kuma low BP da ya addabe ta"

Mommyn ta yi kaman bata san bata da lafiya ba tace
"Asshaa ka ga aikin rashin wayaun Afeefar ko? Babu fa wanda ta sanar wa bata da lafiya, mutum kullum a ma™ale a Waki ya ba za'a yi zazzabi ya dame shi ba? Allah dai ya kyauta"
Sulaiman ya Wan murmusa don wannan ba hujja bace a gareshi idan kai ka kula da mutum ba lafiya ba sai ka jira ya gaya maka ba, haka kuma idan baka ji mutum ba ana dai zaune tare kai ke da alhakin le™a wa ka ji shin yana lafiya?

"Ai duk alamun rashin lafiyar ne Hajiya, a likitance duk wadda ba ya son interracting da kowa ya fi gane kaWaici da rashin magana yana shiga ™uncin ko damuwa duk akwai alamar tambaya kanshi, Don Allah a taya mu kula da ita idan tana samun kulawa in No time za ta ji sau™i ta komawa aikinta in Shaa Allah"
Sameera ta riga mommy magana
"In shaa Allahu Dr. Za mu yi duk yadda ka ce Allah ya bata lafiya"
Yayi mata murmushi kan ya amsa da Ameen itama dai fuskar nan cike da fara'a take ta kallonshi.
Mommy ta ce
"Ba na son ka faWawa Salim, ka ga yana wurin aiki kar ya zaci ba ma saka ido ne a kanta duk hankalinshi ya tashi, bills Win ka dinga turomin zan ke covering"
Ya gyaWa kai kawai yana kokarin Mi™ewa Sameera tace
"Ko ruwa baka tsaya ka sha ba?"
Ya ce
"No na gode, ai daga gida na fito"
Daga an suka fice suka bar su.
Wayanshi ya zare bayan ya yiwa motar tashi key ya Wan zubawa Layin salim ido yana nazarin abin da ke faruwa, Salim ya ce kar mamanshi ta san shi ya turo su, mamansu ta ce kar salim ya san Afeefah bata da lafiya to me kenan? Šan shrugging Kafada yayi kan ya danna ™iran salim yana ficewa daga harabar gidan, kaman jira ko ringing na farko bai yi ba salim ya Waga
"Ya ya jikin nata Dr.? Is it worst? Sai an tafi hoapital ko?"
"Calm down Captain jikin da sau™i"
Nan ya shiga koro mishi bayanin yadda suka yi da mommyn. Numfashi ya sau™e bai wani ji damuwarshi ya ragu ba don ya san da matu™ar wuya su bi ta kanta, ro™on Sulaiman yayi da akan ya dinga zuwa yana duba masa ita kaman yadda yayi alkawari.
Yana dan murmushi yace
"ba ka da matsala in shaa Allahu"
"Thank you so very much Doctor"
"Šo not mention"
Daga nan suka ajiye wayar.

"Oh ashe wannan baiwar Allahn aiki take gidan su salim Win?"
Baaba tayi maganan da alama dai har yanzu tana jimamin yadda suka tafi suka bar Afeefah Win.
"Ni ma sai yau nake fahimtar hakan Baaba, kaman kuma mutanen gidan ba su Wauki ma'aikatan su da muhimmanci ba"
Ta Wan juya kai cikin manyanta tace
"ko kuma ita Afeefar ce ba su Wauke ta mutum ba ba"
Ajiyar zuciya ya sau™e daga nan bai sake magana ba itama haka har suka isa gida, ta sauka kenan yana shirin ™arasar da motan parking space ta juyo ta kira shi
"Alhj ™arami Don Allah idan za ka koma da dare ko ban bi ka ba zan baka kunun gyaWa ka kai mata kila ta iya shan shi"
Ya amsa da
"Toh Baaba Allah ya kaimu dare Win"
Ya ™arasa da motan yayi parking kan ya nufi cikin gidan shi ma don bashi da aiki da safen sai dare za shi asibitin ya kwana, Salim ne ya fitar dashi dole.

Da misalin ™arfe bakwai na dare ya fito a shirye tsaf cikin kananun kaya da suka amshi kalarshi na ba™i, skin Win shi da yake kalkalewa tamkar mace sai shining yake don shi mutum ne mai tsananin tsafta, hannun shi rike da ninkakken labcoat Win shi, mahaifiyarshi Hajiya Amina da ke zaune cikin kujera ta Waga kai ta kalleshi
"An fito kenan bokan Turai?"
Yayi murmushi yana furta
"Eh umma zan fara bi gidan su saleem akwai patient da zan duba kan na wuce asibitin"
"A'ah ko dai wacce Baaba jummai ke ta jajenta tun safe?"
"Ita fa Umma da safe mun fita kina bacci, ko da na dawo ban le™o ba ashe Baaba kam tayi ta baki labarin Afeefah"
Tana murmushi tace
"Ai ina ga zuwa yanzu kowa ya san labarinta a gidan nan, Allah ubangiji ya bata lafiya. Sai ka le™a kitchen ta yi mata kunu da ferfesu ka karSa ka tafi mata dashi"
Yayi murmushi kan ya amsa yana nufan kitchen Win baabar tana side Win su bai neme ta bane saboda ba gida zai dawo ba daga chan asibiti zai wuce shiyasa ma bai ba kanshi wahalar neman ta ba don sai yayi mata dogon bayani da kyar ta fahimce shi, kwando ne mai kyau da tsari ta shirya mata komai ciki, ya dauka kawai ya fito yana yi wa Ummarshi sallama take sanar mishi Abban su yace ta sanar mishi lallai lallai yana son ganinshi da safe saboda kullum a saSani suke.

Ko da ya isa gidan su saleem a mota ya cigaba da zama yana tunanin yadda zai nemi iso don bai ga gilmawan kowa ba, sai time yake dubawa ganin zai iya makara ya sa ya sauka ya nufi mudi dake zaune bakin gate da iliya.

"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Yayi musu sallamar yana sake mi™a mishi hannu duk da sun gaisa Shigowar shi
"Don Allah ku dan yi ha™uri zan shiga lokacin aikin ku, Afeefah nake son gani ko za ka min iso?"
Shiru suka yi cikin tunanin wacece ma Afeefah a gidan, a tare suka tuna ta sai suka kalli juna suna zazzaro ido, mudi ya ce
"A'a malam sai dai ko in nema maka Talatuwa ta maka iso amma mu kam magana ma da wacce ka ambata ya haramta tsakanin mu har Abada"
Ya ™arasa cıÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹Œ‘’“”•–—˜™š›œŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏĞÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜİŞßàáâãäåæçèéêëìíîïğñòóôõö÷øùúûüışÿikin yanayin jimami da tabbatarwa iliya ma na gyaWa kai tabbacin hakan ne.

"Magana ya taSa haramtuwa tsakanin musulmi da musulmi kuwa Malam mai gadi?"
Yayi maganan yana Wan dariyar yadda suke reacting.
"Kai dai in ana sallah ba'a magana"
Iliya ya faWa, tuni mudi ya nufi ciki ta baya ya bi ya tsaya daga kofan mashigan kitchen Win
"Talatuwa akwai wadda ke neman iso wurin yarinyar nan mai wanke-wanke zo ki ji da shi"

Sameera da ke shigowa kitchen Win ta Wan yi jimmm kan tace
"Talatuwa ci gaba da aikin bari na je"
Da kallo Talatuwa ta bi ta har ta Sace, sai da ta koma Waki ta dubi kanta ta kuma ™ara turare kan ta fito ta nufi waje, Sulaiman na ta bugar cikinsu don ya ji dalilin rashin mata magana kuma wai na har abada dole ya sa suka shiga bashi labarin abin da saleem yayi musu, Sossai Sulaiman ke dariya... Tahowar Sameera ta wani zuba mishi idanu tana tsintar kanta da murmushi.

Kallon farko da ta mishi ya tafi da imaninta, ya shiga ranta fiye da yadda tarin samarin da suke bibiyar ta, a yanzu da ta ci karo da shi yana dariyar nan kuma sai taji tana narkewa, zuciyarta na wani irin macewa a kanshi, ganinta ya sa ya tsagaita dariyar shi, ta shiga gaishe shi ya amsa yana murmushi

"Whats so funny haka Dr.?"

"Ki bari kawai ni da su mudi ne, zan iya shiga?"
Ta Wan yi farrr
"Sauri kake haka?"
Ya Wan duba time a agogon dake Waure bisa tsintsiyar hannun shi
"Kusan hakan don kaman na shiga lokacin aikina"
Ya ™arasa yana nufar mota, ta bishi suka jera.
"Ai ma kuna ™o™ari SLT nake karantawa amma ji nake kaman na gudu bare likitance da aikinshi"
Ya Wan yi dariya bai ce komai ba, ta tsaya tana kallonshi har ya buWe booth ya Wauki kyakyawar basjet da Baaba jummai ta shirya mata kunu da ferfesu Win kayan ciki da suka nuna suka yi tuSus cike da kayan kamshi, ganin basket Win sai da ya ba Sameera haushi amma ta danne, ta sake ganin ™atuwar leda sai zuciyarta ya shiga tambayarta Anya ala™ar nan na likita da marar lafiya ne ko akwai abin da bata sani ba?

Amma me Afeefah take dashi da guy irin Sulaiman zai so ta? Dukda haka zuciyarta bai huta da bugun tara-tara ba, kar dai ta faWa soyayyar abin da ba za ta samu ba, ji tayi bata da ™warin gwiwar bin shi don tabbas matukar ta bishi ta fahimci akwai alaqa tsakaninsu zuciyarta zai iya bugawa ko ta sha™e yarinyar har lahira, ba za ta iya bin shi ba sam bata da ™warin gwiwar. Ta manta cewa kwata-kwata ma yau ne ta fara ganinshi har da za™ewa haka, wayar ™arya ta ™ir™ira ya Wan kalleta

"Ka je Dr zan sameka"
Tana kai nan ta juya tana cigaba da magana a ™arya, shi kam bai damu ba ya nufi Wakin Afeefah Win a kan varender ya tsaya yayi knocking, a jiran da ya Wan yi ya fahimci maza ne cikin ainihin Boys quaters Win don ga wani murya na waya, kuma shine aka ajiye mace tare da su? Sam tsarin bai mishi ba... Anan ne kuma ya shiga tuna hirar su iliya sai ya fahimci saleem yayi hakan ne don ya bata kariya Dukda haka shi abin bai burge shi ba, ya juya ya kalli main building na gidan, yanzu duk girman gidan nan a ce babu inda za'a ajiye Afeefah sai cikin maza?

Kimtatar lokaci yayi daga knocking da sallamar shi zuwa yanzu kan ya tura kofan ya shiga da wani sallama again, ta lallaSa ta tashi zaune ta sanya hijabi tana jingine da gini ™afafunta na cikin bargo
"Sannu da zuwa Dr"
Ta faWa cikin sassanyar muryarta da ya ™ara ™asa sossai.
"Sannu Afeefah ya jikin dai?"
Ya faWa yana ajiye abubuwan hannunshi
"Da sau™i"
Plate na safen nan ya ™ara gani a yadda aka ajiye da safe, wani tunani ne ya darsu a ranshi hakan ya sa ya mi™a hannu ya buWe ga mamakin shi abincin nan na safe ne still zaune cikin plate Win, bata ci ba don ko da Talatuwa ta shigo ta duba ta ta Wauka ta tafi da shi don ta kawo mata wani mommy ta koro ta akan ba za su yi almubazzaranci ba sai dai ta cinye shi kan a saka mata wani.

"Afeefah tun safe baki ci komai ba?"
Da Wan tausayi haWe da zafi yayi maganan ranshi na sosuwa kwarai.
Ta Yi shiru
"Ina za ki samu ™arfin jiki idan ba kya cin komai? Ai ko mai azumi zuwa yanzu dai ya sha ruwa"
Tsam ya mi™e ya nufi bayin ta, ta lumshe ido bayan ya shige chan sai gashi ya fito da bowl haWe da brush ya bata, ruwan goran da ya shigo dasu ya buWe bakin Waya ya dinga zuba mata tana wanke bakin sai da ta gama tsaf ya mayar yaje ya zubar, ya dawo ya tsuguna ya saka mata peppersoup Win da kunun ya ajiye mata a kan kafafunta Wayar hannunta na hagu ya mi™a mata kofin kunun ta karSa ta ri™e idanunta na kallon cikin bowl na psoup Win, sai turiri da kamshi yake fitarwa.

"Oya ci yanzun nan, ko in baki da kaina?"
Ta girgiza kai ta sanya hannu ta dauki spoon Win ta shiga sha, da kaWan da kaWan yana matsa mata har ta sha dayawa ta sha kunun kuwa sossai, fruits da ya sayo mata ya kara mata da shi. Ta marairaice
"Zan yi amai fa idan na ci, cikina ya cika"

"kin manta kina tare da likita? Ai aman ma tsorona yake ji Harara Waya tak zan mishi ya koma"
Ta saki murmushi karo na farko da har hakwaranta suka bayyana, ta sanya hannu ta karSi ayaban da ya bare mata.
Magungunan ta ya duba ya haWa Allura yayi mata a canular tana ta wash wash ya ce
"Wato Wazu ma saboda bakya hayyacinki ne kika manta da raki

Please Login or Register in order to submit comment